Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 41
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 41: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 41. Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo…
3,366 words
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 4️⃣1️⃣
Sai da ta bar gurin sannan na fito na sallami mai achaba na koma ciki na rika ɗana dake ta ihu, gaba daya ya ki yarda da ni saboda be gane ni ba. Kansa na rike na saita shi ya fuskanci sai na koma kiransa da sunanyen da nake masa ina hadawa da Momy, a take ya tsagaita kukan da yake ya kalleni sai na yi masa dariyar dake tafe da hawaye na rungume shi ina jin kamar za a sake raba ni da shi ne.
Kwana na uku a coci, a tsawon kwanakin nan bana sallah bana saka hijab duk wani abun da ya danganci musulunci bana yinsa, saboda na fada musu zan koma addinin Christianity, sai dai a can kasa zuciyata na ni na san ban shirya barin addinin musulunci ba, ba dan mutanen cikinsa sun yi min gata ba sai dan ina jin natsuwa da addinin a cikin zuciyata, domin addinin musulunci addinin mai tsari da tsabta da dokoki, ni kuma mace ce mai son zaman lafiya mai son natsuwa. Sun mutunta ni sosai a cocin domin gidan wani pastor aka kai ni, abinci sai na ture gurin kwanciya mai kyau, matarsa tana ta nanata min halayyen musulmai basa da kyau kuma daman su basa son kafirai, har take cewa na yi kuskure da na bar addinin da ace ban gane gaskiya na dawo ba da Yesu yayi fushi da ni kuma ya kona ni.
Kusan duk wa'azinta jinsa kawai nake, amman a zuciya ina kyamar abun, ana gobe Lahadi wanda ta kama ranar coci a ranar za a min wanka da ruwa mai tsarki kuma a maida ni addinin kirista a ba ni bibles kamar yadda na sani yake a hukunce kuma matar ta jaddda min, sai na dauki London na goya ma sanya hijab dina cikin giyon na fito da sunan zagayawa harabar cocin, na nufi gate da yi ma mai gadin karya cewar zan fita naje na dawo kuma sun san da fita ta, domin an fada masa duk wanda ya zo nemana kar ya bar mutum ya shiga sai an sanar saboda ni da su muna tunanin Ammy zata dawo nemana.
Salin salin na fice daga gidan, ba kuma dan na san inda zan je ba sai dan ban shirya komawa addinin ba, na hau achaba na tambaye shi dan Allah wace umguwa ce nesa sosai da cikin gari, unguwar da san yi tafiya sosai sannan a isa gurin, ya fada min sai na ce ya kai ni can, mun yi tafiya sosao kamin muka isa unguwar dake kama da sabuwar unguwa ma sauka na ba shi kudinsa na nisa cikin unguwar ina ta kallon yadda tsare tsarenta yake, har na hango wani gida dake da fanfo da kwararo a ciki, na dauki leda na tara ruwan na fara sha sannan na shayar da ɗana na yi alwala sallah na fara yi na rama duka wandada aka biyo ni har na ji na gaji, a lokacin kuma wata zuciyar take ta fadan min na koma dai domin wannan addinin be karbe ni ba, amman dayar data ci karfina ta hana ni komawa na zauna a gurin har dare, a nan yunwa ta fara tunkaro ni ga yarona be san babu ba. Kukansa ya saka mai gadin lekowa ya tambayi tafiya na fada masa yunwa yake ji sai ya shiga ya dauko ragowar abinci ya bani na bawa yaron da muka gama yace dan Allah mu kara gaba kar mai gidansa ya dawo ya same mu a nan zai masa fada.
Na yi masa godiya na tashi na kara gaba, haka na yi ta rayuwa a unguwar daga wannan kwararo sai wannan wani gurin a hantare ni wani gurin a bani abinci ko sutura wani gurin kuma a ba ni hakuri, gaba daya na koma wata kazama saboda babu gurin da zan raba na yi wanka, bahaya ma sai na shiga daji, rayuwa ta yi tsanani gareni a lokacin, ga ciki ga yaron da ba lafiyayye ba, idan ciwonsa ya tashi sai dai na yi ta kuka domin ban san wani abu da zan yi ba bayan wannan, ni da shi muka rame muka lalace, nakan shiga gida gida neman aiki ko wanki, idan na samu mai son wanki na yi ta murna na wanke a biyani na ciyar da kaina da ɗana, na samu wani tsohon shagon kwano na laba ciki nake kwana ciki nake wuni idan ina cikin unguwar.
Tun mutane ana jin tsorona a unguwar har aka fara sabo da ni wasu ma idan sun raga abinci da kansu suke kawo min saboda suna min kallon mahaukaciya, wani lokacin ba ni sadakar kudi ko abawa ɗana da haka nake ta fadi tashi har cikina ya tsufa, wani sa'in sai na yi tafiya mai nisa zuwa wata unguwa nake samun abun da zan ci, kuma ban sake bawa kowa labarina ba, idan naje gida sai dai na yi bara ko kuma na tambaya idan suna bukatar a musu wanki ko wani aiki. Wasu suka kam tambaye ni waye uban yarona ko kuma cikin da nake dauke da shi sai nace musu ban sani ba ni ma, hakan ya saka suka kara daukata mahaukaciya suna tunanin kamar fyade aka min na samu cikin ko kuma wani ya yaudare ni.
Akwai masu fadar wai ko dai kishiya ta yi min asiri saboda ina kyau ta raba ni da mijina? Su tambaya daga ina nake sai na ce Lagos, idan aka ce Lagos a ina? Sai na ce ban sani ba, to gurin wa zan ce daman? Har lokacin ina jin da kamar akwai sauran kurciya a tare da ni, wata kila kuma shiga mawuyacin hali ne yasa ban taba kula da watan cikina nawa ba, ban taba kirgawa na gane ba, ciki dai yana ta girma kuma yana motsi, idan na ji motsin cikin sai na ji zuciyata ta yi fari tas kamar ba ni da damuwa, ni dai burina na haihu lafiya na samu karin wasu iyalin...
Ana haka wata rana nakuda ta fara taso min tana kwantawa na kwashe kusan kwana biyu sai ta motsa min sai ta koma, idan ta laba min sai na cigaba da harkokina, wata rana na fita neman abun da zan ci ban karasa inda zan je ba aka sako ruwan sama na kuda ta taso min mai karfi kamar zan fita hayyacina gashi kuma na yi nisa da gida ba zan iya komawa ba, ɗana kuma ya firgice saboda tsoron ruwan da iska sai ihu yake min ni ma kuma ihun nake a gefen hanya babu wanda ya kula ni sai kai Aliyu, shi ne farkon haduwata da kai, na zan iya manta wannan alherin ba, na gode na gode Aliyu, a lokacin ne na rike hannunka har agogon ya cire ya dawo hannu sai na matse shi ina ihu na yi tunanin mutuwa zan yi ma gaba daya, ka taimake ni ka dauke ni ka kai ni Asibiti, duk wani taimako daya kamata likitocin nan sun ba ni na wahala sosai kamin na samu na haihu da kaina, ada har ina tunanin ko dai sai an fasa ni za a iya cire abun da ke cikina saboda na kasa nishi.
Da na haihu sai suka bukac a kawo kayan jaririya ba ni da su, zanen da aka hadeta a ciki ma tsohon zanen wata mata ta bada a gurin aka lulkube Fatima, suka ce ina audugar da zan saka ina kaza ina kaza, na ce duk ba ni da, sai suka tambaya wanda ya kawo ni waye shi? Nace ban san shi ba taimakona yayi, a nan wata nurse ta fita ta shigo min da pad ta pant ta kuma ba ni zane na daura sannan suka canja min daki suka kawo ni wani dakin na dabam suna tambayar ina yan'uwana ya kamata na ci abinci na ce musu ba ni da kowa, daya daga cikin wadanda suka karbi haihuwa ta ta kawo min agogonka ta ce ga wannan kin saki a kasa dazun na karba na rike ga. Daker na iya awa hudu a asibitin na kamin na saci kafa na gudu da ɗana da kuma jaririya dana haifa, zanena mai jini da uwar da ke fadowa bayan haihuwa a asibitin na bar musu na gudu. Ban nisa sosai da unguwar da asibitin take ba jiri ya debe ni na fadi ban sake sanin inda kaina yake ba.
Sai da na farko naga ana min fifita ga jaririya a kusa da ni ga kuma London yana ta kuka, mutane nata min sannu aka ba ni abinci na ci sannan aka dauke ni zuwa gidan wata mata dake kusa ana tambayar a ina nake daga ina na fito na fada musu a gidan na kwana sai washe gari bayan na karya matar ta siya min wani pad ta bani tsohon wandonta na saka bayan ta dora min ruwan zafi na yi wanka, ta bani wani tufafin na saka da hijab, makota kuma suka kawo min tsofin kayan jarirai na sakawa Fatima, ta kawo min abinci na ci na sha kunu sannan mai gidanta da wasu mutum biyu yan unguwar da kuma ita matar kanta, suka dora ni a napep muka tafi unguwar da nake rayuwa na nuna musu inda nake kwana sai suka fara tambayar wadanda suka san ni a unguwar, kowa sai yace da rana tsaka ya gan ni a gurin kuma ba ni da cikakiyar lafiya, cikin ma suna zargin yi min aka yi ta karfi, wasu kuma su nanata wai asiri aka min.
Ni dai jinsu kawai nake idan aka tambaya daga ina nake sai na ce Lagos wane guri a Lagos nace ban sani ba, sai suka yanke shawarar za a kai ni police station ayi report, ina jin haka nace ba zan je ba da suka matsa na saka musu kuka a dole suka koma can gefe suka yi maganarsu sai aka dawo aka fada min wai zan bi matar zuwa gidanta na koma can da zama a nan ma na tirje domin na san akwai abun da suka shirya, ni kuma ina tsoron a yadani Cocin da na gudu su gani ko kuma Ammy. Na dake akan nan gurin zan zauna da kowa ya watse na goya jaririyata na kama hannun dana na bi ta cikin gidanen dan kar ma wani ya gan ni na gudu na bar unguwar.
Tafiyar kuma wani sabon labari ne, domin ba san kowa a inda na tafi ba, haka na kwana a jikin wata tsohuwar gina sauro ya cije ni ya cije yarana musamman Fatima dake ta jaririya a lokacin, a daren ne na rana mata suna Fatima sunan da ba a yanka mata rago ba kamar yadda kuke yi a addinin musulunci, a lokacin akwai son addinin a raina shiyasa na zabi sunan da yake min dadi bayan Aisha, da gari ya waye na barka dankwalina na yi amfani da shi domin pad din ya lalace kuma ba ni da wani, na cigaba da tafiya kafafuwana sun gaji haka nake ta mika su ga danyen jego ga yaro karami idan ya fasa min wani ihu sai na rikice, na daukeshi idan na gaje na aje shi haka dai har na isa wata unguwar marowata domin duk gidan da na shiga na yi roko hakuri ake ba ni wasu kuma su koroni.
Yunwa ta ci ni sosai ga tafiya na gaji har na fara ganin jiri, tsakaninkanin kafafuwana ma ciwo nake ji sosai domin ban samu hutu da kulawar daya kamata ba bayan haihuwar da na yi kwana biyu da suka wuce. A haka har na isa kofar wani karamin gida irin na mazan nan da ba su da aure a bude na sallama na sallama na ji shiru sai na taka ciki kadan na jiyo kamshin girki, sai na yi sunsun na dawo baya na koma can bayan gidan dake da wata gona na samu wani guri na raba na kwance Fatima dake bachi yarinya kyakkyawa fara sol na kwantar da ita a gurin na zaunar da London dake ta kukan yunwa na fito na koma wacan gidan dake bude na kara sallama ina sallama ina shiga ciki har na kai inda nake jiyo kamshin a wani karamin Kitchen na duba waiga na ga babu mai ganina na nasa kafata a Kitchen din, sai na yi arba da mutum kwance cikin jini farar vest din dake jikinsa duk ta bace da jini, da sauri na dawo baya ina numfashi daker, na ga tashin hankali kala kala amman ban taba ganin gawa ba sai a ranar, na fito da sauri na falfala da gudu na dawo gurin yarana ina dawowa na samu London yana ihu yana yunwa, ni kaina kuma yunwar nake ji, sai hakan ya saka na manta da tunanin abun da zai biyo baya na sake komawa zuciya na zillo kamar zata fado na shiga Kitchen din na duba ko'ina har na hango karamin gas a kusa da kafar mutumen da ban san ko waye ba, da alama dai girki yake aka kashe shi, na fito na sake leka waje na dawo da sauri na nufi girkin na bude indomie ce har ta fara kamawa na tara hijabina na juye na saki tukunyar na fito a guje ga zafin indomie ga tashin hankali na dawo gurin da yarana suke na cire hijab din gaba daya na aje a gurin na bude indomie na saka hannu ina hurawa ina ci ina bawa London.
Ban an kara ba ma ga mutum tsaye a gabana dana daga kai na kalleshi sai na ga fuskarsa babu annuri ga katon Cross a wuyansa, ashe ma ba shi kadai yake ba har da wasu mutun uku.
"Miye alakanki da Risk Guy"
Ya tambaya cikin hausarsa da bata gama zauna wa a bakinsa ba.
"Ban san waye shi ba, ni abinci kawai nake nema"
Ashe yayi zaton na ga lokacin da ya aikata kisan kan ne, a take ya nuna Fatima da bindiga.
"Jaririya ce, bata san komai ba bata maka komai ba karka dauki alhakinta"
Ya maida bindigar a gurin London dake ihun ganin bakuwar fuska.
"Ba shi da lafiya, Autism ne kuma be maka komai ba"
A take ya dawo da bindigar a kaina.
"Idan ka kashe ni yarana ba su da wanda zai rike su ba su da kowa sai ni, ni ma ba ni da kowa sai su, Wallahi ban ga abun da ka aikata ba kuma bazan fadawa kowa ba, abinci kawai naje nema tun jiya rabona da abinci ni da yarona yunwa muke ji, dan Allah ka yi tafiyarka ni ban san waye kai ba, kuma daga nan tafiyata zan yi daman a hanya nake, ina neman mafaka ba ma dan yarana da sai nace maka na shirya mutuwa a yanzu"
Ina maganar cikina da muryata suna rawa ina kuka sosai a take Fatima ta farka ta fara kuka ga London yanayi. Ya kalli yaran ya sake kallona sannan ya sauke bindigar ya juya ya tafi, ni kuma na dauki yata na rumgume London a dayar cinyata ina hura abinci ina ba shi ina kuka. Kamin na daga kai sama na kwala wani irin ihu iyakar karfina sai kuma na tashi na goya Fatima da sauri na dauki London na dauki agogon ka Aliyu da nake ta yawo da shi na fita gonar domin na fara hango mutane kar ayi zaton ni na kashe shi alhalin ban ma tana ganinsa ba sai ranar. Na yi nisa da gonar na samu wani ice na zauna a gurin na rumgume yarana ina kuka jikina nata rawa ina fargabar me kuma zai sake faruwa da ni. Ashe mutumen daya tashi kashe ni yana biye da ni saboda yana ganin kamar zan iya tona masa asiri ne, a nan kamar daga sama a sake ganinsa gabana sai ya saka hannunsa ya dago fuskata ya kalleni ni ma na kalleshi sai ya hura min abu a fuska mai kamar farar hoda amman yana da karfi sosai da zogi domin ina shakarsa hankalina ya bace...
***. ****. ****
Aliyu ya lumshe ido ya jinginar da kansa yana kallon sama, kwallar dake makkale a idonsa suka sauko masa ta gefen idon, Fatima na gani ta fara masa tambaya.
"Ba za mu isa Lafiya ba? Mutuwa za mu yi?"
Ya bude idon da sauri ya kalli Fatima yana murmushi domin be san ma kwallar ta sauko masa ba. [6/28, 10:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 4️⃣2️⃣
Tausayinta da na mahaifiyarta ya ratsanshi ya saka ya tare hawayen yana murmushi sannan ya shafa kanta.
"Aa Lafiya za mu isa In Shaa Allahu, kawai wani abu nake saurare na ji tausayinta shi ne"
Ta yatsina baki irin na su na yara tana wani iyayi.
"Ni bana yin kuka wa mutane, mutum idan yana da matsala ai shi zai yi kukansa ko?"
"Eh amman tausayawa yana da kyau, ana son haka"
"Okay"
Ta amsa ta cigaba da kallon da take.
"Mun kusa sauka"
"Okay"
Ta amsa ba tare da damuwa ba. Aliyu ya sauke numfashi a hankali idonsa basa masa gizon komai sai fuskar Emily, and he remember yadda suka tsabanin kira har ta yi ta masa dariya a waya, sauti dariyar nata dawo masa, ya tuna haduwarsu a office da tsabanin da suka samu na shiga Elevator da lokacin da ta yi masa tambaya har ta so ma magana da yaren da bata yi zaton yana ji ba, tunani na ya jefo masa ganin da yayi mata na karshe da yadda take ta murmushi kuma murmushi yayi mata kyau a cikin bakar abayarta kamin ya ankara sai gashi yana nasa murmushin a take.
"You deserve happiness..."
Fatima ta amsa masa da sauri tana dagowa ta kalleshi.
"Yes i deserve it"
Kakkaurar dariya ce ta subuce masa irin mai gunna da kal kal.
"Yeah you deserve happiness too baby"
A rasa kuma sai ya ce.
"And now i know why Vito hate you, idan baki son mutum ya shiga uku wannan baki naki is something else"
Ya kunna dayan voice din wanda shi ne na karshe ya cigaba da saurare, wanda a cikin yake son tabbatar da wani aukuwar wani abu ko akasinsa.
***. ****. ****.
Daga lokacin da na shaki wannan hodar ban sake sanin inda hankalina yake ba, ban kuma san tsawon awanin dana dauka cikin gushewar hankalin ba, ni dai na farko da karfi ina jan numfashi, numfashi yana janyewa sai dakin da duk abin da yake ciki yana ta juya min ina jin jiri ga jikina a jike da alama ruwa suka zuba min.
"Yarana yarana yayana, su kadai gare ni yarana"
Yarana kawai nake nema domin su ne a raina, ruwan suka kara watsa min aka kama kaina aka soma a cikin wani bokiti dake cike da ruwa aka cire suka rike gashin suka jijjiga ni da karfi, a take na fara amai domin akwai yunwa a tare da ni ga kuma abin da na shaka warin da nake jinsa wani iri a hancina yana kai min har makoci, ga kuma jijjigar da suke min. Yar indomie da na ci ce na amayar na kwanta a gurin a wahale ina ta kiran sunan yarana.
"Fatima ta... Ibraheem.... Yarana..."
"Ke musulma ce?"
Ita ce tambayar dana fara ji, na dago na kalli mai tambayar daker har lokacin ina dan ganin jiri ga jikin nawa ya kara mutuwa.
"Mu kashe ta kawai boss, duk yadda aka yi budurwarsa ce ko kuma ta san wani abu kansa kawai tana wasa da hankalinmu ne"
Na ji dayan ya fada da halshen igbo, sai dayan ya ce.
"Ko ma ba matarsa bace wannan ai kazama ce daga ganinta, zamu iya kashe ta dai saboda ta san mu muka aikata kar ta kara a gaba ta fada"
"Dauko wuka"
Wanda yake babbansu ya fada a take na tashi zaune na ce.
"Wallahi ban san wanda kuka kashe ba, bani da alaka da shi, ku yarda da ni mana"
Chapter notes and social links
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/26, 9:29 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL