A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 14
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 14: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 14. Allah yakare mu daga kusantar zina🙏
3,365 words
Allah yakare mu daga kusantar zina🙏
A ba'ngaren sarki Ali kuwa tunda yakoma gida hankalinsa yagaza kwanciya ko fada bai je ba sai safa da marwa yakeyi akatafaren dakinsa dake sashen unni kuma kuma ya hana kowa yashigo masa sashen duk da yasan gimbiya hassanat da Amintacciyar masarauta kadai ne sai yan yansa ke iya shigo masa kai tsaye. k'arar wayar sa ce ta tsayar dashi da zagayen da yakeyi uwar dakin nasa daukar wayar yayi dan ganin mai kiransa khadijan hajiya yagani yabayyana a screen d'in,bakowa bace wannan khadija sai autarsu dake aure a kano picking call din inda cikin d'an tashin hankali take masa bayani bayan sun gaisa...
"(Hajiyar safkare) ce gimbiya halimatu. mahaifiyarsu Suce dake wurinta ta tada hankalinta sai tadawo zamfara yau saboda mafarkin da tayi na Abdul rashid dinta yadawo gida....
Hankalinsa Ne yakara tashi sosai sai dai bai bayyanar afili ba gudun kara tashin nata hankalin,A yanzu ma tana masa bayanin ne kamar zatayi kuka domin hajiya ta sako ta gaba,lallashinta yayi tare da bata umurnin taje tabawa hajiyar waya...
tafiya kadan tayi zuwa hadadde d'akin da hajiya take bayan tayi sallama an amsa mata wayar ta makala mata a kunne A hankali yar tsohuwar dake kan sallaya tana ta jan charbi tasanya hannunta ta dafe wayar da mama dije ta daura mata sunan da yaran ke kiranta dashi kenan.
Muryar Sarki ali ce ta doke kunnenta sai ta fashe da kuka wanda dama haka yake fama da ita kullum indai zai kira ta,ta dalilin abu guda biyu muryoyin su umar da Abdulrashid take tunowa a duk lokacin da tayi taji muryarsa Takance Ali Allah kabayyanar da haske acikin duhu dan haka take kiransa..
Dama dalilin da yasa tazabi tadawo wurin mama dije da zama shine sanadin tun lokacin da aka nemi Abdul rashid aka rasa taji masarautar ta ta isheta da ma jihar har zuwa lokacin da umar yakone da iyalansa alokacin da mama dije tayi Aure a garin kano sai tanemi takoma gurin ta da zama babu yadda sarki Ali da rashin yan uwansa yadamesa zaiyi haka yabar ta ta koma chan da zama sai dai aka rufe sashen ta domin yafahimci kamar hankalinta zaifi kwanciya chan, kuma duk abunda mahaifiyarsu keso shine abun da suke so tun suna yara.
Kuka take sosai cikin jin radadin abunda baka da yadda zakayi dashi sai dai fatan Allah yayi maka mafita yakawo maka karshen komai,acewar ta muryoyinsu duka iri d'aya ne tun suna yara shine dalilin kukan nata sai aduk lokacin da suka yi magana dashi.
Ta bangaren sarki Ai shima hawayen kawai yake zubarwa na tausayin mahaifiyarsa dake cikin damuwa cikin raunin ta da yafara bayyana wanda take kokarn boyewa na shekara talatin da takwas dan ma Allah yasa hajiya macece mai tawakalli dasai hawan jini yakamata da wasu cututtukan.
Bayan tagama kukan yakara lallashinta yana furya Umma kiyi hakuri inaji ajiki na komai zai bayyana in sha Allah kuma komai yakusa zuwa karshe wanda duk suke da sa hannu akan cutar damu Allah zai tona musu asiri,kanta kadai take iya d'aga masa cikin kara jin natsuwa na saukar mata,mama dije dake zaune bakin gado itama taci kukan ta dan yau dukkaninsu abun yadawo musu kamar sabo sai kallon mahaifiyar tata takeyi cikin tausayi...
hakuri yakara bawa hajiya tabar tafiyar sai gobe za,a turk private jet yadauko ta saboda ynzu baisauko ba yana kasar paris da wakillan kasuwancinsa sukaje taro na manyan yan kasuwa da suka wakilcesa,Amma zai sauka da daddare.
©°••••••••••••••••••••••••••••••••°©
FIRST LADY🙌
A bangaren hajiya kuwa tacije tsaf bata son jirgin a mota take so tazo dole ba yadda ya iya Ya amince maata da zuwan ta mota sallama sukayi ta mikawa mama dije wayar tare da sakar mata haraara na kiran sarki Ali da tayi taso ace sai dai aganta tsididit a masarautar,wayar mama dije takarba tana mai sunkuyar da kanta cikin d'an sakin murmushi domin tasan dalilin hararar da tasamu D'akin ta fice cikin d'an rashin gaskiya..
BAyan fitar tane sai ga wani kiran na sarki Ali yana mai sanar mata zai turo mota biyu yau gobe tunda sassafe sai su taso tunda bata son tabiyo jirgin,ki shirya mata kayanta touh Hamma tace,tambayar ta yayi ina inayah?tana makaranta tabasa amsa dayake ma yau suke yin hutu shiyasa bata dawo da wuri ba,kigaishe ta ya furta cikin kulawa sallama sukayi tana furta zataji
Tare da yanke kiran...
💫Fa'eeh Bg💫
FIRST LADY🙌
kai amma fa nayi kokari yau babatun manaji duk da bani lafiya kunsamu long page.. Kusanya ni a addu'ar ku ina fama zazzabi ne.
Kuyi sharing pls.
Kuyi muna like,da comment...🙏
https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free book* 📙
EPISODE1️⃣
PAGE3️⃣4️⃣
TYPING📲📲📲
*BUG*
©°•••••••••••••••••••••••°©
A bangaren Baba Adee ya isa gida lafiya inda ya tarar da su Halee sun dawo makarantar boko har sun chanza kaya izuwa na gida saboda ba,a islamiyya yau alhamis,khady na ma Halee fira itakuma tana ta wankinta na kayan Baba Asabe dake zaune agefen barandar tanashan redion ta...
Sallamar sa ta mik'ar da Baba Asabe daga zaunen datake tana kame kame,domin ita ko karar babur dinsa bataji ba,turus yayi ganin abunda baiyi zato ba waton dai har yanzu bata bar cutar Da yarinyar nan ba ya furta acikin zuciyarsa,
su Halee ne dake masa sannu da zuwa ne suka dawo dashi dai dai daga maganar zucin da Dayakeyi Amsa musu yayi yayi cikin d'an sakin fuska sannan dakin sa bayan ya ajiye ledar da yashigo musu da ita.
'Baba Asabe da batayi tsammanin dawowar sa yanzu bane tasha jinin jikinta tana masa sannu da zuwan da yak'i Amsa mata,Baba Adee ne bayan shigar sa dakin nasa ya kwala kiran Lauratu ! Lauratu ! Amsa masa tayi jiki Amace dan tasan yau ta k'ara ballo ruwa, aiko shigar ta dakin kenan yahau ta dafad'a dan me zata bar Halee cikin wannan uwar rana rana wanki gashi tasan bata isasshiyar lafiya,take ana jikinta zai iya chanzawa sai kuma ankoma yawon ganin likita.
Shiru tamasa shikuma yacigaba da fadansa yana furta kiji tsoron Allah Lauratu yarinyar nan kinsan cewa Wata babbar Amana ce agurin mu karki bari ubangiji yakama ki da laifin cuta mata dan bata miki komai ba hasalima akoda yaushe cikin kyautata miki take.
nasha fada miki irin son da nake wa yarinyar nan batun yau ba tabbas inajin ta Araina kamar yar da na haifa tawa tajini na,domin nafi jinta araina fiye da khadija saboda maraicin ta,yanzu ko dan ni baza ki rike ta Da gaskiya ba kamar yarcikin ki.
Baba Asabe dake jin fadan nasa a cikin kunnuwan ta kamar ta saki ihu take jin ya had'a da yakeyiwa Halee dana Khady ranta ya mugun b'aci sosai sai dai ba halin nunawa, A hankali kamar zancen yashiga kunnenta ta fara basa hakuri tana furta ai Halimatun ce tace inbata zatayi ka tambaye ta kaji,ta furta hakan ne domin tasan Halee bazata tab'a karyata taba.
murmushin bakin ciki yasaki tare da girgiza kansa domin ya fahimci manufarta tanason kare kanta ne A hankali ya tunda kince ita tace kije ki karb'i wankin ki iyar da kanki ko kibawa khadija ko kira almajiran da kewankin.Amsa masa tayi da toh,sannan ta fice daga d'akin tana guna gunai kasa kasa cikin ranta afili kuwa badamar fitarwa,Dai inda Halee ke duk'e cikin rana tana wanki wanda bayan fakon idon na Baba Asabe khady ta taso ta rika mata dan kayan nada yawa,jin motsin fitowar tane daga d'akin Baba Adeen ne yasanya khady runtumawa aguje zuwa d'akinsu wanda har sai da Halee tayi d'an murmushi duk da yanayin da take ciki na kuncin zuciya,domin kuwa khady bata mance da kashedin da tamata ba na inta sanya hannunta cikin wankin sai lakad'amata na jaki.....
ooh ni fa'izatu ke kam wannan Baba Asabe anyi futinanniya,har da yar son taki ma baki ragawa to kenan koni mai kwaso rahoton baza ragawa in ankamani kai aiko bari inyi takaina inkara boye kaina.😝
"ke ta furta bayan tsayuwar ta gaban Haleen ki Aje wankin nan ki kira min su idi suzo su idasa shi takai karshen maganar tana sakar mata harara Kinyi arziki Amma ko yanzu akwai wata rana zamu hadu zaki idasa aikin ki takara furwa Halee kasa kasa,A hankali Haee tajawo dogon hijab d'in blue dake mak'ale a igiya tasanya adan karamin dake jikinta cikin dan yanayin sanyin jiki tafice gidan wanda sai da takai zagayen gidan sannan wasu hawaye masu zafi suka samu damar silalo mata tana sharar zufan data tara acikin ranar mai kyaifi da tasha,share hawayen take da gefen hijab dinta aranta tana Addu,ar Allah yabayyanar da iyayenta in suna raye da ahalinta baki d'aya,sannan tafice bayan tsai da hawayen nata.
Wasu yarane guda biyu daKe zaune achan gefen barandar masallacun dakE unguwar tasu ta kyafato da alamar su zo,biyota sukayi har cikin gidan Alokacin Baba Asabe duk ta hada musu kayan dan fita dasu idi almajiri zasuyi ,direct bohol din unguwar sukayi Domin idasa wankin bayan kwasar kayan.
Halee dakinsu ta wuce achan ta tarar da khady na assignment din da aka basu,dashigar ta d'akin ta fad'a toilet dan yin wanka wanda kuma achan cikin bayin ne ta darji kukanta kamar ranta zai fita gwanin tausayi khady tayi tayi tabud'e kofar ta lallasheta ta yi banza da ita hasalima da ta murd'a handle din arufe kofan yake ansanya sakata dole takyale ta tayi mai isarta..
Wankan ta tadauro tare da dauro alwallar la,asar bayan ta lallashi kanta
'karar bud'e kofa ne yasanya khady bud'e idanunta dake rufe wanda dama tsumayin fitowarta takeyi bare datas
Ji shiru.kyakkyawar Halee ta kalla datayi jawur da ita sosai abun ka da jar fata abun sai yabaka tsoro yadda eyes dinta sukayi luhu luhu dasu,gab gab d'in da jikinta keyi ne da khady tagani yasanya ta mikewa da sauri tana taimaka mata tazaunar da ita kan katifarsu tana rika mata kayan ta da tacire a toilet din,taba goshinta khady tayi rau da zafi taji shi,mai ta d'auko ta shafa mata alallausar fatar ta ganin alamun bata iya komai sannan ta fito mata da kayan da zata saka mata mai dan nauyi wanda zai taimaka wurin rage mata sanyin jikinta,dakyar ta amince ta taimaka mata ta sanya mata kayan jikinta zuwa wata rigar yadi mai d'an nauyi da rigar sanyi mai hula da dan hijab din ta baki.
(hijabban gado)😜hijaban gado mana kullum mutun cikin hijab bawani shan iska Allah ni masu wannan dabi'ar tausayi suke bani da dariya kai bawa kullum kamar matar liman ko matan malan ai suna cirewa agaban malan bare ke da ba matar mai sittin ba😂su Halee araga wa kai sako 💬ne sako ne fans nata ku isar dashi koma samu hasken💡💡
💫FA'EEH BG💫
FIRSTLADY🙌
ALLAH YA JIKAN IYAYENMU DA RAHAMARKA YAA ALLAH WAYENDA MUKA RASA🙏😭 DA WAYENDA KE A RAYE🙏
turare tasanya mata sannan tabata paracetamol dan tasamu relief dawuri da kuma bacci,Bayan sunyi rigima gurin shan maganin dan bata son ganin ko kwalin kwayar magani ne Ko allura,tamata dolene wurin shansa ta hanyar furta mata zata sanarwa da (daddy)Baba Adee dakyar ta karba tasha tana ya mutsar fuska.
Allah sarki Ashe muna😩 da yawa Halee shan magani ko wahala😾Allurar ma basauki kai Allah yakara muna lafiya mai inganci🙏
Bargo khady ta lullub'a mata tana mata Addu'ar samun waraka kamar yadda annabi saw💙ya yadda sahabbai suka samodaga garesa idan kaje ganin mara lafiya idan har ciwon bana ajali bane to za,a warke da yardar ubangiji bayan Ankaranta ta sau bakwai akusa da marar lafiyar wannan Addu,a sahihiyace domin tazo alittafan hadisi da dama irin su umdatul ahkam,hakkul mubin,gulubul mara .Da dai sauransu...
Ga Addu,ar kamar haka ..............
*"AS ALUL HAHUL AZIM RABBAL ARSHIL AZIM,AN YASFI YAKA*"Face sai Allah ya yayema masa,sahih ne abu dawud ya ruwaito sa..
wannan lamirin namiji ne in macece za,a ce anyash fiyaki...
kiduba acikin kitabul hakkul mubin na hud'u hadith no.100:cif
a page 10.
zaki samu dayar addu'ar ma wadda annabin yakasance yanayi in yaje ganin mara lafiya apage din..
Allah ne mafi sanin daidai
Allah yasa mudace🙏
Sannan tacigaba da solving din assignment dinda aka basu yau inji malamin maths,A hankali dake kwance tana kallon yar uwar tata cikin so da kauna, cikin yanayin zazzabinta bacci yakwashe ta
*WACECE HALEE*
cikakken sunanta halimatu sadiya umar,tana zama garin bungud'u ita kamar Amana ce a gidan Baba Adee domin kuwa halee yar tsintuwa ce tsintuwa mafi daraja agaresa shiyasa kullum yake jin tausayinta na rashin bayyanar iyayenta,Halee dai kyakkyawa ce takarshe ga shagwab'a da saurin kuka.Halee tasamu gwargwadon karatun arabia duk da yadda Baba Asabe ke addabar ta duk da wani lokcin bata samun damar tafiya islamiyar ma bare boko,ta haddace wani kaso acikin alqur,ani mai girma,kuma tayi manyan littafan fiquhi da hadisai da sauran su domin Halee akwai hazak'a tako ina da ace tasamu bground na kwarai da sai ta fi haka.Halee takasance bata da yawan son magana shiru shiru ce inkaga maganar ta mai tsawo da to Baba Adee ne ko khady,tana musgunawa sosai agurin Baba Asabe sai kuma Allah yasanya mata wani irin hakuri na ban mamaki da tausayi,Baba Adee yanason ta sosai shiyasa komai zai musu ita da khady yakeyi shiyasa har a makarantarsu ma kawayen su da wasu daga cikin malanmansu yan biyu suke kiran su duk da jin ba sunan uba d'ay suke amfani dashi ba amma ganin yar kamar dasuke da juna da kuma shakuwar da tsakaninsu sai ba,a dauki Banbancin sunan uban da komai ba sai suka barshi amatsayin may be sunan wani ne na familynsu take amfani dashi,suma halee su sun san suna kamar dan wasu lokuttan sukan tsaya gaban madubi sudubi kansu tun lokacin da aka fara furta musu suna kama amakaranatar dan kara tabbatarwa dakansu sai dai suma basu daukesa komaiba,Suna kama kam tabbas sai dai banbancin dake tsakanisu na fata ita Halee fara ce tass kamar farin nan na larabawa mai kyau kamar ka k'wanta jini ya fito sabanin itakuma khady black ce ko ince chocolate irin mai kyau d'in nan,khady bata da bata wani saurayi agefe duk da yadda samarin ke musu turu turuwa saidai suna bin umurnin Baba Adee ne da yace sai sungama secondry sannan zasu fara tsayawa da wani wanda itakam dama halee bata tab'a tunanin tasamu damar tsayawa da kowa ba domin acewar basu ne gabanta ba,iyayenta sune abu nagaba da takeson ganawa dasu idan har suna raye awannan duniyar.
wannan kenan agaba zan warware muku komai munma kusa kaiwa inda yadace kuji asalinta da yadda akayi tazamo yar ysintuwa mafi daraja agurin Baba Adee har yake kiranta da Amana agaresa.
©°•••••••••••••••••••••••••••••••••°©
©°•••••••••••••••••••••••••••••••••°©
💫FA'EEH BG💫
FIRST LADY 🙌
IN THE BUILDING👓 EYYH DJ KARAMUN VOLUME💃💃
au ashe typing 📲nakeyi Allah yashiyeni🚲🚲
Allah ya muku Albarka fans💋👏👏
*KHADY*
itama yakamata mubata nata shafin,ko dan yadda tadamu da Haleen mu.
Khadija Abdul rashid shine cikkaken sunanta Haifaffiyar garin bungud'u lg a unguwar sarki mahaifin khadija Abdul rashid ana kiransa da Da Baba Adee inji mutanen unguwar yara da samari yana aiki a talatar mafara wanda duk kwanakki yake dawo wa gida yana aikin taimakon likitoci a chan wanda ada kawai matsayin warda servant security ne mai tsaron kofa sai kuma aka fahimci yana da wani talent kan abunda yashafi tiyata da dai sauran ayyukan likitota sai suka dawo dashi cikin ward din yana taimaka musu da wasu ayyukan,sannan yana d'an madaidaicin kanti achan na saida provision.
Khady ita kad'ai Allah yabawa su Baba Adee da Baba Asabe wadda sunanta na asali yake Lauratu sunyi Auren soyayya da Baba Adee Alokacin yaje yin aikin noma agonar mahaifinsu a kauyen na bungud'u mai suna (gada) gada gadajen Allah kauyen akwai dadi arado.
Ya had'u da ita ne achan lokacin takawo musu tallan fura tun alokacin soyayya mai zafi ta shiga tsakaninsu wanda dan danan manya suka shiga maganar tasu.
Anyi Aure Amarya ta tare agidan da mahaifinsa yabasu wanda sai bayan kusan shekara biyar Allah yabasu haihuwa ta ya mace inda yarinya taci suna khadija,dan shine sunanda Baba Adee ya zab'a duk da saida akayi rigima da mutuniyar fafur bata son sunan,tun alokacin Baba Adee yafara takawa abun burki yakuma san Lauratu bata mutunci dama lunbu lumbu tamasa,take kuwa shima ya bure mata.
Khady itama dai kyakkyawa ce yar black beauty kamar yadda nasanar muku alabarin Halee sai dai kuma ta d'an d'ara Halee girman jiki, A yanzu shekarar ta goma sha takwas a duniya da yan watanni sabanin halee mai shekara goma sha tara cif da wata biyar.
Khady takasance tana mugun son HAlee tana jinta kamar yar uwar ta tajini tasha furta ma Halee ni inajifa kamar tsatso d'aya muke dake inaji jininki na yawo ajiki na sai dai kawai Halee tayi murmushi tace nima haka. duk wata Damuwar halee tasani sai dai bata yadda zatayi,dan lokacinda ta fahimci itama Halee ba innarta ta haifetaba sai tausayin ta yadarsu azuciyarta mai girma wanda shine yake tasiri haryanzu.
itama gwargwado tasamu ilimin arabiya dana boko dan kamar ma komai d'aya sukeyi da Haleen duk da yadda Baba Asabe ke son sakanta ta hakan ya faskara itama tasamu gwargwadon tarbiyya awurin Baba Adee.ta fannin samari babu dokar dai ta mahaifinsu na aiki.
WAZAI MINI TYPING💂
muje zuwa🚲🚲
*GUSAU*
A bangaren sarki Ali yasanarwa da Unni game da dawowar Hajiyar safkare tayi farinciki sosai dan danan takira Ummi tasanar mata farincikin su bai b'oyuwa awannan rana take aka fara shirye shiryen gyara mata sashenta da yakasance arufe duk da duk bayan dan lokaci ana gyaransa,ayanzu ankara kimtsa komai dan jiran dawowarta wanda dama shine kowa ke tsumayi domin hajiya mutunce mai kima a idon Al ummar masarautar don macece mai son mutane.Duk wanda yaga irin gyaran da akeyiwa sai yaji fariciki domin kuwa sun san tabbas dawowa zatayi.UMMI ce takira Ammie dake k'asar jidda tasanar mata,Ammie tayi farinciki sosai jin wannan abun farinciki take itama anan tasanarwa da Ummi zata dawo itama karshen wata sai dai ta gargad'i Ummi da kar tagayawa kowa tanason basu suprise ne,farin cikin da Ummi tashiga baya faduwa yanke wayar sukayi cikin farinciki..
labarin dawowar hajiyar safkare ya karade masarauta har ya isa kunnen gimbiya fulani matar tsohon sarki mai rasuwa wanda itama yanzu mustapha Yashigo yake sanarmata bata wani nuna jin dadinta face Addu,ar sauka lafiya datamata,tana mai furta ita taje ita tadawo bayan fitar mustapha daga gidan,tana mai kyab'e baki irin yadda tsofaffin masifaffun nan keyi Wayenda suka ga jiya sukaga yau.
FULANI TAMU••••••••
Shima muhammad( malan) dayaga irin gyaran da akeyiwa sashen bakinsa yashiga tabewa yana wucewa sashen fulani da shigarsa ko sallama babu ya furta Fulani ki tsaida khairyya daga zuwa gidan nan bansan ubanda zatazo yi ba kawai dan hajiya zata dawo shine itama zata wani kwaso kafafu,kallonsa kadai takeyi tana taunar goronta,cigaba da magana yayi jin bata tanka masa ba.ta kirani fa wai inturo mata kud'in mota saboda bata dasu kuma mijinta baya nan,tafiya kamar ta dole natambayeta mezatayi da kud'in wai mota zata shigo tazo tarbon hajiya,tunda hajiya uwar tace yakai karshen maganar cikin jan guntun tsaki,nace bazan turamata ba indai dan hajiya zatazo shine dan iskanci takira yaya mustapha dan tasan dole ma ya tura mata yakai karshen maganar cikin b'acin rai.
Kallon sa kadai keyi bayan gama jin zancen sa rai b'ace.
Mikomun wayata gata chan kan madubi ta furta cikin wani bacin ran da yakara taso mata,wayar ya mika mata tasanya gilass dinta tana mai dialing numban da aka saving da Auta,ringing biyu ana uku tad'aga cikin shesshekar kuka khairiyyah ke furta na shiga uku fulani abun na alhj har ya kai yafara shigo mini da karuwai cikin gida kuka take kasharban har tana shid'ewa saboda bak'incikin dake cin zuciyarta,fulani ma data kira da niyyar masifa dakarfi take raunar goronta cikin bakincikin da ke turneke ta,sai kuma tasamu kanta da yin shiru, dan tun Auren khairiyya shekara talatin yanzu da yan kai babu cigaba,kuma shegen mijin yaki sakar mata "yaa wanda kuma ita dakanta ta had'a auren rayi danasani marar iyaka ga rashin haihuwa da bayayi ga kashin da yake bata da rashin kula domin ko abinci wannann dakyar khairiyya take samu duk da kasancewar alhjin mai tarin dukiya.