Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 57

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 57

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 57: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 57. Gaba daya sun fusata,ganin suna ƙokarin zame belt ɗin…

4,042 words

Gaba daya sun fusata,ganin suna ƙokarin zame belt ɗin wandonsu don su jibgeta,Abba yayi saurin dakatar dasu"Innallaha ma'assabirin!Kubarta da Allah Shiyasan yarda zaiyi da ita,ban amince ɗaya daga cikinku Ya ta6a lafiyar jikinta ba,Azmee bata kashe mun kowa ba,Iya cuta dai ta cutar damu,Ina neman alfarma a wurinku,daku miƙata wurin hukuma su yanke mata hukuncin daya dace da ita,Sannan kuma Ina umartarku da ku hanzarta Ruguza ƙungiyarsu,Da duk wani wanda ke cikinta,Kamar yarda kakanku salahudeen yayi,haka nakeso kuma Kuyi,Kada ku raga masu,banaso daya daga cikinsu Yasha,gawawwakinsu kawai nakeson Gani,"Yana kai ƙarshen maganar,Ya juya tare da barin wurin Ya koma bedroom ɗinshi,Idanuwanshi cike tab da kwalla,a ƙopar ɗakin ya tsaya yayin da idonshi ke akan Junaid dake kwance saman gadonshi Yana ta sharar bacci abunshi,Har cikin ranshi baiso Azmee Ta kasance haka ba,Koma miye ita taja ma kanta,Ya Allah kakare mu daga aikata Aikin dana Sani,

Bayan tafiyar Abba,Ya Mu'allim Yace"Shawarar da zan baku shine,Kuyi amfani da Azmee wurin kama sauran masu aikata laifin,saboda tasan komai,Tasan inda ƙungiyarsu take Inyaso daga bisani Sai a miƙata ga hukuma,zamu tayaku da Addu'a akan Allah ya baku nasara,"

Sosai sukayi ma Ya mu'allim Godiya,domin kuwa ya basu shawara mai kyau kuma Ya taimakesu,batare da 6ata Lokaci ba,suka tasa ƙeyar Azmee zuwa Ɗakin horonsu,Tambayoyi suka shiga jero mata,tana amsa masu,In tayi kuskuren yi masu taurin kai kuwa,zazzafan Mari take sha,Anan suka samu bayanin inda Ya sayyadi Yake,Ashe baya ƙasar tun Lokacin da abu ta kashe mashi idanuwanshi,Suka fiddashi ƙasar waje,Don a duba lafiyarshi,Da wayar Azmee sukayi amfani wurin gano Duk wani mugun abu da suke aikatawa,A ranar suka shirya tsaf cikin kakin Sojojinsu gaba dayansu domin fara yaƙar ƙungiyarsu,Manya manyan makamai suka ɗauka,Sai da Abba ya fara sanya masu Albarka,Yayi masu addu'a,Mommy ma tayi masu tare da sauran Mutanan gidan Kafin Su kayi masu sallama,A tare da Azmee suka tafi Asaman Helicopter kusan guda shida Ya ɗaga dasu,

Kasa samun natsuwa su Sehrish su kayi,kowa zullumin yake yi game da tafiyarsu Babban Yaya,wurine mai matukar haɗarin gaske acikin wani ƙurmamin daji,inda suka kafa ƙungiyarsu ta matsafa,kodai su kashe ko akashe su,Allah kaɗai yasan wanda zaiyi nasara,

Abu kamar wasa har goma sha ɗayan dare basu dawo ba,babu wani labari dangane dasu,Wayoyinsu kuma duk in aka kira bata shiga,Hakan Ya ƙara tayar masu da hankalinsu,shi kanshi Abba sai daga baya ya fara danasanin turasu,Mommy kuwa tuni ta fara zubda kwalla,tsoranta kada ta rasa Ƴa'ƴanta,

A 6angaren su Sehrish kuwa,Babu wanda ya runtsa acikinsu,kwana su kayi saman darduma sunayin sallah akan Allah ya basu nasara ya kuma dawo dasu Lafiya,abu kamar wasa Tsawon kwana biyu kenan su Sgr basu dawo ba,lamarin ya fara tsoratar dasu,Gashi ba'a samun Layinsu balle asan awani hali suke Ciki,

Sai adaren Rana ta biyu ne,Allah yayi suka dawo,Sunyi nasara sai dai sunyi babban rashi na mutun ɗaya acikinsu,Irfan Allah yayi mashi rasuwa,sunji mutuwar nan kamar kamar me,tare da gawarshi suka dawo,wasu daga cikinsu kuma sun raunata sosai,Dan Fawan Allah ne yayi zai rayu,Twins kuwa sun jigata sosai,kowa Yaji ajikinshi,Nasarorin da suka samu sune sun ruguza Ƙungiyar matsafan,sun lalata masu komai,Sun kuma kashe mutanan cikinta gaba ɗayansu,don sunyi masu zuwan bazata,kuma sunci sa'a adai dai lokacin suna kan yin meeting ne,kowa Ya hallara,Hada shugaban nasu Ghali,Da taimakon Azmee suka kashe shi,Yanzu mutun ɗaya ya rage masu su kamashi Wato Ya Sayyadi,

A washe garin ranar akayi jana'izar Irfan,Abba Yafi kowa jin mutuwar nan,Abubuwa sunyi mashi yawa,Ga Junaid dake kwance yana jinya,Ga kuma fawan shima Yana ƙarkashin kulawar likitoci,

Bayan kammala Jana'izar Ifran,Batare da 6ata Lokaci ba,Sgr Ya tura Armstrong tare da wasu daga cikin sojojinshi,Suka hau jirgi zuwa ƙasar Malaysia,Don bala'e har asibitin da aka kwantar da Ya sayyadi suka Cafko shi,idanuwanshi Na manne da uban bandegi,da Alama aiki akayi mashi a wurin,Cikin jirgi suka sanyoshi,Sannan Suka dawo dashi Nigeria,har cikin gidan suka taso ƙeyarshi gaba,a garden ɗin gidan Sgr ya sanyasu suka Kwantar mashi dashi,kafin ya yanke mashi hukunci,Sai da Ya fara kiran Abusufyan tare dasu Jahad,da oummansu gaba ɗayansu suka hallara a garden ɗin, Abusufyan yace"dama saida na faɗa maka,Wannan ranar zata zo,kuma gata Allah ya nuna mun da raina da lafiyata,Gani ga kuma Yaran daka zalunta,Ga kuma mahaifiyarsu,Kaji haushin rayuwarka Sayyad,A yau ƙarshenka yazo,tun a gidan duniya zaka fara ɗanɗani raɗaɗin azaba,kafin ka koma Ga Allah," gaba ɗaya yabi ya ruɗe,jikinshi sai kerma Yake yi,daga yayi ƙoƙarin buɗe baki zai basu haƙuri,Sai Sgr ya Kai mashi naushi a kuncinshi,duk saida Ya zubar mashi da haƙoran bakinshi,Jini jaga jaga A bakinshi, "Mugu azzalumi,Ni Ko kaɗan banji tausayinka ba,Allah yaji ƙanka don nasan cewa taka ta ƙare,Allah ya ƙara nauyin ƙasa,"Abuce tayi maganar, Jahad da sehrish basu ce komai ba,Hosana dai ce Ta tofa mashi Miyau Asaman fuskarshi,bayan sun gama gaya mashi magana,Sgr Yaba sehrish umarnin ta kawo mashi tafasasshen Mai,

Jiki na rawa ta juya ta koma cikin gidan,Oummansu dasu Jahad suka bi bayanta,Bada jimawa ba ta dawo hannunta ɗauke da ƙaramar tukunya,Tafasasshen mai ne aciki sai tartsatsi yake yi, Umarni yaba Su armstrong,Su cire wandon jikinshi,Ganin haka yasa Sehrish ta ajiye man,ta watsa da gudu ta koma cikin gida gabanta na faɗuwa, Bayan sun cire wandonshi,suka yi mashi zirr,sojoji guda biyu suka tale ƙafafunshi,Abun nan da yake takama dashi yana yi ma mutane iskanci dashi,Sgr ya ɗauki tafasasshen man nan ya kwarara mashi agabanshi gaba ɗaya, Wa'iyazubillahi!Wata irin kururuwa Ya sayyadi yayi,lokacin da gabanshi ke ƙonewa,wani irin raɗaɗin azaba Ya dinga ji,Gaba ɗaya ya zauce ya gigice Ya fita hayyacinshi,

Umarni Ya basu Su ɗauke shi su kaishi can cikin ƙurmin daji,ko namun dawa sun samu abinci,A ƙarshe dae Ya sayyadi A cikin daji rayuwarshi ta ƙare,gawarshi A wulaƙance A ƙasƙance abun ba kyan gani,

Ita kuma Azmee Tare da Saratu,Jami'an ƴan sanda ne suka tafi dasu,Bayan an tattara hujjoji,Suka miƙasu Court domin Yin shari'a,A ƙarshe Aka yanke masu hukuncin zama gidan Yari,A ɗakin duhu na tsawon shekara 20,Sehrish tasha kuka,Saboda har lokacin tana son Azmee,Lokacin da aka kammala shari'ar za'a tafi dasu gidan Yari,Daƙyar aka rabasu,Sun rungume juna sosai suna kuka,ita da Sehrish,ita kam Amrish kin zuwa tayi wurin Mommynta balle ma ta rungumetan dama dakyar ta biyo su kotun,kowa baiji daɗin halin da Azmee ta jefa kanta ba,ba lalle ne lokacin da zasu fito ɗakin duhu ba,su dawo da idanuwansu ba,zaiyi wuya in basu makance ba,idan ma sun rayu kenan,'

Lokacin da Labarin mutuwar Irfan ta riski danginsu,Lokaci bai cika kwana biyu da rasuwa ba,Gidan Ya cika fam da masu zuwa yi masu jajen abunda Ya faru,Da kuma Yi masu gaisuwar rashin da suka yi,Mutane dayawa Sunyi mamakin jin cewa Azmee ce take ɗaukar fansa akan mutanan gidan,Sunyi Allah wadai da halinta,Tasha Zagi wurin jama'a don wasu da suna da halin da zasu ganta sai sun kasheta da bugu,Yanzu Alhamdulillah basu da wata sauran fargaba,NO MORE TENSION,

Kowa yayi dakyau don kanshi,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 6 na marece,A jere motoci suka dinga shararowa izuwa cikin gidan,dankara dankaran gaske,Bayan sunyi parking ɗin motocin,Mota ta farko,Wani sergent Ya fito tare da zagaya Ya buɗe gidan baya,A hankali ta sauko daga cikin motar,jikinta sanye da code lace fari,Bakowa bace face Hajiya Azeema,fuskarta ɗauke da murmushi,other side ɗin hafsat ce ta fito jikinta sanye da atampa,Ta ruƙo hand bag dinta, Motar bayansu,Ammi ce tare da Gwaggon katsina,Dr harriss ne yayi driving dinsu,Saude na a gefenshi, Daga Motarsu kuma sai Motar MG Osman,Tare da Captain adam,basu kaɗai bane a motar,Akwai Ƴan matan da suka zo dasu kyawawan gaske daga Gani ƴan uwansu ne, Motar dake bayansu Motar Captain Najeeb ce,su biyu ne aciki shi da Talal autansu na biyu,

Babu wanda yasan a ranar zasu dawo,

A lokacin gaba ɗayansu sun hallara asaman dining suna Cin dinner ɗinsu,banda mutun biyu Omar da Sgr basu kaiga dawowa daga wurin aiki ba,They're busy for work ga prepation ɗin da suke yi Na Komawa U.S tafiya ta kankama,kowa ka kalli fuskarshi daurewa kawai suke yi akwai sauran jimami,Yanzu babu Azmee sai dai Abu dasu Jahad ke girka abincin gidan,

Sehrish ta zabga uban tagumi,Bakowa take tunani ba,face Aunty azmee,Duk in oummansu Nayi serving ɗinsu abinci,Sai ta dinga tunawa da ita,

Binsu da kallo ta soma yi ɗaya bayan ɗaya,tun daga kan mommy dake ta faman jujjuya cokali acikin abincin gabanta,Abba kuwa tunda ya zauna Bai ta6a komai ba,Lemu kawai yake tasha, Su twins Da ɗan dama,Sun saki jikinsu suna cin abinci,Haka kanal yusif ma sosai yake Cin abincinshi,Irfan da jabeer still sai a hankali,Duk sun kasa sakewa saboda rashin Irfan da su kayi acikinsu,

Kallon Hosana tayi,Cinyar kaza ta ɗauko ta tura abakinta sai tauna take yi kamar akuya ta samu ciyawa,Murmushi sehrish ta ɗanyi tare da ɗan girgiza kanta,Mayar da idanuwanta tayi kan Amrish dake zaune daƙyar take tura abinci abakinta har yau ta kasa sakewa acikinsu,ɗagowa tayi suka haɗa ido Da sehrish atare suka sakarwa Juna murmushi,

Miƙewa Jahad tayi,"Where are u going"?Abusufyan ne ya tambayeta ganin ta miƙe tsaye bata kammala cin abincin ba, Sunnar dakai ta ɗanyi kafin tace"Zanje na duba jikin junaid ne" Murmushi ya saki,kafin yace"Je ki abunki,Allah yabar ƙauna,"

Kunyace ta rufe ta,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta,da sauri tabar wurin ta nufi bedroom ɗin abba,

Bayan tafiyar Jahad mommy ta mike"Zanje na duba jikin fawan,Inaso naji idan akwai abunda yake buƙata sai in kai mashi,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kama hanyar bedroom ɗinshi, Lokacin da jahad ta ƙarasa bedroom ɗin a ƙopar ɗakin ta tsaya,tare da sanya hannu ta ruke handle ɗin ƙopar,Slowly ta tura ƙopar ɗakin ta ɗan leƙa,har yanzu bawan Allah a kwance yake baisan inda kanshi yake ba,Da alama Ya samu bacci,kullum sai Ya mu'allim yazo duba shi,yanzu ya zama tamkar ɗan uwa agaresu,

A hankali take tafiya harta ƙarasa gefen gadon ta zauna,Zuba mashi ido tayi tana kallonshi,Yanzu bata da burin daya wuce taga junaid Ya dawo cikin hayyacinshi,Fargabarta kada Ya manta da soyayyarsu,

A hankali ta kwantar da kanta gefenshi,Allah ya baka Lafiya My Romeo,ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta,Unexpect Taji Saukar hannunshi acikin Sumar kanta,A firgice ta ɗago da kanta tana kallon fuskarshi,slowly ya buɗe dara daran idanuwanshi farare ƙyal akan fuskarta,La66anta na kerma Ta ambaci Sunanshi JUNAID! da mamaki akan fuskarta,Binta da ido yayi yana kallonta,Matsawa tayi saitin fuskarshi, Cike da tsantsar farin ciki ta kuma ambaton sunanshi"Junaid" Lumshe mata idanuwanshi yayi tare da sake budesu akan fuskarta,Saboda tsabar farin Ciki,Da sauri ta sauko daga saman gadon ta watsa da gudu ta fito daga ɗakin,Jin takun takalmata yajanyo hankalinsu akanta, Tunkafin ta isa ta soma magana"Abba Junaid ya farka,Ya dawo cikin hayyacinshi,"Gaba ɗaya suka miƙe Fuskar kowannansu ɗauke da tsantsar farin Ciki suke kallonta,Adai dai Lokacin Gwaggon Katsina Ta dako masu Sallama da ƙarfin gaske tana fadin"Gafara dai,Mai wuri yazo Me tabarma ya naɗe,Masu Gidan sun dawo,"

*Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*

[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋

𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤ 𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*

Koda su kayi arba dasu Ammi wani irin farin ciki ne Ya lullu6esu,Watsawa Hosana tayi da gudun gaske tana faɗin"Ga gwaggo!Ga gwaggo!"Washe baki gwaggon katsina ta soma yi"Yawwa ya'yan abusufyan ɗina,Nayi kewarku sosai,"Rungumeta hosana tayi,Tana ta faman tikar dariya,Sehrish kuwa Tana yin arba da hajiya azeema,Da gudu ta nufeta,Murmushi Hajiya azeema ta saki tare da janyota jikinta,Ta rungumeta sosai tana shafa bayanta"I really missed u My daughter,Nasan kinyi kewata sosai," ƙarasowa wurinsu Jahad tayi kaitsaye ta nufi Hafsat,wani irin farin cikine ya lullu6e hafsat ganin ta tunkarota fuskarta ɗauke da fara'a tayi tunanin har lokacin fushi suke yi da ita,Rungume juna sukayi sosai, "Wato kowa nashi ya sani ko?kun manta da kakarku,"Abba ne yayi maganar fuskarshi ɗauke da murmushi,Ya ƙarasa wurin Ammi,ta rumgume shi ajikinta,Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke,lokaci guda yaji idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla, Shafa bayanshi Ammi tayi"Nasan ban kyauta maka ba,nayi nesa dakai a lokacin da kake buƙatar kulawata,Kayi haƙuri hossein Banji daɗin abubuwan da suka faruwa ba,abun ya ta6a zuciyoyinmu"Sosai ammi tashiga tausarshi, ƙarasowa Su Kanal yusif su kayi,Abusufyan ya rungume Dr harris,Yusif kuwa Wurin Captain adam Ya nufa rungume juna su kayi,Jabeer ya rungume Mg Osman,Kowannansu fuskarshi ɗauke da murmushi,

"Mu shiga daga ciki,Kun kwaso gajiya,"abba ne yayi maganar tare da ruƙo hannun Ammi,Suka nufi cikin Falon, "sassannunku da zuwa,Ya hanya Ya gajiyar tafiya,Ya kuka baro su"?acewar abusufyan Hajiya azeema tace"Lafiyalou,duk suna gaisheku," Bayan ta ƙare maganar,Mg osman ya soma magana"ashe irfan Lokaci yayi,Allah yaji ƙanshi,Ya gafarta mashi zunubbanshi,Wlh naji mutuwarshi"yakai ƙarshen maganar tare da curo hanky daga aljihunshi Ya rufe fuskarshi,jikin kowa dake a wurin yayi sanyi, Talal tuni ya fara zubda kwalla"Abba ashe haka abu ya faru?munyi babban rashin na irfan acikinmu,Allah yasa ƙarshen wahalarshi kenan,Allah Yaji ƙanshi," "Ameen ameen,"daƙyar abba yake amsa masu saboda yanayin da suka jefa shi,Dama dauriya ce kawai yake yi, "Yaya hossein,Ya haƙurin rashin da mu kayi"?hajiya azeema ce tayi maganar yayin da take kallonshi,daƙyar ya iya amsa mata,Kowa dake a wurin sai da yayi masu gaisuwa,Hatta Ƴan matan da Ammi tazo dasu, Shigowa palourn Abu tayi hannunta ruƙe da faffaɗan tray,Cups ne asama mai ɗauke da Lemu mai sanyi,sai da ta fara yi masu sannu da zuwa,kafin ta soma ƙoƙarin raba masu abunshan,. Gyaran Murya abusufyan yayi mata,Da sauri takai idanuwanta kanshi,da ido yayi mata nuni da Ammi alamar ta fara miƙa mata,Murmushi tasaki kafin ta nufi sofa ɗin da ammi ke zaune tare da Abba,cikin girmamawa ta gaishe da ita"Sannunku da zuwa Ammi,Ya gajiyar tafiya," "Alhamdullillah,"tayi maganar tare da miƙa hannu ta kar6i cup din da abu ke miƙa mata, "Ince ko Mahaifiyar ƴan ukun nan ce"?tayi tambayar tana nuna su jahad dake zaune wurin gwaggon katsina, Abba ne ya bata amsa da cewa"Itace oummansu" Murmushi ammi tayi tare da kallon abusufyan,A hanzarce ya kawar da kanshi gefe yana murmushi ƙasa ƙasa, "Alhamdulillah Naji daɗi sosai,mun samu ƙaruwa acikin zuri'armu Allah ya ƙara hada kawunanmu,"atare suka amsa mata da ameen Kasa haƙuri Talal Yayi"Abba Ya jikin junaid da fawan?na kasa samun natsuwa,Burina in sanyasu acikin idanuwana na," Tunkan yakai ƙarshen maganar Gwaggwon katsina tace"Allah sarki junaidu bawan Allah,An ji jaki,Amma Allah wadaran me hali irin na Azmee,Matar nan ta cuce mu,Munafuka mai zuciya irinta Kafiran farko,Yadda kasan A jahiliya period aka haife ta dama ni banyarda da ita ba,Shisshiginta yayi yawa,Sumumu kasau macijin sari ka noƙe.....Wannan matar tafi bomb bala'e,Wlh bazamu yafe mata ba,Allah ya ɗebe mata sauran albarkar dake......"bata ƙarasa maganarba,Abbba yayi hanzarin cewa"Gwaggo,Dan Allah adaina tuna abunda ya wuce,Azmee yanzu bata atare damu,Tana can prison tana kar6ar sakamakon abunda ta aikata, Tunkan yakai ƙarshen maganar tace"Haba hossein,Ai ni banso kuka kaita prison ba,So nayi ku kulleta acikin akurki irin na kaji har mu dawo,Wlh data yaba ma aya zaƙinta,Azmee bata kyauta mana ba,Kaga fa matar nan kamar tafi kowa tsoron Allah,Kullum Zaka ganta cikin zumbulelen hijabi kamar matar liman,Hannunta ruƙe da zungureran cazbi kamar duka kenan"cika da takaici tayi maganar,. "Wlh ni dama banyarda da ita ba,shiyasa tun farko banso Yaya hossein Ya bata rainon junaid ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,babu yarda zamuyi,Allah Ya kyauta gaba,Yanzu sai musan dawa zamu yarda,"Azeema ce tayi maganar ranta a 6ace, "Ae azmee ta bamu mamaki,Ta koya mana hankali wlh,ɗan adam ba abun yarda bane,Mutun mugun icce ne,duk irin halarcin da akayi mata tarasa dame zata saka magana sai da wannan,"acewar abba, Gyaran Murya ammi tayi kafin ta soma magana a tsanake, "Kuskure ne tun farko an riga da an tabka,sai dai fatan Allah ya tsare gaba,bai kamata kuna tada maganartaba,tunda yanzu babu ita,amma duk da haka ina me ƙara jan hankalinku Akan ku daina saurin yarda da mutane,musamman bare a zamanin da muke ciki Na jikinka ma ana iya haɗa baki dashi a cutar dakai balle kuma wanda baku haɗa komai dashi ba,Iya cuta dai Azmee ta cutar damu,Amma mu gode ma Allah da bata kaiga yi mana illa ba,Don da taso da tuni ta jima da halaka wasu acikin gidan nan,Allah ne ya tsare mana ku,"bayan takai ƙarshen maganar,ta ɗan sauke ajiyar zuciya kafin taci gaba da cewa"Yanzu a wani Hali jikokina suke ciki?Fawan da junaid,Ya jikin nasu,"

"Alhamdulillah suna samun sauƙi sosai,Junaid yana kwance a bedroom ɗinta fawan kuma yana a dakinshi"miƙewa tayi tare da nufar ɗakin Talal ma Yabi bayanta,Gaba ɗayansu ma suka miƙe domin zuwa duba jikin nashi,Lokacin da suka shiga ɗakin,A zaune suka same shi,Ya sauko ƙafafunshi ƙasa,Da alama so yake yayi tafiya,jin an buɗe ƙopar ɗakin Yasa ya ɗago da manyan idanuwanshi yana kallonsu, Farin ciki ne Ya lullu6esu,Musamman Abba,jiki na rawa ya ƙarasa gefenshi ya zauna,rungumoshi yayi xuwa jikinshi,Yana shafa bayanshi, "Alhamdulillah,Da alama Jikin nashi yayi sauƙi,ba kamar yarda aka bani labari ba,"acewar ammi fuskarta ɗauke da murmushi, Zuƙunnawa Talal Yayi saitin fuskarshi"Junaid ɗan uwana,Ya jikin naka"?zuba mashi ido junaid yayi yana kallonshi batare da yace uffan ba,Yaƙi buɗe baki yayi magana,Sae dai kallonsu da yake yi ɗaya bayan ɗaya kamar baison su ba, "Allah yasa baiyi loosing memory ɗinshi ba,Naga ko magana ma ya gaza yi mana Sai dai yabi mu da ido,"acewar captain adam, Osman yace"nima abunda nake tunani kenan,Junaid dana sani kullum fuskarshi ɗauke da murmushi kamar Gonar auduga" "Kada ku damu,Yanzu ya fara jin sauƙi,Nasan zuwa gobe zai warware in sha Allah,shikaɗai yasan me yake ji acikin zuciyarshi,"yayi maganar yayin da yake cigaba da shafa sumar kanshi, Kowa sai da yayi mashi yajiki,Kafin suka Yi mashi sallama suka koma Falon,basu jimawa da dawowa ba,Mommy ta fito hannunta ruƙe dana Fawan,Daga shi sai short ajikinshi,ba ƙaramin jiki yaji ba,Amma yanzu da sauƙi jikin nashi, Tunkan su ƙaraso,Talal da najeeb suka miƙe,Da sauri suka ƙarasa Wurinshi,Suna yi mashi yaji,murmushi ya sakar masu"Alhamdulillah Am really glad to see you,nayi missing ɗinku sosai," Rungumeshi su kayi,Kafin suka ruƙo hannunshi zuwa cikin falon,Saman Sofa suka zauna,Kowa ya soma Yi mashi Ya jiki,fuskarshi asake yake amsa masu,a tsaye mommy ta gaisa dasu,Kafin ta nufi kitchen donta shirya masu abunda zasu ci,Abu ta samu acikin kitchen ɗin tana shirya masu abinci,Taimaka mata tayi suka shirya abincin atare,

Abba kuwa still Yana a wurin babynsa ya ƙankameshi ajikinshi,ɗago da junaid yayi daga jikinshi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi "Junaid Anya lafiya kuwa?Sai dai kabi kowa da ido kamar baka sanmu ba,dan Allah kayi mun magana,Kona ji sanyi acikin zuciyata, Zuru yayi mashi sam yaƙi ya tanka mashi,Duk ya shiga damuwa,Jan kumatunshi yayi"Haba babyn abbansa,Ko murmushi ne to kayi mun," Still bai tanka mashi ba,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba, "Dan Allah junaid,ka kwantarmun da hankalina mana,duk na damu da rashinka,Nasan Nayi maka laifi amma dan Allah Kayi hakuri kaji My baby Boy,"hada ɗan murmushinshi yayi maganar,junaid kuwa sai binshi da ido yake yi, "Me kake son ci in kawo maka"?yayi tambayar yana shafa sumar kanshi, Sai lokacin Junaid ya buɗe bakinshi,Yana nuna mashi teeth ɗinsa,Sunyi dauɗa sosai, Murmushi Abba yayi"Saboda teeth ɗinka sunyi datti shine kaƙi yi mun magana,to menene aciki"sunnar da kansa ƙasa yayi, Ruko hannunshi Abba yayi tare da miƙar dashi tsaye,Toilet ya shiga dashi,A gaban sink suka tsaya,Brush ya ɗauko bayan ya matsa maclean asama,Yace"Ha bakinka inyi maka brush ɗin dakaina,"buɗe bakinshi yayi,Abba ya tura brush ɗin cikin mouth ɗinsa,a tsanake yake goge mashi hakoran,Yayin da idanuwansu ke kallon cikin na juna, Calmly Abba ya soma magana"Nasan sunyi hurting ɗinka sosai,But pls we should forget about the past,Komai ya wuce,babu wanda Allah baya jarabtarshi junaid,Ka gode ma Allah da basu yi maka illa sosai ba,Nasan ka shiga damuwa ne sosai saboda rashina dakuma ƴan uwanka,ka rayu atare da wasu mugaye marasa imani,Ka tsorata sosai,Shiyasa harka zauce,Amma Yanzu Alhamdullillah,Jiki yayi kyau,"ya ƙarasa maganar tare da kunna tap,zuƙunnowa junaid yayi,Abba ya tarfa hannunshi Ya ɗebo ruwan yana kuskure mashi bakinshi,Bayan ya kammala kuskure mashi bakin,Ya wanke mashi fuskarshi,Kamar wani ƙaramin yaro haka Yake treating dinsa, Hannunsu ruƙe dana juna suka fito daga cikin toilet ɗin,Zaunar dashi yayi gefen gadon, "Yanzu fadamun me kakeson Ci," Daƙyar ya iya cewa"Abbana," Murmushi abba ya saki tare dacewa"Na'am babyn abbansa,"murmushi gefen fuska junaid ya ɗan saki, "Repeat it pls," Sake ambaton sunanshi yayi kamar yarda ya buƙata"Abbana," Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarshi"Na'am sanyin idaniyata,tell me me zaka ci,in kawo maka," Yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana Jahad ta turo ƙopar dakin,Sam batayi tsammanin Abba na aciki ba,da sauri ta juya zata koma,Abba yayi saurin dakatar da ita"Ina zuwa"?kunyace ta rufeta,Har takasa juyowa tayi magana, Murmushi abba ya saki tare da cewa"Yana jin yunwa ki kawo mashi abunda zaisa ma cikinsa," "Toh abba,"ta amsa tare da buɗe ƙopar ta fuce, Mayar da idanuwanshi yayi kan fuskar junaid"Faɗamun har yanzu kana sonta insa a ɗaura maku aure," Sunnar da kanshi ƙasa yayi batare daya tanka mashi ba,ya lura da canzawar da junaid yayi dama Ya mu'allim yace Ba lallai ne ya dawo yarda suka sonshi ba,tunda yanzu babu sihiri ajikinshi,Ya dawo Normal yadda Allah ya halicce shi,Wato Namijin gaske, Cike da zolaya abba yace"Oh ni junaid,Allah yasa ba irin rafayet bane,naga magana ma wuya take yi maka,Fuskarka kuma a ɗaure babu annuri," Turo ƙopar jahad tayi hannunta ɗauke da tray ɗan madaidaci,Food stuffs ne ta dauko asaman shi, Mikewa Abba yayi"Yawwa My daughter,zoki zauna kusa dashi,ki taimaka mashi yaci abincin,Ni bari na koma wurinsu Ammi,"Ta amsa mashi da toh,Juyawa abba yayi yabar masu ɗakin,

Tunda ta shigo junaid bai ɗago ya kalleta ba,tuni tasha jinin jikinta,Yadda kasan ba wannan junaid ɗin ba,mai yawan fara'a ga surutu kamar aku,

Ajiye tray ɗin tayi saman table,ta janyoshi izuwa gabanshi, "Me zan zuba maka,"daƙyar ya iya buɗe bakinshi ya furta"Cornflakes nakeso," "Bari naje na haɗa maka,yanzu zan dawo,"cike da kulawa tayi maganar,A hanzarce ta fuce daga ɗakin, After some minutes,Ta dawo hannunta ɗauke da Cup ta sanya mashi spoon aciki,Gefenshi ta zauna tare da miƙa mashi cup ɗin,ganin yadda yatsun hannunshi ke kerma yasa tace"In baka abaki," ɗaga mata kai yayi alamar Eh,ɗaukar cokalin tayi a tsanake ta soma ɗebo cornflakes ɗin tana tura mashi abaki yana sha,Natsuwa tayi tana kallon lips ɗinsa sunyi red sosai,yadda kasan na jinjiri,ba ƙaramin missing ɗinshi tayi ba,gashi yanzu ya sauya mata,ko son kallonta ma bayayi,balle aje ga magana,. "Junaid"da wata irin kasalalliyar murya ta ambaci sunanshi, ɗago da idanuwanshi yayi akanta batare daya amsa mata ba,murmushi ta ɗan sakar mashi tare da cewa"Ashe da rabon zan sake sanyaka acikin idanuwana?nashiga tashin hankali sosai lokacin da motar nan ta danne motarka,duk a tunanina kana acikin motar,har zaucewa saida nayi,Allah ne yayi zan rayu a lokacin,mun shiga tashin hankali sosai,Nidasu Ya omar...."tunda ta fara zuba yake kallon bakinta,Labari ta soma bashi na abunda ya faru bayan mutuwarshi har zuwa bayyanarshi,hada ƴan hawayenta, "Da ace narasa ka a wannan lokacin bana tunanin zan iya son wani ɗa namiji,zan ƙare rayuwata ne batare dana auri kowa ba," Sai da takai ƙarshen maganarta,Tukunna yace"WHO ARE YOU"? Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rass kakeji!Waro ido waje tayi a tsananin firgice take kallonshi, Hankalinta a matuƙar tashe tace"Junaid!Kana nufin baka sanni ba?i know u are just kidding me" "Pls who are you"?Ya kuma tambayarya again, Abun yayi mugun ɗaure mata kai, "Junaid nifa ce,Jahad ɗinka,Your juliet," Girgiza kanshi yayi"Ni bansanki ba,Bansan wacece ke ba,kin zauna sai zuba kike yi mun kamar radio," Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa Ya nufi cikin toilet ya shige,tare da jan kopar ya datse ta,

Fashewa tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,yana acikin toilet yana jiyo shessheƙar kukanta,A jikin ƙopar ya tsaya can kuma ya buɗe ƙopar yana leƙenta,daga zarar yaga tana ƙoƙarin juyowa sai ya garƙame ƙopar,in ta kawar dakai tana shessheƙar kuka sai ya buɗe yana cigaba da kallonta,miƙewa tayi da ƙyar ta buɗe ɗakin ta fuce,Ajiyar zuciya ya sauke tare da buɗe ƙopar ya fito,Saman gadon ya koma ya zauna,fuskarshi ɗauke da ƙayataccen murmushin side face,

Lokacin da jahad ta fito daga ɗakin Abban,A falo ta samu Ammi tare da matasan gidan dasu Abba da daddynsu,Sae nasiha take yi masu,tare da yi masu addu'a suna Amsa mata da Ameen,

Corridor ɗin ɗakinsu ta shige,a ƙopar ɗakin ta tsaya tare da sanya hannayenta biyu tana goge hawayenta,kafin ta tura ƙopar ɗakin ta shige daga ciki,a kwance ta samu hosana tana ta sharar bacci,Oummansu kuma tana a zaune gefen gadon hannunta ruƙe da qur'ani tana karantawa,jiki asanyaye Jahad ta ƙarasa saman gadon ta haye tare da rufe idanuwanta,Allah kaɗai yasan yarda take ji acikin zuciyarta,

*Boss Bature*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull