Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 4

Abokaina complete book 1 - Chapter 4

Abokaina complete book 1 Chapter 4: Abokaina complete book 1 Chapter 4. "Fak to be frank with you ba zan cigaba da baka kud'i anyhow ba it's like ina…

4,483 words

"Fak to be frank with you ba zan cigaba da baka kud'i anyhow ba it's like ina sponsoring shaye-shayen ka da lalacewar ka." baki Faruk ya bud'e full of amazement yana kallon Fawaz yace "Ah Fizzy kaga dakata! Ba sai ka fito ta wannan siffar ba kawai kace ka gaji dani ne!" fitowa Foxy yayi daga cikin d'akin sakamakon jin maganar Fak da k'arfi-k'arfi kamar fad'a, kallon su yayi d'aya bayan d'aya yace "What's happening here?" kamar dama jira Fak yake yi ya tambaye sa yace "Kaji fa Fizzy kawai don na tambaye sa kud'i zai fara kawon excuses wai it's like yana sponsoring shaye-shaye na, all this while baisan yana sponsoring shaye-shaye na ba sai yanzu?" cikin sanyin murya Fawaz yace "Ba nace ba zan baka kud'i ba Fak, zan baka kud'i but me zaka yi dashi?" a fusace Fak ya juya ya kalli Foxy yace

"Ka gani ko? Ka gani fa wai me zanyi dashi, tsakanin ka da Allah tun sanda muke da Fizzy ya tab'a tambayar me zanyi da kud'i kawai ya fito fili yace ya gaji dani ba wani abu bane!" sannan ya kalli Fawaz yace "Idan sai kaji abunda zanyi da kud'i ka rik'e abun ka bana so, I'll pack all my belongings and leave dama zaman ka nike yi." yana gama fad'ar haka ya juya fuu zai nufi d'akin sa, finciko sa Foxy yayi da hannu d'aya har sai da ya kusa fad'uwa k'asa sannan yace "Come on Fak! Matsala na da kai kenan wannan yawa kake wallahi, meye abun fushi anan? Is it an offence don ya tambayi me zaka yi da kud'i? Fizzy ne fa! Think about the vital role he have been playing in our lives amma da wannan sakamakon zaka saka masa?" a lokacin ba abunda Fawaz keyi sai kallon Fak ya lura ga baki d'aya ya fita daga cikin hankalin sa yana a cikin hali na maye ne, cikin sassanyar murya Fawaz yace "It's all right Fak zan maka transfer but please bana so na k'ara ji wai zaka tafi." don ya fahimci koda zasu kwana yana k'ok'arin fahimtar da Fak abunda yake nufi ba zai tab'a ganewa ba saboda baya a cikin hankalin sa, breaking da murmushi Fak yayi yace "Right, thanks." murmushi Foxy shima yayi ya kalli Fak yace "Nima zan k'ara maka." murmushin dake fuskar Fak sai dad'a k'aruwa yake yace

"Thanks dudeee!" ya mik'a masa hannu suka tafa suka yi hugging juna haka ma Fawaz sannan Foxy ya kalle sa yace "How about you give me another shot?" glass cups na d'azu Fak ya d'auko ya mik'awa Foxy d'aya ya rik'e d'ayan ya tsiyaya musu giyar suka yi toasting suka kurb'e shi zuwa guda sannan Fak ya juya da ragowar sauran giyar a hannun sa ya nufi d'akin sa yana cewa "Sai da safe ni bacci nike ji." dariya Foxy yayi ya zauna kan sofa yace "D'an iska ka shanye rijiyar Tequila ai dole kaji bacci." dariya Fak keyi yana layi yana jan k'afafu har ya shige d'akin sa sannan Foxy ya kalli Fawaz in a calming voice yace "Don't mind him please he's just drunk it wasn't Fak." jinjina kai Fawaz yayi yace "Yeah I know it wasn't him." sun dad'e suna hira har kusan 11pm sannan Fawaz ya mik'e tsaye yace "My bad, nima fa bacci nike ji zanje in kwanta." mik'ewa shima Foxy yayi yace "Nima wallahi." da haka suka yi wa juna sai da safe kowa ya kama hanyar d'akin sa. Fawaz yana shiga d'akin sa ya cire jallabiyar jikin sa yayi saura daga shi sai boxer har singlet d'in ma sai da ya cire sannan ya fad'a kan gado, tunanin rayuwar sa da abokan sa yai tayi tun daga farko kawo yau, lokacin da tunanin Brainy yazo masa ne yasa yayi breaking da wani irin murmushi duk tunanin banzan da yake suka kau wani dad'i da farin ciki suka lullub'e sa, juyawa yayi kan b'angaren sa d'aya ya k'ara matse pillow a kyakkyawan broad chest nasa but damn abunda ya faru tsakanin ta da Foxy d'azu yazo masa a cikin k'ank'anin lokaci wannan tunanin ya sauya farin cikin sa.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*07*

Washegari gari ya kama Lahadi har k'arfe goma ba wanda ya tashi daga cikin su. Sai wuraren k'arfe goma da rabi sannan Fawaz ya tashi ya fito parlor'n ya had'a tea kawai ya zauna ya fara sha. Fak ne ya fito daga d'akin sa da hanzari sai waya yake yana fad'ar yana hanya, kallon sa Fawaz yayi da kyau yace "Mutumi na wannan saurin fa?" tsayawa Fak yayi turus don ko kad'an bai san da akwai mutum a wurin ba. Agogon hannun sa ya duba ba tare da ya kalli Fawaz ba yace "School." "School? Yau Sunday fa." "Yeah da akwai abunda zanyi." kallon sa kawai Fawaz keyi sounding weird sannan ya kad'a kansa ya kurb'i tea yace "Right, sai ka dawo." "Aha!" cewar Fak sannan ya juya cikin taku ya bar parlor'n. Har k'arfe goma sha d'aya na safe Fawaz kad'ai ke zaman sa cikin parlor'n yana kallo, sai wucewar sha d'aya sannan Foxy ya fito da gajeren wando da singlet a jikin sa hannun sa rik'e da waya yana dannawa, gaisawa suka yi da Fawaz ya zauna a d'aya sofa had'i da cewa "Fak fa?" d'an raising shoulders Fawaz yayi yace "Ya fita." "Ina yaje?" "School he said but nasan ba School zaya je ba." ya d'an dakata sannan yace "Fak seems to be hiding something away from me these days." "And you don't have to worry about it, he ain't a kid tunda har bai sanar da kai ba it's not a big deal he can take care of it alone." rausayar da kai Fawaz yayi bai ce komai ba suka chanza zuwa wata hirar. Suna a tsakiya da jokes d'insu Foxy ya kalli Fawaz in a very serious expression yace "Fizzy ina san Afeefah fa." kamar dukan k'arfe haka maganar tazo wa Fawaz, wani irin nauyi yaji kansa yayi nan take yanayin sa ya chanza, murmushin dole yayi bai ce uffan ba ya mayar da kansa a wayar sa zuciyar sa ta cigaba da harbawa "Fizzy!" Foxy ya sake kiran sa a karo na biyu, d'ago kai yayi suka had'a ido, wata zufa ta fara karyo wa Fawaz lokacin da ya dubi k'wayar idon Foxy ya hango ba alamar wasa a tattare dashi, jinjina kai Foxy yayi yace "I love her." k'ok'ari Fawaz yayi ya saita kansa da muryar sa don kada Foxy ya shaida chanzawar sa sannan yace "Amma kasan Afeefah ba ajin ka bace yarinya ce k'arama she is not the kind of babes you are used to." "But I love her, tunda nace ina santa ina santa." ajiye wayar sa Fawaz yayi gefe ya fuskanci Foxy sosai yace "Foxy... Dududu fa shekarun Afeefah sha tara." "I don't care I love her." numfashi Fawaz ya saukar a ransa yana karanto Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un, cikin sassanyar murya yace "Foxy..." katse sa Foxy'n yayi da sauri had'i da cewa "Fizzy..." sai kuma dukansu suka yi shiru lokaci d'aya zuwa na kusan minti biyu suna kallon junan su sannan Foxy ya katse shirun yace "I love her, ina san Afeefah I never thought zan ga Afeefah as lovely as this." mik'ewa tsaye Fawaz yayi cikin rashin k'warin gwiwa yace "It's alright, ka sanar da ita?" "Nah, kai dai nike gayawa yanzu." jinjina kai Fawaz yayi yace "Right, I wish both of you the best." ya mik'a masa hannu suka gaisa had'i da kakiro masa murmushi sannan ya juya ya nufi d'akin sa. Yana shiga ya mayar da k'ofar ya rufe kansa ya shiga sarawa a ransa sai maimaita _I love her, ina san Afeefah I never thought zan ga Afeefah as lovely as this_ yake, zufa ce ta shiga karyo masa ta ko ina a gefe d'aya kuma cewa yake shikenan his best friend is in love with the girl whom he's damn in love with ya zata kasance kenan?

_9:00pm_ Har k'arfe tara na daren wannan rana ba Faruk ba dalilin sa tun fitar da yayi da safe, sun buga wayoyin sa har sun godewa Allah amma ba wacce ke zuwa. Hankalin su ya d'agu sosai musamman Fawaz sai safa da marwa yake a cikin parlor'n yayin da Foxy ke zaune kan sofa yayi crossing legs suna zaman jiran tsammani. Wayar Fawaz ce ta fara ringing wanda ya jawo hankalin Foxy ya juyo da sauri yana kallon sa, duba wayar Fawaz yayi yaga number ce ba suna sliding kawai yayi ya saka a kunne, muryar wani mutum mai haiba yaji tace "It's ASP Abdulsamad from Asokoro Division Police Station Abuja. Faruk Ibrahim Wada mentioned you as his elder brother, he's been held here with charges of knocking some random guy on the street of Maitama and he beat him up but Alhamdulillah the guy is currently in the hospital receiving treatment. Mr. Shattima we ought to see you at Asokoro Division Keffi/Yanya road as soon as possible. Thank you." kit ya kashe wayar, ciro wayar Fawaz yayi yana karanto "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" sannan ya maida kallon sa kan Foxy wanda tuni ya mik'e tsaye sai tambayar sa lafiya yake. Irgo masa komai Fawaz yayi suka yi shiru kowannen su yana nazari, tsuka Fawaz yaja yace "Ka gani ko? This is what I'm telling you, kwata-kwata Fak ya chanza ba abunda yake sai neman fitina these days, fisabilillah meyasa zai knocking wani?" "Ba lokacin k'orafi bane yanzu, muje d'in mu gani" cewar Foxy. D'unguma suka yi su biyun suka fito daga parlor'n suka nufi wurin da motar Fawaz take tsaye suka shiga Fawaz yaja suka bar gidan. Tafe suke ba abunda Fawaz keyi sai irgawa Foxy irin abubuwan da Fak yake yi da irin hasarar da yake janyo masa. Kasancewar Fawaz mai hak'uri kuma mai zurfin ciki ne wanda magana ma ba damun sa tayi ba amma gashi yau sai surutu yake shi ya tabbatar wa Foxy cewar lallai abun yana damun sa, hirar da suka cigaba da yi kenan har suka iso.

*Asokoro Division Police Station* Jagora aka yi musu har zuwa office d'in ASP Abdulsamad aka nemar musu izini suka shiga, wani babban mutum suka tarar cikin shiga ta kamala zaune yana fuskantar ASP Abdulsamad wanda shima yake a zaunen a cikin uniform d'insa na 'yan sanda bak'in wando da riga kalar skye blue. Ganin da mutumin yai wa su Fawaz yasa ya mik'e zumbur kamar jiran su yake yace "Waye Fawaz daga cikin ku?" cike da ladabi Fawaz yace "Ni ne." cin kwalar sa mutumin yayi yace "Kasan ko ni waye ne? Idan baka sani ba let me assure you duk abunda ya samu d'ana I'm gonna hold your brother responsible kuma wallahi a shirye nike muje kowace kotu ce don ganin an hukunta shi." ko motsawa Fawaz bai yi ba haka ma bai ce komai ba har sai da mutumin ya sauka cikin sanyin murya yace "I'm sorry please and as an elder I understand your anger and I'm ready to pay for any damages my brother has caused..." bai kai aya ba mutumin ya daka masa tsawa yace "Kai har ka isa ka biya ni? Waye kai? Me kake da shi da har zaka iya biya na?"Fawaz bai sake bi ta kan mutumin ba ya mik'a wa d'an sandan hannu suka gaisa ya shiga bada hak'uri da neman afuwa wa Fak, cikin masifa mutumen yace "Ba fa zan yarda a sake sa ba tare da naga yanayin da yaro na yake ciki ba." cikin tausasa murya d'an sandan yace "Sir it is illegal and unconstitutional for a suspect to be detained for more than 48 hours without bail or charging him to a court. Advisably, I think muyi hak'uri kuskure ne an rigaya da an aikata kuma dukanmu fatar mu Allah Ya basa lafiya. Bai kamata ayi ta tayar da jijiyoyin wuya ba akan abunda za'a iya samun maslahar shi a cikin sauk'i."sai da aka sha fama da taimakon d'an sandan aka samu mutumin ya sauko yace ya hak'ura a bisa sharad'in idan har wani abu ya samu d'an sa daga baya to kotu kawai zai maka su, godiya su Fawaz suka yi sannan mutumin ya tafi aka yi clearing komai d'an sandan ya bada umurnin aje azo da Fak.

Bayan an zo dashi Fawaz yayi settling dukka bills d'in da 'yan sandan suka yi charging sannan ya fito daga building d'in ya nufi wurin da Foxy da Fak suke tsaye. Jefa masa wayoyin sa da cards d'insa Fawaz yayi cike da b'acin rai yace "You fucked up so bad dude." sannan ya kalli Foxy yace "Kaga abunda nike gaya maka ko? At last ya jawo mana cin mutunci a wurin wannan mutumin kawai!" in an expressionless face shima Foxy ya kalli Fak yace "Gaskiya Fak wannan yawaa kake." ba tare da Fawaz ya tsaya ya k'ara saurarar su ba ya zagaya ya bud'e motar sa ya shiga shima Foxy yana ganin haka ya bi sahun Fawaz ya zagaya ya bud'e front seat ya shiga leaving Fak alone. Kamar Fawaz zai tashi sama haka ya finciki motar suka bar wurin.

A hanya ba abunda Fawaz keyi sai complaining wa Foxy halin Fak da haka har suka iso gida. Basu dad'e da isowa ba Fak ma ya iso cikin Corolla S da yayi knocking wancan yaron dashi, shigowa yayi parlor'n a sanyaye ya same su zazzaune kan sofas, cikin muryar me taushi yace "I'm sorry Fizzy, I know you've wasted so much on me but I'm sorry." shiru Fawaz yayi bai ce komai ba haka ma Foxy, sai da aka shafe kamar mintuna uku haka sannan ya saukar da numfashi yace "It's okay Fak karka damu. It's you guys that matters, money will come and go but the most important thing will always be the people in this room." bai san sanda yayi breaking da wani tattausan murmushi ba yace "Thanks Bro." ya k'araso ya mik'a masa hannu suka tafa haka ma Foxy, nan take kuma b'acin ran da ya shiga tsakanin su ya gushe suka koma nishad'i da raha kamar ko yaushe.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*08*

_Bayan kwana biyu_ *Baze University, Abuja.* _4:00pm_ Foxy ne zaune a cikin motar sa k'irar Audi 2017 mai d'auke da glasses masu duhu ma'ana tint yayi parking a wurin da aka tanada don parking na d'alibai. Wani arnen ripped jean ne blue sanye a jikin sa wanda zaka iya rantsewa da Allah razor aka sa aka yayyaga shi sai bak'ak'en converse daga sama kuma white t-shirt ce wacce tayi daidai da jikin sa ta kamfanin Armani haka ma agogon dake d'aure a hannun sa sai bak'in glasses da ya saka a idanun sa. Zaune yake kawai ba abunda yake sai danne-danne a wayar sa yayin da music sai flowing yake a hankali a hankali a cikin motar tare da sanyin AC dake ratsa sa a rayuwar sa zai iya cewa wannan shine yanayin da yafi k'auna fiye da komai. Duk da cewa motar tasa tint ce amma ya iya hango ta lokacin da ta fito daga wani katafaren building cikin shigar bak'ar jalabiya wacce ta fitar da hasken ta sosai da d'an k'aramin jikin ta. Tafiya take cikin nutsuwa ta dumfaro motar tasa yayin da zuciyar sa sai racing take da ganin Afeefah ya kasa sanin dalili.

Abun da ya tabbatar shine yaga mata da yawa manyan babes but damn it bai tab'a ganin irin Afeefah ba. Duk da cewa Afeefah ba irin high class girls d'innan bane da ya sani but she is beautiful and classy in her own ways da haka ya cigaba da kallon ta har ta kawo daidai wurin motar ta bud'e ta shigo.

"F-o-x-y!" haka ta fad'i kalmomin sunan nasa a rarrabe sai murmushi take, kallon ta kawai yake musamman jikin ta had'i da cire glasses dake fuskar sa ya kasa ce da ita komai, waving lil fingers d'inta tayi daidai idanun sa tace "Foxy?" saukar da wani wahalallen numfashi yayi yace "Sorry... Wannan kyan naki ne it carried me away." had'i da sakar mata murmushi. Murmushin itama tayi ta sauke kanta k'asa tana wasa da hannun ta. Karkatowa yayi completely yana kallon ta wane zai chinye ta murya k'asa-k'asa yace "It's a hectic day huh? Naga you looked tired." d'ago kanta tayi sai wani kallon ta yake ko blinking baya yi, ta d'ago kai ne da niyyar tayi magana but yadda ya tsare ta da ido yasa ta jinjina masa kai kawai ta sake saukar da k'anta k'asa. Murmushi ya sake yi yace "This school completely sucks except for you guys I don't know how on earth zanyi karatu a wannan makarantar." ya fad'a har yanzu ya kasa d'auke idanun sa kanta, sake d'ago kanta tayi jikin ta yayi sanyi k'alau da wannan jarababben kallon da yake mata. Cikin muryar ta mai sanyi tace

"Ba wani be kind and say kai Ajebo ne kawai." dariya yayi sannan ya gyara zaman sa yayi kicking motar ya kalle ta yace "Your highness ina zamu je ne?" far tayi da ido cike da mamaki tace "Ina fa? Ba cewa kayi zamu yi hira ba?" murmushi kawai yake yi yace "Come on! Kinsan ba anan ba ko? We should at least have a drink and yarn together ko ba haka ba?" shiru Afeefah tayi sannan ta kakiro murmushi tace "Right." "So, ina zamu je?" cewar Foxy yana kallon ta, jim tayi kad'an kafin tace "Ko ina ma." jinjina kai yayi a hankali yana kallon ta yana wani murmushi yace "An gama your majesty." a hankali ya ja motar suka bar wurin.

*Millennium Park, Abuja.* Zaune suke a cikin wata rumfa ta alfarma bisa wasu lounging chairs suna fuskantar juna. Abubuwan sha ne birjik a gaban su amma sam Afeefah ta kasa tab'a komai daga ciki kunya da rashin sabo sun had'e mata wuri d'aya sai wasa take da wayar ta. Foxy wanda ya kafe ta da ido ko blinking baya yi sai kurb'ar drink d'insa yake hankali a kwance yana cigaba da kallon ta uncontrollably. D'ago kai tayi suka had'a ido ya masifar kashe mata jiki da wani kasalallen kallo, kasa jure wannan kallon tayi ta saukar da kanta k'asa. Dire cup dake hannun sa yayi kan table dake gaban su Afeefah bata ankara ba sai ji tayi ya kamo lil fingers d'inta. Da sauri ta d'ago manyan idanun ta wanda suka k'ara bud'ewa saboda mamaki tana kallon sa, murmushi kawai yake yana kallon k'wayar idon ta yace "Afeefah wannan emerald eyes d'in fa they're killing me." murmushi tayi kad'an ta saukar da kanta k'asa jiki a sanyaye, shima murmushin yayi yace "Better tun kan in suma." tana jinsa tayi banza dashi shima bai damu da rashin amsar ta ba don yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Cigaba da murza fingers d'inta yayi musamman thumb nata cikin murya k'asa-k'asa yace "Ya za'a yi ne Affee? Ina son wannan." ya k'are maganar yana rik'e da thumb nata ya tsare ta da ido, jiki a mace ta d'ago kai tana kallon sa sai biting lips d'insa yake yana murmushi, murmushin itama ta sakar masa a sanyaye tace "Na baka." "Right, barin samo wuk'a in cire abu na kenan." ya fad'a jokingly, murmushi kawai tayi bata ce komai ba shima yayi wata dariya marar sauti kawai bai ce komai ba. Abunda ya bata mamaki shine yadda ta kasa resisting daga rik'on yatsun ta da Foxy yayi, sai ta tsinci kanta cikin wani yanayi daban wanda ba zata iya misalta shi ba kuma ta k'ara tsintar kanta da k'aunar wannan yanayin.

Sake mata hannu yayi wanda sam bata ji dad'i ba har yasa ta d'ago kai suka had'a ido ya sakar mata murmushi lokaci d'aya ya lak'anci rashin jin dad'in ta da hakan "Afeefah." ya kira sunan ta cikin wata irin murya, d'ago kai tayi suka had'a ido yace "Let's talk serious now." gyara zaman ta tayi sai yanzu ta d'an samu nutsuwa tare da ita at least ya rage mata wannan jarababben kallon da yake mata, kallon ta yake cikin ido sai dai wannan kallon da yake mata ba kamar na d'azu bane wannan tattare yake da seriousness a hankali yace "Waye saurayin ki?" tayi mamakin wannan tambayar kuma bata yi tsammanin ta a daidai lokacin ba, girgiza kai tayi cikin sanyin murya tace "Ba kowa." komawa baya yayi ya jingina da kujerar yace

"Big lie." d'ago kai tayi ta kalle sa da mamaki a fuskar ta yadda tashi d'aya ya k'arya ta ta bayan ita kuma iya gaskiya take fad'a masa. Jinjina kansa yayi yace "Big lie Afeefah... With this cuteness, cunning, soft low voice and most of all this youngish body you gotta tell me you're single? Ban yarda ba, ki k'ara jaraba wata k'aryar ta yiwu you can convince me." dariya tayi har hak'oran ta masu kama da milk teeth suka fito tace "That's the fact... I'm single." kallon ta yake a nutse yace

"Meyasa to?" "I'm not interested." murmushi yayi a hankali ya matso yana fuskantar ta sosai yace "Ok.. Suppose I love you? Suppose you love me too? Me kike tunani? Ain't we gonna make a good relationship?" shiru tayi kamar ruwa ya ci ta zuciyar ta sai harbawa take da saurin tsiya abun har tsoro ya bata, kamo yatsun ta yayi cikin hanzari ta fisge har yanzu kanta a k'asa kallo kawai ya bita dashi shi kam idan tana wannan yarintar dariya take basa cikin sanyin murya yace "Talk, d'ago fuskar ki mana." wani crack ya tsinto a cikin muryar ta kamar zata yi kuka tace

"Suppose I don't love you? Me kake tunani? I think we'll be better off alone" dariya yake yi yanzu sosai har drink da yake sipping ya kusa kama sa in between laughter yace "See? Your voice said it all! And I believe mai k'arya d'an wuta ne." haushin kanta taji ya za'a yi tayi reacting in such a way zai gane? Tsuki taja wanda har Foxy sai da ya jiyo ta tayi k'ok'arin saita kanta ta kalle sa tace "Bana sanka fa." "Alright... Naji ba kya sona but please let me love you Afeefah." ya k'are maganar yana kallon ta had'i da rik'o hannun ta ya k'ara da cewa "Please Afeefah." kallon sa take da alamar tambaya irin kanta ma ya d'aure d'innan, lura yayi da yanayin ta cikin sanyin murya yace "I love you Afeefah since the very first day I set my eyes on you, and I'm not saying kema ki soni I'm only asking a favor from you and that's... Let me love you." shiru tayi kanta a k'asa jikin ta ya bala'in sanyi ta rasa me take ciki, k'ara matse yatsun ta yayi gam da nasa yace "Please Afeefah." girgiza kai tayi cikin muryar ta me sanyi tace

"I can't." wani sudden fears ne suka fara rising down inside him gaban sa ya bala'in rikitowa yace "Why Affee? I'm not worth it right?" d'ago da kanta tayi da sauri tace "A'a ba haka bane." "To menene?" "You see Foxy I can't accept you without Fawaz's say-so." ta k'are maganar tana kallon k'wayar idon sa. Har ga Allah ya d'auka wani dalili ne mai k'arfi sai yaji wannan silly excuse a ransa sai cewa yayi Afeefah kenan had'i da gyara zaman sa suna fuskantar juna sosai yace

"So who's that junky to you? What does your love to me has to do with Fizzy?" "He's not a junky, he's my best friend. I've never made a decision without his consent, when he says something, it goes so I have to ask him first." haushi sosai yaji but he tried to calm himself yace

"So you mean to tell me idan Fizzy bai bani license ba that's final?" dariya kawai tayi bata ce komai ba, shima dariyar yayi yace "Kece baki sani ba but we've talk about this with him before you." mamaki ya kamata a hankali yayi dariya ya cire glasses na fuskar sa yace "Yeah, kema ya kamata ki tambaye ni how do I get your contact and so many things about you, without his say-so you know I won't be able to have them right?" jinjina kai tayi a hankali sai murmushi take yayin da shima sai murmushin yake yace "Now... Does that mean we're cool?" b'oye fuskar ta tayi alamar kunya, dariya ta bashi da haka suka cigaba da hira har marece yayi sosai sannan ya biya bills suka nufi wurin da yayi parking suka shiga ya ja suka bar wurin. Tafe suke yana driving da hannu d'aya yayin da d'aya hannun sa yake rik'e da hannun Afeefah yana wasa dashi, a lokacin duk call da ya shigo wayar sa baya picking a cewar sa baya da amfani tunda har yana tare da Afeefah da haka har ya kawo ta gida. Nan ma sai da suka sha wata hirar sosai sannan ya rabu da ita suka yi sallama suka rabu ya ja motar sa shima ya nufi gida.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA*👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*09*

Shigar ta gida bata zarce ko ina ba sai bedroom d'inta ba tare da ta bari kowa yasan da dawowar ta ba lokaci ne da take so ta kasance da zuciyar ta kad'ai. "Foxy." haka ta kirayi sunan nasa a hankali kamar wacce ke rad'a a hankali kuma tabi lafiyar gado ta kwanta tunanin sa ya mamaye zuciyar ta. Wani irin dad'i da farin ciki taji ya lullub'e ta sai take ji a ranta tafi kowacce mace sa'ar samun namiji kamar Foxy. Turo k'ofar aka yi wanda ya katse mata yanayin farin cikin da take ciki, wata mata ce 'yar kimanin shekara hamsin da hud'u zuwa da biyar ta shigo d'akin tare da yin sallama, tashi zaune Afeefah tayi tace "Wa alaiki salam." ba abunda fuskar ta ke bayyanawa sai wani murmushi mai sanyi, cike da mamaki matar ke kallon ta tace

"Dama kin dawo?" ta k'are maganar tana zama bakin gadon next to Afeefah. Sosa kai Afeefah ta shiga yi uwa mara gaskiya tace "Na dad'e da dawowa ai, tun d'azu ma." "Yo sai kuma kiyi shigowar ki ba wanda ya sani? Ni ina cewa ma baki dawo bane." murmushi tayi a hankali tace

"Ayyah kiyi hakuri Umma.. Aunty Nana fa? Ta dawo?" "Itama dawowar ta kenan yanzun take tambayar ki nace baki dawo sai kuma nayi deciding na duba ki anan." cewar Umma, sannan ta k'ara da cewa "Da alama yau baki jin yunwa tunda kika dawo baki nemi kowa ba." murmushi kawai Afeefah tayi a hankali tayi resting kanta akan shoulder d'in Umman tace "Kawai ina cikin farin ciki ne yau Umma." shafa kanta Umman tayi a hankali tace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull