Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 30

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 30

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 30: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 30. Ta ambaci sunansa da babban baki, madadin yaji haushi sai yayi…

3,356 words

Ta ambaci sunansa da babban baki, madadin yaji haushi sai yayi murmushi, bukatarsa ta biya daman makasudin yin hakan saboda ya gani idan zata ji kishi ne, idan har ta ji kishin hakan ya nuna tana son shi kenan. Ya jimgina da kujerar dinning din yana cigaba da kallonta, kamin ya ciro wayarwa dake vibration ya duba sannan ya amsa kiran. Yayi shiru na dakiku yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai.

"Ganin nan zuwa"

Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana kai lemu a bakinta.

"An sake kama kayanka ne?"

Har yayi gaba sai kuma ya juya ya kalleta.

"Nope wani ne yake wasa da rayuwarsa, someone set me up"

Ta aje glass cup din.

"Me kake nufi?"

"NDLEA aka turo su bincike gidana daga Abuja"

Ta mike tsaya da sauri ta karasa inda yake tsaye.

"Kuma zaka tafi"

"Yes ina bukatar na tafi"

"Aa karka je dan Allah bamu san manufarsu ba, gashi kana da saurin fushi ba mu san abun da zai faru ba"

Ya shafa fuskarta.

"Babu abun da zai faru"

Ta rike hannunsa tana girgiza masa kai idonta har ya fara tara hawaye.

"Ya kamata na tafi ko dan na nunawa wanda ya turo su wanene ni"

"Be zama lallai turowasu aka yi ba, sana'ar da kake yi ba mai kyau bace kana jefa rayuwarka be kawai cikin hadari, daman dole wata rana za a iya bincike za a iya ganeka"

Tana maganar tana kuka jikinta na rawa gaba daya ta tsorata.

"Set up ne, NDLEA da suke da nan ko jami'an tsoron duk mutanenmu ne, shiyasa ba ayi amfani da su ba aka turo baki daga Abuja, amman ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru"

Ta girgiza kai.

"Aa karka je"

"Dole sai na tafi ai, suna bukatar ganina"

"Kace musu baka nan"

"Ina nan"

Ya amsa mata yana kai hannanyensa ya rika fuskarta.

"Toh ka aje bindigarka karka je da ita"

"Zata min amfani"

"Idan zaka je da bindiga ba zan bari ka tafi ba"

Ta rumgume shi tana kuka, sai yayi murmushi ya dago ta daga jikinsa.

"Ba zan je da ita ba"

Ta fara lalaben aljihunsa.

"No idan kika taba zata samu shatin hannunki, idan na aikata wani laifi da ita aka yi bincike za a samu shattin hannunki kai, ba ni bukatar haka"

Ya cire bindigar da kansa ya nufi Kitchen ya dauko wata madaidaiciyar cooler ya saka bindigar ciki sannan ya fito rike da wuka ya nufi gurin da Swimming pool dinta yake yayi gina a inda kasa take ya saka cooler ya rufe sannan ya janyo daya daga cikin kujerar da suke aje a gurin ya dora a sama, sannan ya kalleta ya ce.

"Ko da bincike ya biyo ta nan baki da matsala babu wanda zai san da wannan you're safe"

Ya rika hannunta ya jimke ya saki sannan ya fice daga gurin zuwa gurin motarsa. Biyo shi ta yi ta tsaya tana kallonsa cikin tsoro da tashin hankali, shikam damuwa data nuna masa a yanzu ta gusar masa da duk wani bacin rai da ya ji a lokacin da aka sanar da shi abun da yake faruwa a gidansa. Dawowa ta yi falon ta doshi gurin da jakarta take ta bude ta dauko wayarta, number Aliyu ta fara kira domin shi zuciyarta ta raya mata, wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, ta sake kiransa be daga ba ta sake kira be daga ba, sai da ta jera masa miss calls kusan tara sannan ta maida wayar ta dauki jakarta ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta cause she want to see him badly...

ALIYU POV.

Tana kallon yadda ya saka wayar da ake ta kira tun dazun a aljihu ya ki ya amsa kiran sai ma saka wayar da yayi a silent kuma ya ki ya aje a inda zata ga sunan mai kiran zuciyarta ta raya mata ba kalau ba, amman bata nuna masa ba da ya gama saka turare ta mika masa agogon da ke aje, ya karba ya fara sakawa.

"Yaushe ka siya agogon nan Honey?"

"Wannan agogon ina da shi, bata yayi sai yanzu na ganshi"

"Da alama yana da muhimmanci a gareka kusan tun da na dawo kullum shi kake sakawa idan zaka je aiki"

Ya kalleta da dan mamakinsa domin be yi zaton ta maida hankali a gurin ba.

"Toh har kin saka min ido kenan, yana da tsada ne shiyasa duk wanda zai gan ni da shi zai san babban agogo ne"

"Hmmm"

Ta furta sannan ta mike tsaye ya kama hannunta suka fito seating room, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna ya ciro wayarsa gudun ya zaune ta domin ya sakata aljihun bayan wandonsa ne, sai ya ci karo da sakon Emily.

"Na zo baka shigo ba, ka yi sauri ka shigo akwai matsala"

A take ya mike tsaye ya fasa cin abincin Kameela ta daga kai tana kallonsa.

"Lafiya"

"Lafiya kalau, wani uzuri ne ya taso zan tafi Office yanzu"

"Abincin fa"

"Ki ci zan samu wani abu a can na ci"

Ya sumbance ya sannan ya fice da sauri tana kallonsa. Ya shiga motar sa yana karanto addu'o'i yana tukin har ya isa gurin aikin, kusan al'adarsa karanta addu'a idan ya shiga motar da safe, ya faka a inda ya saba fakawa ya fito ya nufi cikin ma'aikatar, sai da yayi kamar ya fara shiga office din Emily saboda ta fada masa akwai matsala sai kuma ya yanke shawarar fara tafiya Office dinsa albashi ita sai ta same shi a can. Ya shiga office dinsa bayan ya gaisa da sakaterinsa Nick ya shiga cikin Office din ya zauna, sannan ya kira wayar Emily bata daga ba, ya sake kira bata daga ba, sai ya aje wayar yana mamakin matsalar me aka samu? Tana office dinta ko kuma ta wuce gida? Ya sake daukar wayar ya sake kiranta bata daga ba, ya sake kira sai ya ji user busy alamar tana waya, wannan karon be aje wayar ba sai da ya tura mata sako cewar ya shigo ta same shi a office dinsa sannan ya aje wayar ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko gorar ruwa ya rufe, ya murda murfin ya bude ya kai gorar bakinsa, juyowar da zai yi sai aka turo kofar Office din aka shigo ya cika bakinsa da ruwa yana kallon Kameela dake sanye da green Hijab har kasa hannunta rike da bracket. Ya hade ruwan yana kallonta da mamaki.

"Me kike yi a nan?"

"Kana ta sauri ka fita baka yi breakfast, ni kuma hankalina ba zai kwanta ba idan ka wuni da yunwa shiyasa na biyoka da abun karyawa a nan"

Ta karasa kusa da shi ta dora bracket din kan teburinsa tana kallonsa da murmushi a fuskarta.

"Okay Thank You Dear, amman Baki fada min zaki zo ba, kin san bana son ana fita ba da izinina ba ko?"

"Haka ne am sorry"

"Me kike hau kika zo nan"

"Taxi"

Ya dauki wayarsa da nufin turawa Emily sako sai ga Emily ta turo kofar office din ta shigo, daga Aliyu har Kameela juyowa suka yi suna kallon Emily da ta yi tsaye ta kasa karasa inda suke tsaye, Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya kalli Kameela, to his greatest surprise ever sai ganin yayi Kameela na murmushi kamar babu komai.

"Karaso mana Emily shigo"

Ta fada sannan ta juyo ta kalli Aliyu.

"Ashe nan take aiki? Maa Shaa Allah tana da kyau gaskiya"

Ta sake duban Emily tana danne wani turnukun fadan ibilisan dake kirjinta.

"Toh bari na tafi na barku ku yi aikinku, daman na kawo masa abun karyawa ne, idan ke ma baki karya ba sai ya sam miki ki karya"

"Kawai na zo nan ne na.... Na..."

Emily ta makale a maganar ta ki ta fita, Kameela ta karasa kusa da ita tana murmushi ta dafata.

"Karki damu, ba sai kin min bayanin komai ba, ki gaishe min da yarki Fatima"

Ta nufi kofar fita ta bude office din ta fice, Aliyu yayi saurin bin bayanta, sai suka sauka kasa tare.

"Muje na sauke ki gida"

Ya fada yana kallon yanayinta har lokacin bata nuna masa komai ba.

"Okay"

Ta bi bayansa suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya zagaya ya shiga yaja motar, bata ce masa komai ba har suka isa gida shi kuma sai sake saken yadda zai bullo mata yake ba dan yana tsoron ta ba sai dan yana gudun bacin ranta, kuma ya san ko da ace bata da wannan zafin kishin idan ta ganshi da wata dole zata yi kishi balle tana da shi. Sai da ya faka harabar gidan sannan ya ce.

"Da zaka min uzuri ki fahimce ni Kameela..."

Bata bari ya karasa ba ta tari numfashi.

"Dan Allah kar mu yi wannan maganar da kai, ka kaddara ban ga komai ni fa yanzu na yarda da kai, ba ni da matsala ko cikin mata dubu zaka shiga na san zaka fita, hakan be daga min hankali ba ko kadan"

Ta bude motar ta fita tana murmushi.

"Allah ya tsare me zan dafa maka?"

"Anything"

"Okay I Love you"

Shi dai mamaki ya hana shi amsa mata da I love you too sai kallonta yake kamin yaja motar ya fice. Ya faka a inda ya gurin da aka tanadarsa domin aje motarsa sannan ya fito ya shiga cikin ma'aikatar ya shiga Elevator ya sauka hawa na biyar ya shiga office side dinsa, fada Sosai yayima Nick.

"This isn't professional behavior, why would you allow anyone into my office without notifying me first?"

"Apologies, sir. I allowed her in because I recognized her as your wife. As for Emily, she's one of our staff, and you had previously instructed that any staff member who needs to see you should be allowed in. That's why I let her through"

"That policy is now revoked"

Aliyu ya fada a fusace. Nick ya amsa masa cikin ladabi da girmamawa.

"Understood, sir. I apologize and will be more careful going forward"

Ya wuce ya shiga office dinsa. Zaune ya samu Emily ta hade kanta da guiwa.

"Miya faru minene matsalar?"

Kamar jiransa take ta dago.

"Miye ma be faru ba? A wane dalili zaka aikawa Vito da jami'an bincike masu tu'ammali da miyagun kwayoyi? Me ya maka"

Aliyu ya dan yin kamar mai tunanin waye kuma Vito.

"Vito.. Vito... Oh Vito? Me zai saka na yi haka toh? Miye alaka ta da shi?"

"Ni dai na fada maka, idan wani abu ya same shi kamar ni ya sama, domin shi yake dauke da ni, kuma shi ne mutumen da ya taimake ni a lokacin da babu mai taimakona, shi ya maida ni a yadda nake a yau, ko farcensa bana son wani abu ya sama"

"Ahh ahhh ni kika gani kofar gidansa ne? In banda dai kina son ki dora min laifi?"

"Indai kana son na cigaba da aiki a nan na cigaba da mu'alama da kai, to ka cire Vito a idonka"

Ta fada masa har tana nuna shi da yatsa. Ya kalli yatsanta ya kalleta be ce komai ba ya nufi kujerarsa ya zauna ita kuma ta juya ta fice daga office din. Sai da ta koma office dinta sai ya fara jin haushin abun da ta yi ma Aliyu bata san lokacin data fashe da kuka ba, ya wuce makadi da rawa amman bata da zabin da ya wuce haka, saboda gudun jefa Aliyu a matsala, ta san watan wata rana Vito zai iya ganowa kuma komai zai iya faruwa idan ya sani, haka kuma ba ta so wani abu ya samu mutumen da ya tallafawa rayuwarta ta sanadinta ba, ko da yake bata da tabbacin Aliyun ne, wata kila Vito ba zai rasa makiya ta wani bangaren ba tunanin haka ya kara jefa ta a damuwa. Kasa aikin komai ta yi duk kuwa da kasancewar ta yi waya da Vito ya fada mata babu wata matsala har sun tafi, amman kunya da nauyin abun da ta yi ma Aliyu be bari ta iya komai ba a ranar.

ALIYU POV.

Sai da lokacin tashi aikinsa yayi sannan ya sauko compound din ma'aikatar ya nufi motarsa ya shiga ya saka basket din da Kameela ta kawo masa dazun be taba komai ba, yana shiga motar ya amsa wayar mahaifinsa, ya fara tukin da hannu daya dayan hannun kuma manna da waya a kunnensa domin fitar da yayi ta dazun da gaggauwa be bar shi ya fita da Bluetooth dinsa ba.

"Shikenan Daddy na gode sai mun yi magana"

Ya fada sannan yayi ma mahaifinsa sallama ya aje wayar a cinyarsa ya cigaba da tukin har ya isa gida ya faka ya kashe motar sannan ya dauki wayarsa ya bude motar ya fita ya dauki kwando. Taku goma sha daya ya kai shi entrance din shiga cikin gidan, ya tura kofar falon ya shiga da sallama kamar yadda ya saba duk kuwa da ya san ba lallai yau a tarbe shi a yadda aka saba ba domin yau ya bata ran uwargidan ba kadan ba ko da yake bata nuna masa ba.

"Sannu da zuwa"

Ta fada a yanayin da ba na fushi ba kuma ba far'a sosai ba, sai dai kuma ba ta tarbe shi kamar yadda ta saba ba. Hakan be hana shi isa inda take zaune ya sumbance ta ba sannan ya aje basket din a gurin.

"Sannu da gida Gimbiya wannan ado haka?"

"Duk na ka ne kai kadai, je ka yi wanka ka zo ka ci abinci"

"Okay"

Ya haura sama ya shiga dakinsa, tufafinsa ya fara cirewa ya aje wayarsa ya shiga bandakin yayi wanka ya fito ya saka tufafi marasa nauyi ya fito falon domin bawa cikinsa abun da yake wajibun, yunwa yake ji sosai saboda be yi karin safe ba, dan haka ya zauna a seating room din ya nade kafafuwansa Kameela ta zera masa tuwon da miyar taushe ta kawo masa ruwan wanke hannu da kuma na sha da lemun kwakwa, sannan ta zauna gabansa tana game da wayarta. Da ya kalli yanayinta sai ya ji babu dadi, saboda ya san akwai damuwa a tare da ita, amman ta nuna masa kamar babu komai, sai ya ji kamar be kyauta ba.

"Kameela da zaki fahimce ni ki yi min uzuri, da rayuwa bata wahalar da ke ba, na san kina jin babu dadi a zuciyar kuma kin biye ko kin aje a ido kuma kina min kallon rashin fahimta, Wallahi Wallahi Wallahi babu soyayya tsakanin da Emily, abun da zuciyarta ta raya miki ko zata raya miki ko idonki ya gani Wallahi ba soyayya ba ce, kuma na miki rantsuwa na fada miki ne a yanzu ba dan ina tsoronki ba sai dan ina son farincikinki, kuma ina sonki, tsabani ko kadan bana son yana shiga tsakaninmu, farko cikinki a koda yaushe shi ne burina, idan kin yarda da ni shikenan idan kuma baki yarda da abun da na fada miki ba a yanzu shi ma duk daya"

Ya karasa tare da bude Warmers din zai fara zuba abinci, sai Kameela ta yi karaf ta dauke miyar fuskarta dauke da damuwa.

"Karki ci wannan bari na zuba maka wata"

A matukar kidime Aliyu ya kalleta ya samu kansa cikin wani kalar firgice da be taba samun kansa a zamansa da Kameela, ta nufi kitchen da sauri sai yayi hanzari tashi ya bi bayanta ko da ya shiga ya samu tana juye miyar a sink.

_______________________

Sannu 'yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko'ina!

Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/28, 9:27 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

Page 3️⃣1️⃣

"Me kika saka a miyar Kameela?"

Ta juyo a firgice tana kokarin dakewa domin bata yi zaton ya biyo bayanta ba.

"Me zan saka a miyar Aliyu?"

"Miyasa kika zubar?"

"Saboda ta yi sanyi"

"Wannan cooler ba yau na fara cin abinci da ita ba, kuma yanayin miyar be nuna yayi sanyi ba, kuma tun da nake dake ai baki taba sauya min miya ba, dan haka ki amsa min tambaya ne kika saka a ciki Kameela?"

Ya daka mata tsawa yana hade fuska kamar be taba dariya ba.

"Me zan saka a ciki? Ni ban saka komai ba"

"Guba kika saka a ciki? so kika yi na ci na mutu? Da kika ga na miki rantsuwa ina baki hakuri sai tunaninki ya sauya ko?"

Ta dafe kirjinta ta zaro ido.

"Guba kuma? Me zai saka na saka maka guba a cikin abincinka Aliyu?"

"Saboda rashin hankalinki da bakin kishinki, shiyasa na yi mamaki da baki yi hauka kin nuna halinki a lokacin da kika ga Emily ba, saboda kin san abun da kika shirya?"

Ta fara hawaye jikinta na rawa

"Ka zarge ni da kowane irin abu saboda kishina Aliyu amman ban da kisan kai, kuma a kisan ma na rasa wa zan kashe sai kai da nake kauna?"

"Abun da kike yi bana masu hankali ba ne, kwakwalwarki ta samu matsala ki shirya gobe zaki koma Kaduna idan kin je can zan samu likitan kwakwalwa ya duba ki"

Yana kaiwa nan ya juya ya fice daga Kitchen din, ta bishi da kallo kamin ta jefar da kular hannunta kasa da karfi ta fara bin kayan Kitchen din tana watsewa tana kuka, sai kuma ta bi bayansa tana kuka ta shiga dakinsa.

"Ni babu inda zanje, lafiyata kalau ba ni da hauka Aliyu, idan ma wani abun kake zargin na aikata saboda wa na aikata ba kai ba? Yaushe muka yi aure da zaka fara barin wata ta shiga rayuwarka? Idan kuma na yi fada ka buga min warning ko ka dauke kafa kana nuna wata banza ta fi ni?"

Ya katse wayar da yake ya matsa kusa da tsinka mata mari.

"Karamin yaro kika dauka ko marar wayo? Yaushe zan zauna na miki rantsuwa na miki alkawari kuma ki rika dawo da magana baya? Okay saboda ina fada sai kika zabi ki yi poising dina? A tunaninki idan na mutu ke zaki huta ne? Hakki rai ai ba zai barki ki samu salama ba"

Ta zube a kasa gabansa dafe da kunci tana kuka.

"Wannan ba kishi ba ne Kameela, hauka ne kina bukatar likita ya duba kwakwalwarki, wato ki kashe ni kije ki auri wani?"

"Ko mutuwa ka yi Aliyu ba zan iya auren wani ba, ina sonka ka sani ko wata mace ka kalla Aliyu jin nake kamar zuciyata zata fito, idan har ba son yarinyar nan kake ba me yasa baka hadata da Turhan din ba? Me kake jira?"

"Yanzu duk wannan ya wuce na fada miki ki shirya gobe zaki koma Kaduna"

"Ni babu inda zan je, na koma na cewa Hajiya Me?"

Readers Also Read