Abokaina complete book 1 - Chapter 2
Abokaina complete book 1 Chapter 2: Abokaina complete book 1 Chapter 2. _10:30am_ Ba shi ya tashi daga baccin ba sai k'arfe goma da rabi na safe da k'yar…
3,668 words
_10:30am_ Ba shi ya tashi daga baccin ba sai k'arfe goma da rabi na safe da k'yar ya iya barin gadon ya sauko ya nufi toilet, wanka yayi ya fito murmushi kwance kan fuskar sa kamar wanda aka yiwa bushara da wani abu mai mahimmanci a rayuwar sa da haka cikin sauri-sauri ya shirya tsaf cikin k'ananan kaya t-shirt ce mai wasu black stripes sai jean sai black loafers da ya saka a k'afar sa yayi kyau sosai musamman d'an gajeren gemun sa da ya k'awata fuskar sa. Ruwa yasa a k'aramar heater a cikin d'akin nan take suka tafasa ya had'a lipton ya zauna bakin gadon ya fara sha yana wasa da keys d'in motar sa har yanzu murmushin dake kan fuskar sa ya kasa gushewa, yana gama shan lipton d'in ya kwashi wayoyin sa guda biyu da glasses d'insa ya nufi hanyar fita. Fitowa parlor yayi wanda yake a gyare tsaf ba wata hayaniya ballantana k'azanta kamar ba maza ne a ciki ba, wani yaro ne d'an kimanin shekara goma sha tara zuwa ashirin ya shigo parlor'n, juyowa Fawaz yayi yana kallon yaron yace "Ah Ibro har ka shigo?" (Ibro shine amintaccen yaron da yake musu 'yan aikace-aikace a gida da duk wani aika) washe baki yaron yayi had'i da cewa "Na shigo Oga an tashi lafiya?" "Lafiya k'alau." cewar Fawaz sannan ya saka hannu a aljihu ya ciro kud'i ya had'a da wasu keys ya mik'awa yaron sannan yace "Gashi ka d'an k'ara gyara gidan please kuma ka gyara d'ayan bedroom d'in yau zanyi bak'o babban aboki na zai dawo." "Ma shaa Allah! Allah ya kawo sa lafiya Oga." murmushi ya k'ara bayyana a fuskar Fawaz yace "Ameen" ya duba agogon hannun sa sannan ya kalli Ibro yace "K'araso ka fara aikin ka mana ni zanje airport." ya k'are maganar yana tafiya zai bar parlor'n, cike da girmamawa Ibro yace "Toh sai ka dawo, Oga Fak baya nan ne?" "Bakowa a gidan fa shima yaje school" "Toh sai ka dawo" "Aha" cewar Fawaz had'i da ficewa parlor'n, yana fitowa waje ya kafa dark glasses a fuskar sa ya nufi wata mota k'irar Hamann Mystere launin Gold sabuwa dal sai shek'i da walwali take mai d'auke da license plate mai sunan *Fizzy* a jiki, bud'e motar yayi ya shiga nan take yayi kicking yaja ya bar gidan.
*Nnamdi Azikwe International Airport, Abuja.* Fawaz ne a tsaye a cikin filin saukar jirage na Nnamdi Azikwe dake a garin Abuja a sashen tarbar matafiya yana kallon hanyar da suke shigowa. Tsaye yake ya zura hannun sa d'aya a aljihu d'ayan kuma yana rik'e da shafceciyar wayar sa sai kai komo yake a wurin. Hango su yayi tafe suna hira suna raha gwanin sha'awa shima ba tare da jinkiri ba ya nufi wurin su fuskar sa d'auke da lallausan murmushi, sai a lokacin suma suka shaida sa suka k'araso dukansu cike da fara'a, cire glasses d'insa yayi ya rusuna daga gefen mahaifin Foxy yace "Sannun ku da zuwa Abba." ya k'are maganar yana karb'ar k'aramar jakar dake hannun mutumin, murmushi mutumin shima yayi yace "Yauwa Fawaz! Kana lafiya?" "Lafiya k'alau Abba." sannan ya juya ya gaida mahaifiyar Foxy itama cikin sakin fuska da fara'a ta amsa masa had'i da tambayar sa yana lafiya yace k'alau. Mik'ewa tsaye yayi ya kalli Foxy d'an gayun gaske duk da cewa Fawaz ya fice Foxy da tsayi da kuma haske amma duk da haka shima kyakkyawa ne cikin shigar k'ananan kaya, mik'a masa hannu Fawaz yayi alamar gaisuwa in a manly manner yace "My bad." harara Foxy ya dallawa Fawaz tukuna sannan ya mik'a masa hannu yace "Kai dan uban ka I've been calling you kak'i kayi picking ko?" d'an dariya Fawaz yayi arrogantly sannan yace "Sorry bana tare da wayar ne, anyway it's good to have you here ba wai nayi missing d'inka bane I'm only here to welcome my parents." dariya iyayen Foxy suka yi lokaci d'aya sannan mahaifin Foxy'n ya kalli agogon hannun sa ya kalli Fawaz yace "Fawaz don't mind this stubborn muje driver ya dad'e da zuwa." "Toh Abba." cewar Fawaz, sannan suka shige gaba dashi da Foxy yayin da iyayen suke daga baya har zuwa wurin da driver yake jiran su yayi musu sannu da zuwa had'i da karb'ar luggage d'insu ya saka a mota. Juyowa mahaifin Foxy yayi ya kalli Foxy'n yace "Fahad zamu tafi, please bana so naji wani shashanci daga wurin ka kaji ko?" jinjina kai Foxy yayi yana sosa bayan kansa yace "In shaa Allah Abba." "Kaima haka Fawaz duk da dai kai ba irin sa bane, the least I expect from you guys is second class." cewar Abba, murmushi Fawaz yayi shima yace "In shaa Allah Abba za'a kiyaye." sannan suka yi sallama tare da fatar musu Allah ya kiyaye suka hau hanya zuwa Kaduna. Fawaz da Foxy basu d'aga daga wurin ba sai da suka ga tafiyar su sannan Fawaz ya rik'o ma Foxy luggage d'insa suka nufi wurin tashi motar, bud'e motar Fawaz yayi ya saka luggage na Foxy a ciki sannan ya kalle sa yace "Muje." kallon motar Foxy yake cike da tsintsar mamaki da sauri ya juyo yana kallon Fawaz yace "Fizzy kana buroba yanda kake so wallahi! Hamann? What a ride!" dariya kawai Fawaz yayi ya bud'e motar gefen driver ya shiga shima Foxy ya bud'e front seat ya shiga nan take Fawaz yayi kicking motar yaja suka bar wurin.
Hirar yaushe rabo kawai suke sai a lokacin Foxy ya tuna wani abu ya kalli Fawaz yace "Wai ina d'an iskan nan ne? Don uban shi ba zai zo ya tarbe ni ba kenan?" ya k'are maganar yana danna wayar sa, kallon titi kawai Fawaz keyi yana driving cike da k'warewa yace "Waye? Fak kake magana? Yaje school he has a serious morning lecture amma..." ya d'ago agogon hannun sa yana dubawa sannan ya cigaba da cewa "Ina tunanin ya koma gida yanzu." cike da mamaki Foxy yace "Buroba! When did that idiot become so serious like that har yana attending serious lectures?" dariya Fawaz yayi yace "Forget, Fak is a changed person now." dariyar rainin hankali Foxy yayi yace "Ni kake gayawa that idiot is a changed person? Not if I know Fak, kasan me ma?" girgiza kai Fawaz yayi yana dariya k'asa-k'asa yana driving, in between laughter Foxy yace "Was it day before yesterday ne naga yayi posting wani pic in complete Kaftan da hula da babbar riga but guy da ka kalli idon shegen kasan he's over drunk, I asked him mutumi na ya da Kaftan kuma yau kasan me yake gayamin?" har yanzu sai dariya Fawaz keyi don kuwa yasan halin Fak sarai, cikin dariya Foxy yace "Wai shege daga masallacin juma'a yake!" dariya suka fashe at once Foxy ya k'ara da cewa "Kai! Wallahi Fak shegen gaske ne, ni dai ne yanzu I'm a changed person, holy Ustaz Alhaji!" ya k'are maganar sai giggling yake wa Fawaz, harara Fawaz ya jefe sa dashi yace "Wai ni kake gayawa you are a changed person now?" "A'a uban ka nike gayawa." "Better, tell that to the birds." cewar Fawaz, dariya Foxy yayi yace "Allah yasa gidan naku da akwai abinci I'm damn hungry." ko kallon sa Fawaz bai ba yace "K.C kawai" gajeren tsuki Foxy yaja yace "Dallah Fizzy kayi zance na yunwa nike ji seriously wallahi!" share sa Fawaz yayi ya cigaba da driving d'insa disdainfully dama halin sa ne sai ana tsakiya da magana sai yayi shiru ya share mutum, mamaki ne ya kama Foxy yace "Buroba! Ni kake sharewa? Dad'in abun I'm mad as hell kafi kowa sani." yana gama fad'ar haka yasa hannu ya juya steering motar nan take motar ta fara juyawa round, a tsorace kuma cikin zafin nama Fawaz ya ture sa da k'arfi ya samu yaci kan motar ya maida ta kan titi Allah ya taimaka ba mota a gaba da kuma bayan su sannan ya juyo ya kalli Foxy dake ta k'yalk'yala dariya yace "Kashe mu kake so kayi?" "Yeah it will be fun idan muka mutu tare, now tell me ina zamu ci abinci?" cewar Foxy, shafa gajeren gemun sa Fawaz yayi da d'aya hannun sa d'ayan kuma yana rik'e da motar cikin matsanancin gudu yace "Muje gidan Ammi dama na dad'e banje na gaida ta ba." sai a lokacin Foxy yayi resting kan kujerar motar yace "Better!" haka sukai ta hira cike da raha da barkwanci irin ta abokai har suka iso unguwar Maitama a wani tangamemen gida naji na fad'a.
*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *March, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*04*
Kutsa kai Fawaz yayi cikin gidan wanda ya gama had'ewa cif, parking yayi suka fito lokaci d'aya suka nufi hanyar da zata sada ka da babban parlor'n gidan. Door bell Fawaz ya danna basu yi minti biyar ba sai ga Zuhra tazo ta bud'e. Ba laifi Zuhra tana da kyau kuma tana da tsayi amma ba sosai ba cikin doguwar riga na material kalar ja kanta ba d'ankwali, ganin Fawaz yasa ta saki wani lallausan murmushi ta saki k'ofar tazo ta rungume sa, b'ata fuska Fawaz yayi ya ture ta daga cikin jikin sa ya had'e fuska tam sai ka rantse da Allah bai san ya ake dariya ba "Zuhra me haka? Yaushe zaki hankali ne? Ki ta wani shiga jikin mutum kamar mage." jikin ta ne yayi sanyi da maganganun Fawaz ta saukar da kanta k'asa hawaye suka d'an ciko idonta, dariya Foxy yayi yace "Don't mind him Zuhra, tsoro yake kada ki turning d'insa." ya gama maganar yana kallon Fawaz yana dariyan mugunta, da k'arfin gaske Fawaz ya juyo yana kallon Foxy cikin had'e fuska yace "Waye zai turning d'ina? Wannan abar? God forbid bad thing!" tintsirewa Foxy yayi da dariya dama yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, dariya yake yana bubbuga kafad'ar Fawaz yace "Shege mutumi na! Kace dai it was still the same guy; babes meant nothing to him." wani murmushin gefen baki Fawaz yayi sannan ya cire glasses d'in fuskar sa ya kalli Foxy da kyau yace "Every guy is interested in a babe it depends on the babe." dariya Foxy ya k'yalk'yale suka tafa yace "Fizzy ma guy!" kallon Zuhra Fawaz yayi wanda hawaye ya dad'e da wanke mata fuska sakamakon cin fuskar da Fawaz yai mata a gaban abokin sa "Ina Ammi?" ya tambaye ta yana k'are mata kallo, sai da ta fara goge hawayen da suka gangaro mata tukuna sannan cikin murya mai sanyi tace "Tana sama." "Jeki ki kira ta." ya fad'a a tak'aice had'i da kawar da kansa daga kanta, a sanyaye ta juya ta nufi saman yayin da Foxy yabi bayan ta da kallo then back to Fawaz yace "Kai banza ne wallahi, ba kyau kushe mutum fa ji yanda mood d'inta ya chanza all of a sudden." "Is it an offence don na fad'i gaskiya? Zuhra bata daga cikin sahun matan da zasu iya turning d'ina." "It's not but kasan dai ba dad'i wallahi, gashi ka kore ta ko gaisuwan kirki bamu yi ba." "Kai kasan wannan." cewar Fawaz ya k'arisa cikin parlor'n ya samu wata lintsimemiyar kujera ya zauna Foxy ma haka basu dad'e da zama ba sai ga Ammi tana saukowa daga upstairs, da sauri Fawaz ya tashi ya nufi wurin ta suka yi hugging junan su da fara'a kwance kan fuskokin su, breaking hug d'in Ammi tayi tana kallon Fawaz tace "Fawaz yau kaine a gidan nan ko dai b'atan kai kayi ne?" dariya yayi hannun sa a cikin nata yace "Ammi mutum da gidan su zai yi b'atan kai kuma?" "Eh mana ai ka k'i ni ne, sam ka d'auke k'afar ka daga gidan nan ko wani abun akai maka?" soke kai k'asa yayi yana dariya bai ce komai ba, jawo hannun sa tayi suka nufi d'aya daga cikin kujerun parlor'n tana cewa "Ai kuwa yau sai ka gayamin dalilin da yasa baka zuwa gida na." yanzu kam ba Fawaz kad'ai ba harta Foxy dariya yake, cikin sound na dariya Fawaz yace "Wallahi Ammi karatu ne ke hana ni zuwa." har yanzu rik'e take gam da hannun sa tace "Karatu ya tab'a hana ko ya kori wani daga gidan su?" sannan ta juyo ta kalli Foxy suka gaisa tace "You'd be surprised idan na gaya maka ina a matsayin mahaifiyar sa kuma ina zaune a cikin garin Abuja yaje yayi lodging a wani wuri, da nayi magana sai yace karatu, karatun nan kamar akan sa aka fara shi a dole ga jikan Mango Park wallahi wani zubin ma sai ni nike shiryawa naje na gansa har gidan nasa idan na damu." murmushi Foxy yayi yace "Ai Ammi baya da kirki ko kad'an wallahi." dariya Fawaz ya kece da ita don da alama ya fahimci Ammi bata gane Foxy ba "Ammi ba dai tsufa yazo ba, don't tell me baki gane Foxy ba." sake hannun Fawaz Ammi tayi ta tsaya sororo tana kallon Foxy ta nuna sa da yatsa "Fahad ne wannan?" dariya suka fashe ga baki d'ayan su Fawaz yace "Shine" "Yaushe ka dawo?" ta tambaye sa cike da mamaki "Yanzun nan ma daga airport Fizzy ya d'auko ni." "Allah sarki!" cewar Ammi, da murmushi Fawaz yace "Ai Ammi sun dawo Nigeria baki d'aya ma." "Toh karatun shi fa?" "Yayi switching zuwa nan Baze University." "Ma shaa Allah! Allah yayi jagora but please a dage a bada himma sosai, karatu yana buk'atar a lot of sacrifices and dedications." jinjina kai suka yi lokaci d'aya suka ce "In shaa Allah Ammi." "Yanzu da Fahad ya dawo za'a k'ara mantawa dani kenan." cewar Ammi, mik'ewa tsaye Fawaz yayi sannan yace "Haba Ammi wai wanne d'an kirkin ne kika ga ya tab'a mantawa da uwar sa?" "Hmm kaji fa kamar duka kenan, nasan daga yau idan ka saka kai ka bar gidan nan barin sake ganin ka ba ba mamaki ma sai wani k'arnin." Fawaz yana jinta ya share don yasan halin Ammi ko yaron goye ya bata lafiya wurin k'orafi da mita, dining ya k'arasa yana dudduba warmers dake wurin yace "Ammi da akwai abinci a gidan nan kuwa? Yunwa muke ji." tafa hannu Ammi tayi tace "Haba! Ai ni nasan banza ba zata kai zomo kasuwa ba, ashe yunwa ake ji shiyasa aka tuna Ammi." Fawaz dai yana jinta ya share ya shiga serving musu abincin dashi da Foxy yayin da tsakanin Ammi da Foxy sai hira ke gudana wacce ko kanzil Fawaz bai ce musu ba. Foxy ne ma yaci abincin da yawa shi kam Fawaz kad'an yaci yace ya k'oshi da haka sukai ta hira wacce rinjayen hirar tsakanin Foxy da Ammi ne Fawaz yayi shiru sai danna wayar sa yake. Sun fi awa d'aya a gidan sannan suka ce zasu tafi Ammi ta rako su har bakin mota Fawaz yana ta zuba ido ko zai ga Zuhra tazo yi masu sallama amma shiru shima bai neme ta ba kuma bai kawo komai a ransa ba suka yi sallama da Ammi suka tafi. A hanya sai hirar su suke cikin nishad'i Fawaz sai wani dad'i na musamman yake ji dalilin dawowar Foxy da haka har suka iso gida. Bayan yayi parking a cikin gidan ne suka fito suka shiga parlor'n wanda Ibro ya gyara shi tsaf kuma sakamakon ganin sa da suka yi a bud'e ya tabbatar musu Fak ya dawo daga school, fad'awa Foxy yayi kan sofa da gani a gajiye yake yayin da shi kuma Fawaz ya zauna daga kusurwa kan wata sofa, cikin d'aga murya Fawaz ya fara kiran "Fak! Fak!!" daga cikin d'akin suka jiyo muryar Fak yace "Yane wai?" "Fito don uban ka!" cewar Foxy, dariya Fak yayi daga cikin d'akin yace "Duuudeee! Ka diro kenan." "A'a ina a iskan dai." bai gama rufe baki ba sai ga Fak ya fito daga d'aya daga cikin d'akunan gidan bakomai a jikin sa sai boxer da wata killer shirt hannun sa rik'e da wata kwalba wacce nike kokwanto giya ce a ciki, tun daga nesa ya fara wailing Foxy da hannu a gayince yana fad'in "Foxy baabaa!" mik'ewa Foxy yayi tsaye shima yana dariya yace "What's up big dog?" sai kallon juna suke tun daga nesa Foxy ya k'ara da cewa "Shege Fak mutumi na! Nayi missing d'inka wallahi!" dariya Fak yayi ya k'araso parlor'n suka tafa had'i da rungume juna in a manly manner sannan Fak yayi breaking hug d'in sai bin Foxy da kallo yake yace "My bad, you're looking good UK ta karb'e ka fa." wani shed'anin murmushi Foxy yayi irin na 'yan duniya ya koma ya zauna akan sofar da ya tashi yace "Ba UK bace, chicks na UK ne." dariya Fak yayi ya zauna kan hannun kujerar da Foxy ke kai yace "D'an iska a haka zaka k'are ai." "Thank goodness ba a d'an giya zan k'are ba." cewar Foxy yana kallon kwalbar giyar dake hannun Fak "Toh waye d'an giyar?" "Kai mana don uban ka!" duk hirar da suke Fawaz na jinsu ko uffan bai ce ba hasali ma ko d'ago kai bai yi ya kalle su ba, karb'e kwalbar giyar Foxy yayi yana duba ta yace "Wacce iri ce?" gyatsar giyar Fak yayi sannan yace "Tequila, you know Tequila is love." without a second thought Foxy ya d'aga kwalbar giyar ya tittilawa timbin sa sannan ya saukar da kwalbar yace "Yeah Tequila is love." sannan ya kalli Fawaz yace "Fizzy!" d'ago kai Fawaz yayi yana kallon su da abunda suke ciki bai ce komai ba amma a k'asan zuciyar sa kamar an hura wuta ne saboda ya tsani rayuwar da abokanin sa keyi, mik'a masa kwalbar giyar Foxy yayi had'i da cewa "Here!" sai da Fawaz ya gama watsa masa banzan kallo sannan ya saukar da kansa akan wayar sa ya cigaba da abunda yake ba tare da ya tankawa Foxy ba, juyowa Foxy yayi ya kalli Fak yace "This asshole ya gagara wayewa huh?" sai da Fak ya k'ara kwankwad'ar giyar sa sannan yace "Ka dai gani, I've been trying my best but all in vain." mik'ewa Fawaz yayi ya bisu da wani kallo ransa a b'ace sannan yasa kai ya nufi d'akin sa, ko ta kansa basu bi ba suka cigaba da tittilawa cikin su giyar har sai da suka bugu sannan suka fara hirar yaushe rabo cikin hali na maye.
***
Kwance take kan makeken gadon ta tayi ruf da ciki hawaye kawai ke fita daga idon ta jijiyoyin kanta duk sun tashi idanun ta sunyi luhu-luhu amma duk da haka ta kasa hak'ura da kukan kamar wacce za'a zarewa rai, wayar ta dake gefen ta ta jawo ta fara dannawa tasa a kunne had'i da fashewa da wani irin kuka marar sauti, muryar mace ce tayi magana daga cikin wayar tace "Babe." kuka kawai Zuhra keyi bata damu da ta amsa mata ba, k'ara kiran sunan ta tayi tace "Zuhra lafiya? Mi yake faruwa?" kuka Zuhra keyi wiwiwi ta kasa ce da ita uffan, haushi sosai taji tace "Wai lafiya kin kira ni kin kasa ce dani komai?" cikin kuka Zuhra tace "Nens tell me." "Tell you what?" "Ki gayamin gaskiya Nens." sai kuma ta rushe da kuka "Wai me zan gaya miki ne? Dan Allah ki bar kukan nan ki min magana mana ha'an!" tashi tayi zaune ta share hawayen ta sai ajiyar zuciya take tace "Nens me nake lacking na zama cikakkiyar mace?" "Nothing." cewar Nens a tak'aice kuma kanta ya bala'in k'ullewa, kuka Zuhra ta fashe dashi ta koma ta kwanta ta damk'e bedsheet da yatsun ta gam tace "K'arya ne Nens ba gaskiya bane." "Ke zaki min magana da yaren da zan fahimta ko kuwa na kashe waya ta?" kuka ta rushe dashi tace "Nens it's Fawaz." tsuki Nens taja tace "Dama nasan za'a rina... Kin ga Zuhra I'm tired of you and your cousin's daily drama wallahi!" "Nens I love him wallahi ina san shi don't you get it? believe me please." "Then spell it out mana, kin ga Zuhra this is 2018 not 80's lokacin da zaki dinga dakon soyayyar wani without telling him ki gaya masa mana ko yanka ki zai yi ne? Zaki zauna kullum kina b'ata hawayen ki a wofi akan wanda bai ma san abunda kike ciki ba." "Ba zaki gane ba Nens, I tried all my possible best amma ya kasa fahimta na." "Ke wacce irin bak'auyiya ce? I told you this is 2018 an dad'e da wuce wurin jin kunya ko wani abu, inace a nan kike ganin mata suna tallatar da kansu wallahi idan baki daina wannan zurfin cikin ba muna nan dake zaki ga Fawaz da wata ba ke ba silly bitch kawai!" a zuciye ta tashi zaune cikin tsintsar masifa tace "Nens wane maganar banza marar dad'in ji ne kike fad'a haka? Wannan ba shine karo na farko ba da nike gaya miki bana san irin wannan maganar, Nens I don't care ke babbar k'awata ce wallahi zan miki rashin mutunci akan Fawaz, akan Fawaz zan iya b'atawa da kowa koda kuwa Ammi zata kasance d'aya daga cikin wannan mutanen!" cikin mamaki Nens tace "Ammi fa kika ce Zuhra? Your mother? Uwar da ta haife ki zaki iya b'atawa da ita akan wani banza? Lallai sai yau na tabbata baki da hankali." ji tayi kamar ta finciko Nens daga cikin wayar ta fara dukanta, cikin b'acin rai tace "Wallahi Nens next time kika kira Fawaz da banza that's the end of me and you!" sai kuma ta fashe da kuka ba dalili mai tsuma zuciya kamar ba wacce ta gama masifa yanzu ba tace "Nens ba laifi na bane it's my love for him." "Toh Allah ya sawaka but you gotta fix it." share hawayen ta ta shiga yi tace "In shaa Allah" da haka suka yi sallama da Nens suka ajiye wayar. Cigaba da ajiyar zuciya tayi daga kwance da haka har bacci ya sace ta.
*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *March, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*05*