Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 3
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 3: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 3. Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da…
3,313 words
Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da ita. Har ta isa first floor bata hankara ba sai da kofar ta rabe biyu, ta fita ba tare da ta lura da mutanen da suke tsaye suna kokarin shiga elevator ba. Daya daga cikinsu ya biyo bayanta a sirance har sai da ta yi rabin gate din dake da tsayi sosai.
"Excuse me Miss"
Ta juyo ta yi sai ta yi arba sa wani bakin mutum bayanta yana sanye da yellow t-shirt da black jean.
"Can i help you?"
"Yes"
Ya matsa kusa da ita.
"Kin shigo neman wani abu ne? Ko kina daya daga cikin team din Resrezor?"
"No na fara aiki a nan ne"
"Yaushe?"
"Yau"
"A ina? Wane guri office dinki yake?"
"Four floor hannun hagu office na biyu"
"Nice to meet you, I'm William, ina 5 floor office na hudu"
Ta mika masa hannunta kamar yadda ya mika mata nasa.
"Emily"
"Nice to meet you Emily, kin samu aboki yanzu"
Ta yi murmushi tana kallon sarkar Cross din dake wuyansa hakan sai ya saka ta ji dadi ganin kirista ne dan'uwanta.
"Har kin tashi ne?"
"Eh"
"Okay Bye"
Ta yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya tsaya a gurin yana kallon yadda wandon jikinta ya dame jikinta yayi mata kyau.
"Wow..."
Ya shafa kansa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Ta isa gida da wuri saboda ta samu abun hawa da wuri, sai da ta sallame shi sannan ta kwankwasa kofar gate din. Mai gadin ya bude mata ta shiga tana amsa gaisuwarsa. Tura kofar falon ta yi ta shiga sannan ta rufe ta cire talkamin kafarta ta saka na falon sannan ta karasa ciki. Ganin kwalbar giya aje a tsakiyar center Table din dake falon ya karantar da ita V ya bar gidan cikin bacin rai, domin abu ne da ta sani, idan ransa ya bace giya yake sha ko marijuana.
Da sauri ta jefar da Jakarta da file din hannunta ta nufi dakin da London yake ta bude gabanta na faduwa, ta duba dakin har bandakin baya ciki, hakan ya saka hankalinta ya kwanta domin shan abun maye ko drugs abu ne da bata son yana yi a gaban yaranta, wannan yana daya daga cikin dalilin da ya saka ta zabi raba gida da shi, ta zabi rayuwa ita kadai sai yaranta. Fitowa ta yi ta dawo falon ta dauke kwalbar ta shiga Kitchen ta tsiyaye ragowar barasar dake ciki ta fasa kwalba ta zuba a dustbin sannan ta wanke hannunta ta fito.
A gurin da ta jefar da jakarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, tare da daga kanta tana kallon rufin falon zuwa gurin da katon plasma ta yake. Ta sani ahalin yanzu bata rasa komai ba sai kwanciyar hankali, Vito ya jika da kudin da bata jin akwai wata mace mai tarin dukiya irinta, ita kanta bata san adadin abun da ke account dinta ba, domin kowane sati sai ya saka mata kudi ita da yaranta London da Fadima duk kuwa da kasancewar karamar yarsa Fadima bata son shi, amman be taba kula haka ba saboda yana matukar kaunar mahaufiyarta.
A cikin gidan da take rayuwa gidane da ko wucewa kawai ka yi a gaban gate din sai hankalinka ya tashi saboda kyaunsa, shi kansa nasa gidan be kai nata kyau ba, ya zuba mata kayan more rayuwa daga sutura har abubuwan ado na kawata falo ko daki, ga mayan motoci da ya zuba mata a cikin gidan, ga Nannyn da ya dauka mata mai kula da yaronta, ya saka yarta a makarantar kudi ta yayan manya, London kuma da ya kasance Autism ya biya ake karantar da shi a gida. Bayan kudin da ya biya aka yi mata aiki, ya kaita waje ta yi karatu. Amman duk da haka tana jin ta rasa wani abu a tare da ita, she felt something is missing inside her. Ji take bata cika ba har yanzu, tana jin akwai abun da ta rasa kuma bata san miye wannan ba, sai dai ta san dalili daya da ya saka take son tsayawa sa kafafuwanta, wannan sirri ne da ba zata iya budewa kowa shi ba.
"Good Afternoon Ma"
Cewar Chidimma bayan ta shigo falon. Emily ta kalleta da irin fuskar nan na wanda tunani be gama sakin kansa ba.
"Chidimma, a gaban London V ya sha alcohol dazun?"
"Aa bayan na shiga dakin Landon ne na canja masa tufafi saboda za su fita tare"
Ta sauke numfashi a hankali.
"Okay please duk yadda za'ayi karki bari yarana su ga lokacin da Vito yake shan giya, balle har hannunta ya kai gurin"
"Okay Ma zan kiyaye"
"Ki shirya musu wani abu ni zan yi bachi"
Tana fadar hakan ta mike tsaye ta dauki jakarta da file din ta haura sama ta shiga dakinta ta aje jakar da file din a kusa da gadonta ta kwanta, tunani ya fara kawo mata ziyara kamin bachi yayi gaba da ita.
ALIYU POV.
Dagowa yayi a hankali ya kalli kofar office din da aka turo. Mutumen ya karaso gaban teburin cike da girmamawa ya bude masa daya daga cikin files din da suke hannunsa.
"Nan zaka saka hannu"
Sai da Aliyu ya gama abun da yake a computersa sannan ya kalli file din ya saka hannu.
"Ranka ya dade cikin sabin ma'aikatan da aka dauka har da turawa?"
Cewar mutumen dake tsaye gabansa, shi dai be ce komai ba, har sai da ya gama saka hannu a duka files din.
"Na ganta zata fita dazun"
Aliyu ya sake dubansa ba dan ya fahimci inda zancensa ya dosa ba.
"Baka ga sabin ma'aikatan na mu ba"
"Ba ni nake da hakkin ganinsu ba, ban san suwaye aka dauka ba"
"Wata baturiya ce fara kyakkyawa har ta fika haske ga blue eyes"
Aliyu ya dan yi jimmm alamar nazari can kuma sai yayi murmushin da ya kara masa kyau.
"Ka ganta kenan?"
"William, na ganta and what?"
"Tana da kyau, ga fari duk yadda aka yi wannan yarinyar baturiya ce ko half cast, na gode da ka dauketa, and finally kirista ce yar'uwata"
"Ka godewa Amal aikinta ne not mine, ni ban san su waye aka dauka aiki ba ma"
Ya aje zaren zancen a daidai lokacin da wayarsa ta ringing. Kallon wayar yayi yana murmushi.
"Shiyasa ake daudararku koda yaushe kyaun kuke bi ba hali ba"
Ya amsa kiran ya kara wayar a kunnensa, at the same time da William yake fadar.
"Ka rantse da Allah ka na musulunci cewar ka taba ganin yarinyar da ta fita kyau? Ni fa rudewa na yi na kasa rike kaina sai da na yi mata magana"
Da sauri Aliyu yayi saurin yi masa alama da hannu na yayi shiru ya yi tafiyarsa. William zip up his mouth yayi ta tafiyarsa.
"Hello yar kyakkyawata"
"Na'am ya aikin?"
"Alhamdullahi ya cikin?"
"Ban sani ba"
Ya saka dariya daman da neman magana ya saka shi tambayarta.
"Miye laifina dan na tambaya?"
"Ni dai ban sani ba, kawai dai na kira na fada maka Gwaggo ta kira tace Anty Sa'ade ta haihu"
"Maa shaa Allahu, me muka samu?"
"Irina ce aka samu"
"Ki ce irinki marar jin magana ko?"
Ya fada yana wani abu da ido kamar tana gabansa.
"Ba zaka daina ba ko?"
"Na daina yar shawalwalar yarinyar yar dirarar yar black beauty na kyakkyawata"
Ta yi dariya.
"Bye sai ka dawo"
"Okay mai ciki"
Yana fada ya kashe wayar da sauri yana dariya, sannan ya aje wayar ya maida hankalinsa gurin aikinsa.
TURHAN POV.
Ya aje mug din tea dake hannunsa.
