Kenza eBookz

Abokaina complete book 1 - Chapter 11

Abokaina complete book 1 - Chapter 11

Abokaina complete book 1 Chapter 11: Abokaina complete book 1 Chapter 11. "Foxy how could you do this? How could you?" sannan ya shiga maida numfashi…

4,493 words

"Foxy how could you do this? How could you?" sannan ya shiga maida numfashi jijiyoyin kansa suka fara fitowa yace "Haba Fahad! Mesa za kai haka for god sake! Why Afeefah? Mesa sai ita? Of all the bad girls on the streets? Ka rasa wacce zaka yi raping sai ita? It's such a waste of a young life Fahad!" sannan ya dafe kansa da ya fara masa ciwo, shiru ya sake biyo baya sannan Foxy yayi k'arfin hali yace "Kayi hak'uri Fawaz I know I fucked up but please let me take the blame leave me to worry about that." wani murmushin k'arfin hali Fawaz yayi yace

"You see your life? Police! That's all what you're thinking about, ita Afeefah baka tunanin ta right? Don't you think about the pain you caused her? The damages you made?" shi kam Faruk he is totally speechless ya ma rasa abunda yake ciki he feels guilty and ashamed of himself sannan ya tsinto muryar Fawaz yana cewa "I believe koda kaje ka gayawa mahaifin ta ba nine nayi raping d'inta ba it won't change a thing. The first time she fainted ni na kawo ta asibiti claiming ni yayan ta ne tun lokacin mahaifin ta ke zargi na. The second time na kawo ta anyi raping d'inta lifelessly claiming ni mijin ta ne ka gayamin how could I confront them da zancen ba ni nayi raping d'inta ba bayan wad'annan shaidun da suke da akaina?" cikin kwantar da murya Foxy yace

"Fawaz don't make me an outsider please, we are all in this, I'm going to help you in anyway I can." jinjina kai Faruk yayi yace "Foxy is right. We are all in this, wannan abun mu duka ya shafa not just you yanzu the best thing to do is to wait har ya dawo d'in we are not to take any action now." da haka suka samu suka ci kan Fawaz har ya kwantar da hankalin sa.

*Washegari* Fawaz bai yi k'asa a gwiwa ba har sai da yaga yayi convincing likitan sa ya sallame shi a ranar ta hanyar gaya masa yana da jarabawa a ranar, ba yadda likitan bai yi ba amma sam Fawaz yace shi ba zai zauna a asibitin ba. Bayan sun dawo gida Foxy ya fita sayo masu abinci ya rage Fawaz da Faruk kawai. Sanye Fawaz yake da shorts army color sai singlet ba abunda yake sai shan giyar sa yana bin news feed na Facebook d'insa nan take kuma yayi cilli da wayar ya d'aga kwalbar giyar ya tarwatsa ta a k'asa ya dafe kansa ya fara wani irin gurnani idanun sa suka yi masifar ja, tashi Faruk yayi yazo kusa dashi ya rik'o sa cikin kulawa yace

"Fawaz don't let this mess drive you nuts, you had a life before you met Afeefah kuma koda bata cikin rayuwar ka zaka cigaba da rayuwa, maganar gaskiya baka yiwa kanka adalci Fawaz."

"Suppose you stop talking and get the fuck out?" cewar Fawaz wanda idanun sa suka gama yin ja, mik'ewa Faruk yayi ba tare da yace komai ba ya nufi hanyar fita parlor'n "Faruk" Fawaz ya kira sa, tsayawa Fak yayi ya juyo sannan Fawaz yace "Please ka shirya kaje ka duba min jikin Afeefah mana... I've been trying all her lines but switched off." jinjina kai Fak yayi yace

"Alright." sannan ya dawo ya shiga d'akin sa yayi wanka ya shirya cikin Kaftan fari da hula ya karb'i keys d'in d'aya motar su ya fita. Koda ya fito yayi daidai da dawowar Foxy, tambayar sa yayi ina zai je yace masa Afeefah zai duba a asibiti, yaso shima ya bi Faruk su tafi but yasan ba abunda zuwan sa zai haddasa mata sai wani sabon bak'in ciki yasa ya fasa yayi shigewar sa kawai.

Tafe Faruk yake har ya kawo asibitin ya nufi sashen da Afeefah take kwance. Knocking yayi a k'ofar aka bashi izinin shiga. Daskarewa Faruk yayi lokacin da idanun sa suka sauka akan Afeefah wacce take zaune da pillow a bayan ta rame sosai ta k'ara yin wani fari fauu kamar ba Afeefah ba, da sassarfa ya k'arisa wurin ta ya matuk'ar tausaya mata yana cewa

"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un Afeefah, OMG!" kuka ta fashe dashi gwanin tausayi yayin da Faruk ya shiga lallashin ta da bata hak'uri yace "Afeefah komai kika gani muk'addari ne daga Allah and this is a chance for you to start a new kiyi hak'uri ki daina d'aga hankalin ki kinji?" ya k'are maganar yana goge mata hawayen dake ta mata ambaliya. K'ara fashewa tayi da kuka tace

"Faruk I wish I had never been born... I feel bad... I'm upset." sannan ta fara k'ok'arin maida numfashin ta tace "Faruk na cancanci haka daga Foxy? Sakamakon da ya dace ya saka min dashi kenan?" sai kuma ta rushe da kuka tace "How I wish I've had the ears to listen to what Oldie is warning me not to." kukan Umma ne ya jawo hankalin Faruk ya juyo ya kalle ta, tun shigowar sa hankalin sa na kan Afeefah ko kad'an bai san da zaman Umma a d'akin ba, rusunawa yayi yace "Umma ina wuni?" sai da ta goge hawayen ta tukunna sannan tace "Lafiya k'alau ina gajiya?"

"Alhamdulillah, ya me jikin?" "Da sauk'i Alhamdulillah" "Allah Ya k'ara sauk'i." da "Ameen" Umma ta amsa sannan Faruk ya zarce da cewa "Kwana biyu ne bamu ganta a makaranta ba so sai nike tambayar wata k'awar ta take gayamin abunda ya faru." yayi k'ok'arin yiwa Umma k'arya da rufe mata real identity d'insa don yasan da ta fahimci team d'insu d'aya da Fawaz da suke zargin shi yayi raping Afeefah to tabbas korar kare zata masa. Duk'ar da kanta k'asa Umma tayi tace "Wallahi kuwa." "Allah Ya bata lafiya Ya kuma tsare gaba." cewar Faruk, nan ma da "Ameen" Umma ta amsa sannan Faruk ya juya kan Afeefah ya cigaba da rarrashin ta sai kuma cikin ikon Allah ta rage kukan at least taji dad'in yadda Faruk ya damu da ita ya kuma zo takanas don duba ta abunda Oldie'n ta bai yi ba har yau kuma abunda ya matuk'ar bata mamaki. Faruk zai yi kusan awa d'aya a asibitin daga k'arshe ya musu sallama ya tafi.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life*

*23*

_Bayan kwanaki_ Bayan kwanaki da faruwar al'amarin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da chanzawar Fawaz zuwa mashayin k'arfi da yaji a tunanin sa giyar zata sanya shi manta duk abunda ya faru but sai ma k'ara masa bak'in ciki take da barazanar tarwatsa masa rayuwa. Gefen makaranta baya wani karatun azo a gani jarabawa ma ba wani abun kirki yake rubutawa ba, ba zai yi minti arba'in a cikin exam room ba zai fito ya kama gaban sa he hardly speaks to anyone ko a gida Faruk da Foxy sun rasa kansa idan dai bai sha giya ta bugar dashi ba to tabbas fitowa zai yi harabar gidan yai zaman sa shi kad'ai da kuma yaga suna k'ok'arin takura masa to zai bar masu gidan baki d'aya. Gefen Afeefah ma taji sauk'i sosai har ta dawo gida but daga lokacin abubuwa itama suka chanza mata. Umma sam ta daina kula ta gaisuwar ta ma da k'yar take amsawa bata zama ta saki jiki suyi hira Aunty Nana ma haka and the worst part is tun lokacin Oldie bai tab'a kiran ta ba, bai zo ya duba ta ba kwata-kwata bata san cewa shine ya kawo ta asibiti a ranar ba kuma shine yaron da Daddy ke mata maganar sa a duk sanda suka yi waya yake ta shan alwashin sai hukuma ta hukunta shi idan ya dawo ita a zaton ta Foxy ne yake magana.

Da sassanyar marece wuraren k'arfe hud'u da rabi ta shirya cikin doguwar rigar atamfa had'i da d'ora hijab bak'i a sama ba kwalliya a fuskar ta ta sauko parlor, bata samu kowa ba kawai ta nufi hanyar fita don tasan ko tace ta nemi izni wurin Umma ba dole ne ta kula ta ba. Motar ta ta shiga ta tada ta bar gidan bata zame ko ina ba sai gidan su Fawaz. Koda tayi parking ta fito ta samu Foxy da Faruk suna buga tennis yayin da Fawaz ke gefe zaune bisa wasu lounging chairs da kwalaben giya har biyu a gaban sa sam bai san da shigowar Afeefah ba.

Ganin Afeefah a lokacin da basu yi tsammanin ta ba ya matuk'ar bawa Faruk da Foxy mamaki, takawa Faruk yayi ya nufi wurin ta ya bar Foxy tsaye a mace a wurin. Murmushi Faruk ya mata sannan yace

"Oyoyo Affee." murmushin ta mayar masa tace "Oyoyo Fak." "Ya kike ya jikin?" cewar Faruk, nan take yaga yanayin ta ya chanza dubawar da zai yi yaga Foxy ne ke k'arasowa wurin, tuni rahamar dake kan fuskar ta ta gushe ta kalli Faruk tace

"Ina Oldie?" nuna mata shi Faruk yayi da yatsa tun kan Foxy ya k'araso ta juya ta bar wurin. Fawaz yayi nisa a duniyar tunani sam bai ji motsin isowar ta ba har ta k'araso tana kallon sa ya rame sosai yayi bak'i kamar ba Oldie'n ta ba. Idanun ta ne suka sauka kan kwalaben da take tunanin giya ce a ciki, tuni jikin ta ya soma rawa daidai lokacin Fawaz ya juyo ya ganta, mamaki ne ya cika shi nan take ya mik'e zumbur yana watsa mata wani kallo wanda ita sam bata lura da kallon ba jikin ta sai rawa yake idanun ta suka ciko da hawaye ta d'auko kwalbar taga lallai giya ce, cikin rawar murya lips d'inta ma sai rawa suke a tak'aice ko ina jikin ta rawa yake tace

"Oldie..." sai kuma ta dakata sakamakon kallon da yake jifar ta dashi, k'arfin hali tayi tace "Oldie wannan abun kake sha?" ta k'are maganar tana nuna masa kwalbar cike da mamaki. Har yanzu kallon da yake watsa mata ya kasa gushewa sun d'auki kusan mintuna goma a haka ba wanda yace da wani uffan jikin Afeefah sai rawa yake tana so tayi kuka amma yak'i zuwa, d'ora hannun ta tayi kan nasa ai kuwa kamar wanda aka d'ora wa garwashi nan take ya yarfe hannun sa ya fizge kwalbar giyar sa daga hannun ta ya nufi cikin gidan da sauri. Durk'ushewa Afeefah tayi ta fasa kuka mai ban tausayi harta Faruk da Foxy dake tsaye suna hango show d'in ta basu tausayi sosai, mik'ewa tayi tsaye ta fara tafiya ta nufi cikin gidan, koda ta shiga bata same shi a parlor ba straight d'akin sa ta nufa koda ta shiga ta same shi zaune bakin gado ya dafe kansa, ganin ta yasa ya mik'e zumbur yana cigaba da watsa mata kallo

"I know... I know how you must be feeling right now..." ta fara magana muryar ta na rawa tana kuka "I would probably feel the same if I were in your place... Ban ga laifin ka ba Fawaz... I don't blame you for feeling bitter..." sai kuma ta zube kan k'afafun ta, nuna ta Fawaz yayi da yatsa yana so yayi magana amma maganar ta kasa fitowa tsabar bak'in ciki, juya mata baya yayi jikin sa sai shaking yake uncontrollably cikin kuka ya tsinto voice d'inta yana cewa "Oldie... Kayi magana kawai no matter what it is just talk.. You can yell at me if you want to... You can scream if you have to but please talk to me don't keep it to yourself." juyowa yayi yana watsa mata wani kallo she is still lovely and desirable but the innocence and chidishness were now missing, nuna kansa yayi da yatsa tayi mamakin yadda muryar sa ta dishe kamar ba tasa ba yace

"Afeefah do you think I'm made of stone? Nima fa mutum ne kamar kowa, jini ne ke yawo a jijiyoyi na..." tsayawa tayi cak da kukan ta kasa fahimtar ina maganganun sa suka dosa sai tafi kyautata zaton yadda ya sha jan kunnen ta akan Foxy ne tak'i ta saurare sa abun yake damun sa, mik'ewa tayi tsaye har yanzu jikin ta sai b'ari yake tace "Nasan ka sha jan kunne naFawaz...You've warned me several times... " katse ta yayi ta hanyar daka mata tsawa yace

"Excuse me will you? Will you take your frustration and your discomfort out of here? Will you remove your little girl attitude and your attractive body out of my sight and temptation?" sai kuma ya dakata yana huci yana numfashi yayin da Afeefah ta gama daskarewa ko ince mutuwar tsaye saboda tsabar mamaki da kuma mamakin wasu maganganun sa da ta kasa sanin me suke nufi, tsinto muryar sa tayi yana cewa "Kun gama watsewa ke dashi you are tired of displaying and offering yourself to him sai kuma ki dawo min? What do you think I am or do you think I'm made of stone? Ki tashi ki fice min daga idanu and never come back ever! Ki tashi ki fita and find some other fool I know there must be thousands of guys who will fall for you as I did." ba korar ta da yayi ne take mamaki yanzu ba kamar yadda yake zaro wasu kalmomi kamar wanda ya dad'e bearing an unrequited love, d'aga baki tayi zata yi magana ya dakatar da ita had'i da nuna mata k'ofa yace "Ki fita Afeefah!"

"Oldie..." katse ta yayi ta hanyar d'aga mata hannu ya kawar da kansa gefe d'aya yace "Ki fita." "Oldie please ka saurare ni." d'ago kai yayi ya daka mata tsawa yace "Ba kya ji ne? You're testing the limits of my patience ki fita nace!" hannun ta ta d'ora kan bakin ta tana k'ok'arin hana kukan dake neman kufce mata she wants to act strong ta rama masifar da yake mata amma ta kasa, takowa Fawaz yayi yazo gaban ta idanun sa sunyi ja kamar garwashi ya nuna mata hanyar fita cikin kakkausar murya yace "Rest your goddamn feet some place else karki sake tako k'afar ki gidan nan." yana rufe baki ta juya a guje ta fice daga d'akin idanun ta hawaye sun rufe su ko gani sosai bata yi, waige-waige ta shiga yi tana neman Faruk he is the only one she can cry on his shoulders shi kad'ai ya rage mata shi kad'ai yanzu ke tausayin ta, kuka take tana kiran

"Faruk! Faruk!!" tana buk'atar wanda zai yi calming nata, fitowa Faruk yayi ta baya yadda yaga take kukan abun ya basa tsoro da gudu ya k'araso ta kama shi ta k'ank'ame ta cigaba da kukan, bai yi k'ok'arin dakatar da ita ba don yasan shi take buk'ata the most sai da tayi ta gaji sannan ya ciro ta daga k'irjin sa yace

"Affee menene?" "It's Oldie.. He's chasing me out like I'm a kind of cheap trash, used and throw types... Wallahi Faruk ni ba karuwa bace... I'm not a slut and certainly not a whore... Faruk I'm really not.. I was only a fool but since that time I've got wise to myself." share mata hawaye Faruk yayi yace

"Nafi kowa sanin haka Afeefah you are only a lover ke ba karuwa bace." fashewa tayi da kuka tana girgiza kai tace "I'm really not Faruk.. Allah ne shaida ta amma kowa ya kasa yarda dani. Umma bata amsa gaisuwa ta.. Aunty Nana bata kula ni.. Daddy is not here the only family left for me now is Oldie shima kaga kora ta yake.. I'm only born for hurt Faruk." sai kuma ya shiga share mata hawaye yace

"It doesn't matter Afeefah don kowa ya kasa yarda dake, Faruk is here and he is ready to offer any help possible. Karki damu kiyi hak'uri, ba wai basa sanki bane Afeefah they are only mad at you kuma zasu sauka in shaa Allah kinji?" jinjina kai tayi tana goge hawayen ta tace

"Thank you Faruk, you are a sweetheart." murmushi Faruk yayi yace "Ba godiya a tsakaninmu Affee it's called yiwa kai if you ever need anything or you want to talk just give me a call I'm a great listener okay?" Allah sarki Affee sai gashi tana murmushi har hak'oran ta suna fitowa ita dai all she ever wants is a shoulder that supports her, suna cikin haka basu ankara ba sai ganin Zuhra suka yi tsaye a kansu tana murmushi ta k'araso daf dasu har sai da ta taka k'afar Afeefah da MC X converse d'inta ta kalli Faruk tace

"Quite a show Fak, idan kun gama kazo ina son ganin ka please." ta fad'i maganar tana wani Somewhere" chewing gum asalin karuwa sannan ta banki Afeefah a kafad'a ta wuce ta zauna kan wasu kujeru. Faruk da Afeefah kam sai kallon ikon Allah suke da haka Faruk ya cigaba da rarrashin Afeefah ya raka ta har wurin motar ta ta shiga suka yi sallama taja ta tafi. Juyowa Faruk yayi ya kalli Zuhra wacce ta kame kan kujera had'i da crossing legs yace

"Madam" "Get in and change." cewar Zuhra, d'aga gira yayi yace "Ina zamu je?" "Somewhere" "Me zamu yi?" "It's strictly biz." rausayar da kai Faruk yayi had'i da cewa "An gama your highness." sannan ya nufi cikin gidan.

*Shawty*💕 [7/6, 9:36 PM] Ummee Garkuwa: 👬 *ABOKAINA* 👫 (A True Life Story)

*By Shawty*💕 *April, 2018* *Pure Moment of Life Writers*

*24*

Bai dad'e ciki ba ya fito cikin shigar k'ananan kaya ya sami Zuhra a wurin da ya barta, tana ganin fitowar sa ta mik'e tsaye ta nufi wurin motar ta shima ya rufa mata baya. Tafe suke har suka kawo Millennium Park ba mai ce da wani uffan. Zuhra ce tasa aka kawo musu abun sha da ciye-ciye suka zauna shi dai Fak kallon ta kawai yake ya k'agara yaji dalilin kawo sa wurin da tayi. Kallon sararin samaniya kawai Zuhra keyi tana kora abun shan dake gaban ta sai murmushi take, murmushin shima Faruk yayi ya kalle ta yace

"Madam Zent, da alama dai kina cikin nishad'i." girgiza kai tayi har yanzu da murmushin akan fuskar ta tace "Ko kad'an Faruk, hasali ma ina cikin bak'in ciki ne." "Aka ce labarin zuciya a tambayi fuska kuma" cewar Fak, jinjina kai tayi tana murmushi tace "Hakane amma kuma ba koda yaushe yake hakan ba." murmushi kawai Faruk yayi ya cigaba da shan abunda ke gaban sa yayin da Zuhra sai lumshe ido take tana murmushi iskar dake wurin sai karkad'awa take, bud'e idanun ta tayi suka sauka akan Fak dake shan abun shan sa suka sakarwa juna murmushi lokaci d'aya sannan ta cigaba da kalle-kalle tace "Abuja is fine." kallon wurin Faruk yayi ya cigaba da shan lemon sa yace "Yeah a beautiful town of course." lumshe ido Zuhra tayi tana shak'ar iskar wurin tana lumshe ido tana bud'ewa lokaci d'aya tace

"It's fine town for millionaires amma idan baka da kud'i..." ta dakata had'i da yin wata gajeruwar dariya mai ban tausayi sannan tace "It's tougher than a jungle full of wild animals." dakatar da shan lemon Fawaz yayi yana kallon ta yana kuma k'ok'arin auna maganganun ta "Faruk kud'i da kake gani sune komai a yanzu... Idan baka da kud'i yanzu..." nan ma ta sake yin wata gajeruwar dariya mai ban tausayi tace "You can't get a good job.. You can't go to a place worth going to.. You can't mix yourself with people who are worth mixing with.. Fak idan baka da kud'i a wannan lokacin you are nothing wallahi rayuwar ka bata da wani amfani dabba ma ta fika you are just one of a crowd." tuni mak'oshin Faruk ya bushe k'am kamar mai azumi maganganun Zuhra sun tab'a sa, tunanin sa na yau da kullum yazo d'aya da nata tabbas maganganun ta gaskiya ne idan baka da kud'i a wannan zamanin kai ba kowa bane amma kuma me take nufi da hakan?

"Gaskiya ne maganar ki Zuhra..." cewar Fak "Amma me kike nufi da haka?" dakatar da shan lemon tayi ta dire glass cup d'in akan table dake gaban su tace "Let's talk business now." had'i da mik'ewa tsaye ta bada baya tayi taku uku sannan ta dakata tace "Sunan mahaifin ka Malam Ibrahim Wada baya da wata k'wak'k'warar sana'a face koyar da yara a makarantar allo." gaban Faruk ya bala'in fad'uwa sannan ta cigaba da cewa "A cikin wannan sana'ar ya girma har ya auri mahaifiyar ka har kuma Allah ya azurta su da rabon ka da k'anin ka." sannan ta juyo ta fuskanci Faruk sosai wanda fuskar sa ta kasa b'oye mamakin da al'ajabin da yake ciki yayin da ita kuma Zuhra fuskar ta gam ba alamar wasa tattare da ita "Kun taso cikin wahala da talauci ba abunda mahaifin ku da mahaifiyar ku ke fafutuka a kullum sai ganin sun sama maku abunda zaku ci amma duk da haka mahaifin ka bai yi k'asa a gwiwa ba har sai da ya saka ka a makarantar primary ta gwamnati." sannan ta dakata ta dawo ta zauna Faruk wanda ya gama cika da tsintsar mamaki sai binta da ido yake "Kayi karatun ka a wannan primary har ka gama kuma kasancewar ka yaro mai basira ka burge wani d'an siyasa a unguwar ku har ya d'auki nauyin karatun ka a makarantar kud'i wacce sai 'ya 'yan da iyayen su suka kama k'asa ke iya karatu a ciki wato Liberty International Schools a nan ne kuma ka had'u da Fawaz da Fahad."

"Zuhra..." "Dakata Faruk let me do the talking." ta fad'a had'i da d'aga masa hannu alamar yayi shiru sannan ta cigaba da cewa "Tun daga lokacin tunanin ka da mafarkan ka na kud'i ne da yadda za'a yi ka zama matashin me kud'i kamar yadda kaga sauran abokanin ka ke rayuwar dad'i da iyayen su. Bayan kun kammala secondary school rayuwar ka ta sake komawa gidan jiya wato kamar wacce ka fito har sanda Fawaz ya sake zuwa ya tallafi nauyin karatun ka har zuwa yau."

"Me wannan labarin da kika samo a kaina zai amfana miki me kuma fa'idar rewinding d'insa a wuri na?" "Kana son kud'i Faruk ko kuma ince kana da buk'atar kud'i a rayuwar ka and don't you dare deny it." cewar Zuhra wacce ta kafe sa da ido, dariya Faruk yayi yace "Idan ina son kud'i sai me? What's that to you? Wai dakata ma Zuhra... Mesa kika d'auko ni kika kawo ni nan?" "Aiki na samo maka Faruk and it's worth millions but it's an element of risk." dariya Faruk yayi harda buga k'afa yace "Zuhra kenan... Mesa kika damu dani har kika samo min aikin miliyoyi haka? Waye ni a wurin ki?" girgiza kai tayi tace

"Kai ba kowa bane a wuri na sai aminci da abokantaka dake tsakanin mu kuma wannan aikin da kai kad'ai ya dace, kai kad'ai ka cancanta Faruk." dariya ya sake yi yace "Zuhra kenan.. If a guy like me goes after the kind of money you're talking about, sooner or later he's going to get himself into a big trouble... Samun miliyoyi a wannan lokacin ba abu bane mai sauk'i Zuhra kuma naji kina fad'ar it's an element of risk so I won't do it for all the money in the world. " sannan ya mik'e tsaye yace " Nagode sosai da kulawar ki, thanks." ya juya zai bar wurin, tuni Zuhra ta mik'e tsaye itama tace

"Faruk think about your parents what they've been through... Faruk wannan ba dama ce da zasu huta daga wahalhalun da suka sha a baya ba? Ba dama ce da zaka tsamo su daga cikin talaucin da suka dad'e a ciki ba?" juyowa yayi yana kallon ta itama tana kallon sa sannan ta cigaba da cewa "Shiyasa nace da kai kad'ai ya dace... Mesa ba zaka saurare ni ba Faruk? Ko kuwa don kaji nace akwai had'ari a cikin aikin?" sai kuma tayi murmushin yake sannan tace "Is there any legal job that will get you a millions these days? Duk wad'annan mutanen da kake ga suna fantamawa cikin manyan motoci da manyan gidaje an gaya maka gaskiya ce take kawo musu wannan kud'in? Faruk ba aikin gaskiya a wannan zamanin no matter how it is sai ka samu rashin gaskiya da almundahana a ciki koda k'ank'ani ne, kowa da kake gani bai damu da tsaftar kud'i ba a yanzu, everyone is just struggling for survival Faruk." sannan ta d'auki jakar ta tace "Now the ball is in your court do as you pleased amma kayi tunani mai kyau."

"Idan mutum zai baka riga akace ka dubi ta wuyan sa, Zuhra har yaushe kika yi k'arfin samarwa wani aikin miliyoyi?" dariya tayi ta rausayar da kanta tace "Ba damuwar ka bace ta ina miliyoyin zasu fito leave me to worry about that, aikin ne damuwar ka. Faruk da babu wannan kud'in da ba zanzo na b'ata lokaci na da lokacin ka ba." shiru Faruk yayi k'wak'walwar sa ta cunkushe da tunani iri daban daban, k'arasowa Zuhra tayi gab dashi tace "Help me to help you Faruk..."

***

_10:00pm_ Faruk ne kwance a d'akin sa sai juyi yake ba abunda yake yawo a k'wak'walwar sa sai maganganun Zuhra. Wayar sa ya lalubo yayi viewing wani hoton su da suka d'auka da Fawaz, Foxy da Afeefah dashi a ranar da Foxy ya dawo daga UK dukansu suna dariya hoton yayi kyau matuk'a, tunani kala-kala suka shiga yawo a k'wak'walwar sa har bacci yayi awon gaba dashi.

*Washegari* Yau ta kama Lahadi Faruk bai tashi ba ranar sai wuraren k'arfe goma na safe, ya dad'e zaune kan gadon sa yana tunani daga k'arshe dai ya tashi yayi wanka ya fito parlor. Zaune suke dukansu a cikin parlor'n kowa da wayar sa a hannu ba mai ce da wani uffan, Foxy sai kurb'ar wine d'insa yake lokaci d'aya yana danna wayar sa, mik'o hannu Fawaz yayi yana nuna glass cup d'in yace

"Sammin wine d'innan please." "Ya k'are." cewar Foxy a tak'aice, kallon sa Fawaz yayi then ya kalli wine d'in yace "Gashi ina gani zaka ce min wani ya k'are can't you see this nigga is dying of thirst?" tsuka Foxy ya ja a takure ya d'ago kai ya kalle shi fuska a yamutse yace

"Fizzy mana!" sannan ya sake jan wani tsuki ya zunguri Fak a k'afa yace "Wicked boy why can't you give him a double shot of Hennessy? Ni wannan wine d'in fa shi kad'ai ya mun saura I won't give" Fak da yayi nisa a tunani ko sanin abunda suke ciki bai yi ba, jin shiru yasa ya d'ago ya kalli Faruk sannan yasa hannu ya tab'a sa, zabura Faruk yayi wanda duk ya basu mamaki saboda basu saba ganin Fak a cikin damuwa ba

"What's biting you lil kid? You looked disturbed." Fawaz ya tambaye sa, furzar da numfashi yayi ya girgiza kai yace "Bakomai." "Fine! Jeka ka kawo mana wine please." Foxy ya fad'a had'i da resting kansa akan kujera, harara Faruk ya dalla musu su duka sannan ya ja tsuki yace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull