Abokaina complete book 1 - Chapter 18
Abokaina complete book 1 Chapter 18: Abokaina complete book 1 Chapter 18. Sosai Daadan Fawaz ke kula da Afeefah ake kuma gyara ta safe, rana, da dare.…
3,114 words
Sosai Daadan Fawaz ke kula da Afeefah ake kuma gyara ta safe, rana, da dare. Kullum tana tsammanin Foxy zai kira ta amma shiru ba shi ba labarin shi itama bata neme shi ba. Sai da ta shafe sati uku a Kaduna Daadan Fawaz ba abunda take sai gyara ta, Alhamdulillah tayi kyau ta k'ara haske sosai har d'an jiki tayi kuma damuwar ta ta rage, daren da zasu tafi Abuja Abban Fawaz yasa aka kawo mata lefe akwatina set uku ba na rainawa. Washegari tunda safe suka shiga shirin tafiya kai amarya Abuja Afeefah sai kuka take a ganin ta duk abun nan da yake faruwa rashin adalci ne wa Fawaz kawai dududu kwanan sa uku da rasuwa har an ga wurin d'aurin aure? An kaita gidan su Foxy a inda akai mata nasiha sosai daga k'arshe Daadan Fawaz, Maryam da wasu daga cikin 'yan uwan Foxy suka raka ta zuwa Abujan. Tafiyar awa biyu da rabi suka yi suka isa Abujan a gidan su Afeefah, Umman ta kam ba abunda zata yi ma mahaifiyar Fawaz sai godiya yadda taga Afeefah ta chanza tayi kyau. Tunda aka fara maganar kaita gidan Foxy ta fara kuka kamar ranta zai fita a d'akin ta, Aunty Nana ta shigo d'akin ta same ta tayi ruf da ciki sai kukan take
"Affee tashi fa kiyi wanka ki chanza lokaci yana tafiya kar muyi dare." jin sheshshekar kukan ta yasa ta dakata "Affee meye kuma? Meye abun kuka yau kuma? I thought this is a great day for all of us." d'ago jajayen idanun ta tayi tana kallon Aunty Nana tace "Great day? There's nothing like great day in my life." sannan ta tashi zaune ta goge hawayen ta tace "Nasan kawai rayuwa ta zata k'are ne cikin bak'in ciki da k'unci I'll never get the things I longingly want duk abunda nike so ba shi nike samu ba sai akasin haka but that's my fate and I accepted it." a hankali ta mik'e ta shige bathroom ta bar Aunty Nana tsaye sororo a wurin. Bayan ta fito daga wankan ta shirya cikin wani d'ankaren lace mai tsada ba yadda Aunty Nana bata juya da ita ba kan ta bari a mata make-up tace bata so ba yadda suka iya haka suka barta sai powder da aka shafa mata kawai. Sai da aka fara kaita wurin Daddy ya mata fad'a da nasiha sosai Umma ma haka sannan suka tafi along the way ma sai da aka biya gidan Ammi mahaifiyar Zuhra itama ta mata nasiha sosai da fatar mata alhairi a gidan auren ta sannan aka nufi gidan amaryar. Koda suka isa ma baya gidan, straight cikin gidan suka nufa da ita gida sai masha Allahu ya had'u iyakar had'uwa, har cikin d'aki aka kai Afeefah aka k'ara mata nasiha da addu'o'i sannan suka zauna jiran dawowar Foxy kafin su kuma su tafi gida. Ba'a dad'e ba sai gashi ya dawo shi kad'ai ba rakiyar aboki ko d'aya sai feeling wani empty space na abokanin sa yake which they were supposed to be but they weren't ji yake like a lil color went out of his world, cikin shigar shadda Kaftan fari da hula yake shima dai yayi kyau ainun, nan aka had'a su aka sake musu fad'a cousins suka shiga tsokanar sa aka musu addu'o'i sannan suka ce zasu tafi, sai da ya raka su har suka shiga motocin su sannan ya dawo ciki.
Bayan ya dawo ya same ta zaune a inda ya barta, rasa abunda zai yi yayi yayi tsaye yana kallon ta finally ya k'araso ya zauna kusa da ita. D'aga mayafin ta yayi yanda yaga tayi kyau sai shek'i da walwali take a hankali ya saki murmushi, tun lokacin da Fawaz ya rasu bai tab'a jin koda alamar zai iya k'ara wani murmushin ba sai yanzu
"Kukan ya isa haka sai kace wacce za'a yanka." bata ce dashi komai ba a hankali aka fara mata rewinding ranar da ya fara keta mata mutunci nan take jikin ta ya fara rawa she hates to recall that scene, hannun ta ya rik'o a hankali don ganin k'unshin ta cikin zafin nama ta fisge hannun kamar wacce wuta ta tab'a ta mik'e tsaye jikin ta sai rawa yake, haushi yaji har cikin ransa ya mik'e tsaye yace "Drop the attitudes and hold your horses Afeefah! Meye haka ne? Ni fa mijin ki ne yanzu, do you know what it feels like to be shunned by your wife?"
"Bansani ba but I know what it feels like to be raped! Ka tashi ka fice min daga d'aki bana san ganin ka!" mik'ewa yayi a sanyaye ya fice daga d'akin kamar yadda tace. Har ya isa sashen sa zuciyar sa sai tafasa take his whole life ba macen da ya tab'a tunkara ta yarfa shi kamar Afeefah, wanka yayi ya fito yayi tsaye cikin d'akin ya rik'e k'ugu zuciyar sa sai zafi take masa. Ji yake kamar ya kira d'aya daga cikin side chicks nasa just to show that kid shi ba irin namijin da ake yarfawa bane ko kuma ya sha wine koda zai rage jin abunda yake ji duk kuma sai ya tuna alk'awalin da ya d'auka wa kansa tun lokacin mutuwar Fawaz that shan wani abu ko harkar mata duka ya daina, haka ya kwanta har bacci yayi awon dashi.
Washegari ba shi ya tashi ba sai k'arfe tara na safe bai dad'e da tashi ba yana zaune a cikin babban parlor'n gidan cikin shorts da singlet aka aiko driver daga gidan su Afeefah da breakfast, karb'a yayi da kansa ya masa godiya sannan ya jera su a dining saboda tun tashin sa bai saka ta a ido ba and he promised ba zai k'ara shiga sashen ta ba. Da yaga bata da niyyar fitowa yasa yayi breakfast d'insa ya sake wanka yayi ficewar sa, sai da ta tabbatar ya bar gidan sannan ta fito itama tayi breakfast ta tsunduma duniyar tunani. Haka yinin ranar ya k'are bata yarda suka ma had'u ba. Da dare bayan ya dawo gida Daddy'n Afeefah ya kira sa da kansa ya nemi ya turo masa account number sa, ba b'ata lokaci Foxy ya tura masa shi kuma ya shak'e masa shi dam da kud'i a cewar sa yanzu nauyi biyu ke a kansa kuma yasan dukansu karatu suke ba ta hanyar da kud'i ke shigo su haka washegari ya turo musu da motoci biyu Range Rover 2017 kala biyu fara da bak'a saboda zuwa makatanta, Foxy godiya ya masa sosai saboda baya da abunda zai iya biyan sa dashi. A cikin satin suka fara fita school dukansu kuma Alhamdulillah kowannen su yana k'ok'arin coping musamman Afeefah da wancan semester tayi losing wasu exams da bata rubuta ba sai dai kowa harkar gaban sa yake ba mai kula wani magana mai sai a wurin da ta zame musu dole suke yi.
*Shawty* 💕 [7/9, 8:50 PM] 0mmer Farouk: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*40*
A wani yammaci ya dawo gida yana k'ok'arin shigowa cikin parlor'n gidan yaji kamar Afeefah tayi bak'i ana ta surutu, abunda kunnuwan sa suka fara cin karo dashi shine
"Afeefah ke fa matar aure ce yanzu, ko kusa bai dace kina wannan maganganu ba ballantana ma wanda kike yi a kansa ya mutu." taka birki Foxy yayi don jin wane maganganu ne Afeefah ke fad'a, cikin kuka yaji tace "Wallahi ina san shi Laila, not a day goes by that I don't think about him or the memories we had together, I missed him so much Laila." sannan ta ja numfashi ta cigaba da cewa "Nayi kewar shi ba kad'an ba... That boyish smile.. The arrogance which sounded natural to him... That low pitch voice." wani irin kishi ne ya rufe Foxy parlor'n ma da yayi niyyar shiga fasawa yayi ya koma ya shiga motar sa ya bar gidan. Tun daga ranar abubuwa suka fara damun sa ya fara tunanin neman shiri da Afeefah saboda a lokacin yaci ache ta fara mantawa da mutuwar Fawaz but kullum zame mata sabuwa take kuma har ga Allah shi dai yana santa, zuciyar sa ce ta gaya masa idan har yana son ya dawo da soyayyar sa then dole ya fara mata abubuwa irin wanda Fawaz ke mata "A guy with so much kind in his heart." a cewar ta kenan don ya lura abunda ke damun ta game da Fawaz ya wuce so ko kuma shak'uwa it's obsession. Tun daga ranar ya saukar da girman kai ya fara kula ta. Idan suka tashi da safe idan yasan tana da lecture 8am shi zai tashi da wuri ya musu breakfast idan har lokacin bata tashi ba yaje da kansa ya tada ta ta shirya shima yaje ya shirya su yi breakfast tare sannan ya d'auke ta ya kaita school. Idan ka gansu zasu je school zaka iya rantsewa da Allah ba ma'aurata bane sai dai ko saurayi da budurwa haka saboda Foxy iyakar sa shekara ashirin da hud'u zuwa da biyar while Afeefah har yau bata yi clocking twenty ba duk wanda za'a ce ma duk wannan gayun na Foxy yayi aure in his early twenties zai yi wuya ya gasgata shiyasa duk wanda yasan su ma'aurata ne abun dole ya burge sa. Wurin da ya k'ara kama ta shine wurin lissafin nata, idan dare yayi dukansu zasu fito babban parlor'n suyi karatu, dama chan Foxy he's very good in Math kawai lokacin shashanci ne ya masa yawa baya tsayawa ya maida hankali yayi. Wani lokacin idan Math d'in ya hanging nata shi take zuwa ya warware mata ya mata breaking nashi yadda zata gane while shi kuma yana nasa karatun da haka sai su raba dare suna karatu wani lokacin ma a nan bacci ke awon gaba da ita sai shi zai d'auke ta da litattafan ta ya kaita d'akin ta.
Sometimes idan zai yi kallon ball zai bar mata parlor'n ya koma parlor'n dake sashen sa yayi kallon, ita kuma da ta fara karatun zata ji ba dad'i ita kad'ai everything seems to be boring da kanta take d'ibar litattafan ta ta same shi a sashen nasa yana kallon ball while ita kuma tana karatun ta idan wani abu ya d'aure mata ta kai masa ya warware mata. Duk wannan banzan sa kayan da yake ya daina su wannan ripped jeans d'in da yake kamar ansa razor an yayyaga duk ya daina iyakacin sa yasa three quarters, gentility da maturity irin na Fawaz duk yayi wearing ma kansa. Itama idan shine da lecture 8am zata tashi ta masa breakfast kafin ya tafi. Zan iya cewa Alhamdulillah yanzu zaman su yayi kyau har ta fara mantawa da Fawaz, idan har zai tafi school ya kai 4pm bai dawo ba ai kuwa ya fara shan kira kenan ta rasa sanin dalilin da yasa ta chanza sai take ga yana koma mata kamar Fawaz. Haka when they're less busy zasu fito su yi ta sports a cikin gidan saboda Foxy ma'abuci son sports ne ba wanda bai saka ba a cikin gidan, wani lokaci idan ya fara beating nata sai tayi kuka wata rana kuma ya barta tayi beating nasa just to let her feel like a king. Duk wani partying, barbecue, picnicking da duk wani al'amarin shashancin sa ya watsar idan baya school to yana gida tare da Affee sai dai har lokacin ba wani abu na aure da ya tab'a shiga tsakanin su it's not that baya so no Afeefah yake ji saboda gani yake har yanzu she's not completely healed daga abubuwan da suka faru and he don't want to add more salt to the wounds shiyasa yake share ta.
Wani dare ya kasa hak'uri deliberately yayi kwanciyar sa a sashen sa yak'i fita karatun kamar yadda suka saba, ita kuma jin shiru-shiru yasa ta d'ibi litattafan ta ta nufi sashen nasa. Koda ta shiga parlor'n ta ga tv kashe baya nan bata kawo komai a ranta ba ta nufi bedroom, kwance ta same shi kan gado yayi ruf da ciki, ita duk d'auka take ma baya lafiya 'cause it's something odd ya zauna a d'aki bai fito sun yi karatu ba. Koda ta juyo dashi taga duk yanayin sa ya sauya sai ya fara koma mata wannan tsohon Foxy, kuka ta dinga yi ta k'wace kanta ta tafiyar ta ta barshi tun daga ranar kuma ta shiga fushi dashi. Haka suka kasance duk ranar da zai nemi hak'k'in sa to tabbas sai an mata rewinding ranar da ya fara keta ta haka zata yi ta kuka tana yarfa masa maganganu daga k'arshe ta gudu ta tafiyar ta shi kuma ba zai iya forcing nata ba da safe haka zai sauke girman kai ya bata hak'uri shikenan kuma sai su dawo daidai. A kwana a tashi sai da suka shafe five months a haka ranar kawai dubara ta fad'o masa ya samu wata colleague nasa a school ya bata address na gidan sa yace taje ta samu Afeefah tace shi tazo nema, ba yadda bata yi ya gaya mata me yake nufi da hakan ba yace mata ta taimake sa taje kawai, ai kuwa ranar Afeefah bata da lectures tana kwance tana kallo a parlor taji an danna door bell, zuwa tayi taga wata budurwa a tsaye ganin Afeefah yasa ta saki murmushi tace "Sannu ko?" murmushin itama Afeefah ta mayar mata tace
"Yauwa sannu." "Foxy fa yana nan?" budurwar ta tambaya, ita kam Afeefah ko a cikin dangin Foxy bata san da wannan ba, nan take wani kishi taji ya tokare mata k'irji a haka dai ta danne tace "Baya nan wace ke?" shiru budurwar tayi don basu yi wannan maganar da Foxy ba ta rasa me zata ce mata, ba abunda yazo ma Afeefah sai ranar da taje gidan su Fawaz ta sami Foxy da Leslie sai kissing juna suke, wani irin kishi ya tarnake zuciyar ta bata san lokacin da tace "Of all the single guys on the street? You just want to be a married man's hoe?" sai kuma taji tana so tayi kuka she can't hold it nan take tayi shutting k'ofar ta dawo ta fashe da kuka. Kuka ta yini tana yi kuma Foxy bai dawo ba sai da marece ya same ta kwance a parlor'n tana ta kuka, da har zai wuce sai kuma ya dakata yace
"Affee menene?" "Really? Tambaya ta ma kake menene? Su karuwan naka ba zasu tsaya a wajen ba har sai sun biyo ka gida?" yi yayi uwa da duniya bai san me yake faruwa ba
"Me kike nufi? Wace kuma tazo?" "Bansani ba!" fiddo wayar sa yayi ya d'an yi danne-danne sannan yace "Oh! Nabeela ce." ya fad'a disdainfully had'i da mik'ewa tsaye yana danna wayar sa, rigima ta shiga yi masa ba ji ba gani tana kuka "Affee cewa fa kika yi baki sona ba haka kike so ba? Kiga na koma cikin halakar da na fito? Wannan rigimar banza kike saboda ke kika causing komai so beat it please." yana kaiwa nan ya wuce sashen sa, binsa tayi tana ta kuka tana mita sai da ta wahala kusan sati biyu suna abu d'aya da wa'azi da komai da kokawa ya samu yaci wo kanta.
*Bayan shekara daya* A lokacin Foxy yayi graduating har ya fara aiki a company'n mahaifin Fawaz ita kuma Afeefah tana a 300level, lafiya lau suke zaune ba wata hayaniya sai dai har lokacin Afeefah bata samu ciki ba. Sun sha yawo a asibitoci sai dai za'a tabbatar musu k'alau suke sai lokacin da ta shiga 400level Allah ya kawo, abun ka da yara ba wanda ya fahimta daga cikin su saboda wannan laulayin cikin duk ba ta yi k'alau take abun ta, har sai da cikin yayi 1 month ranar daga school ta wuce gida a nan Umma ta fahimta ta shiga tambayar ta abubuwan da take ji last last tace mata su je asibiti, da ta koma gida ta gaya masa cewa yayi Umma teasing nasu kawai take but he promised zasu je asibitin kamar yadda tace. Sun je an tabbatar masu da cikin zo kaga murna gun Foxy haka ma families nasu. Haka suka cigaba da renon cikin ga karatu tana final year ga project sa'ar ta ma bata cika fitinannen laulayin nan ba haka kullum Foxy ya shiga addu'ar Allah Yasa Affee ta haifa musu namiji. Allah Ya karb'i addu'ar su bayan wahala da gumurzun da ta sha Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi d'a namijin, tun lokacin da aka gaya ma Foxy ji yayi uwa yayi tsuntsuwa ya shiga d'akin.
A zaune kan gado ya same ta tana danna waya da sassarfa ya isa wurin ta had'i da hugging nata very tightly yace "Weldone sweetheart I'm damn proud of you." murmushi itama tayi tace "Alhamdulillah I can't ask for a better partner than you, you went above and beyond." sannan ta dakata tana murmushi tana kallon gefe tace "You're an amazing father to him." juyawa yayi don ganin me take kallo ashe nurse ce ta shigo d'auke da baby'n da sauri ya karb'e shi yaro fari kyakkyawa mai kama sak da uwar sa, hugging nasa yayi gam a k'irjin sa hawaye suka ciko masa ido ya kalli Afeefah wacce itama hawayen ne ke neman zubo mata yace "Give him a name." sai da ta share hawayen ta had'i da yin murmushi tace
"Fawaz." shima murmushin yayi ya kira yaron da Fawaz sannan ya masa addu'o'i ya rik'o tiny fingers nasa yace
"So wassap buddy?"
*Alhamdulillah!*
*This is a good true life story and it's highly and solemnly dedicated to every love that was built on friendship and to every heartache that one ever experienced on so-called friendship. I just wish we, friends, could learn how to love ourselves not hurt ourselves.*😭
*Irony how the person you say you can take a bullet for end of being the one behind gun! Ya Allah! What a cruelty! What a cruel betrayal! To me that is the most detestable wickedness, the most horrid of cruelties and the greatest of miseries. This isn't just a story but a good lesson.*
*Wallahi I can't conclude this story without thanking UMMEE GARKUWA and SADNAF💅; thank you for the supportive role you are playing if only most writers could learn from you we'd be able to leave a great footprints in the sand of history. Thank you zillions sweethearts.* ❤
*To other peeps and groups,* *I'm wild in love with your condolences, mournful comments, and deep prayers to Fawaz and I wish this short write up of mine should be used as a learning tool among the youths and in every aspect of friendship. Thank you so much.*
*Shawty*💕