Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 12

Abokaina complete book 1 - Chapter 12

Abokaina complete book 1 Chapter 12: Abokaina complete book 1 Chapter 12. "Ku wine ya dama." sannan ya mik'e ya fice, dariya suka fashe at once Foxy yace…

4,313 words

"Ku wine ya dama." sannan ya mik'e ya fice, dariya suka fashe at once Foxy yace "Wata ja'ira irin shi ta gama dashi." da haka Fawaz ya shiga d'akin Faruk ya samo masu wine kala daban daban suka shiga korawa har sai da suka bugu sosai a yinin ranar dai sam basu fahimci kan Faruk ba.

Washegari wuraren k'arfe takwas na safe Fawaz da Foxy duka suka shirya lokaci d'aya sakamakon ranar dukansu suna da exam a inda Foxy zai rubuta exam d'insa ta k'arshe a wannan semester kuma da ya gama zai wuce KD shi kuma Fawaz saura biyu ya k'ark'are so yana a Abuja har zuwa lokacin da zai kammala. Suna fitowa suka yi kicib'is da Faruk ya janyo wani akwati yana kokarin fitowa dashi daga d'akin sa, dukansu mamaki ne ya kama su suka tsaya suna kallon sa har ya fito ya gansu tsaye suna kallon sa "Fak ya haka ne?" cewar Foxy sai kallo yake binsa dashi

"Tafiya zanyi." ya fad'a yana zura hannayen sa cikin aljihun jeans d'insa "Ina zaka je and exams d'inka da baka k'ark'are ba fa?" Fawaz ya tambaya wanda kansa ya gama d'aurewa, takowa yayi yazo gabansu yace "I've got to make money in anyway so saboda haka zanje Lagos where the money is... Big money Fawaz, not little stuff." "Lagos kuma?" Fawaz ya tambaya sounding weird "Idan kaje Lagos an gaya maka haka kawai zaka samu kud'i?" matsowa Foxy yayi yace

"Me ka sha jiya da dare? Didn't I tell you to stop taking Brewdog? Haukacewa zaka yi wallahi d'an iska kawai!" dariya Fak yayi yace "I'm not joking, da gaske nike wallahi." "Exam dinka fa? Uban wa ka bari da zai k'ark'are maka?" cewar Foxy, murmushi yayi yace "I can carry it over next year ba wani abu bane." "Idan ka tafi kuma sai yaushe?" "Ga waya, I'll holla at you mana." girgiza kai Fawaz yayi yace "Su Baba sun san da wannan tafiyar?" grinning Fak yayi sannan yace

"Nobody knows except my homies." furzar da iska Fawaz yayi shi kam hankalin sa ko kad'an bai kwanta da wannan tafiyar ta Faruk ba ajiyar zuciya yayi yace "Fak suppose something happened... Suppose you have an accident.. Suppose something terrible happened along the way how.." "I'm not going to get an accident and nothing terrible is going to happen so wish me luck and safe trip kawai." "Muje Fizzy kadda muyi latti ka daina damuwa da wannan shegen dawowa zai yi yanzu ma baya cikin hankalin sa ne." cewar Foxy, da haka dai suka yi sallama da Faruk sannan suka fice, yana tabbatar da sun fita gidan ya kira wayar Zuhra ringing biyu ta d'aga had'i da cewa "Is that a YES?"

"Yes! I'm in." Faruk ya amsa.

*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*25*

Bayan Fawaz ya fito daga exam room yana tafiya trying to make it to the parking lot kiran Foxy ya shigo wayar sa yake gaya masa ya fito exam kuma ya d'au hanyar Kaduna, fatar Allah ya kiyaye Fawaz yai masa suka rabu akan shima in the next few days zaya shigo sannan suka ajiye wayar kamar daga sama yaga Afeefah a gaban sa, duk da cewa he is trying to get over her amma sai da gaban sa ya fad'i da ya ganta saboda ramar da tayi, ja da baya ya shiga yi yana girgiza kai he hates to recall ba budurci a tare da ita and it was taken away by his best friend. Hawaye suka zubo mata cikin rawar murya tace "Oldie tsoro na kake?" cigaba da ja baya yayi ita kuma tana k'ara matso sa daga k'arshe har yana had'awa da gudu ya nufi parking lot, binsa tayi ta sha gaban sa daidai zai bud'e motar sa, kawar da kansa yayi yace

"Afeefah ki tafi please." yana fad'a yana rintse ido yana ja da baya, muryar ta sai rawa take da wani crack mai ban tausayi a ciki tace "Oldie tsoro na kake?" bud'e ido yayi ya watsa mata kallon tsana yace "Yes because I have some decency left in me! You Afeefah! You have nothing! You're rotten through and through!" rintse ido tayi yadda kalaman da yake watsa mata suka zame mata kamar wuta, nuna mata hanya yayi da hannu yace "Ki tafi please bana san ganin ki." bud'e idanun ta tayi tace "Fawaz ni ba karuwa bace wallahi kana tunanin if I stay with Foxy I can stay with any rat right?" sannan ta girgiza kai hawaye masu zafi da d'aci suka zubo mata tace "I thought you will be a good friend of mine that we will be sharing feelings, pains and gains." ta cigaba da sobbing heavily tace "Gaskiya ne sometimes you need a little push to recognize yourself. Zan tafi Fawaz kuma ba zan k'ara neman ka ba in shaa Allah but I hope idan labarin mutuwa ta ya riske ka you'll be able to live with the burden of risking a girl's life just because you are too proud to forgive and forget her flaws." tana kai nan ta juya zata tafi, rik'o gelen ta Fawaz yayi sai kuka take ya zagayo gaban ta yasa hannu ya d'ago hab'ar ta yace

"You are not leaving your Oldie Afeefah.. I won't let it happen." kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi a hankali ya ja hannun ta ya bud'e mata motar ta shiga ta zauna sannan ya zagaya ya shiga gefen driver had'i da rufewa har yanzu sai kukan take, cikin kwantar da murya yace "I'm so sorry Afeefah.. I know I wasn't just with you.. I shouldn't act the the way I acted but I had no any alternative rather than to shout and yell at you... I was soo broken, jealous, upset, mad, angry, embarrassed and everything Afeefah." kuka mai zafi cike da nadama da dana sani ta shiga yi, shima idanun sa suka ciko da hawaye a hankali ya rik'o hannun ta muryar sa na rawa yace "Afeefah" d'ago kai tayi idanun ta sunyi jajir yace "I love you.." katse sa tayi sai sheshsheka take tace

"Oldie.." "I love you so much Afeefah and I'm not leaving..." "Oldie..." ta sake fad'a idanun ta sai ambaliyar hawaye suke, share mata hawayen ya shiga yi yace "I'm not leaving Afeefah.. Not now.. Not ever.. Please stop all the negative thoughts about us kinji?" yanzu kam kuka ta fashe dashi sosai a hankali yace "Come here." had'i da bude hannayen sa kad'an, fad'awa tayi cikin k'irjin sa ta hugging d'insa gam tana rusa kuka tana dukan sa sai da ta gaji da dukan nasa sannan ta cigaba da kukan at the same time tana ajiyar zuciya shi kam Fawaz tun lokacin da jikin ta ya had'u da nasa wani irin mysterious chemistry ne ya fara faruwa dashi wanda up till date ba wani chemist da ya tab'a bayanin shi but being him an engineering man he said it is a fusion (Lol). D'ago kanta yayi suna kallon juna yace "Ba kince your kids are gonna be best friends with my kids ba?" nan take ta fashe da dariya tana d'aga kai alamar eh, shima yayi dariya yace "Fine! Let's continue what we started please." cikin lokaci kad'an sai gashi suna fara'a da annashuwa kamar ba su ba, sun dad'e suna hira har lokacin shigar ta exam yayi sannan suka rabu ya nufi gida. Koda ya dawo gidan ba kowa kewar abokan nasa sai yanzu tafi damun sa ya rasa ma abinda zai yi haka yazo parlor ya fara kallon ball tsakanin Man Utd vs Arsenal sai dai the ball is boring 'cause duk ranar da ake kallon ball tare suke kallon ta su uku. Fitowa yayi harabar gidan sai safa da marwa yake daga k'arshe dai ya koma parlor ya samu wine ya shiga korawa. Sai da yayi tatil da giyar sannan ya tuna once bacci ya kwashe sa yanzu ya tashi daga baccin anjima toabu na farko da zai nema abinci ne 'cause da wata mahaukaciyar yunwa zai tashi, as soon as wannan tunanin yazo kansa keys kawai ya sura ya nufi d'akin sa ya cire kayan jikin sa zuwa three quarter fari da killer shirt sannan ya fito ya shiga motar sa don nemowa kansa abunda zai ci. Tafiya yake but honestly bai san ina ya nufa ba kawai dai driving yake saboda giyar ta fara bugun sa, tafiya yake motar sai tangal tangal take kan titin Allah dai kawai ke karewa sai ganin sa yayi kamar ya kama hanyar fita garin Abuja yana cikin tafiyar ya kawo wani daji haka sai ji yayi wata mota ta buge sa a baya, da k'yar ya iya samun damar dakatar da tasa motar ya fara kokarin fitowa don ganin wanne mahaukacin ne ya buge sa a baya, wani saurayin ne mai irin shekarun sa ya gani ya fito daga wata Jeep fara ya nufo sa da masifa yana cewa

"Kai wanne irin mahaukaci ne ya zaka d'auko mota ka fito gari kana tuk'i idan kasan baka k'ware ba kusan sau uku kana neman had'a accident a baya." Fawaz dai kallon saurayin yake idanun sa sai rufewa da budewa suke yayin da saurayin ya kawo daf dashi, Fawaz da ko tsayuwar kirki ya kasa yi sai cewa yayi

"Listen, don't talk to me like I'm some kid." dariya saurayin yayi yace "Oh really? Fine!" kawai ya d'aga hannu zai kai masa duka, duk da cewa Fawaz baya cikin hankalin sa kuma baya da wani kuzari sosai amma yadda ya rik'e hannun saurayin shima saurayin sai da yayi mamaki ya fara kokarin kufcewa daga rik'on da Fawaz ya masa amma ya kasa, murd'e hannun Fawaz yayi nan take saurayin ya kwalla kururuwa ya zube zuwa k'asa yayin da saurayin yasa k'afa ya daki Fawaz a k'afa sai gashi a k'asa kasancewar baya da balance sosai. Kokarin mikewa suka yi lokaci d'aya saurayin ya sake nufar kan Fawaz da wata masifar, shak'e wuyan sa Fawaz yayi tam sai da yaji yana neman dauke wuta sannan ya jefar dashi shi kuwa sai jin wannan kyakkyawan duka yayi da k'arfe ta bayan sa tun lokacin bai sake sanin inda kansa yake ba.

*So sai ana hakuri dani these days saboda rashin samun post frequently trynna keep up with school struggles and soon zan dakata sai after Ramadan in shaa Allah.*

*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*26*

A hankali ya fara bud'e nannauyan idanuwan sa wanda suka masa masifar nauyi, idanun sa suka fara sauka kan rubber ceiling dake d'akin ya karkata kansa dama da hagu kad'an ya fahimci lallai d'akin sa ne yake ciki. Yunk'urin tashi zaune yayi sai dai ba shiri ya koma ya kwanta sakamakon wani azababben ciwo da yaji kansa yana yi. Dafe kan yayi a nan ne ya ji alamar bandage d'aure a kan nasa, da k'yar da sud'in goshi had'i da k'arfin hali ya samu ya sauko daga kan gadon sai layi yake yana dafe da kansa wanda kamar dukan sa ake da guduma, wurin dressing mirror ya nufa yana layi saboda yadda k'afafun suma suka yi nauyi. Gaban sa ne yayi mummunar fad'uwa lokacin da ya tsayu gaban madibin yaga kansa d'aure da bandage fuskar sa kuma da alamar raunuka, kokarin tuna abunda ya faru dashi last yayi amma ya kasa sakamakon azababben ciwon da kan nasa ke masa. Zaunawa yayi bakin gadon har na tsawon minti talatin yana zaune dafe da kan nasa daga k'arshe ya mik'e ya ja k'afafun nasa ya nufi bathroom. Nan ma kasa tab'uka komai yayi ya zauna kan toilet seat ya cigaba da dafe kansa, attempting tuna abunda ya faru dashi last yayi duk kuwa da cewa kan nasa ciwo yake amma haka ya cije ya cigaba da tunanin.

Cikin azabar ciwon kai ya fara tuna abunda ya faru dashi; ya dawo gida ne daga makaranta ya kwankad'i wine d'insa sai kuma ya ji zai bukaci abinci the second wine d'in ta sake sa, ya d'auki keys d'in motar sa ya fita sai tuk'i yake loosely kan hanya sai ji yayi an dake sa da mota a baya nan take yayi hanzarin yin parking ya fito ya had'u da wani matashin saurayi, a nan suka d'an yi rigima da gayen har ya bar sa kwance shima sai jin duka yayi a kansa tun daga lokacin bai k'ara sanin me ya faru dashi ba. D'ago kansa yayi yayi sharkaf da zufa tambayar da ya fara yiwa kansa shine waye ya kawo sa gida har da bandage a kansa? Shiru yayi zufa sai keto masa take ta ko ina a hankali ya mik'e ya zubawa jikin sa ruwa ya fito ya kwanta kan gado don cigaba da kad'aituwa da zuciyar sa, ringing d'in wayar sa wacce tun da ya farka baccin sam bai lura da ita ba yaji a hankali yasa hannu ya d'auko ta yaga Foxy ne ke kira, sliding yayi ya saka a kunne yaji Foxy yace

"Wai ina ka saka wayar ne yau sati d'aya cif ina kiran ka baya zuwa." dumm gaban Fawaz ya yanke ya fad'i cikin sark'ewar murya yace "Kace mene Foxy? Sati d'aya kana kira na baya zuwa?" "Eh mana tun ranar da na iso KD I've been trying to reach you in gaya maka na iso gida but wayar a kashe." Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un abunda Fawaz ya maimaita a ransa kenan saboda ya fahimci ba jiya ne abun ya faru ba he has been in coma for a week, kokarin b'oyewa Foxy gaskiyar lamarin yayi yace "Oh sorry gaskiya ne na cire wannan layin ina amfani da wani ban ma dad'e da saka wannan ba ka kira."

"I for say." cewar Foxy sannan ya zarce da cewa "So ya exams d'in naka? Ba since three days back kace min zaka k'ark'are ba? Me kuma ya zaunar da kai?" nan ma gaban Fawaz ya yanke ya fad'i recalling exams d'in da suka zaunar dashi Abuja ma har anyi su bai sani ba, nan ma wata k'aryar yayi wa Foxy yace

"Yeah na gama ai since that day akwai wani seminar ne da zamu yi shine ya zaunar dani but da na gama zan hawo hanya in shaa Allah." "Yaushe zaku yi seminar d'in ka dawo jare? Baka ba Fak sai ni kad'ai uwa maye ba dad'i, honestly KD without homies is tasteless." wani gajeren murmushi Fawaz yayi yace "I don't know precisely but I'll holla at you idan zamu yi." "Alright kaji daga Fak kuwa? Shima I've been trying to reach him amma ban same shi ba." cewar Foxy, nan ma sai da gaban Fawaz ya fad'i saboda tun ranar da Fak ya tafi bai san ina kansa yake ba ballantana suyi waya. Nan ma k'arya ya masa yace

"Na, nima ban same shi ba." "What about Affee's old man? Ya dawo?" "Bai dawo ba shine ma abunda ya k'ara zaunar dani Abujan." "Right, holla at me idan ya dawo please akwai Uncle K zan masa magana yana da friend a headquarters na Police he'll take care of it." cewar Foxy

"In shaa Allah." Fawaz ya amsa masa "Guy KD is fun wallahi you gotta come back ka ganni nan kwance with a chick beside me sai hutawa nike." tsuka Fawaz ya ja trying to sound casual yace "Foxy! Wai baka tunanin aure sai hutawa da chicks? God help the poor soul that marries you matar ka ta shiga uku wallahi." dariya Foxy yayi yace

"Kai sai dai mun kama d'an buroba sex less zombie kawai." yana gama fad'ar haka ya kashe wayar. Fawaz bai samu damar yin wani tunani ba sai ga kiran Abban sa ya shigo, nan ma cikin girmamawa ya gaida sa kamar kuma yadda ya faru da Foxy haka ya faru tsakanin sa da mahaifin sa don shima ya shaida masa sati d'aya kenan yana neman wayar sa bai samu ba kuma har lokacin da ya d'iba zai gama exams d'insa ya wuce amma bai dawo ba, k'aryar da yai wa Foxy ita yai wa mahaifin sa cewar da akwai seminar da zasu yi sai ya gama zai zo da haka suka ajiye wayar akan duk abunda ake ciki zai dinga sanar musu. Mik'ewa zaune yayi yana karanta Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un tabbas akwai wani abu da ya faru a ranar da abun ya faru. Rud'ani mara misaltuwa ya shiga ya mik'e a sanyaye ya fito parlor yaga everything is just as he left it komai yana nan intact, zarcewa yayi ya fito harabar gidan yaga motar sa da ya fita da ita a ranar da incident d'in ya faru anyi parking d'inta a parking lot wanda ko shakka babu yasan ba shine ya kawo ta gida ba a ranar

"Toh waye? Who's behind this?" ya fad'a a fili ya ja yayi tsaye a wurin sai kuma zuciyar sa tace kila ko waye ya same shi unconscious ne yayi deciding ya taimake sa to amma idan har taimakon sa yayi to ya dace ya wayi gari a asibiti ko wani wuri na daban ba a gidan su ba tabbas ko waye ya san shi kuma farin sani tunda har ya san gidan da yake zaune, kokarin sake wani tunanin yayi ya tabbatar ranar bai fita da ID cards nasa ko d'aya ba ballantana ya bayar da shaidar wani information nasa. Ya dad'e tsaye a wurin yana ta tunani and the more he thinks, the more he gets confused sannan a sanyaye ya juyo ya koma cikin gidan ya nufi bedroom d'insa. Wayar sa ya shiga bincike yana dubawa koda Allah zai sa yaci karo da wani abu new but ba komai a nan ne ya duba calendar yaga tabbas yau satin sa d'aya kenan in a coma. Iyakar rud'ani fa Fawaz ya shige sa, wayar sa ya d'auko ya fito parlor ya had'a tea da coffee cake ya fara ci thinking idan ya rage yunwar dake addabar sa zai iya tunano wani abu, yana a tsakiyar cin abincin wayar sa tayi k'ara alamar shigowar message, bai yi k'asa a gwiwa ba ya bude message d'in wanda ya k'unshi gajeren rubutu kamar haka;

_Kindly check your car throughly now._

Dakatar da cin coffee cake d'in Fawaz yayi yace "My car?" had'i da k'urawa wayar ido kamar itace zata amsa masa tambayar sa. Mik'ewa yayi ya ajiye cup d'insa na tea ya d'auki wayar sa ya nufi harabar gidan, wurin motar tasa ya nufa ya bud'e front seat gefen driver ya dudduba bai ga komai ba haka ya rufe ya koma back seat nan ma ya duba ba komai. Rik'e k'ugun sa yayi hankalin sa yayi masifar d'aguwa duk da cewa bai ga komai a motar ba sai kuma ya sake d'auko wayar ya k'ara duba message d'in yaga _throughly_ aka rubuta ma'ana ciki da wajen ta kenan sai yayi deciding bud'e boot d'in motar, takawa yayi yaje wurin boot d'in yana budewa zuciyar sa ta halba da sauri kuma da k'arfi sakamakon ganin gawar mutum kwance cikin jini a boot d'in motar tasa, ja da baya ya shiga yi yana girgiza kai not believing what he just saw yana karanta duk addu'ar da tazo bakin sa jikin sa sai kyarma yake, duba fuskar gawar yayi wacce ta kasance ta namiji matashi kamar sa yaga kamar ya tab'a sanin fuskar, tunani ya shiga yi cikin tashin hankali ya gane saurayin da suka yi rigima dashi ne a ranar da wannan al'amarin ya faru

"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un." kawai ya fad'a had'i da daskarewa wurin saboda a iyakar sanin sa yasani kuma ya tabbatar they fought each other that very day amma shi kam bai kashe wannan saurayin ba to waye ya kashe sa? Tabbas wanda ya dake sa ta baya shine ya kashe wannan saurayin kuma shine ya kawo sa gida da bandage a kansa kuma shine ya aiko masa message yanzun nan. To me wannan saurayin yayi da ya cancanci kisa shi kuma miye alak'ar sa da gawar sa me wannan al'amarin yake nufi? Wannan shi yake nuna sati d'aya kenan da kashe wannan saurayin to meyasa gawar sa bata rub'e ta fara wari ba? Ko kuwa ba'a dad'e da kashe sa ba? Ko kuwa anyi preserving gawar ne? Zubewa yayi a k'asa cikin mummunar tashin hankali da bai tab'a shiga ba sai tsinto k'arar wayar sa yayi, jikin sa sai b'ari yake ya d'auko wayar yaga number ce ba suna, sliding kawai yayi ya saka a kunne yaji wata murya babba mai matukar girma da amo tace

"Fawaz kaine ka kashe sa?" mik'ewa tsaye Fawaz yayi yana girgiza kai yace "Ba ni na kashe sa ba, da wa nike magana?" "Kana cikin babban had'ari Fawaz amma ka kwantar da hankalin ka ni zan taimake ka." cewar mutumin, cikin kakkausar murya Fawaz yace "Bani buk'atar taimakon ka tambayar ka nike waye kai? Kuma me wannan gawar take yi a mota ta? Waye ya saka ta?" dariya mutumin yayi yace

"Wooow! You've got guts! Kace baka da bukatar taimako na ko? Kenan kai ka kashe sa kuma da alama har ka tanadi wurin da zaka binne gawar." girgiza kai Fawaz keyi yace "Ni bani na kashe sa ba.." "To waye?" mutumin yayi interrupting nasa, kad'a kai Fawaz yayi yace "Nima bansani ba an sakan gawar a mota ne kawai." "To me kake shirya zaka yi da gawar?" shiru Fawaz yayi na mintuna k'alilan sannan yace

"Zan sanar da jami'an tsaro." dariya mutumin yayi yace "Kadda ka kuskura kayi wannan gangancin Fawaz, kasan wannan saurayin ko waye? I bet you don't." "Waye?" Fawaz ya tambaya cike da rud'ani "D'a ne a wurin babban Minister'n man fetur na k'asa yanzu haka labarin b'atan sa ya zagaye ko ina cikin k'asar nan advisably Fawaz kada kayi yunk'urin mik'a wannan labari ga jami'an tsaro saboda ba wanda zai wanke ka da ba kaine ka kashe sa ba." Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un kawai Fawaz ke maimaitawa zufa ta shiga keto masa hankalin sa yayi mummunar tashi "Amma ni zan taimake ka Fawaz." ya tsinto muryar mutumin

"Wanne irin taimako zaka min?" Fawaz ya tambaya kansa ya d'aure ga baki d'aya "Zan turo yara na su taimaka maka kuje wani wuri nesa da gari ku binne gawar ina tabbatar maka shikenan ba wanda zai san abunda ake ciki and you can move on with your life amma idan har ka yarda dani kuma ka amince." "Waye kai?" Fawaz ya k'ara tambayar sa

"Ba lokacin amsa tambayoyi bane yanzu, ka amince?" har Fawaz zai ce bai amince ba sai kuma ya tuna idan har wannan mutumin ya kufce masa to ya zai yi da gawar? Cikin rashin k'warin gwiwa Fawaz yace "Na amince amma waye kai?"

"My name is Cheetah." cewar mutumin kuma yana fad'ar haka ya tsinke kiran.

"Cheetah!" Fawaz ya maimaita a fili yana rik'e da wayar sa sai jujjuya ta yake a hannun sa k'wak'walwar sa ta cunkushe. Wa zai gayawa wannan badak'alar da yake ciki? Tambayar da ta zo masa kenan, ko dai ya kira Abban sa ya sanar masa? Ko kuma Foxy? Ko Fak? Ammi? Sai kuma wani tunanin yazo masa ai wannan mutumin zai taimake sa sai kuma wani b'angare na zuciyar sa yasa masa waswasi anya baka yi gangancin yarda da wannan mutumin ba? Tunani da tambayoyi barkatai dai sukai ta zuwar masa at long last ya ja paralyzed foot nasa ya nufi cikin gidan. Fad'awa yayi kan sofa ya bud'e accounts nasa na social media starting with Twitter yaga tweets na manya-manyan jaridun k'asa suna gasgata b'atan Ra'es d'a a wurin babban Minister'n man fetur wanda a halin yanzu yake a cikin motar sa da kuma garkuwa da aka yi da d'iyar d'aya daga cikin billionaires na k'asa wato Afeefah Jalal duka d'auke da hotunan su. Mik'ewa tsaye Fawaz yayi zuciyar sa sai harbawa take ba kama hannun yaro wane ta faso kirjin sa ta fito jikin sa wane an lik'a masa shocking tsabar tsorata da kad'uwa ya kasa tantance a wanne hali yake ciki

"Afeefah has been kidnapped.. Ra'es was killed... Now Cheetah has showed up... What's really going on?" ya tambayi kansa a fili sai safa da marwa yake a parlor'n shi kad'ai yana tunani barkatai bai ankara ba sai jin tsayuwar mota yayi a harabar gidan nan take kuma sai ga echo na footsteps yana approaching parlor'n.

*Shawty*💕 [7/6, 9:37 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*27*

Mutuwar tsaye yayi a wurin k'wak'walwar sa ta tsaya cik ya tsaya kawai yana jiran mai aukuwa ta auku. Wasu zaratan mazaje ne guda biyu wanda yanayin su yafi kama da thugs kowannen su sanye da jeans da killer shirt da wasu manya-manyan takalma da suka fi kama da jungle boot suka shigo parlor'n. Kallon su Fawaz keyi har suka k'araso cikin parlor'n wanda yafi murd'ewa da k'wanji a jikin sa shine a gaba ya tako yazo gaban Fawaz ya mik'a masa hannun sa kamar icce suka gaisa cikin wata babbar murya yace

"It's about the corpse in your car." kallon su kawai Fawaz keyi ya rasa ma abunda zai ce kansa ya d'auki zafi ba kad'an ba, girgiza sa mutumin yayi yace "Muje ko?" sai da Fawaz yayi ajiyar zuciya sannan ya shige gaba suna biye dashi har harabar gidan a inda motar su da tasa motar suke tsaye, kai tsaye mutumin wurin motar Fawaz yaje ya bud'e boot inda gawar Ra'es take a kwance, k'arasowa suka yi dukansu sai kallon gawar suke daga k'arshe wannan kakkarfan yasa hannun sa biyu ya d'auko gawar cik ya d'ora a kafad'ar sa yayi wa d'ayan alama da ya bud'e masa boot d'in motar da suka zo ai kuwa nan take suka saka gawar a ciki suka rufe sannan ya juyo ya kalli Fawaz yace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull