Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 42
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 42: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 42. Na amsa musu da yaren Igbo sai duk suka cika da mamaki, ogan na su…
3,375 words
Na amsa musu da yaren Igbo sai duk suka cika da mamaki, ogan na su ya taso ta zo inda nake ya turani da kafa na koma kwance ya dake wuyana.
"Taya kika san me nake fada?"
"Ina jin yaren igbo"
Na amsa daker har bakina ya fara zubar da jini domin talkamin da ya take ni da su masu zafi da nauyi ne. Ya daga kafarsa
"Ya kike jin yaren?"
"Saboda na zauna a Lagos"
"Wacece ke?"
"Labarin yana da tsayi"
"i don't care ki fada min yanzu"
A dole na takaita labarin na fada masa abubuwa masu muhimmanci har zuwa inda ya gan ni. Kamin yace komai dayan daya dauko wuka yace karya nake na tsara komai ne.
"Me zai saka na tsara komai?" ai ba biyana za ku yi ba, ba wani abu nake nema daga gareku ba, me zai saka ba za ku bincika ba?"
"ina da mutane a ko'ina har Lagos zan saka a bincika min Idan karya kike zan kashe ki"
"Na yarda"
Na amsa a take, sai ya saka aka dauko masa takardar na bada address din guraren da komai ya faru ya rubuta sannan ya tashi ya fita ina tambayar ina yarana. Har ya fice be amsa min ba, bayan ya fita wani ya shigo min da yaran London yana ta bachi kai langabe wata kila ya dame su da kuka ne suka shaka masa irin abun da suka shaka min, Fatima kuma tana ta tsosai hannu tana sauke ajiyar zuciya irin na babyn da ta yi kuka ta gaji.
"Ba zaki fada mana gaskiya ba ko?"
Na kalleshi na rasa me zan sake cewa, shirun da na yi ya saka shi fiddo wata karamar wuka ya yanki kafata da ita sai da na fasa ihu.
"Ban san komai ba gaskiya na fada"
Na matsar da yarana na rumgumesu domin na lura Fatima yake kallo zai iya cutar da ita. Ya mike tsaye ya fice haka na zauna a dakin har dare jini na zubar min a kafa ga aman da na yi a gurin ga kunzugun da na yi ina son na canja ba ni da wanda zan saka nonona na dauke babu ruwa saboda ban ci komai ba, ga tsoron ban san me zai faru da mu ba, ga kuma ɗana be farka ba har lokacin, abubuwa suka hade min goma da shirin. Ina cikin wannan halin shugan na su ya sake shigowa ya kalleni yana toshe hanci. Ya haska ni da kyau ko'ina na jikina.
"Waya yanke ke ni a nan?"
"Wannan ne ya yake ni, kuma gaskiya na fada muku ban yi karya ba"
"Waye?"
"Wanda ya kawo min yarana"
Ya juya ya fita be jima ba ya dawo tare da mutumen ya haska min shi.
"Wannan ne?"
"Eh"
Mutumen ya bude baki zai yi magana Shugaban na su ya ciro bindiga ya harbe shi a ramen wuya a take ya fadi kasa yana karkari jini ya samu hanya kamar ruwa, ni kuma na shiga aikin ihu yana daka min tsawa bana ko ji sai ihu nake, jikina na rawa hankalina ya tashi ban tana ganin an kashe wani a gabana ba sai ranar, ban daina ihun ba sai da suka shaka min wani abun a hanci hankalina ya sake bacewa. Da na sake farkowa farkowa sai na gan ni a wani daki na dabam yarana suna kusa da ni sun sai kuka suke, ashe tun da suka shaka min ban farko ba sai safe. Na kama su na rumgume ina jin jikina ba karfi, can anjima sai ga wani ya shigo ya tambaya me nake bukata yanzu?
Na fada masa ina son abinci. Sai ya fita ogan da kansa ya shigo min da abinci ya aje min babu ko zancen wanke hannu balle baki a take na bude shinkafar na fara ci, Ibrahim ma ya rika ci da sauri ko minti biyar ba mu yi ba muka cinye abinci har muna neman kari. Shi dai yana tsaye yana ta kallona.
"Akwai bandaki a nan ki yi wanka, za a kawo tufafi ki canja tare da yaranki, and why are you bleeding?"
"Saboda sabuwar haihuwa ce"
Ya juya ya fita. Ya kawo min tufafi dogayen riguna da pad da panties ga kayan yara na maza da na jarirai. Haka na yi rayuwa a dakin na tsawon kwana uku a yan kwanakin nan na samu kulawa da abinci mai kyau wanda rabon da na ci shi tun bayan da na bar gidan Ammy, ko a sudan tura abinci kawai nake ba dan ina iya ci ba kuma ba dan ina jindadinsa ba sai dan babu yadda na iya. A ranar da nake cika kwana hudu ya shigo ya same ni ina zaune a kasa domin a kasa muke kwanciya ni da yarana gashi tiles ne, Fatima har tari take, Ibrahim kuma yana zazzabi har kuma lokacin ban san a wane gari nake ba balle unguwa azo kuma zancen gida. Ya zauna kasa kamar yadda nake zaune yana kallona.
"Emily na bincika labarinki a Lagos, here in Kaduna places din da kika zauna da Kaduna, a Sudan ne kawai ban bincika ba, and you're right akan abun da kika fada baki da alaka da mutumen da kika nake zargi, this is the first time da na ji tausayin wani ya kamani sosai wani da ban sani ba, and na ji dadi da ban kashe ki a take ki ba. Emily ina da kyakkyawan sako a gareki"
Shirun da yayi ne ya saka na kalleshi sai da ya karanci natsuwata sannan ya ce.
"Wannan ne karo na farko da nake son na kyautata rayuwar wani, na yi abun alheri a gareki, Emily ina son ki zauna a karkashina zan baki kulawa zan miki gata ke da yaranki, zaki zama a cikin ikona ni kawai cin amana ne bana so, wanda kika ga na kashe ma amanata ya ci, kina son haka"
Na daga masa kai.
"Tohm amman fa bisa sharadi daya, zaki bar wannan addinin ki koma addinin ki na asali, domin babu abun da na tsana kamar musulunci da musulmai, kuma kin zauna da su a yanzu kin fahimci yadda suke, idan kin yarda ki fito waje ki same ni, yau zan bar garin nan"
Ya tashi yayi tafiyarsa, a lokacin zuciya da tunani suka fara min rawa, har na kasa zaba tsakanin addimai guda biyu, an kai ruwa rana daga zuciyata zuwa tunani kamin na fahimci komawa asalin addinina na shi ne gata ne, kuma shi ne rufin asirina ko da yake ban sani ba a lokacin ko shi ma zai ci amana ta ne, amman ba ni da wani zabi domin na gaji da rayuwar dake. A take na dauki Fatima na saba a kafada na rika hannun Ibrahim muka fita ta kofar dakin da sai a ranar ya bar min ita a bude. Dana fito sai na hango wata kofar a bude na nufi gurin haka na rika bin kofa kofa har na fito harabar gidan dake cike da ciyayi ga kuma wani bangare na gidan da ba a gama ginawa ba.
"Zaki bimu ne?"
Ya tambaya yana kallona da fuskarsa mai ban tsoro. Sai na daga mishi kai.
"Kin yarda da sharadin?"
"Nan ma na daga mishi kai"
"Miye sunan wannan yaron"
"Ibraheem"
"Yarinyar fa?"
"Fatima"
"A cikin sunan mata ina jindadin Lisa, daga yau sunanta Lisa, shi kuma London shi ne sunan da na fi so, ke kuma zaki koma sunanki na asali Emily no more Aisha, that's my number one rule My name is Vito (King)"
Ya kada min kai sai yaronsa ya bude min mota na nufi motar na shiga can baya domin mai gida uku ce, shi kuma ya zauna a tsakiya direbansa a gaba. Daga kaduna da direban yaja motar be tsaya ko'ina ba sai Abuja, muna isa ya wuce da mu Airport tun kamin mu bar garin Kaduna ya tambaye full name dina na fada masa ashe zai siya min ticket ne domin muna isa Airport din bamu wani sha wahala ba muka shiga jirgin ya daga zuwa garin da ban taba tunani ko mafarkin zuwa ba wato Part hartcour.
A gidansa muka sauka akwai tsoro sosai a gidan domin a kowane lumgu da sako na gidan yaransa ne ga Camera ta ko'ina, a wani bangare na gidan ya aje shi, ya wadata ni da komai ya samo mai aikin da zata kula da yarana ya nemawa London asibiti mai kyau aka fara duba shi ya saya masa kayan wasa. A lokacin ne na ji na tsani musulmai har bana son jin labarinsu ko ganinsu. Ya kan ziyarce mu lokaci zuwa lokaci har na shekara daya a gidan ban san sana'arsa ba, amman ya wadata ni da komai na more rayuwa sai dai baya bari na tafi ko'ina kuma babu wanda yake shigo min.
Da jindadin ya samu sai jikina ya dawo, wata rana ya shigo yana kallona yace yanzu me nake bukata, na fada masa da ace zan samu dama zan sha wani abun da zai rage min kiba ne domin ta fara damuna, kuma ina son wani abu da zai iya dauke min hankali domin ina yawan tunanin abubuwan da suka faru har mafarkinsu nake. Tambayar daya fara min ita ce zaki iya karatu? Nace zan iya, sai yace zai sama min duk abun da ake bukata zai fitar da ni waje na yi karatu kuma zai bincika abun da ya kamata akan rage kibata. Kamar wasa sai ga shi ya sama min takardun primary da secondary, ya zaba min London a matsayin kasar da zan tafi na yi diploma in business administration. Ya kuma fada min da yata zan tafi domin akwai gurin da ake bada ajiyar yara a can har sai idan mutum ya dawo daga aiki ko makaranta ya je ya karba. Da na yaye Fatima na bar kasar zuwa London na yi karatu acan na kan kai Fatima day care sai idan na dawo na je na karbota, gida ya kama min apartment daya, kudi kuma har ban sab me zan yi da su ba, sai da na shekara daya a can sannan ya bijiro min da zancen surgery, na ji tsoro amman likitan da zai min aikin ya kwantar min da hankali, ya fada min yadda dokikin abubuwan suke, kuma ya nuna min kudin da za a kashe a rubuce.
Aiki aka min aka rage min nama jiki duk inda kitse yake a jikina suka cire min, na yi jinya na wahala ga dokoki da ka'idodin shan magani da abinci, a haka dai har aka yi nasara. Kamin na gama karatun na dawo kasar nan na zama wata kyakkyawa fari ya kara bayyana ni da turawan ba a banbance da wani, musamman idan na shiga cikin masu jan gashi irin nawa. A gida kuma mai aikin da Vito ya dauka Chidimma tana ta kula da London, shi ma kuma yana kula da shi ta wani bangaren, hakan ya saka suka shaku. Na dawo kasar a lokacin da Fatima ta yi wayo, sai ya zamana bata da wani makiyi irin Vito ba kuma dan ya mata komai ba, shi ma kuma baya wani jituwa da ita London ne na shi. A lokacin ne ya fara ba ni yancin fita yawo amman be yarda kowa ya zo gurina ba, sannu a hankali kishi ya fara shiga kamin ya sanar da ni yana so na, sai da ya fara sanar da ni asalinsa sana'arsa da komai.
Ya fada min shi be taba son mace ba gaba daya aure ko soyayya basa gabansa sai da na zo rayuwarsa, kuma na yarda domin na lura da zaman dana yi a gidan ban taba ganin mace ko daya ba, kuma be taba nuna min son taba jikina ko yin wata mu'amala da banza da ni ba. Har sai da ya fara nuna min yana kaunata, ya cancanci na ba shi kauna amman zuciyata ta yi firrr ta ki karbarsa, na kan duba alherinsa da kyautatawa amman soyayyarsa ta ki zama a zuciyata wata kila saboda basa jituwa da Fatima ne, wata kila kuma saboda zuciyar tawa ta mutu ne bana jin son namiji a zuciyata. Da fatima ta shekara biyar sai kiyayyarta ga Vito, domin Fatima tana da wani irin hali na kafiya da rashin jin magana,karamar yarinya ce amman ta iya muguyen kalamai. Ko kadan Fatima bata dauko daga hali da kamanin na ba, a duk lokacin da kowa zai kalleta Turhan zai gani kamar an tsaga kara.
Gashi da ta yi wayo sai ta tashi da son addinin musulunci ta hanyar CHANNEL din da muke kallo, daga ranar dana fada mata asalin sunanta Fatima ne bata sake amsa sunan Lisa ba, ni kuma bana iya hana ta abun da take so, shiyasa idan Vito ya fita sai na kama mata channel din tana koyon abubuwa na addinin musulunci har ta fara iyawa, domin Fatima tana da wayo sosai da basira ga bakinta a bude yake kamar na babba. Tun tana da shekara daya da wata hudu ta fara kiran Dady ba tare da kowa ya fada mata, sai na hana ta, a lokacin da ta yi wato sai ma fada mata ita bata da mahaifi, shiyasana hade mata suna uku Fatima Emily Aisha.
Ko kadan jininta be hadu da na Vito ba har ta kai yayi tsanani har ya kan gwada dukanta ni kuma na nuna masa ba zan lamunta ba, ga shi kuma yana shan kayan maye ni kuma bana son yarana su taso suna sha, ko suna kallon abun, sai na fada masa ina bukatar gurin zama na wa ni kadai, be musa ba ya sama min gida na koma ya cigaba da kula da rayuwata da ta yarana, ni kuma sai na yi amfani da wannan damar na saka Fatima makarantar Islamiya dake garin ta kan je a duk lokacin da ta ji tana bukatar zuwa, a ranar da Vito ya gane dai da yayi min duka, daman ya saba idan na bata masa rai duka yake min tun ban saba ba har na fahimci haka halinsa yake. Vito yayi min komai Aliyu kuma ya cancanci komai daga gareni, a yanzu ma ya fada min ya gaji, kuma na san yayi kokari yana da gaskiya, yana tsananin kishina yana so na kuma ya kyautata min fiye da Turhan fiye da Khaleefa fiye da kowa, kokarinsa da hakurinsa kullum na jiran lokacin da zan amince da kaunarsa ne kuma na aure shi.
Wannan ce Emily Aliyu wannan ne tarihin rayuwata, wannan dalilin ne ya saka na tsani musulmai kuma ya saka ba zan taba yarda Turhan ya ga Fatima ba, ba kuma zan taba sha'awar arba da Khaleefa ba, na san idan Turhan ya san da Fatima zai karbe ta ko dan ya kuntata min, ba dan yana sonta ba a yanzu kuma bani da kowa sai ita...
Na wahala a lokacin da kowa yake bachi akan tasa rayuwar, na shiga taskun rayuwa a lokacin da babu ni da kowa, na kwankwasa kofofi da yawa ba su bude min ba, a duk inda na saka kafa sai na tarar rame ne na shiga ukuna Aliyu a yanzu ina kokarin gina kaina ne na zama kamar kowa, ni ma na samu yanci ni ma na jidadin da kowa yake ji. Har yanzu abubuwan da suka faru suna ruda kwakwalwata, abu kadan ya kan tuna min da baya, bana nufin cuta ma kowa miyasa ni ake cutar da ni? Shim ko dai ban cancanci farinciki ba? I'm so fighting for peace kwanciyar hankali nake bukata a yanzu, abu kadan zai iya buga kwakwalwata i have done enough i have done everything i can.. I deserve happiness too ko ba haka ba?
****. ****. ***
"Kin cancanci, da ace zan iya dawo da lokaci baya Emily da na gyara miki komai, but it's not too late i Will make things right da yardar Allah Emily sai kin yarda musulmai akwai na gari kuma sai kin dauwama a cikin addinin da ke baki natsuwa har abada"
Yayi furucin ne a daidai lokacin da jirgin ya sauka garin Kaduna, Fatima kuma take bachi.
______
Toh fa masu karatu kun ji tarihin Emily.
[7/1, 9:53 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 4️⃣4️⃣
Aliyu yayi hanzarin saka wayarsa aljihu tun kamin Turhan din ya karaso inda yake, ya zaro handkerchief ya lullubawa fuskar Fatima duk da ya san ba lallai ne a ganin farko Turhan ya gane fatima tana da alaka da shi domin ba zai yi tunanin Emily zata samu ta bangaren Aliyu ba, and he would never think Aliyu zai iya boye masa babban abu kamar wannan.
"Abun mamaki, Aliyu kai ne a nan?"
Aliyu yayi murmushin karfin hali yana ala ala kar Fatima ta farka, domin ya san karamin aikinta ne ta labarta masa waye ita ko be tambaya ba.
"Ni ne, Turhan taya muka hadu?"
Turhan yayi murmushin kasaita yaje zai rumgume abokinsa daman al'adar larabawa ce rumgume juna da sumbanta idan suka hadu da wanda suke so, haka Turhan yayi yunkurin aikatawa cikin murna da farincikin ganin abokinsa sai dai babu dama saboda babyn dake hannun Aliyu.
"Ohhh Baby waye haka ta hana ni rumgumar abokina, ban jidadi ba"
Aliyu ya fadada murmushinsa abubuwa biyu suka zagaye shi, yadda Turhan yake murnar ganinsa ya saka shi jin wani iri na gaskiyar daya boye masa gashi kuma yana fargabar kar Fatima ta farka.
"Baka santa ba, daman wai tun da muka yi waya kace min zaka zo baka zo ba?"
"Ban samu zuwa ba, daman na so mu zo tare da Reem ne amman haka be samu ba"
Ya fada cikin wani yanayi na rashin jindadi.
"Toh ya jikin Ammy?"
"Da sauki take cewa sai dai naje na gani, muje ma tare ai sai ka duba ta ko? Daman ina neman mai raka ni kasan kullum idan zan je gurin Ammy tsoronta sabo yake zame min, saboda maganganu da kuma fuskar da take karba ta da ita, ta daina murna da zuwa na yanzu"
Aliyu can't say no to his friend kuma ya san ba zai yiyu ya tafi tare da Fatima gidan ba hatsari ne ma babba ya tafi da ita gidan.
"Yeah amman na yi waya da direba na ce ya zo ya dauki a nan"
"Malam ba wani babban abu ba ne direbanka ne fa, karkashinka yake ai zaka iya fada masa ya koma kawai, direban da zai dauke ni yana waje yana jirana mu je kawai kasan dai ba zan barka Airport din nan ba"
"Bata zan yi?"
"Aa amman dai ba zan barka ba i miss you Aliyu sosai fa"
"Okay fine mu jira Direban ya karaso sai ya tafi da wannan yarinyar kar mahaifiyarta ta damu, ni kuma sai na bika mu kaika gida tun da ka zama amarya"
Yayi dariya tare da kai hannu ya taba Fatima dake ta bachinta cike da sha'awar yara.
"Yar waye wai"
Hannunsa na kaiwa a jikin Fatima ta zabura da karfi ta sauke ajiyar zuciya a cikin bachin da take.
"Oh Sorry"
Turhan ya fada yana dauke hannunsa da sauri gudun kar ya tasheta, Aliyu ya kalleshi jiki a sanyeye ya juya yana fadin.
"Mu tafi waje mu jira shi"
Turhan ya jera tare da shi suka fito suna dan taba hira, sun tsaya harabar for like 10min direban Aliyu ya kira Aliyu ya kwatanta masa inda yake direban na isowa Aliyu yayi hanzarin nufar motar ya bude baya ya kwantar da Fatima a hankali bachi take sosai kamar wanda ta yi wani katon aiki, Aliyu ya rufe motar a hankali be taba jin ya aikata wani abu na rashin kyautata kamar kin fadawa Turhan Fatima yarsa ce a yanzu ba. Sai yake jin kamar ya ci amanar abokinsa duk da yake yana da laifi.
"Ka tafi da ita gida ka shiga da ita ciki ka kwantar da ita"
Ya saka hannunsa alijihu ya ciro keys ya mika masa.
"Toh ranka ya dade"
Ya karbi keys din sannan ya dauki kayan da Aliyu ya zo da su ya saka bayan mota, sai a lokacin Aliyu ya sami relief ya nufi gurin da Turhan yake tsaye jikin motar da za su shiga, yana isowa Turhan ya ware hannu Aliyu ya ware suka rumgume juna.
"Na jidadin zuwan nan yaushe rabon da na saka ka ido Aliyu"