Kenza eBookz

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 32

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 32

Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 32: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 32. Bayan aunty babba ta shiga, rage kayan…

4,279 words

Bayan aunty babba ta shiga, rage kayan jikinta tayi sannan ta shiga toilet tayo wanka, tafito ɗaure da towel, closet ɗinta ta buɗe ta ɗauko wata rigar kuma doguwa tasanya mara nauyi, tunkan ta idasa sanya rigar Wayarta dake acikin purse ɗinta take faman ringing, Cikin sauri ta idasa zura hannun rigar ta ƙarasa inda purse ɗin take saman gado inda tayi throwing ɗinta time ɗin da tashigo, Zama tayi saman gadon sannan ta sanya hannu ta ɗauki purse ɗin ta buɗe , kuɗaɗe ne aciki sabbi fal Bugun abuja, sauran wanda suka ciro a banki ne na siyayyar da sukayi, Wayar ta ciro ta duba mai kiran nata sunan *AMANI* ne ya bayanna akan screen ɗin, Murmushi tasaki domin dama tun jiya take son kiranta, ɗagawa tayi tare da karawa a kunnanta tana faɗin " Dama tun jira nake son na kira ki abubuwa sun min yawa,' On the other hand , Amani tace "Aunty laila kenan kin manta ni kin share ni,' Aunty babba tace "Ke dallah ba dole in manta ki ba, ke bakisan me ya faru ba, akwai labari zazzafa Cikin zumuɗi amani tace "Bani nasha, am so eager to hear it, Dariya aunty babba tayi tace "Idan ma a tsaye kike to ki zauna," Amani dake a tsaye gaban mirror, taja kujerar dake gabanta ta zauna tana faɗin "Na zauna Auntyna, Ina sauraron ki ' Nan aunty babba ta zayyana mata komai game da su Hosana da jahad da Omar ya kawo mata hada kuɗin da suka kar6a a wurinsa da purchasing ɗin da su kayi masu kaf ta faɗa mata,' Shiru Amani tayi jikinta yayi mugun sanyi, muguntar aunty babba ta razanata, bakomai ya tsaya mata arai ba, face da tace Yaran suna acikin store tun jiya ba abinci, tuni idonta sun ciko da kwalla saboda ita takasance mai tausayi ce sosai, aranta tana cewa meyasa Omar bai kawosu nan ba tabbas ya aikata babban kuskure domin kuwa tasan tabbas Aunty babba bazata ƙyale yaran nan ba, azabtar dasu zatayi............ Sam ta manta waya suke har sai da muryar aunty babba ta ratsa ta da cewa "Kinyi shiru baki ce komai ba....? Cikin sauri Amani tace "Ae daɗi ne ya hanani yin magana Auntyna, gsky naji daɗin labarin nan da kika bani kamar kamar me, kin ga yanzu wuƙa da nama suna hannin ki sai yadda kika so zakiyi da yaran, domin kuwa matsala ne a target ɗinmu, babban ma abun burgewar ta kuɗin da kika samu a wurinsa kin ga mun fara samun na ziyartar wurin bokan..........' murmushi aunty babba tasaki tare da cewa "aikuwa dae kuɗi fa sun fara samuwa, yanzu dae shawararki nake nema akan yaran nifa bazan bari sukai labari ba! Shiru amani tayi tana sauraranta aranta tace "baƙar muguwa, in sun tashi kai labarin ki hana su mu gani, mtssw haɗamammiyar banza,' A fili kuma tace "Auntyna kinsan me? "A'a saikin faɗa" acewar aunty babba, Amani tace "shawarar da zan baki shine, kada kice zakiyiwa yaran horon yunwa sam wannan bai ma taso ba, saboda kinsan Marshal Omar mutunne mai kaifin basira, wlh muddin yazo kallo guda zaiyi masu ya gane cewa akwai yunwa ajikinsu kuma zai tuhume ki akan hakan, sannan muddin kina so target ɗinmu ya tafi yarda muke so dole fa atlease ki jure ki ɗan basu kulawa ina nufin Kayan da kika ce anyi musu siyayyarsu arinƙa basu suna sanyawa, sannan ki rinƙa barinsu suna yin wanka ko sunyi haske............... dakatar da ita Aunty babba tayi tare da cewa "Amani me kke Nufi? Ni zan basu kulawa har haka, Allah yakiyaye wlh, ke nifa natsani yaran tun da nagansu, saboda raina nabani cewa nan gaba sune zasuyi sanadiyar tarwatsa mun plan ɗina," Cikin lallami Amani tace "Aunty na lura baki fahimce ni ba !! Abun da nake ji maki tsoro shine Omar zai iya yin zuwan bazata nan kaduna, kwatsam ya faɗo What will u do? Ajiyar zuciya amani tasaki ta wani 6angaren maganar Amani gaskiya ce don haka tace "Shikenan zan duba nagani, amma fa Allah saina sa an zubar da twins ɗin can,' "Dama wannan ae Wajibun ne Auntyna," acewar Amani acikin zuciyarta kuma tace "Muguwa in Allah ya yarda bazaki ta6a cin nasara akan hakan ba,' Sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi sallama da juna,"

Bayan amani ta ajiye wayarta ta asaman mirror ɗin gabanta,

tace" dama ni Omar ya kawowa twins ɗin tabbas da sun samu kulawa, iya kaci kuɗine nima zan kwasa, tunda nima Lashe Money ce, Ta miƙe tana Zagaye acikin ɗakin ta wani 6angaren taji daɗin ɗaukar shawararta da Aunty Laila tayi koba komai Yaran zasu samu salama, dama wayau tayi mata don ta taimaki yaran da taji tace tun jiya suke acikin store garƙame, haƙiƙa ta tausaya musu, _______________________________________

Ganin har la'asar tayi ba sehrish yasa hankalin azmee tashi baiwar Allah sai faman zirga² take yi tarasa inda sehrish ta shiga, fitowa tayi daga ɗakinta tana faɗin "Anya sehrish lafiya kuwa, karfa ace wani abu ya same ya zanyi nikam, tsayawa tayi riqe da qugu tana tunani can ta tuna cewa sehrish fa tunda ta shiga kaiwa Babban yaya breakfast a ɗakinsa bata dawo ba, Aikuwa cikin sauri Azmee ta wuce Upstairs ɗin jiki na rawa, aranta tana Allah Allah ta same ta acan kota huta da zullumi, time ɗin da tashiga part ɗin tunkan ta isa wurins sofas ɗin taga alamun mutun baje ƙasa, da hanzari Azmee ta ƙarasa zuciyarta na ɗar², tana isa hankali tashe take faɗin "Subhanallahi Sehrish kuma kwance a ƙasa? Meya faru ne? Cikin hanzari ta zukunna tana tatta6a jikin sehrish wani irin Sanyi taji ajikinta, jijjiga ta, ta shiga yi tana faɗin "Sehrish ! Sehrish !!! Ki tashi meya faru ne !? Shiru babu amsa cikin sauri azmee ta miƙe takai hannu saman table inda Sgr ya kammala breakfast yabar stuffs ɗin asama, Robar ruwa ta ɗauka mai sanyi, jiki na kerma duk ta ruɗe tsoranta karta rasa Ɗan Tukur ɗinta 😂 Da sauri take murɗa murfin roban, tayi wurgi dashi cikin hanzari ta ƙarasa inda sehrish take ta zauna ƙasan, sannan ta ɗebo a hannunta ta yayyafa mata shi a face ɗinta, aikuwa arazane sehrish ta farka firgit ta tashi zaune tana faɗin "La'ila ha'illallah muhammadur rasulillah.......' sai faman zazzare eyes ɗinta take cike da tsoro, "sehrish ki natsu Aunty azmee ce, meya faru ne," sai lokacin sehrish ta kalli Aunty azmee wadda ke zaune tana fuskantarta, wani sanyi taji aranta murya na rawa tace "Aunty Azmee babban yaya fa? shine....shine...ya firgitar dani bansan me ya faru dani ba...' a rarrabe take magana duk ta tsorata, Dariya azmee tayi tunkan sehrish ta faɗa mata tasan cewa yau Sehrish taci karo da Sarkin Dawa wato zaki, "Wani abu yayi maki ne"? ta tambaya bayan ta tsagaita da dariyar, "A'a aunty azmee, kawai ina leƙen wayarsa ashe ya fito bansani ba, kwatsam ina juyowa haka mukayi Ido biyu dashi, nan take naji zuciyata ta buga daga nan bansan me ya faru ba...amma aunty azmee babban yaya cikakken mutun ne ? Fashewa da dariya azmee tayi dakyar ta tsagaita tace "Me kika gani"? Sehrish tace "Aunty azmee idonsa irin na Horrrow ne, kuma ko acikin film ɗin Shu'uma na Aman Junaid khan in zasu koma Aljanu idansu ke komawa Blue......' wata irin dariya azmee ke 6a66akawa sam tagaza tsayar da kanta, shiriritar sehrish tafi ƙarfinta, ita kuwa sehrish bil'haƙƙi dagaske take bama azmee bayani, Ganin yarda azmee ke ta dariya yasa sehrish cewa "Aunty azmee meyasa kike mun dariya? nafaɗa miki gsky ne fa,' Ruko hannunta azmee tayi tare da cewa "wlh sehrish shiriritar ki tafi ƙarfinki, wato tunda suma eyes ɗinsu na komawa blue in zasu koma Aljanu shima kenan Jinsinsu ne koma ki ce shine Aman junaid Khan ɗin ke kuma sai ki zama AYYANARSa ,

tayi maganar ne yayin da suka miƙe atare, jin abunda azmee tace yasa sehrish yin murmushi wato zata zama Ayyanar Babban yaya 😂 acikin zuciyarta tace "Kowaye zai zama Aljani kaliya in hakan tafaru"?

"Sehrish bari na gyara masa part ɗin ki kwashe tray ɗin abincin ki kai kitchen sannan nasan kina jin yunwa sosai tun safe baki ci komai ba, ki tabbatar kinci abinci sannan kiyi sallah hada bath ma," azmee ce tayi mata bayanin tare da sakin hannunta data ruƙe, Wucewa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin har takai bakin ƙopa Azmee tace "Gift na nan na ajiye maki,' Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Toh aunty azmeee zan duba," Futowa tayi tana tafiya amma sam tagaza rufe bakinta saboda ance zata zama Ayyanar Babban yaya wato mai basa kariya daga Maƙiyansa masu kawo masa Hari, har ta sauko down stairs tana wannan tunanin aranta tana fatan Allah yasa ta zama Ayyanarsa ta gaske ❤😍

Kitchen ta shiga ta ajiye tray ɗin, sannan ta zuba ma kanta breakfast ta zauna anan taci tayi hani'an (Allah sarki su Hosana) 😥

Bayan ta kammala tashiga bedroom ɗinta, sai da tafara yin alwala tayi sallar azhar da batayi ba sannan tayo wanka ta kimtsa cikin kayanta na gado, Sai da tazo gaban Mirror Don ta kalli fuskarta sai lokacin ta lura da Kwalin wayar da Azmee ta ajiye mata, Zaro ido tayi in Amazing ɗin nan hada sa hannu abaki don mamaki,daga bisa ni tasa hannu ta ɗauki wayar, jiki na rawa ta buɗe kwalin ta ciro wayar sabuwa Ƙal da ita, ga charger ɗinta da sauran abubuwa, Wani irin ihu sehrish tasaki na farin ciki, ita kanta batasan lokacin da tayi tsalle tahaye saman gado tana rawa ba, daga bisani kuma ta koma takwanta saman gadon, jiki na rawa ta kunna wayar sai faman murmushi take saki, haske ta kawo sehrish ta ƙura ido tana kallon screen ɗin wayar, nan fa tashiga dannarta ba Arziƙi can ta tunano dasu hosana jikinta yayi mugun sanyi aranta tace "Allah sarki su hosana,da ace wayar tsohuwa na shiga dana kira ku mungaisa, bansan meyasa ba'a samun su ba, wane hali suke ciki inaso in sani, itama tsohuwa bansan meyasa ba'a samunta ba,' Hawaye ne taji sun zubo mata jikinta yayi mugun sanyi, ajiye wayar tayi gefenta, ta yi uban tagumi cikin takaici ada tana farin ciki da wayar amma yanzu farin cikin ya ragu sosai, dama duk ɗokinta akan waya saboda su Hosana da Jahad ne,😥

Shiru tayi tana tunanin ya zatayi, ƙarshe ta yanke shawarar zata amshi numbarsu wurin Junaid baza'a rasa ba may be~~~~~~~~~~~~

Tana cikin wannan zaman azmee ta kwankwasa kopan cikin sauri ta share hawayenta sannan ta tashi ta buɗe mata, "Sannu da aiki aunty azmee,"

Da murmushi a fuska azmee tace "Yawwa Ayyanar Babban yaya dama inaso nace kin ga wayar ko? Cikin jin kunya sehrish tace "Eh naganta bansan da wane baki zan gode ba, Azmee tace "Nasan yau wata daƙer zata iya bacci don ɗoki," tayi maganar cikin Zolaya,. Kafin daga basani tace "In akwai abun da baki gane ba game da wayar, kiyi ma junaid magana ya koya maki, nagama ya shigo yanzun nan" "To shikenan aunty azmee i will talk to him," Juyawa azmee tayi ta wuce room ɗinta,

Dawo wa tayi ta ciki ta shirya tsaf ta ɗauki wayar sannan ta fuce, a babban falon suka ci karo da Haroon wanda shigowarsa kenan, ji tayi gabanta ya faɗi shi kuwa washe baki yayi yana faɗin "ƴar shila wato guduna kike yi naso ace jiya na Cafkeki da kin gane baki da wayau.. Shiru tayi batace masa komai ba, ci gaba da cewa yayi "kisa me ni a bedroom ɗina yanzun nan ina jiranki, ki taho mun da fresh fruits, in kuma kika ƙi zuwa hmmmmmmm kinsan sauran, Yana faɗin hakan ya wuce yana sakin murmushi,.

Jikin sehrish yyi mugun sanyi,tsananin tsoron haroon takeji saboda gudun karya tona mata asiri, bakowa tafi ji ma tsoro ba face Babban yaya, batasan wane hukunci zasu mata ba, gashi ta tsorata dashi daga kallon kwayar idonsa ta zube inaga ya damƙe ta 😳

Tana cikin wannan tunanin Muryar junaid ta sauka a kunnanta "Ƴan mata sannu fa,' firgit ta ɗago tana kallonsa, saukowa yake yi daga upstairs yana murmushi jikinsa sane da riga da wando, A hankali ta furta "junaid" Ƙarasowa inda take yayi yana cewa "ya kke? Ya nagan ki a tsaye nan"? Yayi maganar yana kallon fuskarta, "Dama wurin ka zanzo Aunty azmee tace nayi maka magana akan wayar nan" tayi maganar tare da nuna masa wayar dake hannunta, Murmushi ya saki tare dasa hannu ya karba yana cewa "me kike son sani game da ita? Tace "Komai ma sannan akwai abunda nake so na tambaye ka ma," "Ok, bazan iya jure tsayuwa ba, biyo ni musa mu wuri mu zauna ya faɗi tare da kama hanyar zuwa bedroom ɗinsa bin shi tayi zuciyarta na bugawa saboda tsoran Abun haroon zai yi mata wato yace taje taƙi zuwa, Ashe haroon na nan yana kallonsu ita da junaid abun ya baƙanta masa rai kuma yaci alwashin sai ya ƙuntata mata,

Shiga ciki su kayi atare wuri yasamu ya zauna gefen gadonsa tare da bata Umarnin ta zauna, Da ɗan tazara kaɗan a tsakaninsu,bayan sun natsu sehrish tace "junaid dama inaso na tambaye ka game da Numbar nan dana ta6a sawa a wayarka ta ƴan uwana bansan ko za'a samu ba ynx," Shiru junaid yayi yana tunani can yace "baza a rasa ba, Last time if i can remember sun turo mun message Lemme check it for u, yayi maganar yana zura hannunsa na dama cikin trouser pocket ɗinsa yayin da right hand ɗinsa ke ruƙe da phone ɗin sehrish, Sehrish kuwa tunda taji cewa su hosana sun turo sako hankalinta ya tashi burinta taga me suka rubuta, Zaro phone ɗinsa yayi tare da kunna ta, yashiga cikin messages ɗinsa yana duddubawa, yayin da jikin Sehrish sai kerma Yake sbd fargabar me suka turo, "Yawwa Allah yaso banyi delete ɗinsa ba gashi ki gani," miƙa mata wayar yayi, hannunta na kerma ta amsa ta soma karantawa kamar haka *sister maganin hosana fa ya ƙare akwai matsala ta zama wata Xararriya ta hana mu sakat pls ki taimaka mana*

Junaid na lura da halin da Sehrish ta shiga, lokacin da tazo ƙarshen sakon, zumbur ta miƙe tsaye cikin tashin hankali murya na rawa take faɗin"Innalallahi wa'innna ilaihirraji'un junaid tun yaushe saƙon nan yake ...? ta tambya a rikice, Miƙewa shima junaid yayi yana cewa "Am sorry sehrish wlh naso na taimaka musu tun lokacin ki duba message ɗin dake a ƙasan nasu ki gani na tura masu sako nace su turomin acct number nasu amma shiru i ave been trying their phone number but always switched off har na haƙura. ' Cikin shesshekar kuka Sehrish tace "Allah sarki hosana, nashiga ukuna bansan ya suka ƙare ba, hosana tana raye kota mutu nasan ba mai taimakon su....." Kuka ne yaci ƙarfinta sosai, Cikin sanyin Murya junaid yashiga lallashin ta, Cikin kuka tace "junaid bazaka gane bane...nasan suna cikin mawuyacin hali babu mai taimakonsu ina so naje wurinsu nagansu....' tayi maganar a kasalance, "Sehrsih in dai anan garin suke ni zan kaiki a mota ta ki gansu,' Girgixa mishi kai tayi tare da cewa "Ba'anan suke ba junaid" duk tabi ta susuce,.. Ajiyar zuciya junaid yasaki tare da cewa "kada Ki damu sehrish nayi maki alƙawarin cewa da kaina zan kai ki, ki gansu koma ina suke, amma sai Babban yayan mu ya koma U.s saboda in yana nan bazan samu hanyar da zan fita ba,' tsagaitawa tayi da kukan ta kalle shi tare da cewa "kayi Alƙawarin xaka kaini " "Eh insha Allah, amma ynx ki goge hawayen naki, ashe kin iya kuka har haka just like a new born baby,' yayi maganar da zolaya yana Imitating ɗinta, Ita kanta batasan sadda ta fashe da dariya ba, saboda yadda junaid yake kwaikwayon kukanta sai ya koma mata tamkar babyn, Hannu tasa ta share hawayenta, sannan yace "Kin natsu yanzu"? "Eh" ta bashi amsa, Komawa su kayi tare da zama, sannan junaid yashiga nuna mata yadda zatayi amfani da wayar, Sam hankalinta baya akan jawabin Junaid ta tafi can duniyar tunanin halin dasu hosana ke ciki, Apps ya tura mata kala kala a wayr masu amfani daga wayarsa, dayake akwai sim aciki mtn nan take ya buɗe mata whatsapp, Duka ya zuba mata numbers ɗin yan gidansu aciki, sannan yasanya ta a grps ɗinshi na friends,. Daga bisani ya bata wayar suka yi sallama ta koma bedroom ɗinta, ganin time ɗin Sallah yayi yasanya ta ajiye wayar saman side drawer ta wuce toilet tayo alwala tayi sallar la'asar,

______________________________________

Bayan Aunty Babba ta kammala waya da Amani Fitowa tayi ta sauko down anan tasamu hafsat ta buɗe akwatinan kayan da suka siyo tana duddubawa, Kayane masu kyan gaske, Cord laces, Materials atampha, dogayen riguna kala-kala, Sleeping dress, Inners ba abunda basu siyo ba,hada Shoes & bags na gayu, ga Ribboms , turarurruka , jewellery everthing fa sun sayo, "Gasky mommy na cha6a fa, kayan nan sunyi kyau saura a ware wanda za'a kai ɗinki,. Hafsat ce tayi maganar tana kallon Aunty babba wadda ke tunkaro ta,. Gefenta ta zauna saman 3 seater ɗin da take, sannan tace "Zamuyi magana akan wannan zuwa gobe, ynz nagama magana da Amani a waya,' ta6e baki Hafsat tayi tare da cewa "kin faɗa mata game da twins ɗin can? "Eh na faɗa mata har ta bani wata shawara,' "Me tace ita"? Hafsat ta tambaya yayin da take ajiye Veils ɗin dake hannunta cikin akwatin kayan data buɗe Nan Aunty babba ta kwashe komai da suka tattauna ta sanar mata, wani irin kallo hafsat tayi ma mommyn nata kafin tace "ke kuma sai kika ɗauki shawararta ko? Aunty babba tace "eh naɗauka saboda gsky ta faɗa Omar zai iyayin zuwan bazata kuma duk sanda yazo zai fahimci halin da suke ciki zai tuhume ni akan hakan, don haka zan basu kulawa ta wani lokaci kafin nasa a Zubar dasu,'. Rai a6ace hafsat tace "Yanzu mommy har shawarar Aunty Amani zata fi tawa mahimmancin a wurinki !? murmushi aunty babba tasaki tare da cewa "Ko kusa, kawai akwai abunda na hango ne shiyasanya," Jinjina kai hafsat tayi tare da cewa "Shikenan Mommy, amma koda za'a rinƙa basu abinci dole suyi mana bauta acikin gidan nan !!". "Wannan ae dolene, zasu aikatu kamar jakuna duk wani aiki na gidan nan kansu zai koma," aunty Babba ta bata amsa, Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "daga yanzu na daina wanki da washing maching, Tun da Allah ya kawo mana sauki lallai ne zasu aikatu, "Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kaisu bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae" ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,

______________________________ Abban sojoji sashe na biyu wasu haryanzu basu fara payment ba, Free pages ne nake sanyawa yanzu don haka ku hanzarta biya tunkan su Ƙare saura pages kaɗan ma, idan kuka ce zaku naɗe hannu nima zan dakata ne🙅, inyi takaina dama ya lafiyar giwa, abun ya bani mamaki many of u sunyi shiru akan hakan, zamu ba juna mamaki ne insha Allah 😂 Boss Lady ce fa,

Abban Sojoji akwai Nrml grp 300 Special grp 500 Vip (700) iya kuɗinka iya shagalin ka, ni nawa tsarin daban ne nasan yadda zanyi da kowa,🙌 Wanda suka shirya 08103884440, su tuntu6e ni,

*sai naji sauƙi insha Allah zan ci gaba*🙏 Just keep praying for me don bani lfy😥, sannan waɗanda suka ga Pictures ɗina pls don't share it, ban bada Iznin ayimun share ba, sbd bansan bakin wasu ba,bansan me zasu ce ba,🙏😿*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_🔥the Father Of Soldiers🔥_

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ_ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💞😍

ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ✨ *Mallakin*

*✨HAFSAT BATURE MOH'D✨*

~BossLady~💋

*Final Page In Part 1*

*page 100*⚡

"Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kai su bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae" ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,

tayi mamakin ganin ƙopan store ɗin abuɗe turowa tayi ta shiga samun su tayi a tsaitsaye sai faman zagaye zagaye suke yi sun jigata sosai,.

Suna ganinta gabansu ya faɗi rass saboda tsoran matar suke ji sam sun gaza magana sai zare ido kawai,

murmushi Aunty Babba tasaki tare da cewa "Ashe kuna raye, gsky kuna da taurin rai,' Jahad ce tayi ƙoƙarin gaishe ta bata amsa ba sai cewa tayi "ku biyo ni" Sannan ta juya ta fice suka bi bayanta aransu suna Allah Allah gudun karta yi masu wani abun,

A wani bedroom ta tsaya ta turo door ɗin sannan tashiga, suma suka bi ta ciki, ɗumemiyar katifa ce a ɗakin sai wardrobe ta bango, da ƴar drawer,

"Kada kuyi tunanin a ɗakin nan zan barku, tsohon store ɗin can shine wurin baccinku in dare yayi, na kawo ku nan ne domin kuyi wanka ku samu kuyi sallah, sannan zan baku abinci duk rana plate ɗaya, amma ku sani zaku Aikatu sosai, don Gwamnati bata aikin banza,'

aunty babba ce ke kora masu bayanin nan ba mutunci a fuskarta, a daga tsayen da suke, Kallon juna su kayi jiki asanyaye koba komai sun samu sauƙi atlease, Jin sunyi shiru yasa ta daka masu tsawa da cewa "Baku ji ina magana bane, kun wani tsayamin kamar ƙerarrun gumaka,'. Murya na rawa suka haɗa baki wurin cewa "Zamuyi komai kke so insha Allah," ta6e baki tayi tana kallonsu tace "kada kuyi tunanin sauƙi kuka samu a wurina, sam ba haka bane don yanzu uƙubar tafara," Jahad tace "Laifin me muka yi maki ?. dariya aunty Babba tayi tare da kallonta ita da tayi magana tace "bakuyi mun laifin komai ba, kawai kun shiga tsakani na da abun Hari na ne shiyasanya,' tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin, Shiru su kayi suna kallon juna bakomai ya tayar masu da hankali ba face abunda Aunty babba tace wato kada suyi tunanin sun samu sauƙi yanzu uƙubar tafara, me hakan ke nufi !?!? ajiyar zuciya Suka saki atare wuce wa Jahad tayi toilet domin ita damuwarta Sallah, Hosana kuwa saman katifar tahau ta zauna idonta cike tab da kwalla luhu luhu Yunwa take ji Over,

Wuce wa kitchen Aunty babba tayi lokacin har hafsat ta koma bedroom ɗinta ta kwashe kaf kayan da aka suyo masu hosana da Jahad ta shige dasu (uwar Son banza)

Sai faman yamutsa fuska take kamar uban wani ya matsa mata ta haɗa musu abinci,.. Duddubawa tayi Cikin kitchen ɗin tana jin bazata Iya girkawa yaran Abinci da hannunta ba, Akwai sauran breakfast ɗinsu na safe da suka rage duk yayi sanyi abincin,

Tsayawa tayi tana tunani aranta kawai ta daure Just for today ta dafa musu ko Indomie ce, Nan da nan ta kunna gas ta aza pot ta zuba ruwa ciki, shaf shaf ta haɗa kayan haɗi aciki ta zuba musu Indomie ɗin aciki, Bayan ta kammala dafuwa, ta ɗauko plate mai ɗan faɗi ta baza musu Ita aciki da zafi zafinta sai ƙamshi take yi,

A tray ta ajiye musu ita sannan ta haɗa musu da sauran kayan breakfast ɗinda suka rage na safe, tare da drinks,. Sai gata tafito ɗauke da tray ɗin ta wuce dashi ɗakin lokacin da ta shiga Jahad har ta fito Tayo wanka tare da Alwala ta maida kayan jikinta, tana a tsaye tana tunanin me zata sa tayi sallah, Sai gata tashigo ba sallama ajiye musu tayi a ƙasa batare da tace komai ba sannan ta fuce, Jikin hosana har kerma yakeyi ganin abinci jiki na rawa tasa hannu ta janyo tray ɗin, saboda zumuɗi ta buɗe plate ɗin dake ɗauke da taliyar, a gaggauce ta tsoma hannunta sam bata lura da hayaƙin dake fita ba saboda a makance take da yunwa nan take hannunta yayi jawur, zare hannun tayi tana kuka, Hankali tashe jahad ta ƙaraso tana faɗin "Hosana meke damunki ne baki ga taliyar tana huci ba ne? Cikin kuka tace "Yunwa nake ji sosai ne" "Nasani ae," jahad ta faɗi tare da zama gaban tray ɗin, hannu tasa ta buɗe ƙaramar warmer ɗin dake ajiye cikin tray ɗin,soyayyen dankalin turawa ne da doya da kwai duk ta haɗe masu sunyi mugun sanyi, Cikin sanyin murya Jahad tace "Ki ci wannan hosana ba zafi duk da yayi sanyi sosai, ruwan kashe gobara ba dole sai da mai kyau ba," Hannu suka sa atare suna ci daker suke tura shi cikin baki musamman yam ɗin data sanƙare, sai da suka rinƙa haɗawa da Coke ɗin data kawo masu, bayan sun cinye ne suka koma kan taliyar lokacin ta ɗan gare zafi,sunji daɗinta sosai, Ba laifi sun ɗan cika cikinsu,

Shiga toilet jahad tayi ta kuskure bakinta sannan tafito ta bude wardrobe ɗin data gani a ɗakin, wasu tsofaffin kayane aciki dama ita Sallaya take nema kuma tasamu,. ɗaukowa tayi ta shimfiɗa don tayi sallah, Kamar daga sama ta faɗo musu hannunta ɗauke da kaya, watsa su tayi saman katifar dake ɗakin tana cewa "Gasu nan in kunyi wanka ku sanya," sannan ta ɗauki tray ɗin da suka kammala cin abinci dashi ta fuce dashi tana murmushin mugunta ita kaɗai tasan me take ƙissawa aranta, duba kayan su kayi kala bibbiyu ne dogayen riguna masu kyan gaske, sai jalbaba guda biyu da takalmi silifas shima biyu, shine abunda suka samu, Jahad tace "ina ji araina yaya Omar ya turo da kuɗi asiya mana kaya shiyasa ta bamu wannan hosana ki tashi kiyi wanka kizo ki canza kayan jikin ki," tayi maganar tare da cire rigar jikinta, ta ɗauki wanda Aunty babba ta kawo musu ta zura ajikinta doguwace mai dogon hannu tayi mata kyau sosai launin rigar Pink colour ce, daker hosana tayi wanka itama ta canza kaya daga nan kuma Aunty Babba ta zo tafita dasu domin nuna musu aikinsu

Readers Also Read