Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 58

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 58

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 58: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 58. A 6angaren Sehrish kuwa,Yanzu sun koma kwana bedroom ɗin…

4,320 words

A 6angaren Sehrish kuwa,Yanzu sun koma kwana bedroom ɗin Azmee ita da Amrish,taso suyi magana da mommy azeema amma lokacin da taje ɗakin da ta sauke bacci ta samu tana yi,da alama ta gaji sosai,ba don taso ba,ta dawo ɗaki,Amrish ta samu a tsaye tana ta faman zarya ta kasa runtsawa,da alama tana zullumin wani abu, "Lafiyarki kuwa?Meyasa baki fita waje ba kun gaisa da ƴan uwanmu da suka dawo," Fuskarta ɗauke da matsananciyar damu tace"Tsoron haɗuwa nake yi dasu,gani nake kamar in suka ganni zasu kore ni ne in suka ji ko ni wacece," "Kina da matsala Amrish,nafa ce maki ki saki jikinki,Family ɗinmu ba kamar yarda kikayi tsammani bane,suna da mutunci sosai,kowa zai kar6eki hannu bibbiyu ne," "Nidai kawai ina fargaba ne,"ta ƙarasa maganar tare da komawa gefen gadon ta zauna, Cigaba da magana tayi"Har yanzu ina jin raɗaɗin abunda dangina suka aikata,abun yana ƙonamun rai duk in na tuna,Ina jin kunya sosai,Yanzu bani da kowa,nikaɗai na rage acikinsu,Labarin rayuwata sam babu daɗin ji,Yanzu wata rana idan nayi aure na haihu ƴa'ƴana zasu tambayeni game da dangina me zance masu?Idan ma ban faɗa masu fa dole suji a wurin mutane,koda yake nasan ma babu wanda zai aure ni,bakowa ne zaiso ya haɗa zuri'a dani ba,saboda gudun kada ƴa'ƴanshi su taso gur6atattu....."daƙyar takai ƙarshen maganarta,hawaye sharkaf Akan fuskarta, Zama gefenta sehrish tayi tare da dafa kafadarta"in sha Allah hakan ma bazai ta6a faruwa ba Amrish!Ki manta da duk wani abu daya faru a rayuwarki,ki manta da wasu dangi dakike dasu,Family ɗina sun zama naki,Miji kuma in sha Allah kin samu,muda muke da Zaratan samari,Kika sani ko ɗaya daga cikinsu wani yayi Wuff dake..."duk da tasan ba abu bane maiyuyuwa ba sai da ta ɗanyi murmushi kalaman sehrish sun ɗan sanyaya mata zuciya, "Fadamun babu wanda ya kwanta maki rai acikinsu,Yanzun nan inje in sanarwa Abba,In aka tashi aurensu Ya omar a haɗa da naki" Murmushi amrish ta saki batare da tace komai ba "Kinsan fa muna da gagarumin biki a cikin gidan nan,Abba yace kowa sai ya ɗaura mashi aure,Ran nan najisu suna tattaunawa da daddy,Kuma kinsan wani abun farin ciki,Yawancin matasan gidan nan duk basu kula ƴan mata,abba yace duk wanda bai da budurwa,Zai haɗashi da ɗaya daga cikin ƴa'ƴan abokanansa ne,ina saran kema Abba zai haɗaki da wani ne acikinsu,Ya kike gani idan Yaya yusif ya aure ki"?Tayi tambayar tana kallonta,Yau ta dage sai zuba takeyi mata,duk don saboda farin cikinta, Murmushi ta ɗan saki Still bata tanka mata ba, "Ko baki son shi"? Sai lokacin amrish ta tanka mata"idan ina sonshi,Shi yana sona ne? "Kuma fa haka ne,Ae ko bashi ba,akwai su Yaya fawan ga twins ga Yaya adam shima fa ya haɗu," "Sehrish ni yanzu ba soyayya bace damuwata ba"tayi maganar a yayin da take gyara kwanciyarta saman gadon, "Are u missing someone"? ɗaga mata gira tayi alamar eh,kafin tace"Bansan a wani hali ya haroon yake ciki ba,bawan Allah baida kowa mu kaɗai muke rage,Ni nasamu dangin da zan rayuwa cikinsu,Shi kuma fa?wazai kula da rayuwarshi?tuni hawaye sun wanke mata fuskarta, Ita kanta Serish ta damu sosai akan Haroon,tun lokacin da suka ji cewa ba yin kanshi bane, Jinjina kai ta ɗanyi kafin tace"In sha Allah,zan yi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin nayi magana da daddy akan su nemo shi,duk da ina fargabar in tunkareshi da maganar....."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar, Kafin taci gaba da cewa"inaso na nemi alfarma a wurin Yaya rafayet,amma nasan daƙyar yayi mun" "Wata alfarma kenan"?Amrish tayi tambayar tana kallonta, "Hukuncin da aka yankewa Aunty azmee yayi tsauri sosai,a ɗakin duhu aka kaisu,zaiyi wuya suyi watanni idanuwansu basu raunata ba,sun ƙuntata sosai,zuciyarsu ma zata iya bugawa su mutu......" "Sehrish ashe baki da hankali?duk girman zunubin da suka aikata maku a haka har kike tunanin nema masu sassauci,Wlh karma ki fara,Ni hukuncin da akayi masu yayi mun kaɗan,So nayi da aka kaisu court nan take alƙali ya yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya"rai a6ace take magana,Sehrish kuwa sakin baki tayi galala tana kallonta,Sai kace ba akan mahaifiyarta take magana ba,sai da takai ƙarshen maganarta sannan sehrish tace"Kece baki da hankali Amrish,Iyayenki fa nake nema ma sassauci,Bawai ina nufin su fito daga prison ba,Inaso ne a fito dasu daga wannan ɗakin duhun, sannan arage shekarun da aka sanya masu sunyi yawa,abunda nakeso ki gane shine,Basu kashe mana kowa ba,Zunubin da suka aikata tsakaninsu da Allah ne,Kuma Allah gafurin rahim ne" Wani irin kallo Amrish ke yi mata, a ƙarshe ma saita juya mata ƙeya,tasanya pillow ta tsoshe kunnuwanta,

Dariya sehrish tayi tare da kai hannu ta dunguri kan Amrish"kar Allah yasa ki ji,"miƙewa tayi daga zaunan da take gefen gadon,ta nufi toilet ta shige, Shigarta keda wuya,Wayarta dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,Amrish ce ta ɗauki wayar tare da duba mai kiran naga *My Boss Man* shine sunan da ta gani akan screen ɗin wayar,bata ɗaga kiran ba,harya katse,after one minute Text message ya shigo cikin wayar,Hannu tasa ta janyo message ɗin ya buɗe,ta soma karantawa, "Am on my way,"shine abunda ya rubuto mata,murmushi amrish tasaki,duk da batasan saƙon wanene ba,Amma tana da tabbacin cewa Yana da kusanci da sehrish sosai,"mayar da wayar tayi saman drawer ta ajiye, "Ko meyasa take yawan yin wankan dare,Oho"tayi maganar tana murmushi,within mins bacci yayi awon gaba da ita,

Lokacin da Sehrish ta fito ɗaure da towel a ƙirjinta,wall clock ta fara kallo ƙarfe 12 na dare,Sgr ya sanar da ita cewa daga yau ya gama zuwa aiki,cos aikinshi Ya ƙare a nigeria,zuwa gobe za'a basu lambar yabo,Sannan za'a ƙara ma matasan gidan matsayi wurin aikinsu sakamon Namijin ƙoƙarin da sukayi wurin kawo ƙarshen miyagun da suka addabi ƙasar,

Acikin month ɗin da muke ciki,Za'a ɗaura aurensu Omar kafin su wuce U.S,duk in ta tuna zai tafi wani iri take ji acikin zuciyarta,ba don taso ba,Amma taci alwashin bazata ta6a binshi U.S ba,kuma bazata ta6a neman ya tafi da ita ba,ko ta nemi soyayyarshi ba,ta lura ba sonta yake yi ba,yana yin amfani da itane don ya biya buƙatarshi kawai,in kuwa har hakane baisan darajarta ba, Jiki asanyaye ta zauna gaban mirror,tajima a haka kafin ta ɗauko handryer,Ta jonata ajikin socket,Nan take iska ta soma busowa buuuu da ƙarfin gaske,Busar da gashin kanta taci gaba da yi,Yanzu tsayin gashinta ya dawo fiye dana da,har waist ɗinta,Ga cikowar da yayi,daga gaban goshinta kuwa wani kwantaccen gashi ne wanda ya ƙarama fuskarta kyau,bayan ta kammala busar da gashin nata,ta shafe ko'ina na jikinta da waɗannan mayukan da aunty Azeema ta bata,Bayan ta kammala,Light make up tayi akan fuskarta,powder tasha fa,ta murza man baki,har wani ƙyalli lips ɗinta keyi, Miƙewa tayi daga gaban mirror ɗin ta koma wurin wadrobe ɗinsu,wata matsiyaciyar baby doll ta ɗauko,Shara shara wadda da ita da babu duk ɗaya ne,net ne kawai ajikin rigar,black color kana hangen komai muraran A bayyane,Iya guiwa rigar ta tsaya mata,komawa tayi gaban mirror ta ɗauki turarurrukan nan da hajiya azeema ta bata,tabi ko'ina ta feshe wani irin shu'umin ƙamshine ke fita daga jikinta,hatta Amrish dake bacci sai da turaren nan yakai mata karo,

Ribbom ta ɗauko,nan fa ta soma kiciniyar ɗaure sumar kanta,yayi yawa sosai gashin,sai tasha wahalar tattare sumar zata ɗaure,gashin Ya kubce mata,tuni ta fara haɗa gumi,tana cikin yin damben ɗaure gashin kanta,Tajiyo sautin shigowar motocinsu,

A jere suka shararo da gudu izuwa cikin gidan,Bayan sunyi parking ɗin Motocin Amstrong Ya buɗe murfin motar,Tare da zagayawa ya buɗe mashi,saukowa yayi daga cikin motar,Jikinshi na sanye da Army trouser,Light green Shirt,ta ɗame jikinshi sosai,Sumar kanshi kuwa ya ɗaureta a bayanshi, Fitowa Major yayi,Ya buɗe wa Marshal Motar ya fito,kaya kala ɗayane ajikinsu, "Sir,muna ƙara tayaku murna akan nasarorin da kuka samu,"Mojar ne yayi maganar, "Duk wata nasara da muka samu,Da taimakon Allah da kuma taimakonku,muna Alfahari daku,Kuma in sha Allah,Da zarar mun koma U.S Za'a ƙarama kowannanku Matsayi,then there's special gift da muka shirya maku,Bazata kawai zamuyi maku,"Omar ne yayi maganar fuskarshi ɗauke da murmushi, "Sir,Ni banason a ƙara mun matsayin aikina,Saboda banason na daina aiki a ƙarƙashinka,Na saba dakai sosai,kyautatawar da kake yi min yasa bana son rabuwa dakai,nafiso koda yaushe na kasance a ƙarƙashinka,"major nakai ƙarshen maganarshi,Amstrong ya ɗaura da cewa"Nikaina Sir banason muƙamin da za'a bani,indai zaisa nadaina aiki a ƙarƙashi Sgr ne" ɗagowa Sgr yayi tare da kallonshi Ya ɗan jefe mashi harara,Dama Yaji ma yana son a ƙara mashi matsayi amma ya kafe akan shi bazai daina driving ɗinshi ba,Sun shaƙu sosai,tun suna 20years a duniya Allah ya haɗa jininsu,Hasalima Laifi Amstrong yayi aka kamashi da nufin a hukunta,Sgr shine yasa aka sake shi,Sannan yasa Shi yi mashi alƙawarin bazai Ƙara aikata laifin ba,tundaga wannan lokacin Yayi ma Uncle Donald magana aka sama mashi Aiki ya fara kar6ar training,gashi yanzu ya mai dashi mutun,Babu abunda amstrong bai mallaka ba,Aure ne kawai baiyi ba,Shima ɗin saboda Sgr baiyi ba,Dashi Yake koyi Hatta gyaran gashin Sgr irinshi ne akan Amstrong,kamar yarda Amstrong yake da Sgr haka Major Yake da Omar,Abokan Juna ne na kut da kut, "Whether u like it or not,dole ku kar6i muƙamin da za'a baku,"ya ƙarasa kamar tare da ruƙo hannun Omar suka wuce cikin gidan,

Lokacin da suka shiga main palour babu kowa,Da alama mutanan gidan duk sunyi bacci,Hannunsu ruƙe dana juna suka haura upstairs daga bisani kowa Ya nufi part ɗinsa bayan sunyi sallama da juna,"

Agajiye ya faɗa bedroom ɗinshi,Ko'ina an gyara shi tsaf Sae ma wani daddaɗan ƙamshi dake tashi,tsaftar sehrish ba ƙaramin burgeshi take yi ba,Yana son mutun me tsafta da son ƙamshi,kasancewar shi ma'abocin Son ƙamshine shiyasa koda Yaushe zaka ji daddaɗan ƙamshi ajikinshi,

Ko takalman ƙafarshi bai kaiga cirewa ba,Ya faɗa saman gadon saboda wani irin bacci dake fisgarshi,adai dai wannan Lokacin Sehrish ta shigo palourn jikinta sanye da dogon hijabi mai hannu,Ta ruƙo tray,a ƙopar bedroom ɗinshi ta tsaya tare da yi mashi sallama,shiru bai amsa mata ba,

Sai da ta shiga cikin bedroom ɗin tayi arba dashi baje saman gadon yana ta sharar bacci abunsa,cikin sanɗa ta ƙarasa gaban table ta sauke trayn hannunta,lalla6awa tayi zuwa saman gadon ta haye,Cire hijabin jikinta tayi tare da ajiye shi gefe ɗaya,ƙafarshi ta ruƙo ta soma kwance igiyoyin takalminshi,ƙasa ta ajiye shi kafin ta cire na ɗayan ƙafar shima ta sauke shi ƙasa,duk yana jin motsinta ƙasa ƙasa dayake baccin nashi baiyi nisa ba,Moving tayi zuwa saitin fuskarshi,Kwanciyar rubda ciki yayi ya danne hannunsa ɗaya,sehrish da karanbani sai ta fara ƙoƙarin curo hannunshi daya danne,da ƙarfi ta ruko hannun tana janyoshi shi,wani irin gumi ta haɗa kamar ba'a kunna A.c a ɗakin ba,daƙyar ta samu ta curo hannun aikuwa tana zare shi gaba ɗaya Sgr ya gangara zai faɗa ƙasan gadon,A gigice tabishi ta ruƙoshi sosai tana ƙoƙarin karkato dashi donya dawo daidai,Aikuwa gaba ɗaya ƙarfinshi ya rinjayeta,ɗungurugum daga ita harshi suka ƙundumo ƙasa,ji kake timmmmmmmm,

Saboda buguwar da kanshi yayi har sai da ya furta"Assh,"a ruɗe sehrish ta ɗago da kanta tana kallon fuskarshi gaba ɗaya tana asaman jikinshi,Sai faman zazzare idanuwanta takeyi,cike da fargabar abunda zai biyo baya,almost 3 mins kafin ya soma ƙoƙarin buɗe blue eyes ɗinshi masu ɗauke da bacci har launinsu ya canza,biji biji ya fara ganin kafin su washe a kan fuskarsa,abun ya ɗaure mashi kai,ganin ya soma motsa lips ɗinsa alamar zaiyi magana,Saboda tsabar ruɗu batasan lokacin data sanya tafin hannunta asaman la66ansa ba,ta toshe mashi bakin don kar yayi mata faɗa,hakan da tayi ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,ƙarfin hali,Tayi silar jefoshi ƙasa kanshi ya bugu sosai,Yanzu kuma ta hana shi yin magana don kar yayi mata faɗa,hada wani zare mashi ido duk don karya ce zai hukuntata,

Daddaɗan ƙamshin turarenta ne ya fara kai mashi karo,har wani shaƙewa yayi,Calmly yake bin kyakkyawar fuskarta da kallo,Man lips ɗin data shafa ba ƙaramin kyau yayi mashi ba,lumshe idanuwanshi ya ɗanyi slowly ya kuma buɗesu asaman wuyanta har izuwa ƙirjinta dake cike tab ga twins ɗin nan nata masu fusgarshi kaitsaye,sai lokacin ya lura da babydoll ɗin dake jikinta shara shara,hatta pant ɗinta yana kallonshi ta ciki,Ya jima yana bin surar jikinta da kallo kafin ya mayar da eyes ɗinshi kan Boobs ɗinta cos he needs it more than everything now,still bata buɗe mashi small mouth ɗinsa ba,Shi kuma ya kasa janyen hannunta daga saman bakinsa,Ƙamshin turarenta ya gama jefa cikin wani irin yanayi mara misaltuwa,kasala duk ta rufe shi, Jikinta sae kerma yake yi,tuni zufa ta wanke mata fuskarta,duk don saboda tsoron hukuncin da zaiyi mata,

Muryarta na kerma ta soma magana"Am sorry ya Rafayet,wlh kuskure ne,ba da son raina ba,Nayi ƙoƙarin na gyara maka kwanciyarka ne,naga kayi rubda ciki,also ka danne hannunka zai iya hurting dinka shine nayi ƙoƙarin in cire hannun bansan ya akai ba,sai dai kawai naganmu mun faɗo ƙasa........"daƙyar ta ƙarasa maganar,ganin irin kallon da yake yi mata,tsit tayi tana faman mazurai,

Unexpected taji saukar hannayenshi asaman bayanta,ƙafafuwanshi ya aza asaman nata,ya danne su sosai,ta yarda bazata iya tsere mashi ba,a hankali ya soma zare ribbom ɗin data ɗaure gashin kanta dashi,dama daƙyar ta samu ta ɗaureshi,Warware shi yayi nan take gashin ya tarwatse gaba ɗaya ya rufe fuskokinsu su,yayi mashi rumfa,wani irin ƙamshi ke fita daga jikin gashin mai daɗin gaske,sosai ya shiga shaƙar ƙamshin gashinta har wani lumshe idanuwanshi yake yi kamar mai jin bacci,Sehrish kuwa har lokacin taƙi janye tafin hannunta daga saman bakinsa,sucking ɗin fatar tafin hannun nata ya soma yi,tana jin motsin tongue dinsa,ba ƙaramar kasala ya jefata ba,

"Ya rafayet"ta ambaci sunanshi cikin sanyayyiyar muryarta, "Ka yafe mun?"sam ta manta cewa ta rufe mashi bakinshi babu halin ya bata amsa,shi kaɗai yasan yarda yake jinta acikin zuciyarshi,tana yunƙurin buɗe baki ta ƙara magana,Ba zato ba tsammani taji shigar hannunshi cikin pant ɗinta,a gigice ta saki bakinshi tana ƙoƙarin guduwa,tighting ɗinta yayi sosai ta hanyar danneta da yayi da ƙafafunshi tamkar ya ɗaureta da igiya,damƙo neck ɗinta yayi azafafe ya haɗa bakinsu wuri guda tamkar zai cinye mata lips ɗinta,Hot kissing ya shiga bata a haukace,duk tabi ta ruɗe,har time ɗin bai daina wasa da hannunshi cikin pant ɗinta ba,ƙoƙarin zaucewa takeyi ,da iya ƙarfinshi na ƙarshen ya ɗago da ita,gaba ɗaya ya dauketa izuwa saman katafaren gadonshi ya kwantar da ita,blacket ɗinsa ya janyo ya rufe su aciki,baka iya jin sauti komai sai sautin gurnanin da yake yi,kura ta samu nama,almost 30 mins kafin ya rabu da ita,ba don yaso ba,wani irin bacci ne ya ɗaukesu,rungume da juna,a ƙankame kamar wani yace zai rabasu,

Wuraren sallar asuba,ya farka daga bacci,tunkafin ya buɗe idanuwashi ya soma shafa gefenshi don yaji in tana a kusa dashi,bai sameta ba,sai dai pillow ya damƙo,kasala duk ta baibayeshi daƙyar ya iya miƙewa zaune,daga shi sae short ajikinshi,wurga eye balls ɗinshi yayi kan trouser ɗinshi daya cire saman gadon tare da Shirt dinsa Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da zuro kafafunshi ƙasa,wata irin yunwace yake ji,kayan abincin data kawo mashi jiya duk sunyi sanyi,An sha romance an manta da ciki, Saukowa yayi daga saman gadon Ya faɗa toilet,Yaja kopa ya rufe,

After some minutes Ya fito jikinshi sanye da rigar wanka"bathrobe"hannunshi ruƙe da short towel yana tsane sumar kanshi,agaban mirror Ya tsaya yana gyara jikinshi,

Yana ƙoƙarin miƙa hannu ya ɗauki kwalbar turarensa,Unexpected Idanuwanshi suka sauka kan Farar paper ɗin dake ajiye gaban mirror ɗin tare da Biro,har sai da gabanshi ya faɗi duk da bai fahimci abunda suke nufi ba,Amma yana ji aranshi cewa Babu alkhairi a tattare da farar takardar daya gani,Slowly ya ɗaura yatsun hannunshi saman paper ɗin yana shafata,Yayin da yake ƙoƙarin yin nazari akan abunda Paper da biro ɗin ke nufi,

"Naga kana kallonta,Babu rubutu ajikinta,its just a paper amma kaine zaka yi rubutu akanta,divorce paper ce,Ta sehrish nakeso ka rubuta mata," Gabanshi ne yayi wani irin mugun bugu,Ji kake rasss!A firgice ya juyo don yaga me wanene ke magana duk da ya shaida muryarshi,Uncle abusufyan ne,Tsaye abakin ƙopar ɗakin fuskarshi a ɗaure,Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,tashin sense, Zuba mashi ido sgr yayi yana kallonshi batare daya ce komai ba, "Saboda halin da muka shiga,Yasa ban tanka maka ba,Amma yau Almost 5 months kenan da yin Auranka da Sehrish,Naji kana ta shirye shiryen komawa U.S,amma banji kana maganar zaka bata takardar sakinta ba,May be ka manta ne,So lemme remind u,Contract marriage ne a tsakaninku,munyi yarjeniya dakai akan zatayi maka aiki for 3 months before ka koma U.S,yanzu time yayi da zaka sake ta,tunda an samu kwanciyar hankali,Gashi kuma zaka koma ƙasarku," Tashin hankalin da ba'a samashi date,Wani irin kallo Sgr ke bin Uncle abusufyan dashi,

*An yanka ta tashi*

*ga masu buƙatar karanta littafin Abban sojoji from book one zuwa 3,Suyi mun magana kaitaye ta whatsapp 08103884440* [3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,Wani irin kallo Sgr ke bin Uncle abusufyan dashi,just speechless,Ya ƙame a tsaye ya kasa motsa lips ɗinsa,Sam ya manta da wata yarjejeniyar aure a tsakaninsu,kamar a mafarki haka yake ganin abun, "Rafayet!"ya ambaci sunanshi don ya lura hankalinshi baya atare dashi,firgigit Sgr yayi yana kallonshi Still bai tanka mashi ba, "Am talking to u!nasan kaji duk abunda nace,we don't ave time to waste,just to make it easy for you that's why na kawo maka Paper da biro,rubutu kawai ya rage maka,nasan within minutes zaka rubuta very simple" Gauran numfashi yaja da ƙarfi tare da runtse idanuwanshi,Da yake ba kunya ce ta ishe shi ba,Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"Uncle,I changed my mind,I have already canceled the marriage contract,now I decided to go with her," Zuba mashi ido abusufyan yayi,cike da Tsantsar mamaki Yake kallonshi, "Zan tafi da ita U.s taci gaba da yi mun aiki," Harara abusufyan ya wurga mashi kafin yace"aiki fa kace?me ka ɗauke ta?idan ka manta bari na tuna maka!Sehrish ƴar cikina ce,your uncle's daughter ba house maid ba,Ni ban haifi ƴar aiki ba,"datakawa abusufyan ya ɗanyi da yin maganar yana fitar da huci,Yaji haushin maganar Sgr,Har yanzu bai daddara ba,Wato Still ƴar aiki ya ɗauketa,bai chanza ba yana nan kan bakanshi kenan,Yafi ƙarfin ya bata matsayin mata a wurinshi,daƙyar ya iya controlling temper ɗinsa Ya ci gaba da magana"Amma rafayet baka da kunya!Har ni zaka kalli tsabar idona kace wai zaka tafi da ƴata U.s,kawai don taci gaba da yi maka aiki!ita Baiwarka ce?so kake ka ƙasƙantarmun da ƴata ne,Duk fa wani abu da kake taƙama dashi,Nima Allah ya hore mun koda bankaika ba,Also she's ur bloodline'yana kai ƙarshen maganar,Rai a6ace Sgr ya juya tare da kai hannu ya damƙi paper ɗin da Abusufyan ya kawo mashi,Yayi tearing ɗinta,into pieces,don ma yasan ba wai zai rubuta abinda akeso ya rubuta bane,

Abun yayi mugun ɗaure ma Uncle abusufyan kai,Shi komai sai ya nuna ƙarfin iko,Ya fi ƙarfin ya miƙa wuya ya roka abashi abunda yake so ta lalama ba,jinjina kai yayi tare da cewa"Ka yage takardar ko?Ko ka manta da agreement paper ɗin dake a wurina da kuma wurin Abbanku!? Gabansa ne yayi wani irin bugu mai sauti ji kake daram!! "Kuma akwai signature ɗinka jikin takardar," Wata irin zufa ce ta soma tsatstsafo mashi,Sae kace ba yanzu ya fito daga wanka ba, Murmushin takaici abusfyan ya ɗanyi kafin yace"As from today!Sehrish bazata ƙara zuwa part ɗinka da sunan aiki ba,Also....."dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana duba wrist watch ɗin hannunsa,Lokaci yake kallo, "Before 24 hours,Ina jiran Takardar sakinta,Idan kaƙi kuma hmmm kasan me zai biyo baya,"yana kai ƙarshen maganarshi,Yayi ƙwafa tare da juyawa ya fuce daga ɗakin nashi, Wani irin jiri ne ya soma ɗibarshi,Ba arziƙi ya koma gefen gadonshi ya zauna tare da kifa kanshi saman guiwowinshi, "Innalallahi wa'inna Ilaihi raji'un" Wannan shine abunda yake ambato acikin Zuciyarshi,hankalinshi yayi mugun tashi,Taya zai Iya rayuwa batare da ita ba?Ta saba mashi da kanta,ta yadda bazai iya rayuwa batare da ita ba,bakomai yake tunawa ba face Romance ɗin da suka sha jiya,Yau rana ɗaya kawai ace za'a rabashi da ita,tabɗijan An taro match kuwa,Allah yasa sun tanadi filin bugata,

Kusan sau uku Marshal Omar yana kwaɗa sallama amma shiru bai amsa mashi ba,sam hankalinshi baya atare dashi, "Rafayet"Ya ambaci sunanshi Yana shigowa cikin ɗakin,Firgit yayi tare da ɗago blue eyes ɗinsa,tamkar na wanda yasha Giya,fuskarshi tayi sharkaf da zufa, Zama gefenshi Omar yayi"bro lafiyarka kuwa?Zaman me kake yi,Muna ta jiranka,Time ɗin sallah yayi fa" Daƙyar ya iya buɗe baki yace"Omar,lokacin da zaka shigo kaga Uncle"? Jinjina kai omar yayi alamar eh, "Ashe ba mafarki bane"Ya ambaci hakan acikin zuciyarshi, "What's wrong with u?ko wani abu ya shiga tsakaninka dashi ne"? girgiza kai yayi"bakomai,bari na shirya mu tafi,"yunƙurawa yayi tare da miƙewa tsaye,Daƙyar yake jan ƙafarshi,Direct ya nufi Closet ɗinshi,after some minute Ya dawo jikinshi sanye da Jallabiya,Omar ya tadda a tsaye hannunshi ruƙe da paper ɗin daya keta,Kallonshi yayi"Wannan fa?naga an yayyagata" Yatsina fuska yayi tare da cewa"Bakomai,mu tafi,"a jere suka fita,Shiru kawai Omar yayi amma tabbas yana ji aranshi cewa wani abu ya faru dashi,Jikinshi duk yayi sanyi,downstairs suka sauko anan suka haɗu da sauran matasan gidan suka ɗunguma izuwa masallaci,

A 6angaren Sehrish kuwa,Tunda ta gudo daga part ɗinsa,Bedroom ɗin Aunty azmee ta wuce,tana shiga ta samu amrish a tsaye saman darduma ta kabbara sallah,lalla6awa tayi cikin sanɗa ta shige toilet,don ta tsarkake jikinta,ta fito ɗaure da towel ta nufi wadrobe,Da yake duk ta kwaso kayanta,Doguwar riga ta zura ajikinta orange colour,mara nauyi ƴar ta shan iska,saman dardumar ta hau,A gefen Amrish ta kabbara sallah,bayan sun kammala Sallar,ko addu'a bata samu tayi ba,Saboda yanayin da take ciki,kasala duk ta baibayeta,Saman gadonsu ta koma ta haye,ta janyo bargo ta lullu6e har kanta,duk amrish na kallonta,ta fara sanya mata ido,in dare yayi ta ɗau wanka,ta fuce daga ɗakin,tsakar dare ta dawo ko wurin asuba,Ta shiga toilet,Wani irin bacci ne ya ɗauketa mai daɗin gaske,hada minshari,

Bayan Amrish ta kammala Yin addu'ar da take yi,Komawa tayi gefen sehrish ta kwanta tana fuskantar ceilling,da alama tayi zurfin cikin tunani,

Tun wuraren ƙarfe 7 na safe,Mommy tare da Oumma suka shiga kitchen domin shirya breakfast ɗin gidan,basu jima da fara ƴan soye soye ba,Saude ta shigo kitchen ɗin tare da hajiya azeema,domin su tayasu aiki,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,Suna aiki suna fira, "Naji kuna ta fira banji kuna zancen gagarumin bikin da muke dashi ba,"Hajiya azeema ce tayi maganar,. mommy tace "Wai har mutun nawa za'a ɗaura ma aure ne?donni abbansu bai sanar dani ba,Amma yace mun in shirya tarbar surukai na," Aunty azeema tace"Ni kaina bansan mutun nawa za'a shafa fatihar tasu ba,Amma ina da tabbacin cewa hada abusufyan acikinsu,"da gangan tayi maganar,cike da zolaya tana satar kallon Abu, Wata irin kunyace ta rufe ta,har ta kasa tanka mata, "Ga kuma saude,Amaryar harrisun gwaggo,Kai gaskiya masha Allah zamu sha bikin da ba'a ta6a yin irinshi ba"abunka ga fulani ga kunya,da gudu saude ta fuce daga kitchen ɗin, Gaba ɗaya suka fashe da dariya, "Tunda saude ta gudu bari in dawo kan Zainabu abu,tauraruwar dake haskaka zuciyar abusufyan,Gaskiya abu ki gode ma Allah,Abusfyan ba ƙaramin Sonki yake yi ba,Ae dole ma yaso ki,Tashin farko kika haifa mashi triplet kyawawan gaske," Murmushi kawai abu ke saki,da alama taji daɗin maganar Aunty azeema, Mayar da idanuwanta tayi kan mommy, "Auntynmu,Kinsan nifa bana 6oye 6oye,nasan su Ya hossein basu sanar dake ba," Fuskar mommy ɗauke da murmushi tae"mekenan? "Nima fa bani da tabbaci nadaiji ƙishin ƙishin wai cikin ƴan ukunta za'a haɗa aurensu da biyu daga cikin zaratan samarin wurinki,Amma fa bansan wanne daga cikinsu ba,"da biyu Azeema tayi maganar don taga reaction ɗinta, Shiru Alex ta ɗanyi jimmm batare da tace komai ba,har na tsawon mintuna,azeema ta kafe ta da ido,don tasan halinta,a lokacin baya tasha faɗin cewa Ƴa'ƴanta bazasu auri baƙar fata ba,ita kanta abu ta lura da sauyawar da tayi tunda akayi mata maganar, Lokaci guda,murmushi ya bayyana akan fuskarta,a tsanake ta soma magana"Zanfi kowa farin ciki,idan Zainab da abusufyan suka zama surukaina,Saboda na yaba da irin tarbiyar ƴa'ƴansu,suna da hankali sosai,ga girmama na gaba dasu," Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Aunty azeema,dama ita fargabarta karta basu matsala, Abu kuwa taji daɗi sosai da irin yabon da Mommy tayi ma ƴa'ƴanta, Cigaba da magana mommy tayi"Dama fa junaid ya sanar dani tun kwanakin baya,duk da na ɗanji nauyi wlh,Ya nuna yana son aure,mukuma a ƙa'ida Yaro kamar junaid ko soyayya bai isa ya fara ba,nayi tsammanin sai ya kai shekera Talatin koda biyar haka kafin ya fara zancen aure,Amma sai gashi tun yana 19 years aure yake so......"da sauri aunty azeema tace"Wannan ae ba wani abu bane,Ya hossein fa,tun yana 20years yayi aurenshi na farko,duk dashi A lokacin ya mallaki komai na rayuwa,Shi kuma junaid sakamakon tauye mashi haƙkinshi da Azeemi tayi,baisamu damar yin karatu ba,Balle aje ga maganar aiki,Amma bai kamata mu damu akan wannan ba,Still junaid yana da sauran damar da zai gyara rayuwarshi,zai cigaba da zuwa makaranta,Sannan za'a sama mashi aikin yi,tunda alhmdllh Allah ya hore mana," Murmushi mommy ta saki,Taji daɗin maganar azeema sosai,daga haka suka cigaba da yin firarsu suna aiki,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala Girke girken nasu,a lokacin saude ta dawo kitchen ɗin,Atare da Oumma suka soma ɗaukar food stuffs ɗin suna kaiwa saman d-table,

Bayan sun kammala jerawa,Saude tabi ɗakunansu tana tashinsu,Don su hallara a fara ɗa'amin,

Turo ƙopar ɗakin ammi tayi,Zaune tasame ta gefen gadon hannunta ruke da ƙur'ani tana karanta,Idanuwanta na sanye da glass fari, Zuƙunnawa tayi cike da girmamawa ta gaishe da ita"Ammi ina kwana,kun tashi lafiya,Ya gajiyar tafiya," Murmushi ammi ta sakar mata"Lafiya lou,Gajiya tabi jiki," Saude tace"An kammala shirya breakfast Anan zan kawo maki,". "A'a,nafison nafito naci atare da jikokina,"murmushi saude ta saki kafin ta miƙe tare da juyawa zata bar ɗakin,. "Ji mana,"ammi ce ta katse mata hanzarinta,"juyowa tayi tana kallonta,. . "Amm..ince ko kinyi ma su Nafisa da khadija magana"?tana magana akan ƴan matan da suka zo dasu jiya "Ae daga ɗakinsu nake,Na same su suna shiryawa," Jinjina kai tayi"Masha Allah,zaki iya tafiya," Buɗe kopar tayi ta fuce izuwa ɗaki na gaba,

Jahad na kwance,since yesterday night bata runtsa ba,tashiga damuwa sosai akan junaid,hankalinta yaƙi kwanciya,tunda ya nuna baisanta ba,duk ta rasa natsuwarta,ita kaɗai Ce kwance saman gadon,Hosana na acikin toilet,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull