Abokaina complete book 1 - Chapter 14
Abokaina complete book 1 Chapter 14: Abokaina complete book 1 Chapter 14. "Jalal ya aka yi wannan al'amari ya faru? Meyasa tun da farko baka sanar da…
4,488 words
"Jalal ya aka yi wannan al'amari ya faru? Meyasa tun da farko baka sanar da hukuma ba? Wannan shine abunda muke k'ok'arin fahimtar da jama'a every single time irin wannan abun ya faru ku dinga fatali da duk wani abu da zasu fad'a ku dinga sanar muna da abunda ake ciki." saukar da numfashi Daddy yayi ya cire tagumin yace
"Officer he threatened to kill her the second I called you in ya kake so nayi? Na sanar daku nayi risking rayuwar ta? It's a difficult decision to make at last na aminta da k'in sanar daku d'in."
"I can't say I blame you Jalal." d'aya daga cikin 'yan sandan ya amshe da cewa "Ko nine a matsayin ka abunda zanyi kenan amma yaushe ne ganin ka na k'arshe da 'yar ka Afeefah?" d'ago da kai yayi ya kalli Umma wacce ta toshe bakin ta da mayafin ta nema take ko ta halin yaya ta mayar da kukan da ke neman kufce mata sannan ya kawar da kansa cike da alhini yace
"Ranar da na dawo daga tafiya ranar abun ya faru. Na dawo gida ban same ta ba mahaifiyar ta ta shaida min taje gidan wata k'awar ta. Haka muka yi ta zaman jiran tsammanin dawowar ta amma shiru har dare ba labarin ta, munyi k'ok'arin zuwa har gidan su k'awar tan kuma ta tabbatar mana a ranar sunyi waya da ita akan zata zo ta kawo mata ziyara amma bata zo ba. Abun wasa wasa har gari ya waye ba labarin Afeefah washegari d'aya daga cikin ma'aikatan gidan nan ya shaida min yaga motar ta amma bata ciki. Nayi k'ok'arin zuwa da kaina naga motar anan muka samu wayar ta a ciki and according to what I examined ba ta k'arfi aka fitar da ita daga motar ba saboda ba wani alamar wani abu ya faru kamar dai mutum yayi parking ya fita daga cikin motar sa ne. Har a lokacin abun bai tayar da hankali ba saboda a cikin 'yan kwanakin Afeefah ta fara mu'amala da yaran banza har tana satar fita garin haka har tsautsayi ya cika da ita aka yi mata fyad'e. Har a lokacin ban daina zaton wurin saurayin ta taje ba har sanda aka yi sati d'aya da faruwar al'amarin kidnappers d'in suka kira ni suka sanar dani komai game da kidnapping d'in da kuma ransom demand d'in. Na kai musu kud'in da kaina a wani daji hanyar Gwagwalada a inda suka sanar dani zanga flashing light sai nayi dropping kud'in kuma hakan ta faru suka bani tabbacin zuwa k'arfe uku na dare zata dawo amma har yanzu shiru." jinjina kai 'yan sandan keyi sannan na farkon da ya fara magana yace
"Ka samu ganin wanda yake haska flash lights d'in?" girgiza kai Daddy yayi yace "Ban samu ba saboda ya b'oye a cikin ciyayi da kuma tsananin duhun da ke akwai a wurin." jinjina kai d'ayan d'an sandan yayi yace
"We'll want to check those bushes, zaka iya biyo mu don ka nuna mana where exactly?" "Why not?" Daddy ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya k'ara da cewa "Muje." dukansu mik'ewa suka yi Daddy na a gaba suna baya suka fito parlor'n suka nufi parking lot suka shiga motocin su suka bar gidan. Tafe suke a yayin da Daddy ke zaune da babban d'an sandan a baya suna tattaunawa game da kidnapping d'in yayin da driver ke tuk'in sa kawai d'an sandan yace
"Kayi namijin k'ok'ari Jalal. Ba kowa ne zai iya yin abunda kayi ba, I don't think I would be so controlled and confident if I lose my daughter." Daddy wanda sauraren sa kawai yake amma a zahirin gaskiya yayi nisa a cikin tunani, da haka d'an sandan yai ta surutun sa har suka iso wurin suka yi parking suka fito nan take kuma 'yan sandan suka fidda bindigogin su saboda tsaro suka fara lamb'o wasu daga cikin su suka yi ambush koda wani abu zai faru yayin da uku daga cikin su had'i da Daddy suka taka suka isa wurin, examining daidai wurin da Daddy ya ga flash lights din 'yan sandan suka shiga yi sannan babban daga cikin su ya tsuguna kan k'afafun sa ya k'urawa k'asa kallo ya kira sauran gami da Daddy alamar suzo sannan yace
"Anan wurin ya b'uya and here's his footsteps but it won't mean a thing har sai mun kama shi wearing the same shoes as this." sannan ya juyo ya kalli d'aya daga cikin 'yan sandan yace "Take a picture of this foot print please zai mana amfani." nan take ba ma shi kad'ai ba har sauran 'yan sandan suka fiddo latest Iphones da Samsung suka shiga d'aukar hotunan foot prints d'in, d'aya daga cikin su ne ya hango kwalbar wine daga nesa nan take ya dakatar da d'aukar hoton ya nufi wurin kwalbar yasa handkerchief ya d'auko ta ya kira attention nasu yace
"Sir he is a wine addict!" had'i da nuna musu kwalbar, dukansu k'arasowa suka yi idan ka cire Daddy wanda ya k'urawa gefe d'aya ido yana tunani. Jinjina kai babban d'an sandan yayi ya bada umurnin a kai kwalbar cikin mota suka cigaba da dube-dube a wurin koda Allah zai sa suci karo da wani abun, da k'arfin gaske Daddy ya juyo yana kallon babban d'an sandan yace
"Na san ko waye yayi garkuwa da Afeefah! Wani matashin saurayi ne sunan sa Fawaz Shattima ba ko shakka shine!" juyowa suka yi lokaci d'aya yayin da Daddy jikin sa sai rawa yake yasa hannun sa aljihu ya fiddo wayar sa da wayar Afeefah sannan ya bud'e wayar sa ya lalubo number Fawaz da ya kira sa da ita sannan ya shiga kwafe number a wayar Afeefah ya danna call sai ga suna mai d'auke da 'Oldie' ya bayyana a wayar Afeefah, a rikice Daddy ke kallon 'yan sandan yace "Wannan yaron ne wallahi! Shine! Fawaz ne! Dama ni hankali na bai kwanta ko kad'an dashi ba!" dafa kafad'ar sa babban d'an sandan yayi cikin kwantar da murya yace
"Ka kwantar da hankalin ka kayi mana bayani sosai Jalal." k'ok'arin saita kansa Daddy yayi daga rud'anin gaggawa da ya shiga yace
"Fawaz shine yaron da nike gaya muku yayi wa Afeefah fyad'e. Da farko ta tab'a suma a makaranta wanda muma bamu san miye ya haddasa shi ba Fawaz ya kai ta asibiti ya kira mu ya sanar damu har yayi claiming shi yayan ta ne..." daga nan Daddy ya shiga zayyana masu har zuwa fyad'en da Foxy ya ma Afeefah wanda suke zargin Fawaz da shine yayi fyad'en da kawo ta asibitin da yayi da kuma claiming shi mijin ta ne a karo na biyu da kuma yadda ya sha alwashin sai an hukunta Fawaz muddin ya dawo daga tafiyar sa sai dai dawowar sa a ranar aka sace Afeefah. Abu na biyu kuma shine tabbas ya rik'e muryar Fawaz kuma hankalin sa sai yanzu ya maro ya gano kamar yasan muryar da ta kira sa tana basa instructions kuma zargin sa ya karkato ya dawo kan Fawaz sai kuma gashi number Fawaz d'in ta bayyana da suna na musamman a wayar Afeefah tabbas babu ko tantama Fawaz ne. Nan take 'yan sandan suka fiddo da laptops d'insu aka yi tracking number Fawaz ai kuwa dukka details na Fawaz ya fito including his full name, picture da kuma muhimman informations da yayi registering layin dashi a nan kuma Daddy ya gasgata hoton da ya fito a profile d'in Fawaz, suna a cikin haka sai ga waya daga headquarters a inda ake sanar dasu an tsinci hotunan kisan Ra'es da wani saurayi mai suna Fawaz Muhammad Shattima yayi.
*A wannan shafin nike shaidawa masu karatu zan dakata da rubuta wannan labarin saboda kusantowar azumin watan Ramadan. Ina rok'on Allah Ya sada mu da falalar sa da gafarar sa a cikin wannan wata mai albarka Ya kuma bamu ikon bauta masa cikin lafiya da kwanciyar hankali. Immediately bayan sallah zamu d'ora daga inda muka tsaya in shaa Allah. Just know that if it weren't with the joy of being in this holy month leaving you without the continuation of this story will be too hard for Shawty. Stay blessed Allah Yasa muna daga cikin masu kai bayan sallah, ameen.*
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👭 (A True Life Story)
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*30*
Tsayawa suka yi cak suna duban junan su dukkanin su sun kasa gasgata abunda yake faruwa musamman Daddy tabbas Fawaz ya zama green snake in a green grass
"Dama na gaya muku Fawaz ne! Shine wallahi!" fad'ar Daddy cikin rud'ani mara misaltuwa ya fara tafiya ya nufi motar sa, dakatar dashi babban d'an sandan yayi ta hanyar cin gaban sa yace "Ka kwantar da hankalin ka Magayak'i, idan har muka yi bincike kuma shaidu suka tabbata akan Fawaz, then I pray may God have mercy on him because the Nigerian Police won't have none." bambami Daddy ya shiga yi yana cewa "Yo Officer har wane shaidun kuma kuke da buk'ata bayan wad'an da suka bayyana? Ko har yanzu baka yarda Fawaz ne ya d'auke min 'ya ba?" tapping kafad'ar sa d'an sandan yayi cike da alhini yace
"It's alright." sannan ya dubi sauran abokanin aikin nasu yace "Muje! Muje headquarters!" ba b'ata lokaci suka shiga motocin su su duka suka danna suka nufi headquarters. Bayan isar su suka zauna suka auna shaidun da suka samu akan zargin su akan Fawaz kuma suka zo daidai nan take babban d'an sandan ya mik'e tsaye yace "Make a team right now! Whatever cave, cavern or hole Fawaz is I want you to get him in less than twenty four hours." mik'ewa 'yan sandan suka yi lokaci d'aya suka sare masa har suna had'a baki wurin cewa "Yes sir!" sannan suka fice d'aya bayan d'aya. Rik'o hannun Daddy babban d'an sandan yayi suka nufi hanyar fita ya shiga lallashin Daddy had'i da bashi baki kan ya kwantar da hankalin sa komai zai daidaita da yardar Allah.
***
Fawaz ne ke fitowa daga gidan su janye da trolley lokaci d'aya kuma da waya mak'ale a kunnen sa yana waya "Yau zan taso in shaa Allah." cewar Fawaz dake k'ok'arin rufe gidan da alama tafiya zai yi don kuwa ga motar sa nan parked a wajen, yana cikin wayar ne sai ga Ibro yaron dake musu aikace-aikace suka gaisa sama-sama ya cigaba da wayar sa yana k'ok'arin saka trolley d'insa a mota daidai lokacin ne ya hango motocin 'yan sanda sun danno, dakatawa Fawaz yayi cak yana karanta "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un." a fili yana kallon motocin na k'arasowa. Daga cikin wayar Foxy ke tambayar sa "Fizzy menene? Me yake faruwa?" "Police! I'm in a jam, a serious one Foxy!"
"Police? Ban gane ba me yake faruwa?" "I'm trapped Foxy! Ina cikin matsala!" " Come on Fizzy wace irin matsala? Ka nutsu ka min bayani mana." tsuki Fawaz ya ja yace
"In nutsu? Ina gaya maka ga Police nan zuwa kana gayamin wani in nutsu? Koda yake it's easy for you to say when your ass ain't on fire." a daidai lokacin har 'yan sandan sunyi parking motocin su sun fito sun nufo wurin da Fawaz da Ibro ke tsaye d'aya daga cikin su yasa hannu ya fizge wayar Fawaz gami da tsinke kiran ya rik'e wayar a hannun sa. Fitowa babban su yayi daga cikin mota yana murmushin mugunta yana kallon Fawaz wanda ya gama rikicewa fata kawai yake Allah ya tayar dashi daga wannan mummunar mafarkin da yake yi. K'arasowa babban d'an sandan yayi yana tauna chewing gum yana dariya lokaci d'aya yana tafa hannayen sa biyu yace
"Malam Fawaz barka da rana." kallo kawai Fawaz ke bin su dashi cike da rikici da d'aurewar kai tare dashi yace "Me yake faruwa ne? Me nayi..." "Ka adana maganganun ka ta yiwu zasu maka amfani nan gaba." cewar d'an sandan sannan yayi displaying ma Fawaz ID card nasa ya gani ya zarce da cewa "Mu 'yan sanda ne daga Police Headquarters an bamu umurnin tafiya da kai da akwai tambayoyin da zaka karb'a mana a chan." sannan ya dubi sauran 'yan sandan yace "Cuff the super star." ba tare da b'ata lokaci ba aka sakawa hannayen Fawaz ankwa. Fawaz bai yi yunk'urin yin komai ba haka yana kallo suka saka masa ankwa suka ingiza k'eyar sa zuwa cikin motar su suka bar Ibro tsaye cike da mamaki.
***
Ammi da Zuhra ne zaune a parlor suna kallo jefi-jefi kuma suna tab'a hira wacce hirar k'arfin ta daga gun Ammi ne don kuwa Zuhra tayi nisa a cikin wayar dake hannun ta. Wayar Ammi dake ajiye a gefen ta ne ta shiga buzzing alamar shigowar kira, da hanzari Ammi ta d'auko wayar ganin Foxy ne yake kiran ba k'aramin bata mamaki yayi ba, d'aga kiran tayi tana murmushi suka gaisa Foxy yace
"Ammi anya Fawaz lafiya kuwa?" "Lafiya k'alau mana duk da cewa dai kwana biyun nan bamu yi waya ba." kasa yarda Foxy yayi yace "Kai Ammi bana tunanin lafiya saboda yanzu ya kira ni yake gayamin zaya taso daga Abuja muna tsakiya da wayar sai ji nayi yana salati yana cewa ga police nan yana a cikin matsala tun daga lokacin kuma wayar sa bata tafiya." "Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" cewar Ammi wanda ya sa Zuhra ta d'ago kai tana kallon ta "To me yake faruwa ne?" Ammi ta tambaye sa a diririce "Wallahi bansani ba Ammi shiyasa nima na kira ki." "Nima bansan komai ba Fahad." cewar Ammi yayin da take mik'ewa tsaye cikin rud'ani, jin Ammi ta ambaci Fahad ne yasa Zuhra ta kashe kunnuwan ta don jin abunda yake faruwa don kuwa daga yanayin da Ammi ke wayar kasan ba lafiya "Kai kana ina ne yanzu?"
"Ina Kaduna naje hutu.. Please Ammi kiyi wani abu akai ki duba a chan gidan kiga abunda yake faruwa idan 'yan sandan da ya fad'a ne suka tafi dashi sai mu sani nima yanzu zan hawo hanya in shaa Allah." cikin sanyin jiki Ammi tace
"In shaa Allah zan duba Fahad, nagode." da haka suka ajiye wayar. Gyara zama Zuhra tayi tana k'ok'arin had'a ido da Ammi wacce fuskar ta ta kasa b'oye damuwar ta tace "Ammi lafiya kuwa?" "Ba lafiya Zuhra wai Fahad ne ya kira ni yake cewa yana kyautata zaton 'yan sanda sun tafi da Fawaz." zabura Zuhra tayi ta mik'e tsaye saura kiris ta fad'i "Ammi Fawaz kuma? A wanne dalilin?" "Ina nike zuwa sani Zuhra? Yanzu dai barin zo in tafi gidan nasu." shiru Zuhra tayi ta koma ta zauna jiki sanyaye.
***
Fawaz ne zaune cikin wani d'aki kan kujera da table a gaban sa anyi cuffing hannayen sa duka biyu a table d'in yayin da ya kifa kansa a kai sai hawaye ke zubar masa ya rasa abunda yake ciki tunda suka kawo sa suka rufe sa basu sake dawowa ta kansa ba kusan awanni biyu kenan. Takun tafiyar mutane ne ya jiyo wanda ya sanya shi d'ago kansa ba shiri a inda fuskar sa tayi sharkaf da hawaye, su uku ne gami da babban su da suka zo d'azu da aka kamo shi. Zama babban yayi kan kujerar da ke kallon Fawaz yayin da d'aya daga cikin sauran ya zauna kan table yana fuskantar Fawaz sauran kuma suka yi tsatstsaye suna kallon shi, murmushi babban yayi ya sark'a hannayen sa biyu yace "Fawaz Shattima ina fatar na fad'a daidai." kallon su d'aya bayan d'aya Fawaz keyi kurum hawaye na cigaba da malalar masa "Me nayi? Me na muku? Mesa zaku kawo ni nan ku rufe ba tare da kun sanar dani abunda na aikata ba?" dariya wanda ya zauna kan table d'in yayi gami da yin tafi yace
"A fuska dai ga ka very young and innocent but it only hide the bad things you do. You're smart Fawaz, but this time not smart enough." kan Fawaz ya gama d'aurewa shin akan fyad'en da Foxy ya ma Afeefah ne? Ko kuwa Cheetah ne ya cinno masa 'yan sanda? To amma mesa Cheetah zai cinno masa 'yan sandan bayan yayi abinda ya umurce sa? Yana cikin wannan tunanin ne yaji muryar babban d'an sandan yace
"Fawaz hawayen mene ke zuba a idon ka haka? Bak'in cikin mun harbo jirgin ka ne ko kuwa takaicin baka yi completing mission naka ba?" sannan ya dakata yana murmushi ya gyara zaman sa yace "Namiji mai irin sana'o'in ka baya zubar da hawayen sa akan kawo sa interrogation kawai! You have to be very brave because the bigger the crimes, the bigger the challenges!" kamar d'an sandan ya ingizo wasu hawayen ne daga idanuwan Fawaz don kuwa haka suka ta zuba uwa lalacaccen famfo zuciyar sa sai zafi take masa, dukansu kallon shi suke da wani irin crack a voice nasa yace
"What crimes? Me ake zargi na dashi?" "Cewa zakai me aka tabbatar a kanka don ba zargin ka ake ba." cewar d'aya daga cikin 'yan sandan dake tsaye, karkato da fuskar sa Fawaz yayi yana kallon d'an sandan da yayi magana sam ya kasa gane me suke nufi juyowa yayi yana kallon babban nasu sai kuma ya fashe da kuka gwanin tausayi yace
"Mesa ba zaku gayamin ta yanda zan fahimta ba? Me nayi?" "Saurin me kake haka Fawaz?" cewar babban d'an sandan yana wani makirin murmushi "Ai abunda ya kawo mu kenan." sai kuma yayi shiru yana ta kallon Fawaz yana murmushi. Ganin Fawaz bai ce ko k'ala ba sai kallo yake binsu dashi yasa ya cigaba da cewa "Ta ina zamu fara? Abubuwan naka suna da yawa fa." nan ma Fawaz bai ce dashi uffan ba "Akace tushe mafari hakane?" nan ma dai Fawaz bai ce komai ba sai idanu ya bishi dasu kamar kurma, yunk'uri d'an sandan yayi ya gyara zaman sa yace "Zan zayyano maka ayukkan ka wanda ba zargi ake akan ka ba bincike ya tabbatar mana da haka daga k'arshe zan maka tambaya guda d'aya kacal, idan har ka amsa mana cikin sauk'i to shikenan hukumar 'yan sanda ta gama aikin ta sai mu mik'a ka ga kotu don itama ta gudanar da nata aikin ta hanyar yanke maka hukunci da ya dace da laifin ka."
"Wallahi ni ba laifin da na aikata." cewar Fawaz yana girgiza kai cikin wata disashshiyar murya "Laifuka ka aikata Fawaz ba laifi d'aya ba." cewar d'an sandan "Na d'aya kayi wa Afeefah Jalal fyad'e. Na biyu kayi garkuwa da ita ka karb'i mak'udan kud'i a hannun mahaifin ta a matsayin musaya da ita kuma har yau baka dawo da ita ba. Na uku sa'in sa ya shiga tsakanin ka da Ra'es d'a a wurin babban ministan man fetur har ka hallaka shi ma'ana kayi sanadin mutuwar sa gaskiya ne ko kuwa?" girgiza kai Fawaz yayi yana zubda hawaye yace
"Ba gaskiya bane!" "To muna da shaidun da zasu tabbatar maka da haka!" cewar d'an sandan gami da mik'ewa tsaye "Dr. Shafeek likita kuma mamallakin asibitin Prince ya tabbatar a wani dare ka kawo Afeefah Jalal an mata kaca-kaca kuma a gaban Dr. Shafeek, mahaifin ta, mahaifiyar ta, yayar ta da kuma wad'an su likitocin ka tabbatar kaine ka mata fyad'en." rintse ido Fawaz yayi hawaye na zubar masa zuciyar sa sai k'una take wane garwashi yayin da d'an sandan ya cigaba da cewa "Na biyu kayi garkuwa da ita; number da ka kira mahaifin ta da ita don neman kud'in tayi daidai da number ka kuma tayi daidai da number da aka samu cikin wayar Afeefah kuma an samu hotunan ka a cikin wayar tata wanda yake nuna ka dad'e kana bibiyar ta. Mahaifin ta ya baka wannan kud'ad'en da ka buk'ata sai dai har yau baka mayar masa da 'yar sa ba. Na uku d'azu d'azun nan muka tsinci hotunan ka a lokacin da kake fad'a da Ra'es da kuma lokacin da kake gina rami zaka binne shi, banyi mamakin tsintar hotunan da aka yi ba watak'il wanda ya ganka lokacin da kake aikata ta'asar yana tsoron amsa tambayoyin 'yan sanda shiyasa ya nemi sakaya kansa." sunkuyar da kai Fawaz yayi hawaye na zubar masa don shi kam baisan ta ina zai fara kare kansa ba "Tambayar da zan maka itace ina ka b'oye Afeefah?"
*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫
*By Shawty*💕 *June, 2018* *Pure Moment of Life Writers*
*31*
D'ago kai Fawaz yayi ba zaka iya tantance zufa da hawaye a fuskar sa ba yace "Na yarda nayi wa Afeefah fyad'e amma wallahi ni ba ni na sace ta ba kuma ba ni na kashe Ra'es ba." dariya 'yan sandan suka shiga yi su duka yayin da hawayen bak'in ciki sai dad'a wanke fuskar Fawaz suke yana girgiza kai yace "Ku yarda dani, wallahi bani bane." lokaci d'aya suka dakatar da dariyar da suke d'aya daga cikin 'yan sandan ya buga table d'in da k'arfi yace
"Kai Fawaz! Karka nemi raina mana hankali mana! Waye ya kira mahaifin Afeefah a waya yana gaya masa ka'idojin yadda zai kai kud'in musaya da ita? Number waye aka gani? Iye? Waye aka ga yana fad'a da Ra'es har ya shak'e sa? Waye kuma aka gani yaje dokar daji yana gina rami? Ko an gaya maka bamu yi tracing wurin muka gino gawar ba? Ko kuwa an gaya maka bamu san aikin mu bane haka kawai zamu d'auko ka mu kawo ka nan?" sai yanzu Fawaz ya tabbatar da maganar da ya gaya ma Foxy cewar he's in a jam and a serious one gaskiya ce saboda ya lura ba zasu saurari duk wani abunda zai fad'a ba
"Wallahi bani na sace ta ba kuma bani na kashe Ra'es ba, na yarda ni nayi mata fyad'e amma wallahi sauran bani bane Officer ku yarda dani..." babban d'an sandan ba abunda yake sai dariya sannan ya dubi sauran yace "Me nake gaya muku a koda yaushe? Dig enough and something comes to the surface saboda tashin farko k'aryata duka laifukan yayi amma yanzu gashi yana gasgata shi yayi mata fyad'e kun gani ko?" sannan ya juyo yana kallon Fawaz yace "Da haka zaka amsa sauran Fawaz." rud'ewa Fawaz yayi zuciyar sa na masa zafi kamar zata faso k'irjin sa ta fito yace
"Officer ku saurare ni wallahi bani bane, ku jira in gaya muku wani abu..." "Me zaka gaya mana Fawaz? Tatsuniyar gizo da k'ok'i? Don't except miracles 'cause I don't think there's anything that can save you abu d'aya zaka gaya mana shine ina ka b'oye Afeefah? Kuma wallahi Fawaz idan har Afeefah ta mutu to ka kuka da kanka... " shigowar wani d'an sandan ya katse sa daga maganar sa, sai da d'an sandan ya sare masa tukuna sannan ya zarce da cewa
"Sir the IG wants you." zaro ido d'an sandan yayi yace "IG da kansa?" "Yes sir!" "Muje muje!" ya tasa k'eyar sauran 'yan sandan a gaba har sun kai bakin k'ofa ya juyo ya jefi Fawaz da wani kallo mafi muni yace "We are not done." saukar da kansa Fawaz yayi k'asa kawai yana kirawo sunayen Allah yana neman agajin gaggawar Sa.
IG, mahaifin Afeefah da kuma mahaifin Ra'es ne a cikin Ofishin zazzaune. Shigowar d'an sandan ya katse masu abunda suke tattaunawa ya gaida su cikin girmamawa sannan IG ya masa nuni da kujera alamar ya zauna, bayan ya zauna ne IG ya gyara zama yace "Ina fatar ba sai na maka bayanin zuwan wad'annan mutanen ba, so far what did you dig for them?" cikin girmamawa d'an sandan ya fara magana "Eh ranka ya dad'e mun samu nasarar arresting yaron yanzu haka yana hannun mu ya amsa cewar shi yayi ma yarinyar fyad'e amma yayi denying sace ta da kuma kisan Ra'es yanzu haka muna tsakiya da interrogation d'in ka aika min."
"Good" cewar IG sannan ya zarce da cewa "But before you pin the kidnap on Fawaz, you better start digging around for the other man for there must be a second person. Mutum d'aya ba zai iya garkuwa shi kad'ai ba dole akwai wad'ansu da zai yi influencing, kuma bana so ku dogara kan abunda zai sanar daku a interrogation room kawai, ina so investigation ya cigaba saboda zai iya cigaba da delaying naku yak'i gaya muku gaskiya har suje su illata yarinyar kaga anyi kuma ba'a yi ba. Our absolute priority now shine sanin wurin da wannan yarinyar take ka gane ai?" jinjina kai d'an sandan yayi IG ya mik'a masa hannu suka gaisa sannan yace "Ku k'ara himma please."
"In shaa Allah ranka ya dad'e." sannan ya juya ya fice.
***
Parking tayi ta suka fito da gaggawa suka kutsa kai cikin gidan. Ibro ne kawai suka samu zaune a tsakiyar gidan ya buga tagumi, shigowar su Ammi da Zuhra ne yasa shi mik'ewa wane wanda aka tsunkula cikin sanyin jiki ya k'araso wurin da su Ammi suka yi tsaye cirko-cirko, cikin girmamawa ya gaida Ammi sannan ta zarce da cewa "Ina Fawaz? Kada dai abunda yake fad'a gaskiya ne?" "Gaskiya ne Hajiya, 'yan sanda sun tafi dashi." tuni jikin Ammi yayi lis Zuhra ma haka "To wai a wanne dalilin za'a kama shi a tafi dashi? Me ya aikata?" fad'ar Zuhra sai faman bambami take
"To wallahi Hajiya nima bansan me ya faru ba sun dai tafi dashi kawai." kasa tsayuwa Ammi tayi ta samu wani lounging chair ta zauna tana maimaita Innalillahi wa innaa ilaihi. Wayar ta dake cikin jaka ta ciro ta kira mahaifin Fawaz ta zayyana masa komai yace yanzun zasu hawo hanya zuwa Abujan bata dad'e da ajiye wayar ba Foxy ya kira ta shaida masa tabbas 'yan sanda ne suka tafi da Fawaz kamar yadda yake tsammani, kwantar mata da hankali yayi yace mata in shaa Allah yana gab da shigowa Abujan.
A ranar suka iso Abuja dukansu sai dai koda suka iso dare yayi, ba yadda mahaifiyar Fawaz ba tayi ba kan ita dai aje aga wane hali d'an ta yake ciki mahaifin sa ya hana yace a bari har gari ya waye sai su je headquarters d'in saboda Ibro ya shaida musu headquarters yaji babban d'an sandan yana fad'a lokacin da za'a tafi dashi.
*Washegari* Mahaifin Fawaz, mahaifiyar sa da k'anwar sa Maryam sai Ammi, Zuhra da kuma Foxy ne zaune a ofishin d'an sandan wanda case na Fawaz yake a hannun sa, bayan ya gama duba wasu takardu dake gaban sa ne ya d'ago kai ya kalli Abban Fawaz wanda tun zuwan sa ba abunda yake sai bambami akan a wane dalilin za'a kama masa yaro a rufe "Officer on what charges? Wace dokar ce ta baku damar zuwa ku kama yaro na ku kawo shi wurin ku ku ajiye shi haka kurum ba laifin sama ballantana na k'asa? Me ake zargin yaro na ya aikata ne?" "Ranka ya dad'e ba zargin sa ake ba, munyi bincike kuma binciken da muka yi ya tabbatar muna da hakan kuma har shima ya karb'a d'aya daga cikin laifukan sa." kuka mahaifiyar Fawaz ta fashe dashi yayin da Ammi sai girgiza kai take tace