Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 1
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 1: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 1. *๐ ABOKIN RAYUWA ๐*
4,394 words
*๐ ABOKIN RAYUWA ๐*
*ยฉ Khadeeja Candy*
To my big sis, Hajiya Habiba Muhammad, words are not enough to express your worth and my love for you. I pray that Allah grants you the highest place in Paradise, fulfills your desires, and answers your prayers. I'm speechless You're even more than I imagine Wallahi. I dedicate this book to you, Hajiya Habiba Muhammad. You mean more than words can express you are everything I could ever ask for in a big sister. You treat me like your own little sister -I LOVE YOU deeply ๐คโค๏ธ
I couldn't introduce myself without mentioning you, Salma Ahmad Isah ๐ฅฐ I cherish you Salma, nasan ke ma kin san haka. If anyone is looking for another version of me, they'll find it in you.
NOTE...
Labarin nan ya zo da sabon salo akwai abubuwa da yawa a ciki, sai mun taru mun yi hakuri sannan zamu iya isa gurin da nake son muje. Na san halinku abu kadan ku fara attacking mutum.
Na fara rubuta labarin tun kamin na rubuta Hurriya, wani gari, da kuma taki zaman aure, amman Allah be ba ni ikon kammalawa shi ba sai yanzu, Allah ya ba mu ikon amfana da darasin da ke ciki..
*ยฉยฎHakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye โ *
Page - 1๏ธโฃ
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Kai na daga sama ina kallon bakin hadarin da ya fara saukar da ruwa, iska mai karfi na kadawa kamar zata tashi gari.
"Mamy.. Mamy... Ahhhh ahhhh ahhhh"
Kasa na dawo da kaina na kalli saitin da dana yake, wanda ya kasance autism, sai ihu yake yana murza ido da nake kyautata zaton kasa ce ta shigar masa. Hawaye ne suka sauko min tare gumi, duk kuwa da kasancewar iska ne yake kadawa ko'ina, amman zafin nakudar yar da zan haifa ya tare duk wani jindadi da zai rabeni a lokacin. A hankali na dafa kangon dake gabana na jingina sai kuma na sulale kasa na zauna, sai ruwan sama ya fara saukowa, ฤana ya fara ihu na fitar hankali, nakuda ta sallamomin da gaggawa, gani ya fara min nisa, numfashina ya fara yin sama...
Babu kowa a tare da ni, babu wanda yace Emily, ki yunkura zaki iya, babu mai fada min haka ake yi ba haka ake yi ba, ba ni da gatan da wani zai damu da ni balle ya kai ni asibiti, zan iya haihuwa da kaina ko sai an sake fasa ni CS kamar wacan karon? A haihuwar ฤana London haihuwata ta fari. Jin wani azababben zafi ya ratsa marata zuwa cinyata ya sakani ihu da dukanin karfina, a gurin da babu mai cetona.
"Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?"
Na ji wata sabuwar murya, idanuwana suka yi arba da wata bakuwar fuska dake duke a gabana yana leken tawa fuskar, saukar ruwan sama da kuma zafin nakuda, ba su ba ni damar tantance waye tsugune a gabana ba. Na mika hannayena duka biyu na riko hannayensa ina numfashi daker, azabar nakuda ta hana ni magana.
"Subhanallahi... Christen ce ke?"
A kokarinsa na zare hannunsa daga nawa agogon hannunsa ya zame ya tsaya a hannuna sai na jimke agogon da karfi ina nishi mai karfi.
"Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?"
Na girgiza kai alamar aa, to ni a kaf duniyar ma wa na sani balle kuma a kusa da ni.
"Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan..."
Kai kawai nake iya daga masa, ni dai burina a taimake ni a raba ni da abun da nake ji a yanzu. Da alama maji karfi ne, domin cak na ji ya daga ni yana istigifari.
"Astagafullah Allah ka yafe min ba da niya na taba ta ba"
Ya saka ni a motarsa, be damu da lalacewar da jikina yayi ba, be damu da ihun da ฤana yake kamar zai fasa kunne ba, be damu da banbancin addininmu ba, be duba talaucina da arzikinsa ba, haka ya ja motar da karfi yana tukin yana min sannu, yi hakuri mun kusa karasawa asibitin, kai kace ni din yar'uwarsa...
*** *** ***
Karar bude kofar dakin da take ciki ne ya dawo da ita duniyar tunaninta. A hankali take shafa tsadaden agogon dake hannunta mai ruwan zinari, hawaye masu zafi na sauko mata.
"Emily..."
Ta daga kai ta kalli mai kiran sunan nata ta cikin madubin dake gabanta. Da sauri ya karaso kusa da ita ya tsaya yana kallonta, a cikin kallonsa akwai tashin hankali, akwai kauna, akwai tsoro, akwai fargaba da suka rufe shi lokaci daya saboda ganin hawayenta.
Risinawa yayi kasa a yayinta take zaune agaban madubi mai cike da kayan kwalliya. Fari ne, mai yalwatacciyar bakar fuska mai kama da bakin hadari, kallo daya zaka masa ka fahimci annuri da far'a ba su da muhalli a fuskarsa, sai dai kuma shi din kyakkyawa ne, namiji ne mai kirar mazaje. Sarkar Cross ce a wuyansa irin wadda ke wuyanta, banbancin tashi da nata tata karama ce tashi kuma babba ce wanda ta cika kirjinsa dake dauke da zanen tattoo. Dubansa ya kai kan agogon dake hannunta a take ya kara hade rai.
"Har zuwa yaushe zaki daina dauko agogon nan dake tuna miki rayuwar baya?"
Ta kalleshi da idanuwanta masu matukar kyau da daukar hankali, da bakin da yayi daidai da tsarin fuskarta ta furta.
"Har zuwa lokacin da zan iya manta alheri"
Ta maida dubanta a gurin agogon da take jin kamar shi din ya taimaki rayuwarta, a lokacin da mutuwa ta so ta kusantota.
"Ko waye mai wannan agogon, yana da kirki, yana da tausayi, yana da kyakkyawar zuciya, shi din ya banbanta da sauran musulmi"
Zabura yayi kamar zai dake ta cikin ihu ya rufe ta fada.
"Babu banbanci tsakaninsu, babu banbanci tsakanin ko wane musulmi, kin gwada daya kin gwada biyu kin gani, baki bukatar wani ya baki labari, miye a cikin kanki? Meyasa kika kasa manta rayuwarki ta baya? Kina da komai yanzu, baki bukatar kowa I'm here for you and I Love you"
Ya rumgumeta daga tsayen da yake sai ta fashe da kuka ta rikeshi sosai. Bayanta ya shafa yana maida numfashi a hankali tare da rarrashinta.
"Kina da duk wani abun da kike mafarkin samu a yanzu Babe, kina da Luxury Home and Cars, kina da komai Babe"
Dagowa ta yi daga jikinsa ta share hawayenta ta bude aljihun madubin ta saka sarkar ta mike tsaye ta shiga bandanki ta wanke fuskarta, ta cikin madubin dake bandakin take kallon kanta. Ta canja, hallitarta ta sauya, halinta ya sake, kyauta ya ninku, kyaun jikinta ya bayyana.
"You can do this Emily, you have to do this, ke din a yanzu Emily ce ba wacan Emilyn ba, ke din a yanzu Emily ce, ba Aysha ba, jaruma ce baki bukatar kowa a kusa da ke"
Ta fadawa kanta domin karfafawa kanta guiwa, daman waye zai karfafa mata? Idan ba ita din kanta ba, turawa suka ce when you have no one to push you push yourself. Takawa ta yi baya tana cigaba da kallon kanta sannan ta dauke idonta ta kalli kofar bandakin, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kofar ta bude ta fita.
Gaban madubin ta sake zaunawa ta fara shirya kanta, har ta yi kwalliyar ta gama Vito be ce mata komai ba yana zaune ya dora kafa daya saman daya, wayarsa a hannunsa sai dai duk abun da take jajayen idanuwansa suka kanta. Gurin da ta ware tufafin da zata saka ta nufa ta dauka ta nufi wani karamin daki ta canja tufafin sannan ta fito tana gyara gashinta dake hade da gashin doki attachment.
"Kin yi kyau"
Ya fada yana nufar gurin da take tsaye, ta yi kyau kam iyakar kyau, kyaun da ya wuce ayi mata kallo daya a dauke ido, yadda aka tsara hallitar fuskarta da kirar jikinta, kai kace ma ita ta yi kanta.
"Ban san miyasa kika dage sai kin yi aiki ba, ban san manufar da kike son cin ma ba, na wadata ki da kudi, ban san miya hana zuciyarki natsuwa da hakan ba, arzikin da zaki je nema a wani gurin be taka kara ya karya na arzikin da na aje miki a nan ba, amman dai ko miye, zan goya miki baya saboda ina sonki ina son farincikinki sosai"
Magana yake yana zagayeta kamar mai tantance komai na jikinta.
"Ba arziki nake nema ba, so nake kawai na yi rayuwa irin na sauran mutane, ka canja ni kuma na canju, na watsar da komai ina rayuwa ne irin na mutane, karka ji tsoro"
Ya tsaya daidai fuskarta har numfashinsa yana gauraya da nata.
"Vito be san tsoro ba, amman shi tsoro ya san Vito shiyasa idan ya gan ni yake boya, you belong to me karki manta wannan"
Ya sumbance ta.
"Wish you all the best, fatar ki fara aiki a sa'a i love you, good luck on your new Job"
Ya mata murmushi kadan ya shafa fuskarta sannan ya dauke hannunsa ya fice. Tsaye ta yi a gurin na wasu dakiku, sannan ta busar da iskar bakinta ta nufi wayarta da jakarta ta dauka ta fice daga dakin zuwa bangaren da ฤanta yake.
TURHAN POV.
"Baka tafi ba har yanzu?"
Ya mike tsaye yana kallonta idanuwa a raunace fuska dauke da damuwa.
"Ammy..."
Sai kuma ya kasa furta komai saboda yadda ta tsare shi da wani kallo irin na horo daga uwa zuwa ga danta.
"Zamanka ba shi da amfani a nan, kasan ba zan taba barinka ka kwana a gidana ba, toh ba amfanin bata wuni"
Ya bude baki sai kuma ya maida ya rufe a hankali ya taka zuwa kusa da mahaifiyarsa.
"Ammy I'm sorry, na yi nadama kin sani, na tuba ki yi hakuri ki yafe min"
Ya durkusa kasa ya rike hannayenta.
"Me zan yi ki yafe min Ammy? Me zan yi ki yarda na yi nadama?"
"Nadamar ka ba zata gyara abun da ka bata ba, ni ban kullace da komai ba, kawai alaka ce irin ta da na yanke"
"Ammy mi zan yi ki fahimci na yi nadama? Mi zan yi ki yafe min? Ina cikin damuwa ina cikin matsala"
"Na yafe maka Turhan na dade da fada maka haka"
"Ba irin wannan yafiyar nake so ba, irin wanda idan zan bar kasar nan kike kewata, idan na zo kina murna da zuwana, mu zauna mu yi hira mu yi wasa da dariya, Ammy me zan ki min irin wannan yafiyar"
Ya tambaya yana shirin fashe mata da kuka.
"Zan maka irin wacan yafiyar da kake tsammani ne, only if Aysha ta yafe maka..."
Ya girgiza kai.
"Ammy karki yi haka, idan kika alakanta yafiyarki da Aysha to ba zaki taba yafe min ba, domin ban san ina Aysha take a yanzu ba, ban san inda zan ganta ba, Ammy idan kika yi haka ba ki min adalci ba..."
A take ta daka masa tsawa.
"Kai ka yi min adalci kenan? Saboda kai yarinyar nan ta bar addinin musulunci, duk wani gata da na so na yi mata na addinin musulunci ka ture, duk wata shimfida da na yi na yaye mata damuwar da wani ya saka ta ka nade shimfidar ka jefar, na shirya zama mata uwa saboda bata san wannan gatan ba, duk wani buri da nake da shi akanta da akanka ka ruguza shi,
aikinka da yadda ka riketa yadda ka wulakantata ya goge duk wani karatu da na shimfida a cikin kanta cewar mu musulmai halinmu ba daya ba ne, a ranar da ka sauke ta garin nan da idona na ganta a gaban coci tana rokon su taimaketa, saboda tana ganin mu musulmai mun gaza. Turhan ka saka Aysha ta ji cewar mu musulmai ba ma iya kaunar wanda ya shigo musulunci, ka saka ta ji cewar ba mu da kirki, da karfi da yaji kun cire mata son addinin musulunci, da karfi da yaji kun nuna mata tubabe ba shi da gata a addinin Musulunci, duk wani buri da nake da shi akanka da ita ka rusa shi... Ka zabi Masarautarku, ka bi mahaifinka, to ka dawo na yi maka?"
"Ammy kamar kin fi son Ay..."
Be karasa ta wanka masa mari.
"Na fi son Aysha da kai Turhan, haka ne baka yi karya ba hashenka a daidai yake, da ka rike ta a yadda na so wata kila da rikon zai iya zame min silar shiga aljanna, duk wani hali da ta shiga ko zata shiga kai ne sila..."
"Ba ni ne sila ba... Ammy ba ni ne mijinta na farko ba, kuma ban mata wulakancin da kike tunani ba, yadda kike daukar abun be kai haka ba"
Ya fada yana hawaye shi dai kokari kawai yake ya fahimtar da ita kuma ya wanke kansa. Sai ta nuna masa kofar fita falon.
"Tashi ka fice min daga falo, ai kasar nan bata cikin rikon ubanka ko? Iyakar mulkin sarautarku da ikonku ya tsaya a Sudan ne, to tashi ka koma can ka rike sarautarka da matarka da yan'uwanka da mahaifinka, ka bar ni da nawa"
Ya mike tsaye kai a kasa ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo har ya fice sannan ta juya ta kalli Amal dake tsaye stairs tana kallon abun da ke faruwa.
"Ammy dai kin yi hakuri na ga..."
Ammy ta kalleta fuska babu alamar wasa.
"Idan kika furta wani abu akan matsalar nan, to zaki hada kayanki ne ki bar min gidana"
Ta rufe bakinta da sauri ta juya ta koma sama. A mota Turhan ya samu kansa ya jingina da sitiyarin gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Wayarsa ya dauka ya amsa kiran dake shigowa yana gyaran murya domin damuwa ta gama cinye karfinsa.
"Ihm ihm Hello"
Sai aka amsa masa daga dayan bangaren.
"Hello Turhan ya gidan?"
"Lafiya Kalau"
"Ashe ka shigo kasar, dazun nake ji a gurin Uzee"
"Haka ne amman dai yau zan koma"
"Why?"
"Ba dadi, Aliyu har yanzu babu wani abu sabo, Ammy ta ki karbata, ga damuwar abubuwa da yawa suna rufe ni, na rasa me ke min dadi"
"Har yanzu babu labarin Aysha?"
"Babu, kuma yau Ammy ya tabbatar min ba zata yafe min ba, sai Aysha ta yafe min, ban san inda zan ga Aysha ba"
"Bana jin fa tana raye, domin da tana raye neman da ka yi mata da yadda aka zuba kudi da yanzu an gane ta, ni ma ta gurina ba wani labari gaskiya, ina ganin abun da zai fi, ka koma nan da kwana biyu idan na duba time da ya fi sai ka dawo muje tare mu samu Ammy mu rarrasheta wata kila zata yafe maka"
"Abu ne da kamar wuya, ta hau sosai ta yi fushi Aliyu"
"Karka karaya, za mu samu kanta In Sha Allahu, ba wai mu kadai zamu tafi ba sai mun gayyaci mutane, ka yi magana da amininka ku tattauna idan kun yi shawara da kuke ganin ya kamata mu shigo ciki sai mu shiga"
"Toh Allah yasa ta yafe min, ko da ya yafe min dole zan cigaba da neman Aysha, ina da bukatar ganinta ina son ganin..."
Yayi shiru be karasa ba.
"I will call you Back"
"Okay"
ALIYU POV.
Ya sauke wayar tare da bude bakinsa ya karbi plantain din da Sultana take kai masa baki.
"Uhmm so kike cikina ya fashe ko?"
Ta yi dariya tana jan hancinsa.
"Eh so nake cikinka yayi kato kamar nawa"
Ya saka wayar aljihu ya kai hannunsa ya shafa cikin nata.
"Ai da ba zaki zauna da ni ba, amman yanzu saboda kin ga saurayi kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa shiyasa kike zaune da ni"
Ta bude baki.
"Sai kace ba ni na saka ka yi kyaun ba, kamin na aure ka ai baka da kiba amman ina aurenka ka yi kiba ka kara kyau"
Ya zagaye cikinta da hannayensa.
"Ke ma dai kin ce na kara kyau, that's mean ina da kyau tun farko shiyasa kika rude kika ce ke sai ni"
Ta kai masa yatsina a fuska har sai da ya matsa baya yana dariya.
"See this girl"
"Zaka yi latti fa, ka tafi ko na kira Momy na fada mata"
"Sai nace mata ke kika rike ni kika hana ni tafiya aikin, kin ga idan ta min fada sai na rama akanki"
Juyar da shi ta yi ta fara turashi har sai da ya fita daga falon dan dolensa.
"Ni da gidana a rika korata"
"Ka dame ni ne, and Point of correction gidana ne ba naka ba"
Dawowa yayi kusa da ita ya sumbance ta ya shafa cikinta.
"I Love you, sai na dawo ayi min addu'a mai ciki"
A take ta kai masa rankwashi akai sai ya zuba da gudu gurin motarsa yana dariya
"Allah ya kiyaye ya tsare min kai, dan kyakkyawana"
"Amin yar kyakkyawata"
Ya dago mata hannu ta daga masa sannan ya shiga motar yayi addu'a yayi mata key yayi horn mai gadin da ya kasance inyamuri ya bude masa gate ya fice, zuciyarsa cike da so da kaunar matarsa.
____________________
Share fagen sabuwar tafiyar kenan. Da fatar zaku karbe shi da hannu biyu.
Khadeeja Candy... โ๏ธ +2348036126660
A hankali ta tura kofar dakin da danta yake ta shiga sautin dariyarsa ya saka ta farinciki tun kamin da karasa gurin da yake zaune. Vito ya juyo ya kalleta ko kadan babu murmushi a fuskarsa sai ka rantse da Allah ba shi ne yake yi ma London din wasa ba yana dariya.
Kallonta yake har ta karaso kusa da shi gurin da danta yake zaune, ta rage tsaye ta kai hannu ta shafa fuskar danta, shi kuma ya kai hannu zai shafa fuskarta sai ta kauce ta yi saurin mikewa tsaye, a nan ma da kallo ya bi ta, wani irin so yake mata wanda ba zai iya dorashi a mizanin awo ba.
"Karfe nawa zaki dawo?"
Ta kalli agogon hannuna.
"Ban sani ba, sai idan na tafi"
"Karki zauna da yunwa idan babu abinci a can ki fada min zan aiko a kawo miki"
Ta kalleshi kawai ta dauke kai sannan ta sakarwa danta murmushi, ta sake rage tsayinta tana kallon danta.
"London zan fara fita aiki yau, zan wuni ba a gida ba, kai kuma zaka wuni da Chidimma your Nanny..."
Bata rufe baki ba ya girgiza mata kai ya bata fuska zai yi kuka.
"Ni bana son zama a tare da Chidimma ina son zama tare da Uncle Vito"
Ta saka hannayenta biyu ta rike fuskarsa tana masa magana a hankali, domin karami abu ne ya birkice mata a take.
"Uncle Vito zai fita yana da aiki, amman idan na dawo...."
"Zan zauna tare da shi"
Vito ya amsa mata yana kallon gefen fuskarta. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce.
"Amman kana da gurin zuwa"
"Ba karamin abu ba ne London ya sake jiki da mutum, ya fara cewar baya son zama gurin Nannynsa so let him be with me, ko kuma ke ki fasa tafiya aikin ki kula da shi"
Ta cire hannunta daga jikin danta ta mike tsaye
"Ka zauna da shi ni zan tafi"
Ta juya ta nufi kofar dakin ta bude ta fice, da kuzari ta fito cikin gidan ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice. Tafiya sosai ta yi sannan ta samu taxi ta shiga sai da ta zauna sannan ta fada masa gurin da zai kaita. Direban ya saka sauti mai dadi yayi kasa da volume din yana tukin a hankali. Idanuwanta ta maida gefen titin tana kallon hanya da ababen hawa da kuma shagunan suka yi ma hanyar ado, sai dai gaba daya hankalinta yana wata duniyar da ta kasa mantawa da mutanen cikin da kuma rayuwar da ta yi a ciki.
"Idan baki iya larabci ba karki gwada, ba a nigeria kike ba, al'adunmu sun shan banban, saboda haka bana son ki yi magana har zuwa lokacin da zaki koma gida, zan sanarwa kowa cewar ke kurma ce"
"Saboda me?"
"Saboda bana son kowa ya san wani abu a tsakaninmu, addininmu da na ki ya shabanban, ina da daraja mai girma a nan, ni dan sarauta ne jinin sarauta, ina da iyali da rayuwa a nan"
"Ni ma musulma ce ai a yanzu"
"Kowa ya ganki ya ji muryarki ya san tuba kika yi, ba wai an haife ki a ciki ba ne, sanin cewar na auri tubabbiya zai zubar min da kima, kuma babu wanda ya san maganar auren nan daga ni sai ke sai Ammy, Ammy kuma bata nan daga ni sai ke ne a nan"
"Allah yana nan, be kamata ka yi min haka ba, be kamata ka wulakanta ni ba, wannan zalinci ne kuma Allah baya son haka"
Ya dalla min harara.
"Ke Allah kika sani? Kin san Allah kika tashi cikin kafirci? Karki kuskura ki ce zaki fadi wani abu akan hakan, domin ke baki san komai ba, sallah ki ma ba a fara karba ba, domin ba mai kyau kike yi ba"
"Amman Turhan..."
"Kul... Karki kuskura kiran sunana a nan, karki kuskura nunawa kowa cewar kin san ni, ni ba mijinki ba ne a yanzu, na aureki ne a inda aurenki ya zame min dole, a nan kuma ina da wasu iyalin..."
*** *** ***
"Madan a nan zan tsaya ko ciki za mu shiga"
Tambayar da direban Taxi din yayi mata ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, hannunta ta saka ta share siraren hawayen da suka zubo mata.
"Shiga ciki"
Ya kunna kai kamar yadda ta masa umarni har sai da ya isa gurin da aka tanada domin aje motoci, ta bude motar a hankali ta fita ta dauko kudinsa ta mika masa sannan ta nufi babbar kofar ma'aikatar da mutane suke hada hadar shiga da fita, sosai gabanta ya tsananta faduwa domin abu ne da bata taba yi ba zata fara a yanzu, wato aiki, a yanzu zata yi mu'alama da mutane bayan ta yankewa kanta mu'amala da kowa sai mutumen da shi ne silar dalilinsa take tsaye a yanzu wato Vito.
Bata bukatar wani yayi mata iso domin wannan ne karo na uku da ta zo ma'aikatar bayan zuwanta na farko da ta kawo CV ta, sai kuma zuwan da ta yi interview. Third floor ta nufa bayan ta shiga elevator and she pressed the buttom. Kanta ta daga sama tana kallon gurin tare da aje numfashi a hankali, feeling awkward and excited as the same time. Elevator ya rabe biyu ta fita tana kara gyara gashinta, kai tsaye ta nufi office din da aka musu interview ta yi knocking sannan ta tura ta shiga. Wani saurayi ne a ciki da ba zai wuce sa'arta ba, ta dan yi mamaki domin wacan zuwan nata na farko ba shi ta tarar ba, ta gaisa da shi cikin mutunci ta gabatar masa da kanta.
"Nice to meet you Aisha, a nan an muku interview ne kawai, a hawa na hudu dama dake akwai wani office na farko shi zaki shiga, ki gabatar masa da kanki zai fada miki gurin da office dinki yake"
"Okay na gode"
Ta juya ta fita har lokacin bata jin sakewa domin yau ne ranarta ta farko kuma abu ne da bata saba ba. A tsanake ta nufi gurin da Elevator ke daf da rufewa mutumen dake ciki yana tsaye yana kallonta ita ma kallonsa take bata dauke ido ba har sai da elevator ta rufe. Tsaye ta yi a gurin tana kallon floor din da kowane office yake rufe. Babu tsammani elevator ta sake budewa mutumen da ta hango dazun a ciki shi ne har yanzu, matsawa ta yi gefe domin ba shi hanya a zatonta fita zai yi, sai ta ga tsabanin haka, be ce ta shigo ba kuma shi ma be fita ba, ganin kofar na kokarin rufewa a karo na biyu ya saka ta yi hanzarin shiga sai ta matsa daga gefe.
Kamata yayi ta gode masa? Saboda ita ya sake pressing floor din da take ko kuma dai wani abu zai yi, ya fasa. Ta dan dago ta kalleshi kadan sai ta ga idonsa yana kanta ta yi hanzari dauke kai.
"Okay Momy zan yi, i love you"
Ta ji ya fada sannan ya kai hannu ya taba black iPod din dake kunnensa. Da sauri ta dube shi jin ya ambaci uwa, a duk gurin da mutun yake tare da mahaifiyarsa ko ta ji ya ambace ta, ko kuma ta yi arba da alakar uwa da da, sai hankalinta ya tashi, sai ta ji wani abu ya tsaya a zuciyarta, domin ita bata san wannan gatan ba, bata san mutum daya a duniyar da zata nuna a matsayin dan'uwanta na jini ba balle kuma uwa. Ita din wane laifi ta yi ma iyayenta suka jefar da ita a gidan marayu? Su waye iyayenta? Wane addini suke yi? Wane yare suke ji? Ita ce tambayar da take yawan yi ma kanta.
"Excuse me, can i help you?"
Ashe kallonsa take da kyakkyawan blue eyes dinta masu matukar daukar hankalin mai kallonsu. Blue eyes din ne suka karafafa masa guiwar kallonsa har yake jin kamar ta taba wanzuwa a wani bangare na rayuwarta ta baya, wata kila kuma kyauta ne yake masa gizo har yake ganin haka, but this is the second time da yayi arba da mace mai blue eyes a Africa.
"No, I'm sorry"
Be sake ce mata komai ba, sai dai har lokacin kallonta yake ta gafen ido, ita din ai ta kai ayi mata kallo fiye da goma ma, ba daya ko biyu ba, but wait ina ilminsa da tarbiyarsa da koyarwar addininsa suka tafi? A take yayi hanzarin dauke idonsa gaba daya daga barin kallon abun da ba halalinsa ba.
'Astagafullah'
Ya furta a ransa a daidai lokacin da elevator ya bude a hawa na hudu, ta dan kalleshi tana jiran ya fara fita sai ta ga be fita ba sai danna Apple watch dinsa yake, hakan ya saka ta fita cikin rashin sakewa ta fara tafiya. Sai a lokacin ya dago mistakenly idanuwansa suka sauka bayanta, sai ya rufe ido da sauri ya taba numbers din da suke jikin Elevator a take ya rufe yayi sama da shi to 5 floor.