Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 8

Abokaina complete book 1 - Chapter 8

Abokaina complete book 1 Chapter 8: Abokaina complete book 1 Chapter 8. "Sannu Afeefah" Umma ta fad'a had'i da dafa goshin ta tace "Kukan ya isa haka…

4,378 words

"Sannu Afeefah" Umma ta fad'a had'i da dafa goshin ta tace "Kukan ya isa haka kinji?" ita dai kam jinsu kawai take but honestly bata ma san a wane yanayi take ciki ba. Daddy ne ya k'araso kusa da ita ya had'a hannun sa da nata yace

"It's alright Afeefah kar kiyi kuka please kinji?" jinjina masa kai kawai tayi hawaye na cigaba da bin kuncin ta amma ita kam tasan kuka yanzu ta fara, haka ma Aunty Nana tazo duk suka taru suna rarrashin ta akan kada tayi kuka considering yadda kukan yake cuta mata. Tashi tayi Aunty Nana ta taimake ta suka shiga toilet tayi brush suka fito Aunty Nana ta had'a mata tea ta bata, rik'e cup d'in tayi ta kasa sha sai sobbing take bitterly. Likita ne ya shigo bayan sun gaisa a nan ya fara nuna musu illar b'ata mata rai wanda har ka iya sanya ta kuka don kuwa da ache ba'a gaggauta kawo ta asibiti ba da akwai yiwuwar a rasa ta, saukar da numfashi Daddy yayi yace

"Doctor matsalar yadda kaga Afeefah haka muma muka ganta, bamu san me ya faru da ita ba, ta fita gida da zummar zata je makaranta sai kiran mu aka yi a waya akace mana tana asibiti." mamaki ya kama likitan yace

"Amma wannan saurayin da ya kawo ta ya tabbatar muna yayan ta ne." "Haka ya gaya muku?" jinjina kai likitan yayi yace "K'warai da gaske." kallon juna Daddy da Umma suka yi da sauri sannan likitan ya zarce da cewa "Ko ba yayan ta bane?" girgiza kai Daddy yayi yace

"Maganar gaskiya bamu san shi ba amma kuma shine ya kira mu da wayar Afeefah'n yake shaida mana shi d'in abokin ta ne yanzu haka bata da lafiya tana asibiti kuma ya nuna mana incident d'in a makaranta ya faru." duk maganar da suke akan kunnen Afeefah kanta sunkuye tana sauraron su ta fahimci Oldie ne ya kawo ta asibitin kenan, karkatowa Daddy yayi ya kalle ta yace "Afeefah" muryar ta raga-raga kamar zata yi kuka tace

"Na'am" "Look at me" cewar Daddy, d'ago kai tayi ta kalle sa idanun ta taf da hawaye, sai da ya fara goge mata hawayen sannan yace "A ina wannan abun ya faru and who caused it?" ajiyar zuciya tayi wasu hawayen suka sake zubo mata tace

"A makaranta" "Who's behind it?" shiru tayi sai kuma ta fashe da kuka recalling Foxy is the one behind it, chan ta tsinto muryar Daddy na cewa "Wannan saurayin ne da ya kawo ki asibiti?" duk da cewa kuka take amma bata san lokacin da ta d'ago kanta da sauri tace

"Wallahi Daddy ba shi bane he just helped me" "To waye?" kuka ta fashe dashi mai tsuma rai da ban tausayi wanda yasa likitan ya dakatar da Daddy daga tambayar ta suka shiga lallashin ta da kwantar mata da hankali, sai da likitan ya tabbatar tayi shiru sannan ya nemi ganin Daddy a office d'insa.

_Bayan kwana biyu_ Alhamdulillah she is regaining lafiyar ta da ta rasa and she is trying to get over everything about Foxy duk kuwa da cewa abun yana da matuk'ar wahala. Duk wani possibility na had'uwar su tana k'ok'arin guje masa, call d'insa ma haka take bouncing d'in shi a duk lokacin da ya shigo wayar ta, chats and any other means da zai iya samun damar yi mata magana duk tayi blocking ta d'aukar wa kanta alk'awalin ba zata k'ara kula sa ba ever again. In those days, Oldie ne nata. At least zai kira ta thrice in a day don yaji lafiyar ta kuma sai a lokacin ta gane abunda yake k'ok'arin fahimtar da ita game da Foxy gaskiya ne. Cikin kwana biyun 'yan gidan su ma sun yi mamakin ta kamar kada wannan accident d'in ya faru duk ta chanza kamar ba ita ba duk da cewa walwalar ta ta ragu amma dai she is trying. Haka zata baje litattafan ta idan ta dawo makaranta tayi ta lissafin nata haka ma tana fitowa parlor ayi hira da ita unlike other days kullum tana d'aki da waya manne da Foxy sai dai akai-akai suna samun ta tana kuka wanda basu san dalili ba kuma da sunce zasu matsa da tambayar ta to ta fara kukan ne ba ji ba gani wanda yake sa dole su k'yale ta.

*School* _2:00pm_ Parking tayi ta fito cikin shigar jallabiya bak'a fuskar ta ba kwalliya da ka ganta koda shine ganin ka na farko da ita zaka tabbatar akwai damuwa tattare da ita. Tafiya take kamar ko yaushe cikin natsuwa ta nufi department d'insu yayi daidai da kawowar motar Foxy wurin, hango ta yayi ta bada baya tana tafiya dubawar da zai yi gefen sa yaga motar ta a wurin. Bud'e motar sa yayi ya fito ya nufi motar ta ya gwada bud'e ta cikin sa'a yaji ta bata yi locking d'inta ba, bud'e k'ofar gaba yayi gefen wurin zaman driver kawai yayi zaman sa a ciki. Bata dad'e ba ta fito kasancewar motar tint ce yasa bata lura da zaman sa a cikin motar ba kuma kwata-kwata hankalin ta baya wurin, tafiya take har ta kawo wurin motar ta bud'e ta shigo ta zauna dubawar da zata yi gefen ta taga Foxy zaune cikin shigar k'ananan kaya kamar koda yaushe jikin sa sai k'amshi yake fitarwa, yunk'urin bud'e motar ta fita tayi ya chafko hannun ta ya rik'e gam yace

"At least kin wahal dani enough Afeefah." jikin ta ne ya shiga kyarma tsintsar masifa tace

"Ka sake ni! Whatever it is you are dreaming, idan ma mafarki kake, then wake the hell up! You have nothing else to defend! Ba abunda zaka sake gayamin in yarda." shiru yayi yana kallon ta yadda duk ta rame and she still have the guts da zata dinga barking haka "Ka fice min a mota Fahad! Don't think I'll be deceived or carried away by your lies again!" yadda take tsiwan kuma at the same time take so tayi kuka ya bashi tausayi shi kansa yasan Afeefah tana matuk'ar son sa, kwantar da murya yayi har yanzu yana rik'e da hannayen ta yace

"I'm sorry Afeefah... I know the things you brought out of me were wrong but I'm sorry kiyi hak'uri dan Allah and give me a listening ear... Nasan ba dole ne ki yarda da duk abunda zan gaya miki ba but please ki saurare ni." har yanzu jikin ta rawa yake tace "Ka sake ni Fahad!" "Promise idan na sake ki ba zaki fita motar nan ba?" jinjina masa kai tayi alamar eh not looking at him, murya gwanin tausayi kamar wani na kirki yace "Thank you Afeefah." bata ce masa komai ba har yanzu, cikin muryar rarrashi yace "Nasan na miki laifi Afeefah but nayi ne without my conscience... Kuma I'm not here to ask you back, I'm here to apologize for what I made you go through that day I'm sorry." d'ago kai tayi idanun ta sun fara ja jijiyoyin kanta sun fara fitowa cikin kakkausar murya tace

"Naji you are sorry zaka iya ficewa." "Afeefah I won't forgive myself if I let you go... Wallahi ina sanki Allah ne shaida ta." shiru tayi kanta a k'asa maganganun sa suna nema su fara tasiri a kanta abunda idan ya faru ba zata tab'a yafe ma kanta ba kenan "Afeefah" ya kira sunan ta cikin wata iriyar murya, nan ma banza tai masa kamar bata ji ba, langwab'e kai yayi kamar zai yi kuka yace "Afeefah you are killing me softly dan Allah ki d'ago kanki ki min magana koda zagi na zaki yi ki zagen I know I deserve it." d'ago kai tayi tana masa kallo wanda shima ya kasa fahimtar tsana ce kome tace

"I hate you Fahad! Bana sanka! Bana sanka! Believe me I don't! You manage to shake my life, nasan ba haka kaso ba, so kayi ace na bar duniya ga baki d'aya to ina da sauran kwana gaba saboda haka ka tashi ka fice min a mota bana san ganin ka!" murmushi yayi yace

"I can't go with 'ba kya sona', k'arya ne wallahi but I can go with 'you need time'... Afeefah you are that stubborn part of me that I tried to cut up but can't go away... Wallahi Afeefah ina sanki kuma bana so mu rabu but you are making us..."

"Ka tashi ka fitar min mota!" ta katse shi had'i da daka masa tsawa, shima cikin fushi ya rik'o kafad'un ta had'i da daka mata tsawa

"Afeefah!" tsoro taji yadda taga shima ya shak'a lokaci d'aya, cikin masifa yace "Don't get it twisted... If not 'cause of the feelings I have for you I won't apologize after all the shit you made me go through! Kinsan halin da kika jefa ni ne all this while? Why are you so selfish? Ko an gaya miki ke kad'ai kike son kanki ne? You are not the only victim Afeefah, you are not. Kin kasa fahimta ta... You are getting it all wrong, abunda kike tunani ba haka bane... You should at least hear me out." sai kuma suka yi shiru lokaci d'aya suna kallon k'wayar idanun juna, cikin tausasa murya yace "We break up to make up... I believe in the saying 'there is no true love without jealousy' and you also need to know 'there is no true love without fights'. Haba Afeefah! Mesa sai yanzu zaki chanza min as if there is some bhad girl inside you wacce ban tab'a sani ba? You are not the girl I used to know... Afeefah na da na sani will do everything to make her boo smile. Do you want us to keep going through this shit?" sannan ya kwantar da murya yace "Afeefah mesa kike sa ina miki tsawa? Bana so I don't like it please don't push me to the wall." kuka ta fashe dashi a sanyaye jin cewar Foxy har yanzu nata ne, d'ago kanta yayi a hankali yace "Affee" though sobbing take uncontrollably but duk da haka sai da tayi k'ok'arin cewa

"Na'am." kallon juna suke sannan ya mata murmushi yace

"I love this girl... Am I loosing her? Is she loosing me? What's really happening please?" hawaye masu zafi suka zubo mata a hankali ya shiga share mata sannan yace "Dan Allah ki bar kukan nan Afeefah... Ba kya sona I understand, kinsan kina da matsalar numfashi you don't want to go back into that intensive condition again. Ba kya sona I understand kuma zan fita in tafi as you demanded but I love you and I'm happy we are at the point you are exactly what I needed in a relationship Afeefah... Ina sanki Affee because you are a wife material kuma kinsan me?" shiru tayi masa ba abunda ke fita idanun ta sai hawaye yayi wani murmushi kad'an yace "I'm gonna tell my kids everything about you, I'm gonna tell them their mom was supposed to be Afeefah but she left me... I'm gonna tell them how much I love you but you left me and they will curse you so bad for letting me go." sannan ya sake ta ya bud'e motar zai fita, rik'o shi tayi gam tana kuka tana saukar da numfashi d'aya bayan d'aya chan k'asa-k'asa tace

"Don't please." jawo ta yayi kacokan ta dawo bisa jikin shi ya rungume ta gam-gam yace "I won't I'm here." sai kuma tausayin yarinyar ya kama shi, bai so ache tana masa irin wannan azababben son ba so yayi ache irin sa ce su more rayuwar su kawai a wuce wurin but Afeefah ba haka bane. He feel bad kuma ya k'uduri aniyar ba zai sake hurting nata ba duk kuwa da cewa ba sonta yake da gaske ba, baya ma lissafi da aure ma ballantana ya aure ta but zai cigaba da sweet talking d'inta har ranar da zata girma tayi wayon fahimtar sa saboda albarkacin son da take masa. Ajiyar zuciya ta shiga yi fuskar ta cikin k'irjin sa tace

"I'm sorry I just can't control it kuma laifi na ne da nazo gidan ranar uninvited..." d'ago kanta yayi da sauri yace "But Afeefah nothing happened! Ba abunda ya faru tsakani na da ita I swear, iyakar abunda idanun ki suka gani iyakar abunda ya faru kenan nothing more." kishin ta ne ya motsa ta fara sheshsheka tace

"Are you sure?" jinjina mata kai yayi yana murmushi sometimes wani silly childish na Afeefah na burge shi, shafa bayan ta ya shiga yi yana murmushi yace "Sure sweetheart nothing!" "Swear" nan ma murmushi yayi yace "Pinky swear." murmushi tayi jin yayi amfani da slang d'inta na pinky, d'ago kanta tayi tace "But I know girls like her... She is a bhad girl... I saw it through her fake lashes and her watermelon ass, are you so dumb to fall into that girl's trap?" ta k'are maganar kamar zata yi kuka, maida ta yayi cikin k'irjin sa ya cigaba da shafa ta yace

"I'm an idiot Afeefah sharrin shaid'an ne kawai but zuwan ki ai yayi amfani 'cause you prevent me from fucking that bitch." murmushi tayi ta k'ara kwantawa cikin k'irjin sa sannan yace "Baby shine kikai ta bouncing min calls ko? Kikai ta wahal da this poor innocent guy ko? Bakomai akwai Allah." murya k'asa-k'asa tace

"If I don't you won't know that I'm pissed." dariya yayi yace "I have so much to tell you Afeefah.. So many gist for you." d'ago kai tayi tana murmushi tace "Da gaske?" d'aga mata gira yayi yace "Yeah!" "You can start with that bitch." ta fad'a tana turo baki, dariya ta basa sosai he can't help sai da yayi dariyar sosai har sai da ya gaji sannan ya lakaci hancin ta yace

"Afeefah! Kishi!"

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*17*

Rungume suke da juna suna jin heartbeat na junan su. Gefen Afeefah life was becoming alive again kenan saboda tun ranar da abun ya faru bata sake tsintar kanta tana murmushi hakanan ba dalili ba, sakin ta yayi yana kallon ta yace

"Allah sarki my Affee, haka kika rame dama? I'm really sorry for everything." ya k'are maganar yana shafa gefen fuskar ta, murmushi tayi mai sanyi tace "Stop apologizing ba laifin ka bane Allah ya rigaya da ya hukunto da hakan so dole sai ya faru we can't avoid it." murmushi shima yayi yace "But idan wani abu ya k'ara samun ki ta dalili na believe me I won't forgive myself." shiru tayi tana murmushi kawai bata ce komai ba, rik'o hannun ta yayi yace "Yanzu gida zaki tafi ko?" jinjina masa kai tayi a sanyaye kawai "Yaushe zaki zo wuri na to?" nan take yanayin ta ya sauya jikin ta ya fara rawa tace

"Ba zan k'ara zuwa ba." murmushi yayi yace "Saboda kin daina sona ko?" girgiza kai tayi alamar a'a "To saboda me?" ya tambaye ta, cikin rawar murya tace "Everything about that place reminds me of that bitch..." matse hannun ta yayi yana murmushi yace "Nasani Afeefah.. Har yanzu kin kasa yarda dani kina tunanin idan kinzo zaki sake gani na da wata ko?" jinjina masa kai tayi alamar eh, murmushi ya k'ara yi yace "Trust me for the last time Afeefah... Delete me out of your life if such happens again, just give me the chance to proof this lie lie love of mine kinji?" jinjina masa kai tayi alamar to sannan ya gyara zama yace "Ni kin gane, it's not what you think. Ba abunda kike tunani bane Afeefah naga kin kasa yarda dani, I just wanna sit with you and talk senses into your skull da bana sanki I would've let go off you long ago but it's the love." murmushi tayi wata wutar son shi sai yanzu take k'ara ruruwa a zuciyar ta zata yi magana ya riga ta yace "Are you still my Affee?" nodding tayi alamar eh tana murmushi "Am I still your Foxy?" nodding ta sake yi sannan yace "Then come to my place let's talk things out wannan maganar motar it's not enough kinji?" sai lokacin ta motsa bakin ta tace

"Ok" "That's my boo... To yaushe zaki ko?" "Gobe" ta fad'a a sanyaye, dad'i yaji har cikin ransa yace "Thanks Afeefah.. Thanks for trusting me." shafa fuskar sa tayi tace

"I trust you baby, you know I always do." dad'i kashe sa, bata san sadda ya sake jawo ta ba yace "Ya Allah bless me with this girl that believes in me." "Ameen" ta fad'a tana murmushi sannan yace "Wallahi Afeefah I love you.. Duk ranar da kika barni ko? Hah!" sai kuma yayi shiru, d'ago kanta tayi tana murmushi tace "Me zaka yi?" "I'mma shoot you with pump action then shoot myself sai mu had'u a lahira just so nobody can have you." dariya ta fashe wata irin dariya wacce ta manta when last da ta yi irin wannan dariyar shima haka ya biye mata sukai ta dariyar. Sun sha hirar su mai dad'i sai da ya tabbatar ya wanke mata duk wani b'acin rai sannan suka rabu da cewa gobe zata kawo masa ziyara.

***

Shigowa parlor'n yayi yana karkad'a keys d'in motar sa yana whistling, Faruk wanda shi kad'ai ne zaune a parlor'n yana zuk'ar giyar sa yace "Shege wa ka cuta ne?" dariya Foxy yayi yana zama next to Faruk yace "Affee mana" zaro ido Fak yayi yace "Don't tell me ka sake brain washing yarinyar nan?" "Ahap! An gaya maka ni d'in na wasa ne? Ba zaka sha mamaki ba ma sai gobe idan ka ganta gidan nan" sannan ya tsiyaya giyar da Fak ke sha a cup ya fara tsotsa, cikin alhini Fak ke girgiza kai yace "Allah Ya shirye ka Ya kuma kare Afeefah daga sharrin ka d'an iska kawai!" dariya Foxy yayi yace

"Duk d'an iska yana bayan ka ai shege mashayi kawai!" "Thank goodness ban tab'a danne 'yar kowa ba." "Yo dama wacce banzar ce zata yarda ka danne ta shege mai bak'in jini uwa shed'an." dariya Fak yayi had'i da damk'o wuyan sa yace "Wallahi Foxy zanci buroban ka" "Ah kaga Fak dakata bani wasa da lafiya ta." sakin sa Fak yayi yace

"Shege kai" "Ina Fizzy ne?" Foxy ya tambaya "Yaje school" "Ok" Foxy ya amsa ya nufi d'akin sa ya rage kayan jikin sa ya fito suka cigaba da hira. Suna cikin hirar Fawaz ya shigo nan kuma hirar ta dawo farko ba su suka tashi ba sai da aka yi sallar la'asar. Bayan sun yi sallah sun dawo Foxy yake sanar da Fawaz ya samo kan Afeefah har sun shirya, gaban Fawaz ya bala'in fad'uwa amma dai ya kanne ya musu fatar alkhairi nan take ya tashi ya bar wurin.

_9:00pm_ Foxy ne shi kad'ai zaune bisa lounging chairs a harabar gidan rik'e da wayar sa, kiran Afeefah ne ya shigo wayar sa wanda ya saka shi murmushi had'i da yin sliding ya saka a kunne

"Baby" ta kira sa murya k'asa-k'asa kamar wacce ke jin bacci, murmushi yayi yace "Yes sweetheart ya kike?" "Fine.. Was just lonely I decided to call you up." murmushi yayi yace "Nima gani zaune waje a banza ina ta tunanin ki." murmushi tayi wanda har sai da ya jiyo sannan tace

"Me zaka yanka min gobe idan nazo?" "Rak'umi yayi?" ya fad'a teasingly, dariya tayi tace "Yayi" "Right, sai kinzo." sai ga Fawaz ya fito wajen ashe dama duk wayar da suke yi a kunnen sa he just can't believe Afeefah ta sake trusting wannan lil rat d'in, zuwa yayi next to Foxy ya zauna yayin da shi kuma Foxy ya cigaba da wayar sa yace

"I miss you so much baby." murmushi tayi tace "I miss you too sweetheart." "Sure? Wah did you miss about me?" "My whole baby." ta fad'a tana jin kunya, murmushi yayi mai kama da dariya yace

"Your baby misses you too and everything about you." sannan ya ja numfashi yace "I just wish kina kusa dani right now Afeefah so that na miki fad'a and tell you how much I hate it when we had issues... Kinsan yadda nike jin kaina yanzu kuwa? Just like a brand new engine.“ dariya tayi a sanyaye tace

"Baby ka iya fasan kai wallahi you know how to bribe my heart ehn." dariya shima yayi yace "Da bribe ne da kin dad'e da harbo jirgi na ai, the truth is your baby loves you sooooo much." sannan ya juyo ya kalli Fawaz yace "Sheikh Fizzy!" ko kallon sa bai yi ba kansa akan wayar sa yace "Sai yanzu ka ganni?" "Na hau jirgin soyayya ne yanzu ma ta window na ganka." "Bari har ka sauko." cewar Fawaz, dariya Foxy yayi da haka suka cigaba da nonsense yana magana da Fawaz at the same time yana waya da Afeefah, sun dad'e suna hira sannan suka yi sallama. Fawaz yaso yayi masa magana game da Afeefah sai dai kuma ya ja bakin sa yayi shiru bai ce komai ba da haka suka yi wa juna sai da safe suka rabu.

***

*Washegari* Yau ya kama Lahadi, tunda safe Afeefah ta tashi ta fara safa da marwa tsakanin d'akin ta, parlor da harabar gidan tana tunanin wacce k'arya zata shirga don ta samu ta fita. Shigowa parlor'n tayi jiki a sanyaye kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki ko kad'an bata so tayi failing Foxy a hankali ta taka ta haura upstairs ta nufi d'akin Umma. Shiga tayi tana bin bango kamar mara gaskiya ta samu Umma zaune da glasses a fuskar ta tana ta aiki akan system d'inta da gani dai business d'inta ne, ganin Afeefah ta shigo jiki ba k'wari yasa ta dakatar da abunda take ta d'ago tana kallon ta had'i da cire glasses tace

"Auta na lafiya kuwa? You seem somehow worried." k'arasowa tayi ta zauna bakin gadon cikin muryar ta mai sanyi tace "Umma saloon nike so inje." "To kuma don zaki je saloon zaki bi ki damu kanki?" murmushi tayi sannan tace "Daga nan kuma ina so naje gidan su Laila da akwai materials da nike so zan karb'o hannun ta." shiru tayi ita kam Umma a iyakar sanin ta da Afeefah yawo gidan k'awaye bai dame ta ba, jinjina kai tayi tace "Tam but ki hanzarta kinsan yau Daddy'n ku zai dawo ya gayamin k'arfe biyu na rana ma jirgin su zai sauka kinsan baya so ya dawo bai same ki ba." farin ciki ya bayyana a fuskar ta ta mik'e tsaye tace

"In shaa Allah Umma ba zan dad'e ba." murmushi kawai Umma ta bita dashi har ta fice d'akin sannan ta mayar da kanta akan system dake gaban ta. Tana shiga d'akin ta daka wani uban tsalle ta cire kayan ta ta fad'a bathroom. Wanka ta tsala ta fito ta zauna gaban madubi ta fara tsara kwalliya. Ta b'ata awa d'aya tana fimfa fuskar ta ita kanta sai da tsaya tana imagining wai itace kuwa sannan ta d'aure gashin ta in a ponytail style ta saki jelar a baya finally ta shirya cikin wata gown peachy color da complete outfit d'inta ta d'aure kanta da wani black veil leaving jelar gashin ta a baya ta d'auki handbag d'inta bak'a sannan ta shiga zuba turaruka. Kallon kanta tayi cikin madubi tayi murmushi ta fito ta samu Umma da Aunty Nana a parlor, dukansu sunyi mamakin ganin Afeefah da irin wannan kwalyar Afeefah wacce kullum ke fad'ar she is a proud member of 'I don't draw on my eyebrow club' yau itace da wannan heavy makeup d'in, Aunty Nana ta kasa hak'uri tace

"Afeefah wannan kwalya haka sai ina?" "Saloon zanje." ta fad'a tana d'an turo baki alamar bata son zancen "Saloon zaki je da wannan kwalya Afeefah? Anya kuwa?" cewar Aunty Nana, b'ata fuska tayi ta turo baki kamar anja catapult tace

"To Aunty Nana sai ki bini muje ki gani ai." murmushi Aunty Nana tayi tace "Allah Ya baki hak'uri." juyawa tayi ta kalli Umma tace "Umma na tafi." "Allah Ya kiyaye a dawo lafiya." cewar Umma, da "Ameen" ta amsa ta fice ta bar gidan.

Koda ta iso gidan tayi parking ta bud'e motar ta fito confidently ta nufi cikin gidan, Fawaz ne ta samu zaune a cikin parlor'n da headphones a kunnen sa ya k'ure volume yana jin music lokaci d'aya yana karatu dama al'adar sa ne sauraren beats while reading. Sau uku tana maimaita sallama amma sam bai ji ba a hankali ta tako tazo kusa dashi tana murmushi, shi kuwa jikin sa ne ya basa da wani tsaye a wurin da farko ya d'auka Fak ne ya shirya zai fita har yayi niyyar share sa sai kuma turaren da ya mamaye d'akin ya tabbatar masa ba Fak bane, d'ago kai yayi idanun sa suka masa revealing Afeefah cikin kwalyar da bai tab'a ganin ta a ciki ba. Headphones d'insa ya cire yana kallon ta cike da al'ajabi yayin da sai murmushi take ta zauna kusa dashi. Ko k'ala baice mata ba wanda yasa taji ba dad'i sai ma cigaba da karatun sa yayi, cikin kwantar da murya tace

"Oldie" "Brainy" shima ya kira ta sai kuma ta rasa me zata ce suka yi shiru. D'ago kai tayi ta k'ara kwantar da murya tace "Ba zaka min magana ba kenan?" kamar dama jiran ta yake yayi jifa da pen dake hannun sa ya fuskance ta sosai yace

"What the hell do you want me to say?" shiru tayi ta kawar da kanta daga kallon sa sannan ya zarce da cewa "Zaki iya gayamin me ya kawo ki gidan nan or you can tell me to mind my biz." sannan ya juya ya maida kansa akan karatun sa, cikin sanyin murya tace

"Foxy fa yana nan?" bai d'ago ya kalle ta ba haka kuma bai amsa mata tambayar ba sai ma jifar ta yayi da tasa tambayar yace

"Foxy? What happened to baby today? Ba baby kike kiran sa ba?" jikin ta ne yayi sanyi a hankali ya juyo ya fuskance ta yace "You know what I know for sure? Ki yarda ko kadda ki yarda matsalar ki ce Foxy baya sanki he's just toying with you." gaban ta ne ya yanke ya fad'i ras cikin rawar murya tace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull