Kenza eBookz

Abadan complete hausa novel - Chapter 5

Abadan complete hausa novel - Chapter 5

Abadan complete hausa novel Chapter 5: Abadan complete hausa novel Chapter 5. kai ta gyada hawaye na layi bisa kuncinta,wannan sam bai dadashi da qasa ba…

3,303 words

kai ta gyada hawaye na layi bisa kuncinta,wannan sam bai dadashi da qasa ba ya miqe ya fice abinsa,kai ta hada da gwiwa ta rushe da kuka,duk yadda taso daurewa zuciyarta ta kasa ''wai me yasa baba baya sona ne mama,me nayi masa?''ta tambaya cikin kuka ''kul maryam,kada na sake jin wannan mummunar maganar a bakinki,mahaifinki ya isa da ke,saboda haka nima bana buqatar wani qorafi kibi umarninshi kawai'' bata iya cewa konai ba face miqewa da tayi ta shige dakinsu zuciyarta na zafi tare da jin tsanar wannan sabon aikin,aikin da zai nisanta ta da mahaifiyarta,zai nisan tata da 'yar uwarta,mama binta tayi da kallo tana jin tausayin diyar tata sosai na sauka cikin zuciyarta,addu'a kawai take mata cikib ranta Allah ya yanke mata wahala,ya kawo lokacin da zata zauna ta huta cikin dakin mijinta

🎄🌲🎄🌲🎄

jikinta duka a sanyaye take shirya kayanta cikin sabon dan trolly dinta mai kyau pink wato ruwan hoda,hindatu ce ta rufe mata sannan ta jawo mata shi cikin parlour don bata da kuzarin da zata iya janshi

tsaye tayi cikin falon ta kasa cewa maman nata komai,don hawaye ne fal cikin idanunta da suya da zuciyarta ke mata,ji take kamar ta bar gida kenan,tana jin tamkar ta bar mamanta kenan,sai maman ce tace ''kuje hindatu jiranta suke,Allah ya bada sa'a,abu guda zan fada miki,ki riqe mutuncinki a duk inda kike,ki tsarw ksnki maryam ki kuma ji tsoron Allah,don babu wani abu da zan iya yi miki a lahira,iya kacin amfani na a duniya ne wajen tunatar da ke bin hanyar Allah,ki riqe amsna ki zauna da kowa lafiya'' kuka ta saki ta fada jikin mama,sai da taci kukanta sannan a sabule ta fice hindatu tabi bayanta da akwatin

sam basu lura da su ba sai shewa suka ji,inna hadiza nw da binta har da tafawa kamar sa'annin juna ''haka dai za'a qare a boyi boyi''inji inna hadizar,hindatu na shirin maida mata martani maryam ta damqe hannunta ta jata suka fice ba tare da ta bata damar tsayawa sun taya yinsu ba

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [16/09, 21:00] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺

▶🔟

shiru tayi cikin motar tana maida ajiyar zuciya,zugi take jo tana yi mata har ga Allah da tana da iko ba zatayi aikinnan ba,sam bai kwanta mata ba ko kadan a rai ''maryam,kiyi haquri kinji,na fuskanci baki son aikin nan,amma ni mai sonki ce maryam,na yadda da tarbiyyarkk,ke yarinyace mai hankali da nitsuwa,idan da nasan zaki cutu a gidan wlh bazan gaba kaiki ba,ki kwantar da hankalinki na tabbatar zaki samu nutsuwa da jin dadi cikin gidan *haj hasiya*na da dadin mu'amala,insha Allahu ba zaki samu matsala ba,ki cire damuwa a ranki don Allah kinji maryamu''

ta sake sakin ajiyar zuciyar a bayyane ''to msma insha Allah''ita kanta tasan ta fada ne kawai amma Allah ne kadai yasan ranar daina damuwarta,bata taba rabiwa da maman nata ba sai yau

tafiyar mintina kimanin talatin suka iso unguwar,tun daga farkon unguwar zaka gane cewa ba qananan muta ne ke zaune cikinta ba,daga get din farko allo ne mai dan girma dauke da rubutu kamar haka *welcome to millonier quaters*

sannu a hankali suke ratsa layukan,layuka ne tsararru tamkar a qasar waje,shuke shuke ne jere reras qofar kowanne gida,hakan sai ya yiwa layin ado ya zamo cike da furanni,layin ya burgeta sosai,duk,da uadda,zuciyarta ke mata babu dadi

qofar wani gida suka ja suka tsaya,dauke yake da madaukakiyar katanga da get mai tsawo da girma,horn tayi har kusan uku kafin wata qaramar qofa ta bude kallo daya zaka masa ka tabbatar cewa qaqqarfan mutum ne,sanye cikin kaya riga da wando ruwan bula wanda ke alamta unifoarm ne a jikinsa

fuska a hade yake tambayarsu cikin karyayyen turancinsa na brooking ''wa kuke nema?'' haj atika ce ta amsa masa''gurin hajiya muka zo,ta san kuma da zuwan mu''ya sake tambayarta mene sunanta ta gaya mishi bai sake cewa komai ba ya wangale mamakeken get din motarsu ta fada ciki

gurin parking ne wanda yake cike da motoci na alfarma a qalla guda goma,haj atika ta raba tata gefe kana suka fito,sunyi tafiya ta kusan minti biyar kafin su cimma dogon valcony din dake fuskantarsu wanda lullube yake da nau'in furanni kala kala masu qamshi da kyawun kaloli,qofa ce mai fadi cikin valcony din wanda suna shiga ta kaisu ga tafkeken falo wanda ya lamushe rukunin kujeru har set biyar saboda girmanshi

iya qawatuwa an qawata falon iya ganin mai kallo,saidai kawai na barwa mai karatu ya siffanta shi iya yadda zai iya,shiru falon yake sai qamshin freshner da ya gauraye falon da na a.c

_kuyi haquri da wannan don Allah,ku bini bashi gobe uxiri ya riqeni_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [16/09, 21:02] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶1⃣1⃣

tsit falon yake tamkar babu kowa cikin gidan,da ido suke kallon falon tare da yin sallama koda zasu samu wani a akusa ya amsa musu,saidai har yanzu babu motsin kowa qofar dake hannun hagu suka ji an murda an bude,duk da 'yar tazarar dake tsakaninsu suna iya jiyo dariyar su,su biyu ne daya a gaba daya abaya matashiya ce 'yar kimanin shekara ashirin da biyar sai wata agefenta wadda zata iya bata shekaru uku

basu kula da su maryam ba dake tsaye a tsakiyan katafaren falon ba har sai da suka zo daf da su,ta gaban ce mai kimanin shekaru ashirin da biyar din ce ta soma qare musu kallo,kallo ne na qurilla da saka tsarguwa,sai da ta gama tace ''mu je ko jidda na taka miki''ta fada tana kallonsu sama da qasa har zasu gota haj atika tace ''ji mana''ba tare data dawo ba ta waiwayo tana jirqn me zasu ce ''don Allah ko zaki mana magana da haj bintu?''

cikin halin ko in kula tace''ku zauna ku jirayi fitowarta,may be yanzu zata fito''daga haka tayi gaba abinta tare da jan hannun wadda suke tafiyar tare,haj atika tace ''zauna maryam,bari na kira hajiyar'' maganar second uku fayi da ita ta kashe wayar,cikin minti biyar katafariyar qofar dake hannun dama ta bude,kyakkyawar mace ce 'yar kimanin shekara talatin amma a zahiri ta kai shekara hamsin da uku,kyawun jiki iya ado da kwalliya hade da tsafta ne suka wawashe ragowar shekarun suka boyesu

sanye take da swiss lace ruwan toka da adon orange,sai labcoat da ta dora fara tas a sama,takalmin qafarta hill ne shima fari ne qaf kamar ranar ta fara sashi,ta nade wuyanta da mayafi orange,fuskarta qunshe da yalwataccen murmushi ''sannu hajiya,maimakon ku shigo sai kuma ku zauna anan,ku taso don Allah''ta fada tana nuna masu qofar,gaba tayi suka bita abaya

abun mamaki sai gasu a wani gurin,guri ne mai kama da gurin shan iska,saidai dauke yake da tyles fari qal illa tsakiyar gurin da aka yiwa shafe din cycle aka cika shi da 'yan shuke shuke masu furanni dake fidda qamshi qofa ce ta glass wanda na waje baya iya ganin na ciki bayan sun shiga ciki ta fahimci hakan,falo ne shima mai dauke da kujeru set biyu,gini ne sama da qasa wato mai bene,wanda matattakalar na acikin falon,tsarinshi abun sha'awa ne matuqa duk iya iya tsarinka sai ya burge ka,komai na cikin falon fari ne da milk,babu alamun qura ko dauda a tattare da shi sai kace yanzu aka bare komai aledarsa aka sanya

''bismillah''hajiya bintu tace musu tana shirin zama ''hajiya ga maryam na kawo miki,kuma bani da haufi a kanta,ke kanki,nasan zaki ji dadin aiki da maryam insha Allahu''haj atika ta fada bayan sun gama gaisawa murmushi ta sake yi ''ina fatan haka,maryam sannu,ina fata hajiya ta gaya miki komai,girki ne kadai nake so ki dinga yiwa yaro na,kada kiji a ranki cewa wai aiki kika zo,kisa aranki taimako na kika zo yi,ki dauki kanki tamkar diyata,domin dama ina cike da kewar rashin yarinya mace,to ina ji a raina yau Allah ya bani,abu daya kawai nake buqata daga gareki,ki riqe amana don Allah,ki kula ki kuma yi taka tsantsan da abincin yarona,nasan kinsan komai game da abubuwan da ya faru a kanshi,ina son *abdallah* don Allah ki kula min da shi,na rasa babanshi bana son in rasa shi''ta qarashe maganar muryarta na bayyana raunin da zuciyarta tayi

duk sai taji tausayin su ya kamata,sai take jin ina ma ita ta samu wanna gatan,ina ma ita ke da gata har kamar haka ''insha Allahu haj na miki alqawarin ba zaki samu wani abu mai kama da cin amana ba daga gareni'' hakan data fada dukansu yayi masu dadi har haj bintan na murmusawa ''idan kika min haka kuwa maryam kin gama min komaibani da abinda,zan saka miki da shi,gyara guda daya,indai kina son insinga jinki kamar diyar tawa da gaske to kada ki sake kira na hajiya,ki kirani da *mami* kamar yadda *Abdallah na* ke kirana'' sai a lokacin maryam tayi murmushi karo na farko,harga Allah taji dadin karramawar da tayi mata''to,mami'' ''yauwa,na gode,hajiya atika na gode qwarai da gaske,bazan iya manta wannan taimakon da kika yimin ba'' ''babu komai haj bintu,ai abdallah kamar da yake a gurina,ni zan wuce,maryam.....'' hajiyan ta fada tana miqewa

har waiting parlour haj bintu ta taka mata sannan ta dawo,da murmuahin dai nata ta dubi maryam ''taso,maryam na nuna miki daki,don fita zanyi asibiti ina da C S har mutum uku,Allah ne ma yayi ba zamu samu sabani ba''ta gaya mata lokacin da tayo gaba ta bita abaya,wani labule mai kyawun tsari ta daga daga sashen hagu na falon,saiga gajeran corridor ya bayyana,dakuna uku ne a gun,ta tura daki na uku ya bude tace ''bismillah maryam,ga dakinki,ni,zan fita ki zauna ki huta kafin na dawo mu shirya yadda lamuran zasu kasance,yau dai babu aiki,don Abdallan ma baya gari,amma gobe zai dawo'' ''to,mami sai kin dawo''ta fada cikin girmamawa

tabi dakin da kallo bayan mami ta fita,daki ne wadatacce shimfide da carfet mai taushi,sai gado cupboard ta jikin bando da madubi hadi da dressing chair,curtains,dukkaninsu pink da fari,cikin dakin akwai toilet,sai a c daura da window din jikin gado,gefan gadon ta ajjiye kayanta sannan ta shiga toilet din ta dauro alwala ta gabatar da sallar la'asar sannan ta soma jera kayanta cikin sif din

sama sama take jiyo sallama a falon,ta miqe ta maida hijab dinta tayo hanyar falon,budurwar da suka gani ce dazu tsaye tana kalle kalle ''sannu''maryam tace da ita don jawo hankalinta ta fuskanci ta fito a dage ta kalleta ''ina mami?'' ''ta fita aiki'' bata tanka mata ba ta juya ta fice itama maryam ta juya ta koma dakinta

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [16/09, 21:04] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺

▶1⃣2⃣

Har gefin magariba tana gyaran kayanta cikin drower din,dakin tsaf yake don haka bashi buqatar wani sabon gyaran na daban,ta maida qofofin cupboard din ta rufe dai dai lokacin ta jiyo kiran sallah sama sama saboda haka ta shige toilet

har isha'i tana kan abun sallarta,sai da ta bada faralin isha'in sannan ta nannade ta,zaman shirun ya mata yawa,sai kewar gida ta soma damunta,ta jawo wayarta ta lalubu number din hindatu ta kira,ba bata lokaci ta daga ''wayyo ya maryam dita,i missed you wlh wuni guda kawai'' ta gatsine fuska tamkar tana gabanta ''hmmmm,ba wani nan,kinyi missing din nawa kika gaza kira na sai da ni na nemeki'' ''ayyah anty na,kinsan dai halin student,wayan,ba credit,am sorry ya maryam''

''shikenan,ya gidan ina mama ta'' ''gata kusa da ni bari in bata'' kusan minti goma suna hira har aka fara mata warning kudinta sun kusa qarewa sannan sukayi sallama toilet ta koma ta hada ruwan dumi tayi wanka ssnnan ta sauya doguwar rigarta mai kauri ta bacci ta dora hijab,tsna maida kayan da suka fadl daga cikin sif din ta jiyo sallaman mami

kan kujerar falon ta taddata a zaune tana cire agogon hannunta ''sannu da dawowa mami''cikin fara'ar nan dai tata tace ''yauwa maryama,ya baqunta,na barki ke daya ko,gurin nawa ba yara ni daya ce,gun haj laura kuma basu sanki ba bare ki shiga,sannan na manta ban nuna miki kitchen ba,ina fata yunwa bata takura ki ba'' murmushin itama tayi ''banjin yunwa ma mami'' ''a'ah,ban yarda ba,bari na shirya na fito saiki dafa mana wani abun mai sauqi'' ''to mami'' miqewa tayi tana nuna mata jakar da ta shigo da ita ''taimaka ki shigo min da brief case din nan''inji mamin ta haura sama maryam din ta bita a baya tana mamakin sauqin kai irin na mamin,tamkar ita ba wata bace,tsabar sanin qima irin ta dan adam

saman ma wata duniyar ce,komai nashi fari ne tun daga parlour har bedroom din mamin sai dan ratsin baqi kafan wanda bai taka kara ya karya ba ''hmmm,wani aikin sai likitoci''maryam ta fadi a zuciyarta

a falon qasan suka sake zama bayan sun kammala cin abincin daren ''gaskiya maryama my son zai morewa girkinki,haka kija iya abinci''a kunya ce tayi mata murmushi cikin seriouse tone tace ''maryam kamar yadda na fadi miki dazu inason Abdallah so na haqiqa saboda shi kadai Allah ya mallakamin,cikin irin abinciccikan da Abdallah keso akwai irin namu na gargajiya,sannan yanason kayan snacks,aikinki zai kasance ne ranar weekend zaki dinga breakfast lunch da dinner,amma ragowan kwanakin breakfast ne kawai sai dinner,amma idan ke kina da buqatar ci zaki iya dafawa,saidai majority idan da wuri abdallah zai fita yana tafiya ne da breakfast dinshi

sannan anan zaki dinga shirya masa saman dining dina anan yake karyawa,ina fata nima za'a dinga sammin idan an dafa din''ta qarashe cikin sigar tsokana,dariya ta baiwa maryam ''me zai hana mami,ai sai kince ya isheki ma'' ''to godiya nake,amma please maryam ki riqe min amana don Allah,na yarda da muta ne da dama akan Abdallah na amma sun ha'inceni,and pls feel free ke 'yar gida ce'' taji dadin bayanin mamin sosai har zuciyarta

kadan kadan mamin ke janta da hira bayan ta nuna mata store da kitchen din nasu,tace ta duba idan da abunda take buqata ta fada zuwa gobe da safe a siyo tunda da yamna take tunanin zuwan Abdallan girgiza kai tayi ''komai yayi mami'' ''to masha Allah,sai waj.....'' maganr tata ta katse sakamakon shigowar kira wayarta qirar iphone 7 murmusho maryam taga tayi har haskrn haqorin makkar ta ya bayyana ''dan halak,yaqi ambato''mami ta fada a bayyane tana shirin daga wayar ''salamu alaikum my son yanxu nake zancenka'' ''mami na ke da wa?'' ''sabuwan mai dafa abinci nayi maka abdallah'' sai da ya danyi jim ''anya mami ba za'a haqura haka ba?'' ''kada ka damu son,insha Allahu wannan karon ba za'a samu matsala ba kaji,saboda hankali na ya kwanta da ita fiye da wadancan'' ''tunda kin aminta mami shikenan''maryam dake tsaye sai ta danji ba dadi,duk da bata jin abinda yake fadi amma ta fuskanta kamar bai marhabin ne da zuwanta gidan

''insha Allahu ba damuwa,yanzun ma muna tare,muna tsara tarbarka gobe'' ya narkar da murya tamkar qaramun yaro ''ayyah mami na,abinda nakw ta fargabar gaya miki kenan tun dazun,aikin ne mami bai kammalu ba sai nan da kwana uku,kinga ya zama dole na qara kwana hudu kenan,bazai yiwu na taho na barsu ba gudun samun matsala,but....i promise mami na nan da kwana hudu a gida zan kwana kiji mamina,kuma pls kada ki saka damuwa cikin ranki'' ta danji a ranta kam don tana matuqar son Abdallah,amma sai ta share ''shikenan my son,Allah ya kaimu ya kuma kare min kai,ya bada sa'a,ka ci gaba da addu'a don Allah banda wasa'' ''insha Allah mami na,i love you'' sai da tayi murmushi sannan tace ''i love you too my son''

daskarewa maryam ta kusa yi a tsaye,tana sake jinjina soyayyar dake tsakanin mami da dan nata ''kinji ma maryam,abdallah ya hutashsheki,sai nan da kwana hudu zai dawo''tace da maryam wadda ke duba,cikin wani dan qaramin oven dake gabanta wanda a badini duniyar tuna ni ta tafi,ta dan washe fuska ''ayyah,Allah ya nuba mana'' ''ameen ameen,mujeko sai kiyi kwanciyarki abinki'' tare suka fito falon sai suka tadda ta a zaune saman kujera,budurwar dazu ce ''sannu mami''tace tana dan murmushi hade da kallon maryam da hakanan tun ganin farko taji ta tsone mata ido,ko don kyawun da take hangowa baro baro ne kwance a halittar maryam din oho? ''yauwa sannu zubaida'' ''na shigo ai dazu baki nan sai waccar na gani'' mami ta juya tadan kalli maryam ''sunanta maryam....ya akayi zubaida?'' tadan murmusa ''zuwa nayi na amshi key na part din ya abdallah zansa a gyara,naji kamar gobe zai dawo ko?'' '' damuwa jeki abunki zubaida zan gyara miahin da kaina,tunda kinga waccan karon yayi fada'' ''to zan gyara da kaina mami'' ''kada ki damu zubaida,jeki abunki''raahin,kin dadi qarara ya bayyana a,fuskarta,amma sai ta juya zata fice ''am....zubaida''mami tayi kiranta ta juyo a sanyaye,kana ta amsa ''ku tafi tare da maryam ta gaida nene,ma'aikaciyar da na daukarwa abdallah ce'' dif zubaida tayi a ciki ciki tace ''to''ta juya tqci gaba da tafiyarta

momy ta kalli maryam''kije ku gaisheta,abokiyar zama na ce tin kafin rasuwan abban abdallah'' to din itama tace kana tabi bayan zubaida da tuni ta fice daga falon nasu har ta isa filin dake cikin bangaren nasu

Tana biye da ita har suka shiga bangaren nasu,ginishi iri, na mamin ne babu maraba sai bambancin furnitures,mutum biyu ne zaune a falon kallo suke na wani american film a M B C ACTION wanda volume dinsa ya gauraye falon,zubaidaida batayi sallama ba sai maryam wadda siririyar muryarta bata wadatar da su sun jita ba,zubaida ta zauna kusa da matar wadda ta kusa ahekara hamsin da biyar tana fitar da numfashi daga bakinta matar na juya ta dubeta ''um hmmm,ai nasani iska ce ke wahalar da mai kayan kara,ni nasan ba baki za'ayi ba,amma tunda ke kika g....'' ''nene ga mai aiki nan mami tace na kawo miki ki ganta''ta katse babar tata don ta lura basu lura cewa ba ita daya ta shigo ba lokaci daya suka zuba mata ido nenen da daya budurwar dake zaune kusa da ita har maryam din taji faduwar gaba

nenen ta maida kallonta ga zubaida ''mai aiki,kodai baki ji bane sosai'' cikin yamutsa fuska da alamun qosawa tace ''wadda zata dinga wa ya Abdallah girki da ta canza'' nenen ta dawo da kallonta gun maryam,ta dan tara qarfin gwiwarta tace ''ina yini''second kusan biyar kafin tace ''lafiya,Allah ya taimaka'' ''ameen,sai da safenku''maryamun ta fada tana juyawa ta fice a bangare nasu,sai da ta fita sannan ta samu nutsuwa,don ta tabbata rakiyar idanu suka yi mata

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [16/09, 21:06] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺

▶1⃣3⃣

cikin kwanaki ukun da tayi da mami ba qaramin dadin zama da ita taji ba,maca ce mai sauqin kai da iya mu'amala,haba haba da jama'a kowa nata ne,duk lokacin da suka zauna bata da labarin bawa maryam da ya wuce labarin abdallah halayenshi me yakeso mene baya so quruciyarsa da shirmensa tun maryam na daukar abun qarami har ta maida shi babba,lallai qauna ce mai girma tsakaninsu wanda Allah ne kawai yasan iyakarta

takanyi kuka aduk lokacin da mamin ta gama bata labarin mu'amalarta da Abdallah,tana dadewa kafin tayi bacci me yasa ita bata ganin irin wannan qaunar musamman daga gurin abbanta? me tayi masa? wanne irin laifi tayi masa da yasa take samun rashin kulawa da raahin damuwa da ita daga abbanta? saidai tana godiya ga Allah saboda uwa ta gari da ya bata mai jajircewa kan lamuranta

duk lokacin da zata fito zata tadda sashen nasu tas,ma'aikatan har sunzo sun gama aikinsu sun tafi,saboda mami gwanar tashi ce da wuei ta saba,sai aka hada biyu don itama maryam din haka saboda yanayin aikinta da tayi a abaya

Readers Also Read

More by Ayshacool 1