Abokaina complete book 1 - Chapter 15
Abokaina complete book 1 Chapter 15: Abokaina complete book 1 Chapter 15. "Gaskiya wannan maganar ba gaskiya bane Officer, mu muka haifi Fawaz kuma muna…
4,494 words
"Gaskiya wannan maganar ba gaskiya bane Officer, mu muka haifi Fawaz kuma muna tabbatar maka ba wani laifin da Fawaz zai aikata." "Ai kuwa d'an ku ya aikata gagaruman laifuka." "Me ya aikata?" cewar Abban Fawaz da yanzu ma hararar d'an sandan yake
"So far cases uku muke dasu akan Fawaz na farko rape case na biyu kidnap case na uku murder case." zaro ido mahaifiyar Fawaz tayi had'i da dafe k'irji tana karanto kalmar shahada yayin da Ammi ta zaro ido tace "Me?" jinjina kai d'an sandan yayi yace "K'warai kuwa Hajiya." Zuhra kam dafe kai tayi yayin da Foxy zuciyar sa sai da ta buga da k'arfin gaske jin an ambaci 'rape'. Mik'ewa tsaye d'an sandan yayi yace "Ku biyo ni." ya shige gaba suna biye har zuwa d'akin da Fawaz yake wanda yake zaune ya kifa kansa akan table, shigowa suka yi d'aya bayan d'aya wanda yasa Fawaz d'ago kansa idanun sa suka sauka akansu. Dukansu sai da zuciyoyin su suka karaya da ganin Fawaz cikin mawuyacin hali fuskar sa duk ta kumbura ba mamaki 'yan sandan sun lallasa shi ne. Fita Zuhra tayi daga d'akin a guje tana kuka yayin da Abban Fawaz da mahaifiyar sa da kuma mahaifin sa daskarewa suka yi a wurin, Foxy kuwa ba abunda yake nanatawa sai Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un da sauri ya isa wurin Fawaz ya rik'e sa cike da alhini, tuni yayi nadamar abunda ya aikata kuma sai yau ya tabbata Fawaz Abokin sa ne na rai gashi zaune yana serving his own penalty don yana da yak'ini d'aya daga cikin laifukan da d'an sandan yace Fawaz ya amsa shine yiwa Afeefah fyad'e wanda kuwa Fawaz yana kare masa ne kawai hawaye suka ciko masa ido yayin da Fawaz forcing murmushi kawai yayi ya mayar da kansa kan mahaifan sa. A nan ne d'an sandan ya shiga lissafo masu abunda Fawaz yayi da shaidun da suke da a kansa, dukansu sunyi mamaki ba kad'an ba saboda idan dai abunda d'an sandan ya fad'a gaskiya ne to lallai akwai sa hannun Fawaz a cikin wad'annan miyagun ayukka saboda wad'annan shaidun babu na yarwa, baki galala Abban sa ya bud'e yana kallon sa cike da tsintsar mamaki da firgici bakin sa har yana rawa yace
"Really? Fawaz kisan kai? Fyad'e? Garkuwa da mutane? Duk kai kad'an ka?" "Wallahi Abba ba gaskiya bane Yaya Fawaz will never do such a thing k'arya suke masa." cewar Maryam wacce sai kuka take ba ji ba gani, ita kam mahaifiyar sa ko damar magana bata samu ba ta kasa ma yarda da abunda yake faruwa like is this even happening?
"Fawaz d'ago kanka kayi min magana gaskiya ne abunda yake fad'a?" cewar Abba wanda jikin sa har tsuma yake sai k'arasowa yake kusa da wurin da Fawaz yake zaune, d'ago da kansa Fawaz yayi idanun sa sun chanza launi zuwa ja jijiyoyin kansa duk sun fito fuskar sa ma tayi jajir akan azabar kuka yace "Abba bani bane bansan komai akai ba." juyowa Abba yayi ya kalli d'an sandan yace "Kace ya amsa d'aya daga cikin laifukan wanne ne daga ciki?" "Ya amsa shi yayi wa yarinyar fyad'e." tasss Abba ya wanke Fawaz da wani mahaukacin mari yana huci ya finciko kwalar rigar sa yace "Ni zaka yiwa k'arya? Ni sa'an ka ne? Ko an gaya maka wasa ya kawo ni nan?" wani kukan bak'in ciki Fawaz ya fashe dashi Foxy ma bai san lokacin da hawaye suka zubo masa ba har ya bud'i baki zai yi magana kenan suka had'a ido da Fawaz yayi saurin girgiza masa kai ya juya ya kalli Abba yace "Nine Abba nine na yiwa Afeefah fyad'e amma wallahi bani da alak'a da sace ta da kuma mutuwar Ra'es ku yarda dani Abba." sai kuma ya fashe da kuka, haka suka taru shi da Foxy suka yi ta kukan da Foxy ya bud'i baki zai yi magana nan take Fawaz zai yi saurin katse sa ta hanyar cewa shine yayi wa Afeefah fyad'e amma bai san komai game da sauran laifukan ba. Wani kallon bak'in ciki Abba ke bin Fawaz dashi ji yake uwa yaje yayi strangling nasa a wurin, cikin kakkausar murya yace
"Yiwa 'ya'yan mutane fyad'e na kawo ka kayi a Abuja Fawaz? Ni zaka ciwa mutunci haka?" "Abba..." "Dakata!" cewar Abba cike da tsiwa "Wallahi kai ka sani you're on your own ba ruwa na hanyar da ka bi ka saka kanka kabi ta ka fidda kanka!" mummunar fad'uwa gaban Fawaz yayi yace "Abba..." kallon Maryam da mahaifiyar su Abba yayi yace "Muje gida shi ya sani wallahi ba ruwa na." kururuwa Maryam ta saki ta k'ank'ame Abba, damk'o hannun ta Abba yayi ta fizge ta nufi Fawaz da gudu ta k'ank'ame shi tana kuka, hawaye masu zafi suka zubo wa Fawaz ya kalle ta cikin wata wahalalliyar murya yace
"Kuje gida Maryam everything is gonna be alright in shaa Allah." girgiza kai tayi tana sobbing bitterly cikin fushi Abba yace "Zaki shige mu tafi ko kuwa?" "I'm not going Abba!" haka ta fad'i maganar cike da tsiwa "I'm staying with my brother! He's all I've got! Idan muka tafi wa yake dashi? Ba zan tafi ba sai dai su kashe mu tare." ta k'are maganar tana kuka, mamaki ya kama Fawaz ya kalle ta yace "Maryam he's your father! Abban kike gayawa haka?" "Na fad'a I'm not going!" ta sake nanatawa "Shikenan ai." cewar Abba "Ke zaki shige mu tafi ko kina nan?" ya k'are maganar yana kallon mahaifiyar su, ba yadda zata yi don tasan zafin mahaifin nasu mayafin ta tasa ta toshe bakin ta ta juya ta nufi hanyar fita yayi saura daga d'an sandan, Ammi, Maryam sai Foxy a d'akin, dakatar da Abba Ammi tayi tace
"Yaya ya zaka yi haka fisabilillah? Don Allah karka tafi, gaskiya Maryam ta fad'a wa ya rage wa Fawaz idan kuka tafi? Don Allah Yaya kayi hak'uri." harara ya dalla mata yace "Idan muka tafi ai yana da ke ko kuwa?" sannan ya rab'a gefen ta suka fice suka barta sororo a wurin. Kuka ba na wasa ba Maryam da Fawaz keyi yayin da Foxy ya jingina a bango ya rasa ma me zai yi.
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*32*
Dukansu hawaye ke fita a idanun su sun rasa mafita wannan abun akwai rud'ani da kwance kai. Saukar da numfashi Ammi tayi ta k'araso kusa da Fawaz tace "Fawaz ka tabbata ba hannun ka a cikin wannan al'amarin kuwa?" "Haba Ammi! For how many times zai gaya muku ba shi bane? Ba Fawaz bane he's really not kawai an k'ak'aba masa abunda bai ji bai gani ba." cewar Foxy "Da wannan maganar ma we should think of a better dialogue kawai." "Gaskiya ne." cewar Ammi "Ni wallahi kaina ma ya kwance kwata-kwata bansan miye mafita ba." daidai lokacin ne d'an sandan ya k'araso had'i da cewa "We've given you enough time saboda haka..." bai kai aya ba Fawaz ya katse sa
"Officer just give me a listening ear wallahi bani bane." "Fawaz kenan... Is anyone going to believe that? But never mind you can argue that with the jury don idan ka cigaba da yi mana yawo da hankali zamu tattara ka mu watsa ka kotu ne." kuka ya sub'uce ma Maryam ta k'ank'ame Fawaz tam, da k'yar Foxy ya samu ciro ta daga jikin Fawaz tana ta faman kuka da sheshsheka ya shiga lallashin ta sannan ya kalli Fawaz "It's okay Fawaz in shaa Allah komai zai tafi daidai zanje in ga Uncle K idan da akwai abunda zasu iya yi." jinjina masa kai kawai Fawaz yayi Foxy ya bubbuga kafad'ar sa yace "Stay strong it solves every problem." bai ce musu komai ba haka Foxy ya sako Maryam a gaba tare da Ammi suka fito. Koda suka fito suka samu Zuhra sai kai komo take tana waya sam bata san da fitowar su ba
"You drunken fool! Haba! Haba fisabilillah! This is against the plan!" sai kuma tayi shiru na wad'ansu dak'ik'u tana saurarar abunda ake fad'a cikin wayar, cikin fushi da b'acin rai tace "Haka kace ko? You think I don't know how to handle a junky? I'll show you how it's fucking played." nan take kuma ta katse kiran ta buga tsuki had'i da juyowa, mamaki da tsoro suka kama ta lokacin da ta juyo taga Ammi, Foxy da Maryam a tsaye suna kallon ta bata da tabbacin basu ji dukkan maganganun da tayi a waya ba, k'irjin ta sai dukan uku-uku yake lokacin da Ammi tace
"Zuhra ke da waye haka a waya sai faman fad'a kike?" tayi maganar kamar tana zargin wani abu "Bakomai." ta fad'a tana sosa kanta sannan ta mik'a hannu ta jawo Maryam wacce sai kukan d'an uwan ta take suka nufi wurin da suka yi parking. Sai da Ammi da Foxy suka k'ara tattaunawa game da al'amarin sannan suka rabu akan zasu na waya sannan tabi bayan su Zuhra shi kuma Foxy ya shiga motar sa suka kama gaban su.
A kwana a tashi sai da Fawaz ya shafe kwanaki biyar hannun 'yan sanda kullum da kalar wahalar da ake basa don kawai ya amsa laifin sa amma yak'i. Ammi da Foxy sunyi iyakacin bakin k'ok'arin su wurin shige da fice don ganin an gyara matsalar amma abun yaci tura yayin da Abban Fawaz da mahaifiyar sa sun dad'e da tsufa gida Kaduna. Tunda sassafe Foxy yayi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya ya nufi headquarters, da k'yar ya samu suka barsa yaga Fawaz. Zaune yake ya fara fita hayyacin sa singlet d'insa duk ta b'aci da jini haka fuskar sa duk raunuka ne, Foxy bai san lokacin da hawaye suka ciko masa ido ba da ganin abokin sa cikin wannan mawuyacin hali, juyawa yayi ya basa baya ya fiddo handkerchief ya share idanun sa ya tattara confidence d'insa sannan ya juyo ya nufi wurin Fawaz. Dukansu shiru suka yi ba wanda yace da wani uffan
"Fawaz" Foxy ya kira sa. D'ago kai yayi ya kalle sa yace "Na'am" "Fawaz meyasa kake min haka? Why for heaven's sake? Why are you taking the blame for something that is not yours? Duk lokacin da ka shiga matsala you're keeping me out like I'm an outsider meyasa? You're a pal Fizzy, a real pal but tell me am I ever your friend?" sannan ya k'ara goge hawayen da suka ciko masa ido yace "I did all I can amma na kasa samun hanyar da zan fitar da kai daga wannan wurin the only thing left is to share the pain, Fizzy lemme tell them the truth ka bari in gaya musu nine nayi wa Afeefah fyad'en nan." murmushi Fawaz yayi sannan yace "Koda ka gaya musu kaine kayi wa Afeefah fyad'e it won't change a thing Foxy, ba shi zai sa su sake ni ba ko ka manta zargin kisan kai da garkuwa da Afeefah duk suna kaina? Fyad'e ba wani babban laifi bane idan aka alak'anta shi da wad'annan laifukan kawai ka barsu suyi dik abunda zasu yi I'm all prepared." dafe kai Foxy yayi sannan kamar an tsunkule sa yace
"Yauwa Fizzy wai ya aka yi suka yi pinning wannan shaidun akan ka da gaske kaine ka kira mahaifin Afeefah game da sace ta kuma an ganka kana binne gawar Ra'es?" wani hawayen bak'in ciki ne ya zubo ma Fawaz ya kwashe labarin duk abunda ya faru tsakanin sa da Cheetah ya gaya masa, kalmar shahada Foxy ya shiga yi yana tafa hannu yace "Fizzy how could you keep something like that away from us? Meyasa baka gayawa kowa ba tun abun bai yi nisa ba?" shiru kawai Fawaz yayi yayin da Foxy ya mik'e tsaye ya dunk'ule hannun sa d'aya ya kaiwa d'ayan naushi had'i da cewa "Fuck it! Fizzy kayi shirme wallahi."
"Ni yanzu ba wannan ba, I don't care about myself Afeefah ce damuwa ta. Kidnappers are like pack of wild dogs zasu iya yin duk abunda suka ga dama da ita idan har basu kashe ta ba kenan." "In shaa Allah she's safe." cewar Foxy. Hawaye masu zafi suka zubowa Fawaz ya dafe k'irjin sa had'i da cije leb'e ya saki wata k'ara
"Arrrrghhh! Foxy! My chest!" durk'usawa Foxy yayi da sauri ya rik'e sa had'i da cewa "Sorry, chest pain d'in ne?" "Arrrrghhh!" ya sake sakin wata k'ara kafin Foxy yace zai yi wani abu sai gani yayi Fawaz yana tarin jini, da sauri ya sake sa ya fita d'akin a guje yana k'wallawa 'yan sanda kira cikin mintuna k'alilan sai gasu sun dawo tare. Da taimakon wani d'an sanda Foxy ya samu suka d'aga Fawaz aka fita dashi da sauri zuwa asibiti.
***
Jini da ruwa ne suke shiga jijiyoyin sa a lokacin da yake kwance shantam akan gadon asibitin idanun sa a rufe da alama bacci yake. Foxy ne zaune bisa kujera gefen sa yana danna waya yayin da 'yan sanda biyu ke tsaye k'yam a gefen gadon saboda tsaro. Sai a lokacin hankalin Foxy ya dawo jikin sa ya tuna all this while bai sanar da Abba halin da Fawaz yake ciki ba ballantana Ammi, d'aga waya yayi ringing d'aya a na biyu Abba ya d'auka had'i da cewa "Assalamu alaikum" "Wa alaikumus salam ina wuni Abba?" "Lafiya Fahad, kana lafiya?" "Abba ba lafiya." gaban Abba sai da ya fad'i don kuwa k'arfin hali ne kawai yayi lokacin da zuciyar sa ta rufe amma ba don bai tausaya ma Fawaz ba, idan da za'a bud'e zuciyar sa to za'a tabbatar ba wanda yake tausayin halin da Fawaz yake ciki sama dashi kuma tun lokacin da suka koma Kaduna yake ta tsammanin kiran Foxy "Innalillahi! Me ya faru?" cewar Abba. "Fawaz ne ba lafiya yana ta aman jini yanzu haka yana asibiti." "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" fad'ar Abba wanda yake zaune amma sai da ya mik'e tsaye ya bala'in razana saboda Fawaz ne kad'ai d'an sa namiji wanda kuma yake fatar nan gaba zai gaje sa yanzu idan ya rasa sa ya kenan?
"Abba you really need to be here, Fawaz yana matuk'ar buk'atar ku a kusa dashi." cewar Foxy, ajiyar zuciya Abba yayi jikin sa yayi sanyi matuk'a ya kuma yi da na sanin fushin sa "It's alright Fahad zamu zo in shaa Allah. Allah Ya basa lafiya." "Ameen Abba mun gode." da haka suka ajiye wayar. Kiran wayar Ammi yayi itama ya shaida mata halin da ake ciki cikin tashin hankali tace masa gata nan isowa asibitin. Ba'a d'auki awa d'aya ba Ammi, Zuhra da Maryam suka iso asibitin a firgice ganin halin da Fawaz yake ciki yasa kowannen su gwiwoyin sa yayi sanyi musamman Maryam wacce tunda suka baro gida take kuka, zuwa tayi ta zauna kusa da shi tana ta faman tare kukan da ke neman kufce mata da hannun ta, haka ta taso ta k'ank'ame Foxy ta fashe da kuka. Shima Foxy'n k'arfin hali kawai yayi yana lallashin ta amma sai da hawaye suka ciko masa ido. Zuhra wacce ke tsaye k'yam tana kallon Fawaz bata san lokacin da kwalla ta zubo mata ba ta juya a guje ta fice daga d'akin.
***
*Washegari* A washegarin ranar Fawaz ya farfad'o daga allurar dogon baccin da aka masa sai dai jikin yana jin sa sosai sai hamdala kawai saboda jinin sa ya bala'in haurawa har zuwa 195 ga ciwon zuciya, wata allurar baccin suka sake masa don ya samu hutu sosai ana haka sai gasu Abba sun iso. Koke-koke ne ya shiga tashi a cikin d'akin lokacin da suka iso musamman mahaifiyar Fawaz da kuma Maryam a daidai lokacin kuma babban d'an sandan da sauran muk'arraban sa suma suka iso asibitin, bayani likitan dake duba Fawaz ya shiga yiwa 'yan sandan bayan ya kammala ya masu sallama ya fice. Soshe-soshe Zuhra ta shiga yi uwa mai kwarkwata a jiki kamar tana so tayi magana kuma ta kasa. Foxy da Ammi ne kad'ai suka lura da halin da take ciki sai kai da komo take sai ta bud'i baki zatai magana, sai kuma ta kasa
"Zuhra?" Ammi ta kira sunan ta da alamar tambaya "You look disturbed mi yake faruwa?." "No, bakomai." tayi saurin amsawa duk alamun rashin gaskiya sun bayyana tattare da ita. Tambayar da Ammi tai mata ya jawo hankalin d'an sandan ya fara karantar ta ai kuwa nan take ya fara sensing rashin gaskiya a tattare da ita " 'Yan mata?" juyowa Zuhra tayi a gigice tana kallon sa da ka kalli idon ta zaka hango rashin natsuwa a tare da ita "Mi yake faruwa ne kin kasa zaune kin kasa tsaye?" nan ma girgiza kai tayi had'i da kak'iro murmushin dole tace
"Bakomai." d'an sandan yana da tight schedules a wannan lokacin amma yadda hankalin sa ya kasa kwanciya da Zuhra yasa ya fasa tafiyar ya samu kujera ya zauna. Cigaba da safa da marwa Zuhra tayi ta kai nan ta komo ta cije leb'e wani lokacin ta kai wa kanta duka wani zubin kuma kuma ta dunk'ule hannun ta d'aya ta kaiwa d'ayan naushi, tun sauran jama'ar dake d'akin basu fuskanci halin da take ciki ba har suka gane kuma duk wanda zai tambaye ta lafiya zata ce k'alau. Ta kusan shafe awa d'aya a hakan last last ta kalli Fawaz dake kwance bai san halin da yake ciki ba sannan ta kalli Ammin ta ta rushe da kuka, tuni Ammi tayo kanta da sauri had'i da d'ago ta tace "Zuhra akwai abunda yake damun ki gayamin." "Ammi I fucked up!" ta fad'a tana sheshshekar kuka "I fucked up so bad." tuni d'an sandan ya mik'e tsaye ya zura hannuwan sa a aljihu yana kallon ta haka ma sauran jama'ar dake d'akin "Menene? Me kika yi?" "Ammi I don't know how to say all this but Ya Fawaz has nothing to do with all this shit! Baya da hannu a cikin duk abunda ake zargin sa dashi." tuni Ammi ta sake ta kamar wacce ta dad'e rik'e da shocking bata sani ba
"Me kike nufi?" "If only I knew... Da nasan cewa abunda zan aikata zai back-firing nawa da banyi ba wallahi! Saboda Ya Fawaz nayi kuma shine yake cutuwa I have to draw him out of this mess!" k'ara matsowa d'an sandan yayi yayin da kowa a cikin d'akin ya kashe kunnuwan sa don jin ko me Zuhra ta aikata haka in banda Fawaz da bai san duniyar da ake ciki ba "Zuhra me kika aikata? Ni dama a 'yan kwanakin nan I've sensed a change in you, a coldness I couldn't understand me kika yi Zuhra?" cewar Ammi wacce voice d'inta sai raging yake cikin tsintsar tashin hankali "Dake nake magana!" ta jijjiga Zuhra wacce sai kuka take "Ki gayamin wanne rashin hankalin kika tafka!"
"Ammi I falsified your signature and every other details na account naki na kwashe miki duk kud'in da kika dad'e kina tarawa." haka ta fad'a mata maganar ido cikin ido ba alamar tsoro ko shakka tattare da ita. Kan kace kwabo d'akin ya d'auki salati ita kam Ammi zamewa tayi zuwa k'asa yayin da Zuhra ta cigaba da cewa..
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*33*
"Nayi amfani da wannan kud'in nayi hiring abokin sa suka sace Afeefah kawai dan na lura akwai soyayya a tsakanin ta da Ya Fawaz." murmushin gefen baki d'an sandan ya shiga yi yayin da d'akin yai tsit in banda sheshshekar kukan Zuhra ba abunda kake ji. Takowa d'an sandan yayi yazo dab da ita yace "Kwantar da hankalin ki kiyi mana bayani mai gamsarwa, kece kika saka aka sace Afeefah?" a hankali ta jinjina kai alamar eh, murmushi d'an sandan ya k'ara yi mai d'auke da alamomi yace "Ra'es fa? Kece kika saka aka kashe shi?" nan kam da sauri ta girgiza kai "Bani bace." "To gaya mana abunda kika sani." cewar d'an sandan, sai da ta kalli Ammin ta da sauran jama'ar dake wurin tace
"Na dad'e ina yiwa Ya Fawaz wani makahon so wanda ko uwar da ta haife ni bata san dashi ba sai dai shi sam baya sona. Nayi iyakacin k'ok'ari na don shawo kan sa amma abun ya ci tura ko saurara ta baya yi a daidai wannan lokacin na fahimci akwai soyayya a tsakanin sa da Afeefah a kuma daidai wannan lokacin na d'auki mataki ta hanyar kwashe kud'in Ammi nayi hiring d'aya daga cikin mafi kusancin abokanin Ya Fawaz na rud'e sa da wannan kud'in har ya yarda zai sace Afeefah tsawon wani lokaci har in mallaki Ya Fawaz sannan su sake ta." "Ke da Faruk ko?" Foxy ya jefa mata tambayar kamar daga sama yana mata wani kallon tsana "Kune kuka jefa bawan Allah cikin wannan halin ko?" "Ni ku saurare ni mana! Da nasan Ya Fawaz zan saka a wannan yanayin ai da banyi ba!" cewar Zuhra tana share kwalla "Cigaba Zuhra muna sauraren ki." cewar d'an sandan, har Zuhra ta bud'i baki zata yi magana Abban Fawaz ya dakatar da ita ya kalli d'an sandan yace
"Officer ina ganin wannan matsalar ta cikin gida ce saboda haka zamu iya warware ta a tsakankanin mu." "Ba ta cikin gida bace." d'an sandan ya juyo yana duban Abba "Ta yiwu abunda zata fad'a zai leading namu zuwa ga sanin musabbabin mutuwar Ra'es saboda haka wannan maganar bata cikin gida bace." sannan ya maida kallon sa ga Zuhra "Cigaba da bayanin ki."
"Sai da na dank'a masa wannan kud'ad'en daga baya kuma yace min ba zasu isa ba dole sai na k'aro ba yadda ban juya dashi ba yak'i yarda har yayi barazanar fasa aikin idan ban k'aro ba, a lokacin dubara ta fad'o min na shawarce sa akan me ya gani idan suka karb'i wasu kud'in a matsayin musaya da ita daga gun mahaifin ta sai yace ya yarda da wannan shawarar, tun daga lokacin bai sake gayamin wani abunda ake ciki ba sai ji nayi an kama Ya Fawaz a matsayin wanda ya kashe Ra'es kuma ya sace Afeefah amma ni wallahi bani nace su kashe Ra'es ba!" saukar da numfashi d'an sandan yayi yayin da Ammi ta kasa katab'us sai kuka take "Ina suka b'oye Afeefah'n?" sai da ta share hawayen da suka zubo mata tukuna tace
"A Kaduna ne." a nan ta gaya masu local government d'in da wurin, fiddo da waya d'an sandan yayi suka yi amfani da map suka gane wurin nan take yayi forwarding location d'in zuwa office ya gaya musu 'yan sanda suyi fitar sirri zuwa wannan wurin ana kyautata zaton a chan ne ake b'oye da yarinyar da aka sace. Sai da d'an sandan ya tabbatar an tura yaran su zuwa Kadunar sannan ya dakata da buge-bugen wayar da yake yi ya kalli Zuhra ya karb'e wayoyin dake hannun ta yace
"Zamu cigaba da ajiye ki har lokacin za'a ga Afeefah da kuma samun gamsassun bayanai game da kisan Ra'es." kuka ta fashe dashi haka ma Ammi sannan d'an sandan ya bayar da umurnin a saka mata ankwa a tafi da ita headquarter ya bawa biyu daga cikin 'yan sandan umurnin a cigaba da tsare Fawaz.
_4:00pm_ Abban Fawaz, Daddy'n Afeefah, mahaifin Ra'es, IG da kuma wasu manyan 'yan sanda ne a tsaitsaye cikin wani d'aki a lokacin 'yan sandan da suka tafi Kadunan don rescuing Afeefah sun isa kuma 'yan sandan sun had'a su da cameras wanda ke d'auko musu hoton duk abunda ake ciki yayin da ake waya dasu a lokaci d'aya "Sir the place is all surrounded! Mun zagaye wurin ga baki d'aya they can't get away but they refuse to back out sun k'i su bada gari!" cewar d'an sandan a cikin waya "Kill them if they tried to break out but ku bi sannu zasu iya cutawa yarinyar along the way." cewar IG "Yes sir!" d'an sandan ya amsa, daga cikin akwatin talabijin da suka yi connecting da na'urorin su zaka iya hango fitowar Faruk daga cikin gidan gonar da suke b'oye hannun sa rik'e da Afeefah ya saita bindiga a kanta yana barazanar idan har 'yan sandan basu janye ba zai harbe ta not knowing the place is all surrounded, saukar harbi kawai yaji a hannun sa dake rik'e da bindigar nan take bindigar ta fad'i bai san lokacin da yayi cilli da Afeefah ba ya rik'e hannun sa da ke masa zogi kafin ya d'ago kai sai ganin sa yayi 'yan sanda sun masa k'awanya haka ma wasu daga cikin 'yan sandan sun kutsa kai a cikin gonar don damk'o ragowar team nasu
"Good job!" cewar IG lokacin da sauran 'yan sandan suka fito tare da ragowar kidnappers d'in "How's the girl?" IG ya tambaya "She don't seem to be talking sir." "It's okay ta yiwu tsoro ne I'll alert the helicopter zasu zo su d'auke ta." "Okay sir!" d'an sandan ya amsa.
***
Kamar yadda 'yan sandan suka fad'a haka ta tabbata don lokacin da aka iso da Afeefah ta helicopter sam bata magana sai ido, chan ma sai da aka kwashi 'yan kallo kafin ta amince da k'ok'arin wani d'an sanda ta yarda ta biyo su. Koda suka iso d'an sandan ne rik'e da hannun Afeefah tana biye dashi wane jela, da kuka Umma, da Abba suka tare ta sai dai me? Tsayawa tayi tana kallon su cike da tsoro ta fara ja da baya tana girgiza kai, dukansu mamaki ne ya rufe su saboda kallo take musu kamar wacce bata tab'a sanin su ba a rayuwar ta daga k'arshe ta kankame d'an sandan da ya kawo ta ta kawar da kanta daga garesu. Mamaki ne ya cika kowa a wurin daga nan IG yayi suggesting a kaita asibiti kawai.
***
"They have been drugging her." abunda d'an sandan ya shaida wa Daddy kenan lokacin da ya keb'e dasu cikin office d'insa "Suna bata wasu k'wayoyi wanda ka iya chanza hankalin mutum lokaci d'aya she's had a hell of a break." saukar da numfashi Daddy yayi yace "Yanzu meye shawara Doc?" "Ya dace ku barta zuwa wani lokaci before she's used to being free. K'wayoyin da suke bata suna causing alot of brain damages suna iya haukata ta or they can turn her into a zombie." "Wai dakata doctor! 'Yar tawa ce kake nema ka gayamin zata haukace ko me?" "I'm not saying.. Ba haka nike nufi ba, duk da cewa bana tunanin k'wayoyin sun tab'a k'wak'walwar ta but I'm sorry for her 'cause after an experience like this, I doubt if she's going to be one hundred percent normal amma ba wai na tabbatar ba zata dawo daidai d'in ba a'a it's just a theory of mine ta yiwu kuma ta dawo daidai sai dai ba tabbacin hakan."
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" abunda su Umma ke ta maimaita kenan.
*Ayi hakuri da kasancewar wannan shafin gajere zanyi kokarin kara wani zuwa gobe in shaa Allah. Nagode.*
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)