Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 17

Abokaina complete book 1 - Chapter 17

Abokaina complete book 1 Chapter 17: Abokaina complete book 1 Chapter 17. "Abba I can't ba zan iya ba!" "You have to.. Ko ba zaka sallaci jana'iz nasa ba?"…

4,388 words

"Abba I can't ba zan iya ba!" "You have to.. Ko ba zaka sallaci jana'iz nasa ba?" kuka ya fashe dashi a karo na biyu kuka mai tab'a zuciya da alhini da k'yar Abban sa ya fito dashi daga mota suka shiga makeken harabar gidan su Fawaz wanda ya cika mak'il da mutane ana jira a gama masa wanka azo a sallaci jana'izar sa, inna lillahi wa innaa ilaihi raji'un!

Abokanin su suka had'u suna ta bashi baki had'i da tausar sa har Allah Yasa suka samo kansa ya daina kukan ya koma gefe guda ya had'a kai da bango yana kukan zuci. Fitowa da gawar a cikin makara don yi masa sallah ne ya jawo hankalin Foxy ya k'ura wa gawar ido har zuwa lokacin da aka ajiye ta don yi mata sallah. Haka dai aka sallaci jana'izar Fawaz aka d'auke sa da mota zuwa makwancin sa. Akan idon Foxy aka binne shi sai dai ba abunda ya iya tab'ukawa yana ji yana gani aka rufe Fawaz babban abokin sa a cikin k'asa wanda tun suna k'anana basu rabuwa komai nasu iri d'aya ne yau gashi sun yi rabuwa ta har abada sai darussalam a lokacin ya tabbatar d'an adam ba komai bane a wurin Allah. Durk'ushewa yayi bisa kabarin Fawaz yana kuka kamar ransa zai fita kuka mai tsuma rai da ban tausayi koda mutum bai yi kukan mutuwar ba to yadda Foxy ke kukan zai iya sa mutum fashewa da kuka tun daga lokacin yasan ya fara kewar Fawaz kenan har k'arshen rayuwar sa, da k'yar mutane suka d'ago sa daga kan kabarin a zaton su kukan mutuwar abokin sa ne kawai yake wanda kuwa ba haka bane harda kuka da nadamar kisan abokin su da suka yi.

*Shawty*💕 [7/9, 8:50 PM] 0mmer Farouk: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *July, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*37*

*Washegari* _11:00am_ Tsaye take cikin bathroom tana kallon kanta a cikin mirror'n bathroom d'in hawaye sai gangaro mata suke wannan bayan wannan. Tsakanin jiya da yau kawai ta rame kamar ba ita ba, turo k'ofar aka yi wanda yasa tayi hanzarin share hawayen had'i da juyawa don ganin ko waye, Aunty Nana ce tsaye a bakin k'ofar bathroom d'in tana kallon ta sannan ta tako ta shigo ta rik'o hannun ta suka fito tare. A bakin gado suka zauna ba abunda take sai sheshsheka gami da ajiyar zuciya "Afeefah so kike ki kashe kanki? I know what it feels like to loss a loved one amma ya zaki yi? Hak'uri ake yi Afeefah, this world is never perfect for anyone, kowane bawa ana jarabtar sa ta b'angare daban daban haka kowa yake hak'uri ba abunda ya kamace ki a yanzu sai addu'a. Ki ta yi wa Fawaz addu'a itace kawai soyayyar ki da yake da buk'ata a yanzu kinji?" jinjina kai tayi alamar to sannan Aunty Nana ta had'a mata tea sakamakon tun jiya bata k'ara kai komai a bakin ta ba "Ungo ki sha don't starve yourself."

"Na k'oshi." "Me kika ci da zaki ce kin k'oshi? Afeefah kowa ana masa mutuwa fa! Haka kowa yake hak'uri ya cigaba cigaba da rayuwa. Tun jiya ake fama dake kici abinci kin k'i to mutuwar kema kike so kiyi ne?" to her very surprise sai gashi Afeefah ta d'aga mata kai alamar eh tana kuka tana sheshsheka

"I don't think of a better hour to die than now, Aunty nikam wannan wacce irin rayuwa ce wad'annan jarabawoyin wad'anne iri ne? Shikenan haka zan k'are rayuwa ta cikin k'unci? I'm not meant for happiness? Daga wannan sai wannan? Kullum niche kuka da zubda hawaye? Ba ranar da zanyi dariya kenan? My whole life is a mess? Haba Aunty Nana har don banci abinci ba za'a ga laifi na?" murmushi Aunty Nana tayi tace "I know you've gone through a lot amma ba shi zai sa ki yanke k'auna daga farin ciki ba, ni baki ganni ba? Shekara ta nawa a gida ba aure? If I'm not mistaken na baki shekaru d'aya d'aya har goma Afeefah, abun bak'in ciki ne da k'unci amma kin tab'a gani na ina zubda hawaye? Not for once, saboda nasan haka Allah Ya tsara min rayuwa ta dole kuma hakan zata tafi."

"Have you ever experienced a heart break?" Afeefah ta katse ta "An tab'a raping naki? An tab'a sace ki mutum hud'u suka afka miki? Aka nemi a tarwatsa rayuwar ki da k'wayoyi? Ranar da kika gano masoyin ki na gaskiya ranar Allah ya karb'i abun sa? Aunty Nana yau za'a iya zuwa a nemi auren ki kamar kowace budurwa ni kuma fa? Duk sai an zayyano duk wad'annan abubuwan da suka faru, my reputation has been damaged! I'm rotten through and through!" a hankali ta fashe da kuka mai tab'a zuciya. Aunty Nana ta tausaya mata ba kad'an ba, tana da gaskiya wad'annan abubuwan sun yi yawa a k'aramar k'wak'walwa irin ta Afeefah mai k'ananan shekaru "It doesn't matter Afeefah, what matters now is you are moving on. Ki tattara wad'annan tunanin ki saka su a bayan ki and focus on the future, all those annoying thoughts su fita daga jikin ki please they were your past and you don't live there anymore so wassap? Just chin up ok?" murmushi tayi na k'arfin hali tace

"Okay." "Good.. Ki sha tea'n please sai ki shirya kinsan k'arfe biyu Daddy yace zamu d'au hanya." cewar Aunty Nana lokaci d'aya tana mik'ewa tsaye, jinjina kai Afeefah tayi tace "Okay." fitar Aunty Nana ke da wuya hawayen da take ta Allah-Allah kada su zubo suka zubo, wayar ta ta jawo ta fara viewing hotunan Fawaz wanda sun fi hamsin a wayar ta sai kuka da dariya take lokaci d'aya, wani hoton sa ne taci karo dashi wanda bai tab'a sanin ta d'auke shi ba yana dariya da Foxy har hak'oran sa suka fito cas, bata san ya aka yi ba sai ji itama tayi dariya ta subuce mata duk da cewa ga hawaye nan shab'e-shab'e a fuskar ta amma sai kallon hoton take tana dariya, shafa hoton tayi kamar mai rad'a tace

"You'll never be forgotten Oldie, your memories will live on in shaa Allah." ko ta kan tea'n da Aunty Nana ta ajiye mata bata bi sai kwanciyar ta da tayi a nan take bacci yayi awon gaba da ita. A cikin baccin tayi mafarkin ga ta zaune ita da Fawaz sai hira suke yana mata surutu but unlike other times yau sai gaya mata yake yadda yake son ta and how he suffered about it, cike da tausayi ya kalle ta yace

_"Afeefah you are the only girl who's ever affected me like this. You know what beats me?" girgiza kai tayi a sanyaye alamar a'a "Gani gaki but I won't be able to have you that shit hurts so much Afeefah." sannan ya mik'e tsaye tall a gaban ta ya shoving hannayen sa biyu in his pockets ya flashing mata his coolest smile yace "You will be missed every now and then Brainy._

Daidai nan ta neme sa ta rasa a wurin daidai nan kuma ta farka, da ta fahimci mafarki ne take abun ya bala'in tab'a ta cike da tausayin Fawaz ta fashe da kuka ta janyo wayar ta ta fara aikin kallon hotunan sa tana zubar da hawaye "Allah sarki Oldie! I'm so stupid! I cost you your life on one questionable creature! Allah Ya jik'an ka Fawaz." a hankali ta kife wayar ta cigaba da kuka. Aunty Nana ta turo k'ofar ta shigo ta ganta kwance a inda ta barta ga kuma tea'n da ta ajiye mata ko kallon sa bata yi ba "Afeefah wai miye haka ne fisabilillah? Tunda ba kya jin lallashi to ki tashi ki shirya ke kad'ai muke jira." tashi zaune tayi idanun ta sunyi luhu-luhu saboda kuka tace "Aunty can you believe I just saw him?" "Waye kika gani?" "Fawaz mana kuma ya gayamin yana sona and that I'll be missed but..." sai ta kasa cigaba hawaye suka cika mata ido "What sweetheart?" cike da rawar murya jikin ta ko ina yana b'ari tace "Why don't he said this to me when he was alive? Meyasa sai yanzu yake gayamin lokacin da ba abunda zan iya yi? Meyasa zaya min haka?" sai ta dakata ta share hawayen ta tace "But he'll be better off without me ba dani ya dace ba, Fawaz isn't like every other guy, he's good, kind and decent he doesn't deserve to be with a slut."

"Oh my God Afeefah! This is your fate! Wannan k'adarar ki ce you have to accept it, ke baki san k'adara bane? Imanin mutum fa baya cika sai da yarda da ita, I hope Fawaz is in peace and I pray you find yours as well na kuma had'a ki da Allah ki daina kukan nan seeing your tears makes me start crying too." share hawayen ta tayi had'i da mik'ewa tsaye tace "Shikenan ya wuce." sannan ta nufi bathroom. Sai da Aunty Nana ta tabbatar ta fara wankan ta hanyar jin k'aran ruwa sannan ta mik'e ta fice daga d'akin don tasan zata iya shiga bathroom d'in tayi ta kuka abun ta. Wanka tayi had'i da d'auro alwala tazo ta gabatar da sallar azahar, ta dad'e zaune a wurin tana kuka tana rok'ar wa Fawaz rahama sannan ta shafa ta mik'e ta shirya cikin doguwar riga ta saka hijab a sama ta d'auki 'yan kayan da ba zasu fi set biyu ba ta zuba a wata k'aramar traveling bag ta fito zuwa downstairs. Ba yadda Umma da Daddy basu juya da ita ba kan taci abinci kafin su hau hanya tace ba zata ci ba daga k'arshe ma taso tayi kuka don dole suka k'yale ta suka fito farfajiyar gidan a inda driver ke jiran su. Daddy ne ya shiga gaba gefen driver yayin da Aunty Nana, Umma da Afeefah ke baya cikin wata arniyar Jeep bak'a driver ya ja suka bar garin Abuja zuwa Kaduna don zuwa ta'aziyyar Fawaz. Ear piece d'auke da karatun Al-Qur'ani ta manna a kunnuwan ta lokaci zuwa lokaci hawaye sai zubo mata suke. Sun isa garin Abuja lafiya k'alau da marece basu zame ko ina ba sai gidan mutuwar, an karb'e su da hannu bibbiyu cikin girmamawa da mutuntawa, tun lokacin da suka shigo Foxy ya gansu kuma yaso ya je ya musu sannu da zuwa amma saboda bai san abunda ka iya faruwa ba yasa bai je ba. Da dare bayan sallar Ishaa mahaifiyar Foxy ta rok'i alfarmar a bata Afeefah su je gidan ta ta kwana, ba tare da gardama ba Umma ta amince ita kam Afeefah ko kad'an bata ji dad'i ba kawai ba yadda zata yi ne saboda ta tsani koda hanyar da Foxy yabi ache ita zata bi yayin da Daddy, Abban Fawaz da kuma Abban Foxy suka shiga closed door meeting.

Koda suka isa gidan wuraren k'arfe tara na dare, a parlor suka yada zango a inda Hajiya wato mahaifiyar Foxy ta tirsasa ta dole taci abinci. Taci ba da yawa ba ba laifi sannan suka fara jefa hira lokaci zuwa lokaci, suna cikin hirar ne Foxy ya shigo dum gaban Afeefah ya fad'i ta tsaya cik tana kallon sa sanye yake cikin Kaftan sai dai ba hula a kansa ya rame sosai yayi duhu duk da cewa bai cika hasken fata kamar Fawaz ba, shima sai da gaban sa ya fad'i da ganin ta a gidan su sannan ya basar ya kalli Hajiya yace "Ina wuni Mama?" "Lafiya k'alau sai yanzu?" "Eh wallahi." ya fad'a yana juyawa zai bar parlor'n "Abincin ka fa?" tsayawa yayi ya juyo yace "Anya abincin nan kuwa?" sannan yayi shiru ya k'ara da cewa "Kai sai dai gobe kawai."

"Anya kuwa Fahad wannan rashin cin abincin zai haifa maka d'a mai ido? Haka d'azu da rana ma kace ba zaka ci ba sai anjima." gujewa k'orafin Hajiya yayi ya dawo ya zauna yace "Ina abincin?" k'walawa mai aiki kira Hajiya tayi nan take sai gata ta garzayo tace ta d'aukowa Fahad warmers dake kan dining nan take ta shiga jido masa tana direwa a gaban sa, kad'an ya d'iba ya fara ci sai dai ko kad'an baya jin d'and'anon abincin kawai yana tura sa ne don dole yayin da kowane motsi na Afeefah yana kula dashi. Ko rabin wanda ya d'iba a plate bai ci ba ya mik'e yayi wa Hajiya sai da safe ya fice parlor'n da sauri. Afeefah da Hajiya sun dad'e suna hira sannan Hajiya ta raka ta d'akin ta suka yi sai da safe. Da safe ma koda ta tashi komai an had'a mata a cikin k'ank'anin lokaci ta fahimci Hajiya mace ce mai kirki sai tarairaya ta take, tambayar ta Hajiya tayi ko zata je gidan mutuwar tace a'a bata so tana zuwa hankalin ta yana d'aguwa saboda ba wanda zai zo ta'aziyyar Fawaz ba tare da yayi kuka ba, Hajiya bata takura mata ba ta shirya ita kam tace zata tafi, fatar Allah ya kiyaye Afeefah tayi mata sannan ta cigaba da kwanciyar ta cikin parlor'n gidan akan sofa.

Sai wuraren k'arfe goma Foxy ya tashi daga baccin safe, sai da yayi wanka ya shirya tsaf sannan ya nufi cikin gidan. Kwance ya ganta kan sofa tana ta zubar da hawaye, sanyi jikin sa yayi ba kad'an ba ya cigaba da k'arasowa cikin parlor'n sai dai tayi nisa bata ma san mutum ya shigo ba. Ganin haka yasa Fahad ya wuce ta ya nufi d'akin Hajiya bai same ta ba wanda ya tabbatar masa ta tafi gidan mutuwar, fitowa yayi ya samu Afeefah kamar yadda ya ganta, gyaran murya yayi wanda yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta wula lokaci d'aya ta mik'e zata bar parlor'n yayi nasarar chafko hannun ta, gaban ta ya yanke ya fad'i lokacin da jikin su ya had'u a hankali rik'on da ya mata ya fara rewinding mata wasu memories, kici-kicin kufcewa tayi amma inaa bata da wannan k'arfin sai fashe masa da kuka tayi tana cewa

"Ka dubi girman Allah ka sake ni!" "At least ki tsaya in miki gaisuwa mana." ya fad'a yana kallon ta daidai lokacin kuma kira ya shigo wayar sa, koda ya duba yaga Abban sa ne hannun sa d'aya rik'e da Afeefah d'ayan kuma ya d'aga wayar dashi, amsawa yake da to har kusan sau uku sannan ya tsinke kiran ya kalli Afeefah yace "Abba yace in d'auke ki mu tafi they want to see us."

*Shawty*💕 [7/9, 8:50 PM] 0mmer Farouk: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*38*

Da kamar zata ce ba zata bi shi ba sai kuma ta tuna kiran daga Abba ne yace, juyawa tayi ta koma ciki ta d'auko hijab d'inta ta saka ta fito suka tafi. Tafiya kawai suke ba mai ce da wani uffan a daidai lokacin kira ya shigo wayar Afeefah, dubawa tayi taga wata k'awar ta ce ta school cike da sanyin jiki ta d'aga kiran, jaje da ta'aziyyar Fawaz k'awar tai mata da haka suka ajiye wayar Afeefah sai fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma rai. An gaya mata ana sabo da rashi amma ita kam ta kasa sabawa da mutuwar Fawaz duk lokacin da za'a ambace shi sai ta zubar da hawaye. Ji tayi ya saki titi yayi parking akan hanya da sauri ta d'ago kanta sai dai bata kalle shi ba, cikin sanyin murya ya kalle ta yace "Kiyi hak'uri Allah Ya jik'an Fawaz." cikin sheshshekar kuka tace "Ameen." ta shiga goge hawayen ta lokaci guda kuma ta sake breaking da wani sabon kukan "I couldn't... I couldn't tell him... I couldn't love him... I killed my best friend." Foxy ma hawayen suka tsiyayo masa cikin murya gwanin tausayi yace

"Ba ke kad'ai ba Afeefah, we all killed Fawaz." d'ago da jajayen idanun ta tayi ta kalle sa tace "How am I supposed to live with that?" shima Foxy'n hawaye masu zafi suka ciko masa ido yace

"We all stabbed him, dukanmu da kalar raunin da muka ma Fawaz but when Faruk stabbed him, he died." d'ago da rinannun idanun ta tayi tana kallon sa yayin da shi kuma yayi k'ok'arin mayar da hawayen da ke shirin zubo masa yace "Ni dake muka saka masa hawan jini da ciwon zuciya wanda ya zama sanadi amma wallahi Faruk ne ya kashe sa shine ya jawo bugawar zuciyar sa." kuka Afeefah ta fashe dashi mutuwar ta dawo mata sabuwa fil kamar yanzu abun ya faru "Tun daga lokacin da kike fad'ar abubuwan da Faruk ya miki tun daga lokacin Fawaz bai k'ara magana ba kuma daidai lokacin ne ya fara aman jini har lokacin da Allah Yayi ikon Sa." yanzu kam dukansu kuka suke musamman Afeefah wacce kamar ranta zai fita "I'm afraid the guilt of what we did to him will eat us alive. I feared kar alhakin Fawaz ya fara hunting namu daga yanzu Afeefah. We did him a lot of damages, we caused him a lot of pains kina ga Allah zai barmu a haka after all this cruelty?" sannan ya furzar da wani numfashi yace "Wallahi right now tsoro nike ji Afeefah kada mutuwar Fawaz ta zamo farkon namu tashin hankalin, the beginning of our grief Afeefah." kuka mai tsanani Afeefah ta fashe dashi itama sai yanzu ta fara tunanin anya kuwa Allah zai barsu a haka ba tare da ya hukunta su ba? "Nayi kukan rashin Fawaz Afeefah, I cried a river of tears, I cried until I feared I would lose my sight. Ban tab'a sanin haka d'acin mutuwa yake ba, ban tab'a tunanin haka wad'ansu suke ji ba idan suka rasa wani d'an uwa it's the worst pain I ever felt. That night broke me Afeefah, it feels like I'm choking, it feels like I'm drowning naji kamar nima zan mutu and for that I regret everything I've done Allah Ya sani nayi nadamar rayuwa ta baki d'aya." sannan yayi kicking motar ya juyo ya kalle ta ya k'ara da cewa "Ke kanki we've caused you a lot please ki yafe min." yadda ya fad'i maganar a sanyaye koda mutum bai san menene ya aikata ba to tabbas sai ya yarda da nadamar sa saboda gata nan kana gani a cikin idon sa daga nan ya ja motar ya hau titi. Tafiya suke Afeefah sai kuka take yayin da Foxy kam hawaye ne ke ta streaming a fuskar sa da haka har suka isa gidan mutuwar. Parlor'n bak'i wanda yake kyautata zaton a chan ne iyayen nasu ke jiran su ya nufa da Afeefah. Daddy'n Afeefah, Abban Fawaz da mahaifin Foxy ne suka samu a cikin parlor'n a zazzaune, k'arasawa suka yi suka gaida su cike da girmama sannan suma suka nemi wuri suka zauna. Mahaifin Fawaz ne yayi gyaran murya yace

"To Alhamdulillah! Bayan faruwar wad'annan al'amura marasa dad'i mun zauna mun ga ba abunda ya dace illa mu had'a ku ku biyun nan aure." gaban Afeefah ya bala'in fad'uwa ta d'ago idanuwan ta da sauri tana kallon mahaifin Fawaz tace "Abba aure kuma?" "K'warai da gaske aure Afeefah! Kuma ba don kowa muka yi haka ba sai don ke." kuka ta fashe dashi marar sauti yayin da Abban Fawaz ya cigaba da cewa "Na tabbatar abubuwan da suka faru sun isa su zame muku wa'azi da kuma darasi." sannan ya karkato kan Fawaz yana kallon sa yace "Starting from you Fahad, kaga halin rayuwa ko? Yau da ache zaka fita wani wuri neman aure da gudu za'a baka ba wanda zai nemi sanin yarinya nawa ka b'ata, yarinya nawa kayi ma fyad'e as long as kai musulmi ne to ina baka tabbacin ba abunda zai hana a baka aure har cewa za'a yi watak'ila sanadin auren Allah Ya shirya ka ka daina halin ka amma ita fa Afeefah? Gudun ta za'a yi saboda me? Saboda ita mace ce abun yafi illa ga 'ya'ya mata saboda haka ko kana so ko baka so sai ka aure ta." shiru Foxy yayi ya saukar da kansa k'asa yayin da Abban Fawaz ya juyo kan Afeefah ya cigaba da cewa "Ke kuma kiyi hak'uri ki rungumi kadara idan kuma da akwai wanda kike so to ki kawo shi amma ina so ki sani duk wanda zaki aura, duk zuri'ar da kika shiga duk yadda suke k'aunar ki to wallahi wata rana sai an goran ta miki rashin kawo budurcin ki gidan mijin ki ba ma ke ba har 'ya'yan da zaki haifa amma idan kika auri Fahad fa? Kinga kamar dara taci gida kenan saboda Fahad d'an mu ne mu muka haife sa idan har ana maganar abun kunya to a gindin mu yake duk wanda zai tsangwame ki to ki gaya masa abun kunya yana nan tattare a gindin sa kinji ko?" jinjina kai tayi tana share hawaye kawai "Kiyi hak'uri nasan a yanzu ba lallai ne ki fahimce mu ba amma wannan aure rufin asiri ne a garemu baki d'aya." sannan yayi ajiyar zuciya yace "Yau za'a gama zaman makoki in shaa Allah mutane ba zasu watse ba zasu shaida d'aurin auren ku ni zan biya sadakin kuma zan baku d'aya daga cikin gidaje na dake Abuja ku zauna a ciki har ku gama karatun ku, kai kuma Fahad idan ka kammala karatun ka zaka karb'i ragamar babban company na." sai a lokacin Foxy ya d'ago kai cikin sanyin murya yace

"Mun gode sosai Abba Allah Ya saka da alhairi." "Zuwa nan da sati biyu idan al'amarin mutuwar nan ya lafa sai ayi duk shagalin bikin da za'a yi." cewar Abban Fawaz "Ai Shattima ba wani biki da za'a yi da an d'aura auren ya d'auki matar sa ya wuce shikenan." fad'ar mahaifin Foxy kenan, murmushi Abban Fawaz yayi yace "Hakan ma yayi Allah ya muku albarka." Foxy ne ya samu damar cewa "Ameen." duk da cewa shima dai gashi nan ne kamar hoto kamar ba shi ba ji yake he's like an empty tin that is worthless he's neither happy nor sad game da auren ita kam Afeefah sai kuka kawai. Mik'ewa yayi ya taimaka mata ta tashi suka nufi hanyar ficewa daga parlor'n. Maryam ya kira a waya ya dank'a mata Afeefah don ya tabbatar idan ya barta ita d'aya to ba zata iya kai kanta cikin gidan ba. Suna shiga cikin gidan ya fiddo waya ya kira Hajiyar sa yace ta fito ta bayan gidan ta same shi zasu yi magana ta amsa masa gata nan zuwa.

"Mama fisabilillah meyasa su Abba zasu min haka? A barni inji da mutuwar nan mana amma sai a wani tashi a kawon wani aure a gaba na haba dan Allah! Ita kanta Afeefah she's been through a lot a barta ta huta mana." bud'e baki Mama tayi cike da mamaki tace "Eh lallai Fahad ka cika tabbataccen yaro, ka b'ata musu yarinya kuma yanzu ka nuna ba zaka aure ta ba? Ita bata yi protesting an had'a ta aure da irin ka ba sai kai?" "Ni bani nace miki ba zan aure ta ba amma ayi tunani mai kyau mana, a duba al'amarin nan kwana uku da mutuwa sai wani maganar d'aurin aure? Haba sam wannan abun bai yi ba wallahi!" "To k'wararre kai da kasan daidai me ya hana lokacin da suka gaya maka baka gaya musu abun bai yi ba sai ni? Ko ni na shirya d'aurin auren ne? Kai da kana tunani mai kyau zaka aikata abunda ka aikata ne? To dan Allah idan aka d'aura auren ka warware ko kuma a ranar ka sake ta sai mu tabbatar abun ya k'ona maka rai shashasha kawai!" sai da ta tabbatar hararar da take binsa dashi ta nutsar dashi ya shiga hankalin sa sannan ta buga tsuki ta koma cikin gidan. Gefen Afeefah koda suka shiga cikin gidan kuka ta shiga rusawa har numfashin ta ya nemi ya tsaya, sai da aka taru a kanta ana lallashi sannan aka samu tayi shiru har bacci yayi awon gaba da ita.

Kamar yadda aka tsara haka ta kasance bayan sallar azahar aka yi ma Fawaz addu'o'i aka kuma d'aura aure tsakanin Fahad Tambari da Afeefah Jalal akan sadaki dubu hamsin. Kwance yake a cikin apartment na marigayi Fawaz dashi da abokanin su na liberty International Schools tun ranar da aka yi rasuwar a nan suke amsa gaisuwar ta'aziyyar su ba abunda ke fita idanun sa sai hawaye. D'aya daga cikin abokanin su mai suna MK ne ya shigo yana murnar ya samu wuri ya zauna had'i da cewa "Foxy ango!" d'ago da kansa yayi ya kalli MK yace "Har an d'aura ne?"

"Har mun d'aure ka wallahi." cewar MK, Muhammad ne dake latsa wayar sa ya d'ago kai ya kalli MK yace "Maza irin planned marriage d'innan fa yayi if you get to know each other, kawai mutumi na ka basar and chill." Foxy dai jin su kawai yake bai san ya aka yi ba sai ji yayi hawaye sun zubo masa ba abunda ya tuna sai wata rana da suke planning yadda auren su zai kasance a inda suka tsara rana d'aya za'a d'aura auren, irin shagalin da za'a sha da nonsense da za'a buga tare da friends wurin d'aurin auren sai gashi yau ba Fawaz ya rasu Faruk kuma yana gidan yari sai shi kad'ai aka d'aura ma auren da mutane k'alilan ba halartar ko d'aya daga cikin abokanin su, da ache lokacin da suke tsara yadda auren su zai kasance wani zai ce haka zata faru da sun k'arya ta ko wane ne da haka bai san lokacin da ya sake fashewa da wani kukan ba.

Da dare aka tara su aka sake musu fad'a da wa'azi a nan gogan yace shi dai gobe zai koma Abuja saboda makaranta nan take Abban sa yace ya jira ya wuce da matar sa Mama tayi insisting yayi tafiyar sa a bar Afeefah har su gama shirin su na mata sai a bishi da ita da haka aka rabu. Tun da sassafe wuraren takwas da rabi mutumin ya d'au hanyar Abuja don shi a ganin sa bai san abunda zai yi a Kaduna ba yayin da 'yan gidan su Afeefah kuma sai wuraren 11am suka kama hanya aka bar Afeefah a gidan su Fawaz.

*Shawty*💕 [7/9, 8:50 PM] 0mmer Farouk: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*39*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull