Kenza eBookz

Abadan complete hausa novel - Chapter 4

Abadan complete hausa novel - Chapter 4

Abadan complete hausa novel Chapter 4: Abadan complete hausa novel Chapter 4. Cike da tawakkali da yarda da qaddara ta miqa dukkan lamarinta ga Allah,a…

3,326 words

Cike da tawakkali da yarda da qaddara ta miqa dukkan lamarinta ga Allah,a yanzu kam ta sanya jabir ne kawai cikin addu'o'inta kamar yadda raliya ta shawarceta,domin tausayinsa ne fal cikin zuciyarta,tana ji a cikin zuciyarta ta sanadinta ne ya afka wannan qaddarar

abu guda ne ta kasa tinsa komawa walwalarta da aikinta tamkar,yadda take yi a da duk da yadda take son aikin,ta barwa ranta cewa ta ajjiye aikin zata kuma jira har lokscin da ubangiji zai musanya mata da da wani mijin ko da baikai jabir dinta ba

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

misalin biyar da rabi ne na yammaci,zaune take a rumfar tasu wadda ta sha mopping tayi fes,dai qamshin turaren tsinke take,mamanta na dakin babansu tana gyarawa don ita ta amshi girki,don sam bata lamunce don ranar girkinta bane ta tura yaranta su share dakin baban nasu ba kamar yafda taga su huwaila nayi tsabar ganda,yayin da hindatu ke makarantar islamiyya

sanye take da maroon din material dinkin doguwar riga da yake ma'abociyar son dogayen riguna ne ko don tsahon da take da shi,yatsunta sunyi kyau da jan lallen da tadan qunsa iya yatsu,a lokaci irin wannan idan bata da abinda duka zatayi,taka duqufa wajen research din girke girke a daga sashukan dake watso kalolin abinci na qasashe daban daban,kadan kadan hankalinta ke rabuwa gida biyu,wani lokaci yayi tsakar gida da yaran inna hadiza keta faman ta'adi cikin falon gyatumar tasu da hayaniya na 'yan fadace fadace atsakaninsu kuma babu wanda ya isa yace zai tsawatar musu

cikin haka ta jiyo sallamar inna hadizar,abu na farko da ya biyo bayan sallamarta shine ashar da ta dura wanda har sai da maryamu tayi ta'awizi cikin zuciyarta ''kaga tsinannun yara shegu,ke balaraba da na bar muku dakin a bude shine kuka maida min shi sansanin fada da kokaye kokaye,kuma saboda tsabar baqincikin Allah yayi maka arziqi a rasa mai tsawatrwa uaran salon su fasa ma abu kosu lalata ma su jawo maka asara,dadin abun ma yanzu kana da arziqin da zaka gyara''

sarai mama tasan da ita take amma kasancewar ko da can ma da jini ajika ba kula shirginta take ba yasa yanzun ma tayi mata dif,saiga huwaila ta fito daga wanka takalleta ''a'a,ina kuma kikaje?'' ''yo ina kuwa zanje da ya wuce gidan doyar albarka jamila''ta fada tana shirin shigewa dakinta sakwatoto huwailan tayi ''amma inace baki tafi ba don wanna wanka da nayi na shirin zuwa ne,tunda munyi tare zamu je'' ''kiji hiwaila da wani zance,don,lawai zaka girin naka sai ka jawo bare?''binta wadda tare suka je da innar tata ta maidawa huwaila raddi ''kinga ba dake nake ba 'yar ayi jikar na saba''

''a'a,dakata don ta fadi gaskiyarta,kada kiyi haushin kaza huce kan dami''inji onna hadiza cikin salon tare mata ''au bayanta kike goyo kenan?'' ''qwarao,yo akan me?'' baqinciki ya,hanata cewa komai sai qwafa kawai da ta ja ta shige dakinta qarar wayarta ce ta sata dawowa daga diniyar da su inna jadizan suka shigar da ita,a kullum kwanan duniya sake gasgata zancan raliya takegame da abinda ya faru tsakaninta da jabir,jikinta a sanyaye tabi wayar da kallo ,da kamar ba zata daga ba amma ganin sunan *mama* ya sata babu jinkiri ta daga,cike da,girmamawa take gaidata ''babu abinda zaki cemin maryamu,wa yafi qarfin qaddara a rayuwa?,abun nan ya riga ya wuce addu'a ce kawai mafita,amma anyi anyi ki koma gun aikinki kinqi,na tambayi haj rabi ko wani laifin aka miki sunce babu komai,ko an miki wani abu ne agun?'' cike da girmamawa tace ''babu abinda aka yimin mama wallahi'' ''to shikenan,indai da gaske haka ne kizo gobe gida ki sameni da la'asar,da akwai aikin da aka samu kuma gaskiya a iya hasashena babu wadda ta dace da aikin sai ke,don na yaba qwarai da tarbiyya gaskiya da riqon amanarki'' ba zata iya musu da mama ba wato hajiya atika abubakar,banda haka da wata ce zqta ce mata ta gode bata buqata,amma girmanta da qaunar da take gwada mata ta wuce haka a gurinta don haka tace ''to mama,na gode Allah ya saka da alkhairi insha Allahh goben ina hanya'' ''to shikenan a gaida mutan gidan'' ''zasu ji insha Allah''

ta sauke wayar tana jin wani abu na dan taba zuciyarta,mama da bata kima da shigowa ba tace ''ke da waye?'' ajiuar zuciya ta saki ''haj atika ce,wai tana nemana gobe'' ''to Allah yasa lafiya,ko zancan komawarki ne gurin aikin?'' ''a'a,tace wani aiki ne ya samu,amma sai naje goben zanji'' ''Allah ya rufa asiri ''ta fada maman tana ficewa dauke da wankakken zanin gado da rigar filo murmushi maryam tayi tana jinjina kai,wato miji da mata sai Allah,maman ta tana burgeta matuqa,bilhaqqi take kula da mijinta,bata duba komai sai zatin Allah da kalmar nan ta *aure bautar ubangiji*

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

washegari ta shirya tsaf cikin atamfa dinkin riga da skert yaluwa sosai tayi,mata kyau ta qara haske da rama,hakan sai ya sake fidda tsayinta,kasancewar lahadi ce yasa ta nemi rakiyar hindatu ko zata ji dadin tafiyar,don ita kanta bata son tafiya ita kadai,gani take kamar idan ta fita nuna ta za'a dinga yi,tsawon watanni kusan biyar amma tunda abin ya faru baifi sau biyi ta fita ba zuwa uku shima sai dare

babu dadewa suka isa gidan maman,a falon qasa aka saukesu mintina biyar aka haura da su samanta wanda ba kowa take kaiwa ba,cike da fara'a ta tarbi maryam din,ita dai ranta yanason maryam din,natsuwarta na burgeta, kayan ciye ciye ta sa aka kawo misi ta dan basu lokaci kadan sannan ta dawo ''maryam''abinda ta fara cewa kenan ''kamar yadda jiya na shaida miki a waya aiki ne ya samu,yayi shige da na gurina amma yana da bambanci domin wannan a gida zaki dinga yinshi,zaki samu albashi mai tsoka fiye da na gurina'' ta,dubeta da aily eyes dinta''mama wanne irin aiki ne a gida?'' ''kinsan marigayi *alhaji abdulkareem mai nasara*?'' sai da tadan shiga tunani sannan tace ''eh ina jin sunanshi mama'' ''yauwa,kinga sanannen mutum ne kuma fitace tun kafin rasuwarshi,yaro daya Allah ya basu wato *Abdallah*duk da cewa yana da wata matar amma Allah abi bata haihuwa da shi ba,saidai ya riqe mata nata uaran da ta taba haifa awani gidan mata ne su biyu da nimiji daya yanzu haka duka suna tare a gidan duk da rasuwan shi alhj abdulkareem din hakan baisa sun raba mazauni ba,mamanshi na matuqar sonshi da kaffa kaffa da lamuranshi,duk da haka ana farautar rayuwarsa don kusan sau biyu kenan ana zuba poising abincinshi,ta rasa daga ina matsalar take,kuma duk lokacin da hakan ya faru idan aka tashi binncike sai a samu da hannun kukunshi,hakan yasa take canza masa kuku kala kala,amma har yau babu wanda hankalinta ya kwanta da shi

abdallah shine shugaban jami'an tsaro na farin kaya wato *S S*na nijeria gaba daya,wanda aikinsa kansa na buqatar ya zamo cikin kulawa da tsaro na musamman

bata da lokacin zama agida kasancewarta cikakkiyar likita kan fannin matsalolin da suka shafi mata,wannan ne yasa ta bayar da cigiyar amintacce ko amintacciya wanda ya qware kota qware afannin girki,to qawarta aminiya ta ce hakan ne yasa ta bani cigiya ni kuma naga ke kika fi cancanta da wanna aikin maryam,ina fatan kin fahimceni abunda kuma ya shige miki duhu kina iya tambaya ta''

shiru tayi domin tana jin abun da kamar wuya,sam bata ji ya kwanta mata ba aikin,tamkar aikatau zata tayi,kenan tunda aikin dafa abinci zata gidan wasu?,anya kuwa zata iya amsar tayin maman,amma tana jin nauyinta ,ba zatq kallon tsabar qwayar idonta tace mata a'a kai tsaye ba,kusan minti biyi sannan ta ajjiye numfashi ''ina ganin mama zanje na sanar da maga batana tukun,idan yaso duk abinda suka yanke akai zan sanar miki'' ''yayi kyau,hakan dai dai ne maryam,wannan shike dada nunamin hankalinki da kaifin tunaninki,amma ina fatan bazaki watsa min qasa a ido ba'' ''insha Allahu'' ta fada ka a qasa'' a haka sula rqbu bayan ta baiwa hindatu dubu daya tace ta siyi kayan kwalliya

cikin mota hindatu ta isheta da karadin wallahi yaya maryam ki amshi aikin nan murmushi kawai tayi ''yarin ya ce ke hindatu har yau baki da hangen nesa'' ''to,ya maryam meye aibu a ciki?'' bata amsa mata ba sakamakon jin ringing din wayarta da tayi ta soma kiciniyar cirota dqga aljihun jakar,raliya ce mai kiran ''hello ummin fadil'' ''na'am mommyn fadil kina ina ne?'' ''kin ganni a hanya na dawo ne a wata unguwa'' ''yauwa don Allah ina son ganin ki ne ya za'ayi?'' ''babu damuwa bari kawai na qaraso'' ''yauwa ta gurina'' dariya ta bata tace ''sai na qaraso''ta maida wayar jaka sannan ta yiwa mai adaidaita bayanin inda zai juya da su''

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

''daga ina kuke da yammacin nan ne?''raliya ta tambayi maryam sanda take dire musu drinks ''hmmm,wallahi kinga haj atika ce tayi kira na,wai ta samamin aiki gidan marigayi abdul kareem mai nasara'' sai taga fuskar raliyan ta sauya ta dan tsuketa ''ba zaki koma wani aiki ba,aure zakiyi maryam''ta gada kai tsaye tana kallon maryam din ba tare,da kawo komai cikin zuciyarta ba tayi murmushi ''banda abinki qawata ba sai Allah ya kawo mijin ba?''ta fada cikin rashin kulawa ''Allah ya kawomiki miji maryam''sai da taji qirjinta ya wani irin buga ''miji?,wa ya gaya miki,qarya ne ni babu mijin da na samu'' matsowa tayi sosai ta kama hannayen ta ''maryam kin amince da ni kin kuma yarda da amincin dake tsakaninmu?'' ''me ya kawo wannan tambayar kuma raliya?''ta tambayeta cikin yanayi na shiga duhu ''maryam so nake ki auri nasir mijina''

a hagunce take kallon raliyan,jo tayi lamar ta doka mata guduma atsakiyar ka,gani take kamar ba'a hayyacinta take ba''raliya,me kika sha yau,ko baki da lafiya?'' murmushi tayi ''nasan zaki fadi haka maryam,amma ras nake,kuma nasan me nake,cewa nayi mijina nake so ki aura nasir'' ''shi ya aiko ki lo ke kika aiko kanki?''ta tambaueta tana mata kallon ba a hayyacinta take ba ''ni na aiko kaina tare da amincewarsa'' zame hannayenta tayi ta miqe ''idan kin warke kya kirani muyi maganar da kika rani domin ita,don dai wannan ban daukeshi da muhimmanci ba'' kamo hannunta tayi ''zauna maryam,wallahi a hayyacina nake,kuma lafiyata lau''

wani kallo ta watsa mata''sake ni raliya,ni 'yar halak ce kuma nasan halacci na kuma yi imani da akwaishi,idan haka kike to ni ba haka nake ba,idan kuma nasir din ne ya saka ki to ki gaya masa ni maryam 'yar halak ce''ta zame hannuwanta ta fice yayin da raliya ta bita tana qwala mata kira amma ko waiwayota bata yi ba,hindatu dake farfajiyar gidan tana waya itama wucewar maryam din ta gani sai binta tayi a baya

kuka zata yi ne ko ihu?me kuma yake shirin faruwa da ita?me yasa guguwar rayuwa ke walagigi da ita?,yau wai amiyarta ke gaya mata ta auri mijinta,ta ina ta yaya ma zata iya auren mijin raliya ko su biyu ne suka rage a duniya,ko da suka ke gida mama kasa gane kanta tayi,don tunda ta shigo gidan dakinta ta wuce kai tsaye,cikin damuwa maman ke tambauar hindatu me ya faru da maryam din ''ni dai mama da mukaje gidan hajiya lafiya lau muka fito,kuma iki ta samar mata gida alhj abdulkareem mai nasara,amma dai mun biya gidan anty raliya,to nidaiina waje bansan me suka tattauna ba naga dai ta fito da sauri ma biyo bayanta'' ''alhj abdulkareem mai nasara?''mama ta maimata sunan don ba boyayyen mutum bane,mai arziqi ne na gani a fada wanda akayi qiyason duka nigeria babu wanda ya kama qafarshi

''to Allah ya kayuta,indai raliyance ai ba'a ashiga tsakaninsu,idan kuma aikin ne ma zamuji,qyaleta hindatu,nasqn zata min maganar da kanta''don shaquwar dake tsakaninsu yasa maryam bata boyema maman tata duka damuwarta

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 [16/09, 20:53] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺

▶9⃣

kwana guda da yini daya bata ce da maman tata komai ba,itama zuba mata idon tayi bata tambayeta ba

kwana na biyun ne qarfe uku taji sallamar raliya,tana kwanve can cikin dakinsu saman katifarta,don yanzu zaman daki da kwanciya kuma ta aira wanda hakan baya rasa nasaba da yawan tunanin da take fama da shi,sai da gabanta ya fadi lokacin da tqji suna gaisawa da mama ta fadi mata tana cikin dakin

jawo dankwalinta tayi tana dauraqa tare da qoqarin yashi duka a lokaci daya,raliya ta iso bakin katifar ta zauna bayan ta shimfide fadil dake sharar bacci a gefanta ''na gode diyana,na gode'' ''ai ni ke da godiya''ta fadi tana sake matse fuska ''wai ni zan ta kiranki maruam amma kiqi dagawa?'' ''kadan ma kika gani matuqar kina kan qudirinki,nan da dan qanqanin lokaci zansa almakashi na datse igiyar mu'amala ta dake,tunda ba son Allah da annabi kuke min ba,so kuke ku cutar da ni'' dafe bakinta raliya tayi tana kallon maryam din kamar yau ta fara ganinta,ta sani babu shakka ba qaramin baci ran maryam din yayi ba tunda har ta iya furta mata haka,tafi kowa sanin halinta na rashin son fada da tashin hankali

''sonki muke kuwa maryam,saidai ke dake ahirin juya manufarmu ta alkhairi ki maisheta ta sharri,meyw aobu cikin aurenki da nasir maryam?''kafeta tayi da ido cikin bacin rai tace ''baki bar maganar,nan ba kenan ko raliya?'' ''ta yaya kikeso nabar alkhairin da na hango miki ha wofanta kenan a banza?'' ''lallai babu shakka kin gaji da hulda da ni.....ina zuwa''sai ta yunqura ta miqe kana ta fice

mintina kadan sai gata sun shigo tare da mama ''wai me ya hadaku ne da raliyan?''maman ta tambaya tana daga tsaye ba tare da ta zauna ba ''mama kinji abunda raliya ke fada kuwa,ba shakka ina tsammanin ta haukace ne,wai mama na auri nasir mijinta fa take cewa'' ba shiri mama ta nemi giri ta zauna,ta dubi raliya sosai ''da gaskene abunda maryama ke fadi?'' cike da tabbatarwa ta girgiza kai ''eh mama haka ne,ni a ganina ni da maryam mun zama daya,na yadda da ita na kuma aminta da kyawawan halaye da dabi'unta,na tabbata ba zata cuce ni ba,to mama laofi ne don na gayyatota tazo mu zauna qarqashin inuwa guda?''

azafafe maryam tace ''kinjifa mama irin abunda take cewa,ro billahil azim indai raliya bata sauka daga kan bakanta ba na miki rantsuwa mama har da Allah daga yau babu ni babu ita har abada'' tsot dakin yayi son su kansu aun sani matuqar maryam ta rantse akan abu to sai ta aiwatar,kuma alamu duka sun nuna irin yadda batun ke taba mata zuciya ba qarami bane,maman ce ta soma magana ''koda maryamu ta amince da maganar ma ni bazan amince ba,haba raliya aisai duniya ta zagemu,jama'a su saka mu a tadinsu,idan banda abunki ma raliya kwata kwata shekarunku nawa da yin auren,banda quruciya haka kawai kuna zamanku gwanin sha'awa ki dinga kira ma kanki kishiya uhm raliya?,na roqeki nima ki bar maganar haka nan kinji?'' qwalla ta cika mata ido ta tausayin maryam don qaunar da take mata ta fisabilillah ''shikenan mama,koda baki roqeni ba zan bar zancen ko don kada na rasa aminiya irin maryam,saidai....maryam na gode,na gode da kika nuna min iyaka ta'' duk da taji rashin dadin batawa raliyan da tayi amma sai taji kamar an tafiyar mata da wani qullutu da ya tokare mata wuya,sai taji damuwarta ta rage farashi zuwa kaso tamanin

durqusawa tayi bayan ta miqe tana qoqarin daukar fadil tace da mama ''mama ni zan wuce'' ''kinga malama ajjiye fadil din ni zan daukeshi,tunda ba ke kadai bace ai uwarshi ba''cewar maruam tana yafagyalenta don yi mata rakiya,don ta fuskanci tafiya,zata yi,ta san halin raliya ciki da bai tasan fushinta koda ta tsaidata ma ba hirar atziqi zasu yi ba ''ni kadai ce mana uwarsa tunda kinqi ubansa''ta maida mat martani tana qoqarin ficewa,murmushi kawai maryam din tayi ta saba fadil din ta biyo bayanta

''halan driver ne ya kawoki?'' ''ban sani ba,idonki ya baki amsa''tave da maryam din lokacin da auka fito tana gaba ita na binta abaya,mirmuahin dai ta kuma yi har beuty points dinta suka loba ''Allah ya baki haquri,yau kam ai akan gwiwa kike sai lallabe'' ''a'ah,akan haba nake'' amsar da ta bata ta sanya maryam tuntsirewa da dariya har itama raliyan ta dan murmusa don fushinta da maryam ba ya wani tasiri suna isa gaban motar ta ganshi zaune,shi ya kawota kenan,raliya ta bude ta shiga yayin da maryam ta galla masa harar lokacin da suka hada ido,dariya ya tuntsure da ita yana kallon raliya da tayi kicin kicin ''kada kice komai,don babu ruwan nasiru,kinga kanwar nan'' ''babu wani nan,waye baisan halinku maza ba,to wllahi bari kaji,idan ka sake ka yiwa aminiya ta kishiya ban yafe ba koda wace ce kuwa,ke kuma kici gaba da nema masa aire kinji ko solobiyo''ta fada harda dan kama kunnen raliyan dariya abun nata ya basu ''ni don Allah sake min kunne,tunda kin gujemu dai ba shikenan ba'' ''indai irin wannan gudun ne raliya am sorry to say....zanta gudunku har abada''ta dan ja da baya ta rue musu qofar tana murmushi sanna ta dan sara mata shigen yadda sojoji suke ''Allah ya huci zuciyar ranki shi dade,oya kai kuma kaja mini aminiya ta ahankali'' ''oho dai abanza tinda yau gaku a rana''ya fadi yana yiwa motar key tare da cillawa raliya gwalo ''wlh a inuwa ka ganmu,kuma duk qwaqwqwafinka ba zaka taba ganinmu a rana ba,ku sauka lafiya,sister am sorry,sai munyi waya''

koda ta koma gidan cikin al'ajabi suke tattauna zqncan da mama,maman ta kuma yabwa qwarai da irin qaunar dake tsakanin maryam din da raliya,ta musu addu'ar Allah ya dorar har tsufansu sai a san nan ne maryam ta samu sukunin yiwa maman zancan aikin da hajiya atika ta samar mata,shiru maman tayi kamar yadda maryamun tayi tana jirqn cewa maman,shudewar mintina kusan biyu kafin tace ''ke me kike gani game da aikin,tunda kinga azahjrin gaskiya zamanki babu aikin babu dadi,tunda kin riga kin saba,hakanan zai debe miki kewa,baya ga haka harkar makarantar hindatu wa zqi ci gaba da daukar nauyinta idan har kika daina?,amma ke me kike gani mene ra'ayinki?'' ''aini mama banida wami zabi sai abunda kika ce''

''kina da zabi mana maryamu zan tauye miki haqqinki ne?,amma dai abinda yafi kawai shine kici gaba da addu'a,Allah yayi miki zabi mafi alkhairi'' ''ameen mama'' da haka suka saki maganar suka shiga kuma wani batun daban kuma,haka rayuwarsu take su uku suke yinta,su kashe su binne abinsu babu maiji,hakan ne ke qara haushinsu,cikin zukatan al'ummar gidan

sati guda da maganarsu da haj atika amma har yau ta kasa yanke komai a kai,kwana bakwai daidai da azahar tana sharar tsakar gida ta jiyo sallamarta,cike da mamaki ta yi mata sannu da zuwa sannan tayi mata jagora zuwa dakinsu

ruwan sanyi na pure water da alalen da sukayi ta ajjiye mata sannan ta zauna suka gaisa ''baki da kirki maryamu''haj atika ta fada tana dubanta murmushi tayi ta dan sunkuyar da kai ''kiyi haquri mama'' ''tashi kike abunki da mamanki ma zanyi magana,ko abbanki yana nan?'' ''eh,bari na dubo miki''ta fadi tana miqewa, taci sa'a kuwa yana niyyan fita ta tadda shi,ta sanar da shi sannan ta zura mayafinta ta fita gidan maman fatima maqociyarsu

mintina talatin suna cikin hira isyaku ya shigo yana zumbure zumbure ''ke kije bana yana kiranki''ya juya ya fice abinsa,maman fatima tace ''oh ni Allah,Allah ya kyauta'' ''hmmmm,ameen bari naje maman fati sai anjima''maryamu tayi mata sallama ta fice

bata tarad da haj atika ba,sai babanta da mama dake zaune ''baba gani''ya fada bayan ta samu guri gefe da su ta zauna ''maryam'' ''na'am baba'' ''ki shirya gobe idan Allah ya kaimu ki hada duka abunda kike da buqata hajiya zata zo zaki tafi gidan nan da kukayi magana da ita ta samar miki aiki'' cikin rashin fahimta ta dubeshi ''amma baba ni ina ganin koda zanyi aikin ma ai bani da buqatar tafiya da kaya na,tunda ba wani garin bane ko?'' ''ke,bani son sakarcin banza,na riga da na gaya miki,ki hada kayanki,suna da buqatar zamanki ne a can gidan,yo idan kin zauna anan din me zaki tsinana min,illa inyita ganinki baqinciki na ci gaba da damu na?,kije kawai banason kuna sauran qorafi kinji ko?''

Readers Also Read

More by Ayshacool 1