Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 3

Abokaina complete book 1 - Chapter 3

Abokaina complete book 1 Chapter 3: Abokaina complete book 1 Chapter 3. _5:00pm_ Da misalin k'arfe biyar na yammacin wannan ranar matasan ne su uku zaune a…

4,478 words

_5:00pm_ Da misalin k'arfe biyar na yammacin wannan ranar matasan ne su uku zaune a cikin parlor'n. Fawaz ne zaune a k'asa cikin farar jalabiya mara nauyi fuskar sa tayi shar sajen sa da gajeren gemun sa da bai cika aske shi ba duk sun kwanta a kyakkyawan fatar sa hannun sa rik'e da wani textbook wanda a bangon sa aka rubuta Drilling Fluid Engineering. A gefe guda kuma Foxy ne kwance akan sofa bakomai a jikin sa sai shorts rik'e da waya a hannun sa yana dannawa yayin da Fak shi kuma zaune yake kan sofa long pencil trouser ne black a jikin sa shima dai ba riga a jikin nasa ba abunda yake sai kwankwad'ar giyar sa. Foxy da Fak ne ke ta zuba hira, dama idan fagen hira ne tasu tafi zuwa d'aya saboda Fawaz ba mutum ne mai yawan magana ba, tashi daga kwance Foxy yayi yace "Dude baka sani ba, the first day I had those huge boobies in front of me I never believed it, the sight was very emotional" dariya suka fashe in banda Fawaz wanda bani da tabbacin ma yasan maganar da suke fad'a saboda yayi nisa a cikin textbook da yake hannun sa, in between laughter Foxy ya cigaba da cewa "Wallahi the sight was very glorious aboki na kasan me ma? I just opened the bra and closed it back then I started crying." dariya Fak ya fashe harda buga k'afa a k'asa cikin dariya yace "Shegge Foxy! Wai wacce babe ce ma lokacin?" shima Foxy'n wata gajeruwar dariya yayi yace "Neelex ce stick bug kawai!" "Oh yeah na tuna! That big booty bitch lokacin you guys were very lovey-dovey, har kuka take if you wasn't in school." dariyar mugunta Foxy yayi yace "Forget, Neelex ta mutu a kaina wallahi." "Kana da contact nata ma kuwa?" cewar Fak "Yeah! Amma ko chat bama yi not to talk of calls except if I wanna exercise my fingers tayi mitan ta har ta gaji ta barni." dariya Fak ya sake yi yace "Duuudeee! Maza Baka da kyau wallahi!" tsuki Foxy yaja sannan yace "Haba Neelex is in the past now four years no be beans ai, ni yanzu wata hot chick ce nake so na gama brain washing a wuce wurin gashi Abba ya balayin fucka ni yasa ni na dawo wannan garin." "Oh! A UK take kenan?" Fak ya tambaya, damuwa ta bayyana a fuskar sa yace "Eh mana! Guy wallahi babe d'in tayi ka ganta kuwa?" yatsina fuska Fak yayi yace "A ina zan ganta idan ba nunan kayi ba?" wata shed'aniyar dariya Foxy ya kece da ita sannan yace "Phew! Then you've missed something, what a dish! Ever since I saw her she's been haunting my dreams." tab'a baki Fak yayi "Wai kana ta wani kod'a ta what's so special about her?" zaro ido Foxy yayi yace "Kai d'an iska kasan abunda kake fad'a kuwa? Dude you must be very stupid! Wait until you see her then you'll realize you've asked the silliest question ever, anyway, abokai na ne." ya k'are maganar yana kashe masa ido had'i da cije leb'e ya k'ara da cewa "You know 'em." dariya suka fashe at once Fak yana jinjina kai alamar ya gano tashar da haka suka cigaba da dirty talks d'insu irin ta abokai sai kuma chan kamar an mintsili Foxy ya kalli Fawaz wanda sai karatun sa yake yace "Hey Fizzy! Kace Afeefah ta samu admission a Baze ko?" duk hirar da suke sai a lokacin Fawaz ya d'ago kai daga kan textbook d'in da wani murmushi mai sanyi a fuskar sa wanda a tunani na ba zaya rasa nasaba da kiran sunan Afeefah da Foxy yayi ba, cikin sassanyan muryar sa yace "Yeah!" "Wow! Wanne course?" cewar Foxy, murmushi ya k'ara bayyana a fuskar Fawaz a karo na biyu sannan yace "B.Sc Mathematics" k'ara exclaiming Foxy yayi yace "Wow! Affee and Mathematics... You can't separate those, kace dai her love for Maths is still living in her." wani k'asaitaccen murmushi Fawaz keyi yace "Afeefah issa brainy kid kaima ka sani." jinjina kai Foxy yayi yace "Nasani wallahi Affee is such a babe, yarinyar tayi ba ruwan ta the most adorable thing about her is that she's very religious and respectful, koda a tsakanin colleagues ne lokacin muna Liberty idan tazo sai ta gaida kowa, Affee isn't used to all that bla-bla bata da hayaniya ko kad'an." har yanzu murmushin da yake kan fuskar Fawaz ya kasa gushewa cikin muryar sa mai sanyi yace "That's what makes her more adorable, I have a special BFF." "But she's a lazy crap, too much stress is enough ya saka Affee kuka harda hawaye." cewar Foxy, dariya Fawaz yayi ya mayar da kansa akan littafin da yake karatu sannan yace "That's Afeefah for you." dariya shima Foxy yayi yace "Shagwab'a... That's what make her more beautiful." sai a lokacin Fak ya tsoma bakin sa a hirar Afeefah da suke yi yace "Idan fa aka zo wurin karatu Afeefah isn't a lazy girl she's a very hard working kid." jinjina kai Foxy yayi yace "Sure... The overall highest scorer every year... Affee kenan, wai har yanzu is her voice tiny?" dariya Fawaz yayi har hak'oran sa suka fito ya shafa sajen sa da hannu d'aya yace "Yeah but now with so much flows." "Gee!" Foxy ya fad'a had'i da tashi zaune lokaci d'aya yace "Mu bata surprise please, take me to her." murmushi Fawaz kawai keyi ya jawo wayar sa dake gefen sa yace "Barin ji tana ina first." sannan ya fara danna wayar sa zuwa contacts d'in sa ya lalubo number Afeefah da yayi saving da *Brainy* ya danna call ya saka a loudspeaker yana ta fad'ad'a murmushin sa, ringing d'aya a na biyu wata k'arama kuma siririyar murya kamar busar sarewar aljanu tayi magana "Oldie oyoyo!" cije leb'e Fawaz yayi yana ta murmushi yace "Oyoyo Brainy kina ina ne haka?" cikin wannan siririyar muryar tan ta sake cewa "Ina gida." "Alright gani nan zuwa with an amazing surprise for you." cike da jindad'i tace "Wow!..." Fawaz bai barta ta fad'i abunda tayi niyyar fad'a ba ya katse wayar har yanzu murmushin dake kan fuskar sa ya kasa gushewa ya kalle su yace "Ku shirya muje." kowannen su mik'ewa yayi in banda Fawaz duk suka nufi d'akin su, cikin k'ank'anin lokaci Foxy ya fito cikin jean da t-shirt kalar blue sai loafers da ya saka a k'afafun sa sai k'amshi ke tashi a jikin sa, k'ara duba wankan nasa kawai yake gaba da baya har ya shigo parlor'n ya samu Fawaz wanda ko motsawa bai yi ba daga wurin da yake zaune "I can't wait to set my eyes on that damsel again." cewar Foxy, murmushi kawai Fawaz yayi bai ce komai ba ana haka kuma sai ga Fak shima ya shigo cikin shirin sa na k'ananan kaya, sai a lokacin Fawaz ya mik'e tsaye ya fara tafiya yana cewa "Sorry ku jira in d'an zuba wa jiki na ruwa please." tsoki Foxy yaja ya fad'a kan sofa ya zauna yayi crossing legs ya d'auki remote control ya fara k'ok'arin chanza tashar da ya tarar zuwa wata yace "Wallahi Fizzy kana da matsala." Fawaz dai bai ce masa ko k'ala ba ya shige d'akin sa, ba yadda Fak ya iya shima don dole haka ya zauna suka shiga jiran fitowar Fawaz. Bayan kamar 15 minutes haka sai gashi ya fito cikin farar jallabiya har k'asa wacce har tana nuna farar singlet d'inshi dake ciki da kuma halittar sa da broad shoulders da broad chest d'insa duka, duk k'amshin da suke sai na Fawaz ya fita daban shi kansa ma daban ne a tsakanin su hannun sa rik'e da wayar sa da keys d'in motar sa, da sauri ya shigo d'akin yace "We are good to go now." da d'aya-d'aya suka mik'e suka nufi hanyar fita, motar d'azu wato Hamann Mystere suka sake hawa a inda Fawaz ke gaba yana driving Foxy yana daga gefen sa sai Fak dake backseat. Wak'ar Eminem Fawaz ya kunna ai kuwa kamar Foxy ne yayi wak'ar sai bin wak'ar da kid'an da rap d'in yake yana kad'a kai yana kallon side road yayin da Fak yayi nisa a cikin wayar sa, kallon sa Fawaz yayi da wutsiyar ido wanda Foxy bai san ma yayi ba kit ya kashe kid'an, da sauri Foxy ya juyo yace "Fizzy me haka ne for fuck's sake?" ko kallon sa Fawaz bai ba sai driving d'insa yake yace "Na gaji, rap kamar don kai aka yi shi." hannu Foxy ya kai ya sake kunna kid'an ya k'ure k'arar sannan yace "Yeah we run this whole thing!" tab'a baki Fawaz yayi ya cigaba da driving d'insa sai kuma ya d'auko wayar sa yayi danne-danne yasa a kunne yace "Brainy we are almost there." murmushi ya bayyana a fuskar sa sannan ya k'ara da cewa "Ameen." sannan ya ajiye wayar. Wani makeken gida naga motar su Fawaz ta nufa ta kutsa kai a ciki, wani mansion ne mai d'auke da 3 storey building mai d'an karen kyau suka wayi gari a ciki, Afeefah ce ta fito cikin riga da skirt na atamfa 'yar fara kyakkyawar yarinya mai doguwar fuska da dogon hanci iyakacin ta shekara sha takwas a duniya sai dai ko kad'an bata da jiki slim ce ta k'arshe zaka iya hango small tit da butt d'inta ta nufo wurin da suka yi parking tana murmushi, gaban Foxy ne ya fad'i kad'an da ganin yarinyar ya kalli Fawaz da mamaki yace "Holy shit! Afeefah ce wannan? Itace ta girma haka?" dariya Fawaz yayi yace "Then? Me kake tsammani zaka gani?" "That same kid I used to know mana. " kallon baka san komai ba Fawaz yai masa sannan yace "It ain't the shit you know." yana gama fad'ar haka ya bud'e motar ya fita, murmushi suka sakarwa junan su cikin siririyar muryar nan tace "Oldie ina surprise d'in?" tana rufe baki k'ofar front seat wacce Foxy ke zaune ta bud'e Foxy ya bayyana, dafe bakin ta tayi da hannu biyu ta fiddo ido cike da tsintsar mamaki tace "Foxy?" murmushi kawai Fawaz keyi yana kallon ta da kowane move nata shi kawai everything about Afeefah is so special to him yana matuk'ar burge sa especially her childish manners, shi kuwa Foxy kafe ta yayi da ido yana mata wani shu'umin kallo na 'yan duniya wanda Fawaz ya kasa zama comfortable da wannan kallon, don ya katse wannan kallon ya kalli Afeefah yana murmushi yace "It's worth a surprise I guess." da murmushi kan fuskar Afeefah ta mayar da kallon ta kan Fawaz tace "Oldie yaushe Foxy ya dawo bansani ba?" gyara tsayuwar sa Fawaz yayi ya saka hannun sa biyu a aljihun jallabiyar sa sai flashing mata wani smile yake yace "Just some hours ago." shi kuwa Foxy ware hannayen sa biyu yayi da niyyar zai yi hugging d'inta in a welcoming way, kunya ce ta kama Afeefah tasan halin Foxy sarai ba k'aramin aikin sa bane yayi hugging d'inta a ko gaban waye, da sauri ta kauce ta koma bayan Fawaz ta lab'e ta d'an jawo rigar sa ta baya tana b'oyewa, dakatawa Foxy yayi ya b'ata fuska yana hararar ta yace "Duk k'udurin ganin ki da naci at last shunning nawa zaki yi ko Affee? Kina so su min dariya ko?" duk'ar da kanta tayi tana murmushi tace "I'm sorry ba haka bane..." nan ma Fawaz harara ya bita dashi yace "See kina wani apologizing as if wacce tayi laifi." sannan ya juyo ya kalli Foxy yace "Anyi shunning d'in naka so bloody what?" hararar wasa Foxy ya watsa masa yace "Ina ruwan ka damu ne?" fita batun sa Fawaz yayi ya kalli Afeefah yace "K'yale shi Brainy you already know him, it takes guts to withstand this dude ni kad'ai nike iyawa." murmushi tayi ta d'ago kai ta kalli Foxy ya sakar mata wani kalar murmushi wanda tunda uwar ta ta haife ta ba namijin da ya tab'a yi mata irin shi, murmushi ne mai d'auke da ma'anoni masu yawa wanda yake iya isar da sak'onni masu dama ba tare da mutum ya fad'a ba, a hankali ya tako yazo gaban ta daf da ita suna fuskantar juna sosai ya sake bud'e hannayen sa duka yana murmushi yace "Karki damu da wannan d'an iskan you know I already missed you where's my hug?" murmushi tayi in a calming voice tace "Ain't no hug but..." ta d'ago hannun ta mik'a masa alamar handshake tana murmushi, without hesitating Foxy yayi grabbing hannun nata wanda ya same shi very soft and small in fact da ya rintse shi a nasa hannun kai kace ba abunda ya rintse don kuwa ya lume a cikin nasa hannun cif. Wasu abubuwa ne suka fara yawo a k'walk'walwar Afeefah wasu irin shocks lokacin da hannun ta da na Foxy ya had'u it touched off a spark inside her that had been waiting to be touched off ever since she had become what is technically known as a woman taji kanta as if tana yawo a sama just like a busby fly in the air a tak'aice dai wani yanayi ne ta shiga wanda bata tab'a sanin akwai kalar wannan yanayin a doron k'asa ba and precisely ba zata iya cewa wanne yanayi ne ba. D'ago d'an k'aramin hannun ta Foxy yayi ya kai bakin sa yayi kissing nashi passionately sannan ya saukar dashi k'asa yasa d'aya hannun sa yana goge wurin da yayi kissing d'in sai wani blushing yake ya kalle ta yace "I'm sorry my rough lips ko?" daskarewa Afeefah tayi ta kasa d'agowa ta kalle sa, shi kuwa Fawaz duk abunnan da yake faruwa akan idon sa zuciyar sa sai harbawa take zan iya cewa ma beyond normal, wani abu da baisan ko miye ba yaji ya tokare masa a mak'oshi ya kasa tantance kishin abunda Foxy yayi wa Afeefah ne ke damun sa ko menene, kawar da fuskar sa yayi ya daina kallon su lokaci d'aya kuma mood nasa ya chanza at that very moment Foxy da Afeefah sai jifar junan su suke yi da murmushi, d'an cije leb'e Foxy yayi shima duk da cewa ya saba sha'ani da 'yammata kuma zan iya cewa ba wata high class girl da bai tab'a gani ba amma sai ya samu Afeefah daban, saukar da wani gwauron numfashi yayi yace mata "Kinsan wani abu? Lemme tell you something..." karaf Fawaz ya juyo ya kalli Afeefah yace "Have you ever heard Shaitan gives something good?" baki Afeefah ta bud'e wangalau tana kallon Fawaz tace "Oldie don't tell me Foxy Shaitan ne." "He's more than that." cewar Fawaz, dariya Foxy ya k'yalk'yale da ita ya juya wurin motar su ya d'aga murya yace "Kai d'an iska come down! See this guy wan cast me for Afeefah place." k'ofar motar ta backseat ta bud'e Fak ya diro yana jan t-shirt d'insa ta baya yace "Fizzy na fuck up guy na." kallon su Fawaz yayi then back to Afeefah yace "One has to take care of his sister and best friend ko ba haka ba Brainy?" murmushi tayi ita kam jikin ta ya riga da yayi sanyi a sanyaye tace "Hakane." d'ago kai Fawaz yayi yana grinning from ear to ear yana kallon Foxy yace "Foxy how market? Ba'a shiga tsakani na da Afeefah you get that?" dariya Fak yayi yace "Muma dai naga Afeefah'n nan tamu ce, she's your best friend as much as ours abun Bros na Bros ne that's the law for brotherhood." girgiza kai Fawaz yayi in disbelief yace "Ah inaa! Not when it comes to Afeefah nayi disregarding wannan law d'in." murmushi Afeefah tayi har hak'oran ta suka fito tace "Fak dama tare kuke shine you can't even come down and say a hi?" tayi maganar ne don ta katse wannan stupid little fights d'in nasu don kuwa basu gajiya once suna tare to sun fara casting junan su kenan musamman Fawaz da Foxy, girgiza kai Fak yayi yace

"Sorry please I was busy with my phone... Ya kike?" d'an rausayar da kai tayi tace "Lafiya k'alau so, you guys decided to pull my leg bansan Foxy zai dawo ba sai ganin sa nayi kamar daga sama." dariya Fak yayi yace "Yeah ance a baki surprise ne hope it's worth a surprise." juyar da manyan idanun ta tayi tace "Yayi kyau!" sannan ta kalli saura tace "Mu shiga daga ciki." tana gama fad'ar haka ta juya ta nufi babbar hanyar da zata sada ka da babban parlor'n gidan yayin da su uku suke biye a bayan ta.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *March, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*06*

Shiga suka yi a wani dank'areren parlor suka samu wuri akan manya-manyan sofas dake parlor'n suka zauna. Itama Afeefah zama tayi suka k'ara gaisawa sai teasing juna suke as usual, hira ce ta kaure tsakanin Afeefah, Foxy da Fak yayin da Fawaz kam shiru yayi abunsa kamar ma baya wurin, suma basu damu da sako shi a hirar su ba don sun san halin sa miskili ne na bugawa a jarida sai dai Afeefah da ta lura da yanayin sa ya chanza baya nishad'i kamar yadda suka zo d'azu. Tashi Afeefah tayi ta nufi dining Foxy yabi bayan ta da ido kamar wani soko, zungurar sa Fak yayi yace "Yadai mutumi na? Wannan kallon fa?" wani deep breath Foxy ya saukar tukuna sannan yace "Ka bari kawai baabaa I never thought zan ga Afeefah as cute as this one, I think I'm in love wallahi." "Mtsww! Dama kai a haka zaka k'are ba macen da zaka ji baka so, maye kawai!" "Naji dai." cewar Foxy. Duk maganganun da suke gudana tsakanin Foxy da Fak a kunnuwan Fawaz suke sauka sai dai bai d'ago kai ya kalle su ba a tak'aice ma bai nuna musu yasan abinda suke magana ba kawai dai ya tsinci kansa da fad'uwar gaba da maganganun Foxy wanda a zahirin gaskiya bai san meye dalili ba. Abun sha da glass cups Afeefah ta dawo dasu parlor'n ta dire a gaban su sannan ta shiga tsiyaya wa kowannen su. Fawaz ta fara mik'awa wanda yake a sofa opposite da wacce su Foxy suke akai, kasa natsuwa tayi da chanzawar yanayin nasa cikin k'ank'anin lokaci, cikin kwantar da murya tace "Oldie lafiya kuwa?" faking murmushi yayi ya karb'i glass cup d'in da take mik'a masa yace

"Lafiya k'alau, thanks." zata iya cewa wani abu ne da bata saba gani ba ko kuma ba kasafai take ganin shi tattare da Fawaz ba kuma shi yasa ta kara tabbatar da cewa he isn't normal saboda slight ciwon kai idan yana damun sa sai ta sani amma yau ta hango wani abu a cikin k'wayar idon sa da yake k'ok'arin b'oye mata a k'ark'ashin inuwar bakomai, tsayawa tayi tana kallon sa a salube tana so ta masa magana amma me zata ce? Murmushin kawai itama ta mayar masa sannan ta dawo tayi serving Foxy da Fak. Sun ci sun sha sun kuma zuba hira Foxy yayi nasarar aika mata da sak'onni masu wuyar fahimta kuma masu ma'ana barkatai daga k'arshe suka yi sallama da ita suka tafi. Bayan ta raka su ta dawo ta shiga wani d'aki jiki a sanyaye ta zauna bakin gado, Aunty Nana ce kwance ta mik'e shal akan gadon tana rik'e da wayar ta gefe kuma laptop d'inta ce ta kamfanin Apple, zungurar Afeefah tayi da k'afa tace "Affee?" juyowa Afeefah tayi ta kalli Aunty Nana kawai bata ce komai ba, mamaki ya kama Aunty Nana don kuwa bata saba da ganin wannan yanayin a tattare da k'anwar ta ba, tashi tayi zaune ta jawo kafad'ar Afeefah tace "Afeefah lafiya? What's it?" duk'ar da kanta tayi a k'asa cikin muryar ta me sanyi tace "Bakomai." murmushi Aunty Nana tayi tace "Ko dai ke da Umma ne?" nan kam girgiza kai tayi alamar a'a, komawa Aunty Nana tayi tai kwanciyar ta tace "Ke kika sani toh." ta cigaba da danna wayar ta. Duniyar tunani Afeefah ta tsunduma, a rayuwar ta baki d'aya ba wani d'a namijin da ya tab'a yi mata abunda Foxy yai mata a yau kuma sai ta tsinci kanta da kasa hana shi, jikin ta ya bala'in sanyi kanta kuma ya masifar d'aurewa sai tambayar kanta take me Foxy yake nufi da abubuwan da yazo mata dasu yau ita kuma mene yake shirin faruwa da ita akan Foxy meyasa ya tsaya mata a rai, ta dad'e zaune a wurin har sanda lokacin sallar Maghrib yayi sannan ta tashi ta bayar da farali. Da dare ma kasa fita tayi wurin da suka saba had'uwa don cin abincin dare, a bedroom tayi kwanciyar ta sai juyi take a tak'aice har sanda bacci yayi awon gaba da ita k'wak'walwar ta a cunkushe take.

***

_8:00pm_ "What's going on hungry folks?" cewar Fawaz yayin da yake k'ok'arin shigowa parlor'n hannun sa rik'e da manyan ledoji alamar abinci ya siyo masu. Foxy ne a kwance kan doguwar kujera daga shi sai boxer yayin da Fak ke fitowa daga d'akin Foxy ya gama shirya masa kayakin sa a ciki, tashi zaune Foxy yayi ya kalle su ya bushe da dariya yace "That's what I want to see! My two slaves hard at work for me!" kukan kura Fak yayi ya shak'e Foxy da ya koma ya kwanta yace "Don uban ka waye slave d'in naka?" dariya da kakari Foxy keyi lokaci d'aya yana nema Fak ya cika sa amma yak'i, shi kuwa Fawaz k'arasowa yayi cikin parlor'n ya dire ledojin a k'asa sannan ya zauna kan kujera ya kalli Fak da har lokacin bai cika Foxy ba sai wrestling suke yaja tsuki yace "Wai me kuke yi ne haka? That shit ain't cute man!" sai a lokacin Fak ya cika Foxy ya dawo kan Fawaz yace "Ina ruwan ka kai kuma? Over sabi kawai!" ko k'ala Fawaz bai ce musu ba sai jawo ledojin yayi ya fara fiddo abincin yace "Idan kun gama kuzo kuci abinci, I don't have time for bullshit and nonsense." mik'ewa Fak yayi ya d'auko kwalbar giyar sa da glass cups k'anana guda biyu ya ajiye su shi kuma Foxy ya tashi zaune dukansu suka yi wa ledojin dirar mikiya, cin abincin suke lokaci d'aya ba mai ce da wani uffan har suka gama. D'aga kwalbar giyar sa Fak yayi ya tsiyaya a cikin d'aya daga cikin glass cups d'in ya fara sipping a hankali, kallon sa Fawaz yayi yana nazarin fuskar sa cike da takaici yace "Fak it's high time now, ya dace ka daina shan wad'annan abubuwan koda ba zaka iya dainawa baki d'aya ba ya dace ka rage at least for your health." ko kallon sa Fak bai yi ba sai kurb'ar giyar sa yake yana lumshe ido, ajiye cup na wine d'insa Foxy yayi yana kallon Fawaz yace "Fizzy kana da big problem wallahi, dole ne sai kowa yayi rayuwar takura irin wacce kake yi? This is a free world man! You don't know the battle he's fighting down inside him, let him ease himself ka barsa ya more rayuwar sa mana." murmushin takaici Fawaz yayi yace "Yeah he may ease himself here but we weren't promised ease in the afterlife, girma fa muke yi every blessing day kuma wannan duniyar da kuke gani bata da tabbas." "Says who? Wa ya gaya maka duniya bata da tabbas? Duniya kuwa take da tabbas for those who believe in it." sannan ya juyo ya kalli Fak yace "Do whatever the fuck you want don't let anyone kid you otherwise." gyatsar giya Fak yayi ya d'an buga kafad'ar Foxy yace "Mazaa k'yale shi kawai, Fizzy is the most dumbest son of a bitch I ever met!" sannan yayi crossing k'afafun sa ya kalli Fawaz yace "Malam kabarin ka fa daban nawa daban, you are living your life I'm living mine." girgiza kai kawai Fawaz yayi ransa sai k'una yake, at first ya d'auka Foxy zai goyi bayan sa wurin yiwa Fak fad'a sai ma ya lura Foxy ne mai defending Fak d'in. Tsuki Foxy ya ja yayi resting akan kujera yace "Kai shikenan don baka san abu dole kowa ma sai ya yak'i shi, kowa mai fidda shi yake yi." dariya Fak yayi ya daki Foxy a kafad'a yace

"Calm down mutumi na! Ni fa na saba da wa'azin nan nasa, idan ka daka ta Fizzy ba abunda zaka yi komai a wurin sa haram ne." jinjina kai Foxy yayi sannan ya kalli Fawaz wanda sai kallon su kawai yake ya rasa abunda zai fad'a, cike da natsuwa yace "Ka fahimce ni Fizzy, we only live once and beside zamu tuba ko ba haka ba?" ya k'are maganar yana kallon Fak questoningly, gyad'a kai Fak yayi ya kora giyar sa sannan yace "Hakane mana zamu tuba in shaa Allah." "So you see? Kawai abunda kake magana ne ba zai yiwu ba and that's mu daina more rayuwar mu in our early twenties, abunda fa kake gani Islamic scholars d'innan suna fad'a a TV that's not what the world is out there, nasan sune matsalar ka idan kuma baka daina saurarar su ba sai sun maka illa a tunani na gaya maka." ya k'are maganar arrogantly ya figi ragowar hamburger ya wuce bedroom d'insa, takaici ne ya tarnake zuciyar Fawaz ya k'urawa tile ido yana wani tunani; a fad'in duniya bayan iyayen sa da k'anwar sa Maryam to kuwa Foxy da Fak ne zasu biyo baya a samun soyayyar sa, yana matuk'ar son su da k'aunar su kamar jinin sa da k'ok'arin ganin rayuwar su ta inganta amma kullum sai tab'arb'arewa take haka yake jin su tamkar ciki d'aya suka fito kuma yake k'ok'arin fahimtar dasu akan rud'in wannan zamani amma basu tab'a saurarar sa ba sun saka duniya da jin dad'in ta a gaba, kamar daga sama ya jiyo muryar Foxy daga cikin d'akin sa yana ce da Fak "Baabaa I need more shots please!" mik'ewa Fak yayi yana tangad'i kamar zai fad'i cikin d'aga murya yace "Gani nan zuwa!" sannan ya d'auki ragowar giyar sa ya kalli Fawaz yace "Guy save your lectures we won't be listening ka gane?" sannan ya ja k'afafun sa ya fara tafiya zuwa d'akin Foxy, har yayi nisa sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon Fawaz yayin da shi kuma Fawaz d'in zuciyar sa sai k'una take ganin rayuwar abokan sa kullum sai dad'a lalacewa take amma ya kasa yin komai, sai rangaji Fak keyi kamar zai fad'i yace "Please Fizzy kud'i nike so." sai da aka d'auki 'yan dak'ik'u Fawaz yana tunani zuciyar sa na gaya masa you have to make your first move, saukar da numfashi yayi yana kallon Fak yace "Me zaka yi da kud'i?" "Kamar ya me zanyi da kud'i? K'aramin yaro ne ni da zaka tambaye ni me zanyi da kud'i?" yana maganar fad'a-fad'a haka, cikin tausasa murya Fawaz yace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull