Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 33
Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 33: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 33. ___________Ataƙaitace________________ A…
1,016 words
___________Ataƙaitace________________ A kwana a tashi yau wata ɗaya kenan da zamansu Hosana da jahad a gidan general Ishaq haƙiƙa sun fuskanci matsanancin tashin hankai kullum cikin tsoro suke da fargabar me zai je ya dawo, sam Aunty Babba da Hafsat basa raga masu sun mayar dasu Tamkar Jakuna marasa Ƴanci, kullum cikin ƙuntata musu suke, gashi duk wani aiki na gidan duka akansu yake ƙarewa, tun da asussuba Aunty Babba ke tashin su daga bacci tasa su fara aikace aikace, sune wanke wanke, sune shara, sune goge tiles tunda ga ƙasa har saman Bango duk girman gidan nan sai tasa sun goge ko'ina, ga Uban wanki hada na barguna, in sukayi mata kuskure kuwa har bugu take kai musu, ta tsane su kamar mutuwarta, tabbas su hosana da jahad suna cikin masifa kullum cikin kuka suke idan baka samu jiƙaƙƙun hawaye a idonsu ba to zaka samu busassu ne, duk wannan uban wahalar a rana plate ɗaya take basu na abinci su biyu don tsabagen mugunta irin nata, wani lokacin ma sai dae Jahad ta bar ma Hosana saboda tausayi ita kuwa kamar zata mutu da yunwa haka zata jure, dai dai da minti ɗaya basu samu na hutu, in ba ƙarfe sha biyu na dare ba take barinsu su kwanta, kuma acikin wannan tsohon store ɗin nan take garƙamesu sai da asuba ta buɗe su atashi ayi aiki, Wani lokacin idan yunwar dare ta addabesu Dankalin hausar nan dake acikin store ɗin suke ɗauka suna 6arewa suna Ci 😭 Duk dare sai sunci dankalin hausar sannan cikinsu ke ɗan cika, 😔
Duk wannan abun dake faruwa Marshal Omar sam bai sani ba, domin kuwa duk lokacin daya kira waya ya tambaye su sai ta shirga mashi ƙarya, in kuwa yace tabasu yayi magana dasu, sai ta fara Ja musu kunne ta buga musu warning akan karsu kuskura su sanar dashi halin da suke ciki sannan ta basu wayar, kuma agabanta suke yin wayar suna yi suna kallonta tana galla musu harara tana ƙara gargaɗinsu,
lokacin da Omar Ya shirya ziyartarsu ya kira Aunty babba ya sanar da ita zaizo, Jiki na rawa ta gyara su tsaf kamar basu ba hada kwalliya tayi musu, sannan taja musu kunne da barazanar zata kashe in suka kuskura suka tona mata asiri a wurinsa ko kuma suka yi yunƙurin cewa zasu bishi,
tsananin tsoranta yasa har Omar yazo yini guda ya tafi basu ce masa uffan fa, duk da yatafi da mamakin meyasa yaran Basa Dariya? Musamman mai ta6in hankalin saboda yasanta kullum cikin murmushi take, amma zuwan nan nasa harya tafi ko kallonsa basa son yi ba don komai ba sai don gudun kada hawaye su kufce musu yagani ya tuhumi Aunty babba, ƙarshe abun kansu zai ƙare, Wannan shi ake kira da Rana Zafi Inuwa ƙuna 😥😥😥
______________________________________
A 6angaren sehrish kuwa ta shiga halin ha'ula'i, domin kuwa Haroon Ya addabi rayuwarta, ya takura mata over, sam bai mata da sauƙi, ya gama firgitar da ita ya tsoratar da ita da yi mata barazana akan zai tona mata asiri in bata biya masa buƙatarsa ba, kullum cikin kuka take tarasa wa zata kai ma kukanta akan haroon, saboda matsa matan dayake sai ta same shi aɗaki kuma ba yadda ta iya dole taje saboda gudun karya tona mata asiri, in taje kuwa haka zai matse ta abango yana shafa jikinta kamar maraye daker take kwace kanta, in jaraba tayi jaraba har bedroom ɗinta yake biyo ta, saboda wani lokacin tana mantawa bata rufe ɗaki ba, saboda tasan ba mai shigo mata in ba Aunty Azmee ba , kamar daga sama yake faɗo mata wani sa'in sai dai taji mutun ya faɗo mata saman gado ya tsoratar da ita, sehrish tasha kuka fiye da tunanin mai tunani duk da haryanzu haroon bai ida tarwatsa mata rayuwa ba, Allah na taimakonta tana kwace wa daga hannunsa ta faɗa toilet ta datse, tasha kuka iya kuka, taso ta sanarwa aunty azmee amma ranta na bata cewa Aunty azmee ba abunda zata iya saboda ƴar aiki ce ita, haka zalika taso ko Junaid ne ta sanar mishi amma sai take ganin tonawa kanta asiri zatayi ƙarshe ma tayiwa kanta sanadiyar barin gidan gaba ɗaya 😥
a 6angaren sgr Sam bai sake tunanin ya tuhumi mai aikin nasu ba, ba don komai ba sai don wasu dalilai, tun ranar da suka haɗa ido ta sume, ya tabbatarwa kansa cewa koma wacece muguwar matsoraciya ce, Muddin yace zai yi mata tsawa to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ta mutu, Saboda irin hakan tasha faruwa dashi, akwai masu laifin da tsawa kawai yake daka musu zuciyarsu ta buga don tsoro, shiyasa ya zubawa lamarin ido zuwa wani lokaci, 👀👀👀👀👀 ~~~~~~~~~~~~~~~~
A 6angaren Junaid kuwa soyayyar sehrish a kullum ƙara ninkuwa take yi, bawan Allah bai da tunani daya wuce na sehrish sometimes ko isasshen bacci bai samu saboda tunanin ta, yaso ace ko chat su nayi don ya ɗebe kewarta sai dai kash a halin da ake ciki ita kanta sehrish batasan inda ta wurga wayarta ba, Saboda tsananin damuwar da take ciki yasa ta manta da wata waya ma, Aunty azmee ta lura da yanayin sehrish domin ko aiki suke wani lokacin tana firgita ita kaɗae, har tambayarta take yi ko akwai wata damuwa, amma sai tace ba komai sai in ta koma ɗaki taita kuka kamar ranta zai fita, duk ta fige ta ram_____
Ataƙaice kenan abubuwan dake faruwa acikin rayuwar waɗan nan bayin Allah, shin me zai faru nan gaba ? kuna ganin Aunty babba zata kyale su hosana ? Mai zai faru in ta sa aka zubar dasu kamar yadda tace? Wane hannu kuma kke tunanin zasu faɗa? Yaya rayuwarsu zata kasance? 😥😥😥
Shin me zai faru da sehrish in haroon ya cimma burinsa? Yaya rayuwar junaid zata kasance aranar da ya gane cewa Sehrish babban yayansu take so bashi ba?😖
ALHAMDULILLAH END OF PART 1 ______________________________________ DOMIN SAMUN CIGABAN LITTAFIN ABBAN SOJOJI PART 2, MUTUM ZAI BIYA 300 NE, VIP KUMA 700, WANDA YA SHIRYA BIYA SAI YA TUNTU6I NUMBER TA, 08103884440 KADA KU BARI ABAKU LABARI WLH 👏👏👏