"Yadda kasan yarinyar nan ta yi ma Ammy magani haka ta juya min baya, gaba daya na kasa gane kan mahaifiyata"
Mannir dake kallonsa ya ce
"Amman dai ka san abun da ka yi mata baka kyauta ba? Baka ji haka ba?"
"Na san ban kyauta ba Manir kuma na ji babu dadi, ina kan jin babu dadin ma a duk lokacin da na tuna, amman yadda Ammy ta hau karamin abu ta maida shi babba shi ke daga min hankali kuma ya ba ni mamaki"
"Iyaye sai hakuri, kuma kasan Ammy ta dora hope sosai akanka game da yarinyar nan, sai kuma gashi ka bata kunya, waya sani ma da ace ita kake aure har yanzu wata kila da yanzu kun haihu, gashi nan wannan yarinyar da ka fifita akanta har yanzu baka baka ďa ko ya ba"
A take yanayin Turhan ya canja duk kuwa da ya san gaskiya aminin nasa yake fada, kuma samu ďa ko ya wani abu da yake fata kuma ya dade yana mafarki.
"Mace bata bawa kanta haihu, duk wanda ka ga ya samu haihuwa hukuncin Allah ba yin kansa ba"
"Haka ne, sai dai kuma wata kila yana cikin dalilin Ammy na yin fushi da kai, kuma yarinyar nan fa abar tausayi ce"
"Na sani, amman Manir ana samun sabani sosai akan abubuwa kuma sai ka samu iyaye sun yafe sun duba dansu, amman ni Ammy ta kawar da idonta a kaina gaba daya"
Manir ya sauke ajiyar zuciya.
"Yanzu ka aje duk wani hange hange da tunanin banza, ta ina zamu fara?"
"Nemanta, zan shirya duk abun da zan yi a yau, gobe zan sauka Lagos zan fara nemanta"
"Wane tabbaci kake da shi cewar tana Lagos?"
"A can aka haife, acan ta taso kuma bata san kowa a nan arewa ba, kamin ta bar nan Ammy ta fada ta ganta a coci, bana tunanin zata iya zama garin nan ma gaba daya, idan har zata zabi zama cikin kista yan'uwanta ba ta da wani gida da ya wuce Lagos, matsalar kawai a Lagos din ban san wane gida take ba"
"Shi ne Matsalar, kuma Ammy bata ffada maka wane gidan Marayu ta zauna ba?"
"Bata fada min ba, amman dai zan yi ta bincike har na gane"
"Baka san kowa a Lagos ba, nemanta ba zai maka sauki ba, gaskiya Ammy ta dauki abun nan da zafi"
Turhan ya busar da iskar bakinsa.
"Zan tuntubi Aliyu yayi zama Lagos kamin ya koma Port Harcourt, maybe zai iya hada ni da wani da zai iya taimaka min mu yi neman tare"
"Oh na manta ma da shi Wallahi, ka yi masa magana mu ji ba zai rasa wanda zai taimaka maka gurin nemanta ba, ni kuma zan yi ta lallaba Ammy a nan ko zamu samu wani abu daga gurinta"
Turhan ya sake daukar Mug din ya sha tea.
"Ta fa yafe min, kawai dai ita wai yadda muke a da ne, ta ki ta dawo min a haka"
"Irin wannan ai sai ya saka ka ji ka tsani yarinyar, ko da yake.."
Manir yayi shiru ba tare da ya karasa ba. Turhan ma be sake ce masa komai ba ya maida dubansa wani gurin sai tunani yake.
EMILY POV.
Jin an taba fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali tana kallon Vito dake zaune gefen gadon kusa da ita. Tashi ta yi zaune tana kallonsa, kallonta yake shi ma irin kallon nan mai cike da kauna, sai dai girman kai da jin isa ya hana shi sakin fuska balle har ta ga murmushinsa.
"Ina London?"
"Yana dakinsa, me yasa baki fita da mota ba?"
"Bana son kowa ya san wani abu akaina, na fada maka wata sabuwar rayuwa nake son yi"
Ta yaye blanket din dake jikinta ta matsa ta saka kan gadon ta dayan gefen, sai yayi hanzarin rikota ya juyo da ita da karfi.
"Fita mota zai hana wani abu daga canjin rayuwar da kike so ne? Mi kike shiryawa ne Emily?"
"Me kake tunanin ina shiryawa? Na sha fada maka ina son na yi rayuwa kamar kowa, ina son rayuwata ta zama daidai, dole ne sai na shiga mota? Bana ra'ayin haka? Me yasa kake cilasta ni yin abubuwan da bana ra'ayi? Why?"
Ya matsa kusa da ita sosai yana kallon cikin idonta.
"Saboda ni kadai na isa na cilasta ki, kuma idan tunaninki ko shirinki na rabuwa da ni ne, to kina shiryawa kanki wani rame ne na halaka, domin ban gane duk wannan abun da kike ba? Me ye ban aje miki ba? Amman tunaninki yana wani gurin dabam, ke tawa ce har abada ba zaki iya guje min ba ki saka wannan a ranki, you're forever mine"
Ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata amman ta kasa.
"You're hurting me..."
Ta yi magana cikin yanayin dake nuna tana daf da fashewa da kuka.
"Mami"
Jin muryar Fadima ya saka shi saurin sakin hannunta domin ko kadan baya cin zafinta a gaban yaranta ko da kuwa me ta yi masa. Emily ta nufi kofar da sauri tana budewa murmushin dole ya ci karfinta a yayinda take kallon Fadime dake kokarin sauke school bag dinta.
"My Baby kin dawo"
Ta karasa kusa da ita ta rika mata jakar, Vito ya fito daga dakin ya karaso kusa da su.
"Lisa"
Ya kai hannu zai shafa kanta, haka yake kiransa saboda ya tsani sunan da Emily ta saka mata na musulmai. Sai ta kauce daga taba kanta da zai yi tana hade rai.
"I'm not Lisa I'm Fadima"
Hakan kuma be hana shi yin gutun murmushin da yayi niya ba, domin idan da sabo ya saba da halin yar Emily na nuna masa kiyayya a fili wani sa'in har ta kan fada masa bata son shi, duk kuwa da irin hidimar da yake da su. Ta kaunce daga gurin gaba daya ta nufi dakin dan'uwanta, daga Emily har Vito binta suka yi da kallo.
"I don't know why, Lisa hate me so much"
"Yarinya ce zata daina nan gaba"
Emily ta amsa masa tana kokarin kare yarta, ta san shi ma be cancanci irin wannan kiyayyar daga gurin yarta ba.
"I hope so, i can't ki haifo min babyn da zata kira ni da babanta"
Ya fada yana kallonta tare da karantar reaction dinta.
"I thought i told you ni na gama haihuwa"
"Nope... Baki gama ba sai kin haifo na wa"
Kallonsa kawai ta yi ta dauke kai ta nufi hanyar kitchen, binta yayi da ido har sai da ta shige sannan ta juya yayi ficewarsa. [4/20, 9:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Barka da warhaka mutanen arziki😍
Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda ɗan mutum da mutum😃
Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser.
Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ɗina.
Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp.
KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less...😊
Page 4️⃣
Ragowar cake din dake fridge ta dumama musu, ta dumama madara a microwave sannan ta zuba a plate biyu kowa da cups dinsa sannan ta fito kai tsaye ta nufi dakin London ta shiga da murmushinta sai ta same shi zaune Nannynsa na karanta masa story book. Gefen gadon ta aje masa cup din da cake sannan ta shafa kansa ta sumbance shi.
"How are you My love"
Murmushi kawai yayi mata daman be cika magana ba, sai idan ta dauro. Emily ta kalli Nannynsa Chidimma.
"Ina fatima?"
"Ta shigo amman ganina a dakin ya saka ta fita ina tunanin tana dakinta"
"Okay"
Ficewa ta yi daga dakin ta tura kofar dakin Fadima sai ta ji ta a rufe, cup din da plate din cake ta hade guri daya ta yi knocking da dayan hannunta.
"Baby, bude kofar mana"
"I won't"
"Na kawo miki cake da madara"
"Bana so"
"Na fada miki babu kyau bachi da fushi, me yasa kike da kafiya ne?"
"Ki fadawa Vito ya daina zuwa nan i hate him"
Emily ta daki kofar dakin da karfi.
"Ki bude kofar nan Fatima and kar na sake jin kin fadi wata kalma marar dadi akan V idan ba haka ba zan bata miki rai"
"Ba zan bude ba!!"
Fatima ta amsa mata a tsawace kai kace Fatimar ce uwa Emily ƴa, runtse ido ta yi tana maida numfashi a hankali, sanin halin yarta da kafiya da rashin kunya ya saka bata sake bata second a gurin ba ta juya ta sauka kasa, tana saukowa kwakwalwarta na tuna mata da wasu kalamai na bakin littafin da zuciyarta ta aje.
_Ka yi hakuri karka rabu da ni, ban san kowa anan ba, ba ni da kowa a nan_
Ina rike da kafarsa nake fadin haka sai ya fisge kafarsa ya matsa baya.
_Ina da kafiya akan abun da nake so, da kuma wanda bana so, karki sake nuna kin san ni_
Ina da akan center table ta aje cake da milk din cikin bacin rai, ta zauna a kujera zuciyarta na yi mata babu dadi.
_Ina da mata ina da iyali, kin zo ne kawai ki ruguza rayuwata Aisha_
Jefe jefa kanana da manyan abubuwan da suke faru a rayuwarta ta baya suke dawo mata a duk lokacin da take zaune ita kadai ko kuma rai ya bace. A fusace ta mike tsayeta ture madarar da cake din har sai da suka zube kasa.
"Daman idan baki yi kafiya ba ai ke ba yarsa bace...!!"
Ta karasa da kara sosai kamar mai shirin yin duka sai haki take, windows falon ta nufa da curtain dinsa suke a bude ta tsaya sai ta hango Sarkin nata zauna kishingiden a cikin motarsa gilashin motar yana kasa gaba daya, yana kallon windows din da take tsaye, rufe curtain din ta yi ta nufi kofar falon ta bude ta fita. Hango fitowarta ya saka shi fitowa daga cikin motarsa yana jiran tsorowarta. Tsayawa ta yi a gabansa hasken kwayayen dake cike a gidan suna haska fatarta mai tsananin fari.
"Akwai abun da kake bukata ne?"
Ta ido yana amsa tambayarta, a sa'ilin da bakinsa yayi nauyi furta mata kalamansa.
"You..."
Ya furta bayan ya kwaci kansa.
Babu bata lokaci ta rumgume shi, ta lumshe idonta dake kwance da ruwan hawaye. Da ace tana da wani abun da zata aikata ta biya V da tuni ta aikata, domin shi ne mutumen da ya mayar da ita yadda take a yanzu, shi ne mutumen da be nuna mata kyama ba, ko da yake shi din kistane dan'uwanta da musulmi ne babu tantama da yanzu ya rabu da ita ko ya ci amanarta, amman shi yana nan tare da ita duk kuwa da irin kyamar da yarta take nuna masa.
Slowly ya zagaye bayanta da hannayensa ya rumgume ta comfortably, idonsa a sama yana kallon window Fatima dake rufe cike da bacin rai, domin ya tsani duk wani abu da zai batawa Emily rai idan aka cire shi kansa, a iyakar gidan yasan babu mai yi mata rashin kunya da rashin magana da kokarin bata mata rai ko tuna mata da rayuwar da ta jefar sai Fatima, domin London ba shi da lafiyar damuwa rayuwar kowa sai idan ciwonsa ya tashi. Ta dago daga cikinsa a hankali ba tare da ta kalleshi ba, sai ya kai hannunsa ya rika pink lips dinta ya dan dagota kadan.
"Karfe nawa zaki tafi aiki gobe?"
"6:30am"
Ya sake kallonta da kyau yana matsawa kusa da ita.
"Wane irin aiki ne ake tafiya karfe 6:30am na safe?"
"Haka matar ta fada min karfe 7 ta yi min a can"
Ta amsa har lokacin bata kalleshi ba. Ya kankance ido kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya kai hannunsa yana shafa gefen fuskarta.
"Shiga ki kwanta, ki samu bachi da wuri"
Ta kalleshi kadan.
"Good night"
"I love you"