Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 72

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 72

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 72: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 72. Kusan inda ba shi da wani aiki a waje to yana gida kusa da matarsa.…

3,338 words

Kusan inda ba shi da wani aiki a waje to yana gida kusa da matarsa. Ita vata yarda ta yi nisa da shi, shi ma kuma be koya mata ba. Idan ya fita har kewar dawowarsa take, takan tanadi labarai kala kala da take ba shi, kama daga na littafi zuwa na mutane da take ganina kafafin sada zumunta, wani lokacin har kudi yake sakawa idan labarinta yafi na shi armashi zai biya, idan kuma nata ya fi armashi zata biya, ita ta kan biya ta wata sigar ne, shi kuma ya biya da kudi. Zamantakewa suke kamar daman can ita ce matarsa ta farko, ita ma shi ne mijinta na farko, ko da yake masu iya magana sun ce macen da miji ke so kullum yar gata ce.

Tun bikin su da sati biyu Ummi ta bar su a garin Kaduna ta koma Abuja gurin mijinta daman can take zama dawowarsa, abubuwan da suka faru ne suka saka ta dawo Kaduna da zama, a yanzu kuma tun da sun kamalla komai cikin aminci da farinciki sai ta koma gurin tata ibadar ta aure. Kamin ta tafi sai da ta yi musu huduba sosai, musamman Aliyu, saboda tana ganin Emily kamar bata da matsala. Ta gargadi Aliyu ta yi mata uzuri da kuma taka tsantsan akan zamantakewarsu, ya rufe ido kuma ya toshe kunnuwansa daga masu suka ko gulma, ita kuma ta yi biyayya ga mijinta ta gujewa bacin ransa, sannan ta toshe kunnu daga wasu kannan maganganu.

Ummi ta roki Emily karta zafafa akan zaman Fatima a hannunta, domin abu ne da dukansu suka sani Turhan ba zai yarda Fatima ta zauna tare da su ba, ko da kuwa tana son haka.

"Ki daurewa zuciyarki ko babu dadi ki masa uzuri, saboda ya so ki be samu ba yanzu kuma yana da yarki, to ki masa hakuri ya ji sanyi ko ta nan, kuma karki bude hanyar da zata kawo baraka da mijinki akan yarki, sannan karki yarda mijinki ya raina yarki ko ya kaskantar da ita, kuma ko da tana can ki rika kula da ita akai kai, dan Allah ku bawa marada kunya, kar a ji kanku, idan sulhu ya gafara da mijinki, akwai mahaifiyarki idan abun ya ci tura, ina nan kuma mahaifinsa na nan, ba fata muke ba, amman dai kar aji a waje"

Nasihar Ummi ta saka Emily ta dauke kai daga damuwa da rashin Fatima a kusa da ita, domin washe garin ranar da aka daura musu aure Ammy ta aiko aka dauki Fatima, har yau Fatima bata san ya dakin Emily yake ba, saboda ta ki kawota ita kuma bata son ta matsa abun ya zame musu matsala. Dan haka ta saka musu ido, Fatima na garin nan bata nan bata da labarinta almost 3 months da bikin babu amo babu labari.

KAMEELA POV.

"Ko da mafarki ban dauka Aliyu zai iya juya min baya har haka ba, kusan duka kawayena na bata da kowa saboda da shi, gaba daya rayuwata ta ta'allaka ne akansa"

Kanwarta Farida ta dafata.

"Kameela ke kika dauki Aliyu wani shege fa, tun farko be dace da ke ba"

Kameela ta dube ta.

"Zaki iya fada min illar Aliyu daya?"

"Zan fada miki da yawa ma, kin ga dai akwai masu sonki masu kudi amman kin nace sai shi, kuma ɗan makiyinmu ne"

Ta yi murmushi.

"Ba zaki gane ba, wannan ba illa ba ce, kuma na gujewa duk sauran ne saboda suna da aure, Aliyu kuma saurayi ne, Aliyu ba shi da wata illa da za a dube shi da ita a hana shi aure, amman ya ci amanata"

"Ko yanzu fa kin ki bawa sauran dama ne, mutane na nuna suna sonki"

"Farida ba zan iya zama da mai mata ba"

"Ko da Aliyun ne ya dawo?"

Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar a yanzu.

"Dan Allah karki bari son Aliyu ko abun da yayi miki ya hanaki kula wasu mazan, ki duba fa da zai yi aure ma be zauna a gidan da kuka zauna ba sai ya zabi zama a wani gidan kuma ya kwaso kayanki ya aiko miki, da kin mana yadda muke so ai da yanzu kin riga shi aure"

"Ba auren ba ai mazan ne, yanzu duk namijin da zaka ce ya saki matarsa ya aureka ba zai yarda ba, ni kawai sai idan na samu saurayi zan yi aure"

Farida ta gwalo ido.

"Eyyy sai kice ya saki matarsa ya aure ki? Tsakani da Allah Kameela ki aje wannan tunanin a gafe, yanzu fa gasar kudi ake ba ta kishi ba, kishi da hauka na talaka ne, indai mutum yana da yan kudadensa iya ruwansa da wani kishi, kuma duk manyan mutanan da ke sonki kowa da matarsa da yara ta ina zai saki matarsa ya aureki? Wani ma mata biyu"

"Ki daina zancen manyan mutane, na auri wanda ya kusa haihuwa da majina zan ji ko da kishi ko yayansa? Ko kuma so kike na sake auren na fito?"

"Aa amman mai kudi wake zancen majinarsa? Murar ma ai sai talaka, da kudinsu wa zai kula wannan kuma mataki suke dauka, ni Wallahi kawai ki yarda hannu ya koma miya bawan Allah nan yana aurenki first lady zai maidaki, daman yana neman yar boko kuma wayayen kyakkyawa ta nuna mai dan jiki fit haka dai kamar ke"

Kameela ta ja tsaki ta tashi ta fice ta bar mata dakin. Ta yi ma kanta alkawarin ba zata sake waiwayar Aliyu, ta riga da ta aje shi a gafe yanzu saboda ya yi aure. Abu kamar wasa kamar gaske, Kameela ta kasa kula kowa, idan ta ji labarin kana da aure da iyali sai ta aje ka a lissafi. Mahaifiyarta da iyayenta suna kokari sosai gurin lurar da ita abubuwan da ya kama ta dauka da muhimmanci a aure amman ta kasa domin ba wai iya rabuwa da mata ba, ita ko mai yayan wata bata so. Burinta ace ita kadai ce agidanta sai yayanta.

Saurayin da take ta jira ya ki samuwa, akan nuna ana sonta, wasu da yawa da suka nemeta lokacin da tana budurwa ba su samu ba, sun dawo amman ta gagara kula ko daya saboda dukansu suna da aure, jiran take sai ta samu marar mata kuma wanda zai fara gina iyali da ita. Ta kasa karyata zuciyarta ta kasa yarda da kaddararta tana da wasa da lokacinta, zuciyarta na ta yi mata hange hange marasa amfani. Kuma ta kasa cire Aliyu a ranta, kawai ta hakura da shi ne, amman sonsa ya ki barinta, kishinta ya ki ya tafi, kusan kullum idan ta kwanta da tunaninsa ai ta tuna a yanzu wata macen ce a kirjinsa ba ita ba, wata macen ce take kula da shi ba ita ba.

Wasa wasa Kameela ta fara nisa cikin burin da zuciyarta ta dora nata, na yaki da umarnin Allah, madadin hakuri da hukuncinsa. Ba iyayenta kadai ba ita kanta abun yana damunta, ta kasa focusing a kan rayuwarta, ta kasa manta Aliyu da zamantakewarsu, ta kasa bawa wasu mazan dama. Tun yan'uwanta suna lallabata mata har lamarin ya fara ba su haushi suna fita sabgarta. Ta kai ita kadai take iya fahimtar kanta, ta kan kebe ta yi ma kanta tambayoyin da ba su da amfani da kuma nadamar da bata haifar mata da komai ba sai bakinciki.

A yanzu ta gane ta inda matsalar ta bullo, sanadin zafin kishinta ne, ya kaita ga kokarin halaka mijinta, domin ita ce babbar damuwarta a yanzu, wata kila da bata yi kokarin kashe su ba, da Ummi ba zata hana su zauna ba, duk abubuwan nan da suka faru da yanzu ba su kawo nan ba.

Wata kila kuma da ta daure ta hana zuciyarta daukar Fatima ta kai ga Turhan mai yiyuwa da yanzu Aliyu be sake ta ba domin ne mafarin tonon asirinta kuma mafarin rabuwarsu. Idan ta so samawa kanta sassauci kuma sai ta tuna ai Aliyun ne ya fara kula Emily bayan kuma yayi mata alkawarin babu karin aure sai kuma ya zagaya yana bibiyar Emily.

Ba ita kadai ba kowace mace ba zata dauka ba balle kuma ita dake da zafin kishi. Wani alkawari da ta daukarwa kanta kuma take da yakinin zata iya cikawa shi ne, hakura da zaman aure da Aliyu, ko da kuwa zai dawo ya ce zai maida ita a yanzu, bibiyar da ta yi masa a baya ma nadama take yanzu, domin ta san ba ajinta ba ne, namiji ya sake ta akan abun da ta fishi gaskiya kuma ta bibiyeshi ya kasa saurarenta.

Ita sam bata ma amfanin zama da mutumen da ya nuna wata macen ta matarsa ta gida muhimmanci ba, ba dan haka ba babu abun da zai saka ba zai aje lamarinta a gafe ta kula Emily ba. Idan yan'uwanta suka so kara mata bakinciki sai su ce

"Ai daman can Aliyun ba wani sonki yake ba. Ke ce kika makale masa, uwarsa ma ba sonki take ba"

Zata iya yarda Ummi bata sonta even though bata mata wani abun dake nuna tsantsar kiyayya ba, sai dai kuma bata taba nuna mata tsantsan soyayya ba, bata yi mata gatan da ta yi ma Emily ba, bata kulata kamar yadda take samun labarin tana kula Emily ba. Kuma a yanzu ma ita ce ta cilastawa Aliyu juya mata baya bayan ta wulakanta a gidanta.

Amman zancen Aliyu be sonta, sam hankalinta ba zai dauka ba, ta san mijinta yana sonta, domin mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, ta san waye Aliyu ta san irin zaman da ta yi da shi, ta san rigimarta da yadda take kureshi kuma duk ya daga mata kafa, ta san yadda yake nuna mata soyayya ciki da waje. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya saka take hango yadda zata yi rayuwa da wani wanda ba shi ba. Yan'uwanta a kullum cikin nuna mata yadda zata walwala su ninka arziki da karfi a siyasa suke idan ta yarda ta auri abokin mahaifinsu.

"Ni gaskiya ya min tsufa ga mata ga yara, ni ba ta siyasar ko kudinsa nake ba"

"Matsalata da ke baki iya daukar shawara ba, ga kuma rashin hangen nesa, ai ko dan ki bawa Aliyun da uwarsa haush da ma matar ya kamata ki aure shi, kullum su yi ta ganinki gaban tv komai za'ayi sai da ke, idan kika yi hakuri ma kina gidan sai ya sake su ki koma ke kadai sai yayan da za ki haifa, ke yanzu ni ban isheki ishara ba? Yau ina Baraka ina Yayanta suke? Sai dai idan ubansu yayi marmarin ganinsu ya je ya gansu ko ya aika musu da sako, ni ko ganinsu ma bana jin yana zuwa yi, domin ko jiya da na masa maganarta cewa yayi na daina tuna masa da ita, na ce ranka ya dade ai dole na tuna maka saboda akwai yaya a tsakanin sai ya ce yara idan suka so ganinsa sun san inda yake ai, shi dai hakkin dake tsakaninsa da su ya kula da cinsu shansu da kuma sauran hidindimun rayuwa, ke har cewa yayi ba dan kar dawowar nan ya zama matsala a gareni da su ba sai ya karbe yaransa sun dawo nan, ni kuwa na yi karaf na ce a'a ya bar mata yaranta ta rike, toh ina zan iya da rikon balagagun yaya?"

Tana magana tana tsire baki dadin ya isheta, yanzu Mama Baraka da yayanta basa gidan. Ta shafa kanta yarta.

" Shiyasa nake son ki fitar da miji ki yi aurenki ki manta da wani Ali, daman can ba ku dace da juna ba, balle kuma yanzu da ya auri shegiya, kuma yar Baraka, ko dan ke na san dole ta aura masa ita, kuma abun kamar ba na banza ba, kin san lamarin yarbawa fa, in ba shi ba yaushe Aliyu zai auri shegiya? Ko da tana da kyau ai Asali wani abu ne mai girma, ko dan yayan mutum"

"Daman ita ta lalata komai gurinta nake tafiya neman shawara lokacin da muna samun tsabani kuma ba ta ba ni shawarar kwarai har cewa take ba laifin yarinyar ba ne, ashe saboda ta san yarta ce"

"Eh mana, dan Allah ki bawa maraɗa kunya, ki zabi mijinki ki yi aurenki ga ki tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wanda ya rasa, idan ma ba ki som shi His Excellency ki zaba cikin masu son ki mana, daman Alhaji yace tun da yayi maganar be sake ba, be zama lallai sai shi ba, ki zaba wanda kike so ki ba shi dama idan vaki bada daman ba baza ki iya kawar da tunani da damuwa a ranki ba, amman fa karki dauko ɗan makiyinmu kuma, karki mana na Aliyu, yanzu kam ba za mu bari ba ma"

Ta kwnatar da kanta a cinyar mahaifiyarta.

"Ki taya ni da addu'a Hajiya Allah ya sauya abun da nake ji a zuciyata kuma ya zaba min inda zan samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, duk masu mata ne, samarin sun ki zuwa wai ko dai dan na yi aure ne?"

"Aa ina ruwan aure da samarin, ke yanzu baki san an fi son zaurawan ba? Kuma saurayin zai iya zuwa, amman dai mun fi son mai kunbar susa, kin san logi be kin dadi, ba mu ki ace surukanmu duk manyan mutane ne ba, su kuma samari nan wasu ba rikon aure ba wasu kansu babu komai ciki sai tunanin abubuwan da ba su za su gina gobensu ba, kadan kake samu na kwarai, yanzu ba ga Aliyu ba? Amman da ace wanda ya san ciwon kansa kika aura inda ba shegen zamani ba ne, babu ruwansa da wani hango wata sai hada hadar kudi, ina za su shigo ina suka fita, daman duk abun da iyaye ba so babu albarka a cikinsa, shiyasa Aliyu ya zama haka"

Hausawa suka ce wanda ya cika da yaƙi ya mallakeka har ƴaƴanka, babu yadda Kameela iya bayan bin shawarar mahaifiyarta da yan'uwanta matukar tana son zama lafiya da su, kuma ta shirya samawa zuciyarta salama. Abun babu dadi kam amman dole ta daure a haka ta budewa masu kwankwaso kofarta dama, ko labarin zai sauya. Tun da wadanda take dakon zuwa sun manta hanya, wato marar mata da yaya ko kuma saurayi, har yau bata samu ko daya ba, masu matan ne dai suke ta kawo mata hari, daga mai daya, sai biyu har da mai uku yana nema ta hudu da ita tsabar sun raina mata wayo. [8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

Page 7️⃣4️⃣

🌟✨ TALIYAR HAUSA - YAR MURJI ✨🌟

🥘 "Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!" 🥘

Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa - Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al'ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida.

✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa - Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa - cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman

📍 Muna a Kaduna - amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed).

💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa - Yar Murji yau!

📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa!

"Okay bari idan na duba zan miki magana"

Ya amsa sannan ya kashe wayar ya aje sannan ya dauki comb din yana gyara mata gashi, suna zaune a falo, shi kan kujera ita kuma tana kan kasa.

"Daga gurin aiki ne"

Ta dago ta kanta ta kalleshi.

"Ban tambaya ba ai, Aliyu i trust you, kullum aka kira idan agabana sai ka ce min ga wanda ya kira, ina son ka san kai ka aje ni ba ni na aje ka, kuma kana aiki dole mu'amala zata hadaka da wasu wani lokacin, dole na yi hakuri, kuma kana da yancin haka, matukar be tsabawa addini ba kamar yadda kake yawan fada, kuma be tsabawa zamantakewarmu ba, ba zai kawo matsala ba, ni na yarda da kai, na san wa na aura"

Ya ja hancinsa yana murmushi kadan.

"Kin ance hadarin da ya baka kashi, gobe idan ka gan shi gudu kake, na dan shiga damuwa ne, saboda irin haka, kuma ya haifar da matsala kala kala a zamantakewata ta baya, na yi iya yadda zan iya wajen ganin ba a samu matsala ba amman hakan be samu ba, kuma ba a raba mata da kishi dole za ku yi kishi ai, kawai dai ba a son ya wuce gona da iri ne saboda yana haifar da matsala, ko ga matar ko ga miji ko kuma duka"

"But don't get mad at me idan na yi kishi"

Ta fada a shagwabe tana turo baki. Yayi murmushi ya saka hannayensa ya dagota

"Come here"

Ta daga ta koma saman jikinsa ya rumgumeta irin yadda ake ma yara har ya dan girgiza ta a hankali.

"Thank you for trusting me, i love you Qalbin, ba zan ji haushi ba idan kin yi kishi, ke ma ina hango kishi a idonki, amman ki iya rike shi ki yi controlling dinsa kar ya cutar da ke"

Ta lafe a jikinsa tana ta zuba shagwaba. Ya cigaba da shata mata kan a haka tana masa raki har da kuka wai da zafi.

"Shiyasa ai nake miki a gida, ba zan yarda kina tafiya shagon gyaran gashi ana kalle min kaya kuma jansa da karfi ana wahalar min da mata ba"

Ta kai hannunta tana taba chin dinsa zuwa wuya.

"Babe..."

"Mhn"

"Ina son na yi ma Dr A-B maganar tafiya gurin baban shi ina son na gan shi na ji yayi shiru be sake min maganar ba"

"Lallai kuma ya kamata ya hadaku ko a waya, kuma ina son idan kin samu time ki tafi ki gurin Ammy ki bincika Fatima ko lafiya"

Ta kara daga kai ta kalleshi.

"Ba matsala?"

"Bana jin wata matsala to matsalar me? Ni da na rike na mallake ki na malleke zuciyarki, na san kin damu ki san halin da take ciki ai, kina da aurena yanzu idan ma Turhan yana gidan dole ya daga miki kafa, balle na san ba ya nan, kuma ba ni da hujjar hana ki ziyarta su tun da Fatima ta shiga tsakani, kawai dai abun da ba zan yarda ba shi ne ki shiga ki dade ko ki wuni, ni zan kaiki na jira ki gama abun da za ki yi na dawo da ke"

"Na damu sosai na san halin da take ciki"

"Na sani, ina karantar damuwarki ko ba ki fada min ba, ya kamata ace ko sau daya ne ta zo gidan nan ai"

"Za mu iya tafiya gobe?"

"Mu tafi anjima da dare"

"Da gaske?"

Ya kai mata rankwashi a kai.

"Ina miki karya ne?"

Ta dafe kan

"Da zafi fa"

Ya kara mata wani, da ta ga zai kara mata na uku sai ta sauka jikinsa da sauri ta dauki fillon kujera ta jefeshi da shi.

"Zan kama ki ne ai"

Ta masa gwalo ta gudu. Bayan Sallah isha'i ta shirya, Aliyu ya sakata mota suka dauki hanyar gidan Ammy. A waje ya faka ta bude zata fita sai ya sumbanci hannunta dake cikin nasa.

"Ko da Ammy ta fada miki wata magana marar dadi karki ce za ki yi fada da ita a gaban Fatima"

"Okay"

Ya sake mata hannun ta fita ta rufe motar, sannan ta kwankwasa gate din gidan aka bude mata.

"Ammy na ciki?"

"Eh tana nan"

Readers Also Read