Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 88

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 88

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 88: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 88. ****** ********* ****** Ya sauka lafiya don yana isa Abuja da…

2,236 words

****** ********* ****** Ya sauka lafiya don yana isa Abuja da safe suka daga sai Mexico gurin taron su. Yakira wayana kafin su tafi tana kashe ina cikin class ban samu magana da shi ba. Yinin daya da sadauki yayi batare da Fatima haka yayi shi a cikin tunanen ta. Sai a lokacin yake sanin cewa akwai wani babbban alamari a zaman ta kusa dashi ji yake tankar itace jagoran duk wani farin cikin rayuwan shi a halin yanzu. Bai samu lokacin kiran ta ba,sai da ya dawo masaukin shi a lokacin dare yayi a can. Yana kwance dakin shi saman gado tunane Fatima kawai ke cikin zuciyar shi har zuwa wanan lokacin. A nan ya fara tina abubuwan da sukai ta faruwa a tsakanin su abaya. Irin yadda yake yawan mata tsanani da hattaran ta cikin gidan su yana daukan ta a matsayin itace mai mashi gulma a gurin maji. Sai yanzun ne yake gane cewa bata fadawa maji komai a gamay dashi sai dai nata kokarin da takeyi gurin ganin cewa ta saka mai ido ya daina shaye shayen daya ke yi kawai. Wani irin bacin rai ne yaji sai yanzu yake gane cewa ashe son shi takeyi da,alheri take hakan gare shi. Yana jin ciwon irin abin da yai ta aikatawa yar mutane a baya a bisa gaskiyan ta. Haka yasa yamike ya fara dan zagaye dakin a hankali yana zargin kanshi da aikata abinda ba daidai ba akan Fatima din. Lalai dole ne ya gyara tsakanin shi da Fatima yadda zata fahince shi ta yadda zata daina mai kallon mugun da take mai koda yaushe. Yace in har bai gyara tsajanin su ba baiyi wa kan su adalci ba don haka zasu dinga zama suna samun matsala a tsakanin su ko yaushe. Gurin tagan dakin ya koma tare da budewa yana shakan fresh ai dake fitowa daga window. Ya daga wayan shi da ke a hannun shi ya kira nomban Fatima bugon farko da,wayan yayi sai da yaji wani iri a zuciyan shi . Ina hanya zan dawo gida naji wayana na ringing, hakali na dauka na duba yaya sadauki ne a layin. A hankali cikin wani murya bayan nayi receive din call din nace hello yaya. Ya dan rikice da jin muryana yana cewa Fatima kina inane haka naji dan hayaniya. Nan dan ajiyan zuciya sai nace ina hanyane yaya nafito school zan koma gida ne yanzu. Sai nace kana lafiya yaya yaya gajiyan hanya da taro sai da yai wani lunshe idon shi ya amsa da taro Alhamdullahi Fatima mun fara yau din nan. Allah ya bada sa,a nace mashi ya amsa da amin fatima. Yace kiyi tuki a hankali don nasan yanzu titi ya cika da motoci yamma yayi nace mai insha Allahu. Yace nakiraki ne naji muryan ki don na kira ki da safe wayan ki baya shiga. Nace ina class alokacin na rufe wayana ne ya sake cewa gashi na kasa barci sai naji muryan yar kauyen matata yaya zanyi da raina dole na kira ki naji ki don mu nan yanzu daryayi sosai . Nace shine kaki bari da safe ka kirani yace abinda ya dace ke nan nayi don na kasa samun natsuwa rashin jinki . Kwata kwata rashin jinki a tare dani ya hanani sukuni Fatima yaya zanyi dole ne na kiraki ai. Take zuciyana ya narke sai naji kamar na shige cikin wayan na isa inda yake din naga kyakyawan suran mijina da nai missing. Yaci gaba da cewa Fatima ina kewan bakar maganan ki ina kewan wanan fadan namu da muka kwana bamuyi shi ba. Murmushi nayi yace kin dauka ina wasa ne ko sai idan kinga nadawo maki don kawai muyi shi zaki gane. Nace a hankali ina murmushi haba yaya don fada kawai zaka dawo na rokeka kayi hamkuri ka zauna har kagama abi da yakai ka. Har nakai gida muna waya dashi inda na ke ce mai na iso gida sai da zanyi sallah mukai sallama dashi yakashe wayan. Wayan dake hannu na dan kalla na ce ikon Allah yau kuma mai ya samu yaya haka ne ya sauya min gaba daya.

****** ********* ****** Yau kwana yaya uku da,tafiya amma Amira shiru batazo ba tun ina saka rai da zuwan ta har nagaji na,fara fitar da rai ga zuwan ta gidan. Yaya da yakirani ya tambaye ni Amira bata zo bane nake ce mai bata iso ba tukun. Ranan Na dawo gida da yamma a gajiye neke a lokacin sai dai ina shigowa get din gidan na hango motan anty Amira a kofan gidan namu. Nashigo gidan da yar fara,a na a fuskana don ganin ta tazo tana zaune saman kujera tayi daidai da ita sai waya take yi abin ta. A sanyaye nai sallama ta dago kai ta kalleni a dan wullakace nace Anty sannu da zuwa. Hannu kawai ta daga min ba tare da ta amsa min ba taci gaba da wayan ta da takeyi. Ido nabi ga yadda ta kaca kaca da falon da yake a gyara tas kafin na wuce da safe. Ganun bata da niyan gama waya yasani na nufi daki na don rage kayan dake ajikina a lokacin. Sai d nai wanka nai sallah nafito falon har lokacin tana zaune a inda na samay ta da farko. Ina batun na zauna take cewa ke ina key din daki na yake na bude naga a rufe yake. Nace au yana gurina anty bari na dauko maki taja uban tsuki tana fadin don isa da sa.un guri zaki kulle ma mutane daki wai ke ga matar gida ko. Nace fita zanyi ai shiyasa na kulle ko ina na gidan kuma ma ban san kina tafe ba yau ai. Dalla Bintu ki dauko min key ni bani son yawan zuba haka kinji. Kallon mamaki nake mata nace yau kuma nice mai zuba anty ki dai gyara maganan ki. Au to abin har yakai kuma zaki min rashin kunyane Bintu ? Wanan ba halina bane anty kinfikowa kuma sanin hakan don ban tabayiwa kowa rashin kunya ba. Kai ta gyada tare da kutawa ta dauki jakar ta bayan na bata key din ta wuce zuwa ciki ran ta a bace. Kitchen dama a rufe yake na dauki abincin dana aje zanci idan na dawo tunda safe na shige daki da abina nace can nafito nasawa gidan key na shige abina na kwanta. Ban fito ba sai da safe na hada breakfast na bar gidan ko fitowa batayi ba tana dakin ta kwance. Bayan fita data gaji da barcin ta tafito ta zauna taci abincin da ta samu na aje mata. Inda taci anan tabar min kayan sai dana dawo na kwashe su na wanke na gyara gurin. Ban fito na girka na dare ba don a gajiye nake nashige kawai abina nai kwanciya na kawai. Amira tafito tasamu babu komai saman tabld din tai mamakin hakan ta nufi dakina lokacin ina bathroom ban maji tana buga kofan ba har tagaji ta,wuce. Tunda safe ina kitchen sai gata ta shigo daga kofa taja ta tsaya tace ke Bintu wai may kike daukan kanki ne halan. Nace namay kuma anty? May ya hana jiya ki girka muna abinci da kika dawo ki ka barni da yunwa na kwana. Nace kiyi hakkuri anty wallahi na gajine jiya sosai kuma ga yamma yayi dana dawo. Eyye samun guri ke nan ke ashe har kinga gurin hutu ke nan to wallahi ki kama kanki da ni. Murmushi nayi kawai naci gaba da aiki har ta fara tafiya ta juyo ki girka abinci dasu salma don sunce anan zasuyi breakfast yau. Yadda tace haka nayi mata na sauri na fita yadda na dawo daga gajiya da yamma haka na samu gidan sai da raina ya baci. Ban fito ba haka nabar falon sai da safe na tashi na shiga gyaran gidan sai da nai ko ina tas har bayin falo duk sun bata shi . Sai na dora muna girkin rana ina tsaka da yine sai ga Anty tafito ta ce yau ma su salma sunce a nan zasu wuni kiyi girki dasu. Ina gama muna girkin na koma dakina na kwanta can na fara jin hayanin yan su har da yan ihun su. Nace yau kuma din nan wai may ke damun anty Amira haka tana son bata rayuwan ta. Ki fito ki gaida su salma naji muryan Amira daga sama ina kwance na dago ina kallon ta kawai. Kamar bazan fito ba sai dai na mike na fito da fara,ana a fuskana nake ce masu sannun ku da zuwa. A lalace cikin kallon banza suka amsa min banji dadin haka ba amna na dake na dan samu guri daga gefe na zauna. Sai naji dayar na cewa wai ashe musty ya auro wata gajar matace can yar kauye da ita. Ke haba inji saura tace wallahi ko kada kiso ki ganta ga gida ga komai ya hada amma ina ba matar gwadawa tsara don bakauya ce wallahi. Sai Amira tace anyi biyu ke nan muma ga.unan da irin matsalan ai a gidan mu kin san yan kauyen nan su iya bakin asiri su mallake miji. Yanzu bari ki gani kwana biyu idan an aaruce shi zakiga ya fara wani bakin rawan kafa bai jin kunyan kowa akan ta. Nagane maganan ta shagube ne amma sai na dake suna sako min magana ina jin su. Bai mata ba sai cewa tayi ke Bintu kwashe kayan nan ki girka muna indomie kubura zataci tace. Kallon mamaki nai mata may anty ta mayar danine yar aiki ko may wai ? Ina gama kwashe kayan sai dana wanke su na,shiga daki in fito sai naga wace tace wa Kubura dauke da cup din tambulan yaya da nake mashi amfani dashi tana shan drinks a cikin. Kamar na wuce sai na dawo nace anty da kun canza cups don wanan din na amdmfanin yaya ne shi. What Bintu may kike nufi lalai ma Bintu kin kai wuyan ki ya isa yanka ashe ? To baza ,a mayar ba sai kiyi abinda zakiyi don an dauki cups din yaya ko sannu mai yaya. May kike gurin yaya din ke nace mata a daure mata mana mai miji kuwa. O lalai naga alama tunda har kin fara bani ansa to baza a mayar ba din tunda daga gidan ku kikazo da shi. Nace may yai zafi haka anty harda giri da zagin gidan mu kuma haka ? An zaga ko zaki ramane ki nuna min wuyanki yai kauri yanzu. Nace bazan rama ba amma koda banzo dashi daga gidan mu ba nawane dai ke ma sai ki jira naki. Aiko sai saura sukacs iyye gorin aure kuma zaki mata Bintu don ke kin samu an maki auren hadi ko ? Nace au haka ta fada maku ashe idan yin hadi banza ne wasu suje ai masu mana mugani. Na bada amsa haka sai na juya zan wuce ji nayi an finciko ni ta baya sai kawai naji mari kyauuu. Cikin mamaki na dafe kumcina da ta mara nace anty abin har da duka kuma sai sauran na fadi kyale ta please kada ta kulla maki shiri kin san su da sheri irin matan nan. Banyi magana ba na juya kawai idona tab da hawaye na,shigd daki ina mamakin wanan irin cin zarafin da Amira tai min a gaban kawayen ta haka. Kiran yaya sadauki ne yashigo min yake kirana na dauki wayan bayan na goge fuskana. Na amsa mashi sallama da sauri naji yace Fatima may ya samay ki ko baki da lafiya ne. Na daure nace may ka gani babu komai yace please nace may ke damun ki ne wai ba komai nace mashi. Baiyarda ba sai dai kawai ya kyaleni tunda nace mai babu komai ina daga kwance nake tunane dole na dage na futar da kawaici na fara gwadawa Amira nima na iya. Bayan kaman awa daya sai gata bazaki dafa abinda nace maki kubura tana so bane ko may ? Ban bata ansa ba na kyale ta haka suka gaji da zaman su har suka bargidan. Da safe ma washe gari haka na gyara gidan tea na hada nasha na koma na kwanta abina. Can cikin barci naji takai min maka a baya da gigin barci na falka ina kallon ta. Bazaki muna abin karyawa bane yau gashi har sha daya da,wani abu na rana. Nace bazanyi ba . Bazakiyi ba fa kika s tsuki nayi na koma na kwanta abina sai ji nayi ta nufo zata kara kai min maka na dago ido waje nace kada ki soma kara tabani don zan rama. Ko dazun ma arziki kikayi a gaban kawayen kine kada ki matsayi yata na disgaki a gaban su shiyasa na barki. Yadda taga na nuna tasan za,a samu matsala sai ta juya tana fada tafice daga dakin. Tana fita wayan yaya sadauki takira tana fada mai wai na hana mata abinci taci. Yace ina ganin bata jin dadin jikin ta nd don tun jiya nake jin ta hakana. Tace shiyasa ban son zusa gidan nan wallahi sai yarinya tai batun raina maka wayon , Kashe wayan yayi yana mamakin iri wanan hali haka da ta sakd lokaci guda. Tun daga wanan rana ban kara girka komai ba koma nayi iya cikina nake girkawa naci

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

A LOKACIN MU KE,,,,

Readers Also Read