Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 11

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 11

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 11: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 11. Ta tuna yadda ruwan nononta yake kafewa saboda yunwa har sai da ta…

3,342 words

Ta tuna yadda ruwan nononta yake kafewa saboda yunwa har sai da ta saci nonon akuya ta shayar da yarta, ta tuna yadda ruwa yake dukanta a rumfar wani bakanike da take fakewa idan dare yayi, ta tuna yadda take bin gidajen masu hali tana neman abun da zata kai a ciki, taya rana tsaka a yanzu Turhan zai bayyana yace nemanta yake me yake nema a gareta? Ya rabata da yarta kamar yadda ya rabata da sauran farincikin da ya rage mata a wacan lokacin? Ya sake dawowa rayuwarta ya haifar mata da matsala? A yanzu ta samu mai bata komai yayi mata ginshiki shi ne yake neman rusawa? Ta kai hannu ta dago yarta, wani mummunan furuci da yayi mata a wani lokaci da farinciki ya juya mata baya ya dawo mata.

"Karki sake nuna kin san ni, akwai banbanci tsakanina dake"

Ta lumshe ido tana tuna wata rana da matarsa ta saka bayinta suka yi mata bulala yana kallo be yi kokarin hanawa ba har sai da suka bar mata tabo a jiki. Ta rumgume Fatima, wani kalar ruwan hawaye ne yake mata zuba mai zafi da dacin zuciya, ashe duk bayan wannan zai dawo nemanta?

"Momy me yasa kike kuka? I'm sorry"

Tambayar Fatima ta dawo da ita hanyacinta, sai ta bude idon ta share hawayen tana murmushi.

"Ina sonki Fatima, no matter what happen, daga ke sai London ne Iyalina, na wahala na yi sadaukarwa kamin ku kawo inda kuke a yanzu, a yanzu ma ban gama ba dan Allah kar wata rana ta zo ki fifita wani akaina"

Ta rumgumeta, sun dade a haka sannan ta sake ta tashi ta fice daga dakin, kasa ta sauka ta zauna a falo zuciyarta cike fal da tunani. Vito be dawo gidan ba sai after 8pm, ya shigo falon tare da Chidimma dake rike da leda tana biye da shi a baya. Emily ta kalleshi ta kalleta.

"Ina London?"

"Bachi yake, na zo na dauki wasu abubuwan ne na yi wanka"

Ta maida dubanta gurin Vito, ya san abun da take bukatar ji tun kamin ta gabatar masa da tambayar ya bata amsa.

"Ya sauko ya daina fushi, na yi magana da shi"

"Thank you"

Ta gyada mata kai kawai, sannan ya kalli Chidimma.

"Ki shirya da wuri direba zai maida ke asibitin kar a barshi shi kadai"

"Okay Sir"

Ta amsa tana wani karairaya daman idan shi ya bada umarni ba ta bata lokaci take aikatawa. Sai da ta fice Emily ta maida dubanta gurin Vito da idanuwansa suka dade a fuskarta.

"Zan tafi na kwana can"

Ya amsa mata kawai da ido sannan ya nufi kujera ya zauna, ita kuma ta haura sama ta shirya ta fito ta shiga dakin Fatima ta yi mata sallama sannan ta sauko suka fice a tare, ya rigata isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya nufi bangaren da Chidimma take ya fada mata an samu sauyi zata kwana da Fatima saboda Emily zata kwana da London a asibiti, ya dawo motar ya ke kunne tun a lokacin da ya faka a harabar, daman a ka'ida baya kashe mota sai idan ya gama fita gaba daya a wunin ranar. Yana tukin yana karantar yanayinta har suka isa asibitin.

"Aikin fa?"

"Na aje"

Ya kalli irin kallon mai cike da tambaya, sai ta sauke kanta kasa tana taba yatsun hannunta.

"Saboda na bawa yarana lokacina"

"Ko dai sun koreki?"

Ya tambaya ne kawai ba dan hana da tabbacin haka din ba, domin ya san yadda ta kwalla fa rai da son aikin kuma har ta fara zuwa ba karamin abu zai saka ta aje aikin ba. Ta bude motar ta fice ba tare da tace masa komai ba, yana daga cikin motar yana kallonta har ta shige ciki sannan ya ciro wayarsa ya duba time, sai kuma yaja motar ya fice daga asibitin.

ALIYU POV.

Ya hade yawu a hankali yana mamakin yadda aka yi ta san hadisin da ta kafa masa hujja da shi, ta san addinin musulunci ne har haka? Ta yi nisa a ciki? Me yasa ma ta bar addinin tun farkon fari. Ya sake karanta sakon ta dayan bangaren yana nisa tunanin a wani bangare na labarin da ta gutsura masa, gashi kuma ta daure shi da kalamanta, be rabi Turhan a zamanin da suka yi rayuwa a Emily ne, dan haka ba zai iya shaidar kyautata ko kishiyarsa a tsakaninsu ba, amman a neman da Turhan yake mata a yanzu da kuma gudunsa da take zai iya fahimta daga rayuwarsu. Sama yayi kadan ya sake kallon hotunan da Fatima ta turo masa, Emily ta kai mace har ta wuce, and ya yaba da yadda hotunan duka basu bayyana tsiraicinta ba duk kuwa da kasancewar ba musulma ba. Ya fita daga chat dinsa da ita ya shiga na Turhan, ya sake karanta sakon da ya aiko masa a dazun.

"Na aureta ne a bisa cilastawar Ammy ba dan ina sonta ba, she's not my type at all, kuma adadin na ji ina sonta sai ma kiyayya ce ta ginu a tsakaninmu, har dai shedan yafi karfina na rabu da ita, amman ban cutar da ita ba"

Kana ta karanta dayan sakon dake biye da shi, a take jikinsa yayi sanyi zuciyarta ta karaya, ya san abokinsa yana neman Emily, and yes ya samu Emily da kuma tabbacin ita din ce, amman yana tsoron kar haifar mata da matsala, ka ya sakata a wani hali kamar yadda ta fada, ta dayan bangaren kuma yana tunanin ya zai yi da abokinsa, idan yayi shiru anya ya kyauta masa kuwa? Ya sani idan Turhan ko mahaifiyarsa suka san da Fatima ba za su bar mata ita ba.

"Lafiya kuwa?"

Aisha ta tambaya tana aje Bowl ta kunna tap ta wanke hannunta tana kallonsa irin kallon nan na jiransa.

"Tun da ka amsa wayar dazun na ga yanayinka gaba daya ya canja"

"Ba komai"

"Ko dai akan yarinyar da aka kora ne?"

Yayi murmushi ya dago daga jikin fridge.

"Ba ita ba ne"

Ya saka wayar aljihu ya nufeta ta rikata suka fice daga kitchen din tana masa zancen business din da take son ta fara.

"Watan cin kudin nawa ya tsaya kenan?"

Ta kyalkyale da dariya.

"Kasan ai kana cewa na rika sana'a"

"Ke da baki san kowa a nan ba, taya zaki fara sana'a, kuma kin san ina binki kudi fa"

"Namiji idan namiji ya rantawa matarsa kudi daman ai bata biya, amman shi idan ya ranta sai ya biya"

"Saboda shi namiji be san zafin kudinsa ba ko?"

Ta saka dariya a tare suka zauna ta kwanta jikinsa tana taba jira kadan bachi yayi gaba da ita, a hankali ya zaro wayarsa wani abun na cizon zuciyarsa ya sake bude sakonta ya karanta a karo na biyar, abu ne da yake bayyana a gurin kowa, zuciyar kowace mace kyakkyawa ce, sai dai wanda ta bar shaidan ya rinjayeta, ko kuma wanda wasu gurbatatun mazan suka yi ma illa. Akwai tambayoyin da yake bukatar amsarsu a gurin Emily, yana son ya ji kadan daga dalilinta na hana yarta da ita kanwata zuwa ga abokinsa dake nemanta kamar zai salwantar da rayuwarsa wata kila hakan ya taimaka masa gurin karfafa rokon da ta yi masa.

Sai dai kuma ba lallai ta saurare shi ba, ba lallai ta yarda ta maida shi duniyarta ta baya ba, yana bukatar ganinta face to face domin amsa masa tambayoyin da ita kadai take da amsarsu. Amman kuma? Anya zata yarda su hadu? Zata yarda ta fada masa a inda zai same ta ko ta same shi? Ya shiga contact list dinsa ya tabo William ya aika masa da sako.

"Please kana da wani information na gurin da Emily Aisha take zama"

William ya masa reply Immediately.

"Wace Aisha?"

"Yarinyar da ka zo kana ta santi, wata half Cast haka mai jan gashi da blue eyes"

"No wani abu ne ya faru?"

"Yeah sun yi fada da Amal ne, har ta bar aikin ina bukatar ganinta face to face na bata hakuri kuma na mata bayanin yadda abubuwan suke"

"Meyasa ka tambaye ni? Sau daya na ganta ban sake sakata a ido ba"

"Saboda baka shigowa Office ne a yanzu, na dauka ko kuna gaisawa da juna ne, na ga ta sace maka zuciya ne"

"Ta sace mana zuciya dai"

"Nooo sam ba abun da kake tunani ba ne, idan ma kishi kake ka daina, ni ai musulmi ne, kuma ni bata cikin tsarin matan da nake so ma?"

"Bata maka kyau ba"

"Bana son macen da ta cika kyau sosai, kyaun idan yayi yawa yana zama illa, kuma ni bari da burin kara aure yanzu ko nan gaba"

Ya dauki William tsawon mintuna talatin kamin ya aiko masa da address din har da number gidan da take zaune.

"Thanks"

Aliyu ya rubuta masa a as reply.

"Me ya hada ta da Amal?"

"Idan mun hadu zaka ji"

Ya amsa masa sannan ya saka wayar alijhu cikin jindadi, ya rika matarsa zuwa bedrooms dinsu bayan ya kashe komai na falon.

#TeamTurhan #TeamVito

A ina kuke?

#KhadeejaCandy [4/20, 10:00 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/Dfp3nf5JwbA22eFdvKklyG

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

Page 1️⃣2️⃣

Assalamu Alaikum. Barka mu da Sallah. Allah ya karbi ibada ya maimaita mana.

*** ***. ***.

Ta tura kofar dakin ta shiga fuskarta dauke da murmushi.

"Hello my beautiful boy"

Ya kalleta kawai ya dauke kai ba murmushi babu far'a kuma babu fushi, ta karasa kusa da shi cike da karfin guiwa ta zauna a kan gadon, hannu ta kai zata shafa shi a take ya saka mata ihu. Da sauri ta janye hannun, ta mike tsaye ta matsa gefe.

"Ka yi hakuri London I'm sorry"

Ta hade yawu tana kallonsa rashin jindadin dake zuciyarta ya bayyana a fuskarta. Hannu ta saka a aljihu jean din dake jikinta ta ciro wayarsta ta yi dialing din number Vito. Ta juyawa London baya hannunta daya a kan lebenta tana cizon akaifarta idonta tab da hawaye.

"Na dauka ka yi magana da London kace min ya hakura fa"

"Yeah na masa magana kuma ya hakura"

"Amman na zo yanzu yana min ihu, baya son na taba shi"

Vito yayi shiru for few seconds yana karantar yanayinta

"Kuka kike yi?"

"To me zan yi"

Ta fada a tsawa tana shessheka kuka kai kace shi yayi mata laifin. Daker ta iya hade yawu sannan ta kashe wayar ta juyo tana fuskantar London, rasa makamar yadda zata ba shi hakuri ya sakata ta zauna a gurin tana cigaba da kallonsa har lokacin hawaye sauko mata suke, tunanin rayuwar da ta yi kamin ta haifi London da kuma wanda ta yi bayan haihuwarsa, da yadda rayuwarsa ta zo mata, halin da ta shiga fargabar matsalar saninta da Aliyu yayi a yanzu duk suka taru suka mata tsaye a cikin kai.

Sai da ta yi da gaske sannan ta iya runtse ido tana maida numfashi a hankali, sai kuma ta kai hannu ta shafa sarkar cross din dake wuyanta. Wayarta ta fara ringing alamar kira, tana kallon kiran har sai da ya kusa yankewa sannan ta amsa ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba.

"I have to take care of something, ba zan iya zuwa ba, amman na yi magana da wani abokina yace akwai wani abokinsa kwararen likitan kwakwalwa, kuma ya shigo garin nan yin wani abu, zai shigo ya duba London kamin ya wuce"

"Dana ba mahaukaci ba ne Vito, ciwo ne kawai yake damunsa"

Ta rufe da fada zuciyarta na bugawa da karfi tsabar bacin rai, ya san yadda zai tafi da ita dan haka yayi shiru be ce komai ba sai na tsawon lokaci.

"Zan aje wayar"

Ta fada jin be ce komai ba har na tsawon minti biyar.

"Na sani, kawai zai duba shi ne ya bashi ya bamu shawarwari wata kila za su taimaka mana"

Tare da ta sake cewa komai ba ta kashe wayar, daga inda take zaune take kallon danta har bachi ya fara daukarta tana angaje har ta kai ta kwanta a gurin, bachi mai nauyi yayi gaba da ita, bata farka ba sai kusan asuba, ta bude idon tana hamma ba tare da ta rufe baki ba, dagowa ta yi kadan ta leki London, ganin yana bachi ya bata karfin guiwar mikewa tsaye ta karasa kusa da gadon da yake kwance ta zauna, ta mika hannunta a hankali ta shafa fuskarsa zuwa kansa, tausayi yake bata sosai saboda lalurar da yake dauke da ita, ba zabin mutun bane ya kasance a yadda yake so, ko kuma waninsa ya kasance a wani hali na dabam marar dadi, abu ne sa yake tsare tun gabanin halittar rayuwa, an rubuta yadda dan'adam da rayuwarsa zata kasance.

Knocking aka yi sau biyu da two fingers, da sauri ta dago ta kalli kofar dakin hakan yayi daidai ta turo kofar dakin da aka yi aka shigo. Cak ta tsaya tana kallon mutumen da ya kasance bakuwar fuska a gurinta, kamar yadda shi ma yake tsaye yana kallonta.

"Lafiya?"

Ta tambaya ganin ya gagara karaso, haka kuma ya gagara cewa komai. Takawa yayi baya ya ja mata kofar ya rufe, bata gama mamakin waye shi da kuma dalilinsa na aikata hakan ba, ya sake turo kofar dakin ya shigo with full confidence... Kallonsa take har ya karaso kusa da ita idonsa cikin na ta.

"Sunana Doctor Adam Bello amman an fi sanina da Dr A-B kwararen likitan kwakwalwa, ina aiki a asibitin Special Care Hospital dake Abuja, abokina ya fada min akwai wani yaro da zan duba a dakin nan, wanda nake kyautata zaton kanenki ne..."

Ya karasa yana kallon London dake bachi, zuciyarsa na raya masa kanenta, a yanayin halittar jikinta da kuma kurciyar dake fuskarta ba su bar masa alamar da zai aje London a matsayin danta ba.

"London ba mahaukaci ba ne"

Ya daga girarsa biyu kadan ba tare da ya kalleta ba.

"Ni ma ban ce ni likitan mahaukata ba ne, mutane ne suke kuskuren fahimtar ciwon sai suke ganin kamar hauka ce"

Ya kai hannu ya kama hannun London yana taba tsatsunsa a hankali.

"Fada min idan kanenki ya farka yana farkawa a firgice? Idan babu kowa a kusa da shi?"

Ta daga masa kai alamar eh.

"Wane kalar turare ya fi so?"

Har lokacin be kalleta ba.

"Ban taba lura da wannan ba"

"Uhm, da wa yake yarda? Bayan mahaifiyarsa da Babansa da kuma ke?"

"Dana ne ni na haife shi"

Sai a lokacin ya sake kallonta, ya dauke shi tsawon dakika biyar kamin ya iya dauke idonsa daga kyakyawar fuskarta mai matukar daukar hankali.

"Ya kamata ki san kalar turaren da yake so, his favorite color, wane kalar cartoon yake so, wane kalar wasa yake so, wane yanayi yake shiga idan yana kuka, su waye mutanen da yake so, ki fahimci idan yayi bachi wane kalar mafarki yake? Ya yanayin sakewarsa da mutane yake?"

"Na san wasu daga ciki, amman dai shi ba mahaukaci ba ne"

Yayi murmushi ya kalleta.

"Da alama zaki sha wahalar rayuwa kamin ki fahimci duniya da mutanen cikinta, ni dai ina baki shawara ne kawai na yadda abubuwa za su miki da sauki tsakanin ke da... Danki..."

Ya fada tare da jan zaren furta kalmar danta kamar mai jin nauyin alakantata da jininta. Sannan ya ciro katinsa a aljihunsa ya mika mata.

"Bana kallon marar lafiya a free ma, balle kuma magana da shi, sai an yi min biya mai kyau, amman da yake ke tafe kike da sa'a, sai ga shi an lallaba ni na zo har asibitin da kike na duba danki kuma na baki shawarwari a free, so hare is my card idan kina son wanin hakikanin waye danki, taya zaki zauna da shi, wane mataki zaki bi har ki yi nasarar sauya rayuwarsa, da kuma yadda zai samu lafiya, sai ki bi matakin da yake kan card din"

Ya aje mata card din ya juya ya fara tafiya.

"Bama bukata daman ka zo nan ne dan ka ci kudinmu ko? Toh ni na san waye ďana kuma shi ba mahaukaci ba ne"

Juyowa yayi yana murmushi.

"Halinku daya sak da matar direban direban Babanmu, amman kuma da ta bi shawarwarin da na dora ta a kai da magani, sai ga shi ta dawo tana min godiya"

A kokarinsa na fahimtar da ita kudi ba matsalarsa ba ce kamar yadda take zato ya ambato mata direban direban babansu.

Da farko she was confused kamar ya Direban direban babansu kamin ta sake kallonsa cike da mamaki.

"Direban Babanku?"

"Nope Direban Direban Babanmu"

Ya furta yana hade lips dinsa.

"Direban Babanku yana da Direba kenan.?"

"Uhm"

'Wane irin kudi babanku yake da shi haka ne? Da har direbansa yake da direba?'

Kamar ya san tambayar da ta yi ma kanta a zuciyarta sai ya taka ya matsa kusa da ita, yana kallon kwayar idonta.

"Babanmu na da kudin sosai, kwatankwacin yadda kike da kyau sosai mai jan hankali"

Ya fada cikin wata murya na irin mutumen da kuzari ya bar jikinsa, gaba daya kyauta ya gama rudashi. Ta hade yawu da karfi tana kallonsa.

"Akwai wata tambayar ne?"

Ta kasa cewa komai, ya kalli agogon hannunsa.

"Lokacin sallah yayi, duk lokacin da kika shirya bata kudinki, zaki iya nema till then good bye"

Ta matsa baya ya fara tafiya.

"To miye amfanin zuwanka? Baka duba yaron ba baka fada min komai ba taya zan tabbatar da kwarewarka ko akasin haka?"

Tana maganar tana daga kafadunta.

"Ko ba komai ai na auna nauyin kyaunki na fada miki matakinsa, yanzu kin san darajarsa"

Ya fada sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ta bi bayansa da kallo har ya fice, sannan ta sauke numfashi ta kalli card din da ya bar mata, ta kalli danta, sai kuma ta dago wayarta ta shiga camera tana kallon fuskarta. Ita kan bata ga wani banbanci a tsakanin kyauta na jiya, shekaran jiya da kuma yau ba. Mai da wayar ta yi ta aje, tana nan tsare da danta har ya farka misalin bakwai da yan mintuna.

"Good Morning Sunshine"

Suna hada ido sai ya koma ya kwanta ta rufe ya bata fuska sosai kamar zai yi kuka.

"Chichi chichi"

"Okay zata zo yanzu"

Ta fada ba dan ranta ya so ba sai dan Chidinma ta fi soyuwa a zuciyar danta fiye da ita a yanzu. Ta dauki wayarta ta nufi kofar dakinta ta bude fice tana jin kamar ta fasa kuka. Ta fito asibitin sai ta tsaya a harabar tana kallon mutanen dake hada hada kamar wacce ta rasa abun yi, gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Daga inda take tsaye ta dagawa wata matar dake tunkaro inda take hannu matar ma ya dago mata tana murmushi. Emily ta fara takawa ta karasa gurin matar dake tahowa.

"Sannu kin gane ni?"

Matar ta dan yi jimmm kamin ta amsa.

"Eh kamar ke ce na kusan kade yarinyar ki ko?"

"Haka ne, kina aiki a nan ne?"

"No na shigo kawo ma wata abincin ne, ke fa?"

"Yarona ne ba shi da lafiya"

"Da sauki amman?"

"Eh"

"Allah ya ba shi lafiya"

Tana fadar hakan ta wuce abun ta ta bar Emily tsaye a gurin da mamaki kuma da takaicin yi mata magana da yi.

"Okay…"

Ta fada sannan ta juya tana kallonta kamin ta tsuke baki ta cigaba ta tafiyarta, tana fita wajen asibitin ta dauki drop zuwa unguwarsu. Har ta isa gida haushin kanta take ji meyasa ta yi ma Matar nan magana gashi ta wulakantata.

"Chere m, a ga m ala n'ulo nweta ego gi ugbua"

Ta fada masa da yaren Igbo cewar ya dan jira zata shiga gida ta dauko masa kudinsa.

"Okay"

Ya amsa mata ta nufi gate din ta buga, mai gadinta ya fara lekowa ya ga ganta madadin ya bude mata sai ya bude ya fito ya nufi motar da ta shigo ya leka mai motar, hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin be taba yi mata haka ba.

"Me ya faru?"

"Babu komai ranki ya dade"

Readers Also Read