Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 10
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 10: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 10. Ya fito wanka rike da karamin tawul yana goge jikinsa sai da ya…
3,365 words
"Ga abincinka can a falo fa, kai nake jira ka sauko mu ci"
"Na ci abincin a waje"
Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, sakin baki ta yi tana mamakin furuncin, tasan waye mijinta cin abinci a waje ba dabi'arsa ba ce.
"Wai duk fushin ne haka? Fisabilillahi ganin chat kawai ya kai ace ka dauki fushi da ni har haka?"
Ya juyo ya kalleta.
"A gurinki abun da kika aikata ba laifi ba ne?"
"Idan ma laifi ne ai ya kamata kayi min uzuri ko? Har sai idan na sake aikatawa"
"Rashin daukarsa laifi shi yake kara bakanta min rai, taya zaki zauna da kawarki ki labarta mata yadda muke rayuwa a shimfidar da ko dan'uwanki ba a yarda ya sani ba, taya zaki ji idan kika kama ni ina fadawa abokina yadda nake da ke a gado?"
"Dadi zan ji mana, ai kana fada masa yadda na iya gyara shimfida ne, Aliyu wannan abun fa is normal, yanzu rayuwa ta canja ba yadda muke a baya ba ne, wacan rayuwar da kake tunani ko iyayenmu ba su yi ta balle kuma mu, amman dai shikenan tun da baka so zan daina"
"Ina fatan haka"
Ya furta yana kokarin danne fushinsa domin kara bata masa rai take da kalamansa na yanzu. Murmushi ya sakar mata ya matsa kusa da ita.
"Muje mu ci abincin"
"Ba kace ka ci abinci a waje ba?"
Ta fada tana masa kallon da yafi kama da harara, ya fadada murmushinsa tare da shafa cikinta.
"Wasa nake kawai ina fushi ne amman yanzu na sauko"
Ya rike hannunta suka fice daga dakin, falo suka sauka ya ci tuwon shimkafa da favorite miyarsa miyar kuka, sai da ya ci yayi nas sannan ya soma bata labari, da hira ta yi dadi sai ya dauko mata zancen sabuwar ma'aikaciyarsu da kuma fadan da ta yi da Amal a yau. Har a ranta ta ji dadin korar da aka yi mata domin bata son kowace mace a kusa da mijinta, Amal din ma dan ta zama dole ne.
"Kasan wasu matan ba ba su da kai, musamman kabilun nan kara ana musu haka, ta nan za su fahimci matsayinsu, kuma wasu ma fa kawai neman maza ke kawo su"
Tana maganar tana yatsina fuska. Kallonta yayi yana girgiza kai.
"Madam ba fa ni kadai ba ne namiji a kamfanin nan, kawai ke da kin ji maganar mata sai kishi ya tashi"
"Matan ne fa yanzu kamar za su auri namiji da karfi, idan mutum be yi taka tsantsan ba sai a aure masa miji"
"Ke da kika san waye mijinki ai be kamata ki daga hankalinki akan ko'ina zan shiga ba, kuma karki manta ke kadai zaki rayu a gidan Aliyu daga ke sai yayanki, ko kin manta alkawarin da na yi miki? Ba ke ba kishiya"
"Ban manta ba amman ku maza ai wani lokacin zaku iya ganin mace ku bi ku rude kanta duk wani alkawari da kuka yi ku watsar da shi, musamman idan ka ga wata fara kyakkyawa yar doguwa"
Yayi murmushi.
"Allah ya saukaka miki wannan kishin, ni bana da ra'ayin karin aure"
Dadi ya lullubeta ta kwanta jikinta.
"To yanzu zaka je ce ta dawo aikin ne ko kyaleta zata ka yi?"
"Aa ai ta riga ta rasa kenan, ni ban san a ina take ba balle nace ta dawo, kuma an riga an yi replacing dinta da wata ai"
Sanin halin matarsa ya saka shi bata wannan amsar.
"Haka ma yafi, waya sani ma ko tana da kyau"
Wannan karon dariya yayi, domin ta canja daidai Emily tana da kyau kuma ya san da ta san haka ba zai zauna lafiya ba.
"Ai ni kowace mace na kalla ke nake gani a fuskarta"
Ta buge masa hanci tana dariya, shi ma dariyar yayi ya dauko mata wata sabuwar hira, sai da aka kira sallah la'asar suka daga falon, a shi ya nufi masallacin dake unguwarsu ita kuma ta gabatar da sallah ta a gida kamar yadda Annabi ya umarta. Misalin karfe biyar da mintuna 58 wayarsa ta yi kara alamar kira, a ka'ida idan yana kusa da matarsa baya taba waya saboda ya bata lokacinsa, sai idan kiran ya tsananta ko kuma ya kasance na gaggawa ne, sai dai jiran amsar Turhan ya saka shi mikewa tsaye ta nufi wayar ta dauka sai ya kira ne ta whatsapp kuma video call da wata bakuwar number da be san waye ba.
Rejecting yayi ya bude whatsapp din ya duba bakuwar number sai yayi arba da hotunan Emily sun fi guda hansi, Hello Hi kuma ya fi ashirin, kamin ya samu damar reply wani kiran ya sake shigowa. And this time around baya son rejecting domin ya fahimci mai kira, gashi kuma ba zai iya amsawa a gaban matarsa ba, dan haka ya fice daga falon ya haura sama sai da ya shiga dakinsa sannan ya amsa kiran dake shigowa da zarar wani ya yanke.
"Hello..."
Fatima ta fada da karfi tana masa waving.
"Hi ya kike?"
A take murmushin fuskarta ya gushe ta bata fuska ta fara kukan da babu hawaye.
"Ba Lafiya ba, Vito yayi min fada sosai har yana cewa sai ya yanka ni, kuma Momy ma fushi take da ni bata so na, saboda na yi mata tsawa lokacin da muke tafiya a hanya dazun kuma, na je gurin titi har mota ta kusan bugeni, muka hadu da wata mata ita ma ta dinga min fada ta kai mu gida, amman ai ina fushi ne na yi, shi ne Vito ya dawo Momy ta fada masa sai yayi min fada, ni kuma na shigo daki na turo maka hotunan Momy ka duba ka gani ko kana sonta"
Daga idonsa har girarsa da bakinsa a bude suke, ya rasa ta ina zai kama zaren zancen ma, yadda ta aika masa rahonta ya saka ya manta labarin farko da na tsakiya, na karshen kawai ya rike wanda shi ya fi bashi dariya. Wato ya duba ya gani ko yana sonta, ita a tunaninta son mahaifiyarta yake.
"Me ya faru ma?"
Ya tambaya domin ya manta labarin nata, yadda ta zayyana masa dazun haka ta sake zayyana masa yanzu.
"Okay wait now, yanzu dai me kika yi ma Momy"
"Tsawa"
"Fada"
"Meyasa kika mata tsawa to? Baki san ba ayi ma iyaye tsawa ba? Babu kyau, ko a gurin wanda ba musulmai ba, balle kuma ke da kika fada min ke musulma ce, yana da ace kin fi kowa tarbiya"
"Ai musulmai ba su da kirki haka Momy tace"
"No ta yi ma musulmai mummunar fahimta ne kawai, amman musulmai sun fi kowa kyan hali da tarbiya"
"To miyasa wannan matar girlfriend dinka ta kore Momy? Why?"
"She's not my girlfriend, kawai abokiyar aikina ce, abun da ta aikata ba abu ne mai kyau ba, amman musulmai ba haka suke ba, idan kina son na yi shiri dake to karki sake yi ma mahaifiyarki tsawa"
"Amman ai bata sona"
"Inji wa tana sonki mana, idan kika bata mata rai ni ma raina zai bace, kina son raina ya bace?"
"Aa"
"Momynki ma ba zata jidadi ba idan kika bata min rai, dan haka ki daina bata mata rai kin ji"
"Zan yi tunani akai"
Yayi murmushi.
"Okay, zan duba hotunan sai mu yi magana"
"Okay, zan turo maka wasu ma idan ka gani sai ka goge komai kar Momy ta gani zan aje mata wayarta"
"Ba zan iya gogewa ba, ai na nuna miki yadda zaki goge"
"Na manta kawai na iya saka number ne, amman zan bawa Momy ta goge min"
Tana fadar hakan ta yanke kiran.
"Nooo nooo nooo nooo"
Ya fada yana girgiza kai, ya sake kiranta videos calls din amman bata daga ba, ya rasa ya zai yi sai ya zauna gefen gadonsa yana dafe goshi.
"Oh Allah matsalar yara kenan"
Ya hade yawu da karfi yana tunanin abun da zai sake yi ba, can wata zuciyar ta bashi shawarar sake kiranta sai ya sake kiran Number ta whatsapp as videos call kamar yadda suka yi da farko. Boom Emily ta amsa kiran ta bayyana gaban screen din wayarsa tana kallonsa da mamaki fuskarta kuma dauke ta hawaye. Shi ma kallonta yake zuciya na bugawa ciki na kukan rashin gaskiya.
TURHAN POV.
"Fara ce sosai, tana da jan gashi da blue eyes amman tana da kima"
"Gaskiya ba mu santa ba, babu mu da marayu masu wannan bayanin da ka bayyana"
"Ba a yanzu ba ne, ta kwana biyu fa, ita kanta yarinyar ta zama babbar mace har da yara"
"Gaskiya ba mu santa ba, amman zan bincika maka, idan na ga wani abu makamancin wanda ka fada zan nemeka sai ka bar mana information din"
Ya busar da iskar bakinsa ya kai hannunsa a kai, gaba daya ya gama zagaye gidajen marayu dake nan kusa be samu Aisha ba kuma ko'ina yaje cewa ake basu san wata mace mai wannan siffar ba. Kamar yadda suka bukata information din ya bar musu ta yadda idan an samu wani abu game da ita za a iya tuntubarsa. Sannan ya fito jiki a sanyaye ya shiga motar da suka shigo.
Ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu sannan ya dago hannunsa ya duba wayarsa, babu wani sabon sako bayan wanda matarsa ta aiko masa sai kuma na Aliyu, ya kasa amsa ko daya daga na matar har na Aliyun saboda baya cikin yanayi mai dadi. Faruk ya tashi motar suka fara tafiya, sai a lokacin ya samu sukunin amsawa Aliyu tambayarsa, tare da dora masa da wani bayanin.
"Abun da Mommy take kokarin yi a yanzu zai iya haifar da matsalar da tafi ta baya, domin har yanzu bana son yarinyar nan, kawai ina nemanta ne saboda Ammy, wahalar neman nan nata da nake sha ya saka na kara tsanarta Ammy ta kasa gane banbanci..."
Be gama amsawa ba ya dago ya kalli Faruk dake kokarin fakawa gefen titi.
"Lafiya"
"Toh gamu gani, tsohon nan ne yake ta min hannu"
"Wane tsoho?"
Turhan ya kalli gefensa, mutumen da ya tarbe su ne a gidan marayun har yayi musu iso a gurin shugaban gidan. Faruk ya sauke gilashinsa.
"Lafiya?"
"Lafiya dai ranka ya dade, kawai dai ina da bayani ne da zai taimaka maka akan neman yarinyar nan"
Turhan ya gyara zamansa da sauri yana leken tsohon da yayi jika da shi.
"Okay Sir muna jinka"
Tsohon ya kalli hanya gefe da gefe sannan ya sauka daga kan okada da yake ya sallami mai okadan sannan ya matsa kusa da su sosai yace.
"Ba zai yi na baku bayani akan hanya ba, saboda za a iya ganina a nan, hakan kuma zai iya haifar min da matsala"
Turhan ya bude motar ya fita ya bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, sannan ya koma ya zauna ya juya yana fuskantarsa. Da yaren turanci tsohon ya fara magana yana hadawa da yarbancin kamar yadda yake da farko, daman kana kallonsa kaga bayarabe tsagen fuskarsa ma ya bayyana haka.
"Na ji lokacin da kake bayani akan matar da kake nema, ai ba a neman mutum haka a babban guri irin wannan, saboda ba mu da tabbacin abun da ka fada akanta haka din ko akasin haka"
"Haka ne"
Turhan ya fada da sauri.
"Ba ni da tabbacin neman da kake mata, amman ina fatan ba zaka cutar da ita ba"
"Babu cutarwa a ciki dan Allah idan kasan inda take ka fada mana"
"Ban san inda take ba a yanzu, amman na san matar da ta dauke ta, akwai information din komai a file din gidan da nake, na san Emily farin sani domin na yi shekaru ina aiki a nan, na gane ta ne ta hanyar kamaninta daka fada amman sunanta Emily ne ba wacan sunan daka fada ba Acha"
"Mun gode sosai, yanzu zaka iya kai mu gurin matar da ta dauketa din?"
"Aa zan dai iya neman file din da addreshin matar yake sai na nuna muku ku tafi nemanta, amman a bisa sharadin guda uku"
Faruk ya kalli Turhan Turhan ma ya kalleshi suka hada ido sannan suka kalli tsohon.
"Miye sharadin"
"Sai kun yi rantsuwa ba za ku cutar da ita ba, kuma ba za ku bayyana komai akaina ba cewar ni na baku wannan bayanin na yadda za a same ta, na ukun kuma za su biya kudin bayanin da na muku a yanzu, za ku biya kudi idan na kawo file haka ma idan kun tafi gidan matar za ku biya kudi ko da ba ku same ta ba, sannan kuma idan kun ga Emily komai tsawon lokaci za ku biya kudi"
Turhan yayi murmushi, kudi daman ba matsalarsa bace, ganin Aisha ne abun da yake buri a yanzu, wai hausawa suka ce bukatar maji hajji Sallah.
___________
Kuna ganin Aliyu zai fadawa Turhan ya san inda matarsa take? Anya da gaske tsohon nan yake ko kuma dai ya shiry cin kudinsu ne.?
Ya kuke gane za a kare tsakanin Aliyu da Emily? Ga barawo ga mai kaya...! Kallon kallo akuya kallon kura... 😅 [4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣1️⃣
Ta kalli Fatima ta sake kallon Aliyu dake zube a gaban wayarta. Amman ta kasa magana.
"My bad"
Ya furta sannan ya kashe wayar, hotunan da Fatima ta tura masa ta duba a lokacin ne ta sake kallon Fatima cikin tsawa ta ce.
"Me ma'anar hakan? Ina kika san shi? Ina kika samu number shi?"
A nan kuma ta kwashe labarin komai ta fadawa mahaifiyarta, babu abun da ta boye ko ta manta tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau.
"Amman na fada miki ki daina magana da mutanen da baki sani ba, miye amfanin abun da kika yi, baki san manufarsa akanmu ba, bayan ganinsa da nake a kamfanin nan ban san waye shi ba, ban san halinsa ba"
"Cewa yayi ya sanki"
"Meyasa baki bari na gabatar miki da shi ba? Kin taba ganin na nuna miki shi ko na masa magana? Kin taba ganina tare da shi..."
Ta sake daka mata tsawa har tana mikewa tsaye kamar zata dake ta, Fatima ta razana sosai ta matsa baya tana fashewa da kuka.
"Sorry Momy"
Ta dafa kanta ya juya ta juyo gaba daya ta tsoro kamar wata marar gaskiya, can kuma ta koma ta zauna ta dauki wayarta ta aika masa da sako.
"Me kake nufi da abun da ka saka yata ta aikata? Me kake nema a yanzu? Bayan korar da kuka min yanzu kuma wani sherin kuke neman bina da shi?"
Ya duba sakon amman be bata amsa ba, kuma da alama be shirya yin hakan ba.
"Kana wasa da rayuwarka ne yaro, baka san waye ni ba, kuma bari na fada maka idan wani abu ya same ni ko ya samu yata sai ka yi nadamar zuwanka duniya"
"Boy? Huh? Hmm"
Ya rubuto mata as reply. Kana ya rubuto mata.
"Mutumen da ya fada min halinki ya fada min babu ruwanki da fitina, amman naga akasin haka, bana nufinki cutar da ke, mu musulmai bama cutar da kowa, kawai ina nemi yarinyarki ta turo min hotunanki ne saboda tantance Aisha da Emily, ina son na san banbancin wacan mai kibar da ke, ina son na gane banbancin wacan marar masifa da kuma ke"
"Waye kai?"
Ta mike tsaye tana kallon wayar gabanta na bugawa da mugun karfi. Hoton Turhan ya turo mata.
"Kin san waye wannan?"
"Aa"
Ta amsa da sauri gumi na karyo mata, sai ta kashe data ta goge chat din ta jefar da wayar akan gado, ta fara safa da marwa cikin dakin kamin hawaye su samu matsugunni a fuskarta. A nan ta fara tambayar kanta? Waye wannan mutumen tun farko? Meyasa yake bibiyar yarta da ita kanta? Yanzu kuma da ya turo mata hoton Turhan me yake nema a gareta? A kokarin samun amsoshinta ta sake daukar wayar ta bude data sai kuwa ta ci karo da sakonsa.
"Meyasa kike boya? Meyasa kika boyewa yarki gaskiyar cewar tana da uba? Why?"
Ta kasa bashi amsa jikinta rawa yake kamar yadda zuciyarta ma take rawa.
"Baki san yarki ta yi farincikin ganin mahaifinta? Baki taba tunanin samarwa yarki iyali ba? Kiran sunanta da ake da Fatima Aisha Emily be taba damunki ba? Idan yarki ta girma ta mallaki hankalin kanta wane irin amsa zaki bata?"
Nan ma bata amsa masa ba.
"Turhan yana ta nemanki babu dare babu rana, yana ta neman hanyar haduwa dake, wata kila baki san da hakan ba, amman yana da kyau ki hadu da shi ko dan yarki"
"Ba kasan komai akan rayuwata ba, baka rayu a cikin duhun da na rayu ba, har yanzu ban gama warkewa daga ciwon da zan bukaci kowane namiji a kusa da ni ba, balle kuma Turhan, ba ni da alaka da shi, alakarsa da yata kuma na yanketa, daman be san da ita, idan ya saka shiga rayuwata da rayuwar yata ne saboda ya san halin da nake ciki, to ka fada masa Aisha da ya sani a da ba ita ce a yanzu ba, kuma kar ya kuskura ya tunkaro gurin da nake"
"Ban riga na sanar masa ba, amman zan sanar masa a yau?"
"Sanar da shi zai jefa rayuwarka da tawa da tasa a matsala ne kawai, karka aikata hakan, karka jefa ni a matsala, ina da yara har biyu yanzu, kokarin gina rayuwa nake, karka maida ni a kangin da na fito, ina da kudi enough zan biyaka ko nawa kake so, zan nika maka abun da ya baka dan Allah karka sanar masa, ina son yata ina son rayuwata, farincikina kankane karka barar da shi"
Tana rubuta masa sakon tana hawaye.
"Na miki kama da mutumen da za a biya kudi a aikata wani abu? Ke kina ganina kin na girmi talauci, duk abun da kike takamar kina da shi, ina takama da ninsa sau dari"
"Amman kace kai musulmi ne?"
"Yes haka ne, babu shakka"
"Ina hada da Ubangijinka Ubangijin gaskiya, da Manzon Allah ( S A W) yace ranar tashin alkiyama Allah baya magana da mutum uku har da wanda aka hada shi da Allah be aikata ba, na roke ka dan Allah dan Allah karka fadawa Turhan komai akaina, idan kuma har ka fada masa to ka canja, dan darajar Manzon Allah S A W na san indai kai musulmin kwarai ne ba zaka aikata ba!!!"
Bayan wannan sakon bata sake aika masa wani ba, shi ma be sake cewa komai ba, ta aje wayar ta mike tsaye hawaye na cika mata ido har suna zuba ta fice daga dakin ta nufi dakin Fatima da tunin ta fice daga dakin na mahaifiyarta bayan ta fahimci nufinsa abun da ta aikata babban laifi ne. Emily ta tura kofar dakin sai ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Fatima dake kwance akan gadonta tana kuka, ta fara takawa tana tafiya jiki babu karfi, wayen da suke zubo mata a yanzu sun sha banban da na farkon. Jinjirar yarta take jangowa tana tuna lokacin da farinciki da kuma kishiyarsa suka lullube a rana daya, ranar da ta haifi Fatima, ta dauki cikin yarta ta yi rainon cikin ba tare da sanin Turhan ko danginsa ba, ta raini yarta irin rainon da bata fatan ko makiyinta ya fuskanci rayuwar data fuskanta, ta tuna lokacin da Nurses suke fadar a kawo kayan jaririya, kuma aka rasa abun da za a lulluba mata sai da wata ta taimaka mata da zane daya, ta tuna tsawon kwanakin da Fatima ta dauka a hannunta tana lullubeta da zane saboda babu tufafi.
Chapter notes and social links
Ya fito wanka rike da karamin tawul yana goge jikinsa sai da ya gama sannan ya zauna gefen gado ya dauki wayarsa yana duba whatsapp dinsa, domin a yanzu ba shi da wani abu mai muhimmancin kamar jiran amsar Turhan, gashi kuma har yanzu Turhan be amsa masa ba bayan kuma ya karanta sakon nasa. Yaje wayar yayi ya mike tsaye ya fara shafa mai ya shirya tsab cikin shigar kanana kaya black T-shirt and White jean, yana tsaka da fesa turare Aisha ta shigo dakin, fuska ba yabo ba fallasa tana kallon bayansa har ta karasa kusa da shi.