Kenza eBookz

Abdulmajid complete - Chapter 6

Abdulmajid complete - Chapter 6

Abdulmajid complete Chapter 6: Abdulmajid complete Chapter 6. Ganin yanayin da ta isko yayarta ciki ga Abdool sai ihu yake amma uwar ko kallonsa ta k'asa…

4,486 words

Ganin yanayin da ta isko yayarta ciki ga Abdool sai ihu yake amma uwar ko kallonsa ta k'asa yi balle tayi tunanin shayar da shi, Abdool ta d'auka, abinci ta had'a mishi saida ta tabbatar ya k'oshi sannan ta goyashi ba dad'ewa bacci yayi gaba dashi sai ajiyar zuciya yace, gurin yayarta ta matsa wanda itama jikinta a sanyaye yake, dafata tayi, nan ta d'ago ta kalleta da rinannun idanunta, "Aunty komai yayi tsanani maganin shi Allah, ki d'aure ki gayamin meke faruwa?"

Kama hannayenta duka biyu tayi, bakinta na rawa, sai a lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo mata, sharewa tayi, nan ta labartawa k'anwarta duk abinda ya faru bayan wucewar ta makaranta.

"Inalillahi wa'inna ilaihirraji'un" shine kalmar da Asma'u tace maimata tawa iya tashin hankali kenan, yanzu ta fita tabar mata da mijinta lafia, amma kuma cikin k'ank'anin lokaci komai ya canja, farinciki ya koma bak'in ciki, batasan lokacin da hawaye suga zubo mata ba, nanta rungume yayarta sukaci gaba da kuka bamai lallashin wani.

Bankad'o k'ofa akayi da k'arfi, a tare suka d'ago dan ganin wanene, da kallon k'ask'anci ta bisu, ba kowa bace face Hajia "to matsiyata 'yan gadon lalata(sadnaf), me kuke jira yanzu kuma?, ina auren ya k'are ko kuma da sauran zance ne iyye" duk cikin masifa tace maganar.

Saida ta saka full stop sannan Asma'u tace "yi hak'uri Hajia yanzu zamu tafi" tsaki tayi tare da cewa "aikin banza sannan ta fice.

B'angaren Rafia kuwa suna isa part d'in Hajia bayan tayi Jim na mintuna tace "Hajia Bari in tafi zanyi wani aiki" part d'inta ta shiga, wannan gardin ne zaune a kureja amma ya maida kayanshi, wata shu'umar dariya tayi sannan ta d'aga mai babban farcenta "weldone Wizzy aikin ka ya tafi yadda akeso" murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba, bedroom ta shiga sai gata ta fito da rafar 'yan duba, bashi tayi tare da bud'emai k'ofar baya ya ware.

Asma'u ce ta d'ibo musu kayan sawarsu trolley biyu, drop suka d'auka sai k'ofar gida.

************************

Lokacin suka isa dak'ar suka shiga ciki, Mama na tsakar gida tana aiki, Mansur kuma na gyara mata alayyahu, ganin da kaya nik'i-nik'i sannan fuskacinsu a jeme duk sun wani yamutse, yasa tasan ba lafia ba, gaisa sukayi sannan suka shiga ciki, itama wanke hannu tayi tabi bayansu, ba wani boye-boye Asma'u ta gayamata abinda ya faru.

Ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, amma saita daure tace "Allah yasan hakan shi yafi zama mafi Alkhairi" dama tunda k'anwarta ta gayamata halin Hajia da irin wulak'anci da tayi musu, yasa ko sha'awa zuwa gidan bata tab'a yi ba, amma wannan sharrin dame yayi Kama, idan so take a saketa basai ta had'a da sharri ba, dan ta yarda da tarbiyar 'yarta ba zata taba aikata hakan ba koda bada Aure ba balle da Aurenta, Allah ya saka Mata, shine kawai ta fad'a a ranta.

Baba ma daya dawo yaji ba ransa ne yayi mummunan b'aci, musamman sharrin da akayi mata, dama Baba akwai zafi, abin ya bala'in k'ona ransa, fad'a yayi tayi da cewa zaije Sokoto gobe, saida Mama ta tausheshi sannan ya hak'ura, dan tasan idan yaje da wuya ayi mai kyau, amma yace gobe su Hafsat da Usman(k'anwar Mama da d'an kanin babansa) suje su kwaso kaya sannan su anso masa takardar 'yarsa.

Auwal kuwa bayan gari yaje bakin ruwa, a can yayi zamansa dan gari ya riga yayi mishi zafi, nan yayi ta sak'awa da warwarewa har dare bai samo mafita, ganin duhu ya shigo, yasa shi hak'ura ya koma gida.

Hajia kuma ganin har dare ba Auwal ba labarin sa gashi ta kira wayoyinsa a kashe yasa hankalinta tashi, bakin k'ofar part d'insa ta tsaya zaman jiran dawowar sa.

Dai2 part d'insa yaga Hajia, jiki sukwana ya k'arasa gurinta tare da gaida ita, bata ansa sai fad'a data haushi dashi "wai kai Auwalu wane iri yaro kake, kabi ka tada hankalinka akan yarinyar da ta gama cutar da kai, gara ka fiddata a ranka dan kun rigada kun rabu kenan ehe, to garama tun wuri ka yakiceta a ranka ka rungume Ummita dan har nayi magana da hajiyarta nan ba dad'ewa za'ayi bikinku, sannan ka rubuta takardar waccen matsiyaciyar ka kawo min, zan aika mata har gida" Auwal da zuciyarsa ta gama k'ek'ashewa "tau Momy" kawai yace, sannan ya shiga ciki, itama ficewa tayi tana fad'in "daga Allah ya tona mana 'yar iska" tana shiga part d'inta nan ma Maryam ta isko ta had'a kai da guiwa, dan tunda ta dawo Hajia ta fad'a mata abinda ya faru, ta shiga damuwa hadda kukanta dan ta saba da Aunty da Asma'u ga Abdool Son d'inta, ita sam bata yadda aunty zata aikata abinda akace tayi ba, dan tasan ta farin Sani kullum cikin yi musu nasiha take itada akan su tsare mutuncinsu sannan ace ta aikata wannan barnar.

Tsaki Hajia tayi "kwayi kwa gama" sannan ta shige ciki tana mitar halin irin na 'ya'yanta Sam basu biyota ba(ai sun huta basuyi bak'in gado ba) waya ta kira hajia Umma mamarsu Rafia danso take ayi komai cikin lokaci, saboda ta k'ara cusawa Ameena bak'in ciki.

Auwal na shiga ciki jin ba motsin wata halitta ko'ina shiru, sabanin da, koda zai shigo a parlour zai samesu suna kallon sunnah TV wata ran kuwa su kalli zee TV ko kuma su zauna suna hirarsu gwanin sha'awa, Murmushin takaici yayi tare da shigewa ciki, takardar ya rubuta kamar yadda ta buk'ata yakai mata.

Washe gari kamar yadda Abba ya buk'ata haka su Hafsat da Usman Suka taho da babbar motar kwasar kaya, amma me Hajia tace ba wani kaya da zasu kwasa ai danta ne ya saya, haka aka shiga rigima sun nace sai kwasa itama tace basu isa ba, hayaniyar ce ta kawo hankalin mutanen gidan wad'anda duk abinda ya faru basuma San anyi ba sai lokacin.

Ganin rigimar tak'i k'are wa yasa Sani kiran Auwal ya tambayesa nan ya tabbatar kayanta ne ko tsinke bai siya mata ba, da yake a hand's free ya saka kowa yanaji yasa ta basu suka kwasa, tana biyarsu da habaici da bak'ak'en maganganu, ba Wanda ya kulata har suka k'are tun kafin su tambayi takardar 'yarsu ta kawo musu, tare cin mutunci.

Auwal da tun safe ya fita zuwa yayi ya tattara duk wata k'addara tasa ya sayar, banki yaje ya bud'e kid account ya zuba kudin, iya wad'anda zai rike a hannun sa ya rage, bashi ya dawo ba sai goman dare, d'akin sa ya shiga yayi wanka ya kimtsa sannan ya d'auka diary sabo kal, rubuta sosai yayi sannan ya sake rubuta wasik'u har uku, part d'in Hajia yaje yace Maryam ta d'auko mishi key din part d'in Alhaji dan duk wannan ruguntsumin da ake Alhaji bayanan ya tafi umrah, d'auko mishi tayi bud'ewa yayi sannan ya shiga bedroom, wardrobe d'insa ya bud'e wata leda ya saka daga can sama sannan ya rufe ya fito, Maryam ya kira ya bata keys d'in da wasik'a tare da tabbatar mata da ta bawa Hajia zuwa gobe da tau ta ansa masa sannan ta shige ciki.

Washe gari bayan sun gama breakfast ta d'auko wasik'ar ta bama Hajia.

"Lahaula walah k'uwwati illah billah" shine Kalmar da Hajia ta fad'i tare da zubewa k'asa a sume........

_friends ina barar Addu'arku akan wata buk'ata tawa, ina da tabbacin zan samu. Love u all_ 😍

💄Meryerm Abdool💄 [8/6, 8:15 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬 🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na 💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers* P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

```Wannan page d'in nakune 'yan makarantar madarasatul nurul Islam littahafizil Qur'ani Kareem,kabino area,Argungu```🕌

_Irinsu Nafisa muh'd, Fareeda Nana b/mashaya, Mamu Aliyu, Saudat yahya, Meena dikko, Amina Garba, Bilkis, Hajjo, Aina'u Idris and rest kuna raina koda yaushe#❤❤❤#_

📝 *Episode* 106-110

Maryam wacce tana mik'awa Hajia sak'on Auwal ta shige bedroom room d'inta, sai jin k'aran fad'uwar abu tayi aiko da gudu ta fito ganin mahaifiyarta kwance ba numfashi yasa tayi Kanta cikin kid'ima tana jijjigata, amma ko alaman tashi batayi ba, aiko da gudu tayi part d'in Rafia tayi sa'a Ayuba nanan, jin abin ya faru yasa suka biyota cikin tashin hankali, Rafia ce tayi Kanta ta rungume ta yayin Auwal yace a kawo ruwa, da sauri Maryam ta kawo ruwa Shafa mata akayi, nan take ta sauke ajiyar zuciya, bud'e ido tayi a hankali ta sauke a kansu sannan ta maida kallonta ga takardar da ke jinke a hannunta, wani kuka ta rushe dashi "why Auwal, meyasa zakayimin haka".

Ayuba ne yayi k'arfin halin cewa " Momy me kuma Auwal yayi miki?" Takardar ta mik'a masa, ansa yayi tare da karantawa a fili.

_"kiyi hak'uri momynah nasan koda wasik'ata zata sameki ba zakiyi farinciki da ita ba, sai ba yadda zanyi dole ce tasa zan barku, bazan iya ci gaba da zama kusa da inda zanji labarin Ameena ba, alhalin bama tare, dole zan nisanta kaina daku da kowa nawa, kada ku wahalda kanku nemana danni kaina bansan inda na dosa ba, pls kiyafemin Momy kiyimin fatan Alkhairi, kada ki tsinemin, idan kikayi haka rayuwa zata ga garari, ma'assalam_

D'anki *Auwal Sada*

Koda ya gama karantawa zuface ke keto masa duk da fanka da na'oural sanyi dake aiki, yama kasa magana, Maryam tuni hawaye ya wanke mata fuskarta, Rafia ma tashin hankali taf fuskarta dan batasan haka abin zai zama ba.

Momy kuwa sai sambatu takeyi tana kiran Auwal dan Momy akwai son d'iya, hakan yasa wutar k'iyayyar Ameena da d'anta ta k'ara ruruwa a ranta dan duka ita d'orama laifi, wai ba a banza tabar Auwal ba, wannan son ya wuce hankali, tunda harya kasa ganin girman laifinta ya barsu saboda ita.

Nan dai suka wuni cikin jimami ga tsoro fal ranta na idan Alhaji ya dawo me zatace masa, gashi gobe Suke tsumayen dawowar sa, dak'yar ta kira Maman su Rafia ta gayamata abinda ya faru, Ummita kuwa da raji rud'ewa tayi, dan ita harta fara shirye,-shiryen Amarcewa(tab to ai sai aje a rungumi big sowie Ummita) lol.

****************************

*Washe gari*

*12:00pm.........*

Jirginsu Alhaji Sada ya sauk'a a Sakkwato birnin shehu, Sani, Hajia, Maryam ne sukaje tarbonsa, yayi farincikin ganinsu amma yafi k'osawa yaje yaga 'yan jikokinsa musamman Abdool dan yaron ya shege masa ransa, sonsa yake sosai bada wasa ba, saidai baya nunawa gudun tashin hankali, sanda suka isa kowa saida yazo gaidashi amma ba Auwal da familyn sa, k'asa daurewa yayi ya tambaya ko sunyi tafiya ne.

Ganin yayi kowa yayi shiru, hakan yasa jikinsa yin sanyi dan yafi ba, lafiya a jikinsa, Hajia ce tayi k'arfin halin cewa "Alhaji ka bari kaci abinci ka huta tukunna sai ayi maka bayanin komai" jiki a sanyaye tayi maganar.

Ba shida zabi hakan akayi bayan yaci ya huta haka ta kora masa bayanin komai daya faru, har zuwa tafiyar Auwal, shiru yayi nad'an lokaci kafin ya dago idonsa da suka rine sukayi ja ya nuna Hajia da yatsa.

"Ke bani mamaki kaltume duk da babu mamaki in ankai la'akari da rashin son da kike nunama Ameena, tau burinki ya cika Ameena tabar miki gida Auwal ma ya bita yanzu sai kije ki zauna da wad'anda kikeso" ta bud'e baki zatayi magana, ya dakatar da ita "bannson jin komai daga gareki tashi ki tafi" ya fad'a yana nuna mata k'ofa dama daga ita sai shine a d'akin, tashi tayi ta fice jiki ba k'wari, dan tasan hak'uri irin na Alhaji duk yakai gayin fad'a to an kureshi ne, amma ai bai kamata yaga laifinta ba, komai ya faru au Ameena ce sila, itakam wannan shine adakeka a hanaka kuka.

Alhaji sai safa da marwa yakeyi ransa a jagule, tabbas Auwal bai kyauta ba, koma meye ya faru bai kamata yabar gida, duk da iya cuta an Riga an cucesa, dan wannan dagaji sharri ne akayi mata, dan yasan Ameena ba zata tab'a aikata wannan danyen aikin ba, kuma yasan Hajia nada tsananin zafi da ak'ida Mara tushe da asali, amma yasan ba zata aikatawa Ameena wannan aikin ba, to abin tambaya anan waye ya aikata? Babu ansa "Allah ya sawwaka" ya fad'a a fili, dama iya zaman da Allah ya d'ibar musu kenan, koda wannan koba sa wannan ba tabbas sai sun rabu dai2 wannan lokacin

Bud'e wardrobe yayi dan d'aukar Abu kawai sai Leda ta Fad'o takardune na bud'e account da komai daya k'unsa sai diary da wasik'u guda biyu, bud'e d'ayar yayi yaga ansa *zuwa ga Ameena* rufewa yayi ya bud'e d'ayar Wanda ta kasance tashi ce.

Shima dai ban hak'urin ne da Neman gafara, sai Amanar *Abdulmajeed* daya d'anka masa da kuma bayanin diary da information na Account ya aje hannunsa har sai Abdool ya mallaki hankalinsa ya mallaka masa, sai wasik'a da yake rokon ya bayar a kaiwa Ameena, bayan ya gama karantawa yace "na yafeka Auwal duk da baka kyauta min a matsayina na mahaifi ba, wannan dalilin bai isa yada ka tafi ba, amma ba komai Allah ya tsareka a duk inda kaje ya kuma dawo mana dakai lafia wuri kusa kazo ka kula da d'anka da kanka".......

B'angaren Ameena kuwa kokai waye idan ka ganta dole ka tausaya mata, ta fita hayyacinta gaba d'aya tayi bak'i ta rame sosai kullum cikin kuka take musamman ganin an kwaso kayanta, yanzu shikenan ta zama bazawara, abin tafi tsana a rayuwarta ada sai takega duk matar da ta zama bazawara a dalilin saki to laifinta ne, ita tayi abinda yasa aka saketa, amma a yanzu ta gane ba haka abin yake k'addara wacce bata wuce fata, ta gane Ashe ba matar da ke son a saketa koda kuwa ita tayi laifi, balle irin su da basuji basu gani(to in banda Ameena wake so yayi aure yau gobe ace ya dawo gidansu ai saida k'addara wacce ba'a fata Allah ya kyauta).

Ga Abdool kullum kukan Dadynsa yakeyi Abu duk ya had'e yayi mata yawa, danma ga Asma'u kusa ita ke d'auke masa kewar Dadynsa, Mama da Baba kullum cikin kwantar mata da hankali suke, Mansur kullum yana cikin kawo Abdool kayan wasa da kayan kwalama irin na yara idan yaje School 'yan Kud'insa duk can suke tafiya duk dan su kwantar Mata da hankali, Firdausi ma tazo lokacin da taji, itama Sam abin baiyi Mata dad'i, musamman ma sharrin yafi komai cin rai, inda Allah ya sota duk Wanda yaji kai tsaye yake k'aryatawa, saboda sanin halin kirkinta(tau zama dan kwarai Nada rana dan wata rana ake gujewa mu d'aure mu k'are mutuncinmu).

Alhaji washe gari yazo Argungu, Baba ya tarbesa kamar ba abinda ya faru dan yasan ba laifinsa bane, hak'uri ya k'ara bashi akan abinda ya faru, tare da tabbatar masa Sam koda abin ya faru bashi gari, saida ya dawo yakeji nan yake gayamai tafiyar Auwal, nan Baba ya jajantamai tare da fatar Allah ya bayyana shi, tsaraba Ameena da Abdool ya fito dasu hadda ma Asma'u yayima dan yasan tana gidan lokacin da ya tafi, tare da kayan buk'atar Ameena da Abdool na yau da kullum, dan yayi Alkawarin kula dasu har sai tayi Aure.

Baba saida Alhaji ya nuna b'acin ransa tukun ya anshi kayan dan yace bazai Ansa ba, saida Alhaji yace bai hak'ura da abin da yw faru ba kenan, ai sun Riga sun zama d'aya tunda har rabo ya shiga tsakani, hakan dai dole ya ansa, har Mama saida ta fito suka gaisa sannan ya bata hak'uri itama.

Lokacin da Ameena tazo nasiha sosai yayi mata tare da bata hak'uri sannan ya tabbatar mata har yanzu shi ubane gareta komai ya sameta ta sanar da shi, kud'i ya bata tare da wasik'ar Auwal, saida yayi mata fad'a sannan ta Ansa, haka ya tafi yana tausayawa mata dan bazaiso hakan ra faru akan Maryam ba.

Sosai ya k'ara daraja da girma akan idon Ameena da iyayenta.

Sai dare ta d'auko wasik'ar Auwal da tunda aka bata ta kaita ta ajiye, dan ita yanzu lamarin maza ya fita Kanta kuma duk haushi Suke bata(dama ai duk macen da aka saka tofa duk maza haushi zasu rik'a bata zata d'auka duk Wanda ta aura zai iya sakinta komai soyayyar da yake mata kuwa.

Bud'ewa tayi ta fara karantawa..

_"gareki masoyiyata tahar abada, Ameena nasan zanyi bak'i a gurin ki dan duk wacce aka saka saki uku kai tsaye tabbas zata girgiza kuma zata tsani wannan mijin, harga Allah duk da abinda idanuwana suka ganemin, zuciyata ta k'asa yadda da abinda wani barinta ke gayamata akanki, saidai ki sani dole ne na shiga rud'u dan nina gani ba ji nayi ba, amma inaso ki d'auki wannan a matsayin k'addarar muce, ki tausayawamin ki tausayawa d'ana *Abdulmajeed* ki zame masa uwa da uba agareshi ki bashi dukkanin tarbiya ta gari, dan kuwa ke uwace ta gari a gareshi, pls kada kibar rayuwarsa tayi garari koda kinyi aure ne, ki zama majib'incin lamurransa a dai2 gab'ar da ya rasa dukannin kulawata a matsayina na uba agareshi, na tafi bawai dan bana k'aunar sa ba Aa sai dan samun maslaha a gareni, ina miki fatan Alkhairi, ki saka a ranki zan rayu da sonki a kowanne second na rayuwa"._

*naki Auwal Sada*.

Koda ta gama karantawa hawaye sun wanke mata fuska, zuciyarta sai rad'ad'i take mata da suya, Abdool ta rungume tsam a k'irjinta tana tausayawa rayuwarsa, yaro k'arami ko wace rayuwa zaiyi nan gaba.

"Allahumma ajirni fi musiba"..................

*ina mai Baku hak'uri sa babbar murya, akan jina da kukayi shiru kwana biyu, na shiga busy ne, amma Ku sani kuna raina#1❤#*

💄Meryerm Abdool💄 [8/8, 7:45 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬 🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na 💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers* P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

👌🏻 *d best way 2 love is love for d sake of Allah. And tell d one u love d fact about him, show him d true faith, never tell him lies just 2 make him happy, hmm day he/she find d true u will become his biggest enemy, may Allahu (S.W.T) show us true way of life ameen👏🏽*

Small quote👌🏻

_Aunty Khaleesat Haiydar ur r so grateful, Aunty Ummi shatu wishing oll d best in ur exams👌🏻_ #heart u aunty's😘#

📝 *Episode* 111--115

Saida aka kai ruwa rana kafin Baba ya yadda da komawar Asma'u makaranta, dan yace ta dawo tayi NCE kawai, dak'yar ya amince amma da sharadin zata kare mutuncin Kanta, ranar da zata tafi da kuka suka rabu da Abdool dan lik'e mata yayi sai taje dashi, Mansur ya fita dashi sannan ta samu ta wuce kice da kewar gida da Son d'inta, dan tasan zatayi missing nashi, Hostel ta koma da zama inda ta dage da karatunta baji ba gani, tayi mamakin rashin ganin Maryam sai daga baya takeji ga k'awayensu an canja Mata school, Hajia ce tasa aka canja mata, a cewarta kada Asma'u ta lalata mata d'iya, tunda tasan muddin suna school d'aya Maryam ba fita hanyar Asma'u zatayi ba, hakanan bataso aka maida ita nursing.

B'angare guda kuwa shakuwa ce ta k'ara shiga tsakanin Asma'u da Abdulrahim kullum zaka Kansu tare yana koya mata karatu musamman yanzu data dawo hostel dama shi a hostel yake dan ba dan garin bane, tun basujin komai a ransu game da juna har takai yanzu sunajin zukatansu sunaso su zama d'aya.

( *Tofah wai waye Abdulrahim?*)

Abdulrahim dan asalin kilgori ne wadda ke k'arkashin Yabo local government dake jahar Sokoto, D'ane ga Malam Umar wadda akafi Sani da Ard'o, sarautace irin ta Fulani wato mai gari kenan, Ard'o ya zamo mai garin kilgori ne bayan rasuwar mahaifinsa wato tsohon Ard'o, yana da matar Aure d'aya Hadizatu wacce akafi sani da Iya Hari, auren zumunci ne akayi musu, Ard'o mutum ne na mutane mai sanyin hali, kowa nasane, yayin Iya Hari ta kasance masifaffiyar mace, Mara mutunci kullum cikin masifa take da bala'i, tunda Ard'o ya aureta bai taba k'arda dad'in ta ba, anadai zaune ne zaman hak'uri, bai isa ya sata tayi ba haka bai isa ya hanata ta hanu ba, amma a haka sukaci gaba da zama da yake Allah ya zuba mishi hak'uri, komai tayi kauda kai yake kamar bai gani ba, sunada 'ya'ya uku Abdulrahim ne na d'aya Wanda take kira da Modibbo saboda kasancewarsa d'an fari, sai Lantana wacce ake kira Lanti sai Aisha wacce ake kira Shatu, sam halin Aisha da Abdulrahim ba irin nata bane halin babansu suka d'auko, kai harma kamar dansu farare ne sirara dogeye, kyawawa dasu, yayin da lantana ta biyo kama da halin uwar sak.

Tun Abdulrahim yana k'arami yake sha'awar boko, mahaifinsa kuwa ganin yana sha'awa yasa ya sakashi A yabo dan lokacin ba'ayi anan garinsu ba, haka yake tafiya kullum zuwa yabo don daga k'arshe da mahaifinsa yaga wahalar zatayi yawa sai ya had'ashi da wani malami, yake zama gidansa sai Hutu yake dawowa, Wanda hakan Sam baiyima Iya Hari dad'i ba, rigima ta tada akan ba inda zaiye ya tsaya yayi kiwo in zaiyi, rokonta yayi tayi akan ta barshi, amma tak'i amincewa, dama Abdulrahim baisan dad'in ta ba Sam, dan bata janshi a jiki, wai d'an fari ne, ba wani sabo a tsakaninsu yafi sabawa da Ard'o, haka kuwa ta dage akan ba inda zaije, saida Ard'o ya nuna b'acin ran yaje ya gayama iyayenta, ganin tunda take dashi bai taba nuna Mata bacin ransa haka ba balle har aje ga kai k'ara yasa ta shiga taitayinta ta amince akan dole.

Hakan Abdulrahim yayi ta karatunsa tun daga primary har secondary duk anan Yabo yayi su, gashi kanshi naja(dama Fulani akwai kai) tunda ya fara harya k'are bai tab'a yin na 3 saidai na 1 ko 2 hakan yasa malamansu bawa Ard'o shawarar kaishi university hakan kuwa ta kasance inda yake karatun medicine, ita dai Iya Hari akan dole yake karatun badon son ranta ba, dan ita gani take lalata yara kawai boko keyi, shiyasa ta hana a saka Lanti Shatu, Abdulrahim kuwa ya goge idan ka ganshi bakace dan k'auyen bane, hakan yasa 'yan matan garin kowa sonsa take, 'yar k'anwar Iya Hari ganin kowa sonsa yasa hankalinta ya tashi, ba kunya taje ta gayama Iya Hari itafa shi takeso, dama itama sunada burin hakan itada k'anwarta na had'a su aure, nanta tabbatar mata da Abdulrahim baida matar aure sai ita, shikam Abdulrahim Sam yarinyar bata mishi ba saboda batada nutsuwa Kanta rawa yake, itakam Saude sai d'aga kai take a garin da tak'ama zata auri d'an boko.

_wannan kenan_

B'angaren Ameena kuwa ganin Asma'u ta koma makaranta, Mansur ma ya koma dake boarding school yake, gidan ba dad'i duk da Asma'u na zuwa duk k'arshen sati, yasa tayima Baba magana tanason itama ta koma makaranta bai musa mata ba, saidai yake ba zataje nursing kamar yadda ta buk'ata ba, dan ko lokacin da Auwal ya kawo mata form abinta ta cike kenan, wannan burinta ne tun suna secondary, amma dole ta hak'ura da ita dan dalilan da Baba ya gayamata na hanata zuwa wani gari kara2, ya gayamata 'yan uwansa zaginsa zasuyi suce a maimakon yayi mata Aure ya turata karuwanci, hakan yasa ta hak'ura zatayi NCE anan *Adamu Augie college of Education Argungu* da kanshi ya anso mata form ta cike inda aka bata Agric/education, nan Baba ya sakata gaba yayi mata nasiha akan taci gaba da tsare mutuncinta tayi abinda ya kaita kawai banda bin k'awaye barkatai, itama Mama tayi tata, nan Ameena ta fara zuwa school cikin nasara, ba abinda takeyi sai kara2 ba ruwanta da kowa haka zatayi shigarta ta kamala taje data gama lec, ba wani tsaye-tsaye direct gida take wucewa dama can daga gida sai makaranta, sai kuma bikin yan uwa ko barka shima akan tilas take zuwa kada ta yanke zumunci, saidai abinda ke kona mata rai data had'u da taubasanta yanzu zasu fara takanarta da kiranta bazawara ina zawarawanta, yake kawai take musu amma Kalmar ba k'aramin k'onata takeyi ba, saidai ba yadda zatayi k'addara ta riga fata, shisa sam bata cika son shiga mutane ba.

Zuwa yanzu ta kwantar da hankalinta ta maida kamarta ta kuma rungume k'addarar ta, saidai Aure ya fita ranta gaba d'aya, shiyasa duk Wanda yazo da sunan yana sonta hak'uri kawai take bashi dan bataji zatayi aure yanzu.

Lokaci zuwa lokaci takan tuna Auwal da rayuwarsu ta baya, koyana ina yanzu oho!, Abdool zuwa yanzu ya manta da Dadynsa yayinda ya d'auki Baba a matsayin Babansa, yana 1¼ ta yayesa dan komai ci yake ga kafafu har gudu yake hak'ora ne kawai bai cika ba, bata sha wahala a yayensa ba, dan wani sa'in sauya wuni baisha ba sai dare, tunda ta aka yayesa ya koma hannun Mama can yake baccinsa.

Ta dage sosai da karatunta k'awa d'aya tayi mai suna Sakina mungadi, department d'insu d'aya, tasu ce tazo d'aya shiyasa sukayi k'awance dan itama sakina ba ruwanta da sha'anin kowa abinda ya kaita kawai takeyi(a kowanne lokaci muyi k'ok'ari muyi mu'amala da mutanen kwarai, dan kuwa har lahira kana tare da abinda kakeso, kuma zama da mad'auki kanwa shika haddasa farin kai) a hostel take zaune dan a bk suke zaune da iyayenta, kullum suna tare idan ka gansu gwanin sha'awa cikin shiga ta kamala, Sakina tasan komai gane da Ameena dan har gidansu tana zuwa, tana kuma son Abdool sosai, haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dad'i gobe sabanin haka, rayuwar duniya kenan haka ta gada, a gefe d'aya kuma Ameena naci gaba da kasuwancinta kuma duk k'arshe wata har Alhaji Sada na zuwa dubasu da hidima sosai kamar yadda yayi alkawari, su Baba ma na iya k'ok'arin su, so batada matsala a yanzu saidai wacce ba'a rasa ba.....

Suna NCE 2 wani malami na education ya basu Assignment to group discussion ne, kuma each group ten people ne, shiya rabasu da kanshi, from d different faculty, anan aka hadasu da wani Yusuf normally tasanshi saboda suna had'uwa GSE da EDU saidai magana bata tab'a had'asu ba, shine team leader nasu ita kuma assistant, shi d'an ENG/ISS, wannan Had'uwarne ta zama sanadin shakuwa tsakaninta da Yusuf, dan Yusuf social man ne, kokai waye ka zauna dashi sati yayi wuya Baku saba ba, dan akwai barkwanci gareshi burinshi bai wuce yasa mutane cikin farinciki ba, Sam shima ba ruwan sa da shashanci, kara2 kawai ya saka gaba kuma ga kwakwalwarsa tana ja ba dama, dan 3point kawai yake bugu ga G.P, hakan yasa ya saba dasu Ameena ko bayan gama assignment d'insu saiya kasance duk lokacin da basu da lectures sukan zauna suyi discussion a tsakaninsu based on their studies.

Yauma Zaune suke suna tattaunawa sai wayanta tayi k'ara, dauka tayi basuji me aka fad'a a d'ayan b'angaren, sun daiji tace.

"Subhanallah Asma'u meya sameshi?"

Still suka k'ara jin tace "tau ganinan zuwa" mik'ewa tayi a rud'e, tare da musu zataje gida, amma yanzu zata dawo, Sakina CE ta tambayeta meya faru, nan take gayamata Abdool ba lafia.

"Aa to inzo muje kawai".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull