A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 15
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 15: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 15. Muryar khairiyya ce tadawo da da ita daga maganr…
3,334 words
Muryar khairiyya ce tadawo da da ita daga maganr zucin da takeyi i nda take furta Fulani zuciya cikin kara fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare..✍️✍️
Wayyoh khairiyyar fulani ke kuma taki kaddarar kenan😫
Nasan dai kungane wannan khairiyyar koh..Domin sai da namuku kwatta kwatta na labarin tundaga kakanni.Kuma nayi haka ne don kugane dakyau.✍️
ko zai faru da khairiyya Allah dai yasa ba zuciyarta ce take shirin bugawa....
Yawan likes yawan comment yawan page....✍️
Like,share and comment pls
[3/27, 10:05 PM] Fa'eehbg writer: 💫A MAFARKI NASANTA💫 In my dream I know her By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
IDAN KINA BUK'ATAR UPDATE DINA DA ZARAN NAYI TO KIYI JOINNING GROUP DINA MATA KAWAI✍️
https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim FIRSTLADY 🙌 ------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free book*📙
EPISODE1️⃣ PAGE3️⃣5️⃣
TYPING📲📲📲
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• not edited..🙏
A hankali ta lallasheta tana mai tambayar ta ya bata umurnin zuwan da zatayi duk "A ah"ta bata amsa bayan ta tsaida kukan nata,kara tambayarta tayi kudin na isar ta eh ta furta tare da kara furta ai dubu hamsin ne ya turo mini cikin mutuwar jiki,umurtar ta tayi da tabishi a alalama dan tasamu gobe yabarta ko jibi tazo,touh tace sukayi sallama.
Fulani ce ta umurci malan cikin wani yanayi da yabata maganinta na hawan jini dake cikin lockern drowern ta na gado dauko mata yayyi tare da jarkar swan mara sanyi yana furta ai duk ke kika ja mata tunda tun farko sai da nace karki had'ata da wanchan tsohon kika kika k'iji tun kafin murabata da Abdul rashid nace miki kibari tasamu wani kika k'i ke ga d'an uwan k'awarki mai kud'i alhaji ai ga irinta nan,Bayan tasha maganin kallonsa take da mamaki jin furucinsa wai duk laifintane,kamar ba dashi da ita sukayi komai ba yanzu kenan ita zai bari ciki tasan idan har khairiyya taji ai tasan ta rasa ta dan zata iya barinta har abada gashi Allah yadora mata son khairiyya kasancewarta itakad'ai mace agareta da kuma Auta,da maln shima tana son sa saboda tasu tazo d'aya shine abokin shawararta amma yanzu jibi yadda yake mata fad'a kamar baisan komai ba kamar kuma ba ita ta haifesa ba.
YAA ALLAH KAR KA BAMU IKON HAIFA "YA "YAN DA ZASU RIKA YIMUNA FAD'A KAMAR SU SUKA HAIFEMU AMEEN🙏
Uffan batace masa ba har ya gama yimata fad'ansa yafice. Take nadamar da ta dade tana tare da ita ta taso mata na raba Ummulkhairi da Abdul rashid a yanzu da komai ya chabe,hawayenta ta share na tausayin khairiyyah.
A kano kuwa b'angaren Hajiyar safkare sun taso daga kano lafiya tun safe cikin jahar zamfara wuraren karfe sha biyu da rabi na ranar Alhamis,sun samu tarba ta musamman dan duka ahalin babu wanda baizo ba sai mutanen india, girke girke kala kala aka musu da sanya hannun Unni da Ummi.
Farincikin su Nisa da Sumy bai Fad'uwa lokacin da suka hajiyar dan basu san da zuwanta ba Ummi tadai ce su shirya yau zasu je Wurin Unni,Dad'i biyu kuma Inayah tare da ita dan sun saba da Inayah sosai a lokutta da dama su mama dije kan kawo musu ziyara itada hajiya,kuma suna waya da ita awayar Unni ko Ummi.
Janye Inayah sukayi zuwa d'akin Nisa dake chan akusa dana sarki Ali fira sukeyimata kala kala duk rabi ta yaya Abdallah ce dan sun san lokacin baya bata da wani wayau Allah yadaura mata sonsa sai dai shi besani ba har kawo wa yanzu.
Sauraren su take kawai insun fadi abun dariya tayi dariya na murmushi ta murmusa babu wadda ke bata dariya Irin Nisa,Dan Harda Gulmar sumy ta kawo mata a kunne kuma agaban sumy d'in akan mahir inda take shaida mata wai har iyaye sun shiga ciki da sungama karatu za'ayi bikin,k'aton rank'washi sumy tayi mata tana furta wallahi Inayah k'arya take miki,sai kuma suka koma dariyar Nisa dake zubar da hawayen rankwashin da Sumy tayi mata,Inayah ce tajawo ta tana lallashi,sai kuma ta warware jin tambayar da Inayah tama ta na " ina Yah Al amin??
Amsa tabata yana india man sai kuma ta dafe kanta tana furta gosh! tare da rufe bakinta tana furta Nabani Amma dai Aunty Sumy Munafuka kike badai kingaya mata bah,tana k'ara b'are baki zatayi kuka Inayah ce ta jawota ta rungume tana lallashi sannan ta rad'a wata magana akunne da bansan ko ta mece ce ba,dukkaninsu suka sanya dariya.
K'wank'wasa k'ofar da akayi ce tasanya su yin shiru,"waye"cewar Sumy, Muryar Husna ce tasanya su yin shiru inda ta furta nice fa Anty tana turo k'ofar tayi jin ance tashigo,da gudu tashigo bako sallama sumy ce tadakatar da ita ta hanyar furta sallamar fa tana hararar ta komawa tayi da baya tayi sallamar suka amsa mata atare,ya akayi ne Husna ta Halan?inji inayah,hajiya ce take kiran ku,kuzo kuci abinci tabasu Amsa,mik'ewa dukkaninsu sukayi suka fice daga d'akin.
FIRST LADY🙌
A had'adden dinning table d'in dake part d'in Unni dukkaninsu suka iske iyayen nasu,tundaga Su Unni da su mahir har kan sarki Ali da sauran su Abdallah dasu yusuf,isowar su wurin yasanya dukkaninsu suka ja kujeru akusa da hajiya suna saka ta a tsakiya itakuma inaya tana akusa da Abdallah da Husnat,kowa shi yake zab'ar abun da za'a zuba masa.. Had'addiyar fried rice jallof ce da taji naman hanta da kuma white rice da stew ta chicken mai hade da cos low da yaji kayan had'i,sai kuma wainar shinkafa da taji had'i,hajiya ce mai son waina itada nisa saboda ita kayita musamman.drinks ne kala kala.
Bayan hajiya Dukkanin su daga mai fried rice sai mai coslow suka zab'a. Ahankali suke cin abincin su tun bayan saving dinsu da masu aikin na Unni sukayi,sai su Nisa ne dake k'us k'us din zaman zaman Inayah kusada Abdallah sukeyi kasa kasa Bayan Hajiya duk da hajiya tanaji bata tanka musu ba.
A hankali dukkaninsu suka fara watsewa suna komawa falo sai yarage daga Nisa sai Sumy suka rage da suka tsaya gulma sai inayah dake tsakurar Abincinta saboda jin ta uncomfortable a wurin,Abdallah ne ya furta mata Ahankali Inayah lafiya kuwa?Dasauri tad'ago manyan dara daran idanunta tana sauke su kansa arazane jin yadda yakira sunan nata ba yadda tasaba ji ba,Murmushi ne ya sub'ucewa masa abazata sai kuma ya d'an sauya murmshin ta hanyar furta Allah yasa dai ba tsoro nabaki ba kai ta girgiza masa tana mai sauke idanunta k'asa,Muryar shi ta tsinkayo yana furta bari inbarki kici Abincin ki koh madamm! Yabar wajen dinning din yana sakin murmushi ya wuce dakin mahir inda suka dosa suma shida Yusuf.
'Su Nisa dake kallon su kamar status gulma ta yi dad'i A hankali suka shek'e da dariya wadda sai da duka su Unni dake firar yaushe gamo suka juyo suna kallonsu,kai kawai Ummi ta girgiza itada hajiya suna masu fad'in Aikin ku kenan Haijya ce ta furta waisu wayen nan yaran yaushe zasu gama boko ne,Murmushi Unni tayi tana furta Hajiya boko ai ba,a gama sa sai dai kai iya yinka, kyab'e baki hajiya tayi,Ganin reaction d'inta sai Unni tayi murmushi ta furta shekarar nan ne ai Hajiya,to ai kam dasun gama makaranta zan zauna da iyayensu amusu Auren sai ahade da inaya itama,kallon hajiya kawai su Unni keyi dan sun san su nisa ko samarin basu dasu bare akai ga fira duk da basu sani ba ko duk suna da wayenda suke so,Dan D'an yau ba'a shaidar shi...
Unni ce ta furta to ai shikenan hajiya ita sumayya yar gida ma za,ayi inaga tana dariyar jin kunyar maganar tata,basu dai tambayeta dawa ba,Amma ita kam Ummi tagane tunda har Unni kejin kunyar maganar toh da mahir take nufin za,ayi yar gidan Murmushi ne yasubuce mata cikin farin ciki sai ta girgiza kai kawai. Muryar Hajiya ce ke furta itama Inaya kamar akwai nata hadin anan dan naji wadanchan ja'iran na maganar wai akalli Inayah da Abdullahi sun dace sun zata banji su ba murmushi dukkaninsu sukayi suna furta Allah yatabbatar da Alkhairi acikin wannan zur'i a tasu Ameeen nikam nace harda mu...
Muryar hajiya ce takara furta da yanzu takwarata NORAH tana duniya da harda ita sai a had'ata da bak'in likitan turai Ammar take nufi haka take cemasa Shikuma Aj bak'in likita.
A hankali takara furtawa cikin sanyin jikin da yasameta Allah yajik'anki da rahama Sadiyaa keda iyayenki,Dukkaninsu suka Amsa cikin yanayin damuwa,sannan suka cigaba da Firarsu har zuwa lokacin da sarki Ali yadawo shida Husnat bayan fitar su falon. "Inayah ce ke harara su Sumy taana furta gulmaAjali in ba'ayiba a mutu tana mik'ewa daga zaunen datake kan dinning suma mikewar sukayi suna dariya k'asa k'asa suna mata gwalo,falon dukkaninsu sukayi suka jone dasu hajiya aka cigaba da firar yaushe gamo wanda hardasu mahir dasuka fito yanzu aka cigaba dasu.
💫 A Mafarki Nasanta💫 Daga Alkalamin Fa'eeh BG FIRSTLADY🙌
©️°•••••••••••••••••••••••••••••••••••°©️
*INDIA MUMBAI* *AMDAVAD*
Amdavad unguwace Babba tana d'ai daga cikin manyan unguwanni agarin mumbai kasancewar ta tara manyan masu muk'aman gwamnati masu fd'a aji.Babban gida ne wanda yake flat katon gate ne golden inda naga wata mota ta shara ro da gudu tana buga horn mai gadin dake gadin gate d'in ne ya wangale mata gate din inda motar batayi tsinke ako ina ba sai a parking space na gidan ko dai daita parking d'in motar ba'ayi ba wata kyakkyawar yarinya ce yar kimanin shekara goma cikin shigar jeans da t shirt masu kyau ta fito da gudu a bayan motar tana kuka,tana nufar kofar dazata sadaka da babban falon gidan dasauri itama wata yar matashiyar budurwa wadda bazata wuce 16yrs ba ta gaban motar a extra seat tana k'wala kiran Lubna! Lubna! Amma ina yarinyar tuni yarinyar ta shige cikin falon.
"Ziyadah k'yaleta kawai naji an fad'a daga bayanta inji yaron da yafito a driver seat shima dai kyakkyawan yarone fari tasa kamar dai yarinyar da aka kira da ziyadah da kuma Lubna,shima dai bazai wuce 16yrs kamar ziyadah inaga yan biyu domin kamar su daya hatta tsawon su sai dai banbancin shi ya d'an fita zama Babba saboda Banbancin jinsi. Juyo tayi cikin yar damuwa ta furta Ziyad kasan fa halin yarinyar chan yanzu zata iya zuwa tagayawa Appah da Aunty laila karya da gaskiya yadda ranta yake bace din nan, yaron da takira Ziyad ne shima A hankali ya furta manta da ita kawai twin sis ai nasan Dukkanin su sauraren ta kawai zasu yi tunda sun san Lubna da karauniy,kuma ma ta tafi tafad'i fad'a ne kawai Appah zaiyi mukam babu ta yarda za'ayi mu yarda tabi mutumin da bata sanshi ba muma bamu sansa ba,bamu tab'a ganinsa ba sai yau.Har sun fara tafiya Ziyadah tace kaga tasa mun manta ma da icce cream namu amota juyawa tayi dasauri tabude bayan motar tad'auko wasu hadaddun shoprite bags sannan ta rufe motar.
Sallamar su ce wata matashiyar kyakkyawar mata da shekarunta baza wuce talatin da biyar ba fara tass da ita kamar balaaraba,gaidata sukayi da yaren indiyanci inda itama ta amsa musu da yaren sannaan ta musu sannu da zuwa.
Tambayar ta sukayi ina lubna bayan sun zazzauna aka tafaren falon dayasha kayan armashi komai na falon milky and white colour manyan hotuna ne makale akaton falon da fuskar wani farin dattijo wanda shima dai bazai wuce 57yrs ba a hoton shida wannana kykkyawar matar tare da ziyada da ziyad agefe da gefensu sai kuma lubna dake zaune ak'afafun tsohon dakuma wani karamin hoto na zane wanda ke d'auke da wata itama kyakkyawar yarinya yar shekara daya duk da azane ne amma duk tafi su ziyad kyau lubna ce mai d'an kama da ita ma,rik'e a hannun kyakkaywar matar nan,yarinyar na murmushi a hoton gwanin burgewa a happy family 👪wanda dukkaninsu suma murmushin sukayi,sai nasu kowa shikad'ai,sai na zanen yarinyar kuma wanda ahoton bazata wuce shekara daya ba da yan watanni ita kad'ai hotunann dan duk nata sunfi yawa wani tana rarrafe wani tana dariya wani tana rarrafe,wani kuma ta wangale d'an karamin bakinta ta had'a hannayenta Alamun tafi gwanin burgewa....
Muryar ziyad ce tadawo dani daga kallon tsaf din danake yiwa hotunan yarinyar mai saurin shiga rai,Anty laila ina Appa? Murmushi kyakkaywar matar dasuka kira Aunty laila da alama dai mahaifiyar su ce,A hankali cikin cikin murmushi ta furta yana nan yana bedroom dinsa naga lubnar dakuke tambaya tashigo tana kuka mai kuka mata?kallon juna sukayi tsakanin ziyad da ziyaada suna masu sunne kansu kasa A hankali ta matso garesu ta zauna garesu ta zauna atsakanin su tana mai sanya hannayen ta ta rike nasu cikin sanyinta ta furta kugayamun zan fahimceku kunji "ya"yana,muryar ziyad ce cikin d'an damuwa ya furta Aunty laila ina lubna take tana gurin Appah ku tana shigowa chan tayi tsinke tabasu amsa ziyad yakara furta kinga Aunty laila sai da kikace kar mufita yau mubar tafiyar nan sai gobe saturday,Amma wacchan uwar rigimar ta matsa sai da muka fita,Uhmm Aunty Laila ta tace tana kara fadar na sani kufito direct kufad'a kugayamun ziyadah,ziyad sai yan kwane kwane yakeyi,Ahankali ziyada tafara bata labarin abunda yafaru bayan fitarsu siyen icce cream din..Maimaita maganar kawai Anty laila keyi aranta har inda ziyada take furta AUnty laila yana kama da didinmu fa harda muma sai dai shi chocolate skin garesa kuma shima baki ga yadda ya rike lubna ba kamar kar yasaketa....✍️✍️
ko wane ne wannan da Lubna ta lik'e?? Su kuma wayen nan daga ina ????
Chakwakiya to bari dai mubi yarima musha kid'a adai juri zuwa rafi...✍️✍️
Next pge tommorrow
Naji sauki sosai ina godiya da Addu'o'inku wayen da suka nuna kulawa dama wayen da basu nuna ba,Allah yabar zumunci.Ameen ✍️✍️
pls Like share and comment... [3/27, 10:05 PM] Fa'eehbg writer: 💫A MAFARKI NASANTA💫 In my dream I know her By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
FIRSTLADY🙌 ------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️ is migthier than the sword 🗡️*
*Free Book*📙
EPISODE1️⃣ PAGE3️⃣6️⃣
TYPING📲📲📲
<><><><><><><><><><><><><><><><><>
........Koda muka zo inda yake rik'e da ita Baki ga yadda yake ta kallon mu ba har muka gaisa.. tambayar kanta ta k'ara yi Shin wane ne wannan wanda yake kama da Norah d'inta da kuma lubna wanda har lubna zata iya kiranshi da BAYYA Indian lang,( yaya) har take son sai yakaita gurin DIDIN SU(DIDI indian lang YAYA MACE) da ahoto kad'ai taganta ta tab'a ganinta,Muryar kyakkyawan tsohon ce take ratsa tsakiyar falon inda yake furta meyasa kuka k'i barinta ta bishi?,D'ago manyan idanun su sukayi irin na mahaifiyarsu har ita Anty laila d'in suka kallonsa dan son tabbatar da indagaske yakeyin maganar dan sun san Appah yana yawan goyawa lubna baya..
Zama yayi A falon tare da Lubna da ke ta tsiyayar da hawayenta yayi lallashi har ya gaji tun bayan shigar ta bedroom nasa d'in .akan d'ai daga cikin manyan rugs d'in falon ya zauna kara jawota yayi jikinsa ya rungume yana shafa lallausar sumar kanta data sha gyara ba,ayi kitso ba kamar dai yadda indiyawa keyi.
Murmushi kawai Aunty Laila tayi tana mai tasowa daga kujerar da take ita dasu ziyad,hannu tasanya bayan ta zauna a gefan Lubnah dake hawaye har yanZu ta rik'o hannunta tana furta "Nima haka nace musu meyasa basu barta tabi ya" y"anta ba tana yin maganar tana kallon Lubna me matso hawaye harda na dole..."Ko zai kaita gurin didinta,Murmushi tsohon yayi afakaice,har dasu ziyad ma Aunty Laila ce tacigaba da magana,Yan zu ke Lubna baby in inbanda ke ya za,ayi ki gane didinku wadda a zane kad'ai kika santa kika tab'a ganinta tana murmushi kuma har kika iya yarda yana tare da didinku,didinku da take Nigeria,Dasauri Lubna ta bud'a baki Tana Furta Allah Aunty Laila nikam na yarda dashi tana maganar cikin sakalci dagani kasan yarinyar akwai wayau "ai shima yana kama da mutanen kasar, Aunty black ne fa shima ni shiyasa ma nak'ara lak'esa ai dan ya tabbatar mun zai kaini gunta tunda yasanta baki gansa ba fa Aunty Laila wallahi kamar sa da didin sosai yakeyi Amma shine su Aunty ziyadah suka hanani binsa da yanzu naga didi na ni na matsu naganta.... kuka Ne yakara kubce mata bayan gama furucinta na karshe.
Sukam su ziyad sunyi zugum suna kallon mahaifiyar tasu da kanwar tasu jin yadda take ta zaro zance kamar an rera shi acikin kanta,jin mahaifiyartasu tana lallashinta Lubna din ne yasanya ziyad furtawa lubna ai sai ki shirya Gobe ma sai mukai ki in Appah ya yarda ya furta hakan ne ganin signal d'in da Appah yamasa domin yasan hakan ne kawai zai kashe wutar domin kuwa ya k'agu yaji komai gun Aunty Laila domin haka kawai tun fara bayanin na Lubna wanda achan duk bata masa shi ba yaji gabansa yana mugun faduwa hankalinsa ya dugunzuma gaba d'aya..
Ai ko da jin furucin ziyad take lubna ta share guntun hawayen ta wanda har yafara kafewa cikin farin ciki ta kalli Appah kallon bani AMsa kai yad'aga mata shima cikin murmushi dukkaninsu murmushi sukayi.
Bayan samun saukowar tane suka wuce nasu dakin itada ziyada don yin fresh up shima ziyadah ya wuce nasa dake farkon nasu.
©️°•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••°©️
A falo kuwa Bayan wucewar nasu ne Aunty Laila takamo hannun mijinta dan son tabbatar da yanayin da yashiga A hankali ta furta ABBAN NORAH !!!! D'ago rinannun idanuwansa yayi wayenda suka sauya tun bayan da aka ambaci nigeria yaji wani k'olon mashi yachaki zuciyarsa na bakin ciki,da kuma yana yin tausayin norah da yazame musu jiki akoda yaushe.
A hankali itama Aunty Laila ganin yanayin nasa sai taji hawaye sun taru a idonta natausayin tilon yarsu dasu kansu basu san a ina take ba,a wani hali take sai dai hope dasuke dashi kasancewarsu iyaye suna fatan ace yarsu lafiya lau take, cikin gargada muryar kuka ta k'ara furta Abban Norah lokaci yayi da zamu bayyanar da kanmu ga ahalinnmu lubna tana son ganin ahalinta haka ma su ziyad wayenda ma suka fita wayau ada mun boye musu norah amatsayin yar uwarsu da muka fahimci hakan bai da amfani munsanar musu matsayinta agaresu duk da bakomai muka sanar musu ba, ni ina ji ajiki na wannan wanda Lubna suka gani jinin mu ne.
Dasauri Appah yak'ara d'ago rinannun idanunsa cikin razanar jin furucin matar tasa,kai ta d'aga masa cikin tabbatarwa,' wanda su Lubna suka gani jininsu ne to wanene wannan kenan?nanata kalmar yayi wurin sau uku ko fiye ma daga karshe babu mai bashi amsa,A hankali Aunty Laila ta bashi labarin dasu ziyad suka bata,ganin shock din da yashiga yahasa yin wani motsi sannan takara masa da wanda Lubna tafadi yanzu wanda ta san hardashi ne yasanya kansa yin zafi damuwar ta mishi Yawa ganin lubna kiri kiri ta nuna tana son ganin yar uwarta wanda sauran maganar tata duk shirme yadauketa a farko sai yanzu da aka bude masa komai....
Kallonta yakeyi kamar yasamu camera bako kyaftawa cikin shock din da k'ara shigarsa,bayan na farkon da yashigesa tun lokacin da tafara basa labarin maganganun ne ke dawo masa akai kamar gabansa akayi komai hango yaron yakeyi a idanunsa,musamman inda tace sunce yana kama da Lubna da Norah mamaki ne yak'ara kamasa sosai yau tsawon shekara talatin da "yan kai basu tare da yan uwansu akan zaluncin wasu azzaluman mutane suna ta b'oyon kansu a wannan k'asa yau gashi rana daya Allah zai nuna nashi iko akansu dama mutanen dake kokarin b'oye su ga ahalin nasu wanda basu san dalilinsu ba nayin hakan duk da taimakon da suka musu na farko wanda kuma su shaida ne ba mutanen Ba Azzalumai bane na kirki ne.
A hankali cikin wani farin ciki da ya mamaye zuciyarsa ya furta tabbas wannan wanda suka gani bakowa ba ne face jinin......................................
Yaya Aliyu!!!!!!!!!!!! Ne
Dan tunda suka ce wanda sukagani ba fari bane tabbas daga tsatson d'an uwana ne domin shine baki acikin mu,sannan in na chan ka Ammar ne suka gani domin shine mai irin fatar yaya,dan mahir fata nace zance ko taki sai kuma jaririyar da muka bar ta aciki ita bamu san kalar taba.....