Kenza eBookz

Abadan complete hausa novel - Chapter 26

Abadan complete hausa novel - Chapter 26

Abadan complete hausa novel Chapter 26: Abadan complete hausa novel Chapter 26. Daf da zata qarasa bangaren nasu tana ci gaba da babaka dariyarta suka ci…

3,313 words

Daf da zata qarasa bangaren nasu tana ci gaba da babaka dariyarta suka ci karo da baaba uwani,wata uwar tsawa ta daka mata ''ina zaki je uwar kinibibi?'' jikin baaba uwani na rawa tace ''ah....ummm...zani mi gaisa da hajiya ne?'' tsatstsareta nene tayi da idanu ''me nace dake tsohuwar banza?'' ''ahh...kince....kince ne kada ki sake ganina bangaren ku indai ba inaso ma rasa aiki na ba'' gyara tsaiwarta tayi ''kin shirya rasa aikin naki kenan?'' girgiza kai ta shiga yi ''a'ah,don Allah hajiya nene kiyimin afuwa'' ''kinsan me nakeao dake?,matuqar bakison rasa aikinki cikin gidan nan kada na sake ganin qafarki a harabar gidan nan,daga yau ziwa gobe jibi ke har gata ma,kina jina ko?''

da sauri take gyada kanta ,kana ta bata umarnin ta koma inda ta fito hawaye ne kawai ke zuba daga idon nene tana sharewa,idan banda darajar mami da take tausayawa babu abinda zai zaunar da ita a gidan,abubuwa marasa dadi da idanunta ke gane mata wanda ke faruwa shine ummul aba'isin zamanta cikin gidan badon wani abu ba

🍂🍃🍂🍃🍂

babu wanda ya sake cewa komai har suka qarasa gidan hisham din,gida ne madaidai ci mai kyau wanda ke dauke da makeken falo kitchen dining area sai dakunan bacci guda hudu

A falo suka tadda abdallah kan kujera,gwiwarta a sanyaye ta qarasa gurinshi kanshi na duqe a qasa,a gabanshi ta durqusa ta sanya hannunta cikin nashi tana kallonshi,sam yaqi daga idanunahi ya kalleta,hakan na nuna mata cikin tsananin bacin rai yake,ta leqa fuskanahi idanunahi biyu don tana iya ganin qiftawar idanunshi,sai zuciyarta ta karya ta tura kanta tsakanin cinyoyinsa da fuskarsa sai a sannan suka hada idanu,ya zuba matq idanun naahi da suke har yanzu kalar ja

shigowar hisham falon ya sata miqewa,ya taimaka suka shiga da abdallah daya cikin dakunan dake falon,dakine mayalwaci mai hade da toilet,gado madubi side bed sai cupboard da kujera doguwa qwaya daya da carfet da ya malale qasan dakin da shi a maimakon tiles ''zan fita amma bazan jima ba zan dawo'' ya qarasa gaban abdallah yace ''abokin sai na dawo mintina kadan zan dawo''kai kawai ya gyada masa ya miqa masa hannunshi sukayi musabaha

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

Qarfe goma na daren ranar suka fito daga maboyar da nene tayi musu cikin dakunan barcinta,gaba dayansu baqaqen kaya ne ajikinsu hatta da mask din da suka sanya,kowannensu wuqa ce boye a jikinsa

taku daya biyu nene tayi ta tsaya a gabansu,dukkansu sun fita tsawo nesa ba kusa ba,ta dubesu daya bayan daya ''banason a samu kuskure ko sabani cikin aikin nan,shekaru na kwashe masu yawa ina neman wannan damar,saboda haka ku tabbatar komai ya tafi yadda ake so'' dqya daga cikinsu wanda da alama shine oga ya buda hanci ya shaqi iska ''haj,sanin kanki ne munsan aikin mu dalilin da yasa kema kika neme mu kenan'' gyada kai tayi ''haka ne kam''

da daya da daya suka dinga fita har suka isa sashen abdallah,jijjiga qofan suka yi suka jita gam hakan ne ya tabbatar musu a kulle take,don haka kansu tsaye ba tare da wani tsoro ko shayi ba tunda sun san cewa babu security ko daya cikin gidan bare su jisu duka nenen ta bawa kowa aikin da har su gama abinda zasuyin ba zasu riskesu ba,take suka hau lallauya qofan da wani shegen qarfe suka ajjiyeta saahe guda kana suka kutsa ciki

