Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 70

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 70

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 70: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 70. "Wata kila tana son ta yi wata magana da ke bata son mu ji ko mu…

3,371 words

"Wata kila tana son ta yi wata magana da ke bata son mu ji ko mu gani, ki tafi ki same ta"

"Okay"

Ta amsa sannan ta bude kofar baya ta kitchen din ta fice daman jikinta a lullube yake da Hijab. Ta nufi gate din ta bude a hankali ta fita, ta yi zaton ganin Mama Baraka ne, sai ta yi arba da Turhan tsaye kusa da motarsa. Da ta duba ko'ina bata ga alamar Mama Baraka ba sai ta juya zata koma.

"Ba zan samu damar da za ki saurare ni ba Aisha?"

"Wata kila zaka fada min magana marar dadi ne"

"Aa dan Allah ki saurare ni"

Ta juyo ta matsa kadan ta tsaya tana rumgume da hannayenta. Da ya kalleta sai ya ji kamar be san miye so ba sai a ranar. Cikin yanayi na sanyi jiki da damuwa ya soma magana.

"Na san idan na ce ni ne, ba za a barki ki fito ba, saboda ke da mutanen gidan kuna kallona a matsayin makiyinku ne, shiyasa na yi amfani da sunan Mama Baraka"

Ba ta dai ce masa komai ba har ya dora.

"Aisha zan kara da kara baki hakuri na abubuwan da suka faru tsakaninmu, kasancewarki a rayuwata ya koya min darasi mai yawa, na san zafin so, na san zafin rashi, kuma na san zafin da kika ji lokacin da na juya miki baya, saboda a yanxu ina jin fiye da abun da kika ji, ke kin ji zafi ne kawai amman ba dan kina so na ba, ni kuma yanzu ina fama da tsabanin haka ne. Jiya da dare ban yi bachi ba, ina ganin abubuwan da suka faru kamar a mafarki, amman yau da safe sai na fahimci wani abu, idan kana son mutum ai zaka so farincikinsa ko? In har zaki yi samu farinciki da ni na kasa baki a gidan wani ne, me zai saka ba zan so haka a gareki ba? Idan na ce miki ban yi bakinciki ba na yi karya, ban kuma ce zan warke ba, amman sannu a hankali zan samu salama"

Ya hade yawu.

"Na gode Aisha, da kiyayyata ko tunanin abun da na miki, da wahala bata saka kin zubar da cikina ko jefar da yata ba, na gode da kika kula da Fatima, na gode da kika yi ma Ammy biyayya gurin aurena, a yayin da ni na kasa yi mata biyayya gurin rike amanarki, kuma ina fatar a duk lokacin da wani abu ya taso na Fatima idan na sanar miki za ki shiga ki tsaya mata kamar yadda kika saba, na kawo ne saboda anjima kadan jirgimu zai daga, zata zauna gurinki na dan lokaci, idan na dawo zan dauketa zan tafi Sudan da ita, na yi magana da Ammy ta amince kuma ina fatan ke ma ba za ki, ki yarda ba, ki yi hakuri amman ba zan iya barin yata ta zauna a gidan wani ba"

Hankalin Emily ya tashi.

"Fatima ta yi kankanta ka tafi da ita masarautarku, har yanzu bata san ta banbance daidai da rashin daidai ba, ta yi kankanta ta fuskanci kalubale"

"Kina tunanin zan iya bari a wulakanta ke da kike mahaifiyarta, balle kuma ita? No babu abun da zai faru"

Yana rufe baki Aliyu ya iso kusa da gate din gidan da motarsa. Ya bude motarsa ya fito ya tsaya inda suke, yana kallon Emily da karantar yanayinta sai dai be ce komai ba, ba shi da nufin zafafa domin Turhan uban yarta ne matukar ba yayi kokarin wuce gona da iri ba ne, dole zai bar wata karamar kofa a tsakani. Turhan yayi murmushi yana kallon Aliyu.

"Ina taya murna, ka yi nasara, amman ka sani, ba a cin amana kuma a zauna cikin salama, kai ma nadama zata tambaye ka kamar yadda ta tambaye ni a yanzu"

"Ba zaka fahimce ni ba, amman Wallahi ban tsare wani abu daga gareka ko daga Emily da nufin na raba tsakaninku ba, kuma ban boye komai da nufin na mallaketa ba, ni da kai da ita, muna zagaye ne da kaddara, a jiya da iyayenka suka zo, Wallahi ban tsammaci zan same ta ba, indai har zan iya cutar da kaina to zan iya cutar da kai Turhan"

Turhan ya kalleshi sama da kasa kawai yayi murmushi, ya juya ya bude motarsa ya riko hannun Fatima ya fito da ita, yayi mata alama da ta tafi gurin Mamanta, ta kalli Emily da ke miko mata hannu tana mata murmushi. A gurin Fatima ta murje ido ta rike rigar Babanta da hannu biyu ta juyawa Emily baya.

"Fatima sweetheart, za ki zauna gurin Momy yanzu kin ji?"

Ta girgiza masa kai ya kara rike rigarsa. Ta kalli Aliyu ta shige da fuskarta a jikin mahaifinta.

"Wani abun ka fada mata?"

Emily ta tambaya tana jin babu dadi. Turhan ya girgiza kai.

"Ban fada mata komai da zai saka ta tsane ki ko ta juya miki baya ba, kina kallona a matsayin makiyinki ne kawai, amman abun ba haka yake ba."

Emily ta matsa ta kai hannu ta riko sai Fatima ta buga hannun Emily tana hawaye ta kara rike Babanta.

"Tun da bata son zama, zan koma da ita idan ta bukaci ganinki direba zai kawota, ina miki fatan alheri ke da sabon ABOKIN RAYUWA"

Emily ta kasa cewa komai idonta ya cika da hawaye bata yi zaton haka daga gurin yarta ba. Turhan ya bude mata mota ta koma ciki ta zauna, ya rufe sannan ya zagaya ta shiga yaja motar ya bar su a gurin tsaye, yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba, amman idan ya juya ya kalli yarsa sai ta ji sassauci. Emily ta bi motar da kallo tana hawaye har ta daina hangota.

"Kowa na zauna da shi sai ya juya min baya, har da ya..."

Aliyu ya rufe mata baki da sauri, ya juyo da ita ya sakata a kirjinsa ya rumgume, yana shafa bayanta a hankali, babu kalma ki yi hakuri rumgumar kadai sai ta ji hawayenta ya yanke, ta haka take iya gane Aliyu ne ABOKIN RAYUWARTA... Ta dago kai ta kalleshi sai ya sake ta ya saka hannayensa biyu ya share hawayenta.

"Kuka be miki wahala ko? Zai na zane hawayen nan da suke bata fuskar matata"

Ya bude mata gate yana rike da hannunta.

"Shiga gida"

Ya saki hannunta ta shiga ciki sannan ya koma motarsa ya yi horn aka bude masa ya shiga ciki. Da ya faka harabar gidan sai da ya tsaya ya jira Emily ta iso ta shiga falon sannan ya bi bayanta. A lokacin da ya shiga falon ya ga babu kowa sai ya jidadi yayi hanzarin kamo hannunta ta baya ya juyo da ita.

"Hajiya ba ki gaishe ni ba fa"

"Mun gaisa dazun"

Ta amsa cikin rada kamar yadda yayi mata. Ya rufe baki ya kashe mata ido.

"Aw haka na tuna"

Ta cire hannunta da sauri ta nufi hanyar kitchen. Shi kuma ya nufi stairs yana murmushi. Dakin mahaifiyarsa ya shiga ya same tana daura dankwali.

"Ummi ina kwana"

"Lafiya kalau an shigo?"

"Eh, Ummi sai na samu Ayusher a waje"

"Eh Hajiya Baraka ce ta zo tana sallama da ita"

"Waye yace Mama Baraka ce? Ba ita na samu a waje ba Turhan ne"

Ummi ta kalleshi da sauri.

"Turhan? Wanda aka aiko ce mana yayi Baraka ce"

"Ummi baku bincika ba kuka barta ta fita, yanzu da wani ne da zai cutar da ita fa? Da yanzu ni za a bari a matsala"

"Na yi zaton ko tana son magana da ita ne Private, ita ma da ta fita ta ga ba ita ba ce ai sai ta dawo"

"To ina zata san wannan idan tana son magana da ita ai ga dakuna ko kuma ta aiko a dauketa, amman sai a bari ta fita a bincika ba kuma ba a bi bayanta"

"Aisha ce ba zata san ta dawo ba?"

"Eh mana, duka duka nawa Ayusher take? Wannan tunanin ba zai zo mata ba, yanzu ne fa kwakwalwata take girma"

Ummi ta saki baki tana kallon Aliyu da a bakin gaskiyarsa yake maganar.

"Toh za a kula next time, yanzu dai ka dawo da ita ko yaya?"

"Ai ba zan bar yarinya karama a waje ba"

Ummi ta yi murmushi kawai ta nufi kofa ya biyo bayanta. A falo suka rabu ta nufi bangaren Daddy shi kuma ya nufi dinning din da matarsa take zaune tare da Nafeesa. Nafeesa na gaishe shi ta mike tsaye ta fice dinning din domin ba su damar karyawa su kadai ba tare da takura ba.

"Kika yi serving kanki? Baki bari na zuba miki ba?"

Ta mike tsaye.

"Bari na zuba maka"

"No it's my duty to feed you, zauna zan zuba da kaina"

Ta koma ta zauna tana murmushi. Ya zuba ma kansa tana cin abincin yana kallonta har ta aje spoon.

"Kin koshi?"

Ta daga mishi kai.

"Ba ki ci da yawa ba, ko wani abun kike so dabam?"

"Aa"

Ta amsa, ganin Nafeesa ya saka ta jin kunya sai ta mike tsaye.

"Bari na dauko wayata"

Aliyu ya juya ya kalli Nafeesa.

"Idan kika aje plate din ki dauko mata wayarta"

Nafeesa ta amsa da tohm. Emily ta koma ta zauna tana dan jin kunya. Nafeesa ta dauko mata wayar ta kawo tana mata wani kallo na zolaya. Emily ta karba ta rike

"Thank you"

Nafeesa ta yi murmushi kawai ta koma ciki, sai a lokacin Aliyu ya sake kallonta ya ce.

"Kamata yayi ta ce you're welcome Mrs Aliyu ko?"

"Idan Ummi ta zo ta same ni a nan zata ce ba ni da kunya"

"Haka fa, ke ce mai kunya ni ne marar kunya ko?"

Ta yi dariyar da bata shirya ba ta sauke kanta kasa tana taba wayar. A nan ta yi arba da sakon da ya sauya murmushin fuskarta zuwa tashin hankali. Tuna Aliyu na gabanta ya saka ta yi kokarin boyewa da murmushin dole.

"Miye?"

"Ba komai"

"Vito ne? Ko Kameela?"

"Miyasa ka zarge su?"

"Saboda Turhan be jima da barin gidan nan ba, ba zai yiyu ya miki wani sako na tashin hankali da zai bayyana a fuskarki ba, ko mutuwa yayi ba ke za a sanarwa ba, amman Kameela zata iya aiko miki da sako marar kyau, haka ma Vito, cikin biyu dole a samu daya"

"Vito ne"

Ta fada kamar zata yi kuka. Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zagaya gefenta ya karbi wayar.

"Congratulations kin yi aure ko? Kin yi min butulci Emily kuma dole ki dandana dacin hakan, ke da wannan Balaraben da ya aure ki, ke da fitinanniyar yarki"

Aliyu ya ciro wayarsa ya kwafi number ya saka a wayarsa bayan ya gama karanta sakon, sannan ya tura masa da sako da wayarsa.

"Ba Balarabe ne ya aureta ba, ni ne na aureta mutumen da ya janyo ta daga PH zuwa Kd, mutumen da suka yi aiki tare, wawa ka zo ka tare ni mana, miyasa kake tsoro?"

Ya kalleta.

"Daman na yi tunanin zai samu number duk da yake sabuwar number ce, amman mai son abun ka ya fika dabara, kuma zuciyata ta raya min yana bibiyar rayuwarki, amman yanzu an zo karshe da yardar Allah, tun da har giyar hauka ta dauke shi ya turo wannan sakon za a gano inda yake"

Emily ta mike tsaye.

"Kashe shi za'ayi?"

A kokarin Aliyu na kwantar mata da hankali ya ce.

"Aa za a dai kama shi, sai a gabatar da shi gaban kuliya saboda kar ya cutar da kowa, haka yayi miki?"

Ta daga kai.

"Zauna kin ji yan matana, bari na nunawa Daddy wannan sakon, kuma zan sanar da Ammy halin da ake ciki, ba lallai idan na yi magana da Turhan ya saurare ni ba, amman na san Ammy zata dauki abun serious"

Ta koma ta zauna ya nufi hanyar da zata sadashi da bangaren Daddy, sai kuma ya juyo ba shi da nutsuwar barinta a falon jin yake kamar wani abu zai same ta.

"Shiga dakin Nafeesa ki zauna, kuma kar kowa ya sake sallama miki ki fito ko ni ne, mai son ganinki ya zo ya same a nan"

Ta sake tashi, zuciyarsa bata bar shi ba sai da ya rakata har bakin kofar dakin Nafeesa ya bude mata ta shiga.

"Karki bar yarinyar nan ta fito, idan ta bata ke na sani"

Ya bugawa Nafeesa warning, sannan yaja kofar ya rufe ya nufi bangaren Mahaifinsa.

TURHAN POV.

Ammy bata yi mamakin ganin ya dawo da Fatima ba, daman ta lura tun kamin su tafi bata son tafiyar, tun jiya tana jikin ubanta tana taya shi jimami ko abinci sai da ta ga yana ci sannan ta ci.

"Shiga ciki ki yi kallo"

"Dady ba zai tafi ba?"

Ta tambayi Ammy dake bata umarnin.

"Eh"

Tohm"

Ta amsa sannan ta nufi hanyar dakinta.

"Fatima"

Turhan ya kirata sai ta juyo, ya tafi inda take ya rumgumeta sosai yayi kissing dinta ita ma ta yi masa kiss.

"I love you"

"I love you Too Dady"

Ya sake ta yana murmushi, ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo kusa da Ammy.

"Bata yarda ta zauna can, ko magana bata yi da Emily ba"

"Daman na ga alamar ba zata zauna ba"

"Ni zan tafi Ammy, anjima kadan jirgimu zai ta shi"

"Ba zaka bari sai next week ba"

"Garin ne baya min dadi gara dai na tafi kawai, ko zan samu salama"

Ammy ta mike tsaye ta bude masa hannayenta sai ta matsa kusa da ita ta rumgume uwarsa.

"Jikinka da zafi sosai Turhan, baka da lafiya ne?"

"Zazzabi ne kadan na ke ji"

Ta sake shi tana taba fuskarsa da jikinsa.

"Ba kadan ba ne, ko'ina ya maka zafi fa, gaskiya ba zaka yi tafiyar nan a yau ba"

Turhan ya zube kasa ya rike kafafuwan Ammy yana kuka kamar ba shi ba.

"Ammy dan Allah ki yafe min, bijirewa umarninki ne ya jefani a halin da nake a yau, da ace na bi yadda kika tsara, da yanzu ban shiga wannan damuwar ba, da yanzu ban shiga wannan bakincikin ba"

"Na yafe maka duniya da lahira, kuma damuwa Allah zai maka maganinta, Emily ba ita kadai ce mace a duniya ba"

Ta daga shi ya zauna kan kujera ya rike kansa dake tsarawa.

"Ba zaka tafi yau ba"

Ya sauka kasa ya zauna ya dora kansa akan cinyar Ammy. Sun dade a haka kamin ya ciro wayarsa yayi canceling flight din, ko kadan a yanzu baya son ya sabawa Ammy domin ya ga illar hakan.

"Zan bari sai next week"

"Allah ya maka albarka, bari na dauko waya na kira Likitana"

Ammy ta tashi ta fice daga falon ta shiga dakinta, tana daukar wayarta ta ci karo da sakon Aliyu daga numbersa da tuni ta goge ta a wayarta. [8/27, 11:03 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

Page 7️⃣2️⃣

🌟✨ TALIYAR HAUSA - YAR MURJI ✨🌟

🥘 "Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!" 🥘

Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa - Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al'ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida.

✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa - Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa - cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman

📍 Muna a Kaduna - amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed).

💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa - Yar Murji yau!

📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa!

TWO MONTHS LATER...

"Ah gaskiya an gyara gidan sosai, Aliyu yayi kokari, iyayenta ma sun yi, ko ku kuka mata kayan daƙin"

Ummi ta yi dariya tana kallon kanwarta Hajiya Larai.

"Hajiya Larai, ba mu muka mata ba, mahaifiyarta ta karbe ragamar komai daga hannunmu, ita ta yi mata komai, da kam har na yi magana da Khadeeja Candy za mu siya kayan Kitchen ta mana breaking down na komai sai gashi ita mahaifiyar tace dan Allah kar mu yi komai mu bar ta ta yi, sai muka cire hannunmu, lefe kawai ta hada mana, sai na yi ma Hajiya Baraka Recommending dinta, indai ba ta canja ba ina tunanin gurin Khadeeja Candy aka siya komai na kayan Kitchen da bedsheet da curtain har frames ma domin komai saidawa take"

"Mhn idan ba ke ba Ummi yaushe za ayi ma yarinya miji kuma ayi mata kayan dakin? Wannan ai shi ke nuna kin an bata sadakar Aliyu kenan, wannan uban lefe da aka zuba ai kam dole uwarta ta dafe ka cire ta a kunya"

"Daman shi lefe idan namiji yayi ai kansa yayi ma, tun da shi za'ayi ma kwalliya, ba faduwa ba ce"

"Haka ne, ta yi kokari gaskiya, dan kan an zuba kaya komai yayi gwanin sha'awa kam, kai kace ma dauko komai aka yi aka zuba kawai a ciki"

"Ai Khadeeja Candy ce ba daga baya ba indai kaya ne, gurinta nake siyan tufafi Laces shadda, Atamfa abaya shoes kai komai fa, har adashe ma na ga tana yi, kuma a kawo maka komai cikin aminci da salama, facebook na fara haduwa da kayanta na gwada saya yanzu kam har mun zama regular customer"

"Ikon Allah wasu fa suna da zafin nema, toh ita kuma a facebook take siyar da kayanta ne? Zan so na gwada dan gaskiya kayan nan sun burge ni"

"Aa fa kin ji Hajiya Larai da wani zance, a ko'ina kika searching dinta za ki same ta, a TikTok ne, ko Instagram har Snapchat, ko a WhatsApp, amman fa ki tabbatar kin shirya siya"

"Hajiya Larai ta yi murmushi, ta dauko wayarta Ummi na karanta mata number Khadeeja Candy wanda take whatsapp chat da ita.

"0 8 0 3 6 1 2 6 6 6 0"

"Zan dubata ta WhatsApp In Shaa Allahu, auren Maimuna da za'ayi sai mu siya mata komai a can ma, tana dai siyar da manyan kaya ko?"

"Sosai, cooler daga 12k har ta dubu tari taskwas za ki samu a gurinta, ya danganta da abun da kike so"

"Aiko zan gwada da yardar Allah"

"Tohm Allah ya amice, ba da ke za a tafi karbar garar ba ne? Ko da yake kin ga dakin amarya har kin gaji"

"Da ni mana, ina za a barku a baya, mun bada sadakar ango kuma ace ba za mu karbo gara ba?"

"Wane irin sadaka Hajiya Larai?"

"Ah yo sadaka mana mai sunan Mama, ke kin san idan ba Aliyu ba babu wanda zai kwashi wannan yarinyar nan haka, a aje zancen kyau a gafe a kalli asalinta"

"Kin gani Hajiya Larai karki bar Aliyu ya ji zancen nan na ki, domin yana son matarsa idan kika fadi wani abu marar dadi akanta karamin abu ne ki ga ya sauya miki fuska, su shegu ba sa da zafi ko gata ne? Miye na su a ciki? Wannan zancen na cikin gidana ne, ni ban san miya ja ni na fada miki ba"

"Aiko dai kin san ni bana barin ta kwana, amman ai ba nuna mata zan yi ba, ko shi ta kasa dai tana saka, tun da ke ma kin bi ina ni ina juya baya?"

"Kawai ki musu fatan alheri, domin babu abun da zai raba su sai mutuwa da yardar Allah"

"Tohm Allah ya sanya alheri, mu din ai sai da hakuri, ko'ina akwai mu, dangin miji ba, mu ga fari mu ga baki, mu koma gefe mu yi magana"

Ummi ta tabe baki tana dariya.

"Wanda be iya zama da ku ba kuke wahalarwa, wanda kuwa ya san ku ya karanci komai ya huta"

"Heeeee Ummi.. Kuma fa haka ne..."

Readers Also Read