A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 17
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 17: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 17. Zufane ke ta ketowa Baba Adee Bayan jin bayanin…
3,328 words
Zufane ke ta ketowa Baba Adee Bayan jin bayanin likitocin,Shi d'an talakansa bawan Allah ina zai samu miliyan goma rana tsaka inbadai satar su zaije yayi ba shi bawata kadarar arziki ba tunani ne barkatai ke shigowa kansa awannan lokaci cikin tashin hankali da rashin madafa.
D'ai daga cikin matasan likitotan ne yakira Baba Adee A office dinsa inda yafurta"Baba kozaka iya samu na office dina yanzu inaso zamuyi magana" kai Baba Adee kawai ya iya d'aga masa cikin rashin karfin jiki domin shi kansa yashaida kafafunsa ne suka kaisa office din inda yake biye bayan matashin likitan.
Kujera yajama BAba Adee yana furta"Baba zauna ganin Baba Adee kamar baya cikin hayyacinsa.
cikin sanyin murya matashin likitan ya furta "karka damu kanka da yawa Baba Allah shi keyin komai duk bayanin da akayi maka kawai hasashe ne Amma Allah Ne mai Aiwatarwa in bai nufa zata sha wahala ba zaka ga cikin ikon Allah tayi rayuwarta batare da ko wace irin sifa ba ta alamar mental problem. Ayanzu ma Baba Adee kai kad'ai ya iya d'aga masa kamar wanda ke d'aukar karatu cikin sagewar guiwa da mik'a wuya Ga ubangiji,Bayan jin maganar ta Dr.Din Inda yaji natsuwa tashigesa.
A hankali bayan yazauna ya cigaba da maganarsa Ni suna na Dr.Yusuf Janyau ana kirana Dr jy. zan taimaka maka yadda za'a yimata aiki cikin sauk'i batare da ko sisin kuba domin na fahimci ta shin hankalin da kashiga Baba na kud'in aikin da aka lissafa maka dakuma abunda zai faru idan ba'a dau mataki da wuri ba. An gina wata Babbar asibiti ta taimakon Marassa karfi yanzu haka wayenda zasu rik'a asibitin basu cikin kasar nan suna INDIA ......
Achan suke aiki wanda nima achan nayi karatun Amma ba makaranta d'aya mukayi dasu ba inda su suka zabi aiki achan bayan gama karatun namu nikuma nazab'i kasata,duk da haka mukan d'an had'u idan taron dalibbai yatashi na nigeria ko na likitota gaba d'aya inada numban dayansu ta nigeria danshine muke shiri dashi sosai duk da dukkaninsu Abokainane.
In sha Allah da sun dawo nigeria zan kiraka in sanar dakai lokacin Anfara Aiki a asibitin,domin yanzu haka anfara daukar ma'aikata kaga da nasamu aiki achan shikenan ba matsala tunda dukkanin abunda za'a saya akwai shi a asibitin zan tsaya dayardar ubangiji domin tasamu lafiya..
Godiya Baba Adee yak'ara yi masa sosai cikin nuna farin cikinsa da wannan bayani na wannan likita,Cikin murmushi shima Dr.Aj ya furta bakomai Baba yiwa kaine.
Cikin sakin fuska Baba Adee ya furta yusuf sanya mun numbanka anan yana mai mika masa wayansa kirar tecno pop 3 murmushi dr yusuf yayi yakarb'i wayan yasaka numban wayansa sannan yayi dialing sai ga numban Baba Adee ta bayya akan wayar tasa kirar iphone 15 saving yayi da Baba,shima Bba Adee yayi saving da Dr Janyau musabaha suka kara yiwa juna sannan Baba Adee yakara yimasa godiya tare da kara saka masa Albarka..
Khady da Bba Adee yasanar mata da komai afarko ta shiga tashin hankali domin kuka tasanya cikin tausayin yar uwarta wadda ayanzu take kwance akan gadon asibiti cikin ciwo gwanin tausayi,sai daya ga tashin hankalin da tashiga yanason d'ara nasa sannan yasanar mata da dik bayanin da Dr. Janyau yayi masa,take itama ta wartsake cikin farin ciki tana mai sanya wa wannan likita albarka wanda bata sanshi ba A hankali takalli fuskar Halee da takara yin fayau kyakkyawar fuskar ta takara kyau na musammamn kasancewar yar ramar da d'anyi Allah yabaki lafiya yar uwata ta furta.......
Wasu alamomi da Dr.Yusuf yake nuna wa da kulawa a asibitin wurin jinyar Halee shizai tabbatar maka da abunda ke cikin zuciyarsa domin dukkanin Alamomin sa sun nuna son Halee yakeyi. Murna Sosai Bba Adee yayi dan ganin yaron yakasance mai mutunci shidama burinsa kenan Halee tasamu mijin Aure nagari ya aurar da ita ko tasamu salama domin zuciyarsa bata yarda da rikon Baba Asabe ba.
Kwanan su Halee shida aka basu discharge tare da magungunan dazatayi amfani dasu kafin asamu kud'in surgeryn nata.Tunda suka zo asibitin Bba Asabe bata leko ba ko aike, dangin Bba Adee da dama sunzo sunga Halee ciki harda iya da Bba mudi iyayensa da kannensa maza biyu Amma itakam Baba Asabe ko lek'e. wanda hakan bai wani damu Bba Adee ba domin ganin yadda Haleen ke samun kulawa agurin khady mai yin jinyar tata duk da iya taso abarta ta kula da ita....
nikam nace toh Allah ykyauta Yasa mufi karfin zukatan mu.Ameen
Toh hwa😂 in muku ta hausar mu ta zamfaranci,ku k'ara gyara zama fans munkusa isa inda kuke so fa Haleen mu da alama fa tayi Saurayi ko ince mijin Aure ....
Kai da alama fa mutanen india sunkusa zuwa nigeria..... yeeeeee Can't wait 💃💃💃
Me kuke tunani game da soyayyar da Halee zata fara...
[3/27, 10:05 PM] Fa'eehbg writer: https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫 In my dream I know her By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Wannan page naka ne Mahaifina⭐⭐taurarona Allah yakara maka tsawon rai Mai albarka tare da lafiya Mai inganci*🤲🤲 ------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free* 📙
EPISODE1️⃣ PAGE3️⃣9️⃣
TYPING📲📲📲
*Barkar ku da Shan ruwa fatan ansha ruwa lafiya,Allah yakarba muna ibadar mu*
*Special thanks goes to the members of A mafarki Nasanta fans group,yan Amana ta luv u Lodi Lodi*😍🤍🤍
*And Big thanks to my sincere people for the support you give me*
*Anty moon(the writer of abarmu da junanmu and mijin bahijja*❤️
*Oum Amjad(the writer of Yan biyu)*❤️
*My best readers*
*Yan Amana*
*Mode*❤️ *Zarah Ibrahim*❤️ *Siddiq Muhammad*❤️ *Halimatu bashar Auki* ❤️ *Fateema A bello*♥️ *Ayeeshat Abdullahi*❤️
Ina alfahari daku sosai irin ba adadi💯 nan
Fans💙💙💙💙💙💙💙 Ina godiya sosai da Jirana da kukayi har natsawon makonni, Wayenda suka kirani da ma wayenda basu kirani ba Ina godiya, kuyi hakuri banyi mentioned sunanku ba nayi hakan ne sbd Kar mucika page din namu da surutu Ina alfahari daku 🙏
<<<<<<<< >>>>>>>><<<>>>>>>>>>>>>
✍️✍️
B'angaren Mahir da Sumee kuwa har sun Kai gidan ummi Sojojin Dake bakin gate din nan gidan na wangale musu gate babu wata fira tsakaninsu.
Inda Abdallah yayi parking tasa motar Shima ya parker tasa,lock yasanyawa motar ganin alamar sumy fita zatayi, kallonsa tayi cikin son sanin dalilin Saka lock din,.
Tsuke fuska yak'arayi ganin irin kallon da take masa.
Bayan kamar minti uku haka ya furta.. cikin gadara saura saura inkika shiga ciki ki sakarwa Abdallah fuska yakai karshen maganar yana cire lock din.
Kallonsa take da mamaki,Ba halin tambayar dalilin maganarsa ficewa tayi dasauri tana murmushi ita kad'ai bayan wani tunani da yashigo zuciyarta,kenan Yana kishinta inko akwai kishi akwai soyayya kenan Yana Sonta farin ciki ne ya mamaye ta kamar ta daka tsalle sai dai ba hali domin tana Jin idanunsa akanta..
Dakarun Sojojin Dake compound din gidan ne suke mata sannu da zuwa tana amsa musu cikin farinciki har wasu nad'an janta da wasa..
Shigewa cikin gidan tayi da gudu sai falo ta dakata,duka ta tarar dasu atsakiyar falon har mahaifin su colonel jabir Muhammad soja ,Wanda suke Kira (dady soja ) suna yin dinner da yadawo gida bayan Yan watannin da ya dauka baya nan.
Duka d'agowa sukayi suna kallonta ganin yadda ta fado dakin fuskar ta sai blushing take Yi tare da sauke numfashi.
cin abincinsu suka cigaba dayi Dan dady soja baya wasa injisu 😆kunsan sojoji fa sakin fuska la la la la🤭in maku ta bakon balarabe✍️
💫 FA'EEHBG 💫 The first lady 🙌🙌
<<<<< > >>>>>>>>>>>>>>>>>> <<<<<
Joining dinsu tayi cikin kame kame na yadda ta fado dakin suna cigaba da cin abin cinsu.
Bayan sun gama ne tayi ma Dady soja sannu da zuwa ya amsa mata cikin sakin fuska irin tasa.
Bayan wucewarsa daki ne suka cigaba da hirarsu.
ummi ce ta lura da mahir Dake chan tsaye agefen cushion tsayinsa ya rungume hannaye ya kafe sumy da eyes wadda keta zuba fira tana bada labarin su sury kawarta Yan class nasu.
'Murmushi Ummi tayi kawai tana girgiza kanta cikin dattako da sakin fuska ta furta "Ina yini Babana "?
'Sunnar da Kansa yayi Jin gaisuwar da ummi ta masa A hankali yatako cikin Jin nauyinta ya durkusa ya gaishe ta,cikin murmushi da kulawa ta amsa masa.
Manyan food flask din da har an maidasu dining inji Yan matan ne Ummi ta d'auko d'aya tana furta"Baba na nan za,a kawo maka Abincin ne ko anan zakaci kan dinning inyi saving Dinka"
''Nakoshi''Ummi ya furta cikin Jin kunya Dan haka kawai yau yake Jin kunyarta wadda Bai San dalilinta ba.
Nikam nace ba dole ba Maheer ka kama mata "yaa🙌 surukantaka wasa ce...duk da bamu tabbatar ba😃😃
Murmushi kawai Ummi tayi bayan gama sauraren sa ganin yadda yake sauke Kai kamar k'adangare.
Sallama sukayi ma ummi suka fice daga falon Yusuf da Abdallah,mahir ne Shima ya biyo su bayan yayima sumayya kallon zamu had'u Yana ficewarsa.
A compound d'in gidan ya had'u da Abdallah da Yusuf suna Jiran fitowarsa.
Musabaha sukayi cikin karrama juna Abdallah ne ya furta "tare zamu koma fa Maheer "
'Shek'e k'e mahir ke kallon sa bayan Jin furucinsa,sai Kuma Ahankali ya ya furta
"ita motar da ka zo da ita fa"?
'Yusuf ne ya furta zan d'an je gidansu Uun Yana Dan susar keyarsa irin na shed'anar nan,dariya kawai mahir yayi Yana furta " to sai ka dawo kagayar da ita"
Shima dariyar yayi Dan yagane abunda yake nufi sallama yamusu sannna yafice daga gidan.
A mota Abdallah ne yake d'an jan Maheer da fira duk da mahir baya amsawa sosai sbd haushin sa da Bai sake Saba har yasako zan cen da yakusa tarwatsa zuciyar mahir..
"Friend nifa nagani inaso tun tuni,d'aure fuska mahir yayi,Abdallah ne yacigaba da maganarsa
"Dan haka nikam zanje insanar wa sarki kafin ruwa su cinye ni,Gaban Maheer ne yafadi Wanda har sai da steering ya so kubce masa sai Kuma yayi ta maza ya furta
"Sai ka dawo"atakaice. Cikin Kara d'aure fuska
Me Abdallah zaiyi inba dariya ba harda rike ciki domin dama yaga yadda steering yaso kufce masa ga Kuma amsar da yabasa..
'kagani ba harka hau Toni ba ita nake nufi ba,Inayah nake magana Akai Dan naga alama kazata da sumy nake Dan da alama ka zurma da yawa...
Farin ciki ne ya ziyarci mahir Mai yawa Wanda tun alokacin da yatabbar Abdallah ba yada wani feeling akan sumy sai yafara bata kulawa.
Soyayya Mai karfi ce ta barke atsakanin sumy da mahir,haka ma Abdallah da Inayah soyayyarsu suke Sha gwanin burgewa wadda har ta bayyana a idon kowa.
*INDIA*
Anty lailah da Appah sunyi farin ciki daganin kyautar da Ammar ya yiwa su Lubna fiye da tunanin Mai karatu,tun daga lokacin kusan kullum sai su Ziyad sun fita da Lubna domin su gana da Ammar.
Wata shakuwa ce tashiga tsakanin Ammar dasu Lubna,sai dai haryanzu Ammar Bai tab'a had'uwa dasu Appah ba.✍️✍️
Wassh hannu ✍️😥😥
Mu had'u anext page Muga saukar mutanen India may be agobe Nigeria zatayi manyan Baki Can't wait 💃💃💃
Masu zuwa tarbon Baki ku shirya mu Isa Airport da wuri ayi landing🛬🛬 agabanmu💃💃
Ina Kuma labarin Halee ya ya take ? 🤔 Shin Baba Asabe taciga da muguntar ta? Su waye iyayen Lubna ? Shin Suma Yan Nigeria ne dagaske?
Ina labarin MISS MALINI ??? HMMMM kwamachala kenan inji bahaushe😆
In Sha Allah duk zaku samo amsar tambayoyinku Ahankali kudai cigaba da bibiyar alkalamina ✍️✍️
Allah yajikanki da rahama kakata yaar Baba😥Allah yasa Aljannace makomarki Allah yakarbi Bakuntarki,ya yalwanta makwancinki yakuma bamu guzurin ishemuku🙏🙏
Pls like,share and comment✍️ [3/28, 12:02 AM] Fa'eehbg writer: https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫 I know her in my dream By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Allah yajikan iyayen mu🥰🥰🥰 wayenda suka Riga mu gidan gaskiya da rahama😭😭🤲* ------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free* 📙
EPISODE1️⃣ PAGE4️⃣0️⃣
TYPING📲📲📲
*NIGERIA & INDIA*
€€€€€€€€€€€❤️ €€€€€€€€€❤️ €€€€€€€❤️ €€€€€❤️ €€€❤️ €€❤️ €❤️
A yaune Mai girma sarki Ali ya alkawarta zai Kira Ammar yasanar dashi Babbar Asibitin Daya Gina masa wadda yake so su rike shida D'an uwansa Dr. Aj.
'Kwance yake Ashe Ashe akan had'add'en gadonsa Yana sharar baccinsa hankali kwance fuskar sa sai k'yalli takeyi na madarar kyawu da Hutu,Ajiya zuciyar yake sauke wa A hankali Yana sauke gajiyar da yakwaso adaren jiya na theatre n da sukayi 6-6 ya duk'unk'une cikin bargo saboda yanayin sanyin garin gashi yakure gudun A. C,Baccinsa yakeyi hankali kwance......
'Ringing din wayarsa Dake charge akan bed drower tayi k'ara cikin sauti Mai dadi,cikin baccin sa da yayi nauyi yajawo wayartasa yanayin picking call din batare da Duba wake kiransa ba.
'Sallamar Wanda baiyi tsammani bace tasanya sa fincike tattausan blanket dinsa white colour Mai taushi.
Ware manyan idanunsa yayi lumsassu masu cike da bacci akanta ,Yana Mai sauke wayan akunnensa Dan k'ara tabbatarwa..
Ganin tabbas shid'inne ga numbansa nan da code din Nigeria da Kuma yadda yayi saving din ta,sunan Yaya Dady ne ya bayyana rad'am akan akan screen din.
Mai da wayar yayi akunnensa cikin wani yanayi bayan karewa sunan kallon. Adayan b'angaren Sarki Ali ne Bayan yin Sallamar sa ba,a amsa Masha ba,yake ta Hello! Hello! Tare da furta "Mai sunan K'anena!, Yarima! Dama Haka yake kiransa da wayen nan sunayen Alokutta da Dama.
'Kwalla ce ta taru a idon Ammar na farincikin da yatsinci kansa ciki Yau shekara d'aya da wata hud'u baiji Muryar Mahaifinsa ba sai yau.
'Sassanyar Muryar Mahaifin nasa ce takara ratsa dodon kunnensa Yana Kiran sunansa Dan yasan tabbaas Yana saurarensa yasan halin kayansa sarai inda yake furta" Nurin UNNI" '' na'am ABBA ya furta cikin wani yanayi na sanyin jiki da farin cikinsa dayake kokarin boyewa da murmushiinsa na dalilin sunan da Mahaifin nasa yakirasa dashi.
Farin ciki ne ya mamaye sarki Ali,Dan ba haka yasaba Kiransa dashi ba, Yaya Dady yake kiransa Dashi,inda sunan ya samo asali. ..Afarko Yana kiransa da Yaya ne kamar yadda k'annen mahifin nasa ke Kiran sarki Alin Daga Baya sai Yak'ara da Dady Bayan yaayi wayau.wannan kenan.
*MUJE ZUWA*🚴🚴🚴🚴
Wasan yanzu ya fara....✍️✍️
A b'angaren Sarki Ali ne yaci gaba da magana Yana furta ''Fatan kana lafiya"? "Lafiya Lau Alhamdulillah Abba" Ammar ya furta.
D'an murmushi Sarki Ali yayi Jin yanayin maganr sa kamar Wanda ke koyon magana Hausan ma Dai Masha Allah.. Yakwana dubu,? Sarki Ali yakara furtawa..
Dan murmushi Ammar Dr Ammar yayi na tambayar ta mahaifinsa Wanda har saida Sarki yaji sautin fitar sa. Dariya yayi k'asa k'asa Jin yaron nasa na cikin farin ciki koba komai yasan cewa komai ya wuce tsakaninsu da d'ansa duk da kafiyar da kowannensu keda ita.
Ya aiki ya masa Bayan ya furta Alhmdllh. Cikin farin cikin da yakara mamaye sa Jin dariyar Mahaifin nasa abun kaunarsa ya yakara furta Alhamdulillah..
Ammar ne yake Tambayar Ina Nurul hayat bayan sun gama musayar gaisuwar ta yaushe Gamo,"Nurul hayat Dinka na nan lafiya,Ni yanzu ma Ina Fada ne "sarki Ali yabasa Amsa.
Shiru dukkaninsu sukayi akan furucin sarki Ali na karshen musamman Ammar domin Gaban sane yayi mummunar faduwa A tunanin sa zancen Baya ne zai dawo duk da Bai ga alamar hakan atare da yanayin Mahaifin nasa ba ...
Sarki Ali ne yayi murmushi Jin shirun da Ammar yayi akan furucinsa nakarshe Wanda dama yayi hakan ne Dan yakara ganin Yana yin Ammar din da dauki kiyayyar duniya yadaurawa sarauta.
Katse shirun nasu yayi bayan yagama tu ajjabin Al amarin Ammar din,Anan yasanar Masa da batun janye murabus dinsa har sai lokacin da yaji Yana Ra'ayin ayimasa murabus din,tare da furta Masa ya yafe Masa laifin da yayi Masa na Rashin Neman sa,duk da yasan Shima yana da laifin sa taurin kan ne iri Daya like father like son.😀
Farin ciki ne Mai yawa Ammar ya tsinci kansa aciki Jin Abunda Bai tab'a zato ba agurin Mahaifin nasa,sai Kuma gist na biyu da yakara Sanya sa farin ciki shine katafaren Asibitin da aka Gina da sunansa wadda har an kammalata tun da sarki Ali yafara maganar Ammar ya fincike blanket dinsa k'asa yasauko daga kan had'add'en bed dinsa na Alfarma, k'ak'k'arfar surar jikinsa ta Bayyana tare da kwantaccen gashin kirjinsa da yakara lafewa guri Daya sanadin Hutun Dake jikin sa komai gwanin buurgewa atare dashi abun son kowace mace 🤫 harta da six spack dinsa dama daga shii sai short ne fari k'al ajikinsa.
Jin cewa mafarkinsu shida d'an uwansa. ya cika nason Gina hospital ta Alfarma anigeria duk da suna da Abunda zasuyi constructing da kansu musamman ma shi Ammar din farin ciki ne kwance akan kyakkyawar fuskarsa and he's speechless about the gist.
Ficewa yayi daga bed room din nasa. Cikin sassarfar sa ta gwarazan maza yake saukowa daga upstairs din sa har Yana hada steps biyu,Kuma wayar na akunnensa Yana furta thank you ABBA! thank you ABBA! you are the best father in the world cikin shauki na soyayyar mahaifinsa da farin cikin wannan albishir.
Hakuri yabawa mahifin nasa na Rashin Neman sa da baiyi ba cikin natsuwa,cikin farinciki dukkaninsu suka Yanke Kiran bayan sunyi sallama da juna.
💃💃💃💃🙌🙌Finally dai Ammar ya shirya da mahifin sa yanzu sai maganar dawowa Nigeria✈️✈️Allah yasa dai su dawo kasar su ta gado don nikam nagaji da kasar India zafinsu yayi yawa arado 🤭🧐🤫
🚴🚴🚴🚴🚴MUJE ZUWA akuya ta sace kura😆.Ko A mafarki Nasan hakan bazai faru ba....Nima nabi maganar bahaushe 😹
Komai Nisan jifa.....🤗🤗
*Hasbunallu wa ni'imal wakil* *Hasbunallu wa ni'imal wakil* *Hasbunallu wa ni'imal wakil*
YA ALLAH DUK WANDA YAKE DA WANI SAB'ANI DA IYAYENSA ALLAH KA DAI DAITA TSAKANINSU🤲🤲
DOMIN ABUNDA WASUN MU BASU CIKA KULA DASHI BANE BABBAR MATSALACE ARAYUWA YIN FUSHI DA IYAYE DOMIN HAKAN NA SANYA ZUCIYA RAUNI,YAKAN HANA JIN DADIN DUNIYA WALLAHI,FUSHIN IYAYE BALA'I NE.WAL IYAZUBILLAH😥
IYAYE BA ABUN WASA BANE,AKWAI HADISSAI DA DAMA DA SUKAYI MAGANA AKAN HAKKIN IYAYEN MU KUMA INGANTATTU,AKWAI HADISIN ANNABI SAW DA WANI SAHABI YA. RUWAITO INDA HADISIN YAKE CEWA "FUSHIN ALLAH NATARE DA FUSHIN IYAYE "KUJIFA ALLAH MA YANA FUSHI DA WANDA IYAYENSA SUKE FUSHI DASHI TO INAGA WANDA SHI YAKE FUSHI DA NASA SUBHANALLAH..😥
ALLAH KA KARE MU DA WATA MUMMUNAR ZUCIYA🤲 DAN HAKA MU SAKA HAKURI, DUK ABUNDA SUKAYI MUNA MU MAI DASA BA KOMAI BA IN SHA ALLAH ZAMU GA RIBAR ABUN.. TABBAS DUK ABUNDA MUKAYI MUSU BAZAMU TABA BIYANSU BA A CIKIN WANNAN DUNIYAR ,DAN HAKA MUDAGE DA KYAUTATA MUSU DOMIN SAMUN RIBAR DUNIYA DA LAFIRA DOMIN IDAN KIKA GAMA DA IYAYE KI LAFIYA TO DAYARDAR ALLAH ITAMA DUNIYA KINGAMA DA ITA LAFIYA. ABUN DA KAWAI BA,A YIWA IYAYE BIYAYYA ACIKIN SA SHINE SABON ALLAH.✍️✍️
ALLAH YASA MUDACE🤲 ALLAH KUMA KASAKAWA IYAYENMU DA GIDAN ALJANNAR FIDDAUSI.🤲 WAYEN DA SUKA RIGA MU GIDAN GASKIYA ALLAH KA HASKAKA KABARINSU KASA HUTUCE AGARESU.
AMIN YA HAYYU YA QAYYUM✍️ ✍️
💫Fa'eehbg 💫 The first lady 🙌🙌
Fad'awa dakin Aj yayi cikin yanayin farin ciki Wanda ko sallama Bai tsaya Yi ba adakin na Aj.
Dr Aj da fitowarsa daga bathroom kenan ta cikin mirror yaga mutun atsaye tsakiyar bedroom din nasa... Cikin mamaki yake kallon ganin Yana ta faman sakin murmushin mai kayatarwa
'Ammar ne yake ta sakin murmushi har ya tako ya rungume Dr.Aj Tsam ajikinsa cikin wani yanayi. Dr Aj abun yaji sa banbarakwai duk da duk da yasan d'abi'ar Ammar ce Rungumarsa inda sabo yasaba da hakan dan duk lokacin da yake cikin farin ciki yakan yi Masa hakan tun suna Yara yake Masa hakan,har yayi niyyar Ture sa sai ya tuna yanayin da yaga fuskar Ammar din da yanayin farin ciki Dake kwance akan fuskar sa Kuma yasan ayanzu bakaramin Abu zai Sanya sa shiga irin wannan yanayin ba...
Bayan kamar minti uku Ammar yad'ago daga jikin Dr.Aj Yana sakin wani k'ayataccen murmushi "Guess who called me right now"? Ya furta ma Aj cikin kafe sa da manyan idanunsa masu haske cikin zak'uwa Dr. Aj ya furta "su Lubna ne Dan saboda yasanar Masa haduwarsu alokacin da ya rubuta musu numbantasa...