Sau uku yama luma wuqa kan tarin filallukan dake tare a kan gadon ganin qamas babu alamun jini ya sanya su yaye bargon,a mamakance suka kalli juna kana daya daga cikinsu ya ciro waya ya kira nene,da zumudinta ta daga kiran ga tsammaninta sun cika aikinsu cikin mamaki da fushi take fadin ''wanne irin babu kowa?kada ku gauamin maganar banza mana,yaron da ko motai bai iyayi ina zaije?,kuma tun jiya babu kowa a tare da shi balle ace ya fidda shi?'' cikin ciccijewa ya maida mata amsa ''kinga hajiya duk ke kika san wannan,kizo kawai idonki ya gane miki'' da azama tq fito ita da zahariyya da danan suka bazamo bangaren abdallan,surutai take tayi kamar wadda ta samu matsala a qwaqwalwarta don bata taba sawa cikin lissafinta cewa wannan karon akwai cikas din da zasu samu ba

cirko cirko sukayi cikin dakin bayan kammala duba ko ina na cikin gidan ciki har uwar dakin mami wadda batasan me ake nema ba,ta dai ga nenwn kai tsaye ta ahige mata daki tana dube dube daga bisani ta fito ''taya ya abdallah ya fita daga cikin gidan nan'' ''ke za'a tambaya hajiya''cewar ogansu yana maida locker da tasa ya balle ta dakin abdallan wadda basuyi katarin samun komai ba sai rafar din dubu hamsin

''miqo min wadan nan kudaden,yanzu hatta da takardun kadarorinsa ma ace babu su cikin dakin nan,anya wani baisan abinda muka shirya ba kuwa cikin gidan nan,anya banu mai,mana labe da leqen asiri?''ta fada tana zare ido kamar wata zautacciya kudin ya kalla kana ya dubeta ''ban fajimci me kike fada ba,wannna kidi ai namu ne ladan zaunar damy da kika yi nuka kwana cikin gidanki,ai lissafi zamuyi kawai ki cika mana sauran miliyan dayan da mukayi da ke zaki cika mana'' ''idan aiki yayi kyau ba,ana ta kai wa yake ta kaya,kwananku kuma cikin gida na ai ku kuka qaru da ni bani na qaru da ku ba asara ce ma ta hauni goma da goma,tunda har 'yata na baka ta tayaka kwana ko?baya ga haka ma ni a yanzu bani da miliyan daya bani da dalilinta,da aiki yayi kyau ne ma na tabbata cikin dukiyar da zamu samu ba komai bane cire miliyan daya daga ciki ''ta fada tana matsowa gabansa tare da zazzare idanuwa,don ji take su suka ma ja mata duk wata asara da ta fada matan

Dariya ya sheqe da ita ''haba hajiya,kinci qarya kin kwana da yunwa,muba qananan makasa bane ba irinnu akewa haka ba''ya sake matsowa inda take har tana jin warin wiwinshi na dukan hancinta,yatsunshi ya daga guda uku ''kwana uku kacal na baki ki turo mana ragowar kudinmu,wlh wlh wlh ko ke kikayo naqudata matuqar baki turo da sauran kudin nan ba ke da 'ya'yanki ki tabbatar kuna cikin masifa,domin duk ranar dana waiwayeku sai kun buraci mutuwarku akan rayuwarku,na baku dama ku gaggauta warware harqallar da kuka qulla dani''

ya juya zai wuce adnan yasha gabansa cike da taurin kai da jin shima karansa ya kai tsaiko yana ciccije lebe cikin son nuna shima jan wuya nebayan shi kansa yasan fanko ne lamba daya,kafin yace komai yasa kan wuqar hannunshi ya daki kanshi saiga adnan din a qasa,ihu nene ta saka tayo kansu,da tsinin wuqar ya juna ta ta koma baya tayi luf sai da suka kammala ficewa ta saka kururuwa ta biyo bayansu ko Allah zaisa taci sa'a wani daga cikin security din sun dawo suyi ram da su,saidai ina,babu wanda ta samu bakin get din kamar yadda ta watsa su don gabatar da aikinta

