Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 13

Abokaina complete book 1 - Chapter 13

Abokaina complete book 1 Chapter 13: Abokaina complete book 1 Chapter 13. "Muje" Fawaz bai yi gardama ba ya kama hanya ya nufi motar tasu sai a lokacin ya…

4,474 words

"Muje" Fawaz bai yi gardama ba ya kama hanya ya nufi motar tasu sai a lokacin ya lura da zaman driver a motar, d'aya daga cikin su ya zauna a front seat yayin da d'ayan kuma ya zauna a back seat yai wa Fawaz alama ya shigo, jiki sanyaye Fawaz ya bud'e bayan ya shiga dukansu suka zauna a last edge na motar driver ya ja motar suka bar gidan. Tafe suke amma ba wanda ke ce da wani uffan motar shiru kamar an mutu yayin da Fawaz sai tunani yake tayi barkatai. Sunyi tafiyar ak'alla minti talatin wacce Fawaz bai ma san anyi ba sakamakon duniyar tunanin da ya shiga shi dai kawai yaga sun yanki daji sun shiga. Sai da suka shafe wasu mintuna goma suna tafiya cikin wannan dajin sannan driver'n ya ja ya tsaya mazajen suka fito. Fitowar su keda wuya suka bud'e boot suka fiddo shovel da digger da gawar da sauran kayakin aiki suka fara gina rami, Fawaz fitowa yayi yana kallon su da aikin digging d'in da suke yi ya kalli dajin yaga ba alamar mutum sai su kad'ai da kukan tsuntsaye, sai da suka kusan yin rabin aikin d'aya daga cikin su ya ajiye shovel d'in ya koma daga gefe sai haki yake alamar ya fara gajiya ya bar d'ayan yana yi. Shima d'ayan bayan kamar minti goma jikin sa ya nuna alamar gajiya ya d'ago kai yayi sharkaf da zufa ya tako yazo gaban Fawaz ya nasa wani shu'umin murmushi ya mik'a masa digger had'i da cewa

"It's better than doing nothing." Fawaz bai ce komai ba ya karb'i digger d'in yaje wurin ramin ya fara digging, zai yi kamar minti goma yana digging d'in but kasancewar ba abunda ya saba yi bane duk sai yaji ya gaji, karb'ar digger'n mutumin yayi yana ma Fawaz dariya alamar shi d'in ajebo ne sannan ya cigaba da gina ramin. Sai da suka gina rami mai zurfi sannan suka d'auki gawar Ra'es dake ajiye gefen ramin suka saka ta a ciki sannan suka fara maida k'asar. Sai da suka kammala aikin ga baki d'aya sannan suka shiga mota Fawaz ma ya shiga suka mayar dashi gida. Koda suka maido da Fawaz gida wuraren k'arfe hud'u na marece sannan suka masa sallama ya musu godiya suka juya. Fawaz dai haka ya zama tamkar gunki sai yadda suka yi dashi haka yazo ya zauna shi kad'ai sai tunani yake marasa tushe da mafari.

_6:00pm_ Wuraren k'arfe shida na marece Fawaz ne kwance a bisa sofa ya rasa abunda yake ciki yanzu ya samu sauk'in tashin hankalin da yake ciki sai kuma na garkuwa da Afeefah da aka yi. Tsayuwar mota ya ji wanda yasa shi mik'ewa ba shiri yana tunanin to kuma waye yanzun, k'arar rufe k'ofofin motar yaji ba'a yi seconds goma ba sai ga wani mutum zabgege bak'i cikin suit ash ya saka wani sun glasses a fuskar sa tare da wad'annan mazajen da suka je suka binne gawar Ra'es d'azu tare dasu. Zuciyar Fawaz ta shiga harbawa gbam gbam yayin da suke k'arasa shigowa cikin parlor'n, wanda yake cikin suit d'in ne ya fara zaunawa had'i da crossing k'afafu d'aya bayan d'aya suma sauran suka zauna. Cire glasses d'in fuskar sa mutumin yayi yayin da criminal face d'insa ta bayyana sai murmushi yake yayi wa Fawaz alama da sofar dake bayan sa yace

"Zauna mana Fawaz." Fawaz ya gama tsinkewa da al'amarin ya samu wuri kawai ya zauna a zuciyar sa kuma ji yake ya tab'a jin irin muryar wannan mutumin, kallon Fawaz mutumin yake yace "Mr. Shattima my name is Cheetah." gaban Fawaz ya bala'in rikitowa ya fad'i sannan mutumin ya saki murmushi yace "We kidnapped Afeefah Jalal." zumbur Fawaz ya mik'e ya nufi mutumin yaci kwalar sa cikin d'aga murya yace

"You bastard! You.." ji kawai yayi an saita bindiga a kansa had'i da pulling trigger ready to shoot, tsayawa yayi cak motionless saboda tsabar firgita abunda yake gani a films yau shine yake shirin faruwa a kansa, d'aya daga cikin yaran Cheetah ne ya saita bindigar a kansa cikin husky voice nasa yace

"Keep your goddamn voice down or else this gun will blow your head to pieces." Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un kawai Fawaz ke maimaitawa yanzu kam ya tabbatar he's in a jam ya rigaya da ya fad'a tarkon wad'annan mutanen, chan ya tsinto muryar mutumin yace "Now get seated." komawa Fawaz yayi ya zauna kamar gunki yayin da mutumin ya raka sa da bindigar har sai da yaga ya zauna sannan shima ya koma ya zauna. Murmushi Cheetah yayi yace

"Fawaz ka cika k'iriniya.." yana fad'a yana wani shu'umin murmushi wanda Fawaz ya kasa gane ma'anar sa sannan ya k'ara da cewa "Kamar yadda na gaya maka mune nan muka sace Afeefah kuma tana hannun mu yanzu haka kuma zamu iya salwan ta rayuwar ta idan har baka yi abunda zamu gaya maka ba." rintse ido Fawaz yayi hawaye masu zafi suka zubo masa zuciyar sa sai zafi take masa, jawo wata briefcase Cheetah yayi daga gefen sa ya fara zipping d'inta yace "It's two trap Mr. Shattima" sannan ya bud'e jakar ya fiddo da wasu hotu na guda uku ya watsa su a gaban Fawaz yace "I believe with this pictures you are sunk." jiki na rawa Fawaz ya tattaro hotunan da Cheetah ya watso masa nan take ya mik'e zumbur hankalin sa da ya tashi yanzu yayi doubling, hotunan sa ne ya gani lokacin da yayi fad'a da Ra'es da lokacin da ya shak'e sa ya zubar k'asa da lokacin da yake digging rami while gawar Ra'es na kwance a gefen ramin ya fahimci wato duka tarko ne suka dasa masa kuma duk sunyi nasara, zufa ce ta shiga karyowa Fawaz bakin sa na rawa yace

"For God sake!.. How could you do this? How could you? Me nayi muku haka?" dariya Cheetah yayi yace "Dalilin da yasa na nuna maka wannan hotunan shine kada ka damu da neman kariyar hukuma, the second ka kai maganar nan ga 'yan sanda to ni kuma zanyi publicizing hotunan nan and the police will come after you kuma ba wanda ya isa ya hana kaje gidan yari har k'arshen rayuwar ka idan har ba a kashe ka ba kenan." a halin yanzu hankalin Fawaz ni kaina ba zan iya cewa ga iyakar d'aguwar da yayi ba, cikin rawar murya yace

"Suppose I don't take orders from you then what?" dariya dukansu su uku suka fashe sannan d'aya daga cikin yaran na Cheetah yace

"Then you are up to your neck in trouble Fawaz. Na lura baka san ko waye Cheetah ba. Cheetah ya fice dukka tunanin ka baya fara business sai yayi lissafi mai zurfi I'm not kidding Fawaz, Cheetah is poison! If Cheetah asks you to do something, then goddamn it you must do it you just don't fool with Cheetah 'cause what he says goes." dariya Cheetah yayi had'i da resting kansa akan kujera yace

"Double cross me Fawaz and I guarantee you that it's the last double cross you will pull." yanzu kam Fawaz ya bayar da gari zaune kawai yake yana kallon su kamar kurma sai da aka shafe minti ashirin ba mai magana daga cikin su sannan Fawaz yayi k'arfin hali yace "Yanzu me kuke so daga wuri na?" "Dama kana da irin wannan tambayar kai ta b'ata mana lokaci Fawaz?" cewar Cheetah sannan ya gyara zaman sa yace "Muna son karb'ar kud'i a matsayin ransom daga mahaifin Afeefah and your voice will be the threatening voice on the phone kai zaka yi mana magana dashi kaine zaka gaya masa terms and conditions namu." sannan ya dakata had'i da jan numfashi ya cigaba da cewa "Idan kuma kace ba zaka bamu had'in kai ba to ba zanyi forcing d'inka ba sai dai zan koma in kashe Afeefah da hannu na in kuma yi publicizing hotunan nan a matsayin kaine ka kashe Ra'es."

"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" Fawaz ya fad'a a fili jikin sa sai rawa yake wane mazari yana cikin haka yaji Cheetah yace

"Zab'i ya rage naka but to me, it's better to be in kidnap case than being in murder case and losing the love of your life." idanun Fawaz sun yi jajir saboda tsabar tashin hankali, cikin wata murya ta daban yace "Mesa kuke so ku k'ak'aba min laifin da banji ba ban gani ba? Me nayi muku haka? Me Afeefah tayi muku?" dariya Cheetah yayi yace "This is what we call business! Dole sai na samu wannan kud'in Fawaz! Dole!" sannan yayi shiru na second biyar haka sannan ya cigaba da cewa "If everything works out I'll have thirty millions on it and I don't intend to lose thirty millions just because of you so me kace?"

"Zanyi shawara." Fawaz ya amsa masa calmly, dariya Cheetah yayi yace "Kana so kayi wasa dani ko Fawaz? Nayi maka kama da d'an jeka ka dawo?" wannan shi ake cewa tsaka mai wuya idan har ya yarda yayi magana da mahaifin Afeefah bai kuma san abunda zai biyo baya ba amma yafi so yayi sacrificing rayuwar sa idan har wannan zai sa Afeefah ta cigaba da rayuwa, cikin kwantar da murya yace "I'm in." murmushi suka saki dukansu Cheetah yace

"Good boy" sannan ya sake fiddo wata takarda daga cikin briefcase d'insa wacce ke dauke da rubutu mai d'an tsayi ya rik'e ta a hannun sa yace "Wannan sune maganganun da zaka gaya masa ga number wayar sa nan a k'asa." sannan ya mik'a wa Fawaz takardar ya cigaba da cewa "Ka saurare ni da kyau Fawaz kada ka kuskure daga abunda yake a cikin takardar nan abunda yake ciki shi zaka fad'a kadda ka kuskura ka k'ara ko alif a sama don't try to act smart..." a hankali yasa hannu ya ciro bindiga daga k'ugun sa yace "The unexpected has always to be taken into consideration wallahi da kayi ba daidai ba zan fasa kanka da bullet just don't dig your own grave do what you are asked to." shiru Fawaz yayi yana sauraren sa lokaci d'aya yana karanta abunda yake a cikin takardar, sai da ya karance ta tsaf sannan Cheetah yace "You have to be careful and confident idan zaka fara magana dashi.. Karka yarda ka basa damar da zai fad'i koda kalma d'aya I don't have to tell you what to say make it raw and crude and the second ka gama fad'ar abunda zaka fad'a ka katse kiran ka fahimta?" jinjina kai Fawaz yayi alamar ya fahimta sannan Cheetah ya juya zuwa ga yaran sa ya musu magana da ido, dukansu mik'ewa tsaye suka yi suka fiddo bindigogi daga jikin su suka taka suka isa wurin Fawaz suka saita bindigogin a kansa sannan Cheetah yace "Now.." kallon sa Fawaz yayi a diririce yace

"Da wacce wayar zan kira sa?" "Wayar ka." Cheetah ya amsa masa, rintse ido Fawaz yayi ya d'auko wayar sa ya kwafe number mahaifin Afeefah dake jikin takardar zuwa wayar sa hannun sa sai rawa yake a hankali ya danna kira had'i da saka call d'in a loudspeaker, k'ara kusanto da bindigogin suka yi daf da kansa shima Cheetah ya fiddo tasa bindigar ya rik'e yayin da wayar mahaifin Afeefah sai ringing take.

*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*28*

Zaune suke su uku dukansu sun rafka tagumi damuwa ta bayyana a fuskar su. K'arfin hali Umma tayi cike da damuwa fuskar ta tace "Daddy'n Afeefah wai haka zamu zauna jiran tsammani? Yau fa kusan kwana biyar ba Afeefah ba labarin ta amma..." sai kuka yaci k'arfin ta kuma, saukar da ajiyar zuciya Daddy yayi yace "Me kike so nayi? Inace duk abunda ya dace nayi nayi. Na bayar da cigiyar ta wa jami'an tsaro ina ce abunda ya rage shine mu cigaba da jira da kuma addu'a ta yiwu ma Afeefah ba b'ata tayi ba tana wurin samarin ta ne." kuka kawai Umma keyi wanda a halin da ake ciki ya zame mata tamkar abinci, tun lokacin da suka nemi Afeefah suka rasa suke cikin matsanancin tashin hankali da damuwa. Wayar Daddy ce tayi k'ara jiki a sanyaye ya d'auko wayar ya duba yaga bak'uwar number ce, kamar yayi biris da kiran sai kuma wata zuciya tace ya d'aga yaji ta yiwu wani abu ne dangane da Afeefah, sliding kawai yayi ya saka a kunne a inda muryar Fawaz ta fara magana

"Ka saurare ni da kyau, mun yi garkuwa da 'yar ka Afeefah yanzu haka tana a hannun mu ka fahimta? The ransom is thirty million naira and it's non-negotiable. Idan har baka biya wannan kudin ba a tsakanin awoyin da muka d'ibar maka to ba zaka sake saka ta a ido ba that's a promise. Kada ka kuskura ka sanyo 'yan sanda ko wasu jami'an tsaro or any other trick a ciki this is a snatch do you get it? Idan har kana so ka sake ganin 'yar ka then you are to do what I'm telling you. Get the money ready by tomorrow, zan sake kiran ka goben and you'll get instructions on where you will deliver the ransom and the sooner you get the money, the better for your daughter. Ina sake gargad'in ka da kada ka kuskura ka sako jami'an tsaro a cikin wannan al'amarin idan kayi kunnen uwar shegu to zaka tsinci gawar ta ne kuma sai na tabbatar yara na sun gama abunda zasu yi da ita." yana kaiwa nan ya katse kiran. Mutuwar tsaye Daddy yayi wayar ta sulale daga hannun sa, Umma wacce ke zaune a kan kujera bata san lokacin da ta mik'e tsaye jiki na rawa a rikice ta nufi wurin da yake zaune tace

"Daddy'n Afeefah me yake faruwa ne?" shima mik'ewa tsaye yayi jikin sa sai b'ari yake yace "Masu garkuwa da mutane sunyi garkuwa da Afeefah suna bukatar thirty million zuwa gobe kafin su sake ta." sulalewa Umma tayi zuwa k'asa tana karanto Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un haka ma Aunty Nana, kallon su yayi cike da firgici da tashin hankali yace "Kada ku kuskura ku fidda wannan maganar, kar ku bari kowa yaji abunda ake ciki idan ba haka ba rayuwar Afeefah zaku saka a cikin had'ari, zanje inyi kokarin fitar masu da kud'in kafin gobe." yana k'are fad'ar haka ya suri keys kawai ba tare da ya k'ara ce dasu uffan ba cikin sauri ya fice daga parlor'n. Tafe yake cikin harabar tangamemen gidan sai tafiya yake har ya kawo wurin motar sa a nan ya d'aga waya ya kira babban aminin sa ya shaida masa anyi kidnapping Afeefah kuma ana bukatar miliyan talatin a matsayin musaya da ita, kasancewar dare ne bai lura da wani yaron gidan sa ba dake tsaye a wurin kuma yaji duk maganganun da yayi a waya, shiga motar sa kawai yayi ya fizge ta ya bar gidan.

Fitar sa kamar da minti uku motar DSP Abdulrashid Ibrahim daga Police headquarters ta danno kai cikin gidan. Tafe yake har yazo daidai tsakiyar gidan yayi parking ya fito daga motar yana k'arewa gidan kallo. Hango yaron gidan yayi daga nesa yana zuwa yayi masa alama da hannu alamar yazo, ba tare da gardama ba yaron yazo suka gaisa DSP Abdulrashid ya zarce da cewa

"Please shiga ka sanar da Jalal gani nazo." kallon sa yaron yayi yace "Oga baya nan ya fita." "Ban gane baya nan ba, yanzu fa muka yi waya dashi nace masa zanzo in same shi." "Ranka ya dad'e ya fita fa." mamaki ya kama Abdulrashid ya gyara tsayuwar sa yace

"Ok shiga ka nemar min iso wurin iyalin sa." ba tare da gardama ba yaron ya juya ya nufi ciki within some minutes ya dawo ya shaida masa Hajiya tana parlor'n k'asa, godiya DSP ya masa ya nufi parlor'n. Umma ya tarar zaune a cikin parlor'n sai sharb'ar kuka take, jikin sa yayi sanyi matuk'a suka gaisa sama-sama sai kuka take ya tambaye ta mijin ta ta shaida masa baya nan kamar yadda yaron ya shaida masa, neman sanin ina yaje yayi sai dai ya lura Umma akwai abunda take b'oye masa daga k'arshe ma tace masa bata san ina yaje ba. Yayi jim lokacin da ta gaya masa maganar sam jikin sa bai amince ba saboda bai dad'e da waya da mahaifin Afeefah ba ya shaida masa zai zo yanzu su gana game da b'atan Afeefah sai dai yazo bai tarar dashi ba, abu na biyu kuma ya lura akwai kokwanto a cikin maganganun Umma. Godiya yai mata had'i da addu'ar Allah ya bayyana Afeefah sannan ya mata sallama ya fita. Koda ya fito ya fara waige-waige dama da hagun sa sai ga yaron ya hanga yana shigowa gidan, takawa yayi ya isa wurin yaron yace

"Dan Allah ko kana da masaniyar ina Jalal ya tafi?" shiru yaron yayi na tsawon mintuna sannan yace "Ya fita." "Nasan ya fita, ina yaje?" shiru yaron ya sake yi sannan ya kalli dama da hagun sa cikin tsoro, lura da yanayin sa d'an sandan yayi yayi murmushi ya tabbatar da akwai wani abu da yake faruwa ko kuma ma ya rigaya da ya faru, dafa kafad'ar yaron yayi yace "Ka kwantar da hankalin ka ni d'an sanda ne kawai ina buk'atar sanin ina Jalal yaje saboda minti kamar ashirin da suka wuce nayi waya dashi har ya nemi gani na domin mu gana dangane da b'atan Afeefah sai dai kuma gashi nazo ban same shi ba, nayi kokarin tambayar iyalin sa sai dai na lura kamar akwai wani abu da take kokarin boyewa, kaima kuma na lura da haka amma abunda nike so ka sani shine ni d'an sanda ne wanda ya dad'e a cikin wannan aikin, I can smell trouble a mile off and I'm smelling it now kawai ka sanar dani idan har kasan wacce fitar gaggawa ce ta fitar da Jalal a cikin daren nan." ajiyar zuciya yaron yayi sannan yace

"To nima dai gaskiya bansani ba amma naji yana waya yana fad'ar anyi garkuwa da Afeefah." kallon sa Abdulrashid yayi da kyau yace "Ka tabbatar da haka?" "Na tabbata ranka ya dad'e." jinjina kai Abdulrashid yayi ya mik'a masa hannu suka gaisa ya masa godiya sannan ya juya ya nufi motar sa. Yana shiga ya bud'e wayar sa ya danna kiran number Daddy ya saka a kunne, ringing d'aya a na biyu ya d'aga Abdulrashid yace

"Assalamu alaikum ranka ya dad'e." "Wa alaika salam Abdulrashid kayi hak'uri fa wallahi wata fitar gaggawa ta kama ni yanzun nan sai dai gobe in shaa Allah zanyi kokari mu had'u." saurarar sa Abdulrashid keyi kawai tabbas akwai k'amshin gaskiya a cikin maganar da yaron ya gaya masa saboda ga baki d'aya ya lura hankalin Daddy a tashe yake, kwantar da murya Abdulrashid yayi yace

"Ranka ya dad'e ina kaje ne da daren nan? Ya dace fa mu tattauna saboda samun sanin ta ina zamu b'ullowa al'amarin b'atan yarinyar nan." "Karka damu Officer, in shaa Allah gobe zan kira ka karka damu." d'an jim Abdulrashid yayi sannan yace

"To ba matsala ranka ya dad'e Allah Ya kaimu goben." "Ameen Abdulrashid." cewar Daddy sannan ya katse kiran, reverse Abdulrashid yayi da motar sa ya ja ya bar gidan. Sai da ya hau titi sosai ya d'aga waya ya kira shugaban sa a Headquarters yace "Sir game da case na b'atan 'yar Jalal Magayaki."

"Yes ina sauraren ka." ya amsa daga d'aya bangaren "It looks as if the girl has been kidnapped saboda Jalal ya nemi ya ganni da kansa a gidan sa kamar minti talatin da suka wuce sai dai naje gidan aka sanar dani ya fita, na tambayi matar sa ina yaje sai dai na lura akwai abunda take boyewa kamar bata so ta sanar dani, da na fito na tambayi wani servant d'in gidan anan ne yake sanar dani yaji Jalal yana waya yana fad'ar anyi garkuwa da yarinyar na kira Jalal d'in don sanin ina yaje shima sai yayi kokarin boye min ya sanar dani fitar gaggawa ce kawai."

"Good job Abdulrashid!" sannan ya zarce da cewa "Matsalar da muke fuskanta a yanzu shine iyayen yara idan aka yi garkuwa da 'ya 'yan su they can't consult us saboda kidnappers d' in zasu gargad'e su akan the moment aka kai maganar ga hukuma to tabbas zasu kashe yaron sai idan sun bayar da kud'in ba'a maido masu da yaron ba sannan zasu yi report but ban ga laifin sa ba saboda kidnappers are the most vicious type of criminals we know amma kasan abunda za'a yi yanzu?"

"A'a" Abdulrashid ya amsa "Har yanzu dai bamu tabbatar da sahihancin labarin ba but still I'm going to make an arrangement with all the bank managers to report sudden withdrawals for any large amount of money daga yau zuwa gobe idan har aka samu kuma ya nuna Jalal Magayak'i ne then definitely the money is for the ransom demand daga nan kuma sai musan miye next move. " "It's a good idea sir." cewar Abdulrashid da haka suka ajiye wayar.

*Washegari* _9:00am_ Babban d'an sandan ne ke fitowa daga cikin building d'in trying to make it to the parking lot sai ga Abdulrashid, gaisawa suka yi d'an sandan ya zarce da cewa

"Jiya da dare as soon as I hanged your call na kira all the bank managers na gaya musu arrangement d'in luckily manager na First Bank ya shaida min Jalal Magayak'i ya kira sa a wannan daren ya sanar masa a bud'e bankin a tanadar masa miliyan talatin kafin gobe da safe, manager'n yayi k'ok'arin nuna masa dare yayi wannan lokacin amma duk da haka Jalal ya cigaba da insisting neman kudin a yau da sassafe and considering Jalal shine babban client na First Bank yasa manager'n ya karb'a masa not knowing what is really going on." shiru Abdulrashid yayi yana nazari sannan d'an sandan ya cigaba da cewa "Har yanzu dai ba abunda zamu iya yi har sai Jalal ya sako mu a cikin wannan al'amarin but kafin nan I'll appoint one of our boys to keep a closed eye as soon as Jalal gets the money from the bank sai yayi reporting a office." jinjina kai Abdulrahman yayi alamar ya gamsu sannan yace

"Excuse me sir just an idea, kamar yadda kace we shall keep a closed eye as soon as he collect the money, sir idan har ya karb'i kudin why not we follow him secretly?" girgiza kai d'an sandan yayi lokaci d'aya yana murmushi yace

"Abunda ba zamu yi ba kenan but suppose we followed him and along the way kidnappers d'in suka fahimci cewa muna tare dashi zasu dauka shi ya kira mu ne kuma zasu iya kashe yarinyar me aka yi kenan? Kaga ba'a yi komai ba" sannan ya bubbuga kafad'ar Abdulrahman yace "Kar ka damu I've talked to the IG on this and his response was we are not to take any action until Jalal calls us in but zamu cigaba da bibiyar sa at least we'll be able to know the moves." jinjina kai Abdulrashid yayi yace

"Yes sir" had'i da sare masa.

*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *May, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*29*

Daddy yana samun karb'ar kud'in ba da dad'ewa ba kiran Fawaz ya sake shigowa wayar sa a karo na biyu, jikin sa har yana rawa ya d'aga kiran a inda ya jiyo muryar Fawaz na cewa

"Have you got the money?" "Yes." Daddy ya amsa masa calmly

"Good here is what you are going to do." cewar Fawaz shima cikin sanyin murya da rashin k'warin gwiwa "Ka bar gidan ka wuraren k'arfe goma na dare zuwa k'auyen Gwagwalada, along the way akwai wani daji which is 15km away da wata hanya da ta yanka cikin dajin, ka bi hanyar straight and again somewhere along you'll see a flashing light kada ka tsaya idan kaga flash d'in har sai kayi nisa sannan ka fiddo kud'in ta window kayi dropping. As you dropped the money nan ma kada ka tsaya har sai kayi tafiyar ak'alla minti biyar sannan kayi corner ka sake dawowa ka fita dajin but mind you you'll be watched as soon as you leave your house. If the money is okay and you don't try to act smart, then expect your daughter around three o'clock in the morning ka fahimta?"

"Na fahimta." Daddy ya sake amsa masa calmly nan take kuma aka katse kiran. A haka cikin kasala da sanyin jiki Daddy ya ja motar ya nufi gida had'i da fayyace ma iyalan sa duk abunda ake ciki. Umma da Aunty Nana sun sha kuka har sun godewa Allah da haka cikin jimami suka zauna zaman jiran k'arfe goma na dare.

_10:00pm_ Kamar yadda suka basa ka'idojin haka ya bi, tun kan k'arfe goman ya kama hanya k'arfe goman ta riske sa a dajin. Duk yadda aka tsara masa a waya hakan ta kasance ya ga flashing light d'in kamar yadda aka gaya masa sai dai bai ga ko waye ba sakamakon ya b'oye a cikin duhun ciyayi da kuma duhun dare. Yana wucewa kuma ya saukar da glass d'in motar sa kamar yadda aka umurce sa ya d'auko briefcase d'in ya jefar a k'asa sannan ya nausa. Yayi tafiyar kamar yadda aka buk'ace sa sannan yayo corner ya dawo ya kama hanyar ficewa daga dajin. Tafe yake amma ya cika da matuk'ar farin ciki sakamakon Allah ya taimake sa ya cika dukka sharudd'an da suka bayar da kuma farin cikin cikin 'yan awoyi zai ga 'yar sa. Bayan ya iso gida ya fayyace musu duk abunda ake ciki kuma ya zuba securities d'in gidan sa round the area koda zasu ga dawowar Afeefah. Haka suka zauna zaman jiran ta har k'arfe uku na dare kamar yadda kidnappers d'in suka tabbata masa wanda a wurin su ya zama tamkar jiran shekaru. Har k'arfe uku na dare ba Afeefah ba alamar ta shi da kansa ya dinga shiga da fice tare da securities a cikin daren amma ko alamar Afeefah babu. Nan fa hankali ya sake d'aguwa sakamakon har asuba na kunno kai amma ba Afeefah ba labarin ta shiru. Zazzaune suke a cikin parlor'n Umma da Aunty Nana sai rizgar kuka suke yayin da Daddy ya buga tagumi yana tunani, rasa mafita yayi finally ya d'aga waya ya kira IG ya zayyana masa duk abunda ake ciki IG ya d'aukar masa alk'awalin tunda sassafe yaran su zasu zo and investigation is going to start har sai lokacin da aka gano Afeefah had'i da kwantar masa da hankali da haka suka zauna har gari ya waye.

Tunda sassafe Abdulrashid da mai gidan sa da kuma wasu daga cikin manyan 'yan sanda suka dira a gidan as instructed from the headquarters, bayan sun zauna a cikin parlor'n kowa ya nutsa babban d'an sandan yace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull