Kenza eBookz

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 26

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 26

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 26: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 26. Duk dogon rattaba zancen da Kameela take Mama…

4,500 words

Duk dogon rattaba zancen da Kameela take Mama Barakat bata ji ko daya ba, gaba daya hankalinta ya tafi gurin kallon hoton Emily kamar mai son tantance wani abu.

"Ya sunanta"

"Emily amman Aisha ake ce mata"

"Tana PH ne tare da shi?"

"Eh yanzu tana PH amman yar Lagos ce a wani gidan marayu ta tashi a can ta girma aka ce, kamin ta auri Turhan din ko a ina suka hadu ma Oho"

Mama Baraka ta hade abu da karfi yanayinta gaba daya ya canja, ta kurawa hoton ido kai kace ranar ta fara ganin mutane.

"Bata fiki da komai ba, hasken fata kawai zata nuna miki, wannan ai bata kai ta kwace miki miji ba, karki daga hankalinki akanta, kuma ita ai ba musulma bace da alama ga Cross a wuyanta"

Tana maganar idonta ya cika da kwalla sai dai bata bar Kameela ta gani ba.

"Eh kafira ce"

"Wata kila ma duk abun da kike zato ba shi ba ne, Aliyu da hankalinsa ai ba zai yarda ya rabi kafira ba, zan yi magana da shi na san zai saurare ki kwantar da hankali"

Ta mika mata wayar.

"Tashi ki koma bangarenku kar ayi zaton wani abun muka shirya ma"

"Tohm"

Ta mike tsaye ta fice daga falon tana jin bakinciki dake zuciyarta yana raguwa saboda shawarar da Mama Barakat ta bata da kuma matakin da tace zata dauka, a yanzu kuma tsoron ta daya kar ya fada mata ko mahaifinta cewar ta saka masa guba a abinci, idan kuma har Ummi taji ta san auren ta da Aliyu ya kare har abada, ta san bata kyauta ba, be kamata ta aikata hakan ba kuma ta yi kuskure, da yanzu ta kashe shi wa gari ya waya? Ai ko mahaifiyarsa ba zata fita jin zafin mutuwarsa ba, haka dai ta yi ta sake sakenta har ta shiga bangarensu ta shige dakinta ta kama hoton Aliyu tana kallo da wasu videos da suka yi a tare tana ta jin kewar mijinta da kuma nadamar abun da ta aikata domin ta fi kowa sanin Aliyu yana sonta, ta san ba dan yana sonta ba wata kila da sakinta zai yi gaba daya ba zai tsaya cewa za a duba kwakwalwarta ba ko ya turata gidansu.

*** *** ***

Mama Barakat ta bi bayan Kameela da kallo har ta fice fuska a raunace, ta yunkura zata tashi kafarta ta hagu ta yi mata nauyi sosai ta gagara daga kafar, zuciyarta ma ta yi nauyi sosai kamar an dora mata dutse.

"Aleeya Aleeya Aleeya... Samira Samira..."

Ta kwalawa yaranta kira Sameera ta sauko da saurinta tana dariya hannunta rike da waya da alama wani abun take kallo a wayar.

"Mama gani zuwa, Aleeya bachi take"

Mama Baraka ta daga kai tana kallonta har ta sauko.

"Rika ni ina son zan shiga dakina na"

Ta fada mata da yaren yarbanci daman da yarenta take magana da yaranta idan su kadai ne a gidan wannan ya saka suke jin yaren sosai. Sameera ta yi hanzarin aje wayarta tana kallon Mama Baraka.

"Mama Lafiya?"

"Kafata ce ta rike, ina son na tashi na kasa"

Sameera ta rika ta cikin karfin hali domin bata iya dagata gaba daya, Mama Baraka mace ce mai jiki, ta mike tsaye daker ta cije baki ta taka dayar kafar dayan kuma ta daga ta, da taimako Sameera suka haura sama suka shiga dakinta Sameera ta dora ta kan gadonta.

"Mama ko asibiti za mu je?"

"Aa zai saki, ai bata taba min haka ba sai yanzu, tafi dakinku zan kwana na huta"

"Okay"

Ta fice daga dakin, Mama Baraka ta kwanta saman gadon ta yi ruf da ciki ta danne zuciyarta take mata nauyi ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. [6/16, 2:18 PM] null: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

Page 3️⃣5️⃣

Ta hade yawun bakinta tana kallon agogon da Aliyu ya bata.

*** ***. ***.

"Matar da na faɗa gidanta neman taimako, har aka ba ni abinci ita ce mahaifiyar Turhan, a lokacin da na bashi shinkafa sai ya dauke numfashi, hankalina ya tashi sosai na yi zaton London ya mutu a wacan lokacin a take na fara girgiza shi ina ihu, matashiyar yarinyar da ta kawo min shimkafar ta fito da sauri tana tambayar lafiya, ya mutu shimkafa na ba shi sai ya dauke numfashi, na shiga uku na mutu ba ni da kowa sai shi. Shi ne abun da nake ta fada ina hargowa, sai ga Hajiyar ta fito tana tambayar me ya faru? Bana iya amsawa sai sambatu nake ina ihu, sai tace a kira direba ta shiga da kanta ta dauko mayafinta ta karbi Yaron ta shiga mota na shiga direban yaja mu zuwa wata babbar asibiti, muka zuwa aka karbi Ibrahim suka bude nasa file suka masa duk abun da ya kamata, likitar data karbe shi mace ce a take ta rufe ni da fada a wane dalili zaki ba shi shimkafa jariri kamar wannan, baki da hankali?

"Ba ni da ruwan nono ne kuma ba ni da wani abun ba shi"

"idan baki da abun bashi sai ki bashi abinci yaushe kika taba ganin an bawa jariri abinci? Haka kika ga ana rainon jarirai"

Na girgiza mata kai ina hawaye.

"Ban san yadda ake ba, ba a taba haihuwa a gabana ba, ba a taba rainon jariri a gabana ba"

Na bata amsa, sai Hajiyar ta dube ni.

"Daga wace duniyar kike?"

"A gidan marayu na taso, ban san duka wadannan abubuwa ba"

Na durkusa kasa ina mata godiya

"Na gode Hajiya na gode"

Sai ta rika ni ta mikar da ni tsaye.

"Sunana Ammy karki damu ki kula dai ko ruwa karki sake ba shi"

"Amman idan be ci komai ba ai zai iya mutuwa ko?"

"Za a kawo abincin da zakiba shi, yanzu zaki zauna ki yi jinyarsa har zuwa lokacin da za su sallame shi, akwai wanda kika sani nan?"

Na girgiza mata kai.

"Ban san kowa ba"

"Labarin yana da tsaye kuma idan na fada miki ba lallai ki yarda ba"

"Zan yarda, saboda na yarda Ubangijina ba zai bari a cutar da ni ba, amman tun da kin ce labarin yana da tsayi ki aje har zuwa lokacin da za mu samu zama"

Na amsa mata da tohm sai ta tafi tare da likitar aka bar ni a gurin, can kuma sai ga likitar ta dawo tace na tafi Ammy tana jirana gurin mota wai zan bita mu koma gida saboda jariri zai zauna a hannunsu ne har ya samu sauki, zuciyata bata gamsu da haka ba dan haka na ki yarda saboda ina tunanin kamar sace min yaro suke son yi, ganin haka ya saka dole aka bar ni a asibiti, Ammy tasa aka kawo min abun shimfida da abinci, aka kawo madara ta jarirai ana bawa yaron, kullum za a kawo min abinci, amman bana iya ci saboda hankalina yana gurin yarona, aka kwana biyu sai Ammy ta dawo duba ni a lokacin ne take tambayata ko na san yarona yana da wata rashin lafiya nace aa, sai tace min likitoci sun fada mata yarona yana da sickle, ban ma fahimci ciwon ba sai da ta yi min bayanin cewar jinina da jinin mahaifin yaron ne ya zo daya, tace min kar na damu zata dauki nauyin maganin yaron, haka kuwa aka yi naira biyar ban taba kashewa ba a tsawon zaman da na yi na asibiti na wata daya, a tsawon watan da na yi asibitin nono be kawo ba saboda bana iya cin abincin kirki kullum cikin tunanin butulci da Khaleefa yayi min da kuma makomar yarona, ban san ina da hawan jini ba sai a lokacin kuma ashe idan mace ta haihu wanka ake mata da ruwan zafi ko kuma a bata magani ban sani ba hakan ya saka na yi ta kumbura, ina jin akwai canji a jikina amman saboda babu mai kula da ni ban damu da lafiyata ba, har sai da Ammy ta same ni ta tambaye ni ina da wani ciwo ne da yake saka ni kumbura haka domin na zama wata babba uwar mata, nace mata aa sai idan abun ya same ni ban sani ba, sai saka aka bude min file aka bincika ni, a nan aka gane hawan jinin da na samu da cikin dana be sauka ba, kuma ba a gasa min jiki ba shiyasa nake ta wannan ciwon. Ni ma gadon suka ba ni ana kula da ni, a tsawon wata daya da na kara a asibitin Ammy ce take kula da ni ni da dana, ta saka mai aikinta tana jinyata har na samu lafiya amman jiki be sauka ba.

Da aka sallamo ni sai na amince na dawo na gidanta na bar London a asibitin, ta ba ni daki daya a cikin dakunan da suke cikin gidanta kuma suke kusa da dakinta, daman tun ina asibiti ta kawo min tufafi sai ta kara min wasu tace idan ina son abinci na sauka na ci kuma na sake jiki kamar gidana. Na jidadi ta karammani a lokacin ba tare da sanin wacece ni ko daga ina nake fito ba. Kwana biyu da dawowata aka sallamo London sai aka dawo da shi gida, sai ta siya masa tufafi kusan kala goma sha biyu bayan pampers da madara da ta karo ta siya masa gadon yara da tawul, mai aikinta take masa wanka ta goya shi wani lokacin kuma ita da kanta zata dauke shi ya wuni a hannunta.

A haka na kwashe wata uku a gidanta, kuma a tsawon lokacin nan bata taba tambayar labarina ba, bata tana nuna min banbanci ba, idan ta ga ina ja baya gurin shiga lamuran gidan sai ta rufe ni da fada, wai na kasa sakin jiki, ita ta lura da wani bangare na ibada ta daya kamata na gyara sai ta fara koya min a lokacin take tambayar a gidan marayun da nake ba a koya mana ibada ni. A ranar na fayyace mata komai na yadda kaddara ta tsara min rayuwa. Ta yi kuka ta tausaya min kuma ta yi min alkawarin zata zame min uwa, itace ta fara saka ni a makarantar islamiya na fara koyon addini. Sannu a hankali na sake jiki na zama kamar yar gidan, wata rana ina zaune falo ta same ni tace Aisha ina jinki kamar yata daman ina sha'awar ya mace Allah be bani ba, samunki a yanzu ya saka na ji kamar Allah ya maye min gurbinki da wanda ban samu ba ne, fadar hakan da tayi sai ya kara karfafa min guiwa na jidadi, ta fada min yaro daya ta haifa amman baya hannunta matashiyar da na gani a lokacin mai suna Nana rikonta take, yanayin yadda take mu'amalantar danta abun sha'awar ba dan na gani ba sai dan labarin da ta ba ni da kuma yadda take idan ya kirata ko ta kira shi, na fahimci tana matukar kaunarsa ne ta yadda take fada min hallayensa da dabi'unsa, har ta fada min idan ya kan shekara biyu kamin ya zo gurin, amman wnnan karon idan ya zo akwai shirin da ta yi masa, ban fahimci me take nufi ba ashe aurena da shi take son ta hada amman bata fada min ba. Sai dai tana yawan ce min musulmai suna da dadin zama kuma Allah zai min sakamako da miji na gari.

A haka har yarona ya shekara daya ina kula da shi, Ammy kuma tana siya masa magani da madara, sai dai ni kam jiki be sauka ba, duk kuwa da kasancewarsa na samu lafiya sosai ga wadata ta abinci, na zama kamar wata babbar mace fari ya fito jan gashina yayi kyau saboda yana samun gyara a yanzu komai a wadace. Wata rana na yi wanka na shirya cikin shudiyar atamfa wanda ta yi mjn kyau sosai, na fito harabar gidan na zauna ina shan iska, da kuma mamakin yadda har zuwa lokacin Khaleefa ba neme ni ba, ba dan ina da bukatarsa ko wani abu daga gareshi ba sai dan cikin da ya sake ni da shi, da kuma irin halin da ya bar ni, amman be biyo sawuna ba.

Da ace ban hadu da Ammy ba wata kila da ina nan cikin gararin rayuwa amman be damu ba. Be yi tunanin alhakina ba ko na dansa. Ban san ba, ashe ina tunanin hawaye suna saukowa min amman ban jin ba saboda zuciyar ta yi nisa gurin tunani har sai da Ammy ta fito ta zauna kusa da ni tana fadin.

"Me kika tuna? Domin na san kin samu lafiya yanzu ballantana nace ciwo kike ji"

"Bana tunanin komai"

"Ga hawaye a fuskarki Aisha karki cutar da kanki mana, ki dauke ni a matsayin uwa bana son kina boye min komai"

Na kai hannu na taba fuskar sai na ji hawaye.

"Kawai ina tunanin yadda Khaleefa ya juya min baya ne, kuma yadda be waiwaye ni ba har yanzu, be damu ta sanin halin da dansa yake ciki ba"

Sai ta yi murmushi.

"Yarinya ce ke shiyasa baki fahimci rayuwa ba, ai a yanzu ne yake cikin shauki da jindadin yaudara, ba zai neme ki a yanzu ba, sai a lokacin da nemanki ba shi da amfani a gurinsa, kuma ina baki shawarar idan ya dawo miki karki saurareshi ban ce karki yafe masa ba, amman karki yarda ki sake saka kafarki a gurin da aka wulakanta ki aka nuna baki da daraja. Aisha maza na gari suna tsada, ba kowa ne yake iya aure ya rike amana ba, amman ina mai tabbatar miki nan gaba kadan zaki samu samu wanda zai mantar da ke komai zai so ki ke da danki, ni ma na sha wahalar rayuwa a aurena na farko kuma banbanci abun da aka miki da nawa kadan ne, ke kin yi ma arziki an barki da yaron, ni nawa karbe yaron yayi kuma ya hana na shayar da shi, sai da na shekara ashirin kamin na samu ganin dana a ido shi ma kuma sai da na yi fadi tashi shiga nan fita nan, daker na samu haduwa da nada na samu ana barinsa ya zo gurin ko kuma ni na tafi, bayan Turhan ban sake haihuwa ba saboda maganin da aka bani a gidan mahaifinsa, shi ma haihuwarsa ta zo ne kawai saboda Allah ya kaddara akwai da a tsakani, shiyasa a yanzu na maida shi abokin ban kalle ta sigar dan fari ba, komai a gidansu ake masa abinci da nake ci ma daker ya iya koyar cinsa, idan ya zo nan tufafi kalar da nake so yake sakawa, zamu yi wasa da dariya mu yi hira mu yu yawo kamar ni da kane na ba dana ba, matar da ya aura ma daga masarauta aka zaba masa, kuma har yau be taba kawo min ita na ganta ba, sai a waya, shiyasa ni ma na yi masa nawa tanadin na musamman kuma na san zai so ki zaki dace sosai"

Na kalleta da kamar mamaki jin ta ambace zan dace, sai na nuna kaina.

"Ni"

"Eh, ɗana nake yi ma tanadinki, na miki alkawari zai soki zai rike ki amana kuma zai so danki, a yanzu ne zaki san miye aure zaki dace, kuma na san zaki so shi domin shi ma kyakkyawa ne, kusan duk yan mata da nake hada shi da su cemin yake baya sonsu amman ke kam ba zai iya juya miki baya ba, domin kina da kyau kina da haske da gashi kamar matan garinsu, shiyasa nake ta boyonki ina fargabar kar wani yace yana sonki ki karba, kin ga idan ya aure shi zai aje ki a nan dole zai rika zuwa akai akai, kuma ni na zan samu nawa jikokin ta bangarena, idan ba haka ba ina tunani gaban kadan dauke shi zasu yi ba za su bari na zauna da shi ba"

Na sauke ajiyar zuciya ina tambayar kaina to idan kuma ya zo ya ga ban masa ba fa. Kamar tasan abun da nake sakawa sai tace.

"Karki damu da wai ba zai so ki ba, sai so ki ina mai tabbatar miki zai kaunace ki Aisha kamar zai yi hauka, ke kanki zaki yi mamaki yadda zai kula da ke, saboda ni na zaba masa ke da kaina kuma kin sha wahalar rayuwa Allah zai saka miki ta hanyarsa In Shaa Allahu, abun da na cutar da ni a zaman da muka yi da mahaifinsa shi ne shi baya so na, da ace yana so na da ba zan wahala a yadda na wahala ba, amman ke na san Turhan ba zai bari ko yatsa a nuna miki ba, dana yana da kirki sosai yana da tarbiyar kuma yana da addini daidai gwargwado na miki alkawarin Turhan ba zai taba cutar dake ba ba zai taba cin amanarki ba"

Ta yi min campaign ta gyara danta sosai da halin da ta san ba nasa ba ne, ta fada min abun da ba haka yake ba, ta lullube danta da kyawawan halayya alhalin akasin hakan ne a tare da shi. Ni dai ban iya cewa mata komai ba, domin kyautatawa tana biyo kyautatawa ne, ta ina zan iya cewa danta bana kaunarsa macen da bata san ni ba ta rike ni ta kyautata min ni da ɗana, gashi ta yi kuskure bata tambayi ra'ayi akan kudirinta ba, idonta ya rufe akan muradinta da kuma burin da take da shi. Dafa ni ta yi

"Aisha karki damu, na lura da kyakyawan halayen dana, kuma ba zan ce ni din mace ce mai nagarta 100 bisa dari ba amman dai na san na kam kamanta na kan kyautata iya yadda zan iya, ba zan yarda a cutar da wani ina gani ba sai inda karfina ya kare, Wallahi ba zan bari Turhan ya cutar da ke ba na miki alkawari, ke din abar tausayi ce Aisha baki da kowa kuma gani ba ki jidadin aure ba, duk wanda ya ji labarin ki dole ya tausaya miki, wata kila ta dalilinki zan samu aljannata gashi ina jinki kamar yata, ba zan taba bari Turhan ya cutar da ke ba"

Ba zan iya amsa mata da aa ba amman a lokacin na ji a jikina ban shirya sake wani auren ba, idan kuma nace ba zan auri danta ba a ina zan zauna? Zai kula da ni wa zai rike ni ni da ɗana? Ina cikin wannan tunanin muka ji kyallowar Ibraheem ni da ita muka tashi da sauri muka shiga cikin falon na haura sama na dauko shi ihu kawai yake na yi rarrashi na na ba shi madara be saurara, sai ya yanke shawarar na tafi da shi asibiti haka na saka hijab cikin tashin hankali muka tafi asibitin, su yi iya bincikensu sun ba mu test da hotuna kala kala amman ba a gano asalin damuwarsa ba sai da ya shekara biyu cif, suka ce min ɗana Autism ne, ga shi yana fama da sickle, daga lokacin hallayarsa ta sake yau ciwo gobe lafiya baya yarda da kowa sai ni sai kuma Ammy mai aikin Ammy ma daker yake yarda da ita, ko sallama aka yi da karfi sai ya fasa ihu jiki yayi ta rawa ya cige, tun ina jin tsoro har na saba, ɗana ya sha wahala gashi kuma yanzu be rayu ba, kuma be ji sauki ba har ya bar duniya, kuma be ga ubansa ba"

Ya rufe baki tana kuka.

Aliyu ya mike tsaye ya nufi windows office din ya tsaya tana kallon harabar ma'aikatar, sai a yanzu na fahimci dalilin Ammy na juyawa Turhan baya, ta ki ta fahimce shi ta saurare shi. Ya sake juyowa ya kalli Emily dake ta kuka, dawowa yayi gurin teburin ya zari tissue ya mika mata ta karba tana shaye hawayenta.

"Ba zan ce na fi sauran ba, amman dai na miki alkawari daga yanzu wani ba zai sake cutar da ke ba, sannan ina son na ja kunnenki akan Tasmia karki sake yarda da ita, abu na karshe da zan fada miki shi na har yanzu Ammy tana sonki, mace ce mai kirki kawai danta ne ya tsaba alkawari, saboda wannan ta juyawa Turhan baya, wannan dalilin ya saka yake nemanki, yanzu haka ya fada min bata da lafiya kuma yana tunanin kamar har da tunaninki ya saka ta ciwo"

Ta kalle shi tana hawaye.

"Asha ma ba nadama yayi ba, ashe ma..."

Ta kasa karasa.

"Dan Allah Aliyu ka yi min alkawari ba zaka taba fada masa inda nake ba"

Ya kalleta sai yayi shiru na dakiku kamin ya amsa mata.

"Na yi, ba zan taba bari Turhan ya san inda kike ba ta dalilina sai idan ke kika yi ra'ayi, you have my words"

Ta daga masa kai alamar gamsuwa.

"Mu je na kai ki gida"

"Zan iya tuki na zo da mota"

"No i want to take you home safely"

"Amman za a iya cewa ranar mun shiga mota daya, kuma yanzu a sake ganin mun shiga"

Ya rumgume hannayensa.

"A duk lokacin da zan aikata wani abu uku nake dubawa kuma nake jin nauyi, Ubangijina, mahaifaina, matata, Ubangijina ya san ba ni da wata mummunar manufa akanki, sai kyakkyawa, Matata ta san da ke, iyayena ne suka rage su kuma na san ba su da matsala, the rest can go to hell, let's go"

Ya fara takawa ya isa kofar ya bude ya juyo ya kalleta sai ya samu shi take kallo.

"Aliyu yana da banbanci da sauran ki saka wannan a zuciyarki, you can trust me"

Ta mike tsaye ta isa kofar ta fito sai ya janyo kofar a daidai lokacin da Amal ta fito office dinta, dan tsaye ta yi da farko irin na mutum da mamakin ganin sabon abu ya rufe shi, Aliyu yayi kamar be ganta ya jera da Emily suka wuce, a tare suka sauka kasa suka isa har gurin motarsa ta bude ta shiga, shi ma ya shiga.

"Amman lokacin tashi aikin be yi ba"

Yana yi ma motar key ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba.

"You need to rest, labarin zaki karasa min wani lokacin, don't stress yourself"

Ya tashi motar suka kama hanya, sai ta maida dubanta gurin agogon da ya bata tana ta murza agogo a hankali. Kallo mace ya wuce sau biyu zuwa uku haramun ne a gurinsa amman Emily ya kasa dauke idonsa a kanta, musamman a yau da tausayinta ya zame masa nauyi, tukin kawai yake amman idonsa da hankali yana gurinta har ya isa gidanta, ya faka a wajen gate din gidan yana kallonta.

"Aliyu..."

Ta kirashi da muryarta kasa kasa. Ya amsa mata yana kallonta zuciyarsa cike da tausayinta.

"Ka taba marmarin abun da baka taba samu ba?"

Ta tambaya har lokacin bata kalleshi ba.

"A'a"

Ya amsa mata bayan few seconds.

"Me kike marmari?"

Ta kalleshi tana kuka.

"Iyayena, ni uwa amman ni ma ina neman tawa uwar ina jin kewarta duk da ban taba kasancewa da ita ba, me yasa suka jefar da ni, me na yi musu? Miyasa gashin kaina yake yake da idanuwa na, ni yar asalin wace kabila ce, wa na biyo mahaifina na ko mahaifiya? Minene asalin sunana? Su waye yan'uwana? Duk ba ni da amsar ko daya"

Ya busar da iskar bakinsa.

"Emily kuka kike son na miki ne?"

Ta girgiza kai.

"Toh dan Allah ki yi daina kukan nan haka, kin cika zuciyata fal da tausayinki, a yanzu kuma bana son ganin damuwarki, ban wanzu a wacan duniyar da kika sha wahalar rayuwa ba, amman ina ta dorawa kaina laifi miyasa ban san ki tun a farko ba? Wata kila duk wannan wahalar da baki shata ba, iyayenki kuma wata kila ma sace ki aka yi aka kai a gurin ba tare da sanin iyayenki ba, domin alama suna nuna ke ruwa biyu ce, amman ki daina kukan kin ji?"

Yana mata maganar cikin sanyin murya da rarrashi. Ta share hawaye.

"Good Girl"

Ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito.

"Na san Fatima bata nan yanzu, amman anjima idan ta dawo school ta huta ni ma na tashi aiki zan zo na dauke ta mu je yawo"

Ta bata fuska kamar zata fashe masa da kuka.

"Aliyu dan Allah...."

Be bari ta karasa ba ya tare numfashi ta.

"No no no noooooo Emily ba abun da kike tunani ba ne, ina son na dandana mata dadin uba ne, tun da kin nuna mata na uwa, kuma kin wahala da yawa ya kamata ki huta, wani ya dauki responsibility, you're not alone we're Family"

Kallonsa kawai take.

"Kin min izini?"

Ta daga mishi kai.

"Thank You, ki yi hakuri da fadan da muka yi dazu ki yafe min"

Ta yi murmushi, shi ma murmushin yayi tana tsaye yana kallonta har ta shige ciki, sannan ya koma motar ya koma gurin aikinsa. Yana shiga office abu na farko da ya fara yi shi ne kiran Ammy ya gaishe ta kuma yayi mata ya jiki domin tabbatarwa idan da gaske bata da lafiyar ko kuma fadar Turhan ne kawai.

"Alhamdulillah"

"Ammy me ke damunki?"

"Sun ce hawan jini ne da ciwon suga, amman dai Alhamdulillah sauki yana samuwa"

"Kina gida ne ko asibiti"

"Ina asibiti"

"Allah ya kara sauki, In Shaa Allahu zan shigo na dubaki"

"Aa karka damu, ba sai ka wahalar da kanka ba ina tunanin da na kara samu sauki kadan za su sallame ni"

"Allah ya kara sauki, amman dai zan shigo In Shaa Allahu"

Daga haka yayi mata sallama, after like one hour, kira ya shigo wayarsa da bakuwar number sai da ya kai karshen typing din da yake sannan ya amsa wayar.

"Assalamu Alaikum"

"Wa'alaikumussalam, Aliyu kana lafiya?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah"

"Baka gane mai magana ba ko? Mama Baraka ce"

Ya dan yi shiru kamin ya amsa.

"Maa Shaa Allahu Mama ya gida fatan kowa lafiya"

"Alhamdulillah, Aliyu idan ka samu lokaci ina son mu yi magana ka kira ni, nasan yanzu kana kan aiki ne ko?"

"Eh gaskiya ina gurin aiki"

"Toh idan ka koma gida ko zuwa dare ne sai mu yi magana"

"Lafiya dai ko?"

"Lafiya amman ba kalau ba, akan matarka ne bata fada mana abun da ya hada ku ba, kai kuma baka biyo sawunta ba, ta zo mana nan duk ta rikice ta zama abar tausayi, sai dai ka samu lokaci za mu yi magana"

"Okay Mama"

Ya sauke wayar ya cigaba da aikinsa. Sai 4pm ya tashi aikin a hanya yayi sallah la'asar ya isa gida ya dafa ma kansa indomie ya ci sannan yayi wanka ya shirya cikin wani voile lace na maza black color mai kyau, ya saka bakar hulla ya sha turare da bakaken talkama kamar wanda za shi zance, ya cika aljihunsw da sabbin kudi sannan ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanya sai gidan Emily, da ya isa unguwar be karasa gidan kai tsaye ba gudun kar ya janyo mata matsala, sai ya faka gida uku kamin nata, sannan ya kirata a waya.

Readers Also Read