Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 32
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 32: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 32. "Tasmia ko hauka nake dai ai ba zan dauki number wayar mijina da…
3,356 words
"Tasmia ko hauka nake dai ai ba zan dauki number wayar mijina da kaina na ba ki ba, tafiya gida dai zan tafi ko dan ya gane ni ba kanwar lasa ba ce"
Tasmia ta watsa mata harara.
"Kin dauka kowa irin Emily ne? Ko mazan duniya sun kare an fada miki ni zan iya auren mijin da zai nuna ya fi son matar waje da matarsa?"
Kameela ta watsa mata wani kallo tana jin zafin kalaminta.
"Mijina ba manemin mata ba ne, balle ki ce ya fi son matar waje akan ta gida"
"Idan ba haka ba akan me zai fifita Emily take da suna ko Imily akan ki? Ke mai dai ki yi tunani mana"
Kameela ta nuna ta da yatsa.
"Ke ki iya bakinki, ban zan dan bana son mijina ba, sai dan na rasa gurin da zanje a cikin daren nan, tun da na zo na fada miki damuwata sai wani zuga ni kike kina zagin mijina, an fada miki rabuwa muka yi ne? Ni fa na zo nan ne saboda na samu mafitar yadda zan shirya da mijina, amman sai wani zakewa kike kina ta zaginsa"
Tasmia ta yi murmushi.
"Matsala ta dake ke zahila ce, idan yabon Aliyu kike son ayi ai nan zaki zo ba, dan ni na san darajar kaina ba zan baki shawarar zama da mutum da har yanzu baki gama sanin ba, Aliyu yana neman hanyar rabuwa da ke ne kawai shiyasa yake wulakantaki domin ba Emily ce kadai budurwarsa ba"
Tasmia ta karasa fuskarta babu alamar wasa.
"Me kike nufi?"
Har Tasmia ta daga wayar sai kuma ta fasa abun da ta yi niya ta dauke kai.
"Ki daina yarda da namiji dai kawai"
"Ai ke baki yi auren ba balle ki fada min kabli da bad'adin namiji"
Fadar bata yi aure Tasmia ta ji abun kamar gorin auren take mata a take zuciyarta ta haye sama san lokacin da ta mayar mata da zazzafar amsa ba.
"Kara ni ban yi auren ba, ke da kika yi auren ai ta wuje ta fiki daraja a gurin mijinki, mijin ma da Emily kadai yake nema ba ni kaina da kansa ya saka min Number wayarsa, kuma idan kin koma ki tambaye shi sau nawa ya zo gidan nan gurina"
"Karya kike yi Wallahi ai ko Aliyu zai kula mata ba irinki zai kula ba, domin ba ki fini da komai ba, sai idan ke kika nemi shiga gurinsa saboda an yi kwantai babu miji kuma ga bakin jini, ga kuma rashin tarbiya, idan ba rashin tarbiya ba yaushe mace cikakkiya rikakkiya kamar ke zata zo ta kama gidan kanta set-contain da sunan bautar kasa? Duk garin Kaduna be ishe ki zama ba sai kin tsallako kin zo garin da mijina yake saboda shi ne abun farautarki ko?"
Ta dago wayar ta kama Number Aliyu ta kira shi na farko be daga ba sai a na biyu.
"Assalamu Alaikum"
Ya fada Tasmia bata ce komai ba ta katse kiran daman burinta Kameela ta ji muryarsa domin ta gasgata karyarta.
"Komai zaki fada ki fada ni dai na riga na gama da ke Wallahi"
Kameela ta rufe ta duka Tasmia ta maida himma suka fara dukan dukan gashi babu mai raba su, ta ko'ina Kameela dukan Tasmia take ba kuma dan ta fi Tasmia karfi ko jiki ba halima Tasmia ta fita cika amman ta yi mata kwance galala tana dukanta, da ta gama da ita ta koma gurin kayan falon ta fara watse su.
"Wallahi Wallahi akan Mijina sai na kashe ki Tasmia, daga ke har Emily sai na yi maganinku"
Ta Dauki Jakarta ta fice daga gidan tana huci. Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa ta hau ta koma gida, tana shiga ta fadi kan kujerarta ta fashe da kuka bakinciki ya mata yawa, yanzu mayakan sun zame mata biyu kuma ba kowa ya janyo ba sai Aliyu, ta san wani abun da Tasmia ta fada gaskiya ne cewar yana neman rabuwa da ita ne shiyasa yanzu yake wulakanta ta, a yanzu ta gano dalilinsa na yi mata alkawarin ba zai kara aure ba ashe saboda yana son ya tara mata awaje ne, gashi daga tafiyarta haihuwa komai ya canja kamar daman dagawarta kawai yake jira, a daren ta siye flight ticket daga PH to Lagos daga Lagos ta hau jirgin Kaduna kwana ta yi tana kuka tana bakincikin da nadamar dama ace ta bar shi ya ci abincin dazun da yanzu duk bata ji wannan ba.
EMILY POV.
Kanta a sama tana kallon taurarin da suka yi ma samaniya ido, har lokacin hakoranta ba su rufu daga dariyar da take na wayar da ta yi da Aliyu ba, bata sauke kanta kasa ba sai da mai gadin gidanta ya bude gate motar Vito ta kunno kai a harabar gidan, tana kallonsa har yayi farkin sannan ta sauka ta karasa inda motarsa take, ya bude motar ya fito yana mata wani irin kauna da ke kara tabbatarwar kaunarta a zuciyarsa musamman data nuna masa kulawa da tsoronta na gudun kar wani abu ya same shi.
"How are you?"
"I'm good, ba su maka komai ba"
"Ba su yi ba, kuma ba su samu komai ba"
"Taya hakan ta faru"
"Saboda cikin kasa nake aje abun da yake dole a gidan, kuma ina da yaran da suke hango abun da zai faru idan suka ga bakuwar fuska sai su shirya komai"
Ta yi murmushi.
"Na jidadi da wani abu be sameka ba"
"Daman babu abun da zai same ni ai, sai dai ya samu wanda ya shirya hakan"
Ya wuce ya nufi Gardenta gurin da ya binne bindigarsa sai ta bi bayansa da tambaya.
"Ka gano ko waye ne"
"Ban gano ba amman zan gano, kuma idan na gane kowaye sai ya dandani kudarsa, sai ya raina kansa"
Har yayi ginar ya ciro bindigarsa bata sake cewa komai ba, mikewa yayi tsaye ya matsa kusa da ita.
"Kin damu da ni Emily ko ba haka ba?"
Ta yi shiru bata amsa masa ba.
"Miya haka ki aurena? Mi ya rike ki daga nuna min soyayya Emily? Ba ki jin cewar lokaci yayi da ya kamata ace mun kasance karkashin inuwa daya?"
Ta sauke idonta kasa tana shafa wuyanta.
"Kina da wani buri ne da kike son cin ma kamin ki amince min ne?"
"Vito bana son sana'arka"
"Bayan shi fa"
"Fatima-... La lall"
Bata karasa ba ya katsi hanzarinta yayi gaba.
"Oh Okay"
Ta bi bayansa suka fito daga gurin ya nufi motarsa ya bude ya shiga har yayi mata key sai kuma ya fito ya dawo daidai inda take tsaye ya shafa fuskarta sannan ya koma motar, tana tsaye tana kallonsa har ya fice, abun da ba su sani ba duk abun da suke Chidimma na lekansu. Emily ta shigo falonta kenan wayar hannunta ta yi ringing data duba wayar sai ta ci karo da sunan Tasmia, babu bata lokaci ta amsa.
"Hello"
Tasmia ta fashe mata da kuka.
"Emily dan Allah ki zo ina cikin damuwa ina cikin bakinciki, ki zo yanzu dan Allah ina da bukatar taimakonki"
"Okay gani nan zuwa"
Ta nufi staircase da sauri ta dauko key din motarta ta fito ta sauri ta nufi gurin da motar take, daga unguwar da take zuwa unguwar da Tasmia take tafiya ce ta mintuna Arbanin amman cikin minti ashirin da biyar ta isa gidan Tasmia hankali a tashe saboda ta ji muryarta tana kuka kuma gashi ta fada mata da bakinta cewar tana cikin tashin hankali. Tana faka motar ta bude ta fita ya fara kwankwasa kofar Tasmia kamin ta tura ta shiga, yanayin yadda ta ga falon a hargice ta san ba lafiya ba, ta zauna kusa da Tasmia dake rusar kuka tana tambayarta abun da ya faru.
"Ni ma ban san miya faru ba, matar nan tana shigowa ta rufe ni da duka wai mijinta yana zuwa gidan nan nemanki, gaba daya Kameela bata da hankali, akan Aliyu zata iya komai Wallahi kara ma ki rabu da mijinta, ni din ta yi min haka ina ga ke kuma"
"Ba soyayya nake da mijinta ba, kuma waya fada mata yana zuwa nan nemana? Yaushe rabon da na zo gidan nan ma"
"Waya sani wata kila bincike tayi har ta gane ko kuma shi ya fada mata ai maza ba su da tabbas, zuwan ba na yanzu take magana ba tun a wacan karon ne, shi ma kuma karya aka shirya mata domin bayan tafiyarki Aliyu be taba zuwa gidan nan nemanki ba"
"Toh yanzu me zaki yi? Reporting dinta za ki yi ma police ko kuma yaya? Ko a fadawa Aliyu"
"Aa bana son kowa ya sani, so nake ki raka ni asibiti"
"Okay tashi mu tafi"
Emily ta fada tana kallon fuskarta data dan kumbura kadan. Tasmia ta mike tsaye
"Ban san inda wayata take ba, ara min wayarki na kira na sanar da iyayena halin da nake ciki"
Ba tare da tunanin komai ba Emily ta mika mata wayar sai ta tashi ta shiga daki da sunan kiran sai dai a badini ba kiran zata yi ba, amfani ta yi da wayarta dake aje a dakin ta saka number Kameela ta aika mata sako sannan ta goge ta duba inbox din Emily ko zata ga sakon Aliyu bata gani ba, ta shiga longcalls a nan ta ci karo da kiransa da kuma wanda Emily ta yi masa ta dago ta kalle kofar cikin wani yanayi sannan ta sake maida idonta gurin wayar ta saka wata fake number ta kira ta yi canceling.
"Kin ga na kira wayar Yayana saboda na sanar masa saboda shi namiji ne, kar na fada musu hankalinsu ya tashi su yi zaton ko wani babban abu ne, bari zuwa gobe zan sake kiransa"
Ta fada bayan ta mikawa Emily wayarta.
"Okay mu tafi asibitin"
"Wace asibiti zamu je ni kin san ba wanin garin nan na yi ba"
"Muje ni na san asibitin, sun gwarai sosai a can ake duba London ni kaina can nake zuwa idan ba ni da lafiya"
"Okay"
Ta shiga ta dauko jakarta da wayarta dake boye a jakar ta fito suka shiga motar Emily, da suka isa likitan dake duty dare ya dubata sai ya rubuta mata maganin ganin kamar ciwon be kai a bata gado ba, amman ta ki yarda wai ita ko'ina ciwo take ji ita dai tafi son a bata gadon, ganin tana bukata ya saka likitan bata gado, a dole Emily ta tsaya tare da ita asibitin ganin bata da kowa kuma be kamata ta tafi ta barta ba, domin ita ma ta tsaya mata lokacin da take cikin damuwar rasa danta.
ALIYU POV.
"Daman abun da kake takama da shi kenan? Shiyasa kace ba zaka min kishiya ba? Sai ta waje? Abun be tsaya iya kan Emily ba? Har da Tasmia kawata Aliyu? Emily ta turo sako ta fada min komai ta fada min ka fi sonta akaina, shiyasa ka zabi korata, ta fada yadda kake ziryar gidan Tasmia gurin nemanta, ka nuna kafira ta yi matarka muhimmanci Aliyu, toh na bar maka gidan sai ka dauko ta ka kawo daman ai ta fada min lokacin da bana cikin gidan har cikin gidan ta kwana ka yi ma danta jana'aiza ka kyauta"
Shi ne sakon da ya fara cin karo da shi kenan a wayewar safiyar yau, ya dafe goshinsa yana kallon Number Emily da Kameela ta yi screenshot ta turo masa ta whatsapp tare da sakon data aiko mata, da yayi coping number ya duba sai ya ga number Emily din ce. Amman me zai saka Emily ta yi haka? Be samu amsar tambayarsa sai ga kiran Tasmia ya shigo wayarsa wannan karon be amsa ba, har wayar ta gaji da ringing be kula kiran ba. Sako ne ya biyo bayaj kiran Tasmia tana sanar da shi Kameela ta yi mata duka jiya da dare a asibiti ta kwana.
"Ahhh Ahhh"
Aliyu ya fada yana zaunawa bakin gadon dake dakin na Hotel. Da kansa ya kirata sai ta daga tana kuka.
"Me ya faru?"
"Baka ga sakona ba"
"Na gani, garin ya ta miki duka?"
"Ban san waya fada mata kana zuwa neman Emily a gidana ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ganinta na yi a falona babu bayanin komai ta hauni da duka"
"Amman jiya ke kika kira ni kika ce kin je gidan nemanta bata nan, ina kika samu number na"
"Mai gadinka ne ya bani da na kira ban same ta ba, sai yace ba ri ya ba ni number ka na kira kace baka dawo gida ba, sai na dawo gidana ina zuwa babu jimawa sai gata ta shigo kawai ta hauni da duka har tana fadar sai ta kasheni, ban san hawa ba ban san sauka ba, Aliyu ba ni da kowa garin nan sai Allah, bana son wani tashin hankali duk abun da za ku yi ya tsaya tsakaninku da Emily da Kameela ka jawa Emily kunne dan Allah ta daina saka ki cikin rigimarku, babu ruwana sa soyayyar dake tsakaninku da ni dai ina zaune da kowa da zuciya daya"
Bata jira abun da zai fada ba ta kashe wayar tana kuka. Ya mike tsaye yana tunanin damuwar Kameela shi ta saka masa guba ta duki Tasmia bayan ta gama haukata akan Emily. Number Emily ya kira domin ya ji dalilinta na turawa matarsa sakon da yayi sanadin da aka duki Tasmia kuma aka kara kunno masa wata sabuwar wutar. Emily ta amsa wayar ba yabo ba fallasa.
"Hello"
"Emily"
"Na'am"
"Kina ina? Me kike yi a yanzu"
Ta kalli kitchen din da take zubawa Tasmia abun karyawar da Chidimma ta shirya domin ita ta kwana a asibiti ne sai washe gari ta dawo.
"Ina gidana"
"Wata magana ta shiga tsakaninki da Kameela?"
"Aa"
"Tasmia fa?"
"Meyasa ka tambaya?"
"Meyasa kika turawa Matata sako cewar ina zuwa nemanki a gurin Tasmia?"
A take ran Emily ya bace
"Matarka bata da hankali, wane irin magana ne wannan? Sai kace akanta aka fara aure? Kwanan baya ta yi min cin mutunci yanzu kuma taje ta daki Kameela hakan be mata ba sai ta hada karyar cewar na aika mata sako?"
"Karki sake kiran matata mahaukaciya karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, ban kira ki dan ki zageta ta ba, sai dan tabbatar da abun da na ji ko na gani"
"Kasan matarka ai zata iya shirya komai saboda da kanta"
"Cikin abun da zata shirya har da tura ma kanta sako da Numberki? Emily karki maida ni dan iska mana, na san matata tana da kishi amman idan an ciza dole za a hura ai"
Emily ta yanke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba, hakan kuma ba karamin fusata Aliyu yayi ba. Keys dinsa ya dauka da wallet ya fito daga hotel din ya shiga motarsa a hanyarsa ta tafiya gida Nura ya kira shi ya sanar masa Dr A-B yana cikin PH.
"Ka je ka ganshi misalin karfe tara, na yi magana da Dr Osman zai hada ku sai ku yi magana ya baka ranar da ya kamata ku hadu, idan a Abuja zaka same shi sai kaje idan kuma a zai iya dubata idan ya shigo PH duk daya domin yana yawan shigowa nan aka ce"
"Okay na gode Nura zan shirya zuwa 9 na tafi gurin ka turo min address da number Dr Osman din"
"Okay"
Daga haka suka yi sallama, Aliyu ya koma gidan sai ya samu Kameela ta yi masa gyara, wato ta hargitsa gidan gaba daya ta fashe abubuwan da zata iya fasawa ta watse wasu. Zaunawa yayi kan stairs din ya dafe kansa yana ta ambaton Allah, daya daga cikin dalilin daya saka yayi ma kansa kuma yayi ma Kameela alkawarin ba zai kara aure ba har da gudun tashin hankali da kannan maganganun ashe dai ko a yanzu bw tsira ba.
EMILY POV.
Cikin bacin rai ta fito Kitchen din, Vito dake zaune a dinning yana karyawa ya bita da kallo.
"Jiya baki kwana a gida ba"
Emily ta kalli Chidimma, domin ta san Vito baya kwana a gidan balle ya san ta kwana ko akasin haka.
"Ni ba karamar yarinya bace, ina da damar na kwana a duk inda nake so"
"You're just 25yrs old kuma kina karkashin ikona dole ne na san a duk halin da kike ciki"
Ta juyo a fusace
"Wai duk wannan gatan da wannan kulawar da ka ba ni ka bani ne saboda ka yi iko da ni? Ka juya ni yadda kake so? Da zarar na yi abu sai kace ina karkashin ikonka bauwa ce ni? Nawa ka biya ka siye ni?"
"Babu kudin da zai siye ki a duniyar nan Emily, ina kulawa da shiga da fitarki ne saboda ke Matata ce"
"I'm not your wife, ni ba matarka bace ba matar kowa ba ce, and i need another maid bana son Chidimma"
Chidimma ta kalli Vito tana girgiza masa kai idonta na cika da hawaye.
"Dan Allah karku koreni aikin nan da shi kadai na dogara da shi nake komai na rayuwata"
Emily ta dauke kai ta fice rike da abincin, motarta ta koma ta shiga ta dauki hanyar asibitin domin kaiwa Tasmia abun karyawa, bayan bacin ran Aliyu na zarfinta da abun da bata aikata ba, yanzu kuma Vito ya kara mata da shi. Ta faka motar a harabar da aka tanada domin aje ababen hawa sannan ta fito rike abincin ta nufi cikin asibitin, tana tafe ranta da fuskarta a bace kamar zata yi kuka.
"Da alama kin fini tsada, shiyasa baki nemi ni ba"
Ta karkato kadan ta kalli gefenta sai ta yi arba da fuskar likita daya taba bata katinsa saboda rashin lafiyar London, tare da wani likita a gefensa.
"Hi"
"Hi, ashe kin gane ni"
Ta yi murmushi.
"Wacan karon na manta ban tambaye ki ba, are you married? Kar mijinki ya fasa min kai"
"No"
"Cool, ya mai jikin?"
"Ai ya rasu"
Ta fada cikin wani yanayi marar dadi idonta na son tara hawaye.
"Ayyah... I'm sorry"
Ya fada cike da tausayawa. Ta sauke kanta kasa ta cigaba da tafiya har suka isa gurin da zai shiga.
"This Way Ma'am"
Ta kalli hanyar da zai bi.
"No ni nan zan bi, akwai wata kawata da bata da lafiya ita na kawoma abinci"
"Toh kuma ba zaki so mu gaisa ba"
"Mun gaisa a nan ai?"
"Asibitin tana da mutane da yawa, ba zai yayu na siyar da ke ba, ni ma akan hanya nake nan da minti arba'in zan bar garinku"
Ya fada yana kallon agogo hannunsa.
"Da alama baki san waye Dr A-B ba ki zo kawai ku gaisa"
Likitan dake tare da shi ya fada, a yanzu kuma Emily bata da wani zabi daya wuce ta yi abun da ya kamata even though bata san makasudinsa na son hakan ba. Da suka jera suna tafiya yake fadar.
"Daman alamu sun nuna min baki da aure, amman na yi tunanin mutumen da ya saka aka nemo ni na duba yaronki shi zaki aura"
"Aa"
"Kin yaudare shi kenan"
"Aa ni bana soyayya da kowa, babu zancen aure a gabana ba zan sake yin aure ba balle na yaudari wani"
Ya dan tabe baki kadan.
"Ihhh da Alama yan'uwa rijalu sun dandana miki gubar soyayya, kin huta ai, ni ma dai ba a dandana min gubar ba amman soyayya bata burge ni, shiyasa mutane har mamaki suke wai ina da shekara 37 na doshi arba'in kuma ban yi aure ba"
Ya bude mata kofar Office din da za su shiga sannan ya tsaya.
"Ladies First"
Sai da ta fara shiga sannan ya shigo, kana ganin Office din ka san ba na shi ba ne, amman a haka yayi mata gurin zama. [6/3, 8:23 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 3️⃣3️⃣
Ya duba agogon hannunsa.
"Wani kake jira ne?"
Ta tambaya tana jin sakewa da shi kamar yadda ta ji a farkon haduwarsa. Sai yayi murmushi