Abokaina complete book 1 - Chapter 5
Abokaina complete book 1 Chapter 5: Abokaina complete book 1 Chapter 5. "Farin cikin me Afeefah?" "Nothing! Haka kawai." tai mata k'arya, murmushi Umman…
4,422 words
"Farin cikin me Afeefah?" "Nothing! Haka kawai." tai mata k'arya, murmushi Umman tayi tace "Allah Ya dauwamar damu cikin farin ciki my Affee." rungume ta Afeefah tayi tace "Ameen Umma na." sannan Umman ta mik'e tsaye tace "Now ki tashi kiyi wanka ki chanza and start doing something regardless, bana san yawan kwanciyar nan." da "To" Afeefah ta mik'e tsaye ta nufi bathroom. Bayan tayi wanka ta fito ta saka jumper da wata sleeveless shirt ta fito ta nufi parlor kai tsaye. Aunty Nana ta samu zaune a k'asa ta baje takardu a gaban ta da system tana aiki kamar koda yaushe, itama Afeefah zaunawa tayi a k'asan had'i da cewa
"Jury my lord!" ta fad'a cike da tsokana, murmushi Aunty Nana tayi ta d'ago kai tace "My Brainy sis kin dawo kenan." "Na dawo tun d'azu.. Aiki kawai kike?" cewar Afeefah tana cin Cheetos da ta samu a gefen Aunty Nana "Wallahi kuwa." sannan ta kalli Afeefah tace "You seem happy today." cewar Aunty Nana, blushing kawai Afeefah ta shiga yi ta chanza labarin zuwa wata tashar.
***
Gefen Foxy kuma bayan ya isa gidan nasu bai sami kowa ba sai Fawaz kad'ai yayin da Fak ya sha giyar sa ya bugu sai bacci yake a d'akin sa. Ba yadda Fawaz bai yi ba don yaga ya tashe sa su yi sallar Maghrib amma innaaa ko alamar samo kansa bai yi ba dole tasa ya hak'ura ya k'yale sa. Basu samu damar yin wata maganar kirki da Foxy ba sakamakon sallar Maghrib da ta gabato, alwala kawai suka yi Fawaz ya limance su suka yi sallah. Da dare Fawaz bai bi ta kan Foxy ba ko parlor'n ma bai zauna ba a d'akin sa ya baje litattafan sa ya fara karatu. Wajajen k'arfe goma na dare Foxy ya turo k'ofar d'akin ya shigo ya samu Fawaz daga shi sai gajeren wando kan gadon sa yana karatu. A bakin gado Foxy ya zauna yana bin sa da takardun dake gaban sa da kallo sannan ya tab'a baki yace "Da safe karatu da rana karatu da dare karatu haba! You're just stressing yourself wallahi." ko d'ago kai Fawaz bai yi ba balle ya kalle sa yace "Naji so bloody what? It's my headache not yours." shrugging Foxy yayi ya mayar da kansa kan wayar sa yace
"Allah Ya bada sa'a mu dai namu ido ne." sai lokacin Fawaz ya d'ago kai ya kalle sa yace "Ameen." sannan ya k'ara da cewa "What about your reg?" d'an kwantawa Foxy yayi kan gadon yace "Ban fara ba." "Sai yaushe?" cewar Fawaz "Zaka fara min sa ido kamar uba na ko? I told you I have everything under control, Uncle K will take care of that." shiru Fawaz yayi bai sake ce dashi uffan ba suna a haka sai ga Fak ya shigo daga shi sai gajeren wando sai mik'a da hamma yake alamar kayan mayen da ya sha sun sake sa, shima samun wuri yayi daga bakin gadon ya zauna ba tare da yace k'ala ba "Kayi sallah?" Fawaz ya jefe shi da tambayar kamar daga sama, dariya Foxy yayi har sai da ya buga k'afar sa da gado da alama yasan za'a d'auki drama tsakanin Fizzy da Fak kenan. Fak ma ya gane dariyar da Foxy keyi cikin husky voice nasa yace "I'm not surprised to hear that since we have an Imam here." sannan ya juyo ya kalli Fawaz yace "Banyi ba." girgiza kai kawai Fawaz yayi yace
"Fak baka kyautawa kanka fa, fisabilillah baka yi sallar Maghrib ba ballantana Ishaa yanzun da ka tashi a maimakon ka fara sauke wannan nauyin dake kanka amma..." katse sa Fak yayi had'i da yin gajeren tsuki yace "Saboda anyi sallah ina bacci is that what you're bitching about? Aiki ya ganka wallahi 'cause it was only 17 shots of Brewdog, you gotta grow up dude." ya k'are maganar yana mik'ewa tsaye ya fice daga d'akin yayin da Foxy sai k'yalk'yala dariyar sa yake. Girgiza kai Fawaz yayi kawai cike da takaici ya cigaba da karatun sa. Suna a haka ne Fak ya shigo all dressed up ya kalli Fawaz yace
"Bani keys na motar ka please." d'an d'ago kai Foxy yayi daga kwancen yace "My bad, sai ina haka?" "It's biz." ya amsa masa a tak'aice, kallon sa Fawaz keyi a nutse a 'yan kwanakin nan ya kasa natsuwa da shige da ficen Fak ko kad'an. Bai ce dashi uffan ba gudun cacar baki ya lalubo keys d'in ya cilla masa shi kuma yayi nasarar kamawa sannan ya juya yace "Sai na dawo." "Aha!" Foxy ya amsa sannan ya fice d'akin. Bayan fitar Fak ne Foxy ya shiga irga ma Fawaz labarin abunda ya faru tsakanin sa da Afeefah d'azun, zufa ta shiga ketowa Fawaz daga sama har k'asa ta kowace kafa ta fatar sa duk kuwa da cewa d'akin a sanyaye yake da sanyin AC, tuni karatun yaji ba zai iya ba jikin sa ya bala'in yin sanyi bai tab'a tunanin Afeefah zata accepting Foxy so easily haka ba, gaban sa ya shiga yankewa yana fad'uwa cikin ransa sai cewa yake he has to stop this! He can't let Afeefah under Foxy's bad influence dole yayi wani abu akai. Har wurin k'arfe goma sha d'aya na dare suna tare da Foxy sannan suka yi sallama ya nufi d'akin sa. Yana fita Fawaz ya rufe k'ofar gam jikin sa har yana rawa ya d'auko wayar sa ya fara dialling number Afeefah, duba agogon d'akin yayi yaga past eleven duk da cewa yasan ba lallai ne tana farke ba amma sai ya tsinci kansa da rashin damuwa da haka iya abunda ya sani shine dole yayi warning d'inta. Gaban sa ne ya yanke ya fad'i lokacin da yaji layin ta busy alamar tana waya, wani irin kishi da tashin hankali suka had'u suka mamaye sa don ya tabbatar ba da kowa take wayar ba sai Foxy, tuni ya koma ya zauna ya tsurawa tile ido yana tunani.
***
*Washegari* _10:00am_ Zuhra ce ke shek'a gudu a cikin motar ta yayin da Nens ke zaune a gefen ta kowaccen su cikin shigar k'ananan kaya zaka iya rantsewa ba 'ya 'yan musulmai bane.
"Breathe...You sound insane wallahi. Wai dakata ma, Fawaz ne kawai namiji duniyar nan ne Zent? Wai me yake damun ki ne? Wallahi sam baki dace da Fawaz ba." idanun Zuhra sun dad'e da chanza launi zuwa ja kamar garwashi sai driving take cikin wata mak'ask'anciyar murya ta kalli Nens tace "If you weren't Nens, I'd kill you for saying that. Wallahi ba macen da ta dace da Fawaz sai ni." dariya Nens tayi hada tafawa sannan tace "Hauka kike yarinya! Then confront him and spell it out mana, sai wani ciccika baki kike kina cewa ba macen da ta dace da Fawaz sai ke bayan kin kasa tab'uka komai." lokaci d'aya fuskar ta ta cika da alhini ta kalli Nens tace
"This girl knows what she's talking about. Nasan abunda nike fad'a Nens, Fawaz is a weird somebody I'm afraid he might turn me down." tab'a baki Nens tayi ta juyar da kanta gefe tana kallon side road tace "You're a soft bitch Zent, anyway, it's your own private grief ke kika sani." ta k'are maganar had'i da shrugging shoulders d'inta in I don't care, share wasu tsirarun hawaye Zuhra tayi cike da tausayi ta kalli Nens tace "Kin fiddo ni da uwar ranar nan... Ina zamuje ne?" "I think hot chocolate is the cure for all the things shitty in life." cewar Nens sai giggling take, dariya suka yi gaba d'aya Zuhra ta k'arawa motar gudu.
*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*10*
_Bayan kwana biyu_ A cikin 'yan kwanakin Foxy yayi nasarar dasa soyayyar sa a zuciyar Afeefah ba kad'an ba Fawaz kuma ba yadda bai yi ba don ganin ya samu keb'ewa da Afeefah don ya ja kunnen ta game da Foxy amma had'uwar tasu taci tura. Yau ya kama Alhamis, tun da safe Fawaz ya tashi ya fara shirin zuwa School ba don komai ba sai sakamakon ya had'a date da Afeefah zasu had'u su tattauna. K'arfe goma cif na safe ya gama kimtsawa cikin d'inkin Kaftan na farar shadda k'al wanda aka yi wa ado da farin sirfani wanda idan ma ba ka saka ido sosai ba ba zaka iya ganewa ba, kansa sanye da hular k'ube fara mai ratsin brown sai k'afafun sa da ya saka black loafers ya kuma d'aure hannun sa da agogo bak'i na kamfanin Gucci. K'amshin sa ga baki d'aya ya cika d'akin shi kansa he can't help sai da ya tsaya yai ta staring kansa a mirror finally ya suri keys da wayoyin sa ya nufi hanyar ficewa daga d'akin. Tafiya yake like the gent he is cikin izzar sa da tak'ama har ya fito parlor'n ya tarar da ba kowa, d'akin Fak ya fara shiga yana kunna kansa wani evil-smelling na abubuwan maye ya daki hancin sa bai san lokacin da ya ciro handkerchief daga aljihun sa ya toshe hancin sa ba yana kallon tarkacen kwalaben giyar sa da packs na Cigars birjik a cikin d'akin. Bai tafi ba haka kuma bai k'arisa cikin d'akin ba haka ya tsaya yana ta kallon sa sai bacci yake da wani evil-snoring dake fitowa daga hancin sa cike da rad'ad'in zuciya daga k'arshe ya jawo k'ofar ya rufe ya nufi d'akin Foxy. Kwance ya same sa yana bacci peacefully unlike Fak da baccin nasa na masifa ne, kutsa kai yayi cikin d'akin had'i da zama bakin gado yana k'arewa d'akin kallo. Sai a lokacin ya lura da wani abu akan bedside drawer gadon wanda ya sa zuciyar sa harbawa da sauri, cikin hanzari ya mik'e ya isa wurin bedside drawer d'in had'i da d'auko abun "Condom!" haka ya fad'a cikin tsintsar mamaki yana zare idanu ya juyo yana kallon Foxy wanda sai sharar baccin sa yake hankali a kwance. Tunanin Fawaz ne yaje yawo ya tabbata mace ta kwana a gidan kenan kuma sun kwana suna aikata fasik'anci, tuni yaji gwiwowin sa sunyi sanyi wanda yasa shi ya zauna bisa gadon ya fara tashin sa, buga sa yake yana fad'in "Foxy! Foxy!!" wani jerking Foxy yayi ya bud'e idanun sa da k'yar suka sauka akan kyakkyawar fuskar Fawaz shi kansa yasan Fawaz kyakkyawa ne, wani gurnani yayi cikin muryar bacci yace
"What's up big dog? Har ka shirya kenan?" wani sour expression ne ya bayyana a fuskar Fawaz ya d'ago condom d'in a k'yamace ya nuna wa Foxy yace "Me wannan?" kallo d'aya Foxy ya masa yayi wani murmushin gefen baki yace
"Condom ne ya aka yi?" "Me kake yi dashi?" da sauri Foxy ya tashi zaune yace "What the fuck me nake yi dashi! Don't talk to me like I'm some kid please! You mean to tell me baka san me ake yi dashi ba ko me?" wani murmushin takaici Fawaz yayi yace "You mean to tell me mace ta kwana a gidan nan?"
"Hell yeah! So what? Ni d'in dutse ne irin ka da ba zan iya kwanciya da mace ba ko kuma yaro ne ni shekaru na basu kai ba?" girgiza kai Fawaz yayi yace "Ko d'aya." "Ma shaa Allah! It's too early for arguments please." cewar Foxy. Shiru suka yi lokaci d'aya sannan Fawaz ya mik'e tsaye yace
"Zan tafi." "School zaka je?" cewar Foxy, jinjina kai Fawaz yayi yace "Yeah!" a tak'aice, dariya Foxy yayi yace "Sheikh Fizzy! Very soon dai zamu saya maka loudspeakers ka fara wa'azi." ya fad'a yana dariya had'i da komawa kwance, ko uffan Fawaz bai ce masa ba ya nufi hanya ya fice daga d'akin. Fitar sa kai tsaye parking lot ya nufa ya shiga motar sa ya ja ya bar gidan.
*School* Fawaz da Afeefah ne zaune cikin cafeteria suna fuskantar juna. Sanye take cikin riga da skirt na atamfa kalar blue mai furanni ja da ratsin fari haka gelen ta ma red. Kallon ta kawai Fawaz keyi tayi masifar masa kyau a ido ya kasa ce da ita uffan a ransa sai cewa yake _I had never seen a girl I wanted so badly as this one, she is the loveliest thing I have ever seen in my life_ wani deep breath Fawaz ya saukar ya sakar mata murmushi yace
"Afeefah!" tayi mamakin kiran ta da yayi da ainihin sunan ta ba kamar ko yaushe ba da yake kiran ta da Brainy, koda kuma ta d'ago kai suka had'a ido ta lura the joking was gone kamar ba wanda ya gama murmushi yanzu ba, a sanyaye tayi murmushi tace "Na'am." cikin sanyin murya yace
"Foxy told me everything and I'm happy for both of you but I want to ask you to be careful.. You need to take breath Afeefah." cikin d'aurewar kai tace "Oldie menene? Me ya faru?" "Ba abunda ya faru, but ina gaya miki ne akan abunda ka iya faruwa nan gaba, Foxy might be poison to every decent girl like you." d'aure mata kai maganganun sa suka k'ara yi tace
"Oldie Foxy fa yana sona I get no wrong with that." "Yeah there's no wrong with that but I want you to be careful 'cause you can't always trust what you heard." shiru tayi na tsawon mintuna goma tana kallon gefe guda sannan ta saukar da numfashi tace "Please Oldie let's go straight to the point, menene? Me zai iya zuwa ya dawo nan gaba saboda Foxy yana sona? Tell me please." duba agogon hannun sa yayi yaga quarter to 12 ya kalle ta yace "Don't you said zaki yi lecture 12?" duba agogon hannun ta itama tayi cike da damuwa a fuskar ta sannan ta d'ago kai tace
"It doesn't matter, please ka gayamin kawai." "Nah, ki tashi kije lecture." ya fad'a yana mik'ewa tsaye had'i da d'aukar keys d'in motar sa da wayoyin sa ya k'ara da cewa "Priority first." cike da damuwa tace "Please Oldie..." bata k'arisa ba ya katse ta yace
"Bana san gardama Brainy, ki tashi muje I'll drop you." ba don tana so ba ta mik'e ta d'auki handbag d'inta cikin taku suka jero suna tafiya sunyi matuk'ar dacewa da juna da haka har suka bar cafeteria d'in suka nufi wurin da yayi parking suka shiga ya tada ya ja suka bar wurin. A hanya tagumi Afeefah ta rafka maganganun Fawaz sai dancing suke a k'wak'walwar ta yayin da shi kuma ba abunda yake sai nazarin ta ya lura Foxy has a special place a zuciyar ta da haka har suka iso daidai lecture room da Afeefah zata yi lecture. Karkatowa yayi ya kalle ta yace
"Don't let our previous discussion keep biting you please... It's study time get rid of everything and focus kinji ko?" jinjina kai tayi a sanyaye tana murmushi ya lura duk ta shiga damuwa cikin k'ank'anin lokaci wanda sam bai so haka ba a duniya idan akwai abunda ya tsana shine ganin Afeefah cikin damuwa, cikin sanyin murya tace "In shaa Allah!" dariya yayi har hak'oran sa farare tas suka fito yace
"Good... I love my brainy girlfriend." dariya itama tayi taja small growing beard d'insa tace "I love my Oldie." sannan ta bud'e motar ta fice tana murmushi, shima murmushin yake ya bita da kallo har sai da ta shige lecture room d'in sannan ya ja motar ya bar wurin. Driving yake bai san dalili ba sai ya samu nutsuwa a zuciyar sa ba don komai ba sai don saboda ya samu nasarar jefa tsoro a zuciyar Afeefah game da Foxy dole ta fara tunani biyu akan sa yanzu.
Gefen Afeefah kuma tunda ta shiga d'akin d'aukar darasin ta samu wuri ta zauna bata k'ara sanin me ake ciki ba. Kalmomin da Fawaz ya barta dasu kawai ke yawo a k'wak'walwar ta musamman _Foxy might be poison to every decent girl like you_ me yake nufi da haka? Tambayar da ta kasa samun amsar ta kenan da haka har suka gama lectures d'in ranar ba tare da ta fahimci komai ba. Da ta koma gida ma kamar ta d'ora ne daga inda ta tsaya don kuwa tunanin maganganun da Fawaz ya gaya mata ne kawai ke hidima da ita.
***
_10:00pm_ Foxy ne ya turo k'ofar parlor'n ya shigo cikin shigar k'ananan kaya na t-shirt fara wacce a gaban ta aka rubuta New York da manyan haruffa sai bak'in pencil trouser da black converse shoes da black cap akansa. Foxy ya tarar cikin shorts launin army color sai sleeveless shirt zaune yana shan tea. Hannu Fawaz ya basa suka tafa yace
"What's up Gee?" zaunawa Foxy yayi kan kujera da ka gansa zaka tabbata ya gaji yace "Fine what's cooking ina Fak?" "Kai zan tambaya ai kai da na barku tare d'azu da safe." cewar Fawaz, zaro ido Foxy yayi cikin mamaki yace "Wai kana nufin tun safe bai dawo ba?" jinjina masa kai kawai Fawaz yayi alamar eh, bai ce komai ba ya mik'e tsaye yace "Allah Yasa lafiya dai." sannan ya juya ya nufi d'akin sa yana cewa "Barin zuba wa jiki na ruwa duk na gaji wallahi" da "Aha!" Fawaz ya amsa masa ya cigaba da shan tea yana kallon tv. Bayan kamar minti ashirin Foxy ya fito cikin pyjamas fari tas ba riga a jikin sa sai danna waya yake yazo ya zauna ya cigaba da danna wayar sa. Wata hayaniya Fawaz ya jiyo daga waje wacce ta ja hankalin sa ya dakata daga kallon tv da yake, hayaniyar dai yaji ta cigaba wanda yasa shi ya rage k'arar tv don k'ara tabbatarwa, jin sautin tv ya ragu yasa Foxy ya d'ago kansa ya kalli Fawaz had'i da cewa
"Yadai?" "Kamar fa hayaniya nike jiyowa daga waje." cewar Fawaz yana mik'ewa tsaye ya nufi hanyar fita parlor'n, shima Foxy mik'ewa yayi ya rufa masa baya zuwa wajen. Wasu samari biyu masu irin shekarun su suka tarar sai d'auki ba dad'i suke da Fak, daidai fitowar su Fak ya samu nasarar naushin d'aya daga cikin samarin yayin da d'ayan kuma ya shak'e sa gam har sai da idanun sa suka firfito
"Innalillahi!" Fawaz ke furtawa ya nufi wurin su da gudu ya finciko Fak daga jikin saurayin, haki kawai Fak keyi wane wanda yayi gasar gudun tsere k'irjin sa sai sama da k'asa yake da ka gansa zaka tabbatar a buge yake baya cikin hankalin sa, cikin sanyin murya Fawaz yace "Haba Faruk! Meye haka? Me yake faruwa ne?" har yanzu sai mayar da numfashi Fak keyi ya nuna d'aya daga cikin samarin wanda yai wa naushi a hanci da yatsa yace "This bitch ass nigga..." ya cigaba da maida numfashi sannan ya k'ara da cewa "Sai na kashe shi wallahi!" tsorata Fawaz yayi da kalaman Fak yayin da saurayin wanda hancin sa har ya b'alle da jini yayo kukan kura ya nufo Fak cike da bala'i yace
"If you can't kill me then it's your funeral!" cike da zafin nama Foxy ya rik'e gayen gam sai fisge-fisge yake yana nema Foxy ya sake sa yayin da Fawaz ma ya rik'e Fak gam shima sai tsuma yake, Fawaz bai ankara ba sai ji yayi Fak ya kufce daga hannun sa ya fara dube-dube dama da hagun sa da alama abun duka yake nema. Bai samu komai a wurin ba wanda yasa ya banzama da gudu ya nufi cikin gidan. Dafe kai Fawaz yayi ya rasa ma abunda zai yi, yana shirin zai bi sahun Fak don ganin me zai yi a cikin gidan sai gashi ya fito rik'e da wuk'a wacce sharp blade d'inta sai k'yalli yake, gaban Fawaz ya yanke ya fad'i yadda yaga Fak ke taku d'aya-d'aya kamar zaki yana huci idanun sa sun chanza launi from weak drunkard he turned into a vicious killer, the drunkard mask slipped away and the killer is there, shima Fawaz nufo sa ya fara yi cikin taku d'aya-d'aya yace
"Faruk put the knife away." "Karka matso ni Fizzy!" cewar Fak cikin kakkausar murya, daka masa tsawa Fawaz yayi yana k'ara matso sa yace "Put the knife away! Baka da hankali ne?" cikin masifa Fak ke kallon saurayin wanda shima k'ok'arin kufcewa kawai yake daga hannun Foxy yace
"Just who the fuck do you think you are?" "He's nobody Faruk, just calm down please." cewar Fawaz cikin sigar lallashi, koda suka kawo daf da juna Fawaz ya rik'e hannun Fak gam wanda ya rik'e wuk'ar dashi suka fara kokawa Fawaz yayi nasarar fisge wuk'ar sannan ya juya ya nufi inda Foxy ke rik'e da d'aya saurayin suka shiga tausar sa da basa hak'uri, jinjina musu kai yayi alamar ya hak'ura sannan ya kalli Fak yace
"With this dudes here, you are damn lucky. But there's gonna be an embarrassing shit if we accidentally meet again." sannan yayi wa abokin sa alama su tafi, sai da suka shiga wata dank'areriyar mota suka tafi sannan samarin uku suka juya suka nufi cikin gidan.
"You're so full of shit man! Haba Fak! Wannan abun da kake yi ba girman ka bane wallahi." cewar Foxy dake k'ok'arin zama kan kujera yayin da Fak ke tsaye rik'e da robar ruwa yana tittilawa cikin sa, sai da ya sha masu isar sa sannan ya dakata ya kalli Foxy yace "Ai wallahi da kun barni nayi gunduwa-gunduwa da naman d'an buroba." numfashi Fawaz ya saukar yace
"Fak me za'a kira abunda kayi yanzu fisabilillah? Karatu fa ya kawo mu Abuja, amma kana amfani da wannan damar kana abunda kaga dama." har Fak ya bud'i baki zai yi magana sai kuma ya tuna bata da wani amfani kawai ya saka kai ya nufi d'akin sa ba tare da yace da Fawaz uffan ba. Foxy da Fawaz sun dad'e suna hira har wuraren 12pm sannan suka yi wa juna sai da safe kowa ya nufi d'akin sa.
*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAI NA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*11*
_5:00pm_ Da misalin k'arfe biyar na yammacin wannan ranar Foxy da Afeefah ne zaune a cikin mota ya maido ta gida bayan d'auko ta da yayi daga School. Yau ba kamar sauran ranaku bane don kuwa yau tayi masa kicin-kicin da fuska sai kace wacce bata san me ake nufi da sakin fuska ba dalili kuwa maganganun da Fawaz ya gaya mata game da Foxy jiya ne. D'ago fuskar ta yayi da hannun sa yana kallon ta har suna iya jiyo numfashin junan su cikin wata kasalalliyar murya yace
"Menene? You seem somehow cold and troubled." cikin sanyin murya tace "I'm only afraid yaudara ta kake ba sona kake da gaske ba." ta k'are maganar kamar zata yi kuka, rud'ewa Foxy yayi yace "Inji waye ne? Wallahi Afeefah I love you so much and I'm not leaving you... Not now... Not ever, I promised to stay till fade." wata natsuwa taji tana saukar mata tare da wani shauk'in kasancewa da Foxy, k'ara matsowa kusa da ita yayi yace "Can you ever find it in your heart to trust me?" murmushi tai masa had'i da jinjina masa kai alamar eh, shima murmushin yayi sannan yace "Ok just give me a chance please... I wanna proof myself to you." murmushi kawai take masa bata ce komai ba a hankali ya jawo ta yayi mata kyakkyawan hugging a cikin k'irjin sa suna shak'ar turaren junan su. Wani yanayi mai wuyar misaltuwa Afeefah ta shiga kuma sai take fata kadda wannan yanayin yayi gaggawar yankewa, cikin sanyin murya tace
"I love you sweetheart." murmushi yayi ya ciro ta yana kallon fuskar ta yace "Kinji abinda kika ce kuwa Affee? Sweatheart fa kika ce! Wow! I have never expect such a compliment." kunya taji tana neman rufe fuskar ta ya sake jawo ta ta fad'a jikin sa yace "I love you too Umm' Abd-rahman." fiddo kanta tayi ta kalle sa da mamaki tace
"Waye Abd-rahman?" shafa cikin ta yayi a hankali yace "My unborn child... Foxy Junior." dariya tayi ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta, shima dariya yayi sannan yace "So now, gida zaki je ko?" turo baki tayi tace "Eh mana." yadda ta turo bakin ne abun ya basa dariya yace
"Oh my God! Girls! Wannan childish attitudes d'in kun nan ko..." bai k'arisa ba ta katse shi had'i da cewa "How do you know it's girls' attitude?" ta fad'a suspiciously and distrusting "Relax! Nima fa ina da sister." "But you told me kai kad'ai iyayen ka suka haifa." dariya yayi yace "Don't tell me you are an FBI Agent... Wannan bincike haka." harara ta dalla masa tace "Just tell me." "Ok I mean k'anwar Fizzy she goes by the name Maryam you must've heard about her, itama haka take da wannan attitudes d'in. Turo baki, harara, murgud'a baki, buga k'afa etc but surprisingly I have a queen here." dariya suka yi dukansu sannan yace "Afeefah! Kishi ko? You thought I go around with girls right?" turo baki ta sake yi tace
"Eh mana! I'm a jealous type." dariya yayi yana biting lips d'insa yace "Then you've come to the right place 'cause this nigga right here has his eyes only on one girl and that's Afeefah." dariya tayi ya rik'o hannun ta a hankali yace "Affee yaushe zaki kawo min ziyara ne?" kallon sa tayi da mamaki tace
"Ziyara kuma?" "Eh mana." "A ina?" "Gidan mu mana and see the cage your man is living in." girgiza kai tayi tace "I'm not going... It's illegal ba darajar mace bane tana zuwa gidan namiji." "Well, ba damuwa ni zanyi ta zuwa ina ganin ki ai but if you visit me like once, kinsan yadda zan ji dad'i kuwa?" nan ma girgiza kai tayi tace "I'm not lying... I won't." haushi yaji amma dai ya danne yace "It's okay you don't have to." kallon sa tayi ta lura kamar bai ji dad'in maganar ba cikin tausasa murya tace
"Baby fushi kayi ne?" murmushin dole ya mata had'i da cewa "Ni d'in banza! Allah Ya tsare inyi fushi da Afeefah." taji dad'in maganar yadda tayi shunning nasa but still bai yi fushi da ita ba, kallon agogon hannun sa yayi yace "Now, sai yaushe kenan?" "Au, kora na ma kake?" "No, naga marece ke k'ara yi but if you tell me to stay I'll stay." murmushi tayi tace "Tam sai munyi waya." kissing forehead nata yayi yace "Right take care. I love you." "I love you too." ta fad'a tana murmushi ta bud'e motar ta fita, sai da ta b'ace daga ganin sa sannan ya ja motar sa ya bar wurin.
***