Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 1

Abokaina complete book 1 - Chapter 1

Abokaina complete book 1 Chapter 1: Abokaina complete book 1 Chapter 1. Compiled By Umar Dalha Funtua.

4,321 words

Compiled By Umar Dalha Funtua.

Copied By Ummee Garkuwa.

[7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *March, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*01*

Fawaz Shattima d'a ne a gurin Muhammad Shattima haifaffen jihar Kaduna kuma babban d'an kasuwa wanda yayi fice a fannin kasuwanci daban-daban a ciki da wajen Nigeria. Yana da mata d'aya kuma uwar 'ya 'yan sa mai suna Halima da 'ya 'ya biyu Fawaz da Maryam. Fawaz da Maryam sun taso cikin arziki da wadata da kowane abubuwa na jin dad'in rayuwa sai dai kuma iyayen su sun tsaya sosai a gefen tarbiyar su. Fawaz kyakkyawan gaske ne kamili, nitsatstse kuma miskili wanda sam ko kusa ba ruwan sa da sha'anin mutane ko kuma ince sabgar da ba ruwan shi.

Fahad Tambari d'a ne a gurin Alhassan Tambari haifaffen jihar Kaduna kuma malami ne a jami'ar tarayya ta Ahmadu Bello University Zaria a fannin sanin halayyar d'an adam wato Psychology. Duk wanda za'a kira da malamin jami'a an san ba wani gawurtaccen mai arziki bane sai dai rufin asiri. Yana da mata d'aya mai suna Hauwa kuma uwar d'an sa Fahad, tun daga kan Fahad Allah bai k'ara basu haihuwa ba duk kuwa da cewa suna tsananin buk'atar ta wannan dalilin ne yasa suka d'auki masifar so da shagwab'a suka d'ora su a kan Fahad. Fahad ya taso mara jin magana da k'iriniya saboda rashin samun kwab'a daga iyayen sa.

Muhammad Shattima da Alhassan Tambari abokan juna ne sosai duk kuwa da cewa ayyukan su na yau da kullum sun sha bamban wanda ya samo asali daga mak'otaka da Allah ya had'a su a wuri d'aya kuma tun kafin su samu haihuwar yaran su na farko wato Fawaz da Fahad. A kusan lokaci d'aya matan su suka d'auki ciki sai dai Halima wato matar Muhammad Shattima ita ta fara haihuwa ta samu d'a namiji, ba'a yi suna ba itama Hauwa wato matar Alhassan Tambari ta sauka itama aka samu d'a namiji a nan ne aka rad'a musu suna Fawaz da Fahad. Fawaz da Fahad sun taso a tare kai d'aya abokan juna sosai wanda bacci kawai yake raba su, sun shak'u matuk'ar shak'uwa wanda yasa daga farko ma sun d'auka akwai wata alak'a ta jini a tsakanin iyayen su sai da suka girma suka k'ara wayo suka gane ba wata alak'a kawai mak'otaka ce da zaman aminci. Suna da shekara uku a duniya mahaifiyar Fawaz ta sake haihuwa ta haifi mace wacce aka sakawa suna Maryam, a haka Fawaz da Fahad suka taso dukansu da k'aunar Maryam.

A tare kuma a makaranta d'aya suka soma karatun su na primary har zuwa aji shida a daidai wannan lokacin ne mahaifin Fawaz ya k'ara samun bud'i da d'aukaka ta fannin kasuwancin sa ya gina musu babban gida a wata unguwar suka kwashe suka koma wannan gidan sai dai sam Fawaz da Fahad basu ji dad'in tarewa a sabon gidan ba domin kuwa ya zamar musu tamkar barazana a abokantakar su ya kasance ba inda suke had'uwa sai a makaranta wannan shiyasa koda yaushe suna a kan hanyar ziyartar gidajen su idan Fawaz da Fahad basa a gidan su Fawaz to ba shakka suna a gidan su Fahad harta iyayen su shak'uwar tasu tana basu mamaki sun ga dai su suka k'ulla wannan abota amma gashi yaran ma sun fi rik'e ta da kyau a kansu wanda kuma ya samo asali ne daga bambancin ayukkan su a inda mahaifin Fawaz koda yaushe yana tafiye-tafiye k'asashe da dama shi kuwa mahaifin Fahad ko dai yana a makaranta ko kuma yana gida yana fama da takardun d'alibai wanda shi ya kawo k'asa a gwiwa wurin tabbatar zumuncin nasu.

Lokacin da suka shiga j.s.s1 ne a wata babbar makaranta a garin Kaduna wanda sai 'ya 'yan attajirai da wad'anda iyayen su suka kama k'asa sosai suke iya karatu a wannan makarantar a daidai wannan lokacin kuma suka had'u da Faruk. Faruk Wada d'a ne a wurin Ibrahim Wada malamin makarantar islamiya. Mahaifin sa talaka ne lik'is baya da wani jigon wurin da yake samun kud'i sai a islamiyar da yake koyarwa yana da mata d'aya mai suna Saratu da 'ya 'yan sa biyu Faruk da Nasir. Da farko dai Fawaz mahaifin sa yana da kud'in da zai biya masa yayi karatu a kowace makaranta yake so a ciki da wajen Nigeria yayin da Fahad shi kuma mahaifin sa ko kusa bai kamo k'afar mahaifin Fawaz a arziki ba sai dai yayi tasa rawar gani kuma yayi bajinta wurin saka Fahad a wannan makaranta duk da yawan mak'udan kud'in da ake biya a kowace shekara sakamakon Fahad ne kawai d'a d'aya tilo a wajen su shi kuwa Faruk koda za'a sayar da duka kadarorin mahaifin sa to kuwa ba zasu iya biyan koda kashi ashirin bisa d'ari na kud'in wannan makarantar ba Allah ya tsago da rabon sa kan lashe wata jarabawa da yayi abun ya burge wani d'an siyasa a unguwar su har ya d'auki nauyin karatun sa a wannan makarantar.

Fawaz, Fahad da Faruk yara ne kyawawa son kowa k'in wanda ya rasa kansu d'aya, shekarun su d'aya, kuma abunda ya k'ara k'awata su shine kasancewar suna da sunaye da suke kama da juna kuma suke tashi da harafi iri d'aya wato *F*. A daidai wannan lokacin zan iya cewa halayyar su iri d'aya ce suna da son karatu da kuma jajircewa. Fawaz da Fahad, duk da cewa iyayen su sunyi wa mahaifin Faruk fintinkau wurin arziki da wadata ba shi yasa suke nuna masa wata isa ko gadara ba, a yadda suke zaune bashi yasa suka tsame Faruk daga cikin su ba ko kuma suke nuna masa bambancin arziki, lafiya k'alau suke zaune ba zaka tab'a fahimtar haka a tsakanin su ba a haka suka zama abokai UKU sai dai Fawaz da Fahad sun kira kansu da *Abokai* saboda shak'uwar da suka yi ba kad'an bace.

Lokacin da suka shiga s.s2 a lokacin sun fara zama abunda ake cewa manyan yara masu ji da kansu har abokanan su suka basu nicknames na musamman a inda Fawaz ake kiran sa da Fizzy, Fahad Foxy, Faruk kuma Fak kuma daidai wannan lokacin ne halayyar su ta fara sauyawa. Fahad da Faruk suka fara zama tsagera marasa jin magana kullum cikin laifi da kai k'arar su ake a hukumar makaranta, sune fad'a, sune rigima uwa uba wurin sha'anin 'yammatan school d'insu yau kaji sun tab'a k'irjin wannan ko kuma sun danne wannan a cikin aji har aka kai duk wani sabon iskanci to a wurin Fahad da Faruk ake kwaikwayo Fawaz yayi fad'an har ya gaji ya zuba musu ido sai dai ba shine kuma ya raba kansu ba. Suna a s.s2 d'in aka kawo wata yarinya k'arama mai suna Afeefah a jss3. Afeefah Jalal yarinya ce k'arama a lokacin iyakar ta shekara sha hudu ko sha biyar kyakkyawa mai d'an k'aramin jiki itama mahaifin ta gawurtaccen mai arziki ne wanda zan iya cewa ya shafe mahaifin Fawaz a arziki kuma haifaffen jihar Kaduna. Su biyu ne a wurin mahaifin su da ita da Aunty Nana wacce a lokacin take karatu a makarantar lauyoyi (Nigerian Law School) dake a garin Abuja. Sai dai har zuwa lokacin bata yi aure ba tana a gaban iyayen ta. Afeefah yarinya ce mai hazak'a da fikra ta fannin karatu musamman lissafi wato Mathematics, ko a makarantar da ta fito kowace shekara ita ce ta d'aya a sakamakon jarabawa, ta sha lashe kyaututtuka da gasa da sauran su. Koda ta shigo makarantar da wata d'aya labarin ta ya zagaye makarantar baki d'aya, a daidai lokacin ne aka shirya gasa tsakanin ajin su Afeefah da ajin su Fawaz, Foxy da kuma Fak ta fannin lissafi. Da hazak'ar Afeefah (don kuwa tana cikin d'aliban da suka wakilci ajin su) da kuma taimakon Allah suka yi nasara kan 'yan ss2 duk kuwa da cewar da akwai Fawaz a ciki kuma shima ba baya ba wurin kaifin basira, tun daga lokacin zumunci mai k'arfi ya k'ullu tsakanin Afeefah da Fawaz saboda tasu tazo d'aya har gulma ta fara yawo a makaranta ana cewa sonta yake saboda a tarihin Fawaz ita kad'ai ce yarinyar da yake tsayawa suyi magana wanda kuwa ba haka bane su kuma Foxy da Fak kasancewar Afeefah yarinya ce k'arama halittar ta ta 'ya mace bata fara bayyana ba shiyasa al'amarin ta ba damun su yayi ba duk kuwa da kyan fuska da take dashi kai dai ka barsu wurin manyan babies wanda suka amsa sunan su, kai bama Foxy da Fak ba harta sauran mutane ba wanda ya tab'a tunkarar Afeefah a matsayin yana k'aunar ta sai dai fa ta ringa burge mutane a fagen basirar ta.

A haka dai lokaci yayi ta korawa zumuncin Afeefah da Fawaz kullum sai dad'a k'ara k'arfi yake suka kira kansu da *Abokai* yayi mata lak'ami da Brainy ita kuma take kiran shi da Oldie, don dole tasa Foxy da Fak suka fara kula Afeefah saboda yadda Fawaz ya damu da ita suna tsayawa su gaisa, a d'an tab'a hira da sauran su. Ana haka ne su Fawaz suka fara rubuta jarabawar su ta k'arshe a cikin makarantar wato SSCE, tun daga lokacin yaran hud'u ba wanda yake farin ciki da hakan. Ta fannin Fawaz dalili shine shi kad'ai mahaifin sa ke jira ya k'ark'are rubuta jarabawar su bar garin Kaduna baki d'aya zuwa Abuja wanda yake nuna dole zai bar babbar k'awar shi wato Afeefah da kuma rashin babban abokin sa wanda tun da aka haife su basu tab'a rabuwa ba wato Foxy da kuma Fak, duk sanda ya tuna haka sai yaji a ransa ina ma ache ba sune ke rubuta wannan jarabawar ba. Shi kuma Foxy kewar sa shine mahaifin sa ya samu tallafin k'aro karatu zuwa k'asar waje (United Kingdom) kasancewar shi malamin makaranta dole sai da fad'ad'a ilimi, shima dai Foxy a tak'aice shi kad'ai mahaifin sa ke jira ya gama rubuta jarabawar sa wanda kuma zai yi daidai da tafiyar sa sai su tafi gaba d'aya, shima idan ya tuna cewar zai bar Fawaz babban abokin sa da Fak abokin shashancin sa a makaranta da kuma babies d'insu ya koma wata nahiyar ta daban wurin da baisan kowa ba wannan abun ba k'aramin bak'an ta masa rai yake ba. Shi kuma Fak tasa kewar ta bambanta da ta saura saboda ba cigaba zai samu a rayuwar sa ba sai ma ci baya, saboda da sun kammala jarabawar su to kuwa bai san fate d'in shi ba, d'an siyasar da yake d'auke da nauyin karatun shi siyasar ta k'wala shi a k'asa ya tabbata da ya gama secondary school d'in to fa ba batun cigaba zai koma gida ne kawai ya cigaba da zaman banza, gashi ya saba rayuwa cikin 'ya'yan masu kud'i bai san ya rayuwar shi zata kasance ba idan Foxy da Fak dukansu suka bar Kaduna da tarin 'yammatan shi wanda a duk safiyar Allah k'aryar mahaifin sa mai arziki ne yake shata musu shima dai wannan abun ba k'aramin ci masa tuwo a k'warya yake ba. Gefen Afeefah kuma ba abunda yake damunta sai rashin Oldie'nta da zata yi bama a makaranta ba a gari baki d'aya saboda sunyi matuk'ar sabo da juna.

A haka dai suka cigaba da zana jarabawoyin su har wannan rana da suke ta zullumi tazo, a ranar su hud'un sunci kuka wane ransu zaya fita ba zan iya cewa ga wanda yafi wani bak'in ciki ba a cikin su. Bayan sun fito daga jarabawar su ta k'arshe kai tsaye Fawaz ya d'auki Foxy da motar sa ya kaisa Airport a inda iyayen sa suke jiran sa, minti goma bayan isar su aka kira passengers alamar tafiya ta tashi, sun yi bankawana da juna kowanen su da ka kalle shi zaka hango damuwa k'arara a tattare dashi, Fawaz bai bar Airport d'in ba har sai da jirgin su Foxy ya d'aga zuwa Abuja daga Abuja kuma zuwa UK sannan ya koma ya ja motar shi cike da sanyin jiki da rashin k'warin gwiwa ya koma makaranta a inda murnar k'are jarabawa ke cigaba da gudana. A nan ma yayi bankawana da Afeefah wanda har ta kai shi ga zubda hawaye sakamakon kukan da take na rabuwar su, da k'yar da sud'in goshi Fawaz ya gamsar da ita akan cewar basu rabu suna nan tare ya karb'i number wayar ta da kuma ta sauran Abokai sannan suka k'ara yin sallama ya ja hannun Fak suka shiga mota suka fasa suka bar Liberty International Schools. Tafe suke a cikin motar Fawaz ke ja amma kai ka rantse da Allah ba mahaluk'i a ciki sun yi tsit kowa da kalar tunanin da yake da haka har suka iso unguwar su Fak. Fawaz ya shiga har cikin gidan yayi wa iyayen Fak bankawana suka shiga sa masa albarka kuwa da fatar masa alkhairi a ko ina sannan suka fito a nan ne kuma suka k'ara yin sallama, Fak yaso ya nemi wani abu daga Fawaz sai dai bai yi magana ba saboda ba wannan ne lokacin da ya dace yayi maganar ba da haka suka rabu da Fak shima ya koma gida washegari suka d'aga zuwa Abuja. Tun ranar da suka shiga garin Abuja kewar abokanan shi da Afeefah suka dawo masa sabbi fil, lokacin ne ya fahimci k'aunar Afeefah yake ba wai k'awance bane kamar yadda ita take tunani. Duk da cewa akwai tazara a tsakanin su, a haka suka cigaba da kasancewa tare a kafofin sadarwa da yanar gizo duk lokacin da basa da wata hidima a gaban su to wad'annan bayin Allah suna tare suna ji daga junan su. Fawaz ya cika form na zaunawa jarabawar share fagen shiga jami'a wato Jamb Allah ya bashi nasara ya samu sakamako mai kyau yayin da Foxy kuma ya samu admission a k'asar waje a tsangayar karatun ilimin kimiyya wato Faculty of Sciences a inda yake karantar Chemistry. A daidai wannan lokacin ne Fawaz ya shirya kai wa Afeefah da Fak ziyarar ba zata a Kaduna don basu mamaki, ba tare da sanin su ba ya kama hanyar Kaduna har ya isa ya nufi gidan su Fak sai dai sabuwar rayuwar da ya riski Fak a ciki ta matuk'ar sosa masa rai, Fak a lokaci k'ank'ani ya sauya ya zama d'aya daga cikin 'yan iskan gari wato Area Boys lokaci kad'an ya koyi shaye-shaye a tak'aice dai Fak ya sauya baya da wani aikin yi ko wurin zuwa sai zaman banza a bakin hanya, Fawaz sai da ya zubar da hawaye bai tab'a tsammanin yadda Fak ke gaya masa a waya cewa rayuwa ta sauya masa abun yayi tsanani haka ba harta suturar kirki Fak bayi da sai da Fawaz ya d'auki mafi yawan suturar da yazo dashi ya bashi ya saka shi kuma ya chanza sannan ya d'auke shi suka nufi gidan su Afeefah. Tayi mamaki kuma tayi murnar kuma taji dad'in ganin Fawaz lokacin da bata tab'a sa tsammanin zata ganshi ba shima haka, Afeefah tana nan ba abunda ya chanza tattare da ita haka suka kirawo Foxy a waya akayi hira sakamakon an had'u shi kad'ai ne baya nan suka kuma sha hotu na aka masa sharing. Kwana uku Fawaz yayi a garin Kaduna a gidan su Fak, duk da cewar ya sha alwashin duk ya shigo garin Abuja sai ya je wurin abokanan su da suka yi Liberty tare duk wannan burin da yaci ganin Afeefah ya shafe shi don kuwa koda yaushe suna tare har wa'adin da ya d'iba ya cika suka yi sallama. Duk da cewar wannan ma rabuwa ce bata kai ga wancan lokacin zafi ba kuma Fawaz ya tabbatar mata abunda yake nanata mata a koda yaushe gaskiya ne wato basu rabu ba ta gefen Fak kuma ya bashi kud'i masu d'an yawa sakamakon a kowane k'arshen wata mahaifin sa yana masa albashi fiye da wani babban ma'aikacin gwamnatin tarayya da haka suka rabu ya koma Abuja cike da kewar Afeefah da Fak.

*By Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *March, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*02*

Fawaz ya koma Abuja da jimamin rayuwar da ya bar abokin su a ciki wato Fak, har ya isa garin Abuja abinda ke d'awainiya dashi kenan kuma ya k'udurta a ransa zai taimaki Fak. Ya labarta ma iyayen sa komai suma basu ji dad'i ba Fawaz ya gayawa mahaifin sa cewar wata shekara zai yi k'ok'arin sayawa Fak takardar cikewa ta zaunawa zana jarabawar share fagen shiga jami'a wato Jamb kasancewar wannan shekarar ta wuce, iyayen sa sunyi na'am da wannan shawarar ya kuma tuntub'i Foxy dake k'asar waje yaya ya gani had'i da koro masa labarin rayuwar da ya riski Fak a ciki shima yace hakan yayi daidai ana haka ne Fak ya nemi Fawaz da ya taimaka masa ta kowane gefe ne nan take ma Fawaz ya zayyana masa komai dangane da k'udurin da yake dashi, ai kuwa Fak da iyayen sa sun ji dad'i sosai suka shiga saka wa Fawaz da iyayen sa albarka. Admission ya fito Fawaz ya samu gurbin karatu a Baze University Abuja dake a garin Abuja a inda zai karanci Petroleum Engineering, Foxy, Fak da Afeefah duk sun taya shi farin ciki cikin sa'a ya fara karatun sa lafiya k'alau. Zan iya cewa kowa yasan yadda rayuwar jami'a da had'arin dake akwai a cikin ta yake a wannan lokacin, duk da cewa Baze University jami'a ce ta kud'i sai 'ya 'yan masu kud'i ke iya karatu a ciki wannan abun bai rud'i Fawaz ya chanza daga abunda ya kai shi ba wato karatu. Idan muka koma gefen Foxy wanda yake a UK zance labarin daban ne, ba wani karatun azo a gani yake ba duk da mahaifin sa yana kwad'aice da hakan kasancewar sa d'an boko. Foxy ba abunda yake sai shek'e ayar sa da 'yammata jajaye da bak'ak'en fata a tak'aice rayuwar sa ta jin dad'i tafi rinjaya kan karatun sa, iyayen ba wani tsawata masa sosai suke iya yi ba saboda ya fara fin k'arfin su dama anche icce tun yana d'anye ake lank'wasa shi a nan ne ya koyi shan barasa kamar ruwa.

Shekara ta sake zagayowa Fawaz da kansa ya saya wa Faruk form na Jamb aka yi komai ranar rubuta jarabawa tayi ya rubuta aka kuma yi nasara yaci aka zauna jiran admission. Ba da jimawa ba aka yi releasing admission ya samu gurbin karatu a makarantar da Fawaz ke karatu wato Baze University dake garin Abuja a inda zai karanci Physics, kowa daga cikin su yayi farin ciki da fatar masa sa'a musamman iyayen sa a nan ya tattara ya dawo garin Abuja a gidan su Fawaz. Komai da ya danganci Fak Fawaz ne ke d'auke da nauyin don kuwa yana da kud'in da zai iya d'aukar nauyin irin Fak biyar ba tare da yaji wani abu ba. A daidai wannan gab'ar ne mahaifin Fawaz yaji ya k'osa da zaman sa a Abuja kuma a lokacin yayi girma sosai a kasuwancin sa duk yaran sa ne ke tafiyar da sha'anin kasuwancin, wannan dalilin yasa ya yanke shawarar komawa mahaifar sa wato Kaduna don ya samu ya huta daga tafiye-tafiye da zirga-zirgar da ya sha, cikin k'ank'anin lokaci kuwa suka shirya komawa Kaduna aka bar Fawaz da Fak a gidan Ammi k'anwar mahaifin Fawaz. Ammi tana da kirki sosai kuma tana da 'ya d'aya tal mai suna Zuhra 'yar kimanin shekara ashirin da d'aya wacce ta dad'e tana dakon soyayyar Fawaz. Mahaifin Zuhra ya dad'e da rasuwa ya bar musu dukiya mai tarin yawa ita da mahaifiyar ta yayin da mahaifiyar take aiki a babbar hedkwatar FIRS dake a birnin Abuja ita kuma Zuhra tana karatu a Baze. Duka-duka basu yi wata d'aya a gidan Ammin ba Fawaz ya samu wani gida suka koma bayan d'aukar 'yan kallo da suka yi da Ammin don sam bata so komawar su gidan ba shi kuma Fawaz ya nace akan zai fi karatu idan yana nesa da gida.

Sun koma gidan madaidaici da farko idan ka shigo zaka sami parking lot mai d'aukar mota uku da wurin hutawa da kuma tennis court idan ka shiga daga ciki zaka sami wani babban parlor da bedroom uku a ciki kowane da toilet d'insa a ciki, gidan ya tsaru ba wata hayaniya haka Fawaz da Fak suka koma a ciki. Karatu suke ba wasa musamman Fawaz ba ruwan sa da al'amarin party, mata, shaye-shaye irin na matasan wannan zamani shi dai boko kawai ya saka a gaba, yayin da Fak kam shaye-shayen bai barsa ba haka mu'amala da mata kamar yadda suka saba a Liberty, ba zai k'ulla wata d'aya a garin Abuja ba tare da yaje Kaduna ya halarci party ko wani bikin shashanci ba kuma kullum abun nasa gaba yake yi da Fawaz yayi magana yanzu zai hau masifar shi ba k'aramin yaro bane. Matsalar Fak zan iya cewa tana kama da matsalar Foxy wanda yake a UK sai dai kuma a wani gefe sun bambanta. Foxy womanizer ne na k'arshe yayin da Fak sha'anin mata bai dame sa ba sosai tun sanda yayi dating wata yarinya da yake masifar so daga k'arshe tayi auren ta ta barshi tun lokacin ya fita sabgar mata sai idan yana da bukata, shi dai ka barsa da saka kansa a cikin 'ya 'yan masu kud'i da shaye-shayen tsadaddun abubwan maye wanda Fawaz ne ke bada kud'in ko yak'i ko yaso yayin da Foxy shi kuma yana shaye-shayen sai dai ba kamar Fak ba.

Tafiya tayi tafiya shekaru sun haura har an wayi gari Fawaz yana a shekara ta hud'u a karatun sa yayin da Foxy da Fak suke a shekara ta uku, dukansu sun girma sun zama wasu zaratan mazaje kamar ba teenagers da suka gama Liberty International Schools shekara hud'u da suka gabata ba. A cikin wannan lokacin ne mahaifin Afeefah ya dawo Abuja ba don komai ba sai saboda Afeefah dalili kuwa tana a s.s2 ta rubuta jarabawar kammala secondary school kuma ta shafawa idanun ta toka ba makarantar da take so sai Baze University Abuja, ba yadda bai yi ba kan ta zab'i kowace makaranta take so a k'asashen k'etare don tayi karatun ta a chan amma ta kafe sai Baze, mahaifin Afeefah yana ji da ita sosai kuma ba zai barta ko kusa ta zauna a campus ba ko kuma tayi zaman kanta a Abuja da sunan karatu wannan dalilin ne yasa ya kwashe su suka koma Abuja ga baki d'aya saboda kurum karatun Afeefah a inda itama ta samu admission tana karantar lissafi ma'ana Mathematics wato gefen da tafi gogewa kenan kuma tana a shekarar ta ta biyu, zo kaga murna gun Fawaz lokacin da Afeefah ta dawo Abuja abun ba'a cewa komai ana haka kuma suka yi waya da Foxy yake masa albishir da mahaifin sa ya kammala karatun da ya kai shi a UK saboda haka zasu dawo Nigeria ya kuma bashi zab'in kowacce makaranta yake so ya k'arisa karatun sa a inda ya zab'i Baze Abuja, dad'i wane ya kashe Fawaz da Fak saboda dawowar Foxy wanda yake nufin gang shit continues.

*By Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *March, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*03*

_8:30am_ Fawaz ne cikin d'akin sa kwance akan gado ya duk'unk'une yana bacci, Fak ne ya turo k'ofar d'akin ya shigo cikin shigar k'ananan kaya wanda yake nuna da alama fita zai yi, k'arasowa yayi bakin gadon sai karkad'a keys d'in mota yake yasa hannu ya fisge blankets da Fawaz ya rufa dashi wanda yayi displaying kyakkyawan halittar sa. Fawaz farin ingarman namiji ne bakomai a jikin sa sai gajeren wando wanda ya gagara rufe dogayen k'afafun sa a inda gashi ne kwance ya k'awata fatar sa, fuskar sa d'auke take da manyan idanu da dogon hanci da madaidaicin baki tare da kyakkyawan sajen sa a kwance da d'an gajeren gemun sa, broad chest da broad shoulders d'insa nan ma duk gashi ne ya rufe su ga muscles da packs sun firfito wanda yake nuna jikin ya sha gym har ya gaji a tak'aice dai Fawaz ginanne kuma kyakkyawan namiji ne wanda sam jikin sa ba zai tab'a determining shekarun sa ba. Da farko idan ka ganshi zaka ce zai kai talatin saboda irin k'irar halittar sa ta mazantaka da tayi saurin bayyana alhali kuwa shekarun sa duka ashirin da uku a duniya. Wani gurnani yayi lokacin da Fak ya fisge masa blankets had'i da yin mik'a ya juya daga kan b'angaren hagu da yake kai zuwa b'angaren dama ya bawa Fak baya, d'an zama Fak yayi kan gadon cikin husky voice nasa yace "Kai d'an iska wake up mana!" sai da aka d'auki seconds haka sannan cikin muryar bacci Fawaz yace "Yane har ka shirya kenan?" "Eh mana kai ba zaka fita bane?" cewar Fak, mik'a Fawaz ya sake yi ya juyo cike da kasala yana kallon Fak da ka kalli idanun sa kasan baccin bai sake sa ba yace "No, bani da lectures yau." k'aramin tsuki Fak yaja had'i da mik'ewa tsaye yace "No wonder kake kwanciyar ka kana bacci." sannan ya d'ago agogon hannun sa yana dubawa ya k'ara da cewa "I'll get going ina da morning lecture." gyad'a kai Fawaz yayi idanun sa a lumshe yace "Right, sai ka dawo." juyawa Fak yayi zai bar d'akin har ya kai bakin k'ofa ya juyo yace "Yauwa! K'arfe nawa ne jirgin su Foxy zai yi landing?" har yanzu idanun Fawaz a rufe suke yace "K'arfe goma sha d'aya." a tak'aice kuma cike da kasala, dariya Fak yayi ya bud'e k'ofar ya fita yana cewa "Foxy baabaa! I can't believe wannan tsohon d'an iskan zai dawo." duk da cewa idanun Fawaz a rufe suke amma zaka iya hango murmushi da ya bayyana a fuskar sa sakamakon maganar k'arshe da Fak ya fad'a, haka ya jawo d'aya daga cikin pillows dake kan gadon ya k'ank'ame ya cigaba da baccin sa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull