Abokaina complete book 1 - Chapter 6
Abokaina complete book 1 Chapter 6: Abokaina complete book 1 Chapter 6. Koda ya isa gida wuraren k'arfe shidda na marece, parking yayi ya fito ya sami…
4,460 words
Koda ya isa gida wuraren k'arfe shidda na marece, parking yayi ya fito ya sami Fawaz da Fak a wurin games na gidan daidai court na snooker suna bugawa, without hesitation shima ya nufi wurin a inda Fak shine ke leading yayin da Fawaz kam he's an amateur he's just playing it for fun ba wani k'warewa yayi ba da ache dai ball ce. Koda Foxy ya iso mik'a masa stick d'in hannun sa kawai yayi don yasan Foxy shima ba baya ba wurin buga snooker. Har ya juya zai bar wurin Fak ya dakatar dashi had'i da cewa
"Forget to tell you gobe fa zanje KD." dakatawa Fawaz yayi ya juyo yace "KD kuma?" "Yeah I have an important BBQ to attend it involves a lot of beer and babes." dariya Foxy yayi ya dakata daga buga snooker yaji anyi maganar babes yace "Wow! Lafiya lau ne mutumi na 'cause a beer and a babe, that's what makes the world go round." "Mtsww... Babes! That's all what you think about." cewar Fak, shrugging Foxy yayi yace
"What else is better to think of? Babes are the most important thing in life." tsuki Fak yaja yace "Money and beer are the best relaxation in life." tsuki shima Foxy yayi yace "Kai matsalar ka kenan, d'an banzan san kud'i kamar inyamuri." dariya Fak yayi yace
"Idan baka da kud'i a irin wannan yanayin I think you might just buy a razor and slit your throat saboda rayuwar ka bata da amfani." Fawaz wanda bai tanka musu ba tunda suka fara arguing d'insu tsayawa kawai yayi yana kallon Fak strangely yana jinjina maganar sa ta k'arshe. Shiru yayi yayin da suka cigaba da gardamar su da Foxy sannan cikin rashin k'warin gwiwa yace "Kwana nawa zaka yi idan ka tafi?" "Ba dad'ewa zanyi ba ai, highest kwana biyu." "Right, Allah Ya kaimu goben." da "Ameen." dukansu suka amsa sannan suka shiga shirin sallar Maghrib.
***
*Washegari* Wuraren k'arfe tara na safe Fak ya turo k'ofar d'akin Fawaz ya shigo ya shirya tsaf ya tarar da Fawaz sai baccin sa yake saboda yau Asabar. Bubbuga pillow'n da yake kwance a kai Fak ya shiga yi yana kiran sunan sa "Fizzy!" a hankali Fawaz ya bud'e idanun sa wanda suke cike taf da nannauyan bacci suka sauka kan Fak wanda yake tsaye a kansa, gyara tsayuwar sa yayi yace "Na shirya fa." cikin muryar bacci Fawaz yace "Tam Allah Ya kiyaye ka gaida gida."
"Ai ba zan shiga gida ba da naje wannan old man d'in zai hau barking ba'a yi hutu ba me ya kawo ni." shiru Fawaz yayi sannan yace "Toh kana da kud'i ko?" "Yeah I have enough." "Right, Allah Ya tsare." sannan ya mik'a hannu ya d'auko keys d'in mota ya mik'a masa, girgiza kai Fak yayi yace "No ka barshi da motar wani friend d'ina zamu tafi." "Alright, a dawo lafiya." "Aha!" ya fad'a sannan ya juya ya fita. Sai k'arfe goma da rabi sannan Fawaz ya tashi yayi wanka sannan ya fito, Akbar tea kawai ya had'a ya sha dama bai fiye cin abinci da sassafe ba sai wuraren 12, litattafan sa ya d'auko ya baje su parlor sakamakon yau Asabar ba zuwa school ya fara karatu. Har k'arfe goma sha biyu yana karatun kuma har lokacin Foxy bai tashi ba gashi ya fara jin yunwa yana so ya fito yaji me zai ci ya fita ya nemo musu, jin Foxy shiru-shiru yasa ya mik'e tsaye ya nufi d'akin sa. Koda ya shiga ya same sa ya lullub'e da blankets sai rawar d'ari yake, da sassarfa Fawaz ya k'araso d'akin ya fara tambayar sa "Foxy lafiya kuwa?" murya k'asa-k'asa yace "Fever!" "Ouch! Sorry, ka sha magani?" girgiza masa kai yayi alamar a'a, mik'ewa Fawaz yayi yace "Barin kawo maka wani." sannan ya juya da sauri ya bar d'akin, ba'a d'auki minti uku ba sai gashi ya dawo da magani da ruwan roba yazo ya tsiyaya masa a glass cup ya mik'a masa had'i da maganin, sai da ya sha sannan Fawaz ya kalle sa yace "Sannu Allah Ya sawak'a me zaka iya ci?" da k'yar ya iya cewa "Anything." jinjina kai Fawaz yayi yace "Alright barin je in dawo." ya k'are maganar yana mik'ewa tsaye ya nufi hanyar fita. D'akin sa ya shiga ya d'ora jalabiya akan shorts dake jikin sa ya suri keys d'in mota sannan ya fice. Motar sa ya bud'e ya shiga had'i da yin kicking yaja ya bar gidan. Yaje ya sayo masu abinci mai rai da motsi ba b'ata lokaci ya nufi hanyar gida, koda ya iso ya samu motar Afeefah parked a parking lot d'insu wanda yasa k'irjin sa mummunar bugawa.
*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*12*
Gaban sa ne ya cigaba da dukan uku-uku har ya bud'e motar shi ya fito yana k'arewa motar kallo tabbas motar Afeefah ce.
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un" ya fad'a a fili sannan ya kama hanya jiki a sanyaye ya nufi cikin gidan. Koda ya shiga parlor'n bai same su ba wanda ya bashi tabbaci suna a d'akin Foxy. D'akin ya nufa ba b'ata lokaci yasa hannu ya tura k'ofar had'i da kunna kai, samun Afeefah yayi zaune a bakin gado yayin da Foxy ke kwance yayi matashin kai da cinyoyin ta. Wani irin azababben kishi ya turnuke Fawaz nan take idanun sa suka sauya daga fari zuwa ja ya fara watsa wa Afeefah wani rikitaccen kallo mai nuna b'acin rai yana cigaba da k'arasowa d'akin cikin taku d'aya-d'aya. Kame-kame ta shiga yi saboda irin kallon da Fawaz ke jifar ta dashi ta shiga ture Foxy daga jikin ta ga baki d'aya ta rikirkice. K'arasowa yayi ya ajiye ledar abincin akan bedside drawer ya kalli Foxy yace
"Ya jikin yanzu?" murmushi Foxy yayi sai wasa yake da lil fingers na Afeefah yace "Naji sauk'i ai since she is here." murmushin dole Fawaz yayi yace "Ma shaa Allah!" daga nan bai k'ara cewa komai ba ya sa kai zai fice "Oldie." haka ta kira shi cikin rawar murya kasancewar bata tab'a ganin Fawaz a cikin wannan yanayi ba, tsayawa yayi cik ya juyo yana kallon ta yace "Na'am." "Ba magana ne?" ta fad'a tana murmushin yake, shima wani gajeren murmushi yai mata sannan yace
"Sorry please na sha'afa ne, ya me jikin?" "Da sauk'i." ta amsa masa a sanyaye, jinjina kai yayi yace "Allah Ya k'ara sauk'i." daga nan bai jira abinda zata ce ba ya juya yayi ficewar sa. Affee crybaby ce ta k'arshe, abu k'ank'ani zai iya saka ta kuka ai kuwa nan take ta shiga share hawaye, mamaki ya kama Foxy yace "Hey! Me ya faru?" cikin kuka tace "Oldie is mad." mamaki ya k'ara kama Foxy zai bud'i baki yayi magana ta riga shi "Don't you see he caught us fooling around?" dariya Foxy yayi yana jinjina girman silliness na Afeefah and that's one of the things he love about her, jawo ta yayi to his chest yace "Affee my crybaby, in banda ke da abunki why would he be mad at us? Nasan abunda yake damun sa it's either yunwa yake ji ko kuma he has a serious test shiyasa kika ganshi ba daidai ba, but this isn't a damn thing to worry about da har zaki na min wasting wannan precious hawayen." cigaba da kukan tayi don kuwa tasan ba haka bane wannan kallon da Oldie yake yi mata daban ne "Ko dai in kira sa ne yazo yayi apologizing?" ya tambaye ta, girgiza kai tayi alamar a'a suna a haka sai ga Fawaz ya shigo d'akin da sauri ta fisge jikin ta daga jikin Foxy ta shiga kame-kame, ko kallon su bai yi ba ya wuce wurin bedside drawer ya d'auki ledar abinci d'aya ya juya zai fita Foxy yace "Fizzy don uban ka kazo kana wani mazurai ka firgita min yarinya a banza" dakatawa Fawaz yayi sai yanzu ya lura da yadda Afeefah ke ta share kwalla, da mamaki ya kalle su yace
"What happened? Me ya same ta?" "You happened!" cewar Foxy "Kazo kana jifar ta da wani strange looks ai dole ta firgita." murmushin dole Fawaz yayi had'i da cewa "I'm sorry Brainy I wasn't myself, kaina ne yake ciwo." jawo ta Foxy ya sake yi wanda jawowar ya bala'in dukar zuciyar Fawaz kamar yayi kururuwa nan take yaji k'afafun sa ba zasu iya d'aukar sa ba he feel like collapsing, zuwa Foxy yayi daidai kunnen ta yana shinshina ta cikin murya k'asa-k'asa kamar mai rad'a yace
"Kinji ko? I told you he isn't mad at us." Fawaz wanda tuni ya bar d'akin sakamakon wani sudden popping da zuciyar sa keyi dama already yana fama da wani azababben chest pain, koda ya fito d'akin ya jingina da bango nan ya nemi yunwar da yake ji ya rasa yaji sam baya sha'awar abincin appetite d'insa ma duka ya nema ya rasa ga kansa da ya fara sarawa a hankali a hankali. Da k'yar ya ja kansa zuwa kan sofa ya zauna ya dafe kansa ba abunda yake maimatawa a ransa sai Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un saboda wannan masifa ce babba a wurin sa; macen da yafi k'auna a duk duniya yau itace kan dausayin fasik'anci da babban aminin sa.
Gefen Foxy da Afeefah kuma soyayya ce kawai ake ta zubawa like no tomorrow, kwance yake akan cinyoyin ta tana masa kitso da sumar kansa sai lumshe ido yake nan take kuma kitson ya fara turning d'insa. Tashi zaune yayi yana mata wani wahalallen kallo yace
"Affee." d'ago kai tayi ta kalle sa bata ce komai ba ta lura duk ya chanza, cikin wata sark'ak'iyar murya yace "Kiss me please." ya fad'a yana k'ara kusanto ta suna jiyo numfashin junan su yace "Please Affee." jikin ta ne ya shiga rawa yadda taga yana bin jikin ta da wani kallo cike da sha'awa lokaci d'aya kuma kamar mayunwacin zaki ya tura kansa wurin neck d'inta ya fara kissing nata passionately had'i da wasu love bites masu zafi. Kuka ta saki k'asa-k'asa tana ture shi duk da cewa ya gama kashe jikin ta ba wani k'arfi ne da ita ba, had'a ta yayi da k'irjin sa yana pulling gashin kanta yana kallon ta idanun sa sun fara chanzawa zuwa ja yace "Affee I love you." hannun ta ta d'aga da k'yar ta shafa sajen sa tace
"I love you too." murmushi yayi yace "Really?" had'i da saka hannu ya fara zipping rigar ta, rik'e hannun sa tayi gam jikin ta na rawa ta kasa ce masa komai sai girgiza masa kai take alamar a'a, haka ya zame mata kamar wani hungry zombie ya kai kansa wurin k'irjin ta ya fara mata wasu love bites akan rigar ta masu masifar rikitarwa. Kuka ta fashe masa dashi ta fara halba k'afafu tana kiran sunan sa cikin wata kasalalliyar murya, d'ago kai yayi ya had'a bakin sa da nata yana wani mahaukacin sucking tare da biting d'insu, cizo ta dank'ara masa a lips wanda yasa yayi gaggawar d'ago kai ya kalle ta yana murmushi yace
"Baby ni kika ciza ko?" jinjina masa kai tayi alamar eh wanda yasa shi k'ara yin murmushi yace "Fine! Nima sai na rama." yana gama fad'ar haka ya tura kansa cikin k'irjin ta yana neman cizon ta yayin da sai dariya take tana neman b'oye k'irjin ta, haka kuma abun ya shiririce ya koma wasa ga baki d'aya gadon sai da suka hargitse sa at last bacci ya kwashe su dukan su.
Afeefah ce ta fara farkawa daga baccin taji Foxy a bayan ta yayi hugging d'inta ta baya had'i da crossing k'afafun sa a cikin nata, murmushi tayi da dubara ta samu ta janye kanta sai da ta k'are masa kallo tsaf tukuna taga idan yana bacci yafi ko yaushe kyau daga k'arshe murmushi tayi ta mik'e ta nufi bathroom. Sai da ta fara wanka saboda wasan da suka yi ba kadan ba sannan tayi alwala tazo tayi sallar azahar har lokacin Foxy yana nan yana ta baccin sa. Sai a lokacin tunanin Fawaz yazo mata ta mik'e ta d'auki mayafin ta ta yafa kanta ta fice daga d'akin. Koda ta fito parlor'n bata same shi ba wanda ya tabbatar mata yana d'akin sa, d'akin nasa ta nufa ta murd'a handle ta shiga da sallama ta same shi kwance kan gado ya k'urawa sama ido gefen sa ga takardu da system sai dai ba abunda yake sai tunani. Shigowar Afeefah ta katse masa tunanin da yake ya kalle ta had'i da tashi zaune, murmushi mai wuyan fahimta suka yiwa junan su sannan tace
"Just checking in... Ya ciwon kan?" wani murmushi yai mata a forced smile but a smile sannan yace "Alhamdulillah da sauk'i." sannan ya nuna mata gefen gado gefen da yake zaune alamar tazo ta zauna, ba musu tazo ta zauna sannan ya fuskance ta yace "Brainy me ya kawo ki gidan nan?" gaban ta ne ya fad'i ba abunda yazo mata a rai sai jiya da Foxy yake tambayar ta yaushe zata kawo masa ziyara tace masa ba darajar mace bane zuwa gidan namiji amma yau gata a gidan maza har tayi sharing wurin kwanciya da wani namiji ba muharramin ta ba, cikin muryar ta me sanyi tace
"I just came to check on him... Ya gayamin baya da lafiya tun daren jiya." "But I thought you knew what you're doing Afeefah... This isn't a lady-like manner, ba darajar mace bane a ganta a irin wannan gidan da ba kowa a ciki sai maza" shiru tayi bata ce masa komai ba ta saukar da kanta k'asa yayin da ya tsare ta da ido, numfashi ya furzar yace "Afeefah." a hankali kuma cike da sanyin jiki ta d'ago kai ta kalle sa tace
"Na'am" "Get rid of Foxy out of your life!" gaban ta yayi mummunar fad'uwa ta d'ago kai ta kalle sa taga shima ita yake kallo, jinjina mata kai yayi ba alamar wasa yace "And you get rid of him fast, all he'll ever bring you is grief." hawaye ne suka zubo mata ta d'ago kai ta kalle sa cikin rawar murya tace
"Wallahi Oldie ina san Fahad, how could I get rid of something I can't live without?" murmushin takaici yayi yace "Foxy is my best friend right?" "Right, but baka san miye a zuciyar sa game dani ba." "Yeah I don't read heartbeats but I do read people. I've known him a hell of a long time Afeefah... Since our childhood... And you haven't been around here long enough to get wise to his little tricks." sannan ya ja numfashi yace "Afeefah get rid of Foxy out of your life 'cause you aren't gonna like where this is heading." kuka yanzu take yi sosai tace
"Stop telling me to get rid of him! I can't! Ba zan iya ba wallahi! He's born for me! He might be whatever you think of him but to me he's sensible, good-humored, lively and I never saw such an impressive manner in every man. I was very much flattered in him, he whispered love words to me and most of all he wants to marry me he even call me the mother of his unborn child tell me..." bata kai aya ba ya dakatar da ita sakamakon maganganun nata sun zame masa kamar tana narka ruwan darma ne tana zubawa a kunnuwan sa ya lura da cewa Foxy has won, cikin sanyin murya yace
"Ya isa haka Brainy." saboda tana da cutar Dyspnea(shortness of breath) kuma yawan kuka ka iya tado da rashin lafiyar, lallashin ta ya shiga yi saboda yaga numfashin ta ya fara sama da k'asa yace "It's alright Afeefah... Calm down okay? Foxy naki ne now and ever in shaa Allah, you know you're having difficulty in breathing kar abun ya taso take it easy please" ya shiga share mata hawayen da suka zubo kan fuskar ta wacce already har tayi ja da hannuwan sa, cikin ikon Allah kuma sai gashi ta fara dawowa normal a hankali a hankali, mik'ewa yayi ya bud'e k'aramin fridge dake d'akin ya d'auko robar ruwa ya bud'e mata ya bata ta sha sannan ya cigaba da calming d'inta. Sai da ya tabbata ta dawo daidai sannan ya chanza hira ya fara cracking mata funny jokes in just a few minutes sai gashi tana dariya kamar ba ita ba, sun share more than one hour sannan ta mik'e tsaye tana murmushi tace
"Oldie you are a sweetheart to worry about me but I'll be fine in shaa Allah... I can't ask for a better friend than you... You went above and beyond... You are a pal; a real pal and I love you." murmushi yayi har hak'oran sa suka fito har cikin ransa yaji dad'in maganganun ta yace "I love you too Brainy." "Lemme check on him koda ya tashi baccin." jinjina mata kai yayi yana murmushi yace "Alright." sannan ta juya ta fice leaving Fawaz stunt and dead inside.
*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*13*
Koda ta shiga d'akin ta jiyo motsin Foxy a bathroom alamar yana wanka, samun wuri tayi gefen gado ta zauna tana jiran sa. Fitowa yayi d'aure da towel a k'ugun sa da wani k'arami a dokin wuyan sa yana tsane ruwan jikin sa dashi ya kalle ta yayi murmushi yace "Sai kika tashi kika barni ko Affee?" murmushi tayi ta chanza maganar tace "I'll get going" dakatawa yayi yace "Tun yanzu? Ki bari zuwa anjima I'll drop you." damuwa ta bayyana a fuskar ta tace
"I gotta go sweetheart... Naga missed call d'in Umma har biyu bata san lokacin da na fito ba kuma da mota na fito." ta k'are maganar tana jujjuyawa wayar ta a hannun ta, shiru yayi jim kad'an sannan yace "Right, yanzu sai yaushe kenan kuma? Sai na k'ara wani ciwon right?"dariya tayi had'i da mik'ewa ta fara gyara d'aurin d'ankwalin ta tace "A bakin ka dai aka ji." d'an tsayawa yayi yana kallon ta da mamaki yace "Don't tell me zaki tafi without helping me get dressed." dariya tayi ta matso kusa dashi ta karb'i shafa man da yake ta gama ta d'auko masa long sleeve fara wacce tayi daidai jikin sa mai wasu black stripes sai jean sai wasu unisex converse bak'ak'e. Tsaye suke a gaban madubi tana b'alle masa buttons na hannun long sleeve d'in ta gama tasa comb ta k'ara taje sumar kansa lastly ta d'auko turarukan sa kusan kala uku designers ta feshe shi dasu. K'ara kallon sa tayi cikin madubin tayi murmushi tace
"You look breathtakingly handsome." murmushi yayi yace "Thanks sweetheart." juyawa tayi zata fara shirya kanta itama karaf ya dakatar da ita yace shi zai mata kwalyan, ganin yana neman takaita fuskar ta musamman eyebrows d'inta da mascara yasa ta karb'e abunta tace bata so. Sai da suka shafe kusan awa d'aya sannan suka gama shiryawa, rik'o hannun ta yayi da hannu d'aya d'ayan hannun kuma ya rik'o mata handbag su fito parlor'n a inda Fawaz kam yana d'akin sa, kallon ta yayi ya matse yatsun ta deliberately har sai da tayi 'yar k'ara yace "What?" turo baki tayi ta fisge hannun wanda har ya fara ja a inda ya matse ta tace
"Kana min mugunta and you're asking me what." murmushi yayi ya d'an mare ta kad'an a fuska yace "Lazy girl!" sannan ya sake rik'o hannun ta yana mata wani intimidating smile yace "I got so bored today... You don't know how much I've enjoyed you coming to my place today... It makes this evening one of the nicest and most exciting evenings I've ever spent in my life... I've really loved it." murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba a hankali ya matso kusa da ita yace "Oya my last kiss." kunya taji ta kawar da kanta gefe tana ja da baya tana murmushi, tsayawa yayi cik yace "Oh really? Kunya na ma kike ji?" jinjina masa kai tayi alamar eh, takowa ya dinga yi yana matso ta yace "And you're gonna kiss the hell out of me whether you like it or not." sannan yayi grabbing d'inta without hesitation ya had'a bakin sa da nata, tun tana ciccijewa har ta saduda ta bada gari idanun ta suka fara lumshewa daga k'arshe ma fad'awa suka yi kan sofa dukansu. Sun kwashe minti ashirin ba abunda suke sai hot romance sannan ya k'yale ta ya d'ago kai ya kalle ta idanun sa har sun fara sauyawa yana licking lips d'insa yace "Affee." d'ago kai tayi ta kalle sa yace "I never knew this type of kiss existed... Wallahi bansan da akwai irin wannan kiss d'in ba Affee... Just like I'm falling and flying." hugging d'insa tayi tightly ta tura kanta cikin k'irjin sa tana jin k'amshin turaren sa tana murmushi, a hankali ya rik'o hannun ta ya d'ora shi daidai zuciyar sa yace "Feel my heartbeat." ji tayi tana bugawa a hankali a hankali, murmushi yai mata yayi kissing forehead nata yace "Muje ko?" jinjina masa kai tayi alamar eh a hankali ya mik'e ya kamo hannun ta itama ta mik'e sannan tace
"Oldie fa?" "Bari in duba shi yana d'akin sa maybe." ya fad'a ya nufi d'akin Fawaz, koda ya shiga ya same shi yana bacci alhali kuwa idon sa biyu duk abunda yake faruwa tsakanin su a parlor a kan kunnen sa kawai he don't have the courage da zai iya fita suyi bankwana, juyowa kawai Foxy yayi ya dawo yace "Bacci yake idan ya tashi zan gaya masa kin wuce."
"Alright." ta fad'a had'i da d'aukar handbag d'inta suka jera tare suka fice. A bakin mota ma sai da suka sha wata soyayyar da k'yar suka yi bankwana ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe sannan ta ja ta bar gidan shi kuma ya koma ciki.
Koda ta shiga gida around five o'clock, sai lokacin ta fara tsoron wacce k'arya zata fad'awa Umma saboda yau shine rana ta farko da ta fara satar fita. Gaban ta ne ya yanke ya fad'i lokacin da ta shigo parlor'n ta samu Daddy, Umma da Aunty Nana dukansu a cikin parlor'n, tsoro da fargaba da rashin k'warin gwiwa suka had'e mata wuri d'aya da k'yar take d'aga k'afar ta har ta k'araso cikin parlor'n, tun kafin ta zauna Daddy ya jefe ta da "Ina kika je tun safe ba kya gida?" kame-kame ta shiga yi tana stammering tace
"Um.. Naje gidan su Laila ne." "K'arya kike!" Daddy ya fad'a cikin tsawa, jikin ta ne ya shiga b'ari idanun ta suka ciko da hawaye tace "Wallahi Daddy da gaske nike kuma a kira Lailan a ji."
"Shine za'ai ta kiran ki ba zaki d'aga ba?" cewar Umma idanun ta sai watsa mata wani kallo suke cike da tuhuma, hawaye ne suka cigaba da gudu a fuskar ta cikin rawar murya tace "Banji ba wayar tana a jaka." ta zura hannu a jakar don d'auko wayar, cikin kakkausar murya Daddy yace
"Yaushe kika fara satar fita ne Afeefah? Haka kika ga yayar ki tana yi? Ko kin tab'a ganin tasa k'afa ta bar gidan nan ba tare da sanin kowa ba?" girgiza kai tayi alamar a'a tana sobbing sai kuma ta basu tausayi gashi tana da matsalar numfashi cigaba da da yi mata fad'an shi zai sa ciwon ya taso saboda zata cigaba da kukan ne uncontrollably, cikin tausasa murya yace "Be a good girl Afeefah... Kar in sake ji kin fita ba tare da sanin kowa ba kinji?" da sauri ta jinjina kai alamar toh sannan ta mik'e tsaye ta kalli Umma a sanyaye sannan ta nufi sashen ta. Umma taso ta cigaba da tuhumar ta saboda ita mace ce ta hango yanayin da ta shigo gidan ba yanayin da ta saba ganin ta a ciki ba sannan ta jiyo wani k'amshin turaruka tattare da ita wanda sam turarukan basu yi kama da na mata ba ballantana tace a gidan k'awar ta ta shafo amma sanin tuhumar ta d'in kamar barazana ce ga lafiyar ta kar aje a b'ata goma biyar bata gyaru ba yasa ta k'yale ta kawai.
_10:00pm_ Afeefah ce kwance bisa makeken gadon ta da waya a hannun ta tana dannawa tana murmushi wanda yake nuna chat take. Umma ce ta turo k'ofar ta shigo amma sam bata ji ba tayi nisa cikin wayar ta sai blushing take. Umma tayi tsayuwar ak'alla minti goma a bakin k'ofar amma sam Afeefah bata san cewa da akwai mutum a cikin d'akin ba
"Afeefah!" ta daka mata tsawa har sai da ta diririce ta saki wayar tana kallon ta "Uban mi kike yi ne a cikin wayar da har na shigo baki ji ba?" saukar da kanta tayi k'asa bata ce komai ba fatar ta kada Umma tace zata duba wayar saboda irin dirty conversation da yake gudana tsakanin ta da Foxy harta pant d'inta a jik'e yake a lokacin "Karatu ya dace ace kina yi yanzu ba a ganki rik'e da waya ba" cewar Umma, nan ma shiru tai mata bata ce komai ba cikin kakkausar murya Umma tace "Afeefah!" d'ago kanta tayi ta kalli Umma bata ce komai ba "Kinsan me? You're no longer the brainy kid... Kin chanza kanki da kanki, ba kya karatu, ba kya zama ayi hira dake kullum kece nan kwance rik'e da waya kuma kece nan kike gayamin in the next week zaku fara tests." shiru tayi idanun ta suka ciko da hawaye ita kanta tasan ta chanza a 'yan kwanakin nan sam ta daina karatu zai mata wuya ma ta iya tuna when last da tayi karatu. D'ago kai tayi ta kalli Umma cikin rawar murya tace
"Umm..." bata barta tayi magana ba tace "Na sani dama. 'Yar gwal! Ba za'a tab'a miki magana ba a kwashe lafiya yanzu zaki fara share hawaye kamar wacce aka daka... Ki cigaba ga wurin nan." tana gama fad'ar haka tayi ficewar ta, hawayen suka cigaba da zubo mata taso tayi karatun amma ta kasa daga k'arshe jawo wayar ta tayi ta kira Foxy suka fara hira.
***
_Bayan kwana biyu_ Soyayya mai k'arfi ke cigaba da gudana tsakanin Afeefah da Foxy, kullum suna tare a makaranta ko wani wurin shak'atawa sai dai tun lokacin tayi k'ok'arin hana kanta daga zuwa gidan su duk kuwa da cewa tana kwad'aice da hakan. Gefen Fawaz kuma k'unci da rashin natsuwa ne kullum tattare dashi game da soyayyar Foxy da Afeefah, ya rasa wacce hanyar zai bi don fahimtar da ita game da had'arin da take ciki amma ya rasa, duk hanyar da zai bi ya bi amma ta kasa fahimtar sa. Faruk ma ya dawo daga tafiyar sa daga garin Kaduna abubuwa kuma sun cigaba da gudana kamar ko yaushe.