A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 7
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 7: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 7. Pha'eezah Almustapha
3,359 words
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️
💫P.E.W.A.💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️
Pen🖊️*is migthier than the sword🗡️*
------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE1️⃣8️⃣↔
TYPING📲📲📲
*TUSHEN MASARAUTA*
"Ali murai shine Asalin wanda yarik'a masarautar yana da mata kwaya d'aya tal,sunan ta Hajiya lubah (iyami) da "ya "ya maza biyar,d'an sa nafarko sunan sa bello,sai nabiyu sunan sa Haruna,na ukun Abdul aziz,sai na hud'unsu Isma'il,sai Autansu yahaya..
Bayan rasuwar sarki Ali murai sai aka nad'a d'ansa na farko Bello wanda shi yacigaba da kula da masarautar yana da mata d'aya da y'a y'a hud'u namiji biyu mace biyu,Bayan wasu shekaru shima Bello yakwanta dama,wanda mutuwartashi ta kowa ya jita A Masarautar saboda sak halinsa irin na mahaifinsa sarki Ali murai,Mahaifiyarsa takoka da rashinsa da y"an uwansa da ma Alummar Masarautar.
Bayan gama zaman makoki Aka nad'a d'an uwansa Haruna,Haruna yak'arb'i mulki cikin salama ,Sai bayan shekaru sittin sannan Allah yakarbi ransa..
..Abdul Aziz Yakarb'a shi kwata kwata ma bai ka shekara hamsin ba akan karagar mulkin saboda ciwon daya ci k'arfin sa na k'oda,sai aka nad'a Isma'il,Bayan Nad'in Ism'el,Sarki Abdul aziz yakwanta dama....
Isma'el ya cigaba da mulkin masarautar Bayan shekara saba'in bisa karagar mulki yakwanta dama,wanda bayan rasuwar sa,Anyi rigima sosai da Yahaya danshi kwata kwata bayason sarautar,acewar sa kayan wahala ce da takura,bai karb'a har sai da mahaifiyar su iyami ta kwanta ciwo akan hakan,ciwon zuciyaar ta yatashi wanda yasameta tun bayan rasuwar mijinta sarki Ali murai,sanadin bak'in cikin
Yahaya da yakafe bazai k'arb'i masarautar ba,masarautar da mijinta sarki Ali murai yasga gwagwarmaya wurin ginata,daga k'arshe dai yakarb'a ganin yadda ran mahaifiyar sa ya b'aci gashi harda kwantawa ciwo....
'Anyi bikin nad'in sarauta da ba'a tab'a yin irinsa ba alokacin kowa kaga fuskar sa da annashuwa da farinciki kamar sauran lokutta domin sun san cewa ba su shiga mugun hannu ba dan duk cikin ya"yan sarki Ali murai babu wanda yamusu mugun riko,Yahaya yakarbi mulki cikin aminci tare da alkawalin kula da Alummar masarautar,yana da shekara talatin akaragar mulki matar shi tahaifi namiji wanda shikad'ai ne rabonta har tabar duniya,yaron yaci sunan margayi tsohon sarki Bello,bayan wasu yan shekaru,Kwatsam ranar aka wayi gari da mutuwar sarki Yahaya murai,wanda mutuwar sa ta girgiza kowa musamman yaronsa sa Bello,Bayan rasuwar sa da kwanakki itama tsohuwa Iyami mai ran k'arfe ta kwanta dama,tana da shekaru D'ari da hud'u a Duniya.
Wanda kowa yaji mutuwar wayen nan bayin Allah Acikin Masarautar da ma wajen Masarautar..
Bayan rasuwar yahya Anyi rigima sosai A fada akan wayenda za,a dora akwai d'an wajen margayi bello da yace yanaso sai kuma d'an wajen magaji wanda yaya ne ga Sarki Ali murai,daga k'arshe dai Muhammadu bello D'an wajen sarki Yahaya shi aka bawa bisa ga chanchantarsa duk da akwai k'aranta atare dashi dan duk sun girme masa.
Anyi nad'in sarauta tareda Daurin Auren Sarki Bello Alokacin yana da shekara ishirin da hud'u A duniya,Bayan hawansa akaragar mulkin yana d'a yan uwansa manyan muk'a man masarauta,domin cigaban Alumma .
Ya Auri yar wajen sarkin zazzau na hud'u alokacin mai suna Gimbiya Ruk'ayya bayan shekara gimbiya Rukayya ta haihu ta samu yan Biyu maza,Alokacin ne kuma matar tsohon sarki margayi yahaya uwar muhammadu bello tabar duniya,Anyi taron suna cikin alhinin wannan rashi,tacigaba rainon yan biyu dinta,Bayan wasu shekaru tasamu wani cikin inda tahaifi Namiji yaci suna Aliyu,sunan tsohon sarki...
'A Daren sunan Aliyu ne wani Babban tashin hankali yafaru inda wuta ta kama ad'akin su hassan da husaini duk suka k'one k'urmus sanadiyyar wutar lantarki suda mahaifiyar su gimbiya Ruk'ayya wadda taje dubasu daga nan ta musu Addu,ar kwanciya bacci duk da tasan cewa bazasu kwanta hakan nan domin takoyar dasu,alokacin suna shekara shidda A duniya,Mutuwar data girgiza Sarki Bello da kuma masarautar wanda sai da sarki Bello yasuma alokacin da aka sanar dashi,Bayan jimamin rashin Sarki Bello yaci gaba da rainon D'an sa Ali....
**Bayan shekara guda sarki Bello yayi Aure ya Auri wadda take baiwa ce Amasarautar, ya Aureta ne saboda ganin irin kulawar da take bawa Aliyu wanda kuma ita kad'ai yake yadda da ita,Sai ya " yenta ta kuma ya Aureta domin samun farin cikin D'an sa tilo daya.
Lafiya lau masarauta take tafiya tareda cigaba mai yawa,Bayan wasu shekaru Sarki Bello na Biyu yabar Duniya yana da shekaru hamsin akan karagar mulki,inda yabar Aliyu cikin maraici mai yawa duk da wannan yentacciyar Baiwa mai suna Nana Asma'u tana sonshi tana bashi kulawa mai kyau saboda yadda take jinsa kamar d'anta na cikinta..
BAyan gama jimamin mutuwar sarki Bello na || biyu aka nad'a d'ansa Aliyu alokacin yanaa da shekaru ishirin da hud'u a duniya.
Bayan na d'insa da shekara guda yayi Aure ya Auri yar masarautar sokoto jikar yar sarkin musulmi na ||| na uku;mai suna ummulkhairi ana kiranta gimbiya (umma),Bikin yatar dubbanin Al umma takowace masarautun nigeria da manyan yan siyasa,masu kudi..Ankawo Amarya lafiya cikin fada acikin sashen ta mai kyau,suna cin Amarcin su lafiya lau tare da zaman Amana....
Komai yana tafiya dai dai ta b'angaren mulki yadda yakamata.
Bayan shekara d'aya gimbiya umma tahaifi santalelen d'anta namiji ranar suna yaro yaci sunan sa HAMZA ALIYU MURAI,Anyi taron biki lafiya,inda tacigaba da rainon yaronta,Bayan haihuwar Hamza da wata takwas tasake samun wani cikin alokacin gimbiya ummulkhairi taso zubarda cikin ganin Hamza ko shekara bai had'a kar yasha ciki,sai dai mai martaba sarki Aliyu yahana zubar da cikin sai dai yasa aka cire Hamza daga nono...
Taraini cikinta lafiya lau batare da tasha wuya ba,watannin haihuwar cikin nayi nak'uda ta motsa amma yaro yaki fitowa ak'arshe dai CS akayi mata aka ciro santalelen d'anta mai kama da uban sa sak,yaron yaci suna Ahmad...
.....Bayan wasu "yan shekaru sarki Aliyu D'an Bello jikan Yahaya D'an Sarki Ali Murai yabar Duniya alokacin,yabar Duniya da shekaru arba'in akaragar mulki,Mutuwar sa tagirgiza y"a yansa guda biyu a duniya da matar sa ummulkhairi,inda tacigaba da kula da yayanta cikin kulawa,Bayan Rasuwarsa da yan watanni Nana Asma'u matar margayi sarki Bello na || tabar duniya...
Sarautar dole aka bawa magajin gari rik'on kwarya kafin ya'yan sarki Ali su kai lokacin iya rike sarautar,domin dukkaninsu bazasu wuce shekara goma sha biyar Alokacin ba.
Bayan wasu shekaru Ahmad yayi aure ya auri matarsa Bafullatanar Adamawa itama yar gidan sarautace sunanta Haleematu sadiya suna kiranta hajiyar safkare wanda sunan da kakarta ta lakamatane,ya Aureta yana da sheakara ishirin da shidda aduniya sunyi Auren soyayya da gimbiya halimatu,kuma aloakacin ne aka damk'a sarauta hannun Ahmad duk da sai da akayi rigima dashi dan yace bazai karb'a ba sai dai abawa y"a yanshi tunda shine Babba,Dakyar aka samu yakarba bayan ya yan nasa ya sanya da mahaifiyarsu gimbiya ummulkhairi suka tasoshi gaba....
Anyi bikin nad'in sarauta lafiya cikin annashuwa da salama,ta fannin zaman takewarsa da matar sa masha Allah za,ace gwanin burgewa.
****Bayan shekara daya gimbiya halimatu sadiya ta haifi santalelen d'anta mai kama da ubansa sak jinin fulani,farin cikin wannan masarauta bazai boyu ba musamman sarki Ahmad da D'an uwansa hamza,wanda ke ji kamar shi akayiwa haihuwar...
*Ranar suna yaro yaci sunan kakan sa sarki Aliyu Bello jikan yahaya d'an Ali murai*yaro yasamu gata ta kowanne fanni,Alokacin shima Hamza yayi Aure ya Auri Gimbiya Hauwa'u yar masarautar Fulanin Bungud'u ana mata lak'ani da fulani,fulani macece mai fadin rai da rashin son talaka,da mugun son kanta,ba kamar gimbiya halimatu ba mutuniyar kirki mai mutunci,BAyan Aurensu da Hamza sai tafara nuna mishi ai sarautar dashi ta dace domin shine Babba yace abashi sarautar,ai shine dana farko ga sarki Ali Bello,sai ya rik'a nuna mata baida buk'ata,kullum haka suke rigima da ita,har zuwa lokacin da tasamu cikin Mustapha A lokacin kuwa matar sarki Ahmad Halimatu tasamu ciki na biyu ta haifi umar,sunan mahaifinta kenan,tana kiransa da emir,Bayan kamar wata takwas sai ga wani cikin na ukku inda ta tahaife sa lafiya,tasamu Abdul rashid,tacigaba da rainon ya yanta cikin kwanciyar hankali.
Daga cikin abin bak'in cikin da yafaru Akwai rasuwar gimbiya ummulkhairi matar tsohon sarki Ali,Mahaifiyar sarki Ahmad da Hamza,sunyi rashin mahaifiyarsu abar kaunar...sai dai muce Allah yajikanta da al ummar musulmi baki daya.........
*Yaa Allah Duk wata mahaifiya 💔💔dake kwance akarkashin k'asa,Allah kajik'anta da rahaama,da musulmi baki daya,Yaaa Allah wayenda suke raye kuma ka k'ara musu lafiya mai amfani tare da tsawon rai mai albarka*🙏
Rashin uwa rashine 😭Babba Arayuwa
Allah yabar mu dasu 🙏
--------------------------------------------------------------
Matar Hamza Fulani tak'ara samun wani cikin nabiyu ta haifi d'anta namiji mai suna Muhammad ana masa lak'ani da Malan,tana da ya"ya biyu kenan.
Itama sarauniya halimatu taka'ara samun wani cikin bayan shekara uku inda ta haifi yarta mace mai suna khadija inda daga gareta haihuwar ta tsaya mata chak......
Sarauniya Halimatu yaranta sun taso cikin soyayyar junansu Da yan uwansu yan gurin magaji hamza,domin shi d'an uwansa ya nada magaji bayan rasuwar wanchan magajin.....
Duk da tsangwamar da Fulani take nuna musu amma hakan bai hanasu jan yan uwansu ajiki bah.
Ta b'angaren magaji Hamza kuwa yana shan matsin lamba gurin Hauwa'u (fulani )kan karbar mulki alokacin takara samun ciki tahaifi ya mace mai suna ummulkhairi suna kiranta (khairiyya) dan taci sunan kakar ta ne wanda daga gareta haihuwar ta tsaya ma fulani chak..
A lokacin Duk fulani tana masa matsin lamba wanda har tafara cin galaba akan sa,dan bata tsaya haka nan ba,sai da talek'a gurin malammaan tsibbo (bokaye) Wal iyazubillah....
bokaye mana domin tahakan ne wasu suke amfani dashi sai suce ai malami ne shi bokan,ana amfani da sunan malamman ana shirka ana cutar Al umma..ALLAH YAYI MUNA TSARI DASU...Masu zuwa gurin bokaye Allah yashiye su🙏
MU HADU GOBE IN ALLAH YAKAIMU
YAU KAM KUNSAMU LONG PAGE,DAN KONI NAJI AJIKI NA,KUNGA NA GOGE LAIFINA NA JIYA,DUK DA BANI DA LAFIYA NE
NAGODE SOSAI ALLAH YABAR KAUNA🙏
KUFARA SHIRI ANKUSA GAMA FREE PAGES,DAN BATUN SAMBAD'O KUD'INKU......
Kucigaba da bibiyar Alkalamina
Yau duk sai A hankali typing din domn page d in yatado mini da rashin da mukayi...Allah yajik'anku da rahama Baba Bello,kakana Baba Yahaya,Alhajin Auki,Mariya,gwaggo yar sarki, Allah yasa Aljannna takasance makomarku da dukkan musulmi baki daya..AMEEEN...
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,Na episode two*!!!✌✌💥💥
*TALLAH!!! TALLAH!!! TALLAH*
*Ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,ga dama tasamu domin Muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harda ma k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntubarmu ta lambobin waya kamar haka*......
+ 2348069059746
+ 2349078741775
-----------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION 📚🖊️
💫P.E.W.A.💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️
Pen🖊️*is migthier than the sword🗡️*
------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE1️⃣9️⃣
TYPING📲📲📲
________________________________________
" Rana ta farko daya isko sarki Ahmad da maganar yana son sarautar ta dawo hannunsa,Sarki Ahmad bai nuna komai ba akan fuskar sa,sai dai murmushi da ya wanzar akanta tare da furta masa zaiyi magana da manyan masarauta,duk da yasan lallai su amince ba,saboda tun farko da yardarsa aka d'orasa,kuma ba,a chanza sarki kai tsaye ba da kwakkwaran dalili ba a wanchan lokacin..
Koda sarki Ahmad yagana da manyan masarauta sun nuna k'in Amincewarsu kaitsaye.
'kiran d'an uwan nasa yasanar dashi domin badashi anakayi zaman ba,kamar ganawar sirri ce,daga su sai maimartaba sarki sarki Ahmad sukayi ta,yana yin yadda yaga D'an uwansa yana kuka kasharb'an hankalinsa yatashi sosai,dole yasanya taron gaggawa yace yayi murabus kan kujerar tare da katse duk wasu tambayoyin da aka so tsiyesa dasu inji manyan masarautar..
'Farin cikin da yagani kwance akan fuskar d'an uwan nasa Hamza shine Abunda yatsaya masa arai,Bayan komawar sa gida bai b'oyewa gimbiya Halimatu sadiya komai ba,Tayu mamaki sosai duk da tasan akwai wata a k'asa sun san halin matar sa sarauniya Hauwa'u zata iya yin komai sun yarda cewa bayin kansa bane..
:::::::Rayuwa tana tafiya yadda yakamata,sarauniya Hauwa,u (fulani) mulki ya shigo hannu sai taka talakawa take yi son ranta duka bayi alokacin sun san halinta tsoronta sukeyi sosai domin wulakanta su bakomai ne awajenta ba,musamman na sashenta,Yadda take da mugun hali haka tab'ata D'anta Muhammad,shi mustapha ba haka yake ba halin babansu suka biyo shida macen da takara haifawa mai suna ummulkhairi,wadda taci sunan kakarsu Ta wajen uba,suna kiranta khairiyyah..
A lokacin da akayi juyin mulkin duka ya yan sarki Ahmad maza basa nigeria suna wajen karatu,Aliyu yana china yana karantar Business Administration,sai umar yana Kasar Uk yana karatu fannin bincike da tsaro,sai Autan maza Abdul rashid yana kasar sudan yana karantar MBBS karatun likitanci kenan,Duk da alokacin sunji mulkin yabar hannun mahaifinsu ba wanda yadamu dan dama basu wani dauki mulkin wata tsiya bah.
Bayan kamar shekara bakwai lokacin umar yagama nasa karatun har masters ya had'o,yadawo gida alokacin ne kuma mahaifinsu sarki Ahmad yakwanta dama,😭mutuwar data girgiza kowa dole dukkaninsu suka dawo nigeria dan ganin gawar mahaifinsu,wanda kafin suzo ma an binne ta,ganin basu iso da wuri ba,khadija kadai tasamu damar isowa da wuri ita dake Adamawa gurin kakaninta tana karatun a wata private school ta Nursing wanda tashiga a wannan year din,koda suka iso rashin ganin gawar ta mahaifin nasu sai takara rikita su,in kagansu alaokacin sai ka sun baka tausayi,wannan mutuwa basu kad'ai ta girgiza ba harda Alummar zamfara baki d'aya domin sanin halayen sa na kirki da kyautatawa al umma da yake yi...
'Matuk'ar girgiza sarki Hamza ya girgiza ba kad'an ba Alokacin da aka sanar dashi yana tsaye,shine ma dalilin dawowarsa hayyacinsa,kuka yakeyi wiwi,yana furta kaichona,na k'untatawa D'an uwa nah,da k'yar fadawa da manyan masarauta suka lallashesa .....
"Gimbiya Halimatu sai da tayi kwana biyu bata farfad'o ba daga suman datayi bah...
Bayan kwanakki da rasuwar sarki Ahmad, Sarki Hamza yatara taron gaggawa na manyan masarauta,take yasanar musu da kudurinsa na son yin murabus,maganar takawo cece kuce a fada lokaci da sarauniya Hauwa,u taji wannnan zance tayi farinciki sosai jin cewar sarauta zata dawo hannun ya yanta,ita a tunaninta Muhammad ko Mustapha za,a bawa tunda mahaifinsu ne yasauka,wanda dama shine burinta tun farko shiyasa ta yishigenta da fice har sarautar ta dawo hannun sa..
Sai kuma 'wani Babban labari na tashin Hankali daya sanya Gimbiya Fulani suma.......
'Jin sarki Hamza yagabatar da 'matar sa ta biyu waddaya aura shekaru sha bakwai da suka wuce,tare da ya yanta mata uku,duka kyawawa,na farkon sune yan biyu hassana da husaina sai ta karshen su Auta mai suna lailat,yagabatar dasu ne A masarautar dan yana so sudawo dazama ciki tare da sauran dangi...
Sunyi Aure da matar sa Fateema yar k'asar makkah,ana kiranta Ammie,Fateema dai balarabiya ce sak gaba da baya,sunyi Auren soyayya da sarki Hamza A lokacin da yaje k'asar ta makkah yin wani taro na sarakuna,Tanuna tana sonsa Alokacin shima kuma yaji yana sonta Duk da lokacin akwai sihiri mai K'arfi ajikinsa wanda ba kowa ke iya ganewa bah...
Ya Aureta ne Achan k'asar jidda inda Asalin iyayenta suke,tana zama wurin ya yan tane sarkin makkah alokacin.
Mutane da dama sun shaida d'aurin Auren fateema hakim da kuma sarki Hamza Aliu murai ...
Bayan D'aurin Aure yad'aukota suka dawo nigeria wanda dik cikin masarautar sarki Ahmad kad'ai yasan da Auren sai kuma wasu daga cikin manyan masarauta,saboda ya nemi Alfarmar yazamo sirri bayaso maganar takai ga sarauniya hauwa,u domin Alokacin harda d'an tsoronta aka saka masa azuciya..
Sarki Ahmad har ziyara yana kaiwa fateema (Ammie) a gidan da sarki yakaita a d'ai daga cikin manyan unguwanne da suka Amsa sunansu na masu naira ...
kuma tun lokacin da Ammie ta haifi twins dinta sarki Ahmad mai mutuwa yabar wasiyyar ko bayan ranshi yana son cikin zaratan mazan ya yansa koda d'aya ne ya Auri cikin wayen nan twins d'in,Bayan twins tak'ara samun mace aka lailat......................
SU FULANI ANGA TASHIN HANKALI WANNAN KAM SHI AKE KIRA TA LEK'O TA KOMA....Zafi bibbiyu...
💫FA'EEH BG💫
Wannan labari yazamo farinciki ga wasu wasu kuwa bak'in ciki,domin itakam gimbiya Halimatu sadiya tayi farin ciki dan dama mijinta yasanar mata da Ammie din wanda sak'o tana basa inzaije,yakaiwa hassana da husaina da lailat,kuma suna musayar gaisuwa wa junansu,har numban wayar juna suna da ita,Murmushi kad'ai tayi dajin wannann labari dama kuma tana dakon zuwansu,suma su umar (emir) da su Aliyu sunyi matuk'ar farinciki musamman Mustapha da khairiyyah sunyi murna sosai ganin sun kara samun yan uwa....
Bayan gabatar dasu ga fada aka damk'a su gurin gimbiya halimatu domin tama rakkiya sashen ta domin itaace Babba Amasarautar,dama tasanya ma,aikata sun gyara sashen da yake Mallakin Ammie ne ita da " ya "yanta...
Bayan gama gaisawa da juna tagabatar da ga dukkanin bayi ma,aikata dake aiki asashen ta da kuma wayenda zasu yi aiki asashen Ammie din..
Sannna suka d'unguma zuwa katafaren sashenta wanda yaji kayan more rayuwa ta ko ina..
"A fada kuwa suna tattaunawa kan maganar murabus na sarki Hamza,ya kuma sanar musu cewà shi ya nemi d'an uwansa sarki Ahmad yasauka yabasa mulki kuma bay in kansa bane shidai yasan ko mene umurni aka basa,Amma bai sanar musu wanda yayi mishi hakan ba domiin kariyar mutuncin ya yanshi..
Kuma yace yana son yamika'a sarautar ka yayen d'an uwansa sarki Ahmad da sarautar tunda dama dukkaninsu sunkai mizanin hankali,sunyi na,am da zancen sa kuma sunga dacewar hukuncin sarki Hamzan,zancen yama wasu dadd'i wasu kuwa bai musu ba,A lokacin inkaga fuskar Muhamad
( Malan )zakaga tsantsar bak'inciki da b'acin rai tattare dashi daga farkon maganar yazata shi za,a bawa baiyi duba da shine k'arami ba ma...Fuskar nan tasa tayi jawur cikin abunka ga farar fata har kwanci jini tayi,ga bak'in cikin bayyanar wasu ahalin nasu inda ma yayi farinciki ba maza bane...
'Baiko bari akagama magana ba yabar fada rai b'ace yayi sashen mahaifiyarsa,wanda achan ma yatarar da wani tashin hankalin sarauniya hauwa,u kamar tayi hauka duk ta rud'a sashenta,ga Ammie da gimbiya Halimatu sunzo sashenta dan agana da juna amatsayinta na uwar gidan Ammie din,dakuma zaman ta na sarauniya matar sarki, su laila dasu hassana da husaina, sai kuka sukeyi khadija nataya su,wadda takejin kaunar yan uwan nata, domin basu tab'a ganin tashin irin wannan tashin hankali ba.
Mustapha ne ke jan ta tana kucce kucce dan shima dama zuwansa sashen kenan ya isko wannan kayan haushi kayan kunya gaban bayi take zage zage zuwa ga maimartaba sarki Hamza da kuma Ammie harda ma gimbiya Halimatu,Bayan mustapha yasamu nasarar janyeta daga falon izuwa uwar d'akinta,shima Muhammad yabi bayanta da fuskarnan tashi kamar tayu aman wuta,itadai khairiyyah sai aikin lallashin yan uwan nata take yi dan itama tunda tagansu taji sun kwanta mata arai tanajin soyayyarsu har cikin zuciyarta...
Gimbiya Haleematu da Ammie A hankali suka bar sashen nata tareda su hassana harda khairiyyah ma zuwa sashen na Ammie kowa zuciya ba dad'i.
A b'angaren sarauniya Hauwa,u fulani kuwa kuka take wiwi kamar wadda akayiwa mutuwa,sunyi lallashinta harsun gaji sai da mustapha yayi dubarar kiran mahaifinta sarkin Fulani sannan suka samu kanta.
"Mustapha gaba d'aya sai da yaje sashen su Ammie da gimbiya Halimatu yabasu hakuri kan abunda yafaru sannan yak'ara lallashin yan biyu da su khadija.......
A bangaren fada kuwa bayan fitar Muhammad maimartaba sarki Hamza yanemi jin ta bakin ya yen sarki Ahmad,Bayan sanar musu da bukatar
sa,Kamar yadda yasanarwa sauran mutanen acikin fadar,bayan gama jin zancensa duk sukayi shiru,dan dukkanin su babu wanda sarautar ke kod'awa ak'asa kanwarsu ce khadija ke d'anjan sarautar,ko yadda suke gudanar da rayuwarsu inka kalla zaka san akwai jinin sarauta ajikinsu mai karfi...
Maganar sarki Hamza ceta katse shirun inda yake cewa yana jiran Amsar su,suka ce abasu nan da,gobe in sunyi shawara da mahaifiyarsu,da haka zaman nasu ya watse anbarshi akan gobe za'ayi hukuncin dasuka yanke......................................................................................
*Nima anan na dakatar da alkalamina*
*Bayan ya subuce daga hannu na😂*
*Sai monday in Allah yakaimu da rai da lafiya*
*Zaku samu cigaba*
Like pls share nd comment
Like pls nd comment kuma atayani sharing Dan Allah...
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥
*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*
*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........
+2348069059746
+2349087741775
💫A MAFARKI NASANTA💫