Kenza eBookz

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 2

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 2

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 2: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 2. Office din farko ta fara murdawa kamar yadda aka…

4,487 words

Office din farko ta fara murdawa kamar yadda aka fada mata ta tura ta shiga. Ya san ko dai ta tsaya a 4 flour ko kuma kasa zata koma, domin ma'aikatan kamfaninsa basa wuce 4 Flour the 5th floor is his and his entire team, and be taba ganin fuskarta a kamfanin ba, maybe she's among the new employees ko kuma ta zo gurin wani ne, ko dai minene she should be tsakanin fourth to first floor. Sai ta samu kanta a babban guri da wasu dakunan a rufe, da dan tsoro irin na rashin sabo ta tura kofar Office din da shi ne farko ta shiga ba tare da ta yi knocking ba.

Matar dake sanye da abaya da karamin hijab half sunna, tana amsa wayar telephone ta dago tana kallonta fuska babu annuri. Emily ta tsaya a gurin gabanta na faduwa zuciyarta na tsanar matar da ko sunanta bata sani ba a yanzu, ba dan komai ba sai dan shigar ta wato suturar jikinta ta isar da sakon addininta ga duk wanda yayi ko zai yi arba da ita. Ta tsaya a gurin har sai da ta gama amsa wayar, sannan ta karasa kusa da ita.

"Am... Sunana Aisha Muhammad ina daya daga cikin sabin ma'aikatan da aka dauka, kuma yau ne zuwana na farko, a office din da aka mana interview yace na shigo nan"

Ta fada cikin sakin fuska da murmushi, sai matar ta kara hade rai ta jefa mata wani kallo.

"Amman dai baki manners, ta ya zaki shigo cikin office ba tare da knocking ba? Kuma a farkon Shigowarki ai ya kamata ki tsaya sai an miki izini tukuna"

Emily ta sassauta murmushinta tana dan ji babu dadi, matar dake gabanta ba san yadda Vito ya jikata da gata ba, wata kila da bata fada mata magana irin wannan ba.

"Ki yi hakuri, mantawa na yi"

"Koma ki yi knocking idan na miki izini sannan ki shigo"

Ta fada kai tsaye tana bude wasu files dake gabanta, Emily ta tsaya kallonta like are you serious right now? Ganin hakan ya saka matar ta sake duban Emily.

"Kurma ce ke?"

"Aa"

Ta amsa sannan ta juya jiki ba kwari ta fice daga office din. Taja tsaki after Emily ta fice.

"Mtswwww, na ga Aisha Muhammad na dauka ke kadai ce Musulma a cikin sabin da aka dauka, ina cewa zan samu yar'uwa ashe kafirar ce, irinsu ne ke batawa musulmi suna, suna aikata abu ace musulmai ne, sunan mahaifinta da nata na musulmai amman fuskar kafirai da sarkar Cross a wuya, na tsani kafiran nan Wallahi"

Sai fada take kamar zata yi duka, abu ne da ta boye a zuciyarta saboda mu'amalarta da mutanen da suke garin Port Harcourt da kuma kamfanin mafiyawancinsu kistoci ne, amman bata kaunarsu ko kadan.

"Na riga na zabe ki, na dauka Musulma ce Wallahi, amman zaki ci ubanki"

Ta fada tana dora hannunta a laptop din dake gabanta. Emily na fita kai tsaye ta nufi gurin Elevator yake a fusace domin ta manta when last a wulakanta, kusan wani be taba gwada yi ma makamancin wannan wulakancin ba a sabuwar rayuwarta ta yanzu. Kamin ta karasa wayarta ta yi kara sai ta saka hannu a jaka ta ciro wayar, ganin sunan dake jikin screen din ya saka ta tsaya ta daidai numfashinta, ta sani idan har ta amsa wayar a cikin yanayin da take a yanzu na bacin rai zai ji haka a muryarta zai iya tashin building din ba tare da tsayawa ya ji dalilin bacin ran ba.

"Hello"

"Emily miyasa baki fita da motarki ba?"

"V, idan na dawo za mu yi magana"

Ta fada a daidai lokacin da ta dora hannunta Elevator zata danna.

"Answer me...!!!"

Ya daka mata tsawa har sai da zuciyarta ta yi rawa, and yes this is not the first time da yake tsawa, ya saba dukanta ko ya takata ko ya yi mata fada ko raunatata but shi kadai zai iya mata haka, idan wanin da ba shi ba yayi mata kallon banza sai ya saka an cire masa ido. Ta kashe wayar da sauri tana maida numfashi da karfi, rauni da damuwa irin na wanda ya rasa madafa suka bayyana a fuskarta. Dauke hannunta ta yi ba tare da ta taba ba, ta juyo ta nufi office din da ta fito. Vito na daga cikin dalilinta na son ta inganta rayuwarta ita kadai a yanzu ba tare da taimakonsa ba, duk kuwa da kasancewar shi ne silar komai nata a yanzu. But tana son ta samu freedom so take ta samu yancin rayuwa ita da yayanta kamar sauran mata, ta jika a kangin bauta har yanzu so take ta yi rayuwa ita kadai ta tsayu da kafafuwanta, ta zama Independent woman.

Sai da ta daidai tsayuwarta ta nemi kwarin guiwa da confidence ta lullube zuciyarta da shi sannan ta kai hannu ta yi knocking Office din. Shiru ba ta ji ance ta shigo ba, hakan ya saka ta sake kwankwasawa a karo na biyu, ta sani a yanzu kam ba zai yi ace bata ji ba, sai dai dan wulakanci zata aje ta a gurin, kuma ba ta yi mamakin wulakancinta ba, saboda ga dukan alamu macen musulma ce, a iya kar ilimin Emily kuma musulmai ba su da kirki. Ta kusa minti biyar a tsaye sannan ta yi mata izinin shiga. Emily ta tura office din ta shiga sai dai wannan karon babu irin murmushi dake fuskarta a wacan karon.

A nan din ma sai da ta sake gabatar mata da kanta, matar ta dan kalleta ta dauke kai, after like 10 seconds, ta dubi Emily tace.

"Aisha sunanki ko what so ever, za ki yi aiki da ni a matsayin Assistant dita, aikinki shi ne kullum zaki shigo 6:30am 7am ta yi miki a nan, zaki yi mopping office din nan ki gyara komai, kamin na shigo, zaki hada min abun karyawa kamar tea ko coffee duk abun da yake available dai ko kuma nake ra'ayi, and duk abun da nake bukata na aika ko yi ke zaki min, and lastly Office dinki yana next to mine"

Ta mike tsaye cikin izza ta isa gurin wata karamar durowa ta bude ta dauko file da keys ta dawo ta mika mata.

"Akwai ID na aikinki a kamfanin mai dauke da sunanki da hotonki, zaki saka a wuya ne kullum idan zaki shigo kamfanin nan, a cikin file din akwai rules and regulations na kamfani ki yi saka hannu ki dawo da shi gobe"

Ta dora mata keys din a saman file.

"Wannan key din office dinki ne, hadi da nawa saboda ki samu damar gyara min nawa ko daukar wani abun idan bana kusa"

"Okay, Ma'am Thank you"

Emily ta furta sannan ta juya.

"And... Sunana Amal not Ma'am, ba dole sai kin yi aiki ba, idan kin duba office din ki yi tafiyarki, gobe ki shigo da wuri"

"Okay"

Ta amsa ba tare da ta juyo ba, Amal ta bita da kallo tana yatsina fuska har ta fice sannan ta nufi kujerar.

"Da wasu idanuwa blue kamar na aljannu, ko mage, waya sani ma ko mayyace, ko wace yare ne ma oho"

Sai kuma ta bawa kanta amsa.

"Zata wuce Igbo dama sune kafirai ai"

emily na fita office din ta nufi office din dake kusa dana Amal, sai da ta karewa kofar kallo sannan ta saka key din ta bude ta shiga. Komai fes ga computer da karamin tebur daidai ita, ita ma tana da karamin dorowa kamar Amal. Window ta kuma yana facing din gari da makwantan gine gine da suke wajen kamfanin sai titi da zata iya hango hada hadar mutane, ta dan samu sakewar zuciya wanda har ta kaita ga murmushin jindadi.

TURHAN POV.

Bude motar yayi ya fito yana shafa fuskarsa ya kalli kofar falon bayan ya rufe motar, sai da sauke ajiyar zuciya irin ta manyan mazaje yayan sarauta sannan ya sake komawa falon mahaifiyarsa. Yana turo kofar falon Ammy ta juyo ta kalli kofar, ba yi mamakin sake ganinsa ba, domin haka yake mata naci a duk lokacin da ya zo gidan.

"Jajirtacen namiji, gwani na gwanaye, mai isa da tinkaho da burinkasa da sarautar gidansu, mai son farinciki ubansa fiye da na uwarsa, mai martaba auren ubansa ya watsar da na uwarsa"

Ya zube kasa yana taba kafarta damuwar dake fuskarsa kadan ya rage ta saka shi birgima, domin ya san ma'anar kirarin da Ammy take masa. Ammy ta matsar da kafarta daga hannayensa.

"Da haka kake da na ci da jajircewa a baya, da yanzu Aisha tana nan tare da mu, bata gudu ba"

Kansa a kasa ya soma magana cikin magiya tare da fatan zata amsa rokonsa.

"Ammy na dawo nan ne saboda na tambaya, a dan zaman da Aisha ta yi a gidan nan ta taba fada miki suna da kuma unguwar da gidan marayun da ta zauna a Lagos yake? Zan tafi Lagos din na bincika ko Allah zai saka a dace"

Har Ammy ta yi shiru sai kuma ta kalleshi.

"Eh ina zuwa"

Ta mike tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta, wani sanyi ya ji ya sauka a zuciya jin cewar kamar ya kusan samun hanyar da zata sadashi da Aisha. Babu jimawa Ammy ta sauko tana kallonsa idauwanta a kankance irin bacin rai, sai da ta zauna sannan ta mika masa takardar dake hannunta.

"A lokacin da ta shigo ta dauki danta ba tare da na sani ba, ta bar min wannan akwai address dinta a ciki"

Turhan ya karba da sauri ya warware takardar da kana ganinta kasan ta jima a ajeye.

_Kin ce danki ya sha babban da sauran, wata kila dai baki fahimci danki ba ne, wata kila kin hada aurena da shi ne saboda kina neman mafitar yadda zai dawo gareki, amman duk halinsu daya, shi ma be san daraja ta ba, na fada miki musulmai ba su da kirki kika karyata ni, akan abun da yake zahirinsa, musulmai basa kaunar tubabben basa son kowa sai wanda ya tashi dan asalin dan musulmi, ba su da mu'alama mai kyau, basu san darajar kowa ba sai junansu, abun da kuke aikatawa dabam karantarwarku dabam, shi ma ďan da kike cika baki da shi ya wulakanta ni kamar wancan, duk akan me? Addininku? To na bar muku, zan koma a gurin da nake da daraja"

Tun gabani ya gama karanta wasikar zuciyarsa ta tsinke hawaye suka taru a idanuwansa har suka sauko a fuskarsa.

"Saboda kai Aisha ta ji cewar bata da gata a gurin Musulmi, ka karyata duk wani abu da na yi amfani da shi na karfafa guiwar yarinyar nan, kuma ka saka ta ji cewar na yaudareta, ba ni da wani addireshinta bayan wannan"

Turhan ya daga kansa ya kalli Ammy, ganin hawaye a fuskarta, ya saka shi cikin tashi.

"Zan nemo ta Ammy, zan nemo ta ko da hakan yana nufin na yawace duniyar nan, zan samo ta ko da hakan yana nufin rasa rayuwata ne, zan kawo miki Ammy wannan alkawarina ne"

Ya mike tsaye ya share nasa hawayen ya fice daga dakin rike da takardar.

_________________________

Wai me Turhan ya aikatawa Aisha ne? Me yasa Ammy ta gagara shiryawa da shi?

Anya kuna ganin Emily zata jure aiki a karkashin Amal kuwa? Bayan kuma Amal bata son kafirai, Emily kuma bata kaunar musulmai?

[4/20, 9:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

3️⃣

Teburin dake office din ta nufa ta dora file din da Amal ta bata, tana karewa karamin office din da be karasa girman na amal ba kallo. Sannan ta nufi windows ta bude tana kallon kasa, iska mai dadi na shigowa office din. Ta dade tsaye a haka sannan ta matsa baya ta rufe, ta nufi gurin da durowar office din take ta fara budewa tana dubawa, kusurwar farko an rabata biyu ne da wani katako tsakiya, daga sama an dor Kur'ane daga kasan kuma Bible, doka ce ta sabon CEO na yanzu, aje Qur'ane mai fassarar turancin, da Bible a kowane office a kokarinsa na son tallata addininsa, ta dayan bangaren kuma gudun complain ya saka yake aje Bible din domin baya kowa hakkinsa, sai idan baka bujata sai ka yi magana a dauke. Risinawa ta yi ta rage tsawonta ta taba Bible din da hannunta na dama. Wani bangare na maganar da Momy ta yi mata ya dawo mata sabo a yanzu.

_Emily karki bari yaron nan ya yaudareki, kar kyaunsa ya ja ki ga halaka, domin bayan kyaun ban ga wani abu da yake da shi ba, mun fi shi arziki a gidan nan, zaki samu miji mai kudi mai komai ba, zan inganta rayuwarki ni da mijina, please karki kunyata mu, abun kunya ne ace kina gidan Pastor kin bar mu kin bi musulmi, karki lalata rayuwarki da kananan shekarunki please Emily, ki rike wannan Bible din ki yi karatu bana son na sake jin maganar yaron nan, kin ji my beautiful Diamond Girl_

Ta dauke hannunta da sauri tana hawaye, ta rufe durowar ta juya ta zauna a gurin ta jingina da ita sai kuma ta fashe da kuka, jikinta na karma kamar wanda ta firgita.

"Hamza ka cuce ni... Ka cuce ni... Ka raba ni da matar da ta rike a matsayin ƴa, kasa na butulcewa macen da suka rike ni da amana"

Ta girgiza kai.. Ta dayan bangaren ba laifinsa take gani ba, laifin zuciyarta ne data barta ta fada soyayya da mutumen da be san darajar addininsa ba balle ita. Wani irin duka ta kai kirjinta tana jin kamar ace zata iya ganin zuciyarta a fili ta yi mata duka. Tuna cewar ba a gida take ba ya saka ta natsu ta sassauta kukan da be gama fita ba, ta hade kanta da guiwa. Ta dauki lokaci tana rarrashin kanta sannan ta mike tsaye ta dauki file din ba tare da sake taba komai ba ta fice daga office din ta rufe kofar da key ta nufi hanyar da zata sadata da elevator.

Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da ita. Har ta isa first floor bata hankara ba sai da kofar ta rabe biyu, ta fita ba tare da ta lura da mutanen da suke tsaye suna kokarin shiga elevator ba. Daya daga cikinsu ya biyo bayanta a sirance har sai da ta yi rabin gate din dake da tsayi sosai.

"Excuse me Miss"

Ta juyo ta yi sai ta yi arba sa wani bakin mutum bayanta yana sanye da yellow t-shirt da black jean.

"Can i help you?"

"Yes"

Ya matsa kusa da ita.

"Kin shigo neman wani abu ne? Ko kina daya daga cikin team din Resrezor?"

"No na fara aiki a nan ne"

"Yaushe?"

"Yau"

"A ina? Wane guri office dinki yake?"

"Four floor hannun hagu office na biyu"

"Nice to meet you, I'm William, ina 5 floor office na hudu"

Ta mika masa hannunta kamar yadda ya mika mata nasa.

"Emily"

"Nice to meet you Emily, kin samu aboki yanzu"

Ta yi murmushi tana kallon sarkar Cross din dake wuyansa hakan sai ya saka ta ji dadi ganin kirista ne dan'uwanta.

"Har kin tashi ne?"

"Eh"

"Okay Bye"

Ta yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya tsaya a gurin yana kallon yadda wandon jikinta ya dame jikinta yayi mata kyau.

"Wow..."

Ya shafa kansa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Ta isa gida da wuri saboda ta samu abun hawa da wuri, sai da ta sallame shi sannan ta kwankwasa kofar gate din. Mai gadin ya bude mata ta shiga tana amsa gaisuwarsa. Tura kofar falon ta yi ta shiga sannan ta rufe ta cire talkamin kafarta ta saka na falon sannan ta karasa ciki. Ganin kwalbar giya aje a tsakiyar center Table din dake falon ya karantar da ita V ya bar gidan cikin bacin rai, domin abu ne da ta sani, idan ransa ya bace giya yake sha ko marijuana.

Da sauri ta jefar da Jakarta da file din hannunta ta nufi dakin da London yake ta bude gabanta na faduwa, ta duba dakin har bandakin baya ciki, hakan ya saka hankalinta ya kwanta domin shan abun maye ko drugs abu ne da bata son yana yi a gaban yaranta, wannan yana daya daga cikin dalilin da ya saka ta zabi raba gida da shi, ta zabi rayuwa ita kadai sai yaranta. Fitowa ta yi ta dawo falon ta dauke kwalbar ta shiga Kitchen ta tsiyaye ragowar barasar dake ciki ta fasa kwalba ta zuba a dustbin sannan ta wanke hannunta ta fito.

A gurin da ta jefar da jakarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, tare da daga kanta tana kallon rufin falon zuwa gurin da katon plasma ta yake. Ta sani ahalin yanzu bata rasa komai ba sai kwanciyar hankali, Vito ya jika da kudin da bata jin akwai wata mace mai tarin dukiya irinta, ita kanta bata san adadin abun da ke account dinta ba, domin kowane sati sai ya saka mata kudi ita da yaranta London da Fadima duk kuwa da kasancewar karamar yarsa Fadima bata son shi, amman be taba kula haka ba saboda yana matukar kaunar mahaufiyarta.

A cikin gidan da take rayuwa gidane da ko wucewa kawai ka yi a gaban gate din sai hankalinka ya tashi saboda kyaunsa, shi kansa nasa gidan be kai nata kyau ba, ya zuba mata kayan more rayuwa daga sutura har abubuwan ado na kawata falo ko daki, ga mayan motoci da ya zuba mata a cikin gidan, ga Nannyn da ya dauka mata mai kula da yaronta, ya saka yarta a makarantar kudi ta yayan manya, London kuma da ya kasance Autism ya biya ake karantar da shi a gida. Bayan kudin da ya biya aka yi mata aiki, ya kaita waje ta yi karatu. Amman duk da haka tana jin ta rasa wani abu a tare da ita, she felt something is missing inside her. Ji take bata cika ba har yanzu, tana jin akwai abun da ta rasa kuma bata san miye wannan ba, sai dai ta san dalili daya da ya saka take son tsayawa sa kafafuwanta, wannan sirri ne da ba zata iya budewa kowa shi ba.

"Good Afternoon Ma"

Cewar Chidimma bayan ta shigo falon. Emily ta kalleta da irin fuskar nan na wanda tunani be gama sakin kansa ba.

"Chidimma, a gaban London V ya sha alcohol dazun?"

"Aa bayan na shiga dakin Landon ne na canja masa tufafi saboda za su fita tare"

Ta sauke numfashi a hankali.

"Okay please duk yadda za'ayi karki bari yarana su ga lokacin da Vito yake shan giya, balle har hannunta ya kai gurin"

"Okay Ma zan kiyaye"

"Ki shirya musu wani abu ni zan yi bachi"

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta dauki jakarta da file din ta haura sama ta shiga dakinta ta aje jakar da file din a kusa da gadonta ta kwanta, tunani ya fara kawo mata ziyara kamin bachi yayi gaba da ita.

ALIYU POV.

Dagowa yayi a hankali ya kalli kofar office din da aka turo. Mutumen ya karaso gaban teburin cike da girmamawa ya bude masa daya daga cikin files din da suke hannunsa.

"Nan zaka saka hannu"

Sai da Aliyu ya gama abun da yake a computersa sannan ya kalli file din ya saka hannu.

"Ranka ya dade cikin sabin ma'aikatan da aka dauka har da turawa?"

Cewar mutumen dake tsaye gabansa, shi dai be ce komai ba, har sai da ya gama saka hannu a duka files din.

"Na ganta zata fita dazun"

Aliyu ya sake dubansa ba dan ya fahimci inda zancensa ya dosa ba.

"Baka ga sabin ma'aikatan na mu ba"

"Ba ni nake da hakkin ganinsu ba, ban san suwaye aka dauka ba"

"Wata baturiya ce fara kyakkyawa har ta fika haske ga blue eyes"

Aliyu ya dan yi jimmm alamar nazari can kuma sai yayi murmushin da ya kara masa kyau.

"Ka ganta kenan?"

"William, na ganta and what?"

"Tana da kyau, ga fari duk yadda aka yi wannan yarinyar baturiya ce ko half cast, na gode da ka dauketa, and finally kirista ce yar'uwata"

"Ka godewa Amal aikinta ne not mine, ni ban san su waye aka dauka aiki ba ma"

Ya aje zaren zancen a daidai lokacin da wayarsa ta ringing. Kallon wayar yayi yana murmushi.

"Shiyasa ake daudararku koda yaushe kyaun kuke bi ba hali ba"

Ya amsa kiran ya kara wayar a kunnensa, at the same time da William yake fadar.

"Ka rantse da Allah ka na musulunci cewar ka taba ganin yarinyar da ta fita kyau? Ni fa rudewa na yi na kasa rike kaina sai da na yi mata magana"

Da sauri Aliyu yayi saurin yi masa alama da hannu na yayi shiru ya yi tafiyarsa. William zip up his mouth yayi ta tafiyarsa.

"Hello yar kyakkyawata"

"Na'am ya aikin?"

"Alhamdullahi ya cikin?"

"Ban sani ba"

Ya saka dariya daman da neman magana ya saka shi tambayarta.

"Miye laifina dan na tambaya?"

"Ni dai ban sani ba, kawai dai na kira na fada maka Gwaggo ta kira tace Anty Sa'ade ta haihu"

"Maa shaa Allahu, me muka samu?"

"Irina ce aka samu"

"Ki ce irinki marar jin magana ko?"

Ya fada yana wani abu da ido kamar tana gabansa.

"Ba zaka daina ba ko?"

"Na daina yar shawalwalar yarinyar yar dirarar yar black beauty na kyakkyawata"

Ta yi dariya.

"Bye sai ka dawo"

"Okay mai ciki"

Yana fada ya kashe wayar da sauri yana dariya, sannan ya aje wayar ya maida hankalinsa gurin aikinsa.

TURHAN POV.

Ya aje mug din tea dake hannunsa.

"Yadda kasan yarinyar nan ta yi ma Ammy magani haka ta juya min baya, gaba daya na kasa gane kan mahaifiyata"

Mannir dake kallonsa ya ce

"Amman dai ka san abun da ka yi mata baka kyauta ba? Baka ji haka ba?"

"Na san ban kyauta ba Manir kuma na ji babu dadi, ina kan jin babu dadin ma a duk lokacin da na tuna, amman yadda Ammy ta hau karamin abu ta maida shi babba shi ke daga min hankali kuma ya ba ni mamaki"

"Iyaye sai hakuri, kuma kasan Ammy ta dora hope sosai akanka game da yarinyar nan, sai kuma gashi ka bata kunya, waya sani ma da ace ita kake aure har yanzu wata kila da yanzu kun haihu, gashi nan wannan yarinyar da ka fifita akanta har yanzu baka baka ďa ko ya ba"

A take yanayin Turhan ya canja duk kuwa da ya san gaskiya aminin nasa yake fada, kuma samu ďa ko ya wani abu da yake fata kuma ya dade yana mafarki.

"Mace bata bawa kanta haihu, duk wanda ka ga ya samu haihuwa hukuncin Allah ba yin kansa ba"

"Haka ne, sai dai kuma wata kila yana cikin dalilin Ammy na yin fushi da kai, kuma yarinyar nan fa abar tausayi ce"

"Na sani, amman Manir ana samun sabani sosai akan abubuwa kuma sai ka samu iyaye sun yafe sun duba dansu, amman ni Ammy ta kawar da idonta a kaina gaba daya"

Manir ya sauke ajiyar zuciya.

"Yanzu ka aje duk wani hange hange da tunanin banza, ta ina zamu fara?"

"Nemanta, zan shirya duk abun da zan yi a yau, gobe zan sauka Lagos zan fara nemanta"

"Wane tabbaci kake da shi cewar tana Lagos?"

"A can aka haife, acan ta taso kuma bata san kowa a nan arewa ba, kamin ta bar nan Ammy ta fada ta ganta a coci, bana tunanin zata iya zama garin nan ma gaba daya, idan har zata zabi zama cikin kista yan'uwanta ba ta da wani gida da ya wuce Lagos, matsalar kawai a Lagos din ban san wane gida take ba"

"Shi ne Matsalar, kuma Ammy bata ffada maka wane gidan Marayu ta zauna ba?"

"Bata fada min ba, amman dai zan yi ta bincike har na gane"

"Baka san kowa a Lagos ba, nemanta ba zai maka sauki ba, gaskiya Ammy ta dauki abun nan da zafi"

Turhan ya busar da iskar bakinsa.

"Zan tuntubi Aliyu yayi zama Lagos kamin ya koma Port Harcourt, maybe zai iya hada ni da wani da zai iya taimaka min mu yi neman tare"

"Oh na manta ma da shi Wallahi, ka yi masa magana mu ji ba zai rasa wanda zai taimaka maka gurin nemanta ba, ni kuma zan yi ta lallaba Ammy a nan ko zamu samu wani abu daga gurinta"

Turhan ya sake daukar Mug din ya sha tea.

"Ta fa yafe min, kawai dai ita wai yadda muke a da ne, ta ki ta dawo min a haka"

"Irin wannan ai sai ya saka ka ji ka tsani yarinyar, ko da yake.."

Manir yayi shiru ba tare da ya karasa ba. Turhan ma be sake ce masa komai ba ya maida dubansa wani gurin sai tunani yake.

EMILY POV.

Jin an taba fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali tana kallon Vito dake zaune gefen gadon kusa da ita. Tashi ta yi zaune tana kallonsa, kallonta yake shi ma irin kallon nan mai cike da kauna, sai dai girman kai da jin isa ya hana shi sakin fuska balle har ta ga murmushinsa.

"Ina London?"

"Yana dakinsa, me yasa baki fita da mota ba?"

"Bana son kowa ya san wani abu akaina, na fada maka wata sabuwar rayuwa nake son yi"

Ta yaye blanket din dake jikinta ta matsa ta saka kan gadon ta dayan gefen, sai yayi hanzarin rikota ya juyo da ita da karfi.

"Fita mota zai hana wani abu daga canjin rayuwar da kike so ne? Mi kike shiryawa ne Emily?"

"Me kake tunanin ina shiryawa? Na sha fada maka ina son na yi rayuwa kamar kowa, ina son rayuwata ta zama daidai, dole ne sai na shiga mota? Bana ra'ayin haka? Me yasa kake cilasta ni yin abubuwan da bana ra'ayi? Why?"

Ya matsa kusa da ita sosai yana kallon cikin idonta.

"Saboda ni kadai na isa na cilasta ki, kuma idan tunaninki ko shirinki na rabuwa da ni ne, to kina shiryawa kanki wani rame ne na halaka, domin ban gane duk wannan abun da kike ba? Me ye ban aje miki ba? Amman tunaninki yana wani gurin dabam, ke tawa ce har abada ba zaki iya guje min ba ki saka wannan a ranki, you're forever mine"

Ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata amman ta kasa.

"You're hurting me..."

Ta yi magana cikin yanayin dake nuna tana daf da fashewa da kuka.

"Mami"

Jin muryar Fadima ya saka shi saurin sakin hannunta domin ko kadan baya cin zafinta a gaban yaranta ko da kuwa me ta yi masa. Emily ta nufi kofar da sauri tana budewa murmushin dole ya ci karfinta a yayinda take kallon Fadime dake kokarin sauke school bag dinta.

"My Baby kin dawo"

Ta karasa kusa da ita ta rika mata jakar, Vito ya fito daga dakin ya karaso kusa da su.

"Lisa"

Readers Also Read