Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 31

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 31

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 31: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 31. "Ki fada musu guba kika zuba min a abinci, kina kokarin kashe ni,…

3,358 words

"Ki fada musu guba kika zuba min a abinci, kina kokarin kashe ni, dan haka ni kuma yanzu ba zan yarda dake ba, ba zan iya kwana gado daya dake ba, ba zan iya sake cin abincinki ba, zamanki a gidan nan ba zai taba bani kwanciyar hankali ba, tafiyarki gida shi zai fi a gareki da kuma ni"

"Ni ban saka maka guba ba, sai idan daman kana neman dalilin rabuwa da ni ne kawai saboda ka kawo wata, Wallahi Aliyu ba zan taba kyaleka ba, Wallahi ko mutuwa na yi ba zan barka ba, sai fatalwata ta addabi rayuwarka, saboda kai ka daukar min alkawarin da ba zaka iya cikawa ba, Aliyu ko rabuwa ka yi da ni ba zan iya kallon ka yi rayuwa da wata macen ba"

Aliyu ya saki baki yana kallonta.

"Ah lallai baki da hankali, ashe abun na ki ma ba kishi ba ne, hauka ce, ilminki be miki amfanin ba tun da har kika iya bari zuciya da shedan suka rinjayeki, abun da kike yi a yanzu Kameela yana nuna min zaki iya kauce hanya kam kishi, zaki iya komai ido rufe"

Ta lumshe ido tana sassauta kukanta ita kadai take iya fahimtar kanta ita kadai tasan halin da take ciki, wata kila ita kam tata jarabawar kenan so da kuma kishin Aliyu.

"Ka yi hakuri Aliyu"

"Ba abu ne da za'ayi hakuri ba, maganar rai da mutuwa ake, kin san idan Ummi ta san da maganar nan aurena da ke ya kare? Kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba sai ta kai ki kotu"

"So kake na tafi Aliyu? Haihuwa daya ka fara juya min baya? So kake na tafi na barka da wata banza mushirika karuwa macen da akanta babu kalar fadan da baka min ba? Idan na kome me zan fadawa Abbana? Miye ma'anar na koma gida? Ka sake ki ne kenan?"

Ya nufi closet dinsa ya canja tufafi jikinsa ya dawo ya dauki keys dinsa da wallet sannan ya ce.

"Bana son na dawo na tararda ke a gidan nan gobe da safe"

Ya nufi kofa yayi ficewarsa tana kallonsa har ya rufe kofar dakin. Wani bakinciki ta ji ya ratsa zuciyarta, ta raba kafafuwanta tana kuka mai taba zuciya, iyakar karatun data iya na son mijinta ne da kishinta, irin kishin da hankali yake rumgumar tunani su gudu a kwakwalwarta ta aikata abun da bata san inda inda illarsa zai kaita ba, da ace Aliyu be bata hakuri ba a yau da ya ci abunda zai yi sanadin ajalinsa, saboda tana ganin kamar hakan ne mafita a gareta da kuma shi, duk kuwa da ta san ba lallai hakkin rai ya barta ta huta ba.

Sai dai sanin bata da wata mafita sai wannan ya saka ta cire batirin agogo falonta ta daka ta saka masa a miya, saboda ta gane hargowa bata canja komai, domin da ta yi haukanta na farko bata samu abun da take so ba. Yau kuma zuciya taso ta kai ta baro, saboda ta biyan mijinta kuma ta tararda abun da take zargi, idan tace bata yarda da shi ba a yanzu bata yi ma kanta adalci ba, amman sanin a guri daya suke aiki da Emily ya fi komai daga mata hankali ko ba komai zai ganta kullum kuma za su yi magana, daga haka bata san iya inda abun zai tsaya ba, musamman data lura kamar Emily tana da muhimmanci a gareshi ko kuma shi din yana da wata manufa akanta, idan ba haka ba miyasa ya sama mata aiki a kusa da shi? Meyasa ba zai hadata da mai nemanta ba? A wane dalili yayi mata tsawa yayi fada da ita saboda kawai ta kira Emily a waya.

"Zan iya rayuwa ko babu kai Aliyu, gidanmu kuma ba gidan yari ba ne da zaka ce na tafi na kasa tafiya"

Ta fadawa kanta sannan ta mike tsaye ta fice daga dakinsa zuwa nata, tana shiga dakin sai kuma ta nemi courage din ta rasa, kawai sai ta rushe da sabon kuka, tana matukar son mijinta tana matukar kishinsa wannan abu ne da ya ke rubuce a cikin littafin kaddararta, rashin aiki da lissafi zai saka ta kashe aurenta da kanta yan'uwa kuma za su mata dariya su ce daman sun fada, ta tashi ta fita dakin da sauri ta dawo seating room gurin da wayarta take ta dauka ta aikawa Aliyu sakon ban hakuri da rokon kar ya saketa.

"Ba zan iya rayuwa babu kai ba Aliyu, ko sakina ka yi ba zan iya rabuwa da kai ba, idan ma har kana tunanin ina kokarin kashe ka ne ka yi hakuri ka yafe min dan Allah"

Ta jira be bata amsa ba, hakan ya saka ta kira shi be daga ba kuma be kira ba, ta san halinsa ta san idan yayi fushi yana da wahalar saukowa, ita ma dai jin ta yi bata bukatar zaman gidan dan haka ta sauya tufafin jikinta ta fice duk kuwa da kasancewar ba kowa ta sani a garin PH sai Tasmia.

ALIYU POV.

Hotel ya kama domin ba zai iya kwana a gidan ba matukar Kameela na ciki hankalinsa be taba tashi ba irin yau, ba dan komai ba sai dan ta fi kowa kusanci da shi ta san lagunsa ta kowane gefe idan har zata iya saka masa guba a abinci to zata iya masa komai ma. A hotel din ya karasa dan yammancin da ya rage masa, kansa a kulle tunanin idan yayi baya tsayawa shi dai gaba daya ya gagara fahimtar kalar kishin Kameela shi ko a tarihi be taba jin irin nata ba, ko da yake a yanzu yana dora abun ne a babin matsalar kwakwalwa. Ya ga kiranta ya kasa amsawa haka ma sakonta be amsa rokonta ba. Ya sani idan be daukar mata mummunan mataki ba abun da zata aikata sai ya fi wannan.

Sosai yayi ma matarsa addu'a a sallarsa da Isha'i ya roki Allah ya sassauta mata wannan mugun kishin ya saka mata natsuwa da kwanciyar hankali a zaman aurensu, ya son matarsa kusan son ne dalilin da ya saka yake mata komai kuma yake daga mata kafa har take kokarin wuce gona da iri. Sai da ya hau gadon dake dakin na Hotel ya kwanta sannan ya kira Family Friend dinsa Nura da suka kwana biyu ba su yi waya ba tun bayan da ya kira yayi masa gaisuwa da barkar haihuwar da aka yi masa. Nura ya amsa wayar yana zolayarsa.

"Manya masu kasa baku nema sai dai a neme ku"

"To yanzu kai ka nemi ki ni na nemeka?"

Nura yayi murmushi mai sauki.

"Malam har garin Abuja ka shigo fa baka neme ni ba, sai da na hadu da Ummi take fada min ka shigo"

"Tafiyar ta kwana biyu ce kuma ban shirya ba tafiyarce kawai ta zo a haka, ka san yanayin aiki ba ko da yaushe muke samun time ba"

"Haka ne, aikin ne kusan da yanke mana komai ai, zumuncin ma idan ba mu yi da gaske ba sai mu bar shi saboda neman duniya"

"Toh Allah dai ta shirya ka"

Nura yayi dariya.

"Ya shirya mu dai. Yanzu dai ya gidan ya kowa da kowa"

"Lafiya kalau, ya naka iyalin"

"Alhamdulillah"

"Nura kai ka fi kusa da ni cikin dukan mutanen da na sani masu aikin lafiya, dan Allah wane likita ne ka sani kwarare ta bangaren kwakwalwa da zai iya duba mutum kuma ya fadi gaskiyar komai"

"Me yasa kake neman Likitan kwakwalwa? Lafiya?"

"Lafiya amman ba kalau ba, Matata nake son a duba"

"Subhanallahi Kameela? Meya same ta?"

"Wani kalar azababben kishi take fama da shi da ya wuce hankali, shiyasa nake son a duba kwakwalwarta abincika ko akwai wani abu"

"Ban katsi hanzarinka ba, domin ni da kai musan duk mata suna da kishi sai dai na wata ya fi na wata, amman miyasa ka ce tana da azababben kishi? Wata kila abu ne da ba saka shi a muhallinsa ba sai ka yi masa fahimta baibai"

"Nura, tun da ka ji na ce maka tana da azababben kishi tana da shi ne, ya wuce hankali"

"Kamar me take yi"

"Kamai ma tana yi har abun da baka tunani, kawai so nake ka bincika min likitan kwakwalwa da zai iya dubata, da ace kai ba likitan kwakwalwa ne ba na yara ba da kai zan nemi ka dubata"

Nura yayi shiru na few seconds sannan ya ce.

"Aliyu, look idan akwai matsala ne za ka iya fada min, kasan sometimes mu bukatar abokan tattauna sirri, kuma akwai abun da iyaye ba zamu iya barin iyaye su sani ba, kuma da can ni da kai bama boyewa juna sirri sai dan girma da kai muna yanzu da aiki da kuma rashin zama a guri daya, ya saka dukanmu muka maida hankalinmu gurin wasu abubuwan, amman ni har gobe idan ina cikin wata babbar matsala Aliyu kai ne mutum na farko da zan kira na shaidawa, domin bana kallonka a matsayin aboki kawai ko abokin karatu ko abokin gari daya, ina kallonka ne a matsayin dan'uwa na jini, domin sanadinka na zama abun da na zama Aliyu sanadinka na samu komai da na samu a yanzu, idan kana cikin wata damuwa dan Allah ka fada min"

Aliyu ya sauki ajiyar zuciya.

"Nura ka san Turhan ai?"

"Eh na san Turhan"

"Amman kamin nan daman Kameela tana da kishi kai ka sani kuma...."

Ya fada masa abubuwan da suka faru tsakaninsa da Kameela da kuma Emily ciki har da alkawarin da yayi ma Kameela cewar ba zai mata kishiya ba.

"Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, a lallai Kameela bata da hankali, taya zaki yi kokarin kashe mijin da be bijiro miki da maganar aure ba ma? Gaskiya rayuwarka tana cikin hadari, kana iya yanzu?"

"Ina hotel na bar gidan"

"Ka yi tunani mai kyau, amman ka yi kuskure Aliyu, tun farko be kamata ka mata alkawarin cewar ba zaka mata kishiya ba, be kamata ka haramtawa kanka abun da Allah ya hallata maka ba, ita mace mai kishi daga lokacin da aka fahimci tana da kishi taka mata burki ake, tun tana haukan tana kishin har ta gaji ta hakura idan ta fahimci ba zaka fasa son wata ko auren wata saboda kishinta ba, bayan kuma kishi ka yi hakuri da abun da zan fada da alama Kameela bata da zuciya mai kyau"

"Na mata alkawarin ne saboda bana da ra'ayin kara auren, kuma da farko na yi tunanin aikata hakan zai saka hankalinta ya kwanta mu samu zaman lafiya ni da ita, shi aure Allah yace idan baka iyawa adalci karka yi, kuma ba lallai ne na iya adalci a tsakanin mata biyu ba, saboda rayuwa ni ba mutum ne mai son yin nan na yi can ba, ba kuma zan so na tashi gaban Allah da hakkin kowa ba"

"Na fahimce ka duk namiji mai son zaman lafiya a gidan sa dole zai bi hanyoyin da yake ganin sun dace domin ya samu salama da matarsa, shawarar da zan baka a yanzu karka sake cin abincinta"

"Daman na yanke wannan shawarar, kwana da ita a gida daya ma ba zan iya ba a yanzu sai ta samu lafiya"

"Bayan samun lafiyarta ma, Aliyu babban abun da zaka yi shi ne kara aure, ta fahimci ba a ketare iyakokin Allah, kuma hakan zai rage mata kishi wata kila har ta zabi rabuwa da kai, dan na fahimci kana sonta sosai shiyasa ba zan iya baka shawarar cewar ka saketa ba, amman Wallahi zama da ita hadari ne sosai ga rayuwarka"

"Zancen aure ko rabuwa da ita be taso ba yanzu Nura, shiyasa ban fadawa Ummi ba, dan na san ba zata bari na zauna da ita ba idan ta ji, kuma komai dan hankali ne, a sannu ake bi ayu bincike, shin yanzu zaka samo min likitan da zai dubata ko kuma na kashe wayata"

"Zan samo maka mana dole na, akwai wane babban likitan kwakwalwa sunansa Dr Adam Bello, sai dai yana da wahalar gani gaskiya kamin ka sami ya duba ka ma sai kana da Connection, zan yi kokari na nema maka appointment da shi idan zaka ganshi sai ku zo Abuja"

"Shi kenan na gode sai na jika"

"Okay"

Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Emily ya shigo wayarsa, ya dade yana kallon kiran baya cikin yanayin da yake son magana da ita a yanzu, sai dai kuma ba zai iya ganin kiranta ya kasa dagawa ba, domin be san dalilin kiran ba, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya kara a kunne, daga ita har shi shiru suka yi babu wanda yace uffan.

"Ba zaka yi magana ba?"

"Ba ke kika kira ni ba"

"Da ka dauka amman kai ya kamata ka fara cewa Hello"

Yayi shiru be sake magana ba. A shagwabe Emily ta fara magana.

"Daman dai kawai na ji babu dadi abun da na yi maka dazun ne"

"Kin san baki kyauta ba miyasa kika kira ni yanzu?"

Tana jin hakan ta san ransa a bace yake wata kila har yanzu be sauka daga fushin fadan da ta yi masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, tana jin haushi meyasa ma to ta kirashi yanzu. After ta yanke kiran sai kuma ya ji babu dadi na furucin da yayi mata, ko ba komai ta fahimci beta kyauta masa ba ta kira be kamata yayi mata haka ba, a yanzu zata kara jin babu dadin ne. Without second thought ya kira layinta ringing daya ta daga. Ita dai data daga sai ta ari irin halinsa ta yi shiru ba tare da tace komai ba.

"Dazun da kika kira cewa kika yi ni ya kamata na farawa cewa Hello"

"Na san yanzu ka kira ka yi min bakar magana ne ko fada"

"Me kika sani a halina da zaki yanke hukunci?"

Ta yi shiru, jin shirun ya saka shi katse kiran, a take ta biyo shi da wani kiran domin bata san dalilinsa na kiranta ba gashi ta yanke masa hukunci kuma ta kara bata masa rai. Da ya amsa kiran ita da shi sai suka yi shiru babu wanda yace uffan har na tsawon lokaci.

"Hello..."

Suka furta a tare, ita a kokarinta na yanke shirun shi ma kuma a kokarinsa na yin magana kar tace ta kira ya amsa be ce komai ba. Sai kuma shirun ya sake biyo baya.

"Zaki ce wani abu ne? Ko wani abu kike bukata?"

"Idan baka da abun da zaka ce, ba sai ka sake kirana ba, mu ba yara ba ne be kamata muna haka ba"

"Remember I'm your boss, ni da ke waya kira wani yanzu?"

Ashe fa ita ta kira shi, bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, shiru yayi yana sauraren dariyarta a kunnesa tun da yake da ita be taba jin dariyarta ba sai yau, and ya san dariyar zata mata kyau domin farinciki ya dace da ita a yanzu dan haka ya fara imaging yadda take dariyar, kamin ita da shi su sake hada baki gurin cewa.

"Okay Bye"

Ya mata sallamar ne saboda ya fahimci bayan dariyar bata da wani abun fada, ita kuma ta masa sallamar ne gudun kar ta bata masa rai tun da ba wani abun zai fada ba. Bayan ta katse kira ya bi number ta da kallo sai kuma yayi murmushi. Be dauke idonsa ba wani kiran ya sake shigowa wayarsa da bakuwar number. Wannan karon ya amsa da sallama domin be san waye ba.

"Sallamu Alaikum"

"Wa'alaikumussalam barka da dare"

An fada cikin wata murya mai sanyi da be fahimci waye ba.

"Barka dai"

"Na san baka gane ni ba, Tasmia ce kawar Kameela, daman na zo gidan ne ban tarar da ita ba shi ne nace bari na kiraka ko kuna tare dan na kira wayarta ban samu ba"

"No ban koma gida ba tukunan"

Yana bata amsar ya katse kiran yana mamakin da ya kamata ace tambaya yayi mata cewar ina ta samu numbersa. [6/1, 9:15 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

Page 3️⃣2️⃣

Ta sauke wayar tana murmushi wani irin jindadi da farinciki suka lullube ta na jin muryar Aliyu, daman tana ta tunanin ta ina zata bullo ta fara gaisawa da shi babu dama, domin a yanayin yadda ta fahimce shi ba irin mazan da mata suke saurin burgewa ba ne, kuma ba irin mazan da ake zuwa ma da bukata kai tsaye ne ba, kusan zuwan Kameela gurinta ya taimaka mata sosai gurin samun damar magana da Aliyu tun a bayan da ta sace Numbersa a wayar Emily. Ta dade tana murmushi kamin murmushin dake fuskarta ya gushe kamar mai tunanin wani abu, ta goge number a gurin kira sannan ta fito bandaki da aje wayar a karamin gadonta ta fito falo ta samu Kameela da ta ci kuka har idonta ya canja kala.

"Toh ke yanzu miye amfanin kukan da kike yi?"

"Ba zaki gane ba, baki san minene soba Tasmia ba"

Tasmia ta zauna kusa da ita ta dafa ta With Straight face.

"Na san miye so, so yana iya haukata mutum domin yana saka ka ka aikata abun da ba halinka ko kuma baka yi niya ba, so yana maida kai kamar wani wawa ko kuma kakkarfa, shi so wani abu ne da ba a iya cusa shi sau daya yake shiga zuciyar mutum, kuma ya hanaka zaman lafiya har sai ka biya bukatarsa"

Ta lumshe ido ta bude.

"Amman ke irin son da kike yi ma Aliyu yayi tawa Kameela shi ya kamata ace yana miki irin wannan son, ke fa mace ce, gashi yanzu har yana kokarin wulakantaki akan wata banza da addininmu ma ba daya ba, ba tare da kin masa komai ba"

"Ban masa komai ba sai kawai dan na zagi Emily, yanzu haka baya gidan yayi tafiyarsa, kuma yace na bar masa gidansa na koma gida wai zai samu likitan da zai duba ni, mahaukaciya ma ya dauke ni kenan, shiyasa na rasa me ke min dadi naji bana son zaman gidan gashi ba ni da kowa a garin nan"

Tasmia ta bude baki.

"Ahhh lallai kuwa mahaukaciya ya dauke ki, amman kin yi hakuri nuna masa kishi da kike ai soyayya ce, shi duk be gani ba sai kora da hali? Da ni ce ke ba zan sake kwana a gidansa ba sai na koya masa darasi"

Kameela ta kalleta.

"Ni ba inda zan je ina son mijina Wallahi, idan na tafi ai na bawa Emily din damar ta rika magana da shi tana samun yadda take so gashi ma gurin aikinsu daya"

Tasmia ta girma mata kai.

"Kameela ke fa yar manyan mutane ce, kina da gata ina da yan'uwa da kudi, be kamata Aliyu ya wulakanta kuma ki zauna ba, ai tun da har ta kai ya furta ki koma gida idan baki koma ba ai zai cigaba da wulakanta ki ne, ai kawai ki yanki ticket gobe ki kama hanyar gidanku sai ya nemi ki, ai ba ayi ma namiji haka, tun da har ya iya nuna wata ta fiki kara ya san darajarki"

"Akwai abun da baki sani ba Tasmia, iyayenmu ba san auren za su iya raba auren idan suka ji cewar Aliyu ya kore ni saboda na kira wata a gurin aikinsu na zageta saboda tana budurwarsa"

Tasmia ta daka mata tsawa.

"Ke dalla can Aliyu autan maza ne da kike ta wannan rawan jiki da tsoron rasa shi? Haba Kameela sai kace maza sun kare aduniyar nan ne"

"Tasmia Aliyu na dabam ne fa, cikin maza dari irinsa daya ake samu, ni na san yana hakuri da ni, yana min komai kuma be taba wulakanta ni irin haka ba sai da bakar Emilyn nan ta zo"

Tasmia ta shiru tana kara jin kalamanta cewar Aliyu na dabam.

"Toh yanzu ko number shi zaki ba ni na kira na ba shi hakuri? Domin na lura baki shirya tafiya gida ba, kin shirya karbar wulakancinsa ne, daman maza ai idan suna son ka babu abun da ba za su maka ba, idan kuma suka ki ka zaka fara ganin wulakanci kala kala"

Readers Also Read