Kenza eBookz

Abadan complete hausa novel - Chapter 27

Abadan complete hausa novel - Chapter 27

Abadan complete hausa novel Chapter 27: Abadan complete hausa novel Chapter 27. firgigit ta farka daga baccin da ya dauketa kan abun sallah,da sauri ga…

3,366 words

firgigit ta farka daga baccin da ya dauketa kan abun sallah,da sauri ga leqa fuskan abdallah dake baccinshi ta tabbata lafiyanshi lau,komawa tayi ta jingina da bangon dakin tana share zufa tare da tuno mafarkin da tayi,tabbas Allah ne ke mata ishara,sam kamar wadda aka dakawa gudumar mantuwa ta mance da mafi yawa daga cikin addu'o'inta,ta waiwaya ahankali ta kunna wayarta ta kawo haske,qarfe uku,na dare agogon ya nuna mata,ba zata iya fita alokacin ta daura alwala ba din haka ta janyo carbinta taci gaba da ja tana ambaton Allah lokaci lokaci tana leqa abdallah

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Tana bakin murhun tana dama musu kunun duk da hanatan da inna wuron tayi qoqarin yi amma ta qiya,don tsakanin kwana ukun da sukayi cikin gidan indai ta kunna risho to abdallah zata dafawa wani abu,ta riga ta saba don rayuwar gidan sun data tashi cikinta marabarta kadan ce da wannan

Mero ce tayi sallama ta shigo gidan,ta dubi maryam tace ''takwara ina kwana''ta waiwayo fuskarta dauke da 'yar fara'a ta amsa mata ''a'ah,mero,yanzu kuma sammako zuwa min aka koya kenan,kodon,kinga kin samu abokiyar hira ne?''inji inna wuro dake fitowa daga daki dariya tayi ''wallahi kuwa inna,na samu larabawa abokan hira''haka take kiransu maryam sabida farin da suke da shi,duk da itama din farar bafulatana ce saidai nata farin baikai nasun ba

Ta shiga dakin inna wuro da suke zaune da mero,suna hira suna cin gyada marau marau,gefansu ta samu ta zauna kana tace da inna ''inna don Allah ina zan samu ganyan magarya?'' ''ganyan magarya me zakiyi da shi?'' ta danyi murmushi,a zaton innan ko maganin mu na mata takeson ta hada ''akwai cikin kayan malam,amma ina tsammanin busashshiya ce,idan danya kike so saidai ko a yago miki can qofar gidan malam haladu'' ''sai nasa yara su ciro miki,yaya abdullahi zakiyiwa magani?''inji mero wadda ta cafe zancan,kallonta maryam din tayi,ta lura da yadda take yawan kulawa da duk wani lamari da ya shafesu hakan yasa ta dan saki jikinta da ita ''eh''maryam tace mata,take ta miqe tana jawo hijabinta tana yafawa ''bari na kawo miki''ta fada tana ficewa,mero sunanta maryam,tsirar gidaje biyu ne kawai tsakaninsu da gidan inna wuro,irin marasa shi din nan ne na azo a gani,hakan ya sanya hatta aurenta iyayenta suka kasa,hakan ya sanya take shigowa take taya inna wuro aikace aikacen gida,taci kuma na rana da dare wani lokaci harda na safe agidan bayan wanda tsoho malam yasa ake zubawa akai gidan naau sabida iyayenta da qannenta

zama tayi suka ci gaba da hira da inna wuron bayan ta mata tayin gyadar,cikin minti goma saiga mero da ganyan kore shar mai yawa kuwa,maryam ta miqe tana mata sannu ta saka hannu zata karba ''bari na kai miki dakin ma''kafin tace wani abu har ta fice ta nufi dakin nasu,binta tayi da kallo har ta dagaabulen dakin ta shiga,duk da ta koma ta zauna amma sai hankalinta ya kasu jiyi ganin ahiru meron bata fito ba,miqewa tayi taa cewa inna wuro ''bari na daura alwala naga an kusa azahar inna'' ''to...to,nima tashin zanyi''.

sai data daura alwalar sannan ta nufi dakin,kan kujerar dakin ta tadda meron tana faman zuba surutu idonta kan abdalladake kwance,abdallah na daga kwancen yana kallonta qarasa shigowa tayi ''kin manta bai da lafiya ne,mara lafiya baison surutu''ta fada tana qarasawa kan katifar ''amma meramu har mirmushi ya yimin fa''sai taji wani dim,ta waiga ta kalli abdallah,idanunshi na alaumshe sabanin dazun da yake tar a bude.

sauka tayi kawai ta janyo,abun salla ta shimfida sannan ta kalli mero ''ya kamata kije kiyi sallah ko,don lokaci yayi'' ''shi kuma abdullahin fa?'' ''zaiyi shima''ta bata amsa tana tada kanbbarar sallah,sai data kusa raka'a uku kafin meron ta tashi ta fita tana yiwa abdallah sallama roba ta saka ta masa alwala sanna ta juyar dashi bangaren gabas,kafin ya idar ta zuba abinci cikin plate ta ajjiye,bayan ya gama ta dora mishi kan,fillow a saman cinyanshi don hisham yace a dinga barinshi wani lokaci ya dinga ci da kanshi don hannun ya dinga motsawa ya dinga jin qwarinshi sosai,ta koma saman kujera ta ta samu roba daya ta zuba ganyan magaryan tana gyarashi tare da cire qayoyin jiki

shirun da taji alamun bai fara ci ba ya sanyata dago kanta,hada idanu sukayi da sauri ta janye idonta,ta rasa dalilin da a kwanakin nan bata iya hada ido da shi na tsawon lokaci,jikinta yaci gaba da bata kallonta yake,a sace ta kuma daga kai zata saci kallonshi suka sake hada ido,ya lumshe idon nashi da sauri ya bude,sign ne da ta lura yana yawan yi mata amfani da shi idan suka hada ido,batasan me yake nufi ba saidai a duk lokacin da yayi hakan takan tsinci kanta cikin wani irin feelings,wani irin abu ne cikin qwayar idanun abdallan da bata taba ganinshi cikin idanun wani ba

ta janye idonta tana fadin ''kaci abinci kada ya huce''kai ya girgiza mata alamun a'a,babu yadda bata masa ba amma yaqi,qarahe sai daya bar abinda take yi din ta dawo kan katifar ta karbi plate din,ta debo ta miqa mishi,babu musu ya bude bakinshi ya karba yana kallon fuskarta,ganin ya karba sai ta ajjiye cokalin tana fadin ''bismillah to''tana maida fuskarta gefe a tausashe taji an kamo habarta ana qoqarin juyo da fuskarta,qin kallonshi tayi kamar yadda shima sam ya hanata sakewa har sai da suka sake hada ido,ture plate din abincin yayi da hannunshi guda kana ya jawota ta fada jikinshi.

tayi ta qoqarin tashi,saidai ya hanata,har mamakin yadda ya iya riqeta haka tayi,kamar zata yi kuka tace ''abdallah,bafa mu kadai bane cikin gidan nan ka sani''shiru taji,alamun bazai kulata ba,tilas ta haqura da yunqurin tashin tayi luf cikin jikinshi,ya lalubi hanninta ya saka nashi ciki ya jade yatsunsu guri guda tare da sauke ajiyar zuciya wadda ta haddasa mata sauyawar yanayin jikinta gaba daya,ta runtse ido tana jin fitar numfashinshi.

*_kuyi haquri da wannan_*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽

[1:55pm, 9/24/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_*

4⃣6⃣

*_Annabi Muhammad S A W yace:duk wanda yaje gurin boka ko dan duba haqiqa ya kafircewa abinda annabi muhammad tazo da shi,hakanan ba za'a karbi sallarsa ta kwana arba'in ba(ba yafe masa su akayi ba,kuma ko yayi Allah baya buqata baxai karba ba,babu wani abu da zaka/ki aikata ya zama kaffarar wannan zunubin da kikayi face ki tubarwar Allah tuba na haqiqa ba tuban muzuru ba,kuma kada ki yarda qafarki ta sake kusantar gurin bama zuwan ba,shin me kike tsammani idan Allah ya dauki ranki a gun ko a hanyar zuwa kota dawowa?,Allah ya kare mana imsninmu,ya,cire mana dukkan wani qulli dake zuciyoyinmu game da 'yan uwanmu musulmi)_*

*_Manzan Allah S A W yana cewa''ka tuna Allah lokacin da kake cikin jin dadi da yalwa,shi kuma sai ya tuna da kai lokacin da ka shiga qunci da matsi da wahala(ba wai ka xauna kara zube ba don kana cikin jin dadi da wadatar rayuwa,ba zaka tashi addu'a ko tuna Allah da girma yake ba sai bala'i da masifu sun maka katutu,wannan kuskure ne babba,Allah yana fushi da bawan da baya roqarsa haka annsbi S A W yace mana,Allah kasa mu dace)_*

Saukar numfashinsa ne ya alamta mata bacci ya daukeshi,ta zare jikinta cikin dabara ta maye gurin da fillow,fuskarshi tarwai,kyawunshin nan mai daukar hankali yana nan,ta zuba masa ido tana tuhumar kanta na wasu 'yan lokuta,ta janye idonta ta lumshesu hadi da sakin ajiyar zuciya,mero ta fado mata arai,sai ta ja siririn tsaki kana ta sauka daga katifar,hijabinta na kanta don haka abun sallah kawai ta gyara ta zauna akai bayan bayan ta samu roba daban ta saka ganyen magaryar qwalli bakwai aciki,a nutse tayi bismillah cikin madaidaiciyar murya ta soma karanta suratul baqara cikin robar da ta zuba ganyan magaryar da ruwa aciki,da ka take karatun cikin daddadan sauti mai cike da nutsuwa,don surar na daya daga cikin surorin data haddace saboda muhimmancin surar.

cikin barcinshi ya dinga jin tashin sautin karatun,sai ya gaza bude idonshi duk da ya farka,sosai yake jin dadin karatun,wani yanayi mai dadi na ratsashi,sannu a hankali ya dinga daga idanun nashi har ya kammala budesu gaba daya,ya zubesu fes kan fuskarta kallonta yake da yadda bakinta ke motsawa cikin gwaninta da ita karanta alqur'ani da bawa kowanne harafi haqqinshi,ba kadan ba ta burgeshi,komai nata mai kyau ne da nutsuwa,saita tunasar da ahi ahima wani bangare mai girma daya manta ko ya saki na karatunshi ya daina tilawa.

kan idanunahi ta kammala,ko kadan batasan yana kallonta ba har ta gama ta karanta falaq da nasi da suratul ikhlas aciki ta girgiza ahi sosai har ruwan ya soma kumfa ta samu murfi ta rufe,ta zare hijabinta saboda zafin data fara ji sakamakon rashin kitso,Allah ya bata yalwar suma kamar yadda ala sana salin fulani ke da ita,ta zare ribbom dinta ta fara sake qoqarin tattara gashin guri gida donta daureshi,bin sumar tata yayi da kallo,don iya zamansu bai taba ganin gaahibta haka ba,ba qaramn hirgeahi abin yayo ba,yana son mace mai yalwar gashi sosai,shi ua sanya yawancin lokuta a zamanin quruciya shi yakewa mami tsifa,rabi wasa rabi tsifa da haka suke gamawa,ya dan lumshe idonshi kana ya bude saboda wani abi da ya soki zuciyarahi da tunawa da mamin da yayi,qaunarta da kewarta ta zamar masa sabuwa.

ci gaba yayi da kallonta ganin yadda ta daureahi ta kuma nannade jelar kamar alkaki,ta juya don sake sanya hijabinta suka hada ido,gabanta ya fadi ''shikenan ya gama qaremin kallo''ta fada cikin zuciyarta,murmushi ya sakar mata ganin yadda take faman qoqarin sala hijabinta ''dubeta,kamar ba mijinta bane ni,banga marabarki da mutanen qauyen nan ba kam,dama ina da ikon miqewa yau da sai na baki kunya fiye da haka yarinya''ya fada shima cikin zuciyarshi,fatanshi daya kada ta gudu,aikam addu'arsa bata ci ba don tana gama sanya hijabin ya gudu a dakin.

a bakin bishiyar darbejiya ta sameau zaune ita da mero ''sannu maryamu,na kiyo ki ai kina karatu,har mero zata shiga nace ta qyaleki,hala abdullahin kike wa'' ''eh inna wuro'' ''ai yana da kyau kam haka din,qur'ani dama ai waraka ne'' ''wani baccin ya koma?''mero ta fada tana kallon qofar dakin nasu,sai data waiwaya itama ta dubi dakin kana ta dubeta ta girgiza kai ''amma aka barshi shi kadai,da fitowa akayi da shi ko inna wuro?''inji mero ta fada tana duban inna wuro ''lallai kam yasha iska shima,duk da akwai fanka,amma ta Alla tafi lafiya''

kafin maryam ta kai ga miqewa har mero ta miqe ta fara yin gaba,da sauri maryam tace ''amma inna bazan iya dorashi kan kujerar ba ni kadai,ga mustafa baya nan''itama miqewar tayo ''muje,zaki iya in sha Allahu,ai jikin ya qara qwari ba kamar da ba''

tuni har mero ta isa dakin ta bude wheel cahir din ta tsaya agaban katifar abdallahn tana kallonshi,shima idonshin na kanta,wani abu maryam taji ya taba ranta sai ta dauke kai ta qaras inda yake,gabanshi ta tsugunna ''inna wuro tace ko zaka fita waje can yafi iska mai dadi?''tana maganar ne idonta na kallon gefe ba inda yake ba,kai ya guada alamun to cikin zuciyarshi yana fadin ''Allah yama inna wuro albarka,ko banza ta samamin hanyar da yau zan wuni ina kallonki,ko ke ba zaki kalleni ba,'yar qauye kawai''.

sau uku tana qoqarin dagashi ta kasa,mero na tsaye ta dameta da maganar kaza zakiyi kinga haka zakiyi,ana hudun ne ta taho da sauri zata tayata kama shi ''me haka ne wai mero?lafiyanki?''madyam ta fada a dan zafafe,ita kanta batasan ta fada din ba sai daga bisani,sai ta waske da aon ci gaba da daga shi din,qarshe inna wuro ce ta taimaka mata suka dorashin ita ta turoshi mero da inna wuron sukayi gaba.

Da ido yake binsu hirar tasu na bashi sha'awa,zaya so ace yana da bakin da zai saka cikin hirar tasu,hakanan yaji jininshi ya hadu da inna wuro,tsohuwa ce mai karamci da dattako kamar maminshi duk da ta fita shekaru,weather din garin yaji yayi masa kamar a qasashen turai ba cikin qasar kano ba,kanon ma cikin wani qauye.

Murmushin da maryam ta ga yana tashi kadan kadan kan fuskarshi ya tabbatar mata yaji dadin zaman gun,hakan neya bawa mero damar matso da kujerarta 'yar tsuguno daura da abdallah ,ta fara bashi labaran qauyen da waqoqinsu,al'a dunsu da kuma yanayin shagulgulansu inna wuro na sa musu baki jefi jefi,yadda maryam taga ya bada hankalinshi sosai kan meron sai taji baa wai,duk da tana ta qoqarin nutsar da zuciyarta kan meye nata?,Abdallah dama temporary ne jiran samun lafiyarshi kawai take ta kaucema rayuwarsa.

Saidai duk yadda taso nutsar da kanta hakanan taji hakan ya faskara,sai tayi zaton zama shirun da tayi ne saboda gaka ta miqe tana fadin ''inna wuro bani garin tuwon nan mana na tankade miki shi'' ''kwano biyar ne fa meramu?ba zaki iya ba'' ''ai inna babu abinda nake Allah zan iya ki bani kawai'' hakanna inna wuro ta bata din sai ta tafi can dan nesa da au kadan bakin rijiya ta zauna ta saka kujera ta tsuguno tana son kauda hankalinta daga garesu,duk da tana iya kallosu tana kuma jin abinda suke fada.

A sace yake kallinta,qarara ya karanto damuwa cikin zuciyarta saidai miskilancinta da wani dalilinta can maras tushe ya hanata gano me take ciki?me take so?mene kuma bata so,duk sanda ya fusknci zata dago kai ta kallesu sai ya dauke kanshi ya maida kan mero,ita kam mero farinciki ya cika zuciyarta kamar ta taahi taka rawa,tqu,balaraben nan ne yake ta kallonta,kai gaskiya tafi kowacce mace dake cikin qauyen ni'ima sa'ar zuwa duniya.

har aka kira sallar la'asar yana nan zaune yana sauraron hirar tasu yana kuma tayasu da murmushi,musamman idan akayi abun dariya,tankaden da ya kamata ace ta gamashi cikin qanqanin lokaci sai gashi zuwa lokacin la'asar din ko rabi bata yi ba,hakanan ta miqe ta karkade jikinta,ta maida saura cikin buhu wani kuma cikin fanteka ta rufe ta share gun ''ayiwa bawan Allah alwala ko?''inji inna wuro,mero ce ta miqe tana fadin ''sai nayi masa inna tunda maryamu na tankade'' ''a'ah,ina aka taba haka mutum da matarsa ba wai bat nan bane,haramci ne ai,ki karbi tankaden ita tayi masa alwalar....af,tama kammala kinga,to bata butar''

haka nan taji tana jin haushin meron,ko da tazo miqa mata butar karba tayi ba tare da ta kalleta ba,abdallah ma kan whell chair dinshi yana kallinsu,murmushi ya aubuce masa kana ya duqar da kanshi yana jin wani sukuni da farinciki na ratsaahi wanda tunda ya kwanta cutar nan baiji irinshi ba sai yau,ya kuma rasa na meye,a gaggauce ta daura mishi alwala ta fuskantar da shi gabas ta bar gurin taje tayi tata,da suka idar ma hirar taau suka zo suka dora,madafa tayi tafiyarta wata rumface ta bunu dake gefe daya na tsakar gidan,anan din ma tana iya hangosu amma sai ta juya musu baya.

haka ta hana kanta sakat taqi zama gu daya har sai da ta kammala tuwon masarar miyar danyar kubewa,shi kuma abdallah ta dafa miahi couse couse da miyar ganye anan din ma dai suka zauna don cin abincin dare,qemem yaqi couse couse din,tayi mamaki matuqa da taga yana cin tuwon masarar,shi da ko na semovita bai dameshi ba ''ato,dama ai tuwo shine abinci,a tsari na abincin gidan bahaushe ma ahekari aru aru ahine abincin dare ba wadannan abinciccikan yahudawan ba da basu qara mana komai face cututtuka''inji inna wuro ta fada har sai da tasa abdallah murmushi.

ido ya zuba mata ganin kowa ya kammala cin abincin ta tattara kwanukan ta wanke ta dawo ta zauna ba tare da ta sa komai cikinta ba,ta lura sarai da yadda yake kallonta don haka ta canza ma gin zama inda ba zasu iya hada ido ba ''abdullshi me kake kallo ne?,ko wani abun kake so?''inji mero ta fada kai ya gyada,bayqn ya kalleta,sai ta sake washe haqora tana fadin ''to me kake so?''ya tsanshi ya nuna saitin maryam,sai ta bi yatsar da kallo har kn maryam sai ta rage farashin fara'ar fuskarta kana tace ''maryamu magana ye dake ko?''ba tare data dubesu ba tana tsincewa inna wuro qulalai daga cikin audugar da take kadi,cikin salon dakiya da shariya tace ''magana ta me kenan?'' ''nima ban sani ba''meramu ta fada tana komawa inda ta taso ta zauna,qarasowar inna wuro gun yasa suka ci gaba da hirarsu,haka ya qarqci kallonta har ya haqura.

inna wuro ce ta lura da yadda ya soma lumshe ido ''bawan Allah bacci ina tsammani yake ji''inji inna wuro ''kaishi daki maza meramu,idan zaki dawo kya dawo''ta fada tana janye daeon audugar daga gabanta,yana sane ya lumahe idon yaji dadi da inna wuro ta masa hanya.

da qyar ta samu dorashi kan katifar,ta janyo masa abun rufa kan ta gama lullubeshi ta tuna da ruwan ganyan magaryarta,taso idanunshi biyu yasha,amma duka da haka ta debo cikin tafukan hannunta ta shafa mishi dukka jikinshi,kana ta masa addu'o'in kwanciya barci ta shafa masa,wani sanyi da nutsuwa yaji suna ratsashi,kamar ta shafa masa ruwan qanqara,ta juya da nufin tashi sai taji an janyota,bata zata ba sabida haka kai tsaye jikinshi ta fada ''ka sake ni''take fada tana mutsu mutsu,saidai ko ajikinshi,bata son me yasa yake yawan son rungumarta ba haka ''haba ka sakeni nace mana,kayita taba jikin mutane haka kawai'' ''jiki na ne,halaliyata,lada ma Allah zaya bani''haka yakeson fada amma ya gaza.

duk yada taso zame jikin nata ta gaza,tanaji tana gani har gajiya ta sauko mata bacci ya qwace idanunta,yan jin saukar numfashinta cikin nutsuwa,shi din ma idanun nasa a rufen auke sai kayi tsammani bacci yake,saidai sam ko daya,tunanin maryam dinne cike fal da kwanyarsa,yana tausayinta,yana jin sonta har cikin jini tsoka da bargonsa fiye da da,sai yanzu yake sake tabbatarwa kanshi Alah ne kawai ya bashi maryam din ba mutum dukiya ko qarfin iko ba,maryam din kadarace mai tsada kai tama shallake kadara agunsa,samun mace mai halacci da juriya kan lalura da halayen mijinta abune mai,matuqar wuta a wananan zamanin namu,ya sani sarai bata zaman qauye iyakacinta da ahi ziyara ta kwanaki uku,sai gashi yau ta amince ta yarda ta zauna cikinsa shi da ita cikin zuriyarta har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya ba tare da damuwa raki ko qorafi ba,lokacin da dukkansu shi da ita basu san sanda zaizo ba don babu wanda ya san iya tsahonsa,baya ga dama da take da shi na tafiyarta ta barshi tunda babu zuri'a ko iddarsa akanta.

A hankali ya dinga tina yininsu shi da ita na yau,murmushi ya subuce masa,fushi da kishi daya dinga ganowa qarara cikin qwayar idanunta,saidai ita sam bata san da su ba,batasan suna bayyanar da kansu bane su duk yadda kakai ga qoqarin boyesu,murmushi ya subuce masa,ya sanya hannunshi ya cire dan hijabin dake maqale a wuyanta,ya sake zare ribbom din kanta ya sa hannunshi yana shafa gashin,santsinsa da qamshinsa na burgeta,yayi imani abinda yake ji game da maryam din wani irin jini a jiki da ba kowa Allah yake bawa ba.

Ta sake zubawa qofar dakin ido a karo na barkatai,mintina kusan goma ta sake janye tagumin da tayi ta saki ajiyar zuciya ta kalli inna wuro da ta duqufa wajen yin kadinta ''kinga inna meramu shiru bata dawo ba'' ''eh.....wata qila itama baccin yayi awon gaba da ita ne,ai yau kam ta aikatu itama,meramu babu son jiki,harvta fiki son aiki''innan ta fada cikin halin ko in kula don bata kawo komai cikin ranta ba ''amma inna bacci da wuri haka,qarfe tara da rabi fa,yanzu ma wasu suke fita dandali'' ''yo su mutan birni barci da wuri a gunau wani abu ne?,rayuwa suke gida a qulle,daga sallar isha idan suka shige gidajensu suka kulle sai kuma washegari'' ''q'nn,bari na tashi nima na tafi'' ''da wuri haka?''inna wuro ta fada tana binta da kallo ''eh''ta bata amsa gana zira sudaddun silifas dinta ''to kinga ga abincin nan kokus yake kome ne?,tafi da shi gida kwaci''duk yadda take kwadayin couse couse rin sanda ake dafashi take fata ya shigo farantinta amma a yanzu sai taji duk ya sure mata,a salube ta dauki kwanon tana fadin ''an gode sai da safe'' ''Allah ya bamu alkahairi''inji inna wuron bata haqura ba sai da ta je bakin qofar dakin tace ''abdullahi da meramu sai da safe''sau uku tana maimaitawa taji shiru,abdallah na jinta amma maryam batasan ma me ake ba don ta jima cikin daddadar duniyar barci ta musamman.

Readers Also Read

More by Ayshacool 1