A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 23
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 23: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 23. A hankali yake takonsa har yakai k'ofar bedroom…
3,361 words
A hankali yake takonsa har yakai k'ofar bedroom nasa d'ai daga cikin k'ofofin Dake ajere yabud'e inda wani daddan d'an k'amshi yaziyarci hancinsa da yasanyasa Lumshe manyan idanunsa Yana sauke su acikin had'add'en bedroom din nasa,Bedroom nasa Shima babbane d'aki ne Wanda yak'unshi makeken gadonsa da wardrobe Mai aiki da controller da taji madubayye ta ko Ina sai walk'iya takeyi kayan d'akin milk ne Shar har labulayye d'akin Masha Allah komai yaji zam zam.
Da shigarsa d'akin ya fara rage kayan jikin sa guntun wandon sa kad'ai yabari.
wani lafiyayyen towel fari k'ar Mai taushi ya jawo bayan bud'e sip din tasa ta hanyar yin amfani da controller nata,A K'ugunsa yadaura inda towel din yakara haskaka surar jikin sa wadda ta Bayyana ta k'ak'k'arfan namiji Mai jini ajika dogo Mai siffar k'arfi kamar d'an wrestling six spacks dinsa sun Bayyana irin na tiger shroff,kayan da yacire ne direct ya wuce dasu toilet,toilet din Masha Allah Shima ya had'u ba kad'an ba fankacece guda,Dan Yana yanayi da na gidan su na India. Kayan yasanya acikin washing machine nasa k'irar k'asar Chinese,busar dasu yayi bayan sunyi tass Dama bawata daud'a ce dasu ba,wankansa yayi acikin had'add'iyar shower dinsa wadda ko Ina tana iya isko ka tare da wanke kwantacciyar sumar sa Mai laushi, wadda gyara ya ratsa ta da sabulu Mai Sanya k'amshi,sannan yak'ara d'auro wani Sabon towel pink Dake mak'ale a hanger d'in toilet d'in,cikin d'ai daga cikin had'add'un towel d'in Dake mak'ale agurin tare da d'an k'aramin towel Wanda yake Dan goge kansa.
Kayan da ya wanke yad'auko a hannunsa da'ya,d'aya Kuma rik'e da towel din da yake goge kansa dashi,Bayan ya fito ne ya a je kayan akan had'add'en gadonsa k'irar Italy.
tsaye yake akan Babban mirror n Nasa Yana goge sumar kansa wadda take Shan gyara Ako da yaushe,Bayan yagama shafe kannasa yasanya Masa mayukkan Dake Jere birjik akan madubin nasa na gyaran Kai masu tsada bayan taje sumar inda take kuwa tad'au shekiyi gwanin burgewa Bayan ya gyara kan nasa yajawo mayukkansa na jiki masu tsada wayenda ke k'ara haskaka chocolate colour skin d'insa,yashafa adukkanin sassan jikin sa, kyakkyawar fatar sa sai shek'i takeyi gwanin burgewa ko Ina lui lui Masha Allah tafen hannayen sa da k'afafun sa sai walk'iya sukeyi,tsadaddun turarrukansa yajawo ya feffesa na body spray masu dad'in k'amshi,man bakinsa ya shafa (lipsbalm)Wanda ya K'ara haskaka kyakkyawan pink lips dinsa,tare da kyakkyawar fuskarsa Mai cike da kwarjini gwanin burgewa. Bayan yagama'yan gyare gyarensa da yan shafe shafensa,Ya Sanya kayan da ya wanke acikin sip din sa bayan ya bud'e ta,domin shi mutun ne Mai tsafta Baya son ganin kowane irin tarkace a inda yake,yasansu agefen da ake mak'ale kayan da ba ayi ironing nasu ba.
kayane birjik a cikin wardrobe d'in tun daga kansu vest da panties na maza da short trouser,jeans da t-shirt da suit sai, harda sashen da towel Suke da handkerchief,sai kayan mu na Hausa tundaga kan kaftani shaddodi kala kala irin su gizner,meter d.s ,da yadudduka zubin k'asar Morocco,dakuma had'add'un huluna kala kala duk Wanda kuka San maza na sakawa Babu Wanda babu agurin komai atsare gwanin burgewa abun ba,a cewa komai sai Wanda ya Gani.
Wani tattausan yadi ash colour ya Ciro mara kauri da farar vest da short din sa black..shirinsa yake Yi Ahankali cikin yadin inda ya fito tsaf kamar kasace sa ka gudu dashi kyakkyawar fuskar nan tak'ara haske kamar tauraro acikin taurari idan ka kalle sa Sau d'aya sai k'ara saboda yadda yadin ya k'arbe sa yayi fitting din sa sosai kamar wani ango.
Towels d'in da yayi amfani dasu ya Sanyo acikin washing machine bayan ya ciresu.
Turarrukansa masu k'amshi yak'ara fesawa ajikinsa Yana k'ara Duba kyakkyawar fuskar sa Dake ta shek'i acikin madubi ganin yadda yadin yazauna ajikinsa kasancewar baicika Saka irin wayen nan kayan ba,lakace tsinin hancin sa yayi da dogon ya tsarsa najin wani yanayi Dake shigarsa na farin cikin dawowar sa ga ahalinsa gaba d'aya Yana sakin wani narkakken murmushin da yakusa sumar dani.💃💃💃💃
*Kai fa'eeh Arage k'arya haka*🥵🥵
Ai shi gida na da banne..✍️✍️ Yo dama ai kowa yabar gida gida yabarsa A halinka sune komai naka malan a duk inda kaje ka dawo sune dai...
Nigeria k'asar mu tagado muna cikin ta har ......💃💃💃💃💃💃💃🚴🚴🚴🚴yau da Banda gobe but wani sati zamu koma india😂😂😂😂
Allah kayafe muna🤲🤲
# Maman Abbah # Maman Muhammad # sis Ayeesha Abdullahi Ina godiya da kulawar ku Allah ya bar k'auna ✍️🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹❤️
*If you have any questions* *U can chat me on my telegram account* *Via dis number* *0806905946*
Kuyi comment please Kuyi sharing Kuyi like.🙏🙏🙏
💫A MAFARKI NASANTA💫 I know her in my dreams By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Firstlady 🙌🙌
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free* 📙
EPISODE1️⃣ PAGE4️⃣7️⃣
Idan Baki karantaba ki fara kar abaki Iabari yar uwa,littafin 📚📚📚 💫💫💫AMAFARKI NASANTA 💫💫💫nadabanne Dan haka nake k'aunar wannan book d'in kasancewarsa haka da yanayin siffar littafin da yadda yazo mini nida masoyansa...✍️✍️ Inkimason ki tabbar da zancena kawai ki fara bibiyar alkalamina✍️✍️✍️ ✓✓✓✓✓✓✓✓✓
TYPING📲📲📲
\\\\\\=\\\\\\\=\\\\\\=\\\\\=\\\\\\=\\\\\=\\\\=\\\\\
A b'angaren Aj Shima Bai zarce ko Ina ba sai A bedroom dinsa D'ayan d'akin Dake kusa Dana Dr.Ammar... Duka yanayin d'akin nasu d'aya ne sai dai kala ce ta banbanta,nasa kayan d'akin purple n lighte da labulayye purple masu haske,wankansa Shima yadauro tare da Alwallar sallar azahar.
Dr.Ammar ne ya fito cikin Shirinsa anan falo ya tarar da Dr.Aj da har ya yashirya cikin blue yadi,da hula jaddara black Mai kyau, da takalmi bak'ake irin na Dr.Ammar.
Kallonsa Dr.Aj yayi Yana tab'e Baki na Rashin ganinsa da hula Bai Yi mamaki ba Dan yasan dama tun suna k'ana bayason Sanya hula akansa acewarsa takurasa takeyi wai.
Cikin tafiyarsa ta mazan jiya ya Furta"kataso muje ko in wuce in barka nan Yana maganar bisa ga har yakai bakin k'ofar fita falon,Aj Dake zaune akan cussion speechless ya Furta "tafiyarka cikin Jin haushin sa,Dan tun d'azu yake jiransa duk da yasan cewa Yana chan Yana shiriritarsa,ganin cewa ya rigasa tasowa dining amma har yanzu Bai shiryo ba.
Hararar bayan sa Dr.Aj yayi tare da tasowa ya biyo bayansa.
Shikuwa Ammar murmushi kad'ai yayi Yana Ida ficewa daga falon,fitowar Aj tasanya Dr Ammar Dake jiransa su wuce tare abakin k'ofa.
Dr.Aj da ya fito ne yayi kamar baiga Ammar ba yacigaba da tafiyarsa,murmushi Dr.Ammar yak'ara saki ganin Abunda Aj yayi Masa,Shima Bai kulasa ba kawai yacigaba da tafiyarsa,har suka jera atare suka Isa Babban falo.
Koda Suka iso falon sun tarar da su Hajiya dasu Unni zazzaune su Dady soja dasu Mahir,Abadallah duk sun wuce masallacin Gaida su sukayi,sannan suka wuce masallacin fada inda dama already kowannen su yad'auro alwallar sa Dan gabatar da sallar azahar.
Bayan dawowar su daga masallacin sun tarar da mama dije ta iso daga garin Kano itada Inayah,su Nisa sunyi farin ciki sosai da zuwansu.
Mama dije ce bayan tayi masu Ammar Barka da zuwa take tsokanarsu,yanzu Kam tunda andawo gida samarin Aunty sai afito da matayen Aure tunda Allah yakoro muna ku,Dan haka take kiransu dashi inzatayi musu irin wannan wasar sbd gimbiya Laila..,takai karshen maganar tana sakin yar dariya..
Cikin yar dariya Dr Aj ya Furta Aunty dije kizab'o mana matayen kawai Dan duk cikin mu nan babu mai budurwar bare Akai ga mag...yakai k'arshen maganar Yana susar kansa bayan yad'aga hularsa irin na Jin kunya tare da sakin yar dariya...
Dukkani dariyan sukayi ta maganar Dr.Aj,shiko Dr Ammar ko tankamata baiyi ba Bai nuna yasan abun da ake magana ba afalon ko mama dije tayi magana, Hajiya ce ta Furta"Kai kafi k'arfin ka amsawa uwar taka,shegantakar taka har ta shafi uwayenka takai karshen maganar tana harararsa ..
Murmushi kad'ai yayi daga jinginen da yake akan hannun kujera batare da yabawa hajiya Amsa ba sannan A hankali ya Furta "Aunty dije kibar hajiya lokaci na zuwa" To Allah ya nuna munashi lafiya ta Basa Amsa,Amin dukkaninsu suka Amsa. murmushi tayi Jin ya Furta tabar hajiya.. Hajiya kuwa wata uwar harara tasakar masa tare da kyab'e Baki tana cigaba da Jan charbin ta murmushi dukkanin su sukayi na hararar.
Inayah ce da yanzu ne fitowarsu daga d'akin Nisa ta rugo da gudu ta rungume Ammar cikin farin ciki tana Furta sannu da zuwa Yaya A,Amsa mata yayi da yawwa cikin sakin fuska har da yimata Yan tambayoyin kulawa. Gurin Dr Aj takoma Shima ta rungumesa tana Masa sannu da zuwa cikin farin ciki kamar yadda tayiwa Ammar shima Yan tambayoyin yayi mata na nuna kulawa agareta.
Bayan takoma tazauna ne inda su sumy Suke ne yad'aga idonta sai acikin na Abdallah wani irin mugun kallo yabita dashi na kishin rungumar da tayiwa yayyen nata,kawar da kanta kawai tayi fahimtar kallon da tayi mata.
Aj ne ke kallon sashen da su Nisa Suke,shi har mamaki yake,magana yake azuciyarsa shin wai har yaushe sukayi wannan girman,girman su yabasa mamaki Dan sun Dad'e basu lek'o Nigeria ba, duk da suna video call dasu Amma ganinsu azahirin girman da sukayi na Fili yabasa mamaki matuk'a....
To kabasu mamakin su man🚴🚴🚴😂da tsegumi😂😂😂😂🥵
Saurin kawar da kansa yayi Bayan kallo ma kansa da yayi tudun Yan madaidaitan breast din Nisa da suka taso akan akan doguwar rigar tata ...
Dr Ammar Dake kalle dashi ne ya girgiza kansa kawai Yana sakin murmushi Akai kaice tare da yiwa k'anwarsa fatan samun soyayyar Abokin nasa Kuma d'an uwansa.
Firar yaushe Gamo suka cigaba da ita ga ba d'ayansu,Anan sarki Ali yasanar da ginin Babbar Asibitin da ya gimawa su Ammar D'in dukkaninsu sunyi farin ciki sosai,har su Unni da suka San da maganar yasanar musu wani sati za'a bud'e Asibiti..
>>>>>>>>>>>><<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>> Ranshi ab'ace yake magana ta waya da Wanda ke akan layin Kiran..ya akayi Baku same su ba kuka bari suka sub'uce muna, wannan maganar banza ce ace operation bai yuyu ba,tun farko sai da nasanar muku tun A Airport ku farmaki Yan banzan ku kashe min su shida Mahaifin nasa,ta D'ayan b'angaren ne aka Furta masa Ai uban nasa Bai je hililln jirgin ba,inda Muryar wani bafullace ke fidda wannan sauti cikin yar damuwa da b'acin Rai.. Ta D'ayan B'angaren malan ne yak'ara furta yanzu kenan wannan damar ta sub'uce muna mun Rasa wannan Babbar damar yakai karshen maganar cikin kunar Rai kamar kamar zaiyi aman wuta.
Shima bafullacen ta b'angaren sa yak'ara Furta "arado oga baka ga manya manyan shojojin Dake a Airhort ba, 😂wai Airhot Kashan bamuje da yawa ba mu biyar kad'ai muka she dagani shai k'ira da jan maje da Mai Adda,da zarto,Dan bamuyi jaton zashu mana haka shojojin arado baka ga makamanshu ba, shunfi namu arado Kuma anzuba shu gurin da yawa kamar shuna gadin wani agurin..
Cikin b'acin Rai ya da d'aga murya ya Furta " wai su wane ne Suke muna zagon k'as a suwaye,duk wani shiri namu suna kan gaba suna rusa muna shi,suwaye muna zagon k'asa Mai muni agare mu ya iyar da maganar cikin k'araji tare da Yanke Kiran...
My team yayi dialing cikin b'acin Rai... bayan d'aga Kiran ne muryoyin su suka fara Bada sauti cikin tashin Hankalin Jin muryarsa Jin Ya Furta kusameni gidan shak'atawa ta yanzu,oga lafiya dukkanin su Suke tambaya inada ya Yanke Kiran batare da yabasu Amsa ba...
Ko minti ishirin ba'ayi ba,sai ga wasu aranayen jif sun shigo gidan bayan wangale musu da aka Yi,parker motocin sukayi a inda yadace.
Babban falon dukkaninsu suka dosa cikin tashin hankali na Rashin sanin Abunda Yafaru Wanda sak'e sak'e yadabaibaye zuciyarsu na dalilin Kiran gaggawar da yasame su...
Samunsa sukayi tsaye ya rungume hannaye abayansa Yana sabbatu shi kad'ai Yana Furtawa shin wannan Mai muna zagon k'asa taimakon mu yake Yi ko cutarmu,a iya binciken danayi su wad'annan Yan sandan da muka kashe kosu basu San dalilin dayasa aka sanyasu k'one gidan ministan (S.I.C) ba da iyalansa Sun dai bi umurnin sane kowaye tabbas akwai Wanda yakeda sirrin mu Bayan (S.I.C) minister,dole muk'ara tsaurara Al amurranmu...
Minister iyaka Muradi ne Dake da mugun tsoro ya Furta cikin d'an tsoro da tashin hankali kardai ace fatalwar minster Umar ce tadawo Dan d'aukar fansa duk da bamu muka k'onasu ba,dukkaninsu dariya suka Sanya duk da tashin hankalin da Suke ciki Banda malan,Dan maganar tabasu dariya
Senator Jamil Babuga ne ya Furta haba kaiko minister aimu ko fatalwarsa tadawo muba Abunda zata Yi muna Kai zata Nema tunda kaine d'an rahoton mu Kai ne Mai yimusu kutse da lamarin su Kai da captain Anas Lemu yakai karshen maganar Yana dariya,Shima Captain Anas dariyar yayi Yana Furtawa senator Jamil ai za,a fara dakai Dan kaima Mai laifine,Emir Kabir Saraki ne yadakatar dasu tahanyar Furta ba wannan ba,yanzu dai oga meye abunda ya faru...
Cikin d'an Yana Yin hasala malan yazayyane musu komai Akan farmakin da yasanya Akaiwa Sarki Ali Da Dr Ammar,inda yasanar musu sojojin da akace anbaza awurin Wanda shikansa abun yad'aure Masa Kai na tunanin ubanda ya turo sojojin,dukkaninsu sunji faduwar gaba sosai musamman captain Anas Lemu Dan basu Yi zaton haka ba,Kuma tabbas da gaskiyar ogan nasu akwai wata ak'asa duk agamata tabbas akwai Wanda yasan da Shirin ogan nasu,duk da kosu bai sanar musu da Shirin ba,Dan bazasu manta da yadda wanchan karon aikin da suka Bada da hannunsu ya chanza ba..
TWENTY TWO YEARS BACK .... WAIWAYE ADON TAFIYA...
A chan Baya...
K'ungiyar "Yan taadda ce da tayi shura ajihar zamfara dama wajajen zamfara ma'ana k'auyukkan zamfara,wadda kusan kullum sai an watsa labarin sunkashe mutane sun tada k'auye,sun sace dabbobi da dukiyoyin Al umma sannna sunyi kidnapping na bayin Allah,Ako dayaushe fama akeyi dasu har yanzu Allah Bai kawo k'arshen su ba..
A bunda ya faru achan Baya......
Cikin k'ungurmin daji ne da ya kasance d'ai daga cikin manyan dazukkan Dake cikin jihar zamafara Wanda Namun Daji kad'ai ke rayuwa agurin ada, Wanda a yanzu Kuma b'arayi suka maidasa mafakarsu,suna rayuwa aciki su wayen nan "Yan ta daddan. Zazzaune Suke akan wasu kujeru su biyar oga Afarkon layi,sai senator Jamil Babuga da captain Anas akusa dashi,sai emir Kabir Saraki,sai minister Isyaka Muradi,dukkaninsu face mask ne afuskar su sai wasu irin mutane dazasu Kai dubu yawansu kewaye dasu da manyan bindigogi da sark'okin albarushi shigarsu Babu kyan gani kowa yasha uban rawani kamar wasu sarakuna wasu bula wasu bak'i sai warin suke tashi agurin da warin tabar da Suke zuk'a da ya garwaye wurin Babu dadin shak'a..
Shigace dai Dake nuna alamar su tazamansu Fulani da zabarbarbawa,wasun su sun Tara uban gashi kamar ka kitse sa kamar dai yanayin mutanen Mali,gasu nan dai ba maganar kallo biyu saboda in ka kalle su har wani mazari jikinka zai dauka...
Oga ne yake magana,Yana Furta tabbas duk da yake d'an uwana ne zanyi maganin sa tunda har yanemi ya tona mini asiri a idon duniya ta hanyar bincikensa tabbasa bazan tab'a ragama Masa ba, duk abubuwa da na shanye akan gidan mu na wannnan sarautar datake mallakin mu wallahi bazan tab'a rufe idona akan wannan ba,tun lokacin da minister Isyaka Muradi yasanar Dani cewa sunyi akan wannnan k'ungiya binciken su zaizo kanmu Asirin mu Yana Shirin toniwa, Kuma duk Wanda aka bincike sa Asirin sa take yake bankaduwa a idon duniya,nayanke wa kaina da ya tona muna asiri,gara ayo mani kidnapping na D'an wana Umar da iyalansa in kashe da hannu na sannan in hau karagar mulkin dayake tak'ama da ita shida Wansa,wadda nadade Ina mafarkinta tun kafin rasuwar Mahaifina,Dan shiru yayi sannan ya cigaba da magana Yana kallon wayen nan k'azaman mutanen Ina ga sunyi Rabin shekara jikinus baiga ruwa ba saboda tsaabar warinsu... Na Baku damar ku shiga har fada duk yadda zakuyi ku yo kidnapping nasaa shi shida iyalansa,Amsawa sukayi da zaka ga aiki oga angama.
D'ai daga cikin su ne fuska ba annuri ya Furta ya mutsatsiyar hausarsa da ta Had'a da fulatanci "oga Koda Kisha ne ayi ko wayaso yashiga Sha kanin mu da aikin " Kai malan yad'aga cikin Bada umurni, Bindigoginsu suka d'aga sama suna harbawa suna ihu Mai ban tsoro ...dakatar dasu Emir Saraki yayi ta hanyar Furta sai kunyi shiri Mai kyau Dan Shima minister Umar wayaune dashi,Amsa Masa sukayi da angama..
Buhuhunan kud'ad'en fansar Al umma ne da Suke k'arbo kwana kwanan nan daga gidan tsohon shugaban k'asa Dr Lukman Murtala Mon na fansar yayansa guda hud'u mata biyu mata uku wayenda akayi kidnapping daga zuwa biki ak'auyen Babban nasu da ya tilasta musu zuwa kasancewarsu Mai son sada zumuci Maison zama da Yan uwansa duk da yabar su achan Yana taimakonsu da biyarsu..
Buhu shida suka jawo na Yan dubu dubu b'arayin suka jawo suka ajiye atsakiyarsu oga Anan take aka zazzage kud'ad'en ana n gurin oga yakasa Kashi bakwai su Kashi d'ai d'aya Yan dabar Kashi biyu,sai na sayen sababbin makamai Kashi d'aya na informer Kashi d'aya ak'alla kowannen su yatashi da million ishirin ishirin,Sauran tumaki da dabbobi suka bar musu amatsayin k'arin ganima agare su murna sukayi sosai ganin tarin dukiyar da aka bar musu..
Bayan watsewar Taron ya ta addan suka fara shirye shiryen shiga fada Banda gobe...
Sai dai Abunda basu sani ba duk wani Abu dasuka tattauna ayanzu Yana recording awata "yar k'aramar na'ura Dake mak'ale a cikin agogon MALAN da matar sa tamasa kyautarshi...
Geng geng Taufa Al amarin nan yafara rikicewa Kaji wata sabuwa✍️✍️✍️
Mudai Allah ya Yi muna tsari da wayen na. Ya taaddan Allah karka basu iKon Had'a hanya damu ka Kara kare mu🤲🤲
Mu had'u gobe in Allah yakaimu Dan Jin yadda zata kaya...
Kuyi hakuri ba editing cos am tired Kuma bana da lafiya Ina maneji ne kawai...
Like share pls and comment ✍️✍️✍️✍️
💫A MAFARKI NASANTA💫 I know her in my dreams By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫
Firstlady 🙌🙌
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️is migthier than the sword 🗡️*
*Free*📙
EPISODE1️⃣ PAGE4️⃣8️⃣
*Kuyi following D'ina A* *Arewa books,@Fa'izatou* *Wattpad @Fa'iza murai*🙏🙏🙏
TYPING📲📲📲
••••••••••∆••••••••••••∆••••••••••∆•••••••••••∆ ××××××××××××××××××××××××××××××××× <<<<<>>><<<<<<<<<<<<<<<<<<<>>>>>>
......sun shirya tsaf Dan Kai farmaki a fada,sai dai sunyi Rashin sa,a domin a safiyar data kasance saura kwana d'aya su shiga fadar,suka samu labarin gobara ta tashi agidan minister Umar Wanda agidan babu Abunda aka fitar agidan harsu kansu sai dai gawawwakinsu da duk suka cinye da wuta.
Labarin ya riski oga agidan shak'ata warsa yashiga tashin hankali ma tuk'a domin yasan wannan ba aikin su bane ba shine Abunda suka shirya ba dan k'ara tabbatar wane yayi Kiran sauran Dan Jin yadda akayi,in su suka cinnawa gidan wuta tunda yabasu umurnin kisa,..
Bayan gama sauraren sa Babban b'arawon yasanar Masa da basu chanza komai ba hasalima su yau ko cikin gari basu shigo ba sun tsaya shirye shirye ne,yanzu Suma suka samu labarin wutar daga d'ai daga cikin informers nasu Dake cikin garin, daga nan ne suka Sanya dogon bincike harsuka gano wayen nan "Yan sandan nan guda biyar nada Sanya hannu acikin k'ona gidan sarki Ali Umar murai,minister of security and investigation crimes,har sukayi nasarar kamo Yan San Dan nan suka wahalar dasu ta hanyoyi masu yawa dan duk suyi bayanin dalilin Wanda yasanya su cinnawa gidan wuta dakuma wane ne shi,duk wahalar dasuka Sha kuwa basu sanar musu Wanda yasanya su ba da dalilinsa inda hakan ne yabawa oga damar kashe su duka wannnan kenan.
Emir Saraki ne bayan gama tunanin sa yasauke ajiyar zuciya Yana Furta yanzu dai muk'ara shiri Akan wannan mission d'in na gidan tsohon gwamna Alhaji mukhtar,cigaba da tattaunawa sukayi yadda zasu k'ara b'oye kansu wa duk wani Wanda yake Shirin Yi musu shigo shigo na shigo ba zurfi a alamurransu
*A MAFARKI NASANTA 📚 DABAN YAKE DA SAURA*
••••••••∆••••••••••∆•••••••••••∆•••••••••••••∆••••
*BUG*
A b'angaren su Halee kuwa, A Ayau ne suka gama zana jarabawar karshe a secondary schl,ta fannin soyayyarsu da Dr.yusuf sai Abunda yak'ara yin gaba,Baba Asabe kuwa har yanzu tana nan tana cigaba yad'awa Halee maganganu tare da wahalarda ita da musguna mata cikin ruwan sanyi.
Yau takasance Lahadi Halee ce Gaban murhu cikin madafa sai faman hura wuta takeyi inda wutar tak'i kamawa saboda kasancewar makamanshin wutar d'anyu ma,ana itace,lu lu eyes dinta sunyi jawur na hayak'in da ke shiga cikin su.