Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 4
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 4: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 4. Ya furta ba tare da jiran ta mayar masa ba, domin be taba furta yana…
3,298 words
Ya furta ba tare da jiran ta mayar masa ba, domin be taba furta yana kaunarta ta amsa masa ba, tun farkon haduwarsu har zuwa yanzu da take kokarin samun kanta, ya mata uzuri domin ya nutsa a labarinta, yayi rayuwa da ita ya san zahiri da badininta, yana iya jin yadda abun ke tsikarta duk kuwa da kasancewar be wanzu cikin wancan rayuwarta ta ba, sai dai a yanzu ya jiku da kaunarta sonta na hana shi ganin abubuwa da yawa a na laifi akanta.
Tana tafiya rumgume da hannayenta har ta shiga falon ta rufe sannan ta shiga wani bangare na falon ta dauko mopper ta gyara gurin, a falon ta zauna na tsawon lokaci, ba kallo take ba, ba tunani take ba, ba bachi taka ba, wani yanayi take ji wanda rabinsa babu bakinciki, kuma babu kishiyarsa, wani yanayi taka ji na dabam. Motsin saukowar Chidimma ya saka ta juyo tana kallon stairs din har Nannyn ta sauko.
"London yayi bachi, Fatima kuma dakinta a rufe yake, na murda bata bude ba, wata kila ita ma ta yi bachin ne"
Nannyn ta fada cike da ladabi, Emily ta dago daga kishingiden da take a jikin kujerar tana cigaba da kallon Chidimma.
"Kina kokarin da yarana, musamman Fatima, halayenta ba masu kyau ba ne na sani, amman ina fatan zata sauya nan gaba"
Chidimma ta yi murmushi tana jindadin yadda Emily ke karfafa nata guiwa tana appreciating duk wani abu da take yi ma yaranta.
"Zata canja ranki ya dade, a yanzu tana da kurciya ne, she's just 6"
Emily ta daga gira.
"I hope so, Good night Chidimma"
"Good Night Ma'am"
Ta amsa mata da kai sannan ta fice daga katon falon, Emily ta mike tsaye ta rufe kofar falon sannan ta kashe komai na kallo da kuma na'urar sanyaya falo ta haura sama, dakinta ta shiga ta dauke wani makullin ta nufi dakin Fatima ta saka key din ta bude dakin. Turawa ta yi ta shiga sai ta same ta kwance a kasa rumgume da teddy dinta, sanin yarta sikila ce ya saka ta fara kashe ac dakin dake kunne domin akwai sanyi a garin, karamin abu ne ta tashi da ciwo washe gari. Gefen gadon ta zauna tana kallon Fatima da kamanin mahaifinta suke zube a fuskarta kamar an tsaga kara, ta kai hannunta ta shafa fuskar yarta.
"Ina da tsada a gareki Fatima, amman baki sani ba, saboda kina karama, kina fada min magana son ranki, kina wasu halaye da bana so, ina jin cewar kamar ke ma kin tsane ne kamar mahaifinki"
Ta share hawayen da suka zubo mata.
"Kin yi sa'a kina da ni a raye, a lokacin da nake sa'arki, ina a wani gidan marayu tare da yaran da suka rasa iyaye ko aka tsinta, macen dake kula da ni ta fada min ina jaririya ba a yanke min cibiya ba aka aje ni a gidan, har yau ban san dalilin da zai saka uwa ta aikatawa yarta haka ba"
Ta shafa fuskar Fatima a karo na biyu, sai kuma ta yi murmushi.
"Na san zafin rashi, na san zafin yaudara, na san zafin kiyayya, ba zan yarda ku fuskanci ko daya ba, zan jure zan mutu saboda ku yara, ku ne kawai iyalina"
Ta sumbanci kumatun Fatima ta ďaga daga kan gadon ta gyara mata lullubinta sannan ta fice daga dakin, ta nufi dakin ďanta na fari. Tana kallon fuskarta sai ta yi murmushi ta gyara masa kwancinsa tana zancen zuci.
'Wata kila ni tawa uwar ta mutu, shiyasa aka kawo ni a nan, amman me yasa yan'uwanta ko yan'uwan mahaifina ba su iya rike ni ba? Haihu ba tare da aure ba a addinin kirista ba abu ne na kunya ba, kamar wasu addinan ba, balle nace ko tana kunyar haihuwata ne'
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ta fito daga dakin ta koma dakinta, gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, sam ba zaka santa a da ka ganta a yanzu kace ita ce ba, sai idan ka yi mata farin sani, domin jikin da take da shi a can da, yanzu babu, ta zama fit da ita like a model, farin fatarta a yanzu ya sauya ya ninku da kaso mafi daraja domin a yanzu ta samu kwanciyar hankali da abinci mai kyau da lafiyayyen gurin bachi, da kwanciyar hankali, abubuwan da ta rasa a baya. Ta fara tsege kanta tana tuna wani lokaci da Khalifa yake yanke mata gashin kai saboda kawai wulakanci da tozarci, har ta gama tsife kan ta cire gashin dokin dake tsarkafe cikin nata red hair din bata daina hawaye ba.
Kwashe gashin dokin ta yi ta zuba a dusbin sannan ta gyara kanta, idan ba ka taba ba, ko kuma an fada maka ko ka sani babu wanda zai yarda gashinta ne domin jan gashi take dashi ba kamar sauran mata da suke da jan gashi ba, ko da yake blue eyes dinta da farin fatarta ya isa ya fahimtar da duk wani mai kallonta cewar ita ruwa biyu ce ba tare da tantama ba. Ta canja tufafin jikinta zuwa na bachi, ta gadonta ta jingina, ta dade a haka sannan ta mika hannu ta dauko file din da Amal ta bata a gurin aiki ta bude tana duba dokoki da ka'idodin kamfanin, bayan ta gama ta saka hannu a duk gurin da aka bukata, sannan ta aje ta kwanta ba tare da ta kashe wutar dakin ba, domin bata bachi da wuta a kashe. Kasancewar a cikin duhu yana firgita kwakwalwarta, ta kan kasa sakewa da rasa natsuwa sa sukuni, sanin hakan da Vito yayi ya saka shi tanadar mata duk wani abu da zai bata haske idan babu wutar nepa.
Bata kwanta da wuri ba, hakan ya saka bachin yayi mata nauyi bata tashi a lokacin da ta so tashi ba wato 4am. Karfe biyar da yan mintuna ta farka tana murza ido, alarm din dake gefen gadon mai hade da agogo ta dauka ta duba. 5:14am ya saka ta zabura da kuzari ta sauka saman gadon ta saka bedroom slipper ta fice da sauri. Tun kamin ta sauko kasa ta soma jin kamshin yana dukan hancinta, tsayawa ta yi ba tare da ta karasa saukowa daga kam stairs din ba tana kallon hanyar Kitchen din da dan tsoro, a iyakar saninta Chidimma ba ko da yaushe take shiryawa yaranta abun karyawa ba, sai idan bata gidan ko kuma ta bukaci ta shirya musu din, and babu wanda ya san kudurinta na son shirya abun karyawa da wuri saboda fita aiki, ita kanta bata shirya musu abun karyawa sai 6am. To waye a kitchen din.
Ta fara bin falon da kallo, har idonta ya sauka akan rigar Vito dake aje a kan kujera, siririyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin kamar hankalinta ya kwanta, daman idan wani abun cutarwa ne ai zata ji hayani ko a tashe ta, tun da akwai mai gadi a gidan. Saukowa ta yi a hankali kamin ta karasa Kitchen sai gashi ya fito rike da plate, dinning ya nufa ya aje plate din sannan ya nufo gurin da rigarsa take ya dauka ta nufota ta rufe mata jiki da rigar ya kai bakinsa saitin bakinsa zai sumbance ta.
"You already know how much i hate physical touch, i hate anything related to love"
Ta fada bayan ta kawar da kanta, sai ya juyo da fuskarta yana kallon cikin idonta zuwa gashin kanta dake red, irin na jajayen turawan nan da ake haihuwa da jan gashi.
"Good Morning"
Ya fada ba tare da murmushi ko sakin fuska ba, daman murmushi da far'a abu ne da suka yi ma fuskarsa tazara, abu ne mai wahala yayi murmushi idan ma yayi kadan ne ko na gefen fuska balle kuma dariya da yake jin bata zame masa dole ba. Hannayenta ta saka ta sauke nasa hannayen dake rike da fuskarta, ta nufi kitchen tana fadin.
"Me kake dafawa? Me yasa ka zo nan da wuri haka?"
Juyawa yayi yana kallonta madadin ya amsa mata sai ya jefo mata wata maganar da ya saba fada mata a duk lokacin da take kokarin kaucewa kaunarsa.
"Da ace zan yi arba da mutanen biyu da suka saka kika tsani soyayya, suka rikita miki lissafi, da na saka sun tsani kansu, da na rikita kwakwalwarsu"
"Sun dade da mutuwa a gurina, rayuwa ta baya ma na jafar da ita, Emily din da ba ita ce yanzu ba, wacan ta mutu wannan kuma yanzu take rayuwa"
Ya taka ta bi bayanta har cikin kitchen din ya tsaya daga gafe yana kallonta, ita kuma sai duba abincin take, farfesun naman kaza, sai dankali da plantain, dayan cooler kuma samosa ne da zafinsa. Ta daga ta kalleshi da blue eyes dinta masu matukar daukar hankali.
"Meyasa ka shirya duk wannan"
Ya matsa kusa da ita sosai.
"Kin fada min 6:30am zaki tafi aiki, bana son ki tafi da yunwa, kuma na san idan kin farka zaki iya cewa sai kin shiryawa Fadima da Londom abinci zaki tafi, shiyasa na zo tun 4am, na shigo kina bachi"
Kallonsa take cike da tausayawa domin hidimar da yake ta yi da ita, bata san wata hanya da zata saka masa ba.
"Me yasa kake takurawa kanka da yawa saboda ni? A irin wannan lokacin kamata yayi ace kana kwance kana bachi ne, V baka bukatar hidima irin wannan saboda ni"
Hannunsa daya ya kai ya rika fuskarta, kaunarta yake karanta a fuskarta da idonta, da ta san yadda yake jinta a ruhinsa wata kila da bata fada masa magana makamanciyar wannan ba. Be ce da ita komai ba ya saki fuskarta ya gyara mata jacket dinsa dake jikinta ya rumgume ta, ya lumshe ido. Ta jure iya juriyar da zata iya na bashi damar rabar jikinta na second goma ne kawai bayan wannan sai ta fara kokari raba jikinta da nashi.
A tare suka karasa dan abun da ba za a rasa ba, sannan ta shiga ciki ta wanke bakinta ta fito ta yi breakfast din yana zaune yana kallon yadda take jindadin abinci, ba lokacin cin abincinsa ba ne, baya karyawa dai 10am, a yau kuma kallonta kadai da jindadin yadda take cin abincinsa ya wadatar da shi, farincikin fada masa abincinsa yayi dadi da ta yi ya kosar da duk wata yunwa da zai ji a wunin ranar.
Ya daga mata kai yana murmushi kadan, yana jin kamar ace su daure a haka, su yi zama irin na masoya ko ma'aurata, sai dai ya san samun haka a gurin Emily a yanzu ba abu ne mai sauki ba. Kallon agogon falon da ta yi ya saka ta yi hanzarin karasa cin abincin ta mike tsaye.
"Bana son na yi latti, karfe 6:30am zan tafi aiki"
"Wane irin aiki ne za'a tafi karfe 6am? Me yasa kike son takurawa kanki a yanzu Emily kina da komai a nan"
Bata ce masa komai ba, ta cire jacket dinsa ta aje a jikin dayar kujerar, ta kwashe kayan da ta bata ta kai kitchen sannan ta wuce ta haura sama. Mikewa yayi tsaye ya nufi jacket din ya dauka yana kallon stairs din kamar mai jiran fitowarta.
TURHAN POV.
"Baka amsa ni ba"
Ta maimaita da yaren da ita da shi suka fi fahimta, wato Larabci. Lemun dake gefen Laptop din ya dauka ya sha ya aje sannan ya kalleta ta cikin Systems din dake gabansa.
"Ba yanzu ba, akwai wani aiki da ya taso min, ina son sai na karasa shi tukuna?"
"ما طبيعة عملك يا حياتي؟" "Wane irin aiki ne Hayatie?"
Ya kawar da fuska kaminnya juyo ya kalleta yana shafa kansa, bata jira amsarsa ba ta sake aika masa da wani zancen.
"لا أستطيع تحمل غيابك عني."
"Ba zan iya jure rashinka a kusa da ni ba"
"Abu mai muhimmanci baki bukatar sani, idan na kammala zan dawo"
"Ka canja min a yanzu"
Ya shafa kansa yana jin wani sabon fushi na kokarin rufe shi.
"Saboda bana haihuwa ne, ko kuma dai ka gaji da zama da ni ne?"
"Zaki iya ba ni ďa? Zaki iya haifa min jinina Jalila?"
Ta yi shiru tana kallonsa kamar yadda shi ma yake kallonta, kamin ya kai hannu ya rufe Laptop din ya kwanta jikin kujerar yana maida numfashi, me yasa ya fada mata haka? Al'adunsu da dokokin sa ake cilasta masa bi ba daga ita ba ne daga masarautarsu ne da kuma mahaifinsa. Ya tashi zaune yana jin fushinsa yana karuwa tunawa da yayi da yadda Ammy ta yi fushi da shi, saboda yarinyar da bata da ala komai da ita. Gaba daya an hada masa zafi ta ko'ina, babu wani daki daya da zai laba yaji sanyi. Wayarsa ya dauka ya kira abokinsa har lokacin be sauka daga fushi da bacin rai da yake ji ba.
ALIYU POV.
Yana zaune a kan gado, matarsa na kwance kanta na cinyarsa, ita da shi sun sakarwa plasma dake dakin idonsu, gadon da suke kai kuma ya karbi amanarsu, domin kana kallonsu zaka san hankalinsu a kwance yake basu da wata damuwa ko kadan. Wayarsa dake can kan karamin tebur ajeye ce ta yi ringing, a take ya ja tsaki domin ya ji dadin zaman baya son motsawa. Gashi be saba zama kusa da wayarsa ko yawo da ita idan yana tare da matarsa ba. Abu ne da ya sabawa kansa da shi aje wayarsa a nesa da matarsa a duk lokacin da yake tare da ita, doka ce ya sakawa kansa matukar yana gida tare da iyalinsa to lokacinsa na matarsa zai bata kulawa iyakar kokarinsa. Gwanar na jin haka sai ta tashi zaune tana kallonsa.
"Na dauko maka ka ba ni dubu biyu?"
A take murmushi ya subuce masa.
"Wai ke ina zaki kai kudi da son kudin nan?"
Ta saka dariya.
"Zaka biya na dauko?"
"Aa ni ma fa na san zafin kudi Hajiya, zan dauko kayata"
Sai ta maida kanta a cinyarsa.
"Ni gaskiya na jidadin kwanciyar nan ba zaka tashi ba"
"Okay saboda ni zan dauko ko?"
"Idan ni zan dauko zaka biya, idan ba haka ba gaskiya ba zan daga a cinyar nan ba, ai kasan idan kana gida kai nawa ne ni kadai"
"Ko ma bana gida ni naki ne har abada, yanzu daga ni na dauko sai na biya 2k din, kin ga wannan tsohon cikin naki ba zan so kina wahala ba"
Ta daga masa saboda ta ji yace zai bata kudin kuma zai dauko wayar da kansa.
"Hmmm ku dai maza idan kuna tare da mu ku namu ne idan kun fita kuma na wasu dai"
Ya mike tsaye ya isa ya dauko wayar yana murmushi already kiran ya yanke.
"Ke dai kishi zai miki illa, me ya kawo wannan maganar kuma?"
"Ai na san halin maza"
"Bayan wa kika aura? Da zaki ce kin san halin maza?"
"Kai kadai na aura amman ai ana fadar halinku"
"Ni dai na banbanta da sauran, yanzu wanda yake da mace yar dumaduma irinki har wata zata burge shi?"
Ya fada bayana bin bayan kiran da aka masa.
"Hello Allah ya taimaki Yarima"
Daga dayan gefen Turhan yayi murmushin karfin hali.
"Tsokanar ta tashi kenan, ya gida?"
"Lafiya kalau"
"Sorry na kira late na san kana tare da Madan ko?"
Aliyu ya kalli uwargidansa yana murmushi
"Kamar ka sani kuwa, daker ta bar ni na amsa wayar ma"
"To a bata hakuri, wani uzurin ne ya taso min..."
Turhan ya shimfida masa kudurinsa sannan ya bijiro masa da bukatarsa.
Aliyu ya dan sosa kansa.
"Akwai wandanda zan hada ka da su ba ma daya ba, amman Turhan kana ganin nemanta abu ne mai sauki? Ni ma fa na saka anbincika maka lokacin da na yi zama a Lagos din nan amman ba a dace ba"
"Wannan karon ina son na bi gidajen marayun da yake cikin garin Lagos ne, na bincika ko zan dace"
"Eh toh kuma ka kawo shawara, amman duk da haka ina ganin zai yi wahala saboda an kwana biyu, kuma ka fada min tun tana karama aka yi rikonta a can, kuma ba lallai ne ka sami ma'aikatan gurin na da ace su ne har yanzu?"
"Yeah amman ina zaton indai sun santa sosai da sosai za su gane ta idan na bada misalinta wata kila za a dace"
"Dama dai kana da hotonta abun zai fi sauki"
"Haka din ma zan gwada wata kila a dace, ina tunanin duk wanda na fadawa sifofinta blue eyes red hair, fara mai kiba sosai zai gane ta matukar ya santa"
"Allah yasa a dace, zan yi magana da wani yarona da yake can da safe sai na hada ku"
"Okay thank you"
Ya aje wayar ya sake zaunawa kusa da matarsa, wannan karon sai ta tashi zaune tana kallonsa.
"Kyakkyawana"
"Hmmm"
Ya amsata yana wani tunanin na dabam, har idonsa suna motsawa, sai kuma ya tabe baki zuciyarsa na raya masa abun da be isa ya fada a gaban matarsa mai tsananin kishi ba.
"Kana ji na"
Ya aje wayar ya mika mata hankalinsa gaba daya.
"Ina jinki Sarauniyata"
"So nake ka yi min wani alkawari"
"Na me?"
Ta yi shiru na wani lokaci kamar mai nauyi fada sai kallonsa take tana nokewa kamar marar gaskiya.
"Na miki alkawari cewar ba zan kara aure ba bayan ke?"
Ta daga masa kai tana mamakin yadda yayi saurin lagonta.
"Eh ya aka yi ka gane me nake son fada?"
"Na sanki da kishi ne ai, zuciyarki zata raya miki idan na fita waje mata nake kulawa ko?"
"Na san ba halinka ba ne, ba zaka kula mata ba, amman su matan za su iya kawo maka hari kuma zuciya bata da kashi, kuma ni gaskiya ba zan iya sharing dinka da kowa ba"
Yayi murmushi ya shafa fuskarta.
"Saka ranki a inuwa, Aliyu na ki ne ke kadai daga ke babu kari babu wanda zata kawo hari na rufe kofa, na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba"
Ta bude ido tana mamakin yadda yayi hanzarin bata hadin kai da wuri haka, ko da yake ta san waye mijinta ba mutum ne mai son mata ba, kuma ya sha fada mata tun kamin ya aureta cewar shi ba shi da ra'ayin aure mace sama da daya.
______________ Anya Aliyu zai rike alkawarin nan kuwa?
Turhan zai samu ganin Aisha kuwa?
Wane irin so Vito yake yi ma Emily?
Meyasa Emily ta dage sai ta yi aiki? Bayan duk gatan da ta samu a gurin Vito? [4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Barka da warhaka mutanen arziki😍
Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda ɗan mutum da mutum😃
Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser.
Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ɗina.
Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp.
KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less...😊
Page 5️⃣
Bata sauko ba sai da ta tabbatar ya fice daga gidan, sannan ta sauko ta sakawa Fatima lunch dinta a lunch box ta shirya mata komai kamar yadda ta saba, Londom kuma da ake masa darasi a gida sai ta zuba masa a nasa na nasa kayan cin abincin, sannan ta haura saman ta shiryawa cikin shiga ta riga da wando ta saka turare ta maida sarkar Cross dinta a gaban rigarta yadda zata fito da kyau.