Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 33

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 33

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 33: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 33. "Abun dariya ne, ni bana jiran wani sai dai a jirani, amman ban…

3,261 words

"Abun dariya ne, ni bana jiran wani sai dai a jirani, amman ban sani ba ko abubuwa za su canja wata rana na zo ina jiranki"

"Miyasa baka jira?"

"Wani mataki ne Allah ya kaini, bana jira sai dai a jira ni saboda kullum na tashi aiko aiki har sai na ture idan ina son hutu, saboda haka ya zama mutane sai dai su jira idan na gama wani aikin sai na fara na su"

"Toh amman me yasa kake duba agogo"

Ya wara ido.

"Hmmmmm ashe dai ke ma kin iya sa'ido"

Ta rufe idon tana murmushi, likitan dake tare da shi yayi murmushi ya mike tsaye ya fice daga office din.

"Ya kamata ki saka min number wayarki, saboda mu rika gaisawa ko? Domin na lura kin fini tsada shiyasa da na baki number wayana baki kira ni ba"

Yana maganar yana kallonta har ta bude ido.

"Gashi ko sunanki ban sani ba"

"Emily, sometimes akan ce min Aisha"

"Ehhhh nice name, Allah yasa baki kyamar musulmi"

"Kai baka kyamar Cristian?"

Ya girgiza kai.

"No... Ko kadan Mahaifiyata ahlul-kitab ce ita christen ce kin ga ba ni da hujjar kyamar ki"

Ta nuna shi

"amman kai..."

"Aa ni Musulmi ne mahaifina Musulmi ne, aljanar data aure ni ma ta hana ni aure musulma ce"

Emily ta kyalkyale da dariya...

"Interesting"

Ya fada yana kallonta da murmushinsa mai kyau.

"Wa yace aljana ta aureka?"

"Haka suke cewa wai saboda kullum cewa nake na ban ga wanda ta yi min ba, amman ina tunanin ta fara gajiya da ni ta kusa sakina"

Ta sake kyalkyalewa da dariya.

"you're so funny"

"Yeah my second job is to make you laugh"

Tana kokarin saka hannunta ta rufe bakin daga dariyar da take, Dr da ya fita dazun ya kwankwaso ya turo kofar ya shigo Aliyu na bayansa. A lokacin ne Dr A-B ya mike tsaye

"Bakonka ya zo a late jirgina ya kusa tashi"

"Hakuri zaka yi Dr ka saurare shi kuma ka ba mu lokaci ba sai mun yi ta daku ba"

Cewar Likitan dake tare da Aliyu, Dr A-B ya girgiza kai zai yi magana Emily ta kalli Aliyu da tun da ya shigo ita yake kallo tace.

"Da dai ka saurare shi, ba zan jidadi ba idan ka tafi baka ji uzurinsa ba"

"Emily ai ba zan ce miki aa ba"

Ya koma ya zauna sannan ya nunawa Aliyu kujera.

"Malam Bismillahi"

Aliyu be zauna ba domin baya son yayi maganar cewar yana son a duba matarsa ne a gaban Emily and the way da ya samu Dr A-B jikinsa ya ba shi kamar ba za su jitu ba saboda alama sun nuna masa Dr A-B is arrogant.

"No ka ba mu katinka kawai i will contact you though it"

Dr A-B ya dan tabe baki kadan.

"Okay Dr Osman zai baka Katina"

Ya mike tsaye yana kallon Emily da murmushi a fuskarsa, ita ma ta mike tsaye.

"Toh yanzu kuma sai yaushe?"

"Sai randa kaddara ta yi nufin sake hada mu sai mu hadu mu gaisa"

"Ehmmm hmmm idan kaddara ta sake hada mu, toh na san manufar hakan kuma zan baki mamaki, fatan alheri"

Ya risina mata kadan sannan ya wuce ya bude kofar ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice Dr Osman yayi masa rakiya. Sai da suka fice sannan ya maida idonta kan Aliyu sai ya gwatsaleta.

"Ashe haka kike da arha?"

Ya fada fuska ba yabo ba fallasa.

A take ta hade rai ta turo baki.

"To miye na min magana ba mun yi fada ba"

"Na miki magana zo ki saka wuka ki yanka ni"

Ta sauke idonta kasa.

"Breakfast kika kawo masa ne?"

"Na Tasmia ne"

Ta amsa da dan fushi.

"Toh ki dauki abincin ki fice ko gadin office din ya barki ki yi?"

"Toh ka daina min fada kamar wani ni yarka ce"

"I'm your boss tarbiyarki a yanzu karkashina take dole na gyara miki zama"

Ta duka ta dauki abincin ta nufi kofa ta bude ta fita sai gashi ya fito.

"Tasmia da kika yi sanadin aka yi mata duka yanzu zaki dauki abinci ki kai mata babu ko kunya?"

A nan ta zaburo masa ta juyo a tsawace tace.

"Ni ban aikawa Matarka sakon komai ba, babu dalilin da zai saka na yi maka karya, babu dalilin da zai saka na turawa matarka wannan sakon, kai ma idan kana neman janye kanka daga jikina ba sai ka yi min shari ba, you can walkway ba tare da ka dasa min bakin ciki ba, ba sai ka zarge ni da abun da ban aikata ba"

Ta karasa maganar idonta na cika da hawaye, kallonta kawai yake har hawayen suka zubo mata ta saka hannu ta share. Ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya kama chat din da Kameela ta aika masa daidai gurin da number wayar Emily ta fito ya nuna mata.

"To wa aika? Vito?"

Emily ta karbi wayar ta duba ganin Number wayarta ya matukar bata mamaki.

"Wallahi ban aika ba, ban tura mata wannan sakon ba, kuma Vito baya daukar wayata..."

"Toh waya aika?"

Ya tambaye sannan ya karbe wayarsa. Ta yi shiru tana nazari babu wanda ta fado mata a rai sai Chidimma da Tasmia domin Chidimma ta taba daukar wayarta, Tasmia kuma ta karbi wayarta a jiya tace zata kira ta sanar da iyayenta, sai dai bata saka ran Tasmia zata shirya mata wannan Chidimma kuma bata iya hausa kamar haka ba, a ina ma number Kameela ta fito bayan ta yi blocking dinta.

"Waya karbi wayarki jiya?"

"Tasmia tace zata kira iyayenta bayan Kameela ta mata duka, amman Tasmia ba zata yi hakan ba"

"Karfe nawa kika je gida?"

Ta yi shiru tana nazari

"Karfe tara tayi bayan mun gama waya da kai ne"

Ya duba time din sakon sai ya ga da safen nan aka turo masa shi, ya duba kiran da Tasmia ta masa jiya sai ya kalli Emily.

"Karki yarda na riga ki isa Office"

"Kamar ya kuma? Yaushe na kai mata abun karyawa har na koma gida na shirya na tafi office"

"Wannan matsalarki ce kamin ki zo nan ya kamata ki yi wannan tunanin ba yanzu ba"

Ta kalleshi tana mamakin yadda yake kokarin tsanarta.

"Why do you hate me now?"

"I didn't hate you"

"Zan aje mata abincin sai na tafi"

Ya daga mata kafadunsa alamar he don't care. Da sauri ta yi gaba da abinci ya bi bayanta har ta shiga dakin da Tasmia take, tana zaune kan gadon tana waya Emily ta shigo, shigowar Aliyu ya saka ta yanke wayar tana yana jin wani yanayi da dabam tare da mamakin ganinsa a lokaci daya. Emily ba zata iya fadar zata je gurin aiki ba saboda kar Tasmia ta ji kamar ta fifita aikinta akan lafiyarta dan haka tace.

"Ga abinci nan ki karya, zan tafi yanzu ina da uzuri"

Ta kalli Aliyu sannna ta fice Tasmia na mata godiya murya kasa kasa.

"Ina kwana"

Tasmia ta fada bayan Emily ta fice ta bar Aliyu. Madadin ya amsa mata sai yace.

"Do you plan all this?"

Ta sake dubansa kamar da can ba kallonsa take ba.

"Ban fahimta ba"

"Kin fahimta Tasmia, don't deny it, Emily tace ba ita ta aika sakon nan ba"

"Kuma ka yarda da ita?"

"💯 percent"

Ta nuna kanta gabanta na faduwa sosai.

"To miyasa ni ka zarge ni? Me zai saka na aikata hakan? Yaushe ma na dauki wayar Emily?"

Ya saka hannayensa duka biyu aljihunsa.

"Ban sani ba tukuna, abun da na sani a yanzu shi ne Emily ta yarda dake, ban sani ba ko ta fada miki labarinta, ta sha wahala sosai kamin ta hadu da mu, ta hadu sa musulmai masu gurbatattaccen tunani da son zuciya sun bar mata tabon da take kallon kowane musulmi ma haka yake, sai dai haduwata da ita da kuma ke ya fara sauya tunaninta, toh be kamata ta same mu da wani nakasu ba, ko da musulma ce be kamata mu ci amanar junanmu ba, kuma mu watsar da yardar mutanen da suka minta da mu"

Yana kaiwa nan be tsaya jiran abun da zata fada ba ya fice ba tare da ya bata hakurin zubar hawayen da take ba. Sai da ya fice sannan ta share hawayenta.

"Shi namiji na gari nemansa ake ba sai ya kawo kansa ba, yadda Kameela tana walawa a gidanka tana watayawa abun so ne a gurin kowace mace, ko da ace baka da kyakkyawar sura kulawarce kawai, dole zata burge duk wata mace mai son auren namiji irinka, ballantaba kuma ka hada duka biyun ko uku ma, ga kyau ga kudi ga bada rayuwa irin wanda mace take so, ku kanku maza wata rana ba kusan wanda ya dace da ku ba, Aliyu kana bukatar mace mai hankali mai wayo ba irin Kameela ba"

Ta sauka daga kan gadon

"Kowa da kalar kaddararsa wata kila ni tawa a haka ta zo, son mijin kawata ko ba komai matarka ta kira ni da marar tarbiya kuma ta yi min gorin aure, toh sai na nuna mata rashin tarbiyan, kuma sai na koya mata darasin da ace kewa mace bata yi ma yar'uwarta mace gori"

Ta zauna a kujera ta bude abinci.

"Sai kace ni na fi kowa bakin jini daga fara plan har ya gano ni, wai ni haka rayuwata zata kare ne? Kalar mazan da nake son aure basa zuwa su ce suna so na sai yan wadanda basa cikin tsarina kamar ni na fi kowa bakin jini, gaskiya ba zan bari Aliyu ya subuce min ba, daman tun ganin da na yi masa da farko ya burge ni"

Tana cin abincin tana magana da kanta kamar wata tabbabiya.

KAMEELA POV.

"Ai dama ya samu shiyasa kuma kin ji hausawa sun ce kowa ya ga rana yayi shanya, da bata karya farashinta ba tun farko ta zubar da kimarta Wallahi Aliyu ko marin uwarsa kike yi be isa yace ki dawo gida sai ya neme ki ba? Me yake takama da shi?"

Cewar Hajiya Asma'u Anty taba ya tsina fuska.

" Wallahi kuwa nan kika watsa mana kasa a ido kika tsaya kai da fata babu mai son auren nan kika ce sai Aliyu, gashi nan tun ba aje da nisa ba ya koraki ya nuna wata banza ta fiki muhimmanci ina alkawarin da yayi miki toh?"

"Alkawarin banza, dadin baki ne irin na maza kuma ni daman na san ba da zuciya daya ya aureta ba, ya aureta ne kawai saboda ubanaa ya karbi mukamin ubanki a yanzu, ke kuma ya aure ki ya wulakanta mu, kuma yayi nasara tun da kin ba shi hadin kai"

Hajiya ta fada, sai Anty Shafa ta sake karba mata

"Ai kara ma auren ya kare kowa ya huta, idan abun be tsaya iya nan ba gaba ba a san ya zai kasance ba, kuma dan Allah Hajiya ki hana D Alhaji kiransa dan jin ba'asi ko kiran iyayensa"

Hajiya ta daga hannu.

"Ai Alhaji ma ya fini daukar zafi shi da kansa yace tun da ya turo masa ya gida sai ya san yarsa tana da gata"

Ganin ba za su barta da damuwar abun da ya isheta ba ya saka ta tashi ta bar musu bangaren gaba daya ta koma part din Mama Barakat ba dan ranta ya so ba, kan kujera ta zauna tana rushe da sabon kuka bayan wanda ta sha har ya kumbura mata ido ya hana ta cin abinci tun da ta dawo gida. Mama Barakat ta aje abincin dake hannunta ta taso da sauri ta dawo kusa da Kameela dake zaune kasa ta zauna kan kujera.

"Subhanallahi Kameela lafiya? Yaushe kika zo?"

"Aliyu ne yace na tafi gida sai ya neme ni"

"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un Me kika masa?"

"Ban masa komai ba, saboda wannan bakar kafirar ne, ba ma ita kadai ba har kawata yake bibiya"

"Abun be yi dadi ba, amman kin yi bincike? Kar ya zama kin masa mumminar fahimta ne, ko kuma kim yanke hukunci cikin fushi"

"Mama Baraka har test fa Emily ta turo min tana fada min magana son ranta"

Mama Baraka ta yi shiru na mintuna tana shafa Kameela alamar rarrashi sannan tace.

"Kina da hoton Emilyn ne Kameela?"

"Ba ni da hotonta"

Mama Baraka ta sauke ajiyar zuciya domin tun a fadansu na farko take son ganin hoton Emily saboda yadda Kameela ta siffanta ta.

"Ki yi hakuri idan mahaifinki ya dawo zamu yi magana da shi"

"Aa ni na hakura ba zan koma ba, kar ma ki masa magana ko Aliyu ne autan maza ni ba zan koma gidansa ba"

"Ba'ayi ma aure haka, tun har kuna son junanku baki san abun da Allah ya tsaro a tsakaninku ba, hakuri zaki yi"

Kameela ta kara fashewa da kuka tana fadar ita ba zata koma ba ta hakura da Aliyu.

_______________________

Sannu 'yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko'ina!

Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/11, 11:51 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

Page 3️⃣4️⃣

Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana.

EMILY POV.

Daga Asibiti kai tsaye gurin aikin ta wuce saboda gargadin da Aliyu yayi mata, duk wanda ya ganta ya san zuwan kawai ta yi ba dan ta shirya ba, domin gashin kanta a yamutse yake tufafin jikinta ma regular one ne irin da wanda ta saba sakawa a gida kafafuwanta sanye da talkamin da ta saba sakawa a gida.

A yau din ma data shigo office sai ta rasa me zata yi saboda bata shiryama zuwan ba, dan haka ta zauna a kujerarta taba ta kallo kofa kamar ta san Aliyu zai shigo, after like 30 min ya turo kofar ya shigo fuska ya yabo ba fallasa.

"Ai na dauka ba za ki ji magana ta ba"

Yana maganar wayar dake hannunsa ta yi ringing da ya duba sai ya ga sunan Abokinsa Turhan kuma direct kira irin wanda ba kadafai yake masa ba, ba ma ta whatsapp ba, Aliyu ya kalli Emily dake cizon akaifa ya kalli kiran what a coincidence.

"Sallamu Alaikum"

Ya amsar wayar idonsa na kan Emily.

"Hello Aliyu, ya kake?"

"Ina lafiya ya kwana biyu"

"Alhamdulillah"

Daga haka Turhan be sake cewa komai ba yayi shiru kamar yana jiran Aliyu ya fara magana, Aliyu ma ya kasa cewa komai feeling so guilty.

"Ya Ammy"

"Bata jindadi, ina shirye shiryen shigowa na ganta, Aliyu har yanzu babu wani labari ta bangarenka?"

Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya juya baya yana shafa kansa.

"Ciwon Ammy yana da alaka da hakan ne?"

Turhan ya sauke ajiyar zuciya.

"No Aliyu i want to make things right, mahaifiyata ta yi going through abubuwa marasa dadi a zamanta da mahaifina, and ni kadai ta haifa ni ne kawai last hope dinta and i failed her, idan na zauna na yi tunanin wasu abubuwan ina jin babu dadi kuma ina son na kyautata mata, ina bukatar Emily a yanzu saboda mahaifiyata if i can turn back the clock, zan gyara abubuwa saboda mahaifiyata, I'm losing my sleep bana cikin kwanciyar hankali a yanzu, Aliyu na shiga na fita na yi iya yadda zan iya just to fix what i broken, amman na gagara samun yarinyar nan, kuma mahaifiyata ta ki ta fahimce ni, rayuwa tana ta tafiya ina tsoron kar ni na mutu ko na rasa mahaifiyata ta tafi da wannan kuncin a ranta"

"Hakan yana nufin ka bata abubuwa da yawa Turhan? Akwai abun da baka fada ba?"

Emily na jin sunan Turhan sai ta mike tsaye da sauri ta zagayo gaban Aliyu ta tsaya cikin tashin hankali tana girgiza masa kai.

"Babu amfanin fada, zamantakewa ce ta aure ka auri wanda ba type dinka ba, ba ka sonta dole za a samu wannan, balantana lokacin tunani be tsaya kamar yanzu ba, and Aliyu you will never know what is arranged marriage saboda kai da Kameela auren soyayya kuka yi, komai zan fada maka ba zaka fahimta ba, yanzu dai Maneer ya ba ni shawarar cewar na saka kudi da tsohon hotonta akan duk wanda ya ganta zan ba shi wannan kudin, ya kake ganin abun?"

Aliyu ya ji gabansa ya fadi gumi ya keto masa, be taba aikata wani abu ya ji kansa mai laifi ba irin boyewa Turhan Emily da yayi, anya zai iya bari Abokinsa ya bata kudi akan abun da zai iya masa kai tsaye.

"Hello.."

Turhan ya fada a dayan bangaren, Aliyu ya amsa a rikice yana dawowa daga duniyar tunanin da yake.

"Ehm Hello, Turhan yanzu ina Office bari idan na samu natsuwa na koma gida sai na yi tunanin abun da ya kamata mu yi"

"Okay"

Ya yanke wayar ya kalli Emily.

"Ban san me kuke tattauna ba, amman dai ba zaka fada masa ina nan ba, i trust you"

Ta fada idonta tab da hawaye.

"Turhan Trust me, ke kin yarda da ni to yardar wa zan karya? Kun saka ni a tsakiya I'm feeling guilty, wadanda ban sani ba ma suna magana da ke like likitan nan na yau? Shi kuma a ina kika san shi? Kina zaune a tare da shi har kina masa dariya bayan abokina yana can cikin damuwa saboda nemanki? Anya na yi adalci"

"Ka riga ka karya nasa tun da har ka kasa fada masa inda nake duk tsawon lokacin ne, hakan yana nufin nawa ya fi karfi a gurinka dan Allah karka karya, idan ya sani ba zai bar ni da yata ba ita kadai ta rage min, kuma baka san iya abun da mutumen yayi min ba i don't need him"

Damuwa karara a fuskar Aliyu, ya nufi kujera ya zauna ya dafe kansa.

"There is something about you Emily, kin saka na yi abubuwa da ba halina ba, like boyewa abokina gaskiya, kamar saka mahaifina ya saka NDLEA su bincike gidan Vito kai tsaye daga Abuja, so that idan an same shi da laifi a dauke shi ki samu yanci, amman kika ci mutunci akan haka, and na kyale haka be bata min rai ba, like sitting here in your office talking to you?"

Ya dago ya kalli Office din sannan ya kalleta. Hawaye ya sauko mata.

Readers Also Read