Abokaina complete book 1 - Chapter 16
Abokaina complete book 1 Chapter 16: Abokaina complete book 1 Chapter 16. *By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
4,469 words
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*34*
*Wannan labari ya faru da gaske wanda kuma kashi casa'in a cikin d'ari gaskiya ne. Ina so duk wanda yake karanta wannan labari to ya k'addara a ransaa yana karanta zahirin gaskiya ne.*
Dukansu sun matuk'ar tausaya ma Afeefah daga nan likitan yace zasu mata allurai wanda suke fatar zasu sa alluran su yi regaining hankalin nata. Ta b'angaren Faruk da mutanen sa da aka chafko had'i da su Cheetah da Zuhra duk sun karb'a laifukan su da ake tuhumar su dasu kuma ana shirin maka su kotu ne don zartar masu da hukunci haka 'yan sandan suka kira mahaifin Afeefah, mahaifin Fawaz da kuma mahaifin Ra'es aka yi setting Fawaz free daga abubuwan da ake zargin sa dashi aka kuma bawa mahaifan sa hak'uri sosai sakamakon har lokacin Fawaz yana asibiti ciwon nasa kullum sai dad'a tsananta yake.
A kwana a tashi sai da Afeefah ta shafe kwana biyar a asibitin amma zance bata a cikin hankalin ta, ga ta dai kamar zata yi magana amma hoto ce kawai komai bata iya fad'a sai bin mutane take da ido sai dai Alhamdulillah ta fara yadda da mutane at least kuma kamar tana fahimtar abunda ake fad'a maganar dai ce ba zata iya ba. Likitan ya basu shawarar komawa gida saboda she's physically fit ba wani abun da yake damunta a jikin ta sai dai wannan rashin maganar kawai ne yayi recommending idan har aka cigaba da jan ta a jiki to wataran zata dawo daidai in shaa Allah. A wani dare Allah cikin ikon Sa ya mayar mata da tunanin ta, ihu mai razanarwa ta fasa a cikin daren wanda yayi sanadiyyar farkawar Aunty Nana wacce take kwana da ita ta tashi a firgice "Afeefah!" Aunty Nana ta kira ta cikin muryar bacci sannan ta mik'e tsaye ta kunna hasken d'akin ta ganta zaune kan gadon sai wara ido take tana waige-waige cikin mummunar firgita
"Aunty Nana." itama ta kirawo sunan ta kamar bata yarda Aunty Nanan bace "Yes it's me." cewar Aunty Nana gami da saukar da ajiyar zuciya sannan ta sakar mata murmushi, k'ara kallon d'akin Afeefah tayi sannan ta kalli Aunty Nana a firgice tace "Aunty Nana.. Those punks down stairs don't like me.. Kashe ni zasu yi!" "No body is here Afeefah.. Kin dawo gida baki lura nan d'akin ki bane?" cewar Aunty Nana had'i da bata damar k'ara kallon d'akin sosai "You're at home and nobody is going to bother you again kinji?" had'i da jawo ta cikin jikin ta. Lamo Afeefah tayi abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata, ta share a k'alla minti sha biyar cikin jikin Aunty Nana sannan ta d'ago kai
"Aunty Nana ina Fawaz?" ta jefa mata tambayar kamar daga sama, shiru Aunty Nana tayi sannan tace "Bayi da lafiya Affee.." "What? Me yake damun sa?" ta fad'a tana wara ido cike da tsoro "Karki damu kanki kinji? Everything is going to be alright." "Aunty take me to him please." ta fad'a gami da fashewa da kuka "Ina so in gansa please Aunty Nana ki taimake ni." "Afeefah dare ne fa yanzu kalli agogo kiga." kallon agogon bangon d'akin Afeefah tayi then back to Aunty Nana tace "The night is still young Aunty zamu iya zuwa yanzun please."
"Umma ba zata so haka ba Affee, ki bari gobe tunda safe zan kaiki kinji?" ba yadda ta iya haka ta hak'ura har zuwa da safen. Mik'ewa Aunty Nana tayi ta fice daga d'akin taje ta tado Daddy da Umma ta gaya masu halin da ake ciki, nan take Daddy ya d'aga waya ya kira likitan ta bayan sun gaisa yace "Doctor alhamdulillah an samu tayi magana sai dai she's insisting on seeing Fawaz ala dole sai an kaita ta ganshi." "Yaushe ta fara maganar?" likitan ya tambaya "Yanzun nan 'yar uwar ta tazo tana shaida mana." "Ka gane ranka ya dad'e." cewar likitan "It's better to let her do what she wants. Zata iya yiwuwa ganin wannan yaron ya k'ara dawo mata da wasu abubuwan while hana ta kuma ka iya janyo wata matsalar."
"To shikenan Doctor." "Yauwa idan Allah Ya kaimu goben sai akaita ta ganshi d'in kamar yadda ta buk'ata." "To shikenan Doctor in shaa Allah haka za'a yi mun gode sosai." "To madallah sai da safe." cewar Doctor'n da kuma haka suka ajiye wayar. Zayyanawa Umma da Aunty Nana komai yayi yace in shaa Allah gobe za'a kaita taga Fawaz d'in daga nan kuma suka d'unguma suka nufi d'akin ta. Zaune take ta cusa kanta cikin k'afafun ta tayi zurfi cikin tunani, jin an tab'a k'ofar ne yasa ta d'ago kai tana kallon su, zuwa Umma tayi ta hugging nata very tightly tana shafa kanta tana hawaye yayin da Daddy ke tsaye akan su "Afeefah you have nothing to worry about now." cewar Daddy "And I promise I'll see nobody get near you again okay?" shiru tayi sannan ta jinjina kai a sanyaye tace "Okay" "Karki damu gobe zaki je kiga Fawaz in shaa Allah." nan ma jinjina kai tayi kurum sun dad'e a haka sannan Daddy yace kowa yaje ya kwanta.
*Washegari* _9:00am_ Yau ta kama Juma'a, tunda safe Foxy ya shirya zuwa asibiti don suna kyautata zaton yau za'a sallami Fawaz daga asitin saboda a kwana biyun da suka gabata jikin nasa da sauk'i. Tuk'i yake ya d'an kunna kid'a a motar zai iya cewa tun lokacin da abubuwa suka birkice bai sake samun damar jin music ba; life is becoming alive kenan sai dai koda ya shigo asibitin yayi parking ya nufi d'akin Fawaz ya tarar da sab'anin abunda yake tunani. Umman Fawaz ne zaune akan gadon yayin da Fawaz yayi matashin kai da cinyoyin ta ba abunda ke fita idon ta sai hawaye yayin da Maryam ke tsaye ta makure jikin window sai goge hawaye take, lokaci d'aya jikin Foxy yayi sanyi zuciyar sa ta karaya ya tsaya daga bakin k'ofa yana kallon su, goge hawaye mahaifiyar Fawaz tayi sannan ta kalli Foxy tace
"K'araso mana Fahad." da k'yar Foxy ya ja paralyzed foot nasa ya k'arisa wurin gadon yana kallon Fawaz dake kwance idanun sa a rufe "Daada" Foxy ya kira sunan ta da alama k'arin bayani yake nema saboda jiya goshin Maghreb lafiya k'alau suka yi hira da Fawaz ana ta raha da nishad'i har likitan ya tabbatar idan har jikin nasa ya d'ore a hakan to yau za'a iya sallamar su su koma gida, sai da ta goge hawayen da suka zubo mata tukuna sannan tace
"Jikin Fawaz ya tsananta bayan tafiyar ka jiya sai gaya mana yake zaya mutu." sai kuma ta fashe da kuka, haka Foxy ya tsinci kansa cikin wani yanayi mara misaltuwa duniya yake lahira yake oho "Daada a kira Doctor mana za'a zauna dashi haka ne?" cewar Foxy very calmly "Ya hana a kira Doctor'n wai ba sai an kira shi ba." "Yo Daada sai abunda yake so za'a masa?" cewar Foxy sannan ya karkata zuwa ga Maryam wacce sai kuka take a jikin window "Sis jeki ki kira Doc please." bud'e ido Fawaz yayi da k'yar ya kalli Maryam "I told you, didn't I? Kadda ki kuskura ki kira sa." bud'e baki da hanci Foxy yayi yana kallon Fawaz wanda ya mayar da idanun sa ya lumshe "Mi yake damun ka ne Fizzy? Haka za'a zauna da kai da ciwo a jikin ka?" sannan ya ja tsuki ya kalli Maryam "Jeki ki kira sa ni nace." nan ma da k'yar Fawaz ya bud'i idon sa sai dai yanzu Foxy yake kallo yana nishi d'aya bayan d'aya yace
"Ba amfanin kiran sa Foxy... I feel it in my bones today... Mutuwa zanyi." "Kaji fa irin maganganun da yake ta fad'a kenan tun jiya." cewar Daada, wani irin bugawa zuciyar Foxy tayi da k'arfin gaske sakamakon jin maganganun Fawaz yayi k'arfin hali dai ya kalli Fawaz yana hararar sa yace "Ya kake magana haka? This is your mother." ya nuna Daada "And here is your lil sis." ya nuna Maryam "Ya zaka dinga sanyaya masu jiki da wannan maganganun haka? Zafin ciwo ba fa shine mutuwa ba zaka ji sauk'i in shaa Allah." nan kam shiru yayi ya lumshe idon sa bai sake cewa uffan ba yayin da Daada ta fara k'ok'arin mayar da kansa akan pillow ta tashi daga wurin tunda ga abokin sa yazo "Daada ina zaki je? Please karki tafi ki jira har in tafi first." mutuwa jikin Daada yayi ta fashe da kuka haka Maryam, jawo kujera Foxy yayi ya ajiye daga gefe guda sannan ya rik'o Daada ya zaunar da ita kan kujerar shi kuma ya koma wurin gadon da Fawaz yake kwance yana kallon sa yace "Na had'a ka da Allah ka daina wannan maganar haba! Wannan Daada kake tayarwa da hankali." murmushi Fawaz yayi a forced smile haka sannan yace "Right.. Na daina." "Haba! Ko kai fa!" cewar Foxy sannan ya samu wuri gefen Fawaz ya zauna "So ya jikin?"
"Alhamdulillah it's getting sicker bit by bit." sannan ya d'an rintse ido had'i da cije leb'e da alama shi kad'ai yasan abunda yake ji "But I suppose it's a test for me or it's the end of me."
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un! For heaven's sake Fizzy! Ya kake magana haka ne? Don't think about that now, you are young and you have lots of things to look forward to dan girman Allah ka daina maganar mutuwar nan." "Calm down na daina." haka yake magana d'aya bayan d'aya yana nishi mai wuya had'i da saukar da numfashi. Ganin yayi shiru yasa Foxy shima yayi shiru na mintuna sannan ya juyo ya kalle sa yace
"Yanzu kafi so ka zauna a haka kadda a kira Doctor?" "Ina Afeefah?" ya tambaye sa don kawar da wancan maganar "An discharging nata daga asibiti ta koma gida." "Tana iya magana yanzu?" girgiza kai Foxy yayi had'i da cewa "Bansani ba nima ina samun labarin ta ne daga gun wata k'awar ta." k'ok'arin tashi zaune Fawaz ya gwada sai dai me? Wata wahalalliyar k'ara ya saki ya rik'e hannun Foxy gam a hankali sai ga hawaye suna bin kuncin sa, tausayin abokin sa ya kama Foxy shima bai ankara ba sai ji yayi hawaye sun cika masa ido "Stay strong okay?" jinjina masa kai kawai Fawaz yayi hawaye na cigaba da fita daga rufaffun idanun sa "Barin gyara maka pillow'n sai ka tashi zaune ko?" "Ok" ya amsa masa sannan Foxy ya d'auko d'aya pillow yasa masa a baya ya tayar dashi zaune daidai lokacin Afeefah da yayar ta Aunty Nana suka shigo d'akin. Kallon kallo ya shiga gudana tsakanin matasan uku a inda Afeefah ke kallon Fawaz cike da tausayi da alhini ya rame ya fara fita kamannin sa a yayin da Fawaz da Foxy suma irin wannan kallon suke mata.
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *July, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*35*
Bayan sun gaisa da Daada Afeefah ta k'araso wurin gadon ba abunda take sai kallon Fawaz ta rasa kalma d'aya da zata fad'i sai fashewa tayi da kuka, kallon Foxy Fawaz yayi yana nishi very heavily yace
"Foxy you know I love her right?" a diririce Foxy da Afeefah suka d'ago kai lokaci d'aya suna kallon Fawaz wanda sai kai da kawo numfashin sa keyi "Wallahi Fahad ina son Afeefah long before you knew her and I have being carrying this burden for years now." "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" Foxy ya fad'a a fili ya juyar da kansa gefe d'aya "Shine sanadin samuwar hawan jini na da ciwon zuciya and Faruk knows everything about it and he's ready to offer every help possible sai dai ni na hana ya gaya maka.." hawaye suka ciko idon Foxy har suka fara d'iga a k'asa yana kallon Fawaz jikin sa da muryar sa na rawa yace "Foxy why?" "Tell me how could I live with the burden that I snatched a girl from my best friend?" cewar Fawaz, kuka sosai Afeefah ta fashe dashi tana sheshsheka Foxy kam sai hawaye ke zarya a kumatun sa, kallon sa Fawaz yayi yace "You never know how your relationship with her is tearing me up.. Wallahi nayi iyakar k'ok'ari na Foxy, I tried my best to push away those disturbing feelings but they won't go away." sai gashi shima yana hawayen, sulalewa Afeefah tayi ta zauna kan gadon saboda k'afafun ta sun kasa supporting nata "Afeefah I love you." d'ago kai tayi hawaye sun mamaye mata fuska ta girgiza kai cikin wata irin murya tace
"Baka sona Oldie." "Believe me I do." "Kana sona? And you let me fall for this monster?" ta k'are maganar tana nuna Foxy sannan ta girgiza kai cikin d'acin rai tace "Kana gani na ina cutuwa but you can't fight my way out of it? Kana sona kenan?" ta sake girgiza kai tace "Baka sona Oldie." "I can't fight my best friend Afeefah and even monsters deserves a second chance ki basa dama I'm sure this isn't the guy you used to know... Ba Foxy bane wannan Fahad ne." ya k'are maganar yana mata murmushi, kuka ta cigaba da yi ba ji ba gani "Kiyi hak'uri Afeefah but you deserve someone better." "I don't want anyone better I want you." bayan kuka da sheshshekar Afeefah ba abunda kake ji a d'akin yayin da Fawaz ya lumshe ido yana dafe da zuciyar sa dake barazanar faso k'irjin sa ta fito suna cikin haka suka ji an tab'a k'ofar d'akin a hankali aka turo sai ga Faruk ya bayyana, razana Afeefah tayi ta haye kan gadon ta k'ank'ame Fawaz jikin ta na kyarma ta tura kanta cikin k'irjin sa saboda fuskar Faruk da ta mutanen sa da irin muguntar da suka mata suna daga cikin abubuwan da ba zasu tab'a gushewa a rayuwar ta ba, fuskar Faruk koda yaushe ta rufe idanun ta itace take hunting nata yayin da ganin sa ya zama nightmare a wurin ta. D'aure yake da sark'a hannu da k'afa jikin sa daga shi sai singlet sai dogon wando da 'yan sanda biyu a tare dashi fuskar sa duk an raunata ta idan baka san shi ba sosai ba zaka iya shaida sa ba
"Afeefah listen to me." cewar Fawaz "D'ago kanki ki kallen." a hankali ta d'ago kanta ta kalle shi sai dai shi ba ita yake kallo ba Faruk yake kallo kawai sannan ya mayar da kansa ga Foxy wanda yake zaune kamar gunki tun zuwan Afeefah bai k'ara cewa uffan ba at last ya maida kallon sa ga Afeefah yace "Can you find it in your heart to forgive Fahad?" tsalle tayi ta dira daga kan gadon ta nuna Foxy da yatsa "This rapist? Shi kake cewa in yafe masa? Someone that manages to shake my life?" gaban Foxy ya fad'i dumm zufa ta shiga karyo masa ta ko ina "Afeefah kina nufin dama Fahad ne ya miki fyad'e?" suka tsinto muryar Daada, karkato da kanta Afeefah tayi tana kallon Daada lokaci d'aya tana kuka tana jinjina kai tace "Shine Daada! Fahad ne!" kuka Daada ta fashe dashi me tsanani ta kasa cewa komai yayin da Afeefah ta mayar da kallon ta ga Fawaz tace "Ko ka manta akan Fahad ne nasan what it feels like to be in love? Kuma a kansa nasan miye heart break kuma shine ya fara mayar dani the person I am right now.. A girl with no virginity, no value, no pride... Nothing Oldie!" haka take maganar da k'yar tana kuka numfashin ta sai sama da k'asa yake yayin da Fawaz har yanzu dafe yake da k'irjin sa shi kad'ai yasan azabar da yake ji "Meyasa koda yaushe abokanin ka sune damuwar ka? Me suka tab'a tsinana maka da kullum kake k'ok'arin basu kariya no matter the situation?" sannan ta d'an dakata tana saukar da numfashi tace "Your friend again kidnap me and he pinned the kidnap on you ya kashe mutum still yace kaine ka kashe sa ya sace ni ya kaini wani gun daban, ya d'aure ni ya dake ni san ransa ya karb'i mak'udan kud'i hannun mahaifi na ya tirsasa ni nasha k'wayoyin da zasu iya hauka ta ni... " sannan ta d'ago jajayen idanun ta tana kallon Fawaz muryar ta ta kusa ta disashe saboda azabar kuka ta cigaba da cewa "But I can call that even.. Bai tsaya a nan ba sai da ya gayyato abokanin sa." a hankali ta wara yatsun hannun ta hud'u ta mak'ale d'aya tace "Four of them! They humiliate me and rape me again!" tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka mai ban tausayi, kowa a d'akin kuka yake har shi uban tafiya wato Faruk ballantana Afeefah wacce kamar ranta zaya fita haka take kukan ga numfashin ta yana barazanar tsayawa "Koda na yafe wa abokanin ka Allah ba zai yafe musu ba." a hankali Faruk ya tako yazo kusa dasu ba abunda ke fita idanun sa sai hawaye ya kalli Fawaz wanda ya had'e kai da gwiwa sai kuka yake yace
"Nasan ban cancanci yafiya daga wurin ku ba but still ina rok'ar ta.. Na kasa hak'uri da rayuwar talaucin da Allah ya tsara min I'm a guy without any character and faith... Wasu idan Allah ya jarrabe su da irin wannan zasu saka wa zuciyar su salama and cope with the situation but me.. " sai ya fashe da kuka "I'm not fitted to cope with anything, bansan komai ba except having a good time, bansan komai ba sai shaye-shaye, bansan komai ba sai san kud'i I have no any sense of value I'm all ashamed of myself..." wata k'ara da Fawaz ya fasa ce ta dakatar dashi kallon su duka ya koma kanshi, feshin jini Fawaz keyi ba kama hannun yaro da gudu Maryam ta fita d'akin tana kuka don kirawo Doctor yayin da Foxy ke rik'e dashi sai aman jinin yake. Doctor yana zuwa ya bada umurnin aje azo da stretcher ba'a dad'e ba sai ga Nurses d'in sun zo da ita aka d'ora Fawaz a kai aka fice dashi da hanzari, Daada da Maryam ne suka rufa musu baya yayin da d'akin yayi sauran Afeefah, Foxy, Faruk, Aunty Nana da 'yan sandan biyu. Kuka Afeefah ta fashe dashi Foxy ma ya zauna sai hawaye ke fita idanun sa ya kasa katab'us haka ma Faruk. An kwashe kusan minti talatin basu ba labarin su kamar daga sama suka ji an turo k'ofar, Maryam ce ta shigo fuskar ta ba walwala sai dai idanun ta sun bushe k'am ba alamar ko d'igo d'aya na hawaye, kayakin su dake d'akin ta fara had'a wa ba tare da ta ce dasu uffan ba wanda ya basu mamaki da tsoro ba kad'an ba, Afeefah ce tayi k'arfin hali tace
"Maryam ya jikin nasa?" d'ago kai Maryam tayi had'i da yin murmushin yake ta kalli Foxy, Faruk da Afeefah tace "I hope kune zaku saka shi a makwancin sa just so you can let him down for the last time." sannan ta juya don d'auko handbag d'inta, finciko ta Foxy yayi da k'arfin gaske kamar wani zaki yana haki jijiyoyin kansa sun tashi fuskar sa ta chanza zuwa ja yace "Me kike nufi?" "Ina nufin burin ku ya cika kun kashe Ya Fawaz." kuka kamar k'aramin yaro mai cike da k'unar zuciya da nadama Foxy ya fashe dashi ya zame zuwa k'asa yana ta faman buga kansa da bango yayin da Afeefah kam mutuwar tsaye tayi basu ankara ba sai ganin ta suka yi ta yanke jiki ta fad'i.
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*36*
*I'm so long and hooked into your comments and deep prayers to Fawaz, Allah Ya karb'i addu'o'in ku ameen.*😭
Kururuwa Aunty Nana ta fasa tayi kan Afeefah tana jijjiga ta sai dai ko alamar motsi babu a tare da ita. Foxy kam zaune yake yayi zaman dirshan sai staring wa tile yake da ache shima zai samu ya suma kamar Afeefah a ganin sa da yaji dad'i at least k'wak'walwar sa zata samu hutu yayin da 'yan sanda suka tasa k'eyar Faruk suka koma dashi. Kururuwa Aunty Nana ta cigaba da yi tana jijjiga Affee har sanda Nurses suka jiyo suka iso d'akin suka ga abunda yake faruwa, da hanzari aka d'auki Afeefah cikin sauri aka fice da ita.
***
Maryam ce rik'e da Daada wacce sai kuka na fitar hankali take ba ji ba gani yayin da Abba ba abunda yake sai kai da komo yake har lokacin ya kasa gasgata abunda yake faruwa, likitan ne ya fito daga d'akin da gawar Fawaz take ciki ai kuwa caraf Abban Fawaz ya tare da muryar sa har tana stammering yace "Doctor da gaske yaro na ya mutu?" "I'm sorry munyi iyakar k'ok'arin mu but Fawaz ya had'u da ajali zuciyar sa ta buga." kallon yadda kalaman ke fitowa daga bakin Doctor Abba keyi jikin sa sai kyarma yake yana karanto kalmar shahada kamar a mafarki yake ganin abun wai yau shine ake gayawa mutuwar d'an sa d'aya tilo "Za'a bayar da Ambulance ku tafi da gawar don yi mata sutura." cewar Doctor'n sannan ya kalle su duka cike da alhini yace "Allah Ya jik'an Fawaz." yana kaiwa nan yasa kai ya wuce. K'ara rushewa Daada tayi da kuka yayin da Maryam ke rik'e da ita kawai ita zuciyar ta dake ko kukan ta kasa, a hankali Abba ya ja k'afafun sa ya danna kansa a cikin d'akin. Gawar Fawaz ya idanun sa suka fara masa revealing kwance shal an rufe ta da farin k'yalle "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" shine kawai ya iya fitowa bakin sa ya ja yayi tsaye a wurin ya kasa k'ara koda one step. Ya shafe minti goma a tsaye yana kallon gawar Fawaz ya k'wak'walwar sa ta cunkushe da tunani barkatai har ma tana k'ok'arin dakatawa, sai da yayi ta maza sannan ya fara d'aga k'afafun sa ya nufi wurin da gawar ke kwance. Nan ma ya shafe wasu mintuna sa'annan jiki na rawa ya mik'a hannun sa da ke shaking ba kama hannun yaro ya fara yaye farin k'yallen da ya rufe fuskar gawar Fawaz, daidai lokacin da fuskar Fawaz ta bayyana daidai lokacin hawaye suka zubo masa, hannun sa yasa ya shafa fuskar sa yace "Fawaz? Fawaz you really couldn't be gone." a hankali ya fashe da kuka marar sauti "You really couldn't be gone without saying goodbye to me inna lillahi wa innaa ilaihi raji'un!" kuka Abba keyi kamar k'aramin yaro duk da yasan hakan ba kyau amma ji yake idan har bai fidda wannan kukan ba to shima zai iya mutuwa. Sai da ya gaji ya mayar da farin k'yallen ya rufe masa fuskar sa yace "Fawaz idan har akwai alhaki na a kanka na yafe maka duniya da lahira." sannan ya saka hannun sa a cikin aljihu ya fiddo handkerchief ya goge fuskar sa sannan ya juya ya nufi ficewa daga d'akin. A bakin k'ofa yayi kicib'is da wanda zasu d'auki gawar Fawaz a Ambulance zasu shiga, hanya ya basu ya fiddo wayar sa ya fara shaidawa 'yan uwa da abokan arziki mutuwar d'an sa Fawaz. Allah sarki mutuwar Fawaz ta zama tamkar guduma ga duk wanda ta riske sa wasu ma k'aryatawa suke yayin da Daada ke zaune ta zuba tagumi sai hawaye ke zubar mata Maryam kuma a tsaye take tayi folding hannayen ta a k'irji tana kallon k'asa kawai.
Daidai lokacin da aka fito da gawar Fawaz daidai lokacin Foxy ya iso wurin duk ya fice daga hayyacin sa. Gawar da ya tabbatar ta aminin sa ce tayi hitting idanun sa wanda ya saka shi daskarewa yana kallon yadda ake tura sa zuwa wurin da aka ajiye Ambulance d'in, ba a abunda ya dawo masa sai moment nasu na jiya da dare a inda Fawaz ke zaune akan gado shi kuma yana zaune a kujera sun sha hirar su da jokes da suka saba kai ka rantse da Allah ba Fawaz ne majinyacin ba suna cikin wannan yanayin mai dad'i Foxy ya kalle sa yace
_"I'm sorry Fizzy I never meant to make my trouble your trouble. " murmushi Fawaz yayi sosai har hak'oran sa suka bayyana yace_ _"I'm pretty sure your trouble is my trouble Foxy so please ba godiya a tsakanin mu what family is for?" murmushi shima Foxy yayi he can't ask for a better friend than Fawaz "What made you think I'll do it?" Fawaz ya tambaye sa_ _"Friendship." Foxy ya amsa masa_ _"Wrong! The bond between us is more than friendship it's brotherhood!" dariya Foxy yayi yace_ _"Thanks tho.. Yaya jikin ne?"_ _"Man I can even smash you down."_ _"Ai kuwa da naci buroban ka wallahi and show you the difference between a man and a sick girl! " daga nan suka tarwatse da dariya._
A hankali ya fara dawowa daga gajeruwar duniyar tunanin da ya wula zufa ta shiga keto masa ya kasa yarda Fawaz ne ya rasu gani yake idan yaje ya masa magana mik'ewa zai yi su fara embarrassing junan su kamar koda yaushe Allah sarki bai ankara ba sai gani yayi an shige da gawar Fawaz a Ambulance d'in su Abba ma sun shiga motar su sun ja zasu bar asibitin, da hanzarin sa shima ya nufi motar sa ya rufa musu baya. Motar su Abba ce a gaba sai Ambulance dake bayan su sai kuma motar Foxy wanda yake daga k'arshe, Allah kawai ke kare tuk'in Foxy ranar saboda sam hankalin sa baya jikin sa shi dai yana tuk'in ne kawai da gangar jikin sa amma k'wak'walwar sa da hankalin sa basu tare dashi. Cikin ikon Allah wuraren k'arfe biyar na yamma suka isa garin Kaduna a inda mutane 'yan uwa da abokan arziki suka yi dafifi suna jiran isowar su. Wasu abokan kuka suke wasu salati wad'ansu hargowa haka ma sauran jama'ar wurin, kasa fitowa daga mota Foxy yayi duk da cewa mutane sun masa dafifi a mota shima a matsayin sa na babban abokin mamacin tun suna k'anana, had'a kai yayi da steering motar sa ya fashe da kuka mai tsanani he want to be strong ya amsa gaisuwa da kalaman jimami dake fitowa daga bakunan abokanin su na Kaduna da kuma Liberty International Schools but mutuwar Fawaz is really tearing him apart ya kasa yin k'arfin hali koda kad'an. Ji yayi an bud'e k'ofar motar an tab'a sa koda ya juyo yaga mahaifin sa ne shima idanun sa sun yi jajir "Weeping bitterly won't bring him back Fahad, ba abunda Fawaz ke buk'ata a yanzu sai addu'ar mu beside, ga abokanin ku nan sai zuwa suke from all over please come out and be strong." fashewa ya k'ara yi da kuka sai yanzu ya samu ya fara fitar da wani k'ololon bak'in cikin yana girgiza kai yace