Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 71

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 71

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 71: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 71. Hajiya Larai ta kyalkyale da dariya ta mikawa Ummi hannu suka tabe.…

3,361 words

Hajiya Larai ta kyalkyale da dariya ta mikawa Ummi hannu suka tabe. Sannan ta sauke kafa daya kan daya ta mike tsaye.

"Bari na fita waje mu zauna kamin su iso"

"Hajiya Larai jibila da cincin kawai za a kawo mana, kayan masarufi a kai ma angon abun sa"

"Toh mu karba ne kawai na mu, ba za a raba ba sai kin ga komai"

"Tohm shikenan"

Ummi ta amsa tana Hamma, kusan tun da aka daura auren na Aliyu da Aisha Ummi bata huta ba, bata wannan bata wacan har aka yi wunin biki da walimar dare domin ya ki yarda ayi kida, haka yayi ko a aurensa na farko, Ummi ta yi zaton a wacan saboda fadi babu dadin da aka yi ta yi ne da family Kameela ya saka yace ba zai yi biki ba, domin su suka yi komai da ake na hidamar kida da raye raye kuma be halarta ba. A yanzu kuma ta gane haline na gujewa tsabawa Allah, ya fada mata ya sake jadada mata cewar Manzon Allah S. A. W ya ce Allah ya tsinewa duk wata ni'ima da Allah yayi ma bawa aka taru aka yi raye raye aka chakudu maza da mata, auren Emily na daga cikin ni'imomin da Allah ya yi masa dan haka na zai yarda ya rayu da ita a karkashin tsunuwar Allah ba, sai dai ba zai hana ta yi nata taron da mata yan'uwanta ba domin addnin ba haramta ba, matukar maza ba su gani ba kuma ba su chakudu ba.

EMILY POV.

Bata san miye auren gata ba sai da ta zama karkashin inuwar kulawar Aliyu. Daga ranar da aka saka musu rana tana karbar kyaututukan kauna da soyayya daga mijinta danginsa da kuma danginta. Sabon gidan da ya siya ma sai da ya dauke ta ya tafi ta ita ta duba komai ta fadi inda be mata ba aka canja, komai zai siya mata sai ya nemi zabinta, abun da take so shi za'ayi, bata taba auren wani ya lalaba kamar yadda Aliyu yake mata ba. Ko a lokacin da zai fada mata ba shi da ra'ayin yin biki ta sigar lalama ya biyo mata yana lallabata yadda zata fahimta kar ranta ya bace.

Sai kuma aka yi sa'a ita ma bata da bukatar bikin saboda bata da wasu kawaye da zata gayyata idan ma za'ayi sai dai Mama Baraka ta yi na ta gayyatar. Haka kuma aka yi, Mama Baraka ta aikawa kowa katin gayyata da wuri, domin Emily ta dawo a sabon gidanta ne ana sauran wata daya biki. Danginta har wadanda suke nesa sai da suka halarcin biki.

Emily ta ji wannan auren a dabam kuma ta kara fahimtar yadda rayuwa take tafiya, a wannan auren ne aka yi mata wankan lalle wanda ake yi ma ko wace budurwa a aurenta na farko, sai dai ita bata samu wannan damar ba sai a yanzu, ba taba shafa mata lalle ba sai a wannan karon, yan'uwanta mata da kawayensu ka shirya henna day wanda Aliyu ya dauki nauyi, domin bikin na duka mata ne babu maza. Anyi Walimar dare walimar data samu halarta manyan mutane daga bangaren Mahaifiyarta da kuma iyayen Aliyu da abokan arzikin Ummi. Ranar wunin biki Mama Baraka ta dauko masu masu kudin kwarya da kuma yarbawa suka kayatar da wunin.

A gurin Khadeeja Candy ta siya duka kayan Kitchen din da aka sakawa Emily bayan, Ummi ta hadasu da ta bincika kuma ta ga akwai abubuwan da take bukata sai kawai ta zaba ta tura kudi aka hada komai ta aika da mota aka dauko mata, wasu kuma daga baya ta kara aka aiko mata ta hannun Driver. Mama Baraka ta shiga ta tsayarwa yarta tun daga gyaran jiki karbar lefe da kayan saka rana har kayan daki da gara bata bar kowa yayi mata ba. Dr A-B ma da so ya dauki wani abu bata ba shiyasa dama ba, sai kudi mai kauri ya turawa Emily ta hanyar Mama Baraka yace a aje mata idan bukatar wani abun ya tashi.

A auren Aliyu Emily ta san miye gata a aure, ta san dadin yan'uwa da iyaye, ta san wasu abubuwan da suke na daga al'adar hausawa da kuma yarbawa. A wannan auren an yi mata gara an yi mata kayan daki da komai da mace take bukata daga iyaye, ga yan'uwanta a kusa da ita komai zata yi su suke shigewa gaba, su bata shawara ko ma su aiwatar ba tare da jiranta ba, yan'uwan Mama Baraka na nesa da na kusa duk an sadata da su wasu ta waya wasu kuma sun zo bikin. Bata kara gode Allah ba sai a daren da Aliyu ya aiko da manyan motoci zuwa daukarta tare da abokansa da wasu daga gwaggonninsa da iyaye.

Mama Baraka da yan'uwanta suka yi mata nasiha suka mata kuduba da uwa ke yi ma kowace ƴa, aka dauke ta tana lullube da zane bayan ta saka tsadadden lace na al'adar yarbawa, Tana sanye da sakarta ta zinari da aka saka mata a lefe, wuyanta da murjani da ya sauko mata har gaban kirjinta, haka ma hannayenta, kafafuwanta da suka sha bakin lallen suna sanye da iborun, tana ta kamshin turare sai guɗa ake masu, suka ta saka mata albarka da yaren na yarbanci. Aka fada mata idan zata shiga gidan ta shiga da kafar dama kuma ta yi addu'a da Bismillah.

Tana zaune falon mahaifiyarta Fatima ta shigo ta ratsa mutane ta zauna kusa da ita tana ta kallon mutane, Emily ta miko hannunta a hankali ta kama hannun Fatima ta rike, idan suka yi magana da yarbanci tana jin duk abun da suke fada saboda tana jin yaren yarbanci da igbo tun a zamansu na can. Can kuma ta juya ta daga mayafin mahaifiyarta ta leka fuskarta.

"Momy kin yi kyau"

Ta fada tana shafa fuskarta tana murmushi, hawayen dake makale a idon Emily ya zubo mata.

"Kin fi kowace rana kyau, har da lalle fa da sarka har biyu, da makeup"

Emily ta lumshe ido tana murmushi, ko kadan bata yi tsammanin jin haka daga bakin yarta ba, ko da yake tun da Turhan ya saka kafa ya bar garin Fatima ta dawo gurinta daker da sudin goshi sai ta waye cikin mutane, musamman da kannen Emily suke janta a jiki. Da kuma aka fara hidimar auren sai ya zama abun ya burgeta, domin bata taba gani irin wannan auren ba, komai a gurinta sabo ne, duk abun da za'ayi ana yi da ita yana gaba gaba. Aliyu idan ya zo gidan zai zo mata da kayan dadi, ko be zo ba zai aiko a kawo mata, wani lokacin idan ya zo ita yake sakawa a sallamo yayi hira da ita ya bata tsaraba ya tafi. Yana iya kar kokarinsa wajen ganin Fatima ta sake jiki da shi kuma ta kwantar da hankalinta dan kar damuwarta ta jefa Emily a damuwa.

Kusan kuma kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya samu fiye da rabin abun da yake nema a gurin Fatima. Wadanda suka kasance iyaye ga Emily ne suka bukaci kanen su daukewa Fatima hankali ta yadda za a fita da Emily ba tare da ta sani ba. Domin suna jin lokacin da take tambayar Emily yau sabon gida za su tafi ko? Da wayo aka fitar da ita, sannan aka fita da Emily, a nan ma ta ga wata al'ada da a bata kyauta a karbi Amarya. Emily ta shiga motar tana hawayen da a yau ta tabbatar na farinciki ne. Tana zaune shiru tana saurari tafiyar har suka isa gidan masoyinta kuma Abokin Rayuwarta. An riko hannunta ta sauko motar kanta a kasa aka shiga da ita gidan da duk wanda ya ga tsarinsa da kayan da aka zuba a ciki sai ya yaba da kokari mijinta da kuma iyayenta.

Bayan iyaye sun fita aka barta da kanenta da wasu daga familyn Mama Baraka da suka zama kawayenta na short period of time. Abokan Aliyu suka rako shi ya shigo falon da manyan tufafi babbar riga har da hula. Kowane yana rike da babbar leda suka cikin big center table din da kayan taba ka lashe da suka shigo da su. A nan ta san wani abu siyen bakin amarya, abokan Aliyu suka siye bakinta da kudi mai kauri da siyayya da, sun yi farinciki sosai domin ba su bar gurin ba sai da kowa ya ji saukar alert.

Sai da kowa ya watse Aliyu ya rufe kofar sannan ya yarda ya bude fuskar matarsa, sannan a hankali ya yaye duk wani abu dake jikinta ya rage daga dankwalinta sai lace ne kadai, har sarkar cire mata yayi saboda yana ganin kamar sun mata nauyi, ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta sannan ya cire abun hannun ya aje, ya sauko kasa ta zauna ya daga kafarta abun adon dake kafarta ya cire bayan ya sumbanci kafar sannan ya aje ta a hankali, ya dago dayar ya cire ya sumbance ta ya aje kasa. Ita kanta ta ji a jikinta jumma'ar da zata yi kyau, tun daga laraba ake ganewa, Aliyu ne kadai Jarumin dake tsoron tana jikinta saboda gujewa tsallake iyakokin da musulunci ya gindaya musu.

Har bayan aurensu, be taba kokarin taba jikinta ko wuce gona da iri saboda ta zama mallakinsa ba, kamin ranar yau idan ya rumgume ta ko ya sumbance to ya fahimci tana cikin damuwa ne sai yayi mata haka saboda ya kwantar mata da hankali, shi ma yana kokarin ganin be tsallake iyakoki ba duk kuwa da ya san halalinsa ce tun da an daura musu aure.

"Abar kauna? Komai na ki yayi kyau"

Ya fada yana kallon kyakkyawar fuskarta, kunyarsa da take ji a yanzu ta fi wanda ta ji a washe garin ranar da aka daura musu aure. Kafarta daya ya daga a hankali yayi mata chakulkuli, ta motsa kafarta murmushi ya cika fuskarta kunya ta saka ta rufe idonta. Yatsansa ya saka yana bin layin lallen da aka zana mata a kafa a hankali kamar mai zanen yana kallon kai kace be taba gani lalle a kafar mace ba. Har sai da ta kasa jurewa ta hanye kafarta. Sai yayi murmushi ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje ya zauna kusa da ita, ya juyo da fuskarta ta fuskance shi.

"Qalbi, bude idonki ki kalli mijinki, masoyinki, mallakinki abokin rayuwarki na har abada, mijin da yake jin ya fi kowa sa'a da rabo saboda ya same ki"

Ya kara matsawa kusa da ita sosai har jikinta yana taba na shi.

"Kin san me, uwar ƴaƴa? Tun daga ranar da kika shigo rayuwata, komai ya canja. Na rasa yadda zan bayyana, amma ke ce farin cikin zuciyata. A duk Lokacin da na gaji, sai murmushinki ya bani ƙarfi. A duk lokacin da na shiga damuwa, sai kalamanki su zama shauki da nutsuwa a raina."

Ya ɗan janyo hannunta ya riƙe, yana tana saman yatsunya, ya ci gaba da cewa

"Kin fi zinari daraja a wurina, kin fi dukiya ƙima. Wallahi idan na dubi idanuwanki, ina jin kamar na mallaki duniya baki ɗaya. Ke ce zuciyata, ke ce abokiyar tafiyata har ƙarshen rayuwata."

Emily ta bude ido tana jin daɗin maganganun a zuciya, kowane harafi yana tsarata ya isar mata da sako. Ya saka karamin yatsansa cikin nata irin yadda yara suke yi.

"Na yi alkawari ba zan taɓa barin ki, ki ji kaɗaici ba. Zan kasance tare da ke cikin farin ciki da bakin ciki. Domin soyayyarki ita ce hasken zuciyata, kuma ke ce sarauniyar gidana"

Hawaye ya sauko mata ya saka yatsansa ya share mata, ya sakar mata murmushi mai taushi ya girgiza mata kai alamar no more tears, ya kwamto da ita kirjinsa yana shinshinar gashin kanta dake kamshi. Slowly and slowly ya dago kanta ta kalli saitin idonsa ya sauko da fuskarsa sai ta lumshe ido tana jin sanyin lips dinsa a saman nata lips din, kamin ya raba lips din gida biyu ya saka nasa a tsakiya. Wani sako mai nauyi da mai wuyar dauka ya aika mata mata ta tsakanin bakinsa da nata, a lokacin da ya cire bakinsa cikin nasa sai ta kalleshi a rikice tana maida numfashi, sai kuma ta lumshe ido ta yi murmushi ta maida kanta kirjinsa tana mai jin kunya.

Sun samu lokaci a haka sannan ya tashi dauro alwala ita ma ta yi suka yi sallah, yayi musu addu'a, ya dauko abun tabawa ya ciyar da matarsa, sannan sauya tufafin jikinsa zuwa ma bachi, ita ma ta sauya nata bayan ya bata guri ya fita falo har sai da ta gama sannan ya dawo. Abubuwa da Emily bata saka ran Aliyu ya sani ba, ko ya iya ta gansu, bata yi zaton zai zo mata a haka ba, saboda yadda take ganinsa da kokarin kawarda kai. Kusan duk wani abu mai sunan damuwa sai da Aliyu ya matar da ita a daren, har take jin kamar ita ce ta kwashe kason jarumin namiji, ta rika jin kamar bayan Aliyu babu wani namiji mai halayya da dabi'un da ya rage irin nasa.

A kirjinsa ta kwana har safe, ba kuma a daren kadai ba, a kowane dare bayan daren tarewarta tana kwana a kirjinsa ne, idan yana gidan da rana kuma tana sarkafe cikin hannayensa, duk wani abun da zai bada space a tsakaninsu be yarda da shi ba. A nan ta gane kalmar soyayya ba a cikin kalami kadai take ba har a cikin aiki da zamantakewa. Matukar hali da hallayar da Aliyu ya sauke ta da su a gidansa zai daure, to bata jin akwai wata macen da zata fita dace ko jindadin aure a halin yanzu. Idan ya fita har kewa take, shi kan shi kamin ya dawo gareta ya yi missing dinta kamar ba a gida daya suke rayuwa ba. Awa ashirin da hudu yana jin kamar a kara musu wasu awanin domin sun masa kadan.

Kusan duk wanda ya shiga gidan sai ya yaba da yadda aka gyara ko'ina kuma aka zuba kaya, sosai Mama Baraka ta yi kokari wajen ganin ta fitar da yarta kunya, kuma ta faranta mata rai, kuma kwaliyya ta biya kudin sabulu domin ta siya komai a gurin Khadeeja Candy ne. [8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

Page 7️⃣3️⃣

🌟✨ TALIYAR HAUSA - YAR MURJI ✨🌟

🥘 "Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!" 🥘

Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa - Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al'ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida.

✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa - Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa - cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman

📍 Muna a Kaduna - amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed).

💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa - Yar Murji yau!

📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa!

Jin alamar mutum a bayanta ya saka ta juyo, sai suka hada ido, yana sayen da wando bachi sai farar vest dake jikinsa. Ya daga mata gira like how far, ta aika masa murmushi.

"Ina kwana"

Ya daga kafadunsa.

"Ni ma ban san inda yake ba"

"Okay good morning"

"it's morning but not Good Morning?"

Ta kalleshi with confuse.

"Why?"

Ya jingina da kofar kitchen din yana bata amsa tare da saka hannayensa aljihu.

"Cox i didn't get a kiss from my wife"

Ta juya ta aje wukar hannunta tana murmushi, kana ta sake juyawa ta nufi inda yake ta yi dage zata sumbance shi ya yi dage shi ma yana kauce fuskatsa.

"Bana so, sai da na yi magana rike abun ki bana so"

Ta zagaye hannayenta a wuyansa.

"I'm sorry haba autan maza, na tuba handsome na maka kiss ma kamin na fito kitchen fa"

"Aa ni ban ji ba, kuma waya ce ki bar ni ki zo kitchen? Ke dai kin dange sai kin wahalar da kanki ko?"

"Babu wahalarwa a cikin hidimar miji ko wace kala ce"

Ta sake kai bakinta da sauri zata masa kiss ya kauce yana dariya.

"Na ce bana so"

"Toh ba ni wanda na baka dazun, da kana bachi dawo min da abuna"

"Kiss din?"

"Eh"

Yayi dariya mai sauti.

"A ina kika ba ni?"

"A nan"

Ta tura masa bakinta.

"Ni na san ba ta nan aka ba ni ba, amman tun da wayo za'ayi min a yaudarini ba matsala"

Yayi mata kiss din. Ta sake shi tana ja baya cikin zolaya da muryar yaudara ta ce.

"Ba a nan na yi maka ba, a nan na yi maka"

Ta nuna kumatunta. Ya fusgota ya dawo da ita jikinsa.

"To dawo min da abuna, na baki na ki"

Ta noke kasa tana dariya. Binta yayi kasa yana mata kyaculculi sannan ya sake ta ya nufi plantain din da take yankawa tana soyawa at the same, ya dauki wukar yana yankawa ta karaso ya kwashe sannan ta dauki daya ta hura ta nufin ba shi.

"Ki daina hura abun da abun da zaki ci, Annabi ya hana, hura abinci"

"Na karu da wannan, amman akwai zafi fa"

Ya aje wukar ya dauki daya ya bude yana riritawa a hannunsa har ta sha iska.

"Bude bakin"

Ta bude ya saka mata.

"Kai zan bawa fa"

"Kuma kuka ci?"

"Kai ka ba ni ai"

Ya kai hannunsa ya rikota suka fara kokawa ala dole sai ya cire wanda ya saka mata a baki, ita kuma ta yi hanzarin taunewa ta hade har tana kwarewa sai dariya take. Sai da ya ji tana dari sannan ya sake ta.

"Wai Qalbin miyasa baki jin magana?"

Ya nufi gurin da ruwa suke ya dauko mata ta bude bottle din ya daga kanta ya saka mata a baki, ta sha kadan tarin ya kwanta.

"Kai ka koya min ai"

Ya kai ruwan bakinsa ya sha kadan.

"Ni din?"

"Ko da aka kawo ni gidan nan har kunyarka nake ji, amman ta bi ka bala ni"

Tana maganar tana dariya. Sai ya kai bakinsa yana hura amsan kanta.

"Haka ake yi ma yarinya idan su ta kware"

"Yarinya matar...."

Ya zaro ido.

"Ni din? Ni za ki duba ki cewa yaro? Gaskiya ne da sauranki"

Ya aje ruwan hannunsa kamin ya juyo ta gudu daga Kitchen din, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ya nufi kofar kitchen din ya rufe ta ciki, be bude ba sai da ya karasa aikin da take ya hada komai a ya zuba a mazubinsa sannan ya bude kitchen din ya kawo musu komai a inda suka saba karyawa. Al'ada ce ta ya sabawar kansa tun a lokacin da ya auri Kameela, idan ya rigata tashi shi yake hada musu komai na karyawa, idan kuma ita ta riga sai ta hada, sai dai ya fita kokarin hadawa domin tana yawan bachin safe shi kuma ya kan fita aiki dan haka baya jiranta yake hadawa musamman lokacin da take da ciki, har na rana ma wani lokacin girka musu yake ko yayi musu takeaway.

A yanzu kuma ya dora daga inda ya tsaya da Emily, banbancin Emily da Kameela shi ne, Emily tana son girkawa Aliyu abinci saboda tana son yi masa hidima tana son ta yi masa abu na faranta rai, abun da zai yaba mata. Tana gwada new recipe wani yayi dadi Wani kuma yayi ba lada ba la'ada, shi kuma da yake gwanin zama da mace ne, be taba kin yaba mata ba. Ko be yi dadi ba yabawa yake ya gode mata, sai dai ya fara mata inda za ta gyara ko su sake yi tare.

Readers Also Read