A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 16
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 16: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 16. Yau yaji labarin da yamasa dadi tun bayan na…
3,372 words
Yau yaji labarin da yamasa dadi tun bayan na norah din,Kurumm yana Cikin maganar dariya ta subuce masa hadi da murmushi harda guntun hawayen da yadade baiyi ba na hango nesar su ta matso kusa mahaifiyarsa yake so yagani ruwa ajallo yana begen yaga ahalinsu a haka ma shidayake namiji mai karfaffiyar zuciya inaga Aunty Laila wadda kullum sai tayi kuka aboye bakowa ta kwallafa rai akan son gani ba sai yar ta nora wadda bata san a ina take ba tadai san tana cikin nigeria...
Allah sarki uwa mai dad'i Allah yasaka ma iyayen mu da aljannar fiddausi.Ameen!
Itama Aunty Laila dariyar take yi had'i da murmushi na farinciki musamman da taga yana yin mijin nata yau da yafara komawa asalin walwalarsa,ikon Allah take ta nanatawa aranta kenan Ammar d'inta ne suka gani yau sai kuma tayi murmshin ta mai kyau tana kasa boye farin cikinta itama....
A hankali ta furta " Allah sarki Norah ko a wane hali take yanzu yata girma shekara ishirin da d'ai da yan watanni ai nasan yanzu duk inda take sun mata Aure takai karshen maganar cikin d'an sanyin jiki yadda ta kwallafa rai da norah sai gashi ashe batare zasu rayu ba kaddara ta rabasu..
Muryar Appah ce ke magana yana furta"wannan bawan Allahn ya tabbatar muna da tana hannun kirki ni nayarda dashi domin ke kan ki shaida ce da taimakon Allah da taimakon sa muke rayuwa to dan haka karki saka damuwa aranki kinji oum norah da nur yakai karshen maganr da yin murmushi itama murmushin tayi cikin farin cikin datakara tsintar kanta jin yahada harda sunan Ammar wanda Unni ke kiransa dashi sai kuma ita a wasu lokuttan.
Cigaba da magana yayi "kuma da ace an mata Aure da ya sanar muna fatana kawai Allah yakara mata lafiya,ya tsare muna ita..Kuma ya bayyanar muna da Autan maza kafin mu koma nigeria ko don farin cikin hajiya yadawwama,kuma ya tonawa wayenda suke da hannu gurin cutar damu sukayi sanadiyyar rabamu da ahalin mu kasar mu,Ameen Aunty Laila ta Amsa.
Fitowar su ziyada ne da lubna sun chanja kaya izuwa na hausa Atamfa chiganvy jaa da bak'i dogayen riguna A shape sun masu kyau gwanin burgewa,da veil baki masha Allah kamar yan nigeria masu zama acikinta,shima ziyad yafito tsaff cikin shigar maroon colour yadi mai taushi harda hular zannan bukar bak'a mai daukar ido kamar wnda zaije gasar kyau.Dama duk ran friday shigar mu ta hausawa sukeyi saboda yadda iyayen nasu suka sabar musu Masha Allah Aunty Laila ta furta tana mai k'ara gyara ma lubna d'aurin ta irin na zahra buhari wanda ziyada tamata wanda Aunty Laila takoyamata.
Shaf shaf shima Appah yaje yashiryo cikin yadi maroon irin na ziyad,suka fice zuwa masallaci dan gabatar da sallar juma,a cikin jam'i har da ziyada ma Aunty Laila kad'ai aka bari tana cigaba da aikin gidan da bawani aiki bane girki ne kad'ai Sai yan gyare gyare dan ko ina tsaf kamar ba yara agidan.
FIRSTLADY🙌
*AMDAVAD* > >>>>>>>>> >>>>> Yau indian dishes ne agaban Amma shi yakasa tab'a koda wani gefe na abin cin dake kan dinning din,tandori chicken ne da pani puri sai kuma pakora sai tashin kamshi sukeyi yaushi ne abunda kukunsu ya girka domin shine a list na girkin yau na rana,DR AJ ne yasanya pock da knife ya yanko tandori chicken sai turu ri takeyi na kamshi bakinsa yakai yana kallon Dr.AMMAR da tambayoyi abakinsa,d'auke kansa yayi daga kallon da yake masa,yadauki pani puri d'aya yakara cusawa a bakinsa yana mai furta "narasa gane maka tunda mukaje shoprite d'in nan har yanzu baka dawo dai dai ba kamar akwai abunda yayi shocking naka agurin,tun dazu fa abincin nan yake gaban ka Amma ko kad'an baka tab'a ba.D'ago Manyan idanunsa yayi masu cike da yanayi na bacci a lumshe yasauke akan Aj dake ta faman cusa pakora abakinsa.
A hankali kamar wanda akayiwa dole maganar cikin dan yatsinar fuska ya furta" yanzu idan nacemaka idan na fad'a maka naga yarinyar mafarki na zaka yadda.......Yakai karshen maganar cikin wani yanayi.
Ai Dasauri AJ yad'auki ruwa ya kora sanadiyyar shakewar da Ya fara da pani puri jin furucin na Dr.AMMAR,Kwalalo idanun sa yayi wanda har Dr.Ammar Sai da yayi dan guntun murmushi mai k'ara k'awata kyakkyawar fuskarsa ganin reaction din Aj.
A hankali yacigaba da magana cikin dakewa kamar wanda akayiwa dole yaa furta "mai kama da ita nagani sai dai wannan yarinyace dan bazata wuce ten yrs ba akalla kallonsa kawai Aj keyi kamar ya ga bakon halitta,cigaba da maganar sa yayi cikin natsuwa "kasan kuma dakyar yarinyar tasaki hannu na......
Labari yafara bawa aj....... Zan bisu in samo muku rahoton.......
Nima zan baku labarin in naga ruwan like da comment.
share pls [3/27, 10:05 PM] Fa'eehbg writer: https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim Join my novel group👆for the new update✍️✍️
https://m.tiktok.com/h5/share/usr/6984456997898863621.html?_d=e8bi3m3l87dmll&sec_uid=MS4wLjABAAAAGOaScTEd7igAj6auum-Z_v0cxncjX7iFemXzcdWjbEL3FLsbTFXlRmOFLgVSMg1a&share_author_id=6984456997898863621&sharer_language=en&u_code=djg8gfjgkd6lbm
💫A MAFARKI NASANTA💫 In my dream I know her By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*BANYARDA ATAB'A MINI WANI B'ANGARE NA LITTAFI BA.INKUMA KIKAYI MINI GANGANCI NABARKI DA RABBA....*
*BAN YARDA A KARANTA MINI SHI AYOUTUBE BA SAI DA IZINI NA.*
*MASU TAMBAYAR COMPLETE BAN KAMMALA LABARIN BA YANZU NAKE TYPING*....
*Note editing...* ------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️is migthier than the sword 🗡️*
*Free book*📙
EPISODE1️⃣ PAGE3️⃣7️⃣
*WANNAN PAGE NAKI NE SISTER AYEESHAT ABDULLAHI MUHAMMAD💙 KIYI YADDA KIKE SO DASHI*
TYPING📲📲📲
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
.....Bayan nabaroka cikin shoprite din na fito in yi picking call bayan nagama amsa call din injuyo kawai sai naci karo da yarinya tsaye abaya na tana ta sakar mini murmushi,ida juyo wa ta kenan,A hankali yarinyar ta furta mun cikin harshen india bayya! cikin murmushi. ganin yanayin yarinyar yasaka nima nasaki fuskata wanda har zuwa lokacin mamaki da alajabi bai sake ni ba naganin kamannin yarinyar da nake yawan mafarkinta..
"Yaya zaka kaini gurin didin mu yanzu koh" da ta furta shine yasanya ni k'ara saita natsuwa ta.Kai kad'ai na d'aga mata badan nasan wacece yayar tasu ba,muna nan tsaye tana zuba mini surutu sai ga wasu samari mace da namiji inaga dai twins ne su sun doso inda muke suma kuma baka ga yadda suke kallo na ba kamar ydda nake kallonsu wanda ninasan kalllon rashin sani ne suke mini gani na tare da kanwar ta su da ko sunan ta bansani Ba dan naga suna kama da yarinyar Sosai.
Gaisawa mukayi dasu Sannan suka nemi in basu kanwar tasu A hankali nazare hannu na dake cikin nata wanda ta rike gamm,rigima suka sha da ita dan tadage sai tabini nakaita gurin didin ta harda kuka sai da na lallasheta sannan nace taje zamu hadu gobe in kaita Amma duk da haka sai da namijin ya fisgi hannun ta tana kuka tana waige na harsuka sanyata bayan seat suka tada motar su,d'an nisawa yayi sannan ya furta a hankali cikin wani kalar sanyi "kaina ne ya daure shiyasa nakasa komawa cikin shoprite din Yakai karshen maganar cikin sauke katuwar ajiyar zuciya na doguwar maganar da yayi.
Kallonsa kawai Aj keyi har yadauki ruwa ya tsiyaya yakai abakinsa",yau nakara shaida son da kakeyiwa wannan yarinyar mai yawa ne,ace har ka iya kallon yarinya yar shekara goma siffarta to ko dai yar shekarar goman zaka Aura yakai karshen maganar cikin kanne ido d'aya "kaga sai muyi rainota...Yakai karshen maganar yana sakin karamar dariyar shakiyyanci aj ke furucin.
Harararsa Ammar yayi sai kuma yasaki dan karamin murmushi yana girgiza kansa na furucin Dr.Aj yana mai yankar tandori chiken A hankali yake taunar naman kazar bayan ya saka bakinsa Tare da lumshe manyan idanunsa da yake jin sun dan masa nauyi kasancewar rashin samun isasshen bacci da baisamu ba jiya a asibiti.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• MUJE ZUWA👓
Tun alokacin kusan kullum sai Dr.Ammar ya tsiri zuwa shoprite din ko zai ga mai kama da su lubna sai da yashare kwana goma bai hadu dasu ba sai arana ta sha d'aya ne ya hangi lubna itada ziyadah hannunsu rike da juna amma ita sai waige waige takeyi kamar tana neman wani abu kamar ance ta waigo daga gefen da yake tsaye ya rungume hannayensa.
'cikin masifaffen gudu ta zare hannunta cikin na ziyadah tana zuwa ta fad'a jikinsa ta rungume sa sai kuma tasaki kuka itakam ziyada sai ikon Allah take kallo,Ajiyar zuciya yasauke a hankali kamar wanda yaron da yake neman uwarsa sai da yaci wuya yaganta sannan ahankali yacigaba da lallashinta yana shafa sumar kanta."Bayya"ta furta cikin sanyi da dariya mai nuna farin cikinta.dama lubna tasha wa Kowa kai gidan su na rashin kara had'uwa dashi da batayi ba kusan kwana uku kenan duk aka tadosu makaranta sai sun kawota gurin Amma sai dai har su bar gurin basa ganinsa saboda suna shan ban ban wurin wani lokaci da rana yake zuwa sometimes kuma da dare su kuma bayan antaso skull ne.
A hankali cikin kara kawata fuskarsa da murmushi ya furta can I know ur your Name cikin harshen india suke maganar "LUBNA BABY " ta furta aunty nace mini haka Appah ma nace mini yaya ziyad ne da ziyadah kadai basa cemun baby murmushi yakarayi sannan yashafa kanta yana dagota daga rungumar da yayi mata ayanzu kan kafadarsa.
Itama ziyada zuwa tayi suka gaisa dashi cikin sakin fuska a hankali tunda yaji sunanta gurin lubna yafurtawa ziyada ya schl Lafiya lau ta amsa mishi cikin girmamawa duk da mamakin jin sunanta abakinsa.
Tattakawa yayi dasu har inda rantsasiyar motar tasa take kirar Benz kamfanin lenovo dan bai fitowa da ko daya daga yaransu inzai zo nan,front seat ya bude yajawo wata katuwar teddy pink colour da tacika extra seat na motar an rubuta mata baby Akan band mai kamar katifa din dake kan ta da ruwan gold.Mikawa lubna yayi cikin sakar mata murmushinsa.Ba lubna ba hatta ziyadah da ziyad da fitowar sa harabar wurin yahango su shine ya shima yafito a motar da yake zaune teddyn ta burgesu ko ni mai kwaso rahoto ta burgeni matuka.
Farincikin lubna yakasa boyuwa tsalle kadai takeyi a wurin bayan takara rungumesa tana furta thanks you Bayya.
Bayan motar yakara bud'ewa ahankali ya fiddo da wasu big bags na shoprite din masu kyau d'auke da hoton chocolate,wanda kusan kullum sai yasayesu sai dai yakyautar inbai ga su lubna ba teddyn ce dai guda tun da yasaye ta saboda tamasa kyau sai ya ajiyewa lubna.Mikawa ziyadah ledodin yayi yana furta keda twins brother naki daya, daya kuma na lubna baby ne ita kadai tsalle ta k'ara dakawa cikin farin cikin wannan kyautar da tasamu ga trddyn ta rungume ajikin ta,Sai ma tamanta da maganar kaita gun didinta.
Godiya ziyad yamasa sosai bayan sun gaiisa sannan sukayi sallama dashi har inda motarsu take Har suka shiga mota tana waigen sa tana daga masa hannu shima yana daga maata har ziyad yatada mota ta dakatar dashi da gudu ta fito da tap dinta ta buga game da karatu kirar samsung ahannu ta inda ake saka numbers tashiga duk da wayan ba mai simcard bace ta furta
"Bayya sanya mun numbanka kar ka kara guduwa baka kaini gurin didi bah"
Murmushi kadai yayi yakarb'i tap din rubuta mata nine digit nasa sannan tayi saving da bayya tana rugawa da gudu tashiga mota ta rufe tana d'aga masa hannu har kanta ta ke leko wa ta glass tana sakar masa murmushi...
Sai da yabar ganin kurarsu sannan yayi murmushi yanajin kansa cikin farin ciki marar misaltuwa naganin lubna hardasu ziyad ma akaro na biyu..
Shima daukar motar sa yayi sai gida dama ga abunda yakawo sa kuma yasamu.
<<<<<<<<<<<<<<<< <<<<<<<<<<<<<<<<< 💫FA'EEH BG💫 FIRSTLADY🙌
shigowarsa baiyi tsinke ko ina ba sai akan katon dinning space nasu a hankali yasanya hannunsa ya wanke akan sink,sannan yazauna a d'ai daga cikin manyan hadaddun dining chairs din dake dinning area din masu kyau ••Butter chichken yajawo dake daure da raping sheet mai kyalli ya bud'e a hankali kamshin hadin hadaddiyar kazar da taji hadi na musamman yabugi hancinsa ne yasanya sa lumshe manyan idanunsa masu haske,A hankali ya yago kazar da pock da knife yakai bakinsa ya tauna a hankali harda kad'a kai saboda yadda d'and'anon da yagame bakinsa,Bhulpuri yajawo dake cikin katuwar food flask mai kyau ya zuba bakinsa yasanya yana taunawa ahankali Dr Aj da yanzu yazauna kan dinning din ne ya furta" acicin banza tun d'azu ina nan ina jiranka shine daga zuwan ka kazame nan maimakon kaje kakirani ko kasanya sabirkhan Ya kirani shiru bai tanka masa ba har sai da yaji cikin sa ya dauka domin Ammar bai wasa da cikinsa ko kad'an,ruwa yasha da lemu sannan yayi hamdala tare da mikewa yana furta cikin arrogant voice nasa" kanka akeji uban mita"yakai karshen maganar yana sakin kayataccen murmushinsa irin wanda ke kular da aj domin smiling ne mai ma,anoni da yawa aciki harda rainin hankali upstair ya wucewar sa dan yin wanka.
yau aj ya ga farin ciki akan fuskar Dr. Ammar kuma yana da tabbacin cewa ya had'u da yarinyar da yake ta zagayen fita yasake gani,murmushi shima yayi kawai yana cigaba da cin abincinsa.
*NIGERIA ZAMFARA* *GUSAU* Ta sambo!!!!
kuyi manage ba yawa. [3/27, 10:05 PM] Fa'eehbg writer: IDAN KINA SON KARANTA LITTAFIN AMAFARKI NASANTA ASAUKAKE KAWAI KIYI JOINING LINK DIN GROUP D'INA👇 https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫 In my dream I know her By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️is migthier than the sword 🗡️*
*Free book*📙
EPISODE1️⃣ PAGE3️⃣8️⃣
*Kema ganaki kawar arziki wannan page din sadaukar wa ne agareki siddiqa muhammad na'ibi👌luv u lodi lodi💔💏*
TYPING📲📲📲
<<<<<<<< < <<<<<<<< < <<<<<<<<<<<<
Khairiyyah d'iyar fulani ce tashigo sashen unni dan gaida hajiya, bayan sun gaisa da unni da mahir da ya gaida ita sannan ta ke tambayar unni ina hajiyar unni ce ta furta "ai takoma sashenta tun shekaranjiya,sallamar su nisa ce da sumy,inayah takatse maganar da Khairiyyah ke son yi
'ina wuni mama khairiyyah dukkaninsu suka had'a baki gurin gaisheta cikin sakin fuska ta karba musu da lafiya lau aa inayan dija harda ke hajiya tazo kenan
"eeh "inayah ta furta cikin murmushi tana mai sunne kan ta kasa. " ya kuka baro dija din lafiya take koh?Mama khairiyya takara furtawa
"lafiya lau"Inaya ta amsa mata.
Allah sarki yara duk sun girma mama khairiyya ta furta bayan wucewarsu daga falon,inda shima mahir tuni yabar falon.
'Hawaye ne shar suka tsiyayo abisa idanunta gwanin tausayi lallashinta unni tayi cikin tausayin rayuwar da mama khairiyyar ta tsinci kanta ciki,anan ta sanar mata ai mijinta yanzu yamata saki daya kuma dama ita kanta ta gaji da hakurin da takeyi.
Hakuri unni takara bata tare da kara lallashinta...
Kukane ya kubce mata,cikin ruwan hawaye da shesshekar kuka take furta duk wanda yarabani da hamma Abdul rashid bazan tab'a yafe masa ba domin nasan farraqu akayi mani dashi,inaji ajiki na komai da akayi masa sanadi nane.....
'Kukane yaci karfin ta, cikin shesshekar kukan tane taci gaba da magana Allah yabayyanar muna da kai, Allah kaine kasan Abunda yake B'oye Allah kakawo muna sauyin Al amurra cikin gaggawa takai karshen maganar cikin k'ara sakin wani mahaukacin kuka tana jin kamar yanzu komai ya faru na rabuwarta da masoyinta nata.
Itakanta unni kukan takeyi cikin jin zafin alamurran dasuka shud'e musu wayend ke wuyar mantawa azukatansu duk da koma mene ne Allah ya riga ya rubuta sa ne Bawa baya taba wuce kaddararsa duk zille zillensa.
Abunda yafaru chan baya ..........
Tun bayan dawaowar Abdul rashid daga sudan bayan ya had'o degreen sa akasar sudan na fannin likitanci .
Soyayya mai tsanani ta shiga tsakaninsa da ummulkhairi( mama khairiyyah )yar wajen fulani wadda take warinsu unni ce auta ga fulani...
Soyayyyarsu gwanin burgewa Amma fulani batason had'in nasu,sai da sukayi makarkashiya itada muhammad (malan)suka raba mama khairiyya da Abdul rashid domin cire masa ita akayi a zuciyarsa gaba d'aya wanda suka je a wurin wani katoton boka yayi musu aikin aka cire masa ita azuciya.
Ahaka mama khairiyya sai da tayi jinya ganin ba itace agabansa ba,kuma fulani ta gargade ta da karta k'ara kulashi tunda yabarsonta ya yaudareta, Bayan rabuwarsu sai kuma aka wayi gari an nemi Abdul rashid Ba'a gansa ba har ciigiyarsa anbada a kafafen sadarwa ba 'a sameshi ba babu wani labarinsa domin kamar an masa kurciya wannan kenan....
Shigowar sarki Ali ce tasanya dukkaninsu yin shiru Bayan lallashin su da yayi da basu baki wanda shima karfin hali ne kadai yayi kasancewarsa namiji,Fira suka d'an fara tab'awa dan kawar da damuwar da ta addabi kowannensu .....
Jakunkunansu suka fito dasu suduka ukun unni ce ta lura dasu A hankali bayan kare musu kallo ta furta"kai lafiya kuka fito da bags haka "
Ehh unni gidan ummi zamu suka hada baki wurin bata amsa "kudawa ,Kuma kun ma hajiya sallama ne " takara tambaya dan taga kamar ma sun dade da shirya tafiyar duk da ba wani nesa bane.
Ehh ai daga sashen ta muka fito d'azu kuma su yaya Abdallah ne zasu kaimu.
Mahir da shigowarsa falon kenan kunnunwansa suka jiye masa maganar da nisa da sumy suka furtawa Unni ai dasauri yakoma inda yayi shigewarsa mota yayi zamansa batare da su Abdallah sun lura dashi ba
Sallama sukayi ma kowa dake falon sannnan suka juya suka fice bayan yimusu Addu'ar sauka lafiya dasukaYi.
Direct compound din gidan suka fito basu doshi ko ina ba sai inda Abdallah da yusuf da yake gaban motar sukayi parking motarsu .
mahir da yaga dai alamar shiga motar sumy zatayi yayi kaza zam ya fito cikin motar yana kwala ma Nisa kira Dukkaninsu sunyi mamaki domin basu yi tsammanin yana cikin motar ba.
"Gani yaya ta furta bayan isowarta inda yake tsaye agaban motarsa cikin daure fuska.
"bake naki raba " ya fad'a cikin da'ure fuska,sakake nisa tayi tana kallonsa jin furucinsa
Cikin jin haushin rainin hankalin na mahir ta furta " NISA fa naji ka kira yaya irin ma fa kiran nan na mafarauta" Cikinta yayo zai kai mata rankwashi ta kwasa aguje tana tikar dariya ...
"Sumy yaya nakira" sumy da har ta zauna ne tafito jin furucin nisa,BAyan fitar Sumy nisa ta furta "Yya Abdallah kumuje kawai,zai kawota daga baya sak'o zai bata,Abdallah da yusuf murmushi kad'ai sukayi Abdallah cikin zuciyarsa yafurta no wonder yanzu nagane murmushi yakarayi sannna yafigi motar suna ficewa daga gidan bayan ma'aikatan dake tsaron katon gate din sun wangale musu katon gate din....
Sumy kuwa ganin motar ta wuce ne kuma gashi tayi tsayin kusan minti uku baice mata komai ba abun sai yafara sanyata jin haushi,cikin tsiwar da bata san tana da ita ba,ta furta"wai yaya mahir meye haka har sun wuce fa"
D'ago idanunta ta yi taga yana kallonta ko k'aftawa baya yi sai taga yakoma mata Dr.Ammar Domin dama dashi yake kama sosai samun kanta tayi da k'ara natsuwa bayan hango kamannin ya" yan nasu marar son wargi da tsare gida.
Bayan yagama k'are mata kallo ya furta shiga mota cikin turo bakinta ta bud'e k'ofar baya tashiga har ta gyara tazaman ta ta ga yana tasakar mata harara wadda tasan dalilinta dole ta dawo gaba "Better ya furta sannan ya rufo kofar yana yin reverse na motar suka fice gidan gaba d'aya bayan wangale musu gate din.
*BUG* A b'angaren su Halee kuwa yau ta tashi da jikin ciwon kan nata yatashi har cikin ido ko iya bud'e idanunta bata yi,Baba Adee Khady ta kira tasanar masa ta hanyar wayar makota dole ya baro gurin aikinsa.Suka shirya zuwa asibitin Babban Birnin tarayya waton federal medical center gusau An karb'e su cikin mutun tawa sai dai bayan binciken jikin Haleen da yan awannni Baba Adee yaji abunda ya girgizasa tabbas likitoci sun sanar masa ciwon Halee daga cikin hypothalamus dinta yake matsala ce babba domin sai anyi aiki ancire jinin da yake acikin kwakwalwarta wanda jinin ya kume mata sanadiyyar wata buguwa da tatab'a yi likitota sun sanar masa da aikin nata yana buk'atar milion goma dan ceto ranta dan idan ba'ayi saurin cire mata wannan jinin ba da yake yawan sanyata ciwon kai zai kai inda ba'aso kuma hakan ne ba,a so domin zai iya zama sanadiyyar zamowarta psycho mai tabin hankali ta samu mental problem Wanda baida ranar warkewa sai ikon rabba.