Kenza eBookz

A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 22

A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 22

A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 22: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 22. A hankali ya Kara tabbatar mata da Abunda take…

3,339 words

A hankali ya Kara tabbatar mata da Abunda take son sani gobe zasu bar India Kuma insun tafi bazasu dawo ba sai in wani aikin yataso Wanda dole ana Neman taimakon su agurin,yakuma sanar mata da Babbar Asibitin da mahaifin sa yagina musu wadda har an kammala ayanzu ma chan zasu cigaba da saving live's ..

Congratulations ta Furta cikin wani yanayi da ta kasa fassara shi na farin cikine ko na bakin ciki... Thanks ya Furta Inda tak'ara Basa amsa tana Furta "It's my pleasure" farin ciki ne Kuma taji ya mamaye ta yau sunyi doguwar magana dashi inda Kuma tak'ara tuno maganar tasa da yace zasu Rika shigowa in ta taso Wanda tasan Kuma dole ne ko sun je su dawo tunda ba'a basu damar yin tafiyar din din ba...

Cikin Rashin kuzari ta Furta I love you my doctor sai dai bansan dalilin da yasa baka Sona ba,nidai ko da baza ka soni ba zan iya biyoka Nigeria murayu tare hakan ,Kuma gaskiya idan dai har naga kadade baka zo India ba zan biyoka nigeria Dan bazan iya jure Rashin ka ba har na tsawon lokaci...

Kallonta yakeyi Ahankali ganin yadda kyakkyawar fuskarta tayi jawur abunka da Jan kosai na kukan da Tasha duk akansa,Kalmar so da ta k'ara Furta masa ce ta k'ara Sanya ya gwiwowinsa cikin kasalalliyar muryar ya Furta mata" karki Damu ai zamu rik'a communication ohk!" Tare da dauke idanunsa kan fuskar ta,inda ya Furta mata hakan ne Dan kwantar mata da hankali,dan ayanzu tausayi take Basa.

Kai ta d'aga Masa alamar gamsuwa da furucinsa,Kad'an suka tab'a fira har da Dr Aj da yashigo yanzu Wanda duk Rabin firar Aj ne da malini keyi shikam ogan iyakarsa juyi a kujerar sa tare da Lumshe idanunsa kamar wani Mai bacci..

Sallama sukayi da dukkanin colleques nasu,inda harda Taron karraamawa aka Had'a musu na musamman daga gwamnatin India na nuna jajircewarsu a wannan asibiiti Mai d'inbin tarihi duk da kasancewarsu Yan Africa, sun samu kyaututtuka da Dama a wurin bukin karramawar tasu da ya gudana adare musamman Dr Ammar.gwamnatin India ta nuna alhinin Rashin gwarazan likitota masu d'in bin tarihi azukatansu dama sauran k'asashen dasuke mak'wabtaka dasu. Gwamnatin India ta Kuma k'ara tabbatar musu da zasu cigaba da biyansu albashin su ba wani chanji har na tsawon shekara arba 'in akan hidimar dasuka Yi da k'asar gurin samun cigaba a fannin lafiya,sannan. Suka tabbatar musu zasu nemesu in wani aikin yaci karfinsu kamar yadda sukayi da MD na Asibitin Maharashtra,a take Kuma Anan suka k'ara sanar musu gidan da Suke zaune acikinsa sun mallaka musu shi halak malak,wanda yake dama na gwamanti ne,duk da yake suna da nasu gidajen na Alfarma akasar sun Fi son na gwamnatin Wanda ta Ginasa musamman Dan su ...

Allah sarki Kunsan indiawa fa akwai karramawa indai ka musu to insuka tashi mayar Maka zaka Sha mamaki..Dan lokacin da nayi zama India haka suka mini naji kamar kar inbaro 🥱😹💃💃💃

Farin cikin su Dr.Ammar a wannan Rana Bai b'oyuwa.Har body guard dinsu da sauran ma'aikatan su sunyi sallama dasu cikin kewar juna,dukkaninsu suka koma barrack Dan dama mafi yawansu Sojoji ne masu farin kaya.

*NIGERIA* Unni ce da masu aikin sashen nata ke ta Kai kawo acikin sashen na kitchen dinta ,sunata shirin tarbar manyan Baki da zasu sauka, yau girkin da akayi musu kala kala ne na musamman, musamman unni ta Nemo wadda ta iya abincin India aka Had'a musu irin su Pani puri shawarma da had'add'iyar basmatic rice dataji kayan Had'i na musamman,da farfesun kaji da had'add'iyar suyar kaji ,sai coconut juice da Madara tare da manyan exotics drinks,aka jere akan dining din da manyan kuloli na Alfarma masu d'an Karan kyau wayenda suka k'ara k'awata dining space din saboda farare ne Kar tass. tsayawa fad'in kalolin abincin zai cika wannan page din idan muka tsaya lissaafo abincin da aka tanadar musu duka zamu iya Cinyesa..

Jere Suke akan dinnng din,kowa kagani ya chab'a ado na musamman tin daga kan k'ana na, su Nisa ansha kwalliya itada sumy har Inayah dasuka zo jiya Dan tarbon manyan Baki itada mama dije,anko sukayi,kowa kagani farin ciki ne shimfid'e akan fuskarsa,Ummi ma tazo itada da Dady soja Dan duk Anan za'ayi tarbon su Anan sashen Unni a Babban falon ta,Sarki Ali yau ko fada ba ' a zauna ba,anyi ma masarautar wani irin gyara na musamman Dan har Sabon fenti sai da aka chanza ko Ina fess fess Masha Allah.

*INDIA*

Dr.Malini ce ta Raka su har Babban filin jirgin Mumbai India itada sauran colleques nasu da manyan wakillan gwamnatin India Dan k'ara karrama su,sallama sukayi ma dukkaninsu cikin Rashin son rabuwa da juna..

Dr.malini harda hawayen rabuwa da masoyi harda rungumar sa taso yi sai dai ya kauce mata.

Dr.Ammar da Aj sunji damuwa sosai alokacin da suka rabu da abokanan arzikin nasu wayenda basu tab'a nuna musu k'yama ba ta kasancewar su musulmai acikin su,Kuma ba Yan k'asar su ba.

Sanarwar da akayi kowa yagyara jirgi zai tashi ce tasanya Dr.Ammar Dake kusa da Dr Aj a first class,bud'e manyan idanunsa da Dake Lumshe tun bayan shigarsu cikin jirgin...Wanda damuwar Rashin samun su Lubna ce ta dabaibayesa,A hankali Yak'ara gyara zaman belt din sa tare da zamansa acikin jirgin..tare da Karanto Addu'ar tafiya azuciyarsa. A take nan jirginsu ya Lula a sararin samaniya..inda jirgin nasu yatashi A Babban filin sauka da jirage da sauka na SHIVAJI Mai suna ......

✈️CHHATRAPATI SHIVAJI INTERNATIONAL AIRLINE MUMBAI✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️

Mudai sai dai muce Asauka lafiya Bokayen turai..

*NIGERIA*

Jirgin da yakwaso manyan bak'i daga k'asar India yasauka karfe uku dai na Rana A Babban filin sauka da tashin jirage Dake Gusau Mai suna...

BAZAMFARE AIRLINE GUSAU ZAMFARA STATE✈️✈️

Mota shida su Unni sukayi Dan tarbon manyan bak'i..

Sanarwar da akayi jirgin zai sauka ne yasanya su Unni da Ummi dasu Nisa fitowa daga cikin motocin su,zuwa waiting space..

A hankali jirgin yasauka inda bayan Yan mintuna mutanen Dake cikin jirgin suka fara fitowa cikin farin ciki kowannen su rike da yar k'aramar jaka ahannu wasu kuwa trolley bag. Sai dai har yanzu su Unni na zuba ido ko zasu ga ya Yan nasu shiru

Har sai da mutanen suka kusa k'arewa sannan su Dr Ammar suka fito,Aj ne agaba sargafe da yar madaidaiciyar jakarsa Mai kama da school bag,Yana sanye cikin k'ana nan kaya wando jeans bak'i da Riga jaa,sai Ammar Dake Bayan sa yasha kyau na musamman cikin had'add'en k'ananan kaya Shima cikin shigar blue wando jeans da Riga dark blue anyi mata farin design na rubutu Mai kyau na Kalmar EASY,sai cover shoes fari masu d'an tuli sai farin glass da yasanya a idonsa Wanda yakara k'awata kyakkyawar fuskar sa Mai cike da haiba ,Masha Allah. fatar nan tasa sai sheki takeyi musamman da Rana tad'an hasko sa fresh dinta yak'ara bayyana k'arara,k'aramar jaka ce Shima goye abayansa sai Kuma had'add'iyar trolley dinsa bak'a Mai amfani da na'ura jaye a hannunsa fuskar nan tasa ba wani sakewa irin haka,Kuma ba Shan mur,ba kamar Aj ba da bakinsa yakasa rufuwa tun fitowarsa acikin jirgin ya shak'i k'amshin Nigeria.

Nisa ce ta fara hango Dr.Aj cikin farin ciki da shauk'in soyayya ta watsa wata iriyar k'ara ta farinciki wadda ta jawo hankalinsu Unni dama sauran tsirarrun mutanen Dake wajen,da mugun gudu ta fad'a jikinsa tana k'ank'ame sa sai Kuma kuka ya kubce mata Wanda yake fitowa tundaga zuciyarta,Dr.Aj da Yaji abun wani irine tun fad'owarta a k'irjinsa da yadda yaga farin ciki kwance akan fuskarta yatsinci kansa a wani yanayi Marar misaltuwa... Hannunsa yadaura abayanta Ahankali Yana rarrashinta har tasamu natsuwa,Su Ummi dasuka ga Abunda Yafaru dukkaninsu murmushi sukayi domin sun San sakar cin Nisa,Amma yanayin da tashiga akwai wani Abu ko basu Yi bincike ba.

Dr.Ammar kuwa sumy ne da Husna da su Ummi suka rungumesa cikin farin ciki.....

...Finally dai sundawo yanzu kallo yadawo Nigeria...sai mu Jira muga ya abun zai kasance...

Allah kabamu iKon kammala wannan book lafiya ya ubangiji🤲

Maman Abba💋 Sis Ayeesha Abdullahi💋 naga comment dinku

Ina godiya

Allah yabar k'auna 🥰🥰💋🌹

Next page tomorrow in Sha Allah

If you have any suggestions or advice you should contact me via my Whatsapp&Telegram +2348069059746 Email -faizaalmustapha1940@gmails.com✍️✍️✍️

Like share and comment pls 🙏

💫A MAFARKI NASANTA💫 I know her in my dreams By Pha'eezah Almustapha Daga Alkalamin✍️✍️ 💫Fa'eeh BG💫

Firstlady 🙌

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------ -------------------------------------------------------------------- *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*

*Free*📙

*NOTED EDITED*

✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

EPISODE1️⃣ PAGE4️⃣6️⃣

*Wannan page sadaukarwa ne agareki Auntyna Kuma abokiyar shawarata k'warin gwuiwataMaman Muhammad (haandy)marubuciyar littafin 📖 BAHAR* *Thanks for the support I really Appreciate it*🌹🌹🌹🌹🌹🌹

TYPING📲📲📲

£££££!🌹 ££££!🌹 £££!🌹 ££!🌹 £!🌹 !!!🌹 !!🌹 !🌹 Mahir ma da hajiya rungumesa sukayi cikin farin ciki,Shima Dr. Aj duk sai da yabisu d'aya bayan D'aya Yana Rungumarsu cikin farin cikin dawowa garesu.

Bayan yagama diramar sa da hajiya Dake ce Masa yazama k'ato ne yarage cin abincin,yaro kamar d'an Dan be kallonta kad'ai yayi tare da yin murmushi Yana Furta bawani nan kedai Kinga santalelen saurayi kyakkyawa Kuma Gani nan bari nan Auren ma da nace zanyi Dake na fasa,dukkaninsu dariya suka Saka ganin yadda hajiya ta kyab'e Bakin.

Unni Dake gefe ma sai data murmusa tana d'an kawar da kanta irin na kunyar nan ta d'an fari ,A hankali ya tako Yana ta faman sakin k'ayataccen murmushinsa Yana dosar inda Unni take tsaye kanta ak'asa Yana zuwa baiyi wata wata ba ya fad'a akan k'irjin mahaifiyartasa ya rungume ta Yana sakin dariyar farin ciki itama Unni dariyar takeyi na farin cikin Jin d'umin jikin yaron nata, Dukkaninsu wani farin ciki ne suka samu kansu ciki Marar misaltuwa Wanda sun Dad'e basu samu kansu ciki ba Marar misaltuwa.

A hankali ya Furta Nurul hayat I 'm back to you kiyi farin ciki Mai yawa,bana son ki k'ara yin Fushi Dani Kona second d'aya kinji..yakai karshen maganar cikin sauke ajiyar zuciya idanunsa na sauyawa daga yanayin daga kalarsu.

Unni kanta kad'ai ta iya d'aga Masa tana taping hannunta akan bayansa alamar lallashinsa Jin ajiyar zuciyar da yasauke,hawayen Daya zubo mata tashare tana Furtawa cikin harshen larabci "marhababika ya Nur",Dan haka take Kiran sa awasu lokuttan,janyesa tayi ajikinta sannan ta d'an d'aga k'afafunta ta sakar Masa kiss a goshinsa cikin farin ciki da murmushi kwance akan fuskarta,kowa Dake kallonsu Unni da Dr.Ammar sun burgesa sosai.

Jikin su Ummi da Nisa yayi sanyi na ganin yanayin da Unni tashiga itada Ammar,A hankali Shima Dr.Aj yatako cikin farin ciki yana rungume Unni barka da zuwa tamasa cikin farinciki itama tana Furta barka da dawowar ka k'asar Haihuwarka Aminullah na,Amsa mata yayi da yawwa Unni cikin farin ciki kamar yadda fuskar ta Unni take wanze da farin ciki,Shima peck ta Masa agoshin sa bayan sa take bubbugawa anatse.

Nisa ce cikin farin ciki ta rungume Dr Ammar tana Furta welcome back Yaya A,cikin farin ciki Shima ya rungume k'anwartasa yana Furta thanks you dear Cikin farin ciki Mai yawa na ganin junansu.

Dukkaninsu rangama sukayi cikin had'add'un motocin su, mota d'aya suka shiga Dr .Ammar da Aj sai hajiya a front seat wadda mahir ya tuk'o su sai Kuma sauran motocin su Nisa da su Ummi,suka shiga sauran motocin wayenda fadawa suka tuk'o da sauran fadawan da suka zo rakiya.

A motar su Dr.Ammar kuwa hajiyace take ta tsokanar su tunda sun dawo gida sai afara maganar Neman Aure Dan ita Kam duk sun mata tsufa,sai dai Dr Aj ne kad'ai ke tanka mata, cikin Jin haushi ta Furtawa Dr Ammar "wai Kai bak'in likita me ka taka ne waih yau,takai karshen maganar tana rike hab'a, Murmushi kawai Dr.Ammar yayi Yana Furta hajiya mezance Miki , uwar harara ta gallara Masa ta cikin madubi wadda tasanya dukkaninsu dariya har mahir Dake driving,A hankali Dr .Ammar bayan Lumshe idanunsa ya Furta dama danki ta ku rani kikace dole atare zamu koma gida ko,nikam zan k'ara maimaita Miki kin min tsufa sai dai daga nesa, hajiya mere Bakinta tayi tana Furta Allah wadaran naka ya lalace ta cigaba da Jan charbinta batare da ta k'ara Furta masa wani Abu ba, dukkaninsu murmushi sukayi kawai.

Tun dosowar su Babbar masarautar suke Jin tashin busa da algaitu aciikin fadar dan Dr.Ammar ya ce Baya son algaitu su bisa har airport shiyasa aka dakatar dasu cikin masarautar kawai,kid'in gangane ta ko Ina ke tashi,wangale musu k'aton gate din masarautar ne ya basu damar shiga daga cikin Babbar masarautar,jama'ace ta ko Ina fadawa da sauran ma'aikatan ma'ana bayin Dake masarautar,ma'aikatan kowanne Sashe sun fito tundaga sashen Fulani,hajiya,fada,Yaya Mustapha, Muhammad (malan ) da sauran dangi,kowa na tsaitsaye a compound d'in masarautar Jiran dawowar yariman masarautar,shigarsu ciki yabada damar fitowarsu daga cikin motocin su.

had'add'iyar carpet ce Mai taushi aka shimfid'a wadda zata sadaka da sashen Unni,wadda yarima zai hau aka rubuta ur welcome ce shimfid'e agurin, a hankali Dr.Ammar ya d'aura had'add'iyar k'afarsa akan carpet din shida Dr.Aj ma'aikata ne ketayi musu gaisuwa ta hanyar bow,ta hanyar sunkuyar da kansu su d'ora hannayensu akan goshin su hannu d'aya bisa d'aya irin yadda Yan Korea Suke Yi a historical films nasu,hannu kad'ai Dr.Ammar ke d'aga musu shida Aj Har suka shiga Babban falon Unni gaba D'ayan su har su hajiya dasu Nisa,sarki Ali Dake tsaye a Babban falon shida Dady soja ne suka mik'e suka rungume "Ya "yan nasu cikin wani farin ciki sarki Ali ne ya furtawa Ammar Barka da dawowa k'asarka ta haihuwa nayi farin cikin ganin ka Kai da d'an uwanka...Kai Dr Ammar ya d'aga cikin farinciki a hankali Kuma ya furta I 'm sorry Yaya Dady cikin farin ciki sarki ya Furta shiii alamar yayi shiru su. Sun Dade rungume da junansu cikin shauk'in soyayyar D'a da mahaifi,sarki Ali ne ya fara jaye jikinsa daga na Dr Ammar Yana komawa yayi kissing din hannun Ammar din,haka yakoma ya rungume Dr.Aj cikin farin ciki,Shima Dady soja rungume Dr Ammar yayi cikin farin ciki bayan sakin aj Yana Masa barka da zuwa.

Bayan dukkaninsu sungama gaggaisawa aka d'unguma ga gaba d'aya zuwa babban dining Area Dake falon,Nisa ce agefen hajiya tana facing chair din Dr Aj ita Kuma sumy tana a kusa da masoyinta Yaya mahir,sarki Ali da Dady soja suna akusa da juna Unni da Ummi sun Saka Husna atsakiyarsu,sai Dr.Ammar Akusa da Dr Aj Yaya Yusuf da Abdallah ma suna agefen hagun hajiya, dukkaninsu Bismillah sukayi bayan kowa yazab'i Abunda yake so ma'aikatan sunyi saving dinsa.

A hankali Suke cin abincinsa Babu motsin da Kake Jin sai na k'arar cokulla da sautin fillet,Dr.Ammar ne Dake cin had'add'iyar basmatic rice wadda taji had'i na musamman,Wanda Unni ce tayi kokarin Had'a Masa ita kasancewarta d'ai daga cikin favorite dinsa, kamar ance ya d'aga idonsa yahango k'anwartasa Abar k'aunar sa Nisa ta Tsurawa sashen da Suke da ido Ahankali ya bi inda take kallo da ido Dan yasan dai bashi take kallo ba dan ya tab'a Jin sumayya nagayawa Aj n irin son da yuhanis din ke Masa Kuma agaban sa ma yasha Furtawa sumyn baijin komai akanta tunano da maganar da Aj yayi suna India ,ya yarda cewa k'ila jarabawar k'anwarsa ce kenan kamar yadda Dr.malini take ta wahala da soyayyarsa,Amma shi ko kad'an bayajin soyayyar ta aransa,sunan Dr.malini ne da yashigo kansa yaji tausayinta ya kamashi abin cin ne ya gunduresa na tausayin k'anwarsa,A hankali yazare hannunsa dake rik'e da spoon,Lemu ya tsiyaya A hankali kurb'a biyu yayi Yana mik'ewa,mik'ewar sa tsaye ce tasanya Aj kallon sa da mamaki Dan yasan badai k'oshi yayi ba,cikin yaren India ya Furtamasa "wai harka k'oshi ne "kai kad'ai Dr Ammar yad'aga Masa ya juwarsa Yana furtawa Unni "Nurul hayat natafi inyi fresh up,tambayar sa tak'arayi ya k'oshine ko Akai Masa d'aki dan batasan tambayar ce Aj yamasa ba,eh" ya furtamata atakaice cikin tattausar murya wadda mahaifiyarsa kad'ai kesamun irin wannnan sautin,juyawa yayi yaci gaba da tafiyarsa batare da ya tamkawa hajiya Dake jansa da wasa ba,har ya b'acewa ganinsu yanajin sautin Muryar hajiyar na fad'in kayiwa ubanka Mustapha Dan murmushi kad'ai yayi Yana girgiza kansa,Yaya Mustapha da shigowarsa falon kenan cikin yar dariya ya Furta hajiya me Kuma muka aikata daga dawowarmu yau,kawar da kanta tayi gefe irin Jin haushin nan tana Furta barni da ja 'irin wai ni zai kyale Ina magana Dan shegantaka to ni nama fasa Auren,dukkaninsu dariya suka Sanya,rigimar hajiya da Ammar akwai abun dariya aciki,duk da Baya kula ta ma.

Mik'ewa hajiya tayi Dan dama tagama cin abin cin ne ta k'oshi tare da barin gurin.

Aj da tun d'azu yake lura da irin kallon da Nisa ke Masa ne yad'an kawar da kansa bayan d'an k'ara nazartar ta da tabbatar da zarginsa arai akan tabbas wannan shine dalilin da yasanya Dr Ammar Barin wurin Dan ya tabbatar ba k'oshine ya tadashi ba yasan yadda yake Baya wasa da cikinsa musamman Abunda yake favorite nasa,k'ara d'ago kansa yayi inda karaf idanunsa sai a cikin na Nisa da duk Rabin hankalinta nagunsa,kasa dauke idanunsa yayi sai dai suka cigaba da kallon junansu Babu d'auke ido,Nisa ce ta Yi karfin halin sauke nata Idanun k'asa cikin yar kunyar data kamata,duk abun nan da ke faruwa atsakaninsu Babu Wanda Bai luraba duk su Unni sungani dasu Dady soja,sumy murmushi kad'ai tayi tana fatan Allah ya karkatowa Nisa Hankalin yya Aj,Dama tasan dole zai so Nisar Dan ayanzu kosu kansu sunsan suncika manyan 'yan mata dan duk wata halitta Dake jikiinsu tak'ara Bayyana tasan duk chan Baya fad'e yake Yi bata cikin tsarinsa tasan cewa Dan baiganta bane ayanzu....

Shima Dr Aj kawar da idonsa yayi yanajin nauyin Had'a idon da sukayi da sarki Ali Lemu ya kurb'a a hankali sannan ya mik'e Shima yabar kan dining zuwa sashen su,Murmushi kad'ai sarki Ali yayi bayan wucewar Aj din tare da girgiza kansa.

Nisa da keta ya mutsar abincin Dake gabanta da cokali na Rashin jinta comportable tun lokacin da Dr Aj yakamata tana kallonsa,itama tayi tsam ta bar kan dinning din, sumy dake k'unshe dariyarta ce ta furta jirani Nisa,isko ta tayi inda take tsaye Sannan suka cigaba da tafiya tana tsokanarta da Mrs Al Amin, Murmushi Nisa keta saki Jin sunan da Sumy ta Kira ta dashi bayan isarsu d'akin Nisa ne sumy keta sakin dariyar da take k'unshewa abakinta tana Furta" wai Nisa Kinga irin kallon da Yaya Aj yake Miki duka fa su Ummi sungani Allah ma ya rufa muku asiri hajiya tabar kan dinning yau da sai kunji kunya ba yar kad'an ba Dan Nasan intafara tsoakanar ku takai karshen maganar cikin sakin karamar dariya......

'Nabani Nisa ta Furta tana d'ora hannayenta biyu akanta sai hawaye yanzu kenan duk su Unni da Abbah sun ganemu hawaye kuwa sai k'ara kwaranya Suke Yi A idonta,lallashinta sumy farayi tana Furta mata "aikin ma jidadi Nisa hakan komai zai zo dasauki bakyaso kowa yasani ne kamar nida Yaya mahir,Kinga hakan cikin sauk'i sai a Aura Miki Yaya Aj sai ki zama Mrs Al AMIN JM SOJA dariya ce ta sub'ucewa Nisa wadda tasanya kyawawan dimples dinta bayyana masu yanayi da na Dr Ammar cikin murmushi da yar k'aramar dariya kamar wata yarinyar yar Sha uku ta Furta wa sumy " hakane Kuma fa Aunty sumy"

K'aramar harara sumy ta sakarmata tana Furta yau Kuma nak'ara samun auntyn dariya suka Sanya. sannan suka cigaba da hirar su sumy nabata shawara yadda zata janyo Hankalin Yaya Aj kanta asauk'ak'e.

A b'angaren Dr Ammar kuwa tun bayan shigarsa had'add'en d'akin nasa da yaji kayan more rayuwa Wanda yaji white paint da pink k'aton falo ne Wanda yakusa girman falon su na India acikinsa akwai kitchen,da store sannan akwai d'aki biyu Jere da juna Babbar Tv ce ta kamfanin Apple jingine a bangon falon wadda takusa cinye Rabin bangon sai kujeru na Alfarma farare k'ar sabbin zubi da akayi musu,sai labulayye pink colour, sai d'an karamin fridge Shima agefe, d'akin batarkace ko Ina sai k'amshi ke tashi ko Ina musamman turaren mamallakin d'akin Wanda yakasance kamar dashi aka Gina d'akin sabo da yadda ya kamsashe d'akin da kamshi Mai dad'i, ga sanyin a.c da yak'ara wa d'akin yanayi Mai dad'i.✍️

🚴🚴🚴🚴🚴

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull