A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh - Chapter 8
A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 8: A mafarki nasanta book 1 mallakin fa'eeh Chapter 8. *💫In my dream i know her💫* 2023 novel *is the…
3,360 words
*💫In my dream i know her💫* 2023 novel *is the story of an* *innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?SHIN WAD'ANNAN* *YAN BINDIGA DA NA HANGO KODAI SUNE SILAR RABA* *HALEE DA IYAYEN TA,?ME KUMA IYAYEN NATA SUKA MUSU INHAKA* *NE?KAI WANNNA ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA*
*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA.*
--------------------------------------------------------------------
------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️
💫P.E.W.A.💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER📚🖊️
pen🖊️*is mightier than the sword🗡️*
__________________________________________
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣0️⃣
TYPING📲📲📲
Bayan barin sarki Hamza fadar bai zame ko ina bah,sai sashen sarauniya hauwa'u dan yasan tabbas akwai matsala yasan bai kyau tamata ba duk da ya fahimci alokacin akwai sa hannunta cikin macin da yasamu na karb'ar sarauta,kuma a lokacin da yayi auren b'oyen duk laifintane shi baisan abunda yashiga kanshi ba na tsoronta ba alokacin,Auren ma nasu da Ammie Allah ne yak'addara shine..
Shigar sa sashen nata ma,aikata nata russunawa tare da fadawan dake abayan sa,kai kadai yake iya d'aga musu har yakai ga shiga Babbar uwar d'akanta wadda take taji komai har kujeru akwai ciki da tv,duk haka d'akunan suke na masarautar kowanne sashen haka yake,gimbiyah halimatu ce kadai tasa aka cire mata ta ta tvn ta uwar dakanta,saboda ita macece mai natsuwa hayaniyar tvn na takura mata acewar ta,tafison taji ta shiru ita kad'ai tana jan charbi tana azkar dinta domin macece mai son ibada kullum bata rabo da charbi a hannunta ko tana karatun alqur'ani.....
Bayan sarki Hamza yayi sallama,acikin uwar d'akanta yashiga bayan yaji shiru,ba,a amsa masa sallama ba...
*Nikam nace dama ya,za,ayi a amsa maka sallmah yallabai kishiya ai ba wasa bace bare ta auren boye,abun akwai ciwo,sai dai dan Allah yan uwa mata mudaina kishin hauka,arika kai zuciya nesa....Akamanta kuma arik'a daukar k'addara Duk yadda tazo,Domin Allah yariga yarubuta cewa matar sace itama,sai dai abi da addu,ar zama lfy da haduwar hankali*..
Jingane take kan gado takura wa tv ido kamar akwai abunda take fahimta hankalin ta baima jikinta..Gimbiya fulani kenan,Fulani! sunan ta da yakira ne yasanyata d'an kallon inda yake tsaye hawaye ne suka cigaba da tsiyaya a idonta ganin ga dukkan Alamu ya nuna maganin yasaki jikin sarki Hamza,.........
*nikam nace dama boka ko malan sun isa su juya mutun ne har karshen rayuwarsa ai abun hajiya nadan lokacine ,ke kuma mai kwasar kafafu kije dan neman agaji gurinsu saboda rashin hankali ,wai harda kayan dakin ki kika siyar dan ki samu wani abun ga wanda shima ubangijin ne ya samar dashi to bari kiji kyi hattara,domin kuwa bokaye kudin ki kadai suke ci babu mai yima bawa face Allah,dan haka kimayar da yar tabarmar ki dakike shirin siyarwa dan kaima kunkurmin kato,wanda zai mutu acikin azabar Allah,inva tuba yayi ba,domin Allah mai jinkan bawansane,Allah yatsare muna imanin mu🙏🙏,masu niyar zuwa Allah kaga nar dasu,domin ko sau daya kika taka gurin malaman tsibbo ko bokaye Allah zai yi fushi dake za,a jingine komai naki na ibada,Har sai kinyi kwana arba'in,kinga idan kika mutu awanna lokaci kin mutu kafira,anyi zuwan zomo duniya,Allah ykara ganar da mu,ya kuma k'ara muna karfin imani domin mai k'aramin imani shiyake kai kansa ga wadannan kafiran musulman*
*-------- *------------*-------------*---------*---------*-------------*
'Da dadane jikinsa narawa zaizo yadurkusa mata yana tambayar ta meya faru,Amma yau gashi yanzu harda kiran sunanta babu alamar tsoronta a idonsa,zafi bibbiyu gana zuwan Ammie da iyalanta gana murabus din zaiyi yamayar da mulkin hannun ya yan gimbiya Halimatu...
Hakuri yabata akan Auren da yayi batare da yanuna mata komai ba,ganin tadan saki yasanya sa fita yakoma sashen sarauniya Ammie baiwar Allah,domin ganawa dasu dakuma jin in sashen yamusu,su hassana sunyi farincikin ganin mahaifin nasu dan sun saba dashi sosai
Hakuri yabata da abunda yaji yafaru lokacin da suka je sashen na fulani domin mustapha yasanar dashi komai bayan barowarsa sashen na fulani.
BAiwar Allah tanuna masa bakomai dan dama Ammie akwai saukin kai,kamar yadda nafada muku chan baya lak'aninta ne har ya yanta ma haka suke kiranta dashi..
A bangaren yaran gimbiya halimatu kuwa sun sanar da ita komai tanuna farincikinta afili dama burin margayi sarki Ahmad ne cikin ya yansa wani ya gaje sa,sun yanke hukuncin abawa umar tunda shi yagama karatunsa kuma har yasamu aiki ma,federal government sun masa appointment na minister of security and investigation crime (S.I.C),ganin yadda takardunsa sukayi kyau da kuma kwazonsa awurin bikin yaye dalibbai,umar yaso yayi ja inja da yan uwan nasa musamman yayansa Aliyu sai da mahaifiyar su tasanya baki aciki ya amince ya karb'a,
"Anan yakawo maganar Aure duk da yanajin nauyin,amma baijin zai iya bari yayi sake ba,yasanar musu da kudurinsa na cewa shikam yayi mata domin yaga laila yana so yar wurin Ammie,tun lokacin yayi arba da ita yaji yakamu da tsananin sonta,sunyi farinciki sosai dajin wannan labari musamman ma gimbiya halimatu,duk da laila tana da shekaru sha biyar ne lokacin dan secondry ma tagama alokacin,su hassana da husaina ne su sunwuce tertiary institution daya tana karantar fasion and designer daya kuma masscom a skyline university a branch dinsu dake gusau.....
Sunyi na,am da zancen sa kwarai dagaske Alokacin da zancen yaje kunnen sarki HAmza yayi farinciki sosai zai cika burin dan uwansa na had'a auratayyar ya yansu...
Itama Ammie tayi farinciki sosai ta bangaren lailat tunda aka sanar mata da maganar sai ta tsinci kanta soyayyar emir,kowa yayi farinciki banda mutun daya itace sarauniya hauwa'u taso hana haduwar auren Allah yahana,tunda taji wanda za,a bawa sarautar shine laila zata Aura,sai taji ina ma khairiyyah yazab'a....kaaji soin kai
*Niko nace tun ran gini tun ranzab'e fulani, matar mutun k'abarinsa*
''Anyi nadin sarauta tare da daurin Aurensu cikin lumana,inda aka k'ara gyarawa da k'awata manyan ginukkan na zamani na masarautar,inda aka ware musu ,bayan angyara dai daga cikin bangarorin masarautar wayenda suke atsare ginukkan gwanin burgewa irin ginin sarauta na asali,anyi taron biki lfya an watse tareda Addu,ain samun zaman lfya ga amarya da angon ta sabon sarki....
Bayan gama bukukuwan kowa yakoma kan harkokin gavansa,Aliyu da Abdulrashid kowa yakoma kasar karatunsa harda khadija dasu khairiyyah da mustapha,dake karatu a suma acikin gari a noun university dake kano ,muhammad(malan) kad'ai akabari domin yace yafison karatu agida shiyasa aka yake karatu a FUG,yana karantar politial science...
''''''''''''''''Bayan wasu shekaru shima Aliyu yazama cikakken dan kasuwa dan yasamu damar da kowace zai iya kafa kasuwancinsa batare da wata wahala ba,yayi Aure ya auri Hassana,inda har ta haifi santalelen yaron ta namiji kyakkyawa jinin larabawa da fulani,inda yaro yaci suna Abdul rashid ana masa lak'ani da Ammar Anyi shagali sosai wanda ba,atab'a yiba,inda itama Husaina ta yi Aure ta Auri wani Babban Abokin sarki umar mijin laila,Wanda yaganta A auren su laila din har ya nemi Aurenta,leutenant jabir muhammad soja Abokinsa ne nak'udda tare su sukayi karatu a uk,bayan dawowarsu najeriya ne shima jabir yasamu matsayin leutenant....
Inda itama ta haifi d'anta sak kamar ta jikinne na babansa bayan tayi arba'in ne,itama Hassana ta haife nata cikin...
Yaron husaina yaci suna Al- amin sunreni ya yansu cikin Aminci da kwanciyar hankali
....A bangaren sarauniya lailat da umar tsif kake ji har yanzu tun abun bai damun laila har yafara damunta,A wasu lokuttan zata zauna tayi ta kuka ganin yan uwanta wayenda ma tariga aure sun haifu ita kuma shiru,sarki Umar shike lallashinta da kuma gimbiya halimatu,kaji*surukar arziki**Allah ya had'a mu da irinsu*🙏
Da kuma Ammie ,daga cikin abun bakincikin da yafaru akwai rasuwar tsohon sarki Hamza,inda mutuwar ta gigita Ammie saboda bata wasu dangi sai shi akasar nigeria shine gatanta sai ya yanta,shine take samun sanyi agaresa saboda gimbiya Hauwa'u kullum cikin musguna mata takeyi aboye tun kafin su hassana suyi Aure take wahalar dasu tahanyar furta musu bak'ken maganganu ko sanya su aiki wanda basu saba da yinsa ba,Amma ammie bata taba fadawa mai martaba ba,zagi kala kala tana sha har cewa da ita takeyi wayasani ma ko sarki takari yakwaso ita ba balarabiyar kwarai bace,*nace su larabawan dama akwai na k'arya*..Duk da taga dukkanin tsarin halitta ta larabawa atare da ammie din..
Sunyi kukan rashin mahaifinsu,khairiyyah
harda suma itada lailat shiko malan ko ajikinshi dan yana ganin kamar mahaifin nasa yatare masa gaban hantsine gurin kwatar sarautar...
Hassana da Husaina laila sunji sosai mutuwar,bayan gama zaman makoki suka cigaba da rainon y yansu.....
"""""'''''''''''''''''''''''""""""''"''"''''''''''''''"""""""""""""Bayan wasu shekaru .....Kyawawaan yara ne wanda ak'alla zasu kai shekara Biyar tare da wata kyakkyawar yarinya d'auke a hannun d'ayan wanda skin dinshi take chocolate colour,kuma kyakkyawa ajin karshe.wadda bazata wuce shekara d'aya ba...
Fuskar sa da alamun damuwa ganin yadda kyakkyawar farar yarinyar dake hannnunsa take zille zille takoma a hannun d'ayan yaron wanda yakasamce fari ne tass afata shima dai kyakkyawane..
Murmushi d'ayan yayi yana furta ni bazan d'auke ki ba,salon kimun fitsari ya iyar da magaanar yana matsawa baya....
Aiko kamar jiratake yana matsawa baya tak'ara b'are baki tana kuka,duk da karantar shekarunta,Amma irin yaran nan ne masu shegen wayo,kukan da ta tsala ne yasanya kyakkyawan yaron sakinta a k'asa saboda yadda kukan yashiga kunnensa Yana yamutsar kyakkyawar fuskar sa Kamar yasaki kukan shima.....
Aiko da gudu d'ayan yaron ya koma cikin gida yana kwala kiran Aunty! Aunty ! wata farar kyakkyawar matashiyar matace wadda bazata shekara ishirin da hud'u ba ta b'ullo daga k'ofar kitchen tasha kaya na alfarma,tana furta lafiya Yarona,cikin shesshekar gudun da yayi yake fad'in Aunty Ammar ne yasaki norah k'asa,bai rufe bakinsa ba sai ga nanny din dake kula da norah tare da yaron danaji ankira Ammar d'auke a hannunsa tana tsala kuka,harda shid'ewa shima kuma Ammar d'in hawaye ne ke tsiyayar masa a ido..
Muryar nanny d'ince take fadin Allah yataimaki gimbiya sarauniya ya matsamun sai nabasa itane,gashi ba wani iya daukar ta yayi ba,shine nabasa nadan zagaya ne sai chan nji kukanta,ki gafarceni,yanzu haka ma nayi nayi dashi yabani ita inlallasheta yak'i gashi shima kukan yake yi,murmushi kawai tayi bayan gama sauraren bayanin baiwar,
Jawo hannun wanda aka kira ammar tayi sannnan ta karb'i yarinyar da naji ankira norah a kafad'ar ta tadaura ta tashiga girgiza ta,shikuma Ammar tazaunar dashi akan kujera tana share masa hawayen sa da suka kasa tsayuwa....Nora da zuwa wannnan lokaci tayi shiru jinta abisa kafad'ar mahaifiyarta sai shesshekarta kad'ai kake ji,tak'ara tsala kuka wanda yafi na farko tanayi tana shidewa fararen manyan idanunta sunyi jawur dasu na azabar datake ji, wanda take jikin ta yagashe,cikin shesshekar kuka Ammar yake furta Aunty kibawa nora hak'uri tadaina kukah yana cigaba da kukan shima,d'ayan yaron ne ya matso kusa gareshi yana fadin Ammar kayi shiru kaji yakai karshen maganar cikin tausayin sa,daga yanayin yadda suke kasan cewa suna mugun son junansu,hawayen sa yashare masa yana k'ara furta norah tayi hakuri Ammar bakaji tay shiyu ba.....................
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥
*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*
*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........
+2348069059746
+2348087504734
----------------------------------------------------------------
💫*A MAFARKI NASANTA*💫
*💫In my dream i know her💫*2023 novel *is the story of an* *innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?SHIN WAD'ANNAN* *YAN BINDIGA DA NA HANGO KODAI SUNE SILAR RABA* *HALEE DA IYAYEN TA,?ME KUMA IYAYEN NATA SUKA MUSU INHAKA* *NE?KAI WANNNA ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA*
*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA.*
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S
📚🖊️
pen🖊️*is mightier than the sword🗡️*
------------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE 2️⃣1️⃣
TYPING📲📲📲
...'Sallamar wani matashin mutun ne cikin shiga ta alfarma ta kayan sarauta alkyabba da rawani masu kyau tare da wani bafade guda amma shi yana bakin bakin kofa ne,Muryar shi ce ta katse da yazo dashi yakin furta meyasamu mamanah labari ya isar mun fada gata chan tana kuka,Murmushi matar da aka kita tana fad'n haba Babban sarki Norah ai ta dena kukan ma ka kwantar da hankalinka baka ji tayi shiru ba,cikin ya nayinsa da sanyin hali ya furta layla miko mun ita inganta,yana zama akan hadaddun rugs d'in dake falon na alfarma,tab'a jikinta yayi bayan tamika masa ita,ajiyar zuciya yasauke,jin jikin nata zau da zafi,lokacin baiwar Allah har ta fara baccin wahala,Murya asanyaye yace meyasameta ne.?..
A hankali gimbiya laila tafurta tafad'i ahannun mutumin tane,kaganshi chan gefe ma shima yana nashi kukan,duban sa yakai inda Ammar suke,Bayan yagama k'are musu kallo tsaf su duka,sai kuma Ahankali ya k'yafato su ,alamar su zo,a hankli suka taso hannyensu rik'e dna juna,Ammar ne ya duk'a k'asa yayi kneeldown tare da kama kunnuwansa yana tsiyayar da hawaye yana kallon norah dake baccin wahala beauty face dinta tak'ara fitowa fess, cikin wani yanayi ya furta kace norah tayi hakri itace fa tasa na sake ta ba da ganganba,dodon kunne na naji zai fashe yakai karshen maganar kamar ya yayi ihu yake ji na jin zafin halin da norah din take ciki.....
Murmushi wanda aka kira da uncle yayi yana share ma Ammar hawayen sa dasuka kasa tsayawa,jawoshi yayi yazaunar agefensa inda D'an uwansa yazauna,A hankali yafurta mai sunan Autan maza yana jin wani abu na taso masa bayan kiran sunan Autan mazan,kayi shiru kadaina kukan nan kaji Halimatu sadiya tayi bacci ma kaga tadaina kukan yakai karshen maganae yana shafa beauty face dinta,
Ajiyar zuciya ammar yasauke mai nauyi kamar wanda waci bakar wahala yasamu hutu,Jin cewa ta hakura, wanda har uncle din saida yaji fitar ta,har Aunty da yanzu tazauna bayan gama bawa ma'aikatan dake cikin kitchen umurnin abunda zasu aiwatar yau domin bazata samu damar shiga kitchen dinba norah ba lafiya...
murmushi mai taushi gimbiya laylat ta sauke tana mai shafa lallausar sumar dake shimfid'e abisa kansa,domin kuwa tana mugun son Ammar musamman yadda yake nuna kulawar ga norah dinta,wadda tun ranar da fad'o duniya yake kokarin daukar dawainiyarta duk da karancin shekarunsa,wannna soyayya dayake ma nora har maamaki take bata ba ita kadai gaba daya a halin ma sun san yadda norah take agurin Ammar ,shiyasa take jin wani kud'uri yana shigarta ahankali ..........
Bayan kwana biyu tun faduwar da norah tayi kullum cikin kuka take ga rashin bacci har saida aka kira family doctor nasu ya duba ta sannaan yatabbatar musu da ciwon kaine ke damunta mai tsanani,tun lokacin tasamu sauki bayan an rubuta mata magungunna,daga baya sai abun yadawo wanda duk bayan kamar watanni sai tayi ciwon kai da zazzabi mai zafi,Ammmar shine mai jinyarta lokacin duk da yarintarsa dan Alokacin yana da shekara shidda itakuma shekara daya da rabi Aduniya, kuma tun alokacin yadau alkawarin zama likita saboda norah ganin yadda take wahala,Domin yakula da ita ita kadai...Wannnan kenan............
*MUKOMA CIKIN LABARI*
Bayine ta ko ina suna gabatar da dukkanin ayyukan dasuka zame musu Al adah wato kai kawo domin gudanar da aikin su,kowa da kalan uniform na sashen da yakewa hidima da masu kula da kofa fada, masu kula duk wani motsi na fadar,masu kula da dawakai,abun gwanin burgewa sai wanda yagani...
Tangamemiyar masarauta ce mai tsaunukkan gine gine masu kyau irin dai yadda kuka san ginin gidajen sarauta suke,tako wanne gefe haskene tar kamar rana na ban mamaki ko lif lif da shuke shuke,ga gurin aje dawakai da motoci na alfarma.
Wata faffadiyar koface wadda zata sadaka da fadar sarki nan na kutsa kaina domin dauko muku rahoto duk da manyan dakarun dake tsaronnata ..
Had'addiyar fada ce mai abun burgewa tako ina fadawa ne atsaitasye ga wata kujera ta alfarma wadda tasha adon gold sai shining take yi ga fadawan dake gefen kujear baibaye da ita sai fifita sukeyi ma wanda ke kan kujerar ta alfarma Ahankali duk da AC din dake huro iska mai dadi wanda yahadu dawani kamshi...
A hankali fadawan suke furta gyara dai sarki Mai dubbanin alkhairai,Allah yakara lafiya,jin tarin dayake yi wanda ke nuna alamar mura ke damun mai yin tarin,Hannunsa yad'aga cikin nuna mulki da Izzah,Alamar ya isa A hankali naji kyakkyawan dattijon da bai haura shekara sittin ba yayi magana da muryarsa mai nuna dattako da manyan taka,yana mai furata "har yanzu yarima baice komai ba ne galadima"?
Mutumin da naji ankira da galadima ne naga yaduk'ar dakansa yana furta Allah yataimaki sarki,ehh haryanzu bai nuna yaga sak'on mubah,yau wata takwas kenan,ni anawa ganin Allah yataimaka sarki kawai akyale sa sannan Ku gyara tsakaninku....
Wani murmushi mutumin yasaki Wanda yatsaya iyakar labbansa,zaka gane hakan inka kura mai ido duk da yana cikin rawani ,shiru baiba galadima amsa ba,saima mikewa da yayi,Dan danan fadawa suka fara karesa suna furta gyara dai sarki mai dubbanin alkhairi,gyara dai sarki mai masarautar gado mai garin na sambo,,,
Mai garin na sambo zai fito,wata murya CE ke d'aga wannnaa sauti a waje,kirari suka cigaba da yimasa tare da kara gyara masa alkyabbar sa ta alfarma sai walkiya take na duwatsun gold,A hankali yake takawa harsuka fito daga babbar fadar tasa sai dai yau baibi ta kofar dazata sadashi da sashen UNNI ba
Yafito ne ta kofar dazaka iya ganin komai dake gudana atsakiyar masarautar,tafiya yake yi Ahankali inda duk inda sukabi ma'aikata bayi sai sun masa irin gaisuwar nan da yan Korea suke yi a series dinsu na sarauta ga shuwagabannisu gamasu kallon su zaku gane yadda nake nufi Niko vow suke cemishi....
( Adan sunkuyar dakai kadan sai alankwasa hannu biyu ahade su guri daya kamar mai daidaton sallah,sai a saita shi akan tsakiyar goshi)Allah yasa kunhgane😜
Kansa kawai yake d'agawa alamar karba gaisuwar tasu acikin lemar da suka ware masa ta alfarma, har ya isa inda manyan motocin suke aparkey na alfarma,Isar sa wurin d'ai daga cikin fadawan da ke lullube dashi ya bude masa wata arniyyar parado new design bak'a wulik mai tinted glass irin yan 57billion dake parkey agefe cikin wata had'addiyar rumfa inda dagani nan ne mazaunin aje wasu motocin na musamman😱 kai FA'EEH wannan karya...koda yake abunda nagani ne ai😇
Ahankali yashiga cikin motar dai dai Wanda ke rike da dai Wanda ke rik'e da had'addiyar umbrellan da suka kara masa tun lokacinda aka shimfida masa bugaggiyar carpet ta alfarma an rubuta MURAI'S PALACE akanta cikin tsari mai kyau....
Bayan shigarsa motar tafiya kad'an sukayi da direban da yatuk'osa da sauran fadawan sa dasuka k'asa da algaitu da busa suna masa kirari,motar drivern yafaka A wani tangamemen gida dake d'ai daga cikin gidajen masarautar na alfarma,take fadawa suka zagaye motar suna masu kakkaresa bayan yafito a lokacin har an kara shimfida masa carpet tare da bud'e masa umbrella ta alfarma abun gwanin burgewa sai Wanda yagani wollah in maku hausar mu ta sakkwato😀.
Tafiya kad'an yayi ya Iso kofar shiga mai rike da had'addiyar kofar ce wadda zata sadaka da falo, ya wangale masa bayan ya rusuna masa alamar gaisuwa
Shigarsa had'adden falon na alfarma yabani damar debe keyar ido nah masha Allah nake furtawa tsayawa kwatantamuku tsaruwarsa bata lokacin ne,falon yaji komai na more rayuwa....
A hankli dukkanin bayin dake kai kawo suna hidima asashen suke rusunawa suna gaidashi hannu kadai yake iya d'aga musu har ya isa wata kofar inda naga wata dattijiwa mai uniform wasu colour masu kyau tafito,Ashe Babbar Amintacciyar masarauta ce tun lokacinsu Ammi take hidima dasu,
Inda yanzu ma ita keyiwa sarauniya hassaana da sarki duk da bawata hidimar bace kawai dan duba sauran ma,aikata ne sai yin iso ga sarauniya,
Iso tayi ma sarki ga sarauniya bayan tagama yimasa kirari nuna gasuwarta bayan ya karba tawucewar Alokacin duka ma,aikatan kowa yacigaba da aaikinsa....