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

ta kai ta kawo tayi hakan ya kusa sau goma sha biyar,ji take kamar zata hau bori ko hauka kafin ta samu guri ta iya tsugunnawa,ta dubi adnan da kanshi yasha dauri da bandeji da zaharkyya wadda ke zaune tana faman hade fuska,babu wanda take ganin laifi sama da nene,don ita kam ta gaji da wanna jeka ka dawo din,ta riga da ta yanke ma kanta hukuncin abinda zata aikata matuqar wannan karon haqarsu bata cimma ruwa ba kamar sauran lokutan baya ''babu shakka cikin hisham da maryam akwai wanda ya fidda abdallah daga cikin gidan nan,ko kuma daya daga cikinsun ya aikata hakan,kuma nafi zargin wanna shaidaniyar ce marya,tabbas kuwa''ta fada tana guada kai hadesake tabbatarwa kanta ''qwarai kuwa nene,nima na zargi haka tunda kinga fitarsu ana gobe za'a gudanar da aikin,cikinsu akwai wanda yake da hannu kan tsirar abdallah''inji zahariyya,shikam adnan ya kasa magana ta kanahi yake,tsanin ciwo yake masa kamar zai tsage gida biyu har zumbur nene ta miqe tana fadin ''wallahi basu isa ba dukkansu,duk wanda yaci tuwo da ni miya yasha''

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Tana cikin kitchen tana qoqarin hada masu abincin rana ta jiyo hisham na qwalla mata kira,cike da mamaki ta ajjiye abinda take yi din ta fito don bata taba jin ya mata makamancin irin wanna kiran ba tashin hankali ta gano qarara cikin idanunshi ''dauko duk abinda kika san kina da buqata ki sameni a mota na riga da na kai andallah ciki,babu lokacin bayani na miki shi a hanya'' bata tsaya tambayar ba kuwa,ta koma kitchen din a gurguje ta kashe gas din ta ahiga dakinsu da suka sauka ta dauki iya abinda take jin zata iya buqata ta fito ta taddasu cikin mota

Tafiya yayi ta kusan mintina hamsin har suka fara barin ainihin qwaryar birnin kano sanna yayi parking a nutse ya dubeta ''maryam,na samu bayanan sirri daga daya daha cikin security din gidansu abdallah wanda nake biyanshi bayan barinmu yake samin ido kan duk wani motsi da yanayi da gidan ke ciki,don na tsammaci dama lallai wani abu na iya faruwa kan barinmu gidan da abdallah da mukaui,hasashena kuwa ya tabbata ya zama gaske iya,suna na ne ma farko cikin jerin mutanen da nene ke tuhuma,don ta saka amata bincike kan inda nake,yanzu haka mutanen na kan hanyarsu ta zuwa gidana,dalilin barowarmu gidan kenan''

kuka ne ya qwacewa maruam,wannan wace iriyar mace ce nene?me ta dauki rayuwar duniya,baza'a mutu ba?dawwama kowa zaiyi yana abinda yaga dama?,me take nema ne cikin duniyar da dukkanta bata kai qima da darajar fika fikin sauro ba agun Allah,wanne jin dadi ne a ginta ta kashe ran mumini wanda qimatsa tafi ka'aba agun Allah?,tana tsammanin idan ta aikata hakan taci bulus ne ko kuwa,zata taira daga hisabi da zabar Allah ne?dukkan amsar itace a'ah,babu

''a halin da muke ciki maryam kuka babu amfanin da zai mana,ki tsaida kukan mu nemi mafita'' tabbas maganar hisham haka take,ba bata lokaci ta ciro wayarta ta sake kiran mama wadda basu yi awa biyu da yin waya ba,magan sukayi ta kimanin minti talatin da ita kana ta kashe wayar ta dubi hisham kasancewar handsfree ta saka yaji komai kansa ya gyada ''maganar mama gaskiya ce,kuma tsarin nata yayi,nima da mun isa gobe zan wuce katsina hometown namu''ya fada yana mai gamsuwa da bayanin maman yana kuma sawa motar key,ta juya ta sake kallon abdallah har yanzu idanunshi a lumshe yake,babu baki balle ya bayyana abinda ke cin ransa,ta tabbata ba magana daya ke dawainiya da zuciyar abdallah ba,suna da dama,koda bao jude idonsa ba,koda baiyi,magana ba tana ki a jikinta zuciyar abdallan a quntace take,takan tashi kokawa afili da boye duk da shi din tsananin jarumtarsa bai taba barinta taga hawayensa ba

Da taimakon bayanin da mama ke masu a waya suka kai ga isa qauyen NI'IMA dake cikin qauyen gaya,tun daga shigowarka garin zaka bawa kanka amsa,tabbas qauyen yaci sunanshi ni'ima,qauye ne da Allah ya wadata su da yawaitar korayen shuke shuke qoramu dabbobi da lullumi ma'ana rashin haske da zafin rana duk da haka sai da sukayi tambaya kafin su kai ga isa ainihin gidan da suke nema,gaya garin kakanninta ne tana zuwa lokaci bayan lokaci saidai qauyen ni'ima din zata iya irga iya adadin zuwanta tunda bata da wani shaqiqin da zata zo gunsa face wannan tsoho qwaya daya da yake qanin kakanta

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽

[6:27pm, 9/22/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_*

▶4⃣5⃣

*_Mazan Allah S A W yace:ku umarci 'ya'yanku da yin sallah suna da shekaru bakwai,sannan ku dakesu saboda ita idan suka kai shekaru goma,kuma ku rarraba musu gurin kwanciya(ma'ana ya zama gurin kwanan maza daban gurin kwanan matan daban yayin da suka cika shekaru goma)_*

Gida ne ginin qasa kamar yadda yake kasancewa ginin gidajen qauyuka,saidai wannan ya dan banbanta da nasu damin uasha shafe da ruwan makuba,hakanan ginin sumul sumul yake sakamakon fulastar kar qasa da aka yi masa da kuma makubar da akabi aka shafe ginin da ita.

Maryam ce ta fara shiga,kamar yadda muka sani yan uwanmu na karkara basa gini quntatacce hakan ce ta kasance ga wannan gida,babban tsakar gida ne mai girma wanda babu sumunti a qasan sa,turbaya ce saidai ta sha shara fes da ita,ga alamun shatin tsintsoya ne,daga can quryar katangar gidan garkene na dabbobi dake a tsaftace shima,sai rijiya daura da shi wanda lema ce duk a bakinta da tukwanen qasa da aka kikkife da alamu wanke wanke aka gama agun babu jimawa.

ta sake yin sallama kin shiru ba'a amsa ba karo na uku,cikin daya daga dakuna hudin dake jere taji muryar matashiya na amsa mata,ta fito sanye da roga da zani na atamfa wadan da suka danyi haske saboda dan jimawar da sukayi a duniya,maryam ta duba itama ta kalleta ''don Allah inna wuro fa?''maryam ta tambaha,sai ta juya ta kalli dakin kana ta kalli maryam ''tana ciki salla take amma yanzu zata....''' ''wake sallama ne mero,a shigo mana'' muryar inna wuro ta katsesu ''inna wuro baqi kikayi'' ''kaddai ace su meramu ne har sun iso haka da wuri''ta fada tana yunqurin fitowa,kasancewar ta san zasu zo din mama ta kirata awaya ta mata bayanin zasu zo din ta wayar mustafa jikan gidan.

hannunta dauke da tabarmar kaba sabuwa dal ta fito,dattijuwa ce wadda aqiyasce zata doshi shekaru sittin,tsaf da ita cikin cikin atamfar itama da hijabi ruwan madara,fuskarta ta fadada da fara'ar ganin maryam din ''to kuma ya na ganki ke daya''itama murmushin ne afuskarta ''inna suna qofar gida'' ''to yi maza kice musu su shigo daga ciki mana''ta fada yayin da take shimfida tabarmar.

Tare suka shigo hisham na tura abdallah kan wheelchair ''hukumullahu min zalika,Allah mai yadda yaso da bayinshi''inna wuro ta fada tama kallonsu ''sannu dam nan sannu''ta qara fada tana kuma gyarq musu gun zama matashiyar da inna wuro ta kira da mero dazu ta qaraso dauke da kwanonsha cike da ruwan tulu mai sanyi fari tas ta ajjiye gabansu,kanq ta ja hijabinta daga kan igiya tana fadin ''inna zanje gida,idan na dawo r yau to,idan kika ga ban dawo ba kuma sai gobe'' ''to mero na gode Allah ya huta gajiya,ki gaida su azimin''

Bayan gaishe gaishe shiru,ne ya biyo baya inna tana kallon ikon Allah ''yanzu mairamu tun yaushe lalurar ta sameshi?''a nutse tayi mata bayani,kamq bqki innan tayi ''matsalar ku kenan mitanen binni,boko tasa baku da kulawa sam,ni kam ba wai zato ba amma wanna lalura ta yaron nan batayi kama da komai ba face sihiri,kuma kinsani sarai qanin kakanki masani ne kan irin wannna matsaloli baki tuntiba ba,yanzu ma zuwa kukayi kenan idan qura ta lafa ku koma ba neman magani ya kawoku ba'' hisham ya guara zqma jin hanyar waraka na shirin samuwa ''a'a inna,har maganin ma mun zo mu nemeshi'' shiru tayi ma wasu 'yan mintina kana tace ''to Allah yasa adace,insha Allahu Allah zai kawo qarshen abun nan kusa''

maryam ta dubi inna wuron ''ina tsoho alhajin ne?'' ''kinsan watan tafiya gabas ne,bana Allah ya kirashi yana can qasa mai tsarki,ina tsammanin yau duka kwananahi uku da tafiya,amma muna sa ran nan da sati uku zuwa hudu zasu dawo insha Allahu'' ''Allah ya dawo da ahi lafiya''suka hada baki ita da hisham wajen fada ''daya dawo insha Allahu zan masa bayanin komai,idan rabo sai kuga ya warke'' ''Allah yasa''inji hisham cike da fata.

In banda sannu babu abinda inna wuro kema abdallah,gaba daya tausayinshi ke damunta,irin wanna lalura mai fama da ita kadai yasan yanayin da yake ciki,da kanta ta bude musu wani daki can bangare daya,ba laifi dakin akwai girma,malale take da leda duk da cewa ba sabuwa bace,akwai labulaye a window da qofar,sai tsohuwar katifa da kujera qwaya daya,a ahare dakin yake fes kasancewar inna wuron bata lamuntar qazanta hisham ya qarewa dakin kallo kana ya girgiza kai ''rayuwa mai juyi kuyi,Allah mai yadda yaso''ta karanci me yake nufi,tabbas ita kanta ta sani abdallah dan gata dan gayu,young millonier yafi qarcin zama cikin qauye ma baki daya ba dakin ba.

maganar hisham ta katse mata zancan zucin da takeyi ''abdallaj bazai iya zama cikin dakin nan haka ba maryam,zan ahiga na laluba inda zan samu kayqn buqata da za'a ma dakin kwaskwarima''kai ta jonjina babu bata lokaci ya fice,ta kalli abdallah suka hada ido uana mata nacin kallon nan nashi ''bari naje nayi alwala nayi sallaar la'asar,idan na dawo sai in maka alwala kayi taka sallar''ta fada kanta aduqe sabida naugin idanunshi da take ji kai ya jinjina mata kana itama ta fice.

Sai bayan sallar magariba sanna hisham ya dawo niqi niqi da kaya cikin akori kura,cikin mintina qalilan da taimakon yaran maqota da kuma taimakon mustafa aka gama ahigowa da komai,kayan daki ne da suka hada da katifa labulaye kujeru cusion guda biyu fanka ta tsaye carfet mai girma da zai iyacinye dakin,robobin wanka food falask har da risho dan madaidaici da set na tukwane,kayan sawa nashi da na maryam akwati wadda zata iya cinye musu kayan,duk dai wani kayan amfani da zasu iya buqata,hatta da kayan abinci ruwan roba da lemuka creet na qwai da sauransu ba inna wuro ba hatta maryam ta jiniina siyayyar,sai da ya niqi tafiya har cikin jigawa sannan ya jado siyayyar,tunda su sinyi tsaki,yasunyo nisa da cikin birnin kano kuma basu qarasa jigawar ba.

A daren mustafa ya taimaka masa ya shimfida carfet da kujeru da katifa suka shimfida sabon zanin gadon cikin dakin hisham ya kwana tare da abdallah ita kuma ta kwana tare da inna wuro

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

zuwa goma na safe dakin ya zama gwanin sha'awa tamkar ba shi ba,sha daya na rana sai ga mutane daga company mtn sunzo hada solar,da mamaki maryam ta dubi hisham ''hidimar nan tayi yawa hisham,sai kace zamu dawwama ne a garin?'' murmushi yayi kana ya girgiza kai ''maryam kenan,baki san waye abdallah ba aguna,abdallah shine tsani na dukka wata rayuwa ko matsay da na take ko nake kan takawa a yanzun,ba don Abdallah ba ina zaton da tuni na jima gidan mahaukata,abinda abdallah ya yimin bazan iya biyanshi ba,ya taimakamin da jikinsa da aljihunsa da lokacinsa ta qwaqwalwarsa ma baki daya,Allah ne kadai zai iya biyanshi abinda yayimin a rayuwa,babu abinda bazan iya bawa abdallah ba,wannan abun da nake masa ban masa kaso daya cikin darin abinda ya yimin ba,abdallah dan halak ne dole nima na nuna masa halacci'' kallo daya ta masa ta tabbatar daga qasan zuciyarsa abinda yake fita bawai daga fatar baki ba

cikin qasa da awa uku suka kammala wearing din baki daya aka kunnata ta fara zuqar chargy,sai gidan ya zama abin kallo,al'ajabin yadda za'a samu hasken qwan lantarki daga hasken rana sukeyi har hakan yaso bawa hisham da maryam dariya,musamman yadda mero da inna wuro suka ce su kuwa zasu ga ikon Allah.

Qarfe biyar sukayi sallama da hisham ya wuce katsina,kafin nan sai da ya danqa mata duk wasu takardu na abdallah da ya debo,qememe taqi karba tace sam,shi yafi cancanta ya riqesu a hannunsa atm,card ya bata shima da fari cewa tayi bazata karba ba don basu buqatar komai,yace a'a,kowanne lokaci buqata na iya kamasu,ta karba din don ya riga da ya kouawa mustafa yadda ake cirk kudin ta wani atm machine da suka gani cikin garin gaya,idan tana da buqata ta bashi ya ciro musu ''saidai akwai magana daya,maryam gwamnati na fara matsantawa da hutun da mukace abdallah ya dauka ne,sabida akwai cases manya da ya fara aiwatarwa kafin cutar nan ta sameshi,so na rasa me zan ce da su,don ina magana da su ne amatsayin abdallah''

shiru tayi na dan qanqanin lokaci ''yanzu idan ka nemi alfaramar qarin watanni bitu zasu qara din?'' ''eh...don sunce na fadi iya kwanakin sa,zai dawo ba tare da ya sake dagawa ba,don qasa na da buqatarsa'' ''to shikenan ka fada musu watannin biyun,kafin nan muga yadda Allah zaiyi'' ''Allah ya iya mana,ya bashi lafiya cikin sauri'' ''ameen''inji maryam,ta rakashi ya yiwa inna wuro sallama cike da kewa ya tafi don a zamansa na kwama dayan har sun soma sabo

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Readers Also Read

More by Ayshacool 1