Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 7

Abokaina complete book 1 - Chapter 7

Abokaina complete book 1 Chapter 7: Abokaina complete book 1 Chapter 7. Yau ya kama Lahadi Fawaz ne ke tuk'i a cikin mota yayin da Faruk ke zaune gefen sa…

4,471 words

Yau ya kama Lahadi Fawaz ne ke tuk'i a cikin mota yayin da Faruk ke zaune gefen sa suna dawowa daga asibiti saboda a 'yan kwanakin Fawaz baya jin dad'i. D'aukar takardar da aka rubuto ma Fawaz magani Faruk yayi sannan ya kalle sa yace

"What did the doctor said?" juyowa yayi ya kalli Faruk duk ya rame idanun sa duk sun fito yace "BP ne." zaro idanu Fak yayi yace "What the fuck! Me yake damun ka haka?" "It's Foxy and Afeefah... I just wanna do something about so-called abomination they are in before it's too late." "Afeefah is smart, she can take care of herself" cewar Fak, girgiza kai Fawaz yayi in disbelief yace "But she is a plain dumb when it comes to Foxy. Bata san halin sa ba, she doesn't know what he is capable of. A iyakar tunanin ta d'auka take yana sonta kuma kai kanka kasan yana sonta ne for a reason best known to himself."

"To ka manta da ita mana, ko dole ne? See Fawaz... No girl is worth a guy worrying himself about, I found out that years ago... If she doesn't toe the line, there are plenty who will and if I guessed right ba Afeefah ce kawai mace ba." yanzu kam idanun sa ma sun chanza kala cikin wata irin murya yace "Faruk ina son Afeefah kafi kowa sanin haka ba zan iya mantawa da ita ba... She makes a picture I keep in mind; a picture that stays in me for the rest of my days.. It beats me how a decent girl like her could think of living with a spoilt guy like Foxy." shiru suka yi dukansu sannan Fawaz yace "Fak that shit is eating me alive."

"You gotta sort it with him." cewar Fak, nan ma girgiza kai Fawaz yayi yace "Foxy matsiyaci ne, he won't stop har sai ya cimma burin sa akanta... That ain't right either. " shrugging Fak yayi yace "Then you've got yourself a job dude... Sai ka zauna har su kashe ka. " duka Fawaz ya kaiwa steering motar murya k'asa-k'asa yace

"Fuck it!"

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*14*

_8:30pm_ Da dare misalin k'arfe takwas da rabi Fawaz da Fahad ne zaune a cikin parlor'n suna hira yayin da Faruk ke d'akin sa, suna cikin hirar ne sai ga Ibro yaron dake musu 'yan aikace-aikace ya turo k'ofar parlor'n ya shigo, dubansa Foxy yayi yace

"Yane Ibro? Har yanzu baka wuce ba?" "Zan wuce ne sai ga wasu sun zo suka ce na nemar masu iso." "Wasu kuma?" cewar Fawaz, jinjina kai Ibro yayi had'i da cewa "Eh Oga." "Ka sansu ne?" Fawaz ya k'ara tambayar sa, girgiza kai yayi alamar a'a yace "Ban san su ba." duba Fawaz ya kaiwa Foxy yace "Ko wurin ka suka zo ne?" girgiza kai Foxy yayi yace "Nah, bani tunani gaskiya." dubar Ibro Fawaz yayi yace "Je kace su shigo."

"Toh Oga." ya amsa sannan ya fice. Cikin k'ank'anin lokaci sai ga wasu maza guda biyu dogaye cikin shigar bak'ak'en suit sun shigo kowannen su ya b'oye fuskar sa cikin bak'in glasses, dubar su kawai su Fawaz keyi har suka shigo parlor'n suka basu hannu ana cikin haka sai ga Fak ya fito daga d'akin sa. Ganin wad'annan mutanen yasa ya tsaya turus cike da mamaki alamar shima bai yi tsammanin su a wannan lokacin ba, murmushi mutanen biyu suka yi sannan suka nufi sofa suka zauna d'aya daga cikin su yace "Faruk kenan nasan baka yi tsammanin mu ba ko?" yatsina fuska Faruk yayi yace "You guys are so full of shit, na gaya muku it should stay between us me kuma ya kawo ku nan?" ga baki d'aya kan Fawaz da Foxy sun gama d'aurewa, dubar wanda ke magana Foxy yayi yace

"Bro what's going on?" "Your friend here..." ya d'aga hannu ya nuna Fak sannan ya cigaba da cewa "Is one of our gang, mun dad'e tare dashi probably two years now. Normally, our gang used to adhere some stuff to its members at an affordable price, tun lokacin Fak yake cin bashin k'ungiya bai tab'a biya ba daga k'arshe ma muka daina ji daga gare sa shiyasa muka biyo sahu." sannan ya juya ya koma kan Fak yace "Kasan abunda muke iyawa Fak, kinda return the money." gyara zama Fawaz yayi yace

"Naji kace you used to adhere some stuff to your members, wanne irin stuff kenan?" "Codeine!" cewar mutumin sannan ya zarce da cewa "And other varieties of illegal narcotic drugs." "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" abinda Fawaz ya fad'a kenan yasa hannun sa biyu ya tallabo fuskar sa dashi yana tunani. Shiru parlor'n yayi na tsawon minti biyar sannan Fawaz yace "Nawa ne kud'in?" "Two hundred and fifty thousand naira" cewar mutumin, zabura Fak yayi ya mik'e tsaye yace "Buroba! Har yaushe suka yi yawa haka? Lemme tell you something, I ain't paying a single kobo you can do your fucking worst!" mik'ewa d'aya daga cikin su yayi ya zura hannayen sa a aljihu yace "Haka kace?" "Haka nace!" cewar Faruk, murmushi mutumin yayi wani arnen murmushi sannan ya kalli wanda suka zo tare yace "Muje." mik'ewa d'ayan yayi ya taka ya isa wurin Faruk yasa hannu ya shak'e wuyan sa gam yace "Goddamn it Faruk! Goddamn it! K'arya kake wallahi! You must pay the money!" mik'ewa Fawaz da Fahad suka yi lokaci d'aya yayin da mutumin ya taka ya isa wurin su Fak yayi k'ok'arin cire hannun d'an uwan sa daga wuyan Fak ya shiga bubbuga kafad'ar sa yace

"Ya isa haka! You don't want break your hand on this kid" sannan ya kalli Faruk yace "Watch out for us Fak, this isn't over." sannan suka juya zasu fita, dakatar dasu Fawaz yayi had'i da cewa "Ni zan biya ku kud'in." juyowa suka yi lokaci d'aya suna kallon Fawaz ya jinjina musu kai yace "Yeah zan biya." sannan ya fiddo wayar sa yayi demanding account number da zai musu transfer, nan take mutumin ya gaya masa cikin 'yan mintuna k'alilan alert na two hundred and fifty thousand naira ya shiga wayar mutumin suka sa kai zasu fice Fawaz ya dakatar dasu had'i da cewa "From now on Faruk baya tare da k'ungiyar ku you get that? Kuma koda ya dawo muku kuka yi gangancin bashi wani abu then it's your own cup of tea 'cause nobody is paying you a damn kobo." murmushi mutumin yayi ya jinjina kai suka yi shaking hands da Fawaz suka fice. Shi kam Fawaz ya ma rasa me zai ce da Fak wanda yasa shi wucewar sa ya nufi d'akin sa kawai ya barsu tare da Foxy.

*Washegari* _2:30pm_ Foxy ne kwance a d'akin sa daga shi sai gajeren wando AC sai ratsa shi yake ta ko ina kuma dawowar sa kenan daga school bayan sun had'e da Afeefah yayin da Fawaz da Faruk duka basa nan Fawaz yaje school Faruk kuma yaje gantalin sa. Sallama yaji daga parlor wanda yasa ya k'ara saurarawa ya tabbatar sallama ce kuma muryar mace, mik'ewa yayi ya zura jallabiya ash akan gajeren wandon sa don yasan ko wacece ke sallama da akwai sauran mutunci a tattare da ita don ya tabbata karuwan sa dake zuwa gidan ba wacce zata tsaya a parlor ballantana tayi sallama. Fitowar sa yayi arba da Zuhra a tsaye cikin hijab bak'i, sakin fuska yayi yana dariya yace

"Ranki ya dad'e yau kece a gidan mu cikin ranar nan?" murmushi tayi tace "Wallahi kuwa." k'arasowa yayi cikin parlor'n ya nuna mata wuri had'i da cewa "Zauna mana." ba musu ta zauna shima ya zauna sannan yace "Ya kike ya gida ya Ammi?"

"Kowa lafiya, Ammi tana gaida ku tunda ku ba kwa zuwa gaida ta." sosa kai Fawaz yayi yana murmushi yace "Wallahi ba haka bane boko ne yayi yawa amma..." katse shi tayi da harara sannan tace "Um... Ai dama bakin ku d'aya." dariya Foxy yayi sannan ya mik'e tsaye yace "Lemme get you a drink." bata ce komai ba sai murmushi da tayi ya mik'e yaje fridge ya d'auko lemon kwali yazo da glass cups guda biyu ya tsiyaya mata ya mik'a mata, murmushi tayi ta karb'i cup d'in had'i da cewa

"Thanks." sannan ya koma ya zauna yace "Kinyi sa'a fa nima ban dad'e da dawowa ba da ba zaki tadda kowa a gidan ba." "Ayyah!" ta fad'a sannan tace "Fawaz baya nan kenan." gyad'a kai yayi yace "Yeah yaje school but ina kyautata zaton yana hanya yanzu 'cause ya gayamin tun 12 zai dawo bansan me ya rik'e sa ba har yanzu." ajiye cup d'in lemon tayi ta mik'e tsaye, da sauri Foxy yace "Ki jira sa mana in shaa Allah yana hanya." bata da zab'i haka ta koma ta zauna ta shiga jiran tsammani lokaci zuwa lokaci suna jefa hira da Foxy. Bayan kamar minti goma sai suka ji tsayuwar mota, murmushi Foxy yayi yace "I think gayanan ma." murmushi itama tayi sai da aka kusa five minutes sannan Fawaz ya shigo parlor'n, ganin Zuhra zaune ya basa mamaki fuskar sa ba yabo ba fallasa yace "My sis yau kece a gidan mu?" murmushi tayi tace

"Niche Ya Fawaz... Sannu da zuwa." "Yauwa ya kike?" ya fad'a yana zaunawa kan kujera "Lafiya k'alau." ta amsa sannan Foxy yace "Ta sha jiran ka fa." "Ayyah!" cewar Fawaz "Ya Ammi?" "Tana lafiya." ta amsa ta cigaba da wasa da yatsun hannun ta, daga nan bai k'ara cewa komai ba sai ma kwantawa yayi akan sofa sai kuma shiru ya biyo baya. Foxy ne ya katse shirun ya dubi Fawaz yace "Wurin ka fa tazo." kallon Zuhra Fawaz yayi yace "Wai haka Zuhra?" jinjina kai kawai tayi kanta a k'asa, tashi yayi zaune sannan yace "Tam gani ya aka yi?" shiru tayi ta kasa magana sai wasa take da hannun ta ya lura kamar zaman Foxy a wurin ne ya hana ta magana, juyowa yayi ya kalli Foxy yace "Baabaa ya za'a yi ne? We need privacy." mik'ewa Foxy yayi yace

"Don fa Zuhra zan tashi ba don wani k'ato ba." murmushi kawai Fawaz keyi don yasan dashi yake sannan ya sake cewa "Bani keys d'inka inje in sayo mana lunch ma" mik'a masa Fawaz yayi sannan yayi sallama da Zuhra ya fita. Fitar Foxy keda wuya ta tashi ta dawo kusa da Fawaz ta zauna har suna gogar jikin juna, mamaki ya kama Fawaz ya kalle ta yace "Me haka ne?" d'ago kai tayi tana kallon sa wanda idanun ta sun cika taf da hawaye, mamaki ya k'ara Fawaz shi d'aukar sa ma ba lafiya ba yace "Zuhra menene? Me yake damun ki?" ji tayi uwa tace kaine kake damuna sai dai tayi shiru ta cigaba da sharar kwalla. Ganin bata da niyyar magana yasa Fawaz ya mik'e tsaye yace "Tunda ba zaki magana ba ni barin shiga daga ciki in huta" shan gaban sa tayi tana kuka tace

"Zanyi magana." ja yayi ya tsaya yace "Ina jin ki." cikin rawar murya tace "Ya Fawaz ina san ka." murmushi yayi ya gane inda ta nufa sarai sai dai ya wayance mata a bai ganen ba yace "Zuhra you are my sister from same grandpa ta ya zan k'i ki? Nima ina san ki." girgiza kai tayi hawaye na cigaba da gudu tace

"Ya Fawaz ba irin wannan son ba, so nake maka na saurayi da budurwa irin so na mata da miji." zaro ido Fawaz yayi yace "Dank'ari!" matso sa tayi ta fashe masa da kuka gwanin tausayi tace "Ya Fawaz wallahi ina san ka... I've been carrying this burden for years without telling you please don't make me regret opening it to you... Wallahi Ya Fawaz ina san ka and I'm ready to give my all... Ya Fawaz please don't say no." ja da baya Fawaz yayi don ya lura saura k'iris ta shige jikin sa sannan yace "I'm sorry Zuhra.... You know I don't have it in me to cast anyone but right now I don't have a role for love to play kiyi hak'uri." fashe masa ta k'ara yi da kuka ta yaye hijab dake jikin ta da k'arfi surar ta ta bayyana cikin wata 'yar gown shara-shara kamar nightie tace

"Ya Fawaz me na rasa ne? Me na rasa na 'ya mace?" shi kam Fawaz kallon ta kawai yake saboda daidai da rana d'aya Zuhra bata tab'a burge sa ba, duk da cewa Afeefah suna wata haramtacciyar soyayya da Foxy amma duk da haka yafi jin soyayyar Afeefah a ransa fiye da Zuhra saboda Afeefah wani ne ya gurb'ata tunanin ta lokaci d'aya unlike Zuhra wacce a tantagaryar fitsararriya ta tashi, matsowa tayi kusa dashi har k'irjinta yana gogar nasa k'irjin kuma suna iya jiyo numfashin junan su tace "Ya Fawaz komai kake so zan maka..." bai san lokacin da ya kife ta da wani mahaukacin mari ba lokacin da tayi k'ok'arin had'a lips d'inta da nasa cikin b'acin rai yace

"I've never found you seductive Zuhra... Baki tab'a burge ni ba and next time kika yi gangancin had'a k'azamin jikin ki da nawa zaki gane kuren ki." dafe take da kuncin ta ba abunda take sai kuka cikin kakkausar murya yace "Now take your goddamn garbage life out of the here!" yayi daidai da shigowar Foxy, d'agowa tayi cikin kuka tace "Ya Fawaz..." "Get out!" ya fad'a cikin b'acin rai yana nuna mata hanyar fita "Ya Fawaz..." "Get the fuck out!" ya daka mata tsawa wacce har Foxy sai da yaji tsoro sannan yasa kai ya shige d'akin sa ya rufe ya barta nan. K'arasowa Foxy yayi ya shiga lallashin ta da bata baki, cikin rawar murya idanun ta sunyi jajir saboda kuka tace

"Fahad me na rasa? Meyasa Ya Fawaz yake wulak'anta ni?" "Ba abunda kika rasa Zuhra, the truth is that Fizzy is a sex less zombie tun tashin mu ba macen da yake kulawa har yanzu he is as dangerous as that." shiru suka yi tana jinjina maganganun Foxy sai lokacin ta samu sauk'i a zuciyar ta tunda ba ita kad'ai yake yiwa haka ba, cikin kwantar da murya Foxy yace "Kiyi hak'uri kije gida yanzu I'll try to talk to him." jinjina kai tayi tace "Ok." sai da ya raka ta har wurin motar ta yana cigaba da bata hak'uri har ta shiga motar ta ta tafi.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*15*

_2:00pm_ Leslie shine taken ta, tantitiriyar 'yar duniya ce wacce tayi k'aurin suna a garin Abuja. Sun had'u da Foxy a wani cocktail party da wani abokin sa ya gayyace shi a nan garin Abuja, tun lokacin da ta saita idanun ta akan Foxy kuma ta fahimci cewa shima d'an hannu ne irin su tasha alwashin sai ta d'and'ani zumar sa. Basu bar wurin ba sai da suka yi musayar number had'i da k'ulla soyayya ta kuma yi alk'awalin kawo masa ziyara. Sanye take da wani arnen ripped jean wanda kamar an saka razor an yayyaga shi na tommy hilfiger sai wata 'yar k'aramar riga wacce ta gagari rufe cibiyar ta da facing cap sai wani sun goggles da ya rufe fuskar ta da wasu kafiran hills. Tafiya take d'aya bayan d'aya tana juya butt d'inta tana tauna chewing gum k'aras-k'aras ta shigo parlor'n gidan ta tarar da Fawaz yana kallo, murmushi ta sakar masa suka gaisa ta tambaye sa Foxy yace mata yana d'akin sa, juyawa tayi ta nufi d'akin shi kuma Fawaz ya tashi ya nufi harabar gidan bisa wasu lounging chairs hannun sa rik'e da textbook ya zauna.

Gefen Foxy da Leslie kuma hot romance kawai ke gudana har sai da suka kai ga tub'e junan su tsirara daga nan kuma labari ya chanza. Sun shafe awa biyu suna abu d'aya at last dukansu bacci yayi awon gaba dasu. Sai wuraren k'arfe biyar suka farka Leslie tayi wanka ta fara shirin tafiya. Daga harabar gidan kuma motar Afeefah ce ta danno cikin gidan wanda yasa gaban Fawaz dake zaune a harabar gidan ya yanke ya fad'i, parking tayi a parking lot d'insu ta fito cikin d'inkin riga da skirt na atamfa da mayafi ta nufi wajen da Fawaz yake zaune. D'aya daga cikin lounging chairs d'in ta zauna tana murmushi suka gaisa suka d'an tab'a hira sannan tace

"Foxy fa?" gaban sa ya sake fad'uwa kamar shine mai aikata rashin gaskiyar amma a ransa cewa yake _It's time I had to help you Afeefah_ murmushin dole yayi mata yace "Yana ciki." "Right barin gansa." ta fad'a tana mik'ewa tsaye ta nufi cikin gidan, koda ta saka kanta parlor'n idanun ta suka hango mata wani mummunan bak'in ciki, Foxy da Leslie ne suke kissing juna hungrily kamar wasu mayu yayin da hannayen Foxy ke akan boobs d'inta, sai a lokacin ta k'arewa Leslie kallo ta gane tabbatattar 'yar duniya ce ga wani polished silver hair akanta da wasu zara-zaran nails fuskar nan an fimfa ta da heavy make-up. Daskarewa Afeefah tayi ta kasa wani k'wak'k'aran motsi jikin ta sai kyarma yake uwa wacce ke fama da zazzab'i yayin da idanun ta sai ambaliyar hawaye suke, sam basu san da shigowar Afeefah ba sunyi nisa cikin jin dad'in su, wani irin wahaltaccen kuka mai k'araji ta fashe dashi ta zame zuwa k'asa, kukan nata ne ya jawo hankalin su suka dakata had'i da juyowa idanun Foxy suka sauka kan Afeefah nan take yaji wani sudden fears suna rising daga zuciyar sa. Kallon Afeefah Leslie tayi a lalace then back to Foxy tana yatsina fuska tace

"Wannan fa?" da k'yar Foxy ya iya motsa bakin sa yace "She is my Bae." dariya Leslie tayi harda tafawa sannan tace "Wannan abar? Come on! Wannan bak'auyiyar? Haba! She is way out of your class mana." sannan ta nemi had'a bakin ta da nashi but this time bata ci nasara ba saboda ba abunda Foxy keyi sai kallon Afeefah yanda take wrestling da numfashin ta, juyowa tayi ta kalli Afeefah ta daka mata tsawa tace "Ke yarinya tashi ki tafi gidan ku!" sannan ta girgiza butt nata da gashin kanta tace "Because with this hair and this booty it's like walking around with black 2018 Avensis and I'll never get denied." sannan ta juyo kan Foxy tace "Baby me zaka yi da wannan mitsitsiyar? Me a cikin ta? It's like you invite a man to do a woman's job." ta nemi had'a bakin sa da nata for the second time murya k'asa-k'asa irin muryoyin hatsabiban karuwan nan tace

"Baby one more time please... Lemme suck this thick sexy lips." ta fad'a tana jan belt d'in wandon sa passionately, wani burning need nata ya sake tasowa Foxy yayi grabbing big ass d'inta da k'arfi ya manna ta a bango yana pulling gashin ta yana kissing d'inta hungrily tuni suka manta da Afeefah wacce sai kokawa take da numfashin ta dake neman tsayawa. Fawaz wanda yaji shiru-shiru Afeefah bata fito ba ya tabbata ba lafiya, ba da son ransa ya barta taga abunda Foxy da Leslie ke ciki ba sai don ita tasan abunda take ciki. Shigowa yayi ya ganta numfashin ta sai kai da komo yake a wahalce, rud'ewa yayi bai san abin zai yi tsanani haka ba ya d'auke ta cak ya nufi d'akin sa da ita suka bar Foxy da Leslie a wata duniyar. Kwantar da ita yayi kan gadon sa but damn it bai san wani emergency aid da ake bawa masu irin matsalar su ba. Ganin numfashin nata yana neman tsayawa ne yasa ya fige ta ya fito da ita a lokacin Foxy da Leslie sun dawo cikin hayyacin su, ko kallon su bai yi ba ya wuce da Afeefah a hannu breathlessly. Motar ta ya saka ta a baya ya rufe sannan ya shiga a 360 ya ja motar ya bar gidan zuwa asibiti. Koda ya isa aka shiga bata taimakon gaggawa don ceto ranta sai a lokacin hankalin Fawaz ya d'an kwanta ya fito yaje wurin motar ya d'auko wayar ta don ya sanar da halin da ake ciki a gidan su sai dai me zai sanar dasu? Dubara ce ta fad'o masa ya shiga contacts d'inta ya lalubo number da tayi saving da Umma ya danna kira, ringing d'aya a na biyu ta d'aga had'i da cewa

"Hello Afeefah." gyaran murya Fawaz yayi cikin ladabi yace "Umma ba Afeefah bace..." "Waye?" Umma ta fad'a cike da tsoro, cikin kwantar da murya Fawaz yace "Ni abokin ta ne a makaranta kuma yanzu haka bata da lafiya tana asibiti a kwance unconscious you need to be here." kuka Umma ta fashe dashi tana ta salati tace "A wacce asibitin?" gaya mata yayi sannan tace "Toh shikenan gani nan zuwa." tana gama fad'ar haka ta ajiye wayar. Fawaz jingina yayi da motar had'i da lumshe idanun sa with so many thoughts on his mind. Ba'a dad'e ba wata mota k'irar Benz 2017 bak'a wulik ta faso asibitin nan take kuma kira ya shigo a wayar Afeefah dake hannun Fawaz suka nemi sanin inda yake, fitowa yayi yayin da suma suka fito daga cikin motar Daddy, Umma da kuma Aunty Nana da ka gansu kaga wad'anda naira ta gama ratsawa. A rud'e Umma ta k'araso wurin da Fawaz ke tsaye ta shiga tambayar sa

"Ina Afeefah na? Me ya same ta?" Fawaz zai yi magana sai ga su Daddy sun k'araso cikin girmamawa Fawaz ya gaida shi yayin da sai wani kallo yake jifar Fawaz dashi yace "Me ya same ta ne?" "I don't really know, na same ta ne tana kuka and gasping heavily sai nayi deciding kawo ta asibiti kawai." cewar Fawaz, jinjina kai Daddy yayi yace "Then why don't you take her to school clinic sai ka kawo ta nan?" Daddy ya tambaya, tsoro Fawaz yaji 'cause ya lura Daddy ba tambaya yake ba kamar tuhumar sa yake, nan ma cikin kwantar da murya yace

"I suggest nan zata fi samun taimakon gaggawa akan school clinic." jinjina kai Daddy yayi alamar ya gamsu sannan yace "Ina motar ka ne? Naga kamar motar Afeefah a parking lot ko da ita kuka zo ne?" nan kam tsoro sosai ya kama Fawaz ya lura idanun Daddy are suspicious and prying on him and there is a slight doubt in his voice he did not sound like a man who is sold on what he's asking, jinjina kai Fawaz yayi yace "Yeah da motar ta muka zo." "Toh meyasa baka..." katse shi Umma tayi fuskar ta da damuwa tace "Haba Daddy'n Afeefah! Idan bamu godewa yaron nan akan taimakon da yai mana ba bai dace ka dinga jifar sa da tambayoyi irin haka ba." sannan ta juyo kan Fawaz tace "Yanzu ina Afeefah'n?"

"Tana a d'akin hutawa." cewar Fawaz "Muje." Fawaz ne a gaba yayin da Umma, Daddy da Aunty Nana ke baya har suka iso d'akin da Afeefah ke kwance tana bacci, da sauri Umma da Aunty Nana suka k'arasa sai duba ta suke yayin da Daddy yayi tsaye k'am sai nazarin ta yake, juyowa yayi ya kalli Fawaz fuskar sa d'auke da murmushi ya mik'a masa hannu yace "Mun gode sosai Allah Ya saka da alkhairi." murmushi Fawaz yayi cikin girmamawa ya karb'i hannun Daddy suka gaisa yace "Bakomai Daddy."

"Ya sunan ka ne?" "Fawaz." "Fawaz wa kenan?" "Fawaz Shattima." fad'ad'a murmushin sa Daddy yayi yace "Thanks Mr. Shattima." nan ma Umma itama ta masa godiya sosai sannan ya dank'a musu keys na motar Afeefah ya mata addu'ar samun lafiya sannan ya juya ya fita. Yana fitowa Foxy ya kira sa ya nemi sanin asibitin da ya kaita ya gaya masa cikin mintunan da ba zasu kasa sha biyar ba sai gashi ya iso yana fitowa daga mota ya kalli Fawaz yace "Ina Affee?" harara Fawaz ya dalla masa bai ce komai ba "Muje in ganta please" cewar Foxy, haushin sa Fawaz yaji ba kad'an ba yace "No need, her family is here." "I don't care muje please." harara Fawaz ya sake binsa dashi yace "Wai sai yanzu da idan ma kwanan ta sun k'are ta dad'e da mutuwa ka damu da ita?"

"Wallahi Fizzy ba haka bane I was carried away by Leslie..." tsuki Fawaz yaja ya karb'e keys d'in motar sa da Foxy yazo a ciki yace "I ain't going back there, her Dad is suspicious of me idan kai zaka je ne it's cool with me sai ka dawo." yana gama fad'ar haka ya nufi motar sa, biyo bayan sa Foxy yayi suka shiga motar suka bar wurin. Sai da suka hau titi sosai Foxy ya kalli Fawaz yaga ransa a b'ace cikin murya mai sanyi yace

"I'm sorry Fizzy... I know a lot of this is my fault but me ya kawo ta gidan lokacin? Ba fa ni na gayyace ta ba." wani haushin sa Fawaz yaji yace "Ain't you the one that taught her? Ba kaine ka koya mata zuwa wurin ka ba?" shiru Foxy yayi baya da bakin magana sai da aka d'auki seconds haka sannan yace

"Yanzu ya jikin ta? How's she feeling?" "She is still unconscious." Fawaz ya amsa masa a tak'aice, dunk'ule hannun sa d'aya yayi ya kaiwa d'ayan naushi had'i da cewa "Fuck it! Wallahi Leslie matsiyaciya ce!" ko uffan Fawaz bai ce masa ba don ya lura ma ya raina masa hankali sai da aka shafe mintoci sannan yace

"Kawai ka sani duk abunda ya sami Afeefah wallahi kaine sanadi, idan mutuwa Afeefah tayi kaine ka kashe ta." "Haba Fizzy! Ya kake fad'ar magana haka?" "Ya ba zan fad'a ba? Ko k'arya nayi? Idan baka san yarinyar nan da gaske just spell it out mana! Bai dace ache da k'ananan shekaru irin nata ta fara experiencing heartbreak ba. Please Foxy I beg you idan baka san Afeefah da gaske then let her live in peace." shiru yayi he feels guilty da maganganun Fawaz da haka har suka k'araso gida.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*16*

_8:00pm_ Afeefah bata farka ba sai wuraren k'arfe takwas da rabi na dare, koda ta bud'e ido ta sami Daddy, Umma da Aunty Nana zagaye da ita suna mata sannu. Kallon su take a hankali da mamaki don a halin da ake ciki ta manta komai da ya faru da ita. Lumshe ido tayi tana k'ok'arin refreshing da tunano me ya faru da ita, slide shows na hot romance na Foxy da Leslie ne ya fara dawo mata da lokacin da take gasping heavily da kuma sanda Fawaz ya kinkime ta, k'ara lumshe ido tayi hawaye suka zubo mata zuciyar ta sai bugawa take wane zata faso k'irjin ta she hate to recall that scene kuma sai replaying yake a cikin idanun ta zuciyar ta sai k'una take